Showing 258001 words to 261000 words out of 321711 words

Chapter 87 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

da sauri, Maimoon ce ta shigo dakin da sallama ya ci kwalliya tayi daurin ture kaga
tsiya, rike ha6a tayi tana kallon Jiddah tace "Shine ko kira babu Jiddah, kika sa muka raka ki mota muna
matsar kwalla, amma yau sati daya mun ji ki shiru a dakin ki" Jiddah tayi murmushi bata dai ce komai ba
amma har ranta tayi farin cikin xuwan Maimoon, tayi missing dinta sosai sosai, Maimoon ta karaso cikin
dakin tace "Ni da na damu dake ai gashi na biyoki, kuma kar ki ce min sai yanxu kika tashi bacci? Aa gaskiya
wnn dai ba yi bane, ko irin er kwalliyan nan da amare ke yi da safe babu kin wani xumbula doguwar riga
kina xaune gefen gado?" On a serious note Maimoon tayi maganan, cikin sanyin murya Jiddah tace "Umma
fa??" Maimoon tace "Umma tana gida, ita ma ai kin manta da ita daga tarewa, gobe sati daya amma ko
kira daga ke har yayan" a hankali Jiddah tace "Ban manta da ita ba, ai bani da waya ne" Maimoon tace
"Toh baxa ki amshi wayarsa ki kirata ba" Jiddah dai tayi shiru tana kallon Maimoon, Maimoon tayi kasa da
murya tace "Ke na ji gidan shiru, ina yar dabar gidan take, ko ta bar maki gidan ne ta kasa xama?" Jiddah ta
wani harareta, Dariya Maimoon tayi tace "Ke Allah kuwa kamar ke kadai ce a gidan, naji shiru, shi dama
yaya ban ga motarsa ba a parking space" Jiddah ta sunkuyar da kai tace "Kika san ko tare suka fita?"
Maimoon ta hade rai tace "Tare suka fita xuwa ina? Har yanxu fa satin ki daya bai cika ba, sai gobe xai cika,
to sai kika yi shiru kika barsu suka fita tare" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, amma haka kawai taji
abinda Maimoon ta fada ya tsaya mata a rai, tunda gashi baya nan kenan assumption dinta dai dai ne, fita
yayi tare da Aneesah ita kuma ya bar ta nan tana wahala, Maimoon ta mike da sauri tace "Auu tare fa
muke da kawayena suna parlor, ki taso mu je ku gaisa yan Islamiyyan mu ne" Jiddah ta kasa ce mata komai
amma tasan baxata iya tashin ba, kafin Maimoon ta sake cewa komai tace "Ki ce su shigo nan, kaina ciwo
yake baxan iya fita ba..." Maimoon tace "Ciwon kai kuma? Toh kin sha magani?" A hankali Jiddah tace "Na
sha" Maimoon tace "Kina ciwon kan suka sa kai suka yi fitarsu?? Lallai, dama Umma tace idan na xo in sa
ido ko da akwai wata matsala" Shiru Jiddah tayi, gaba daya taji ranta babu dadi, kawai imagine take da
gasken sun fita ne da Aneesah, Maimoon tace "Tabdi..." Daga haka ta fita daga dakin, Jiddah ta wani hade
rai don ba karamin tasiri xancen Maimoon yayi a xuciyarta ba, Maimoon na fitowa daga dakin Jiddah ta
hangi Aneesah tana sauka downstairs ita ma dai da doguwar rigar kamar sannan ta tashi bacci, wani kallo
ta bi ta da shi, Aneesah na fitowa parlor ta dinga kallon yan mata biyun dake xaune saman kujera a parlon,
maimakon ta tsaya amsa gaisuwarsu, a takaice tace "Daga ina?? Wa ku ke nema?" Muryar Maimoon taji
daga sama tace "Wajen matar gidan muka xo" Aneesah ta juya da sauri tana kallonta, Maimoon ta karasa
sauka kasa tace "Jamila ku taso ku hauro sama ku gaisa, tana daki" Nan da nan Aneesah ta ji ta nemi ciwon
kai da xaxxabin da ya rufeta tun sanyin safiya ta rasa, wani kwari ya xo mata, tana kallon kawayen
Maimoon da kyau cikin daga murya tace "Toh idan nan din gidan ubanku ne sai ku haura saman in gani!!!"
Duk suka yi turus suka tsaya, Cike da tsiwa da fitsara Maimoon na kakkanne ido tace "Toh ai kema naga ba
gidan ubanki bane da xa ki ce baxa a hau sama ba, kuma sannan ba wajenki muka xo ba" Aneesah ta wani
xaro ido ta nufeta da sauri tana huci tace "Ubana kika xaga?? Uba na??" Maimoon ta jefar da jakan
hannunta ta cire mayafinta ta daura a kugu tana gyara ture kaga tsiyan kanta tace "Ohh ashe babu dadi,
ance maki uba ya fi uba ne??" Jamila ce tayi kan Maimoon da sauri ta janyeta daga wajen kafin Aneesah ta
cakumota, Hankali tashe Jamila tace "Kinga ki xo mu wuce Maimoon mu ba abinda ya kawo mu ba kenan
wllh, don Allah mu wuce kawai" Maimoon tayi wani shewa tace "Inje ina?? Wllh ina nan, ki bar ta ta ta6a
ni idan ta sha codin ne, wllh xata ga yanda ake kasa kasa da d'an mutum yau, ko ance mata nan din gidan
babanta ne da xata hanamu shigowa? Gidan yayana ne fa kuma wajen yar uwata na xo don haka gomanta
basu isa su hanani xuwa gidan nan ba wllh wllh" Aneesah tayi wani kukan kura tayi kan Maimoon tana
kunduma mata xagi ta uwa ta uba amma tuni Jamila da Farida suka shiga tsakaninsu suna ba Aneesar
hakuri, Kamar mahaukaciya Aneesah ta nufi kitchen a guje, Jamila ta dinga jan Maimoon su fita Maimoon
taki fita ita ma tana kunduma ma Aneesah xagi, amma me? tana ganin Aneesah da tabaryan karfe da wuka
daga ita har su Jamila suka haura sama a guje hakan kuma bai hana Maimoon dinga xaginta ta uwa ta uba
ba, suka shige dakin Jiddah da gudu suka sa makulli, Jiddah dai sai kallonsu take don tana jin hayaniyar
amma ta kasa tashi, gashi duk hankalinta ya tashi, da damuwa tace "Me yasa xa ki kulata Maimoon? Me
yasa don Allah" a fusace Maimoon tace "Na kulata din, ita uwa ta ce da xan ji tsoronta inki kulata, ni baki
ganta ba ma wllh naga duk ta rame ta yamushe sai kwala kwalan ido da kashin wuya kamar xa a jera
duwatsu, kinga da gaske dai ta fara samun sleepless night a gidan ba a sani ba, to wllh bari yaya ya dawo
duk inda ya tafi yayi min iyaka da ita don bata isa ta hanani xuwa gidan nan ba, kai ko shi ma bai isa ba
balle ita, kullum idan muka tashi Islamiyya idan na ga dama sai na leko na ganki Babu wanda ya isa ya
hanani" Daga Jamila har Farida kallon Maimoon kawai suke dukkansu a tsorace suke da Aneesah, Jiddah ta
sauke wani ajiyar xuciya tana kallonsu tace "Sannun ku da xuwa Farida" Jamila tace "Hmm sannu Jiddah,
mu dai da mun san haka xai faru da bamu fara xuwa ba wllh, Allah ya gani ba tashin hankali ya kawo mu
ba, Maimoon da baki biyeta ba wllh" Jiddah dai tayi shiru, Maimoon tace "Lallai tunda ina tsoronta ai dole
in ki biyeta... Ai da nasan haka xai faru yau da Rumasa'u xa mu xo gidan nan ayi duk bala'in da xa ayi, ayi
fashe fashen kai" Bude gate din gidan suka ji anyi, Maimoon ta nufi window da sauri, har sannan tana huci
tana kallon motar da xai shigo, wata sabuwar mota dal ash color sai wani talli yake ne ya shigo compound
din, Maimoon ta wara ido a hankali tace "Waooww motar waye wannan, yaya ya canxa mota ne?" Jiddah
dai sai kallon Maimoon take amma babu daman ta tashi taga motar, Maimoon ta dinga kallon wanda xai
sauka daga motar ta ga Abuturrab, ta rufe bakinta tace "Lahh wllh yaya ne, ya canxa mota, waow latest
ride wllh, wannan shi ake kira da ride" Jamila da Farida dai suna xaune kan kujeran da suka xauna a dakin,
Maimoon tace "Ta so ki gani Jiddah wllh sabuwar mota ce..." Jiddah na ganin Maimoon xata dagata ta ga
motar da sauri tace "Noo Maimoon am not feeling fine ina jin jiri" Kyaleta Maimoon tayi sai yaba kyan
motar da yayi mugun tafiya da ita take, haka ta sa sai da su Farida suka taso suka ga motar ta window su
ma suka ya6a sosai, Lkci daya Maimoon ta dawo sense dinta ta kalli Jiddah tana xare ido da sauri tace
"Yaya nan xai shigo?" Jiddah bata kai ga ce mata komai ba suka ji an murda kofar dakin, Maimoon ta nufi
kofar da sauri ta shiga bude makullin, tana budewa tace "Yaya sannu da xuwa" Daga sama har kasa yake
kallonta kafin yace komai ya ga su Farida a xaune, gaishesa suka yi gaba daya kansu a kasa, ya amsa masu
da murmushi fuskarsa yace "Yauwa sannunku da xuwa" Maimoon ta marairaice tace "Yaya in gaya maka
wllh Aunty Aneesah hana mu xama tayi a parlor..." Da mamaki yace "Saboda me?" Tace "Wai ba gidan
ubanmu bane, sai kaga abinda ta mana yaya, gashi da bak'i yan makarantan mu na taho duk ta bani kunya,
ta xageni ta xagesu, ni dai ban kulata ba yaya, muna dai xaune parlon still sai ga ta da ta6arya da adda daga
kitchen shine fa muka hauro sama da gudu muka shigo nan muka kulle kofa, Banda haka da Allah kadai
yasan abinda xata aikata mana yau, ni dai ban kulata ba" Kallonta kawai yake boiling from inside, can ya
kalli su farida yace "Ku yi hakuri don Allah" Duk suka ce ba komai wllh, Ya ajiye ledan hannunsa gaban
mirror, ya kalli Maimoon yace "Kun ci abinci??" Maimoon ta rufe bakinta tace "Ina fa yaya?? Ko ruwa bamu
sha ba tana neman rotsa mana kai da tabarya da adda balle abinci" Yace "Mu je ki daura maku abinci" Tayi
wani murmushi tace "Toh yaya" Tana biye da shi suka sauko downstairs, su Farida ma duk suka fito daga
dakin wanda su basu ki su yi wucewarsu gida a lkcn ba, Aneesah na xaune parlor har lkcn, Maimoon ta fara
wani cartwork tana jujjuya ido tana biye da Abuturrab, shi kam ko kallon Aneesah bai yi ba ya nufi kitchen
Maimoon na wani smiling ta yi ma kawayenta alamar su biyota kitchen din, da yake duk sun sha jinin
jikinsu da Aneesah haka suka nufi kitchen din gaba daya, Aneesah ta bi su da kallo xuciyarta na suya taji
kamar ta kwala ihu ko xata samu saukin abinda take ji a xuciya, is this really happening to her?? Yau ita ce
ke witnessing wannan abubuwan, ko a mafarki bata ta6a xaton haka ba, bata ta6a xaton akwai daren da
xai xo ta gansa yanda ta ga rana ba, a da idan taji wani na cewa bai yi bacci ba throughout dare ta xata
karya ne, sai gashi yau hakan ya faru a kanta, don ko rintsawa bata yi ba, bata yarda tayi kukan dake cinta
ba xuciyarta na mata xugu, ta wani dake tana huci daga xaunen da take, Sai da Abuturrab ya nuna ma su
Maimoon foodstuffs din kitchen din sannan ya juya ya fita, yana kallon Aneesah da kyau ya nufeta yace "I
think i told u the other day, i think i warned u cewar only my relatives are allowed into this house, and i am
giving u this last warning today Aneesah, ko kallon banxa kar ki sake yi ma wani jinina idan ya xo gidan nan,
that is idan har kina son ci gaba da xama da ni..." Mikewa tayi tana iya kokarin ganin bata fashe da kuka ba
tana wani vibrate tace "Do ur worst Aliyu!! Wannan sabon threat din da ka tsira yi min na miye? Abu
kadan kace idan ina son xama da kai, ka fito ka gaya min abinda ke ranka game da ni mana, ka fito ka fada
nace, na gaji da walakancin ka, na gaji da walakancin da kake min, don ban gane ma'anar idan ina son ci
gaba da xama da kai ba, a kan wata yar iska can kanwar bayana xaka tsaya kana gaggaya min wannan
magana Aliyu, duk ka sa kanninka sun raina ni, to wllh wllh hakurina ya kare, bayan kauda kai da nake ta yi
ina tausan kai na akan auren cin amanar da kayi sai an kara min da wani xafin" Abuturrab ya mata wani
kallo yace "Idan har a tunaninki ina threatening dinki to ki dau matakin da kika ga ya dace, find a way out
for ur self idan kin gaji da walakanci na kuma hakurin ki ya kare da ni, ki dau action din da ya dace and stop
barking" yana fadin haka ya nufi stairs ya bar ta nan tsaye, ta sulale saman kujera ta rike kanta tana dannar
xuciyarta kar ta fashe da kuka sbda su Maimoon dake kitchen, wai yau ita Captain ke mata wannan
abubuwan, yau ita Captain ke gasa ma magana anyhow har da ce mata she is barking?? mutumin da a
baya ko ci kanki baya ce mata komai tayi masa sai dai yayi overlooking baya tanka ta, what is happening to
her!! Abuturrab na haurawa sama ya bude kofar dakin Jiddah suna hada ido ta sunkuyar da kanta, ya isa
gabanta ya durkusa yana kallonta, ita dai ta ki yarda su hada ido, ya kamo hannunta yace "How are feeling
now?" Bata ce masa komai ba, yace "Kina jin yunwa ko?" Still tayi shiru, yace "Ohk u need to sit bath first
before eating" Daga haka ya mike ya cire agogon wrist dinsa ya ajiye kan bedside drawer ya nufi bathroom
ta bi sa da kallo, bayan ya hada ruwan xafi a bathing tub ya fito, ya bude ledan drugs dinta ya dau iodized
salt ya koma bandakin, yana fitowa ya ajiye ledan sauran yana kallonta yace "Should i?" Sai a sannan ta
kallesa kamar xata yi kuka tace "Ni wllh bana so, i am okay" Bai tsaya ya saurareta ba yayi leading dinta
with his help xuwa bandakin. Abinda tayi masa da safe shi din dai ta kara maimaitawa yanxu ma, ga uban
shagwaba da ita ma bata san tana yi ba, shi kam hakan narkar masa da xuciya yake, ya dinga lallabata yana
bata hakuri, da kansa ya ciro mata atamfarta da aka yi ma dinkin doguwar riga, ta shirya bayan yayi mata
duk abinda ya kamata.... har ta gaji da kunyan nasa ta hakura and she felt much relieved now don da kanta
ta maida turarrukan da ya kwaso gaban mirror, sannan ta dawo a hankali ta xauna gefen gadon, ya durkusa
gabanta yace "Tell me, me xaki ci? Nasan baxa ki jira Maimoon ta gama girki ba ko?" Tayi shiru bata ce
komai ba, yace "Talk to me pls wife" A hankali tace "Xan jira ta gama" Yace "Are u sure?" Ta gyada kai
kawai, mikewa yayi ya isa gaban mirror ya dauko ledan da ya ajiye ya dawo ya xauna gefenta ya ciro kwalin
dake cikin ledan ya mika mata yana kallonta, kallon kwalin wayar k'iran samsung ta dinga yi sai kuma ta
kallesa, murmushi ya sakar mata yayi kasa da murya yace "For u" Sauke idonta tayi ta amsa cikin sanyin
murya tace "Nagode Allah ya kara budi" Bata rufe baki ba ya kamo hannunta ya saka mata makulli a palm
dinta sannan ya rufe palm din a hankali yace "For you wife" Bude hannunta tayi tana kallon makullin
motar, sai kuma ta kallesa with surprise, ya gyada mata kai yace "Naki ne" fadawa jikinsa tayi ba tare da ta
shirya ba ta rungumesa ta ma rasa abinda xata ce masa.... Ya lumshe ido a hankali yana jin wani sabon
sonta na fixgarsa, ya kai bakinsa kunnenta underneath his breathe yace "I love you Jidderh, i have always
love you, ban san tausayi na rikidewa ya koma so farat daya ba sai a kanki, i sacrificed a lot because of u
wife, and u changed my mentality toward many things in life, the worst day of my life was the day i was
forced to divorce u, i felt empty Jidderh... I was hurt, i was devastated, amma duk yanda Allah ya tsara abu
dole hakan xai faru, and the most happiest day of my life was yesternight..." A hankali ya ci gaba yace "I am
happy ur pride was mine, and i am appreciating it with a car key, in return i am giving u all my heart, i
mean all...." Hawayenta da yaji na sauka jikinsa ya sa ya dago kanta, a hankali ya dinga goge idon nata,
gaba daya ta kasa ce masa komai, ya mike ya dagata ya dau mayafinta ya mika mata yana rike da hannunta
ya nufi kofa, a hankali take tafiya tana bin sa, har suka sauko downstairs, har sannan Aneesah na xaune
parlor yanda Abuturrab ya bar ta, tun da Jiddah ta hangota suna saukowa stairs bata sake kallonta ba har
suka shigo parlon, shi kansa Abuturrab bai kalleta ba ya nufi kofa still holding onto Jiddah's hand, Aneesah
ta bi su da kallon gefen ido, dai dai nan Maimoon ta fito daga kitchen tare da su Jamila bayan sun daura
girkin, ganin Abuturrab da Jiddah sun fita waje ta lallaba ta bi bayansu ba tare da ta bi ta kan Aneesah ba
ta tsaya window tana lekansu, Abuturrab na rike da Jiddah har xuwa gun sabuwar motar ya kalleta ya wara
ido a hankali yace "Ya maki ko aje a canxa wife?" Rufe bakinta tayi don ta ma kasa ce masa komai, ta bi
compound din da kallo ganin babu mai gadin gidan ta nufesa ta rungumesa tana shessheka, Sai da
Maimoon ta murxa idonta don tabbatar da abinda take gani sannan ta maxa ta fito daga parlon, wani kara
tayi ta nufesu almost running, Jiddah na son sakesa jin muryan Maimoon shi kam ya ki sakinta ya
rungumeta gamm, Maimoon na xaro ido tace "Yaya motar ta ne?" Yana murmushi yace "Yeahhh" Ai da
gudu ta tafi ta gayyatosu Jamila cike da murna kamar ita aka siya ma mota tana cewa "Ku fito, ku fito, wllh
wannan tsaleliyar motar ta Jiddah ce wllh tata ce, ita Yaya ya siya ma ashe..." Gaba dayansu suka fito daga
parlon, Maimoon ta dinga tsalle a bakin kofa tana kallon Aneesah dake kokarin fahimtar abinda Maimoon
ke cewa, Maimoon ya dinga cewa "Wllh na Jiddah ne motar..." Lkci daya Aneesah ta mike, Maimoon na
ganin haka ta bar bakin kofar ta fita tsakar gida don dama so take taga ta tashi, Aneesah ta nufi window da
sauri tana lekan waje taga ubansun motar, ga Abuturrab rungume da Jiddah har sannan....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




MG'S SKINCARE

In kid'a ya chanza rawarma semutaru asauyata,
Wani Kaya se amalende
Haka Wani Hadi na musamman se MG'S,

Ina ma'abota amfanida kayan MG'S SKINCARE?

To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan
gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin,

Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan
Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal👌🏻

Beauty kit:11k
Student package:7k
Soap:3k
Bridal kit 18k

Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA

Chat:08062991549 or 07046881166


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login