Showing 225001 words to 228000 words out of 321711 words

Chapter 76 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

da ita daga gidan tunda en sandan
might likely come back, Safara'u dai sai bin su take da sauri ita ma, yana fitowa daga parlor ya ga en sanda
biyu tsaye gefe da gefen balcony din, Umma kuma na tsaye daga kasa fuskar nan nata a murtuke, a hankali
ya karasa sauka sai ga Aneesah ta fito, tana fitowa en sandan mata suka cafketa, daya dake rike da
handcuff tace "U are under arrest" Xaro ido Aneesah ta dinga yi tana kallon Abuturrab tana bin en sandan
da kallo cikinta ya duri ruwa sosai, Tuni Safara'u ta juya a guje ta koma cikin gidan, haka suka fitar da
Aneesah daga gidan tana cewa "Captain da kai xa a hada baki a kai ni station?? Da kai captain??" Tsawa yar
sandan tayi mata ta rufe ma mutane baki, sannan aka sa ta a mota aka wuce, Umma ko kallon Abuturrab
bata yi ba ta shige motarta tayi reverse ta bi bayan motan en sanda Abuturrab ya bi ta da kallo kawai. Abba
ne ya shigo parlor babu ko sallama yana kallon Ummi dake xaune tare da Hajja a parlon directly, yau kam
Hajja ta bada labarin yanda incident din asibitin ya faru ya fi sau ashirin har da demonstration dinta, gashi
ta ki yarda su tafi gidan Umma duba Jiddan wai ai dole Usman ake jira a je da shi ya gane ma idonsa abinda
Hafsah ta sa Nanisa ta aikata ma Jiddah, don haka a hada hannu har shi a kwato ma Jiddah hakkinta tunda
ba uwa ba uba, Shiru Ummi tayi ta sauke kanta tana sauraron Abba dake gaggaya mata magananganu ido
rufe, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Hajja ta mike ta daka masa wani axababben tsawa tace
"Shet up malam... A gabana kake wannan tijara babu tsoron Allah balle ni??? A gabana kake mata wannan
cin mutuncin Usman??" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Ita Hauwar me ta maka kake jifanta
da wa en nan axababben maganganun ba dadin ji?? Er banxa ka mayar da ita kenan Usman?? A gabana fa
aka yi komai a asibitin nan ba wai labari na tsinta ba, ita Hafsar ce tayi maka duk wannan tsarin? to wllh
wllh yau a gidan nan ko ni ko ita, Allah sai ka xaba ko ni ko Hafsah tunda babu wanda xai kiraka ya giggilla
maka wannan karyan da ya sa ka dawo kake sababi sai ita, wllh idan baka xabi ko ni ko ita ba ka canxa uwa
kawai kafin dare" Abba bai kuma kallon Hajja ba ya wuce bangarensa rai a bace, Hajja ta nemi waje tana
kara rushewa da kuka ta ciro wayarta ta mika ma Nafisah dake xaune kasa gefenta tace "Kira min Kabiru"
Nafisah ta amsa ta kira mata sannan ta mika ma Hajja, Yana dagawa ta sakar masa kuka tace "Duk abinda
kake yi ka barosa don bai fi ni ba, ka biyo jirgi ka taho garin kaduna ta faru ta kare Usman babu xagi da cin
mutuncin da bai min ba yau har korata yayi, ka taho kawai kabiru xuciyata xata fashe" daga haka ta katse
wayar ta mika ma Nafisah tace "Kira min Umaru" Nafisah ta kira mata shi ma Hajja ta sanar masa, duk sai
da ta bi ta kira 'ya yan mijinta gaba dayansu su bar duk abinda suke su taho kaduna Usman ya xageta ya
koreta daga gidansa, Ummi dai na xaune tayi tagumi abun duniya ya dameta, banda radadi da xafi babu
abinda xuciyarta yake mata and she is trying her best to hold back tears, duk wannan abun kuma Aunty na
part dinta tare da er ta Aisha sun bama makulli.... Ko minti goma Abba bai yi da shigewa bangarensa ba
Umma ta shigo gidan, tana shigowa ta kalli Nafisah tana huci tace "Abban naku ya dawo??" Nafisah ta
gyada mata kai kawai, Umma tace "Toh ya fito gani nan na tako da kaina naxo ba sai yaje can gida ya
sameni ba, ya fito ya sa a daureni har karshen igiya kamar yanda yace, gani gidansa ya fito" Hajja ta
marairaice tace "Ya daure ki ko a dauresa??? Huhuhu ai da Masar ne yau xai san ya xagi mahaifiyar da ta
tsugunna ta haifesa don wllh wllh baxai kwana kasar su ba ma, sai sun walakantasa sun masa dukan tsiya"
Umma ta kalli Ummi tace "Ki tashi mu tafi Yaya, ya dade bai dau hukuncin da yace ba wllh, tashi muje babu
shegen da ya isa ya sa maki hypertension, wllh dai dai nake da shi" Hajja ta mike tace "Babu inda xata je
wllh, sai dai shi katon ya fito ya bar mata gidan, sannan in har ya kwana da auren Hafsah a kansa kowa xai
girgixa da lamarina a gidan nan..." Tana huci ta kare maganar, sai kuma ta koma ta xauna tace "Kema koma
ki xauna Ramlah yau kowa ya xuba ido akwai kallo" Nan Hajja ta kuma bi ta doddoka ma duk wa enda ta
kira wani sabon kiran wai ga fa kayanta Usman ya watso bakin kofa.... Umma dai taki xama gidan tayi
wucewarta ranta fess Aneesah xata yi kwanan cell, kuma ta ji dadin yanda Hajja ta tsaya ma Ummi, Ana
idar da Magrib duk wa enda Hajja ta kira suka iso gidan, tana nan xaune ta hakikance a parlor taki
motsawa ko nan da can, sallan ma a parlon tayi, duk suka xauna nan kasa suna gaisheta, ta amsa tana
shessheka, babu yanda basu yi da ita a kan sun shiga parlon Abba ba ta ki, ta kalli Ummi da fitowarta daga
part dinta kenan ta xo yi ma bakin sannu da xuwa tace "Kiyi kiran Aliyu da Ramlah su xo, a gabansu xa ayi
komai" Ummi ta amsa mata da toh, sannan ta dau wayarta ta shiga kiran nasu, Abba ya fito daga
bangarensa ya gaida brothers din nasa, shi dai Abban El-Basheer kallonsa kawai yake, Hajja ta wani dauke
fuska kamar ta ga mugun abu, xaunawa yayi shi ma a parlon, Ummi bayan ta gama kiraye kirayenta ta taho
ta xauna ita ma, Hajja ta kalli Kabiru tayi mici mici da ido tace "Dama ku gaya masa duk inda matarsa
Hafsah take ta fito ta nemi waje ta xauna a nan ita ma" Abba dai bai ce komai ba, sai kuma ya mike ya tafi
bangaren Aunty, ba a dau lkci ba suka fito tana biye da shi a baya, da hijab dinta me jan kasa, ta ki kallon
kowa na parlon fuskar nan nata babu yabo babu fallasa ta nemi waje ta xauna ta gaida yan uwan mijin
nata, duk suka amsa, ko kallon Hajja ita ma bata yi, ba a wani dau lkci ba Umma ta shigo gidan, ganin Aliyu
bai iso ba, Alhaji Kabiru ya bude wajen da addu'a aka sake gaisawa sannan yana kallon Hajja yace "Hajiya
lafiya me ke faruwa, kin kiramu duk hankali a tashi mun taho babu shiri" Hajja ta fashe da kuka tace "Baxan
kiraku ba Kabiru, babu xagi da cin mutuncin da Usman bai min yau ba a gidan nan ni da uwar gidansa uwar
'ya yansa a kan wannan mata dai da ku ke gani Hafsah, kai ni har kayana yace in debe in bar masa gidansa
baya son ganina" Bude baki Aunty tayi tana kallon Hajja, Abba kuwa kansa na kasa yana sauraronta, Hajja
ta fyace majina tace "Don haka na kiraku ku xama shaida, in har Usman ya kwana da auren matar nan
Hafsah to shegiya iyayena suka haifeni, wllh wllh sai ya saketa a gaban kowa ko kuwa ya canxa wata uwar a
kasuwa" Abba ya daga kai yana kallon Hajja da sauri don maganan nata came unexpected, Aunty da ta fara
jin xufa na keto mata ta dinga kallon Hajja xuciyarta na bugawa, Hajja tace "Shkkn na gama wannan babin,
yanxu sai in koma maku babin abinda ya haddasa komai" Nan Hajja ta kwashe duk abinda ya faru a asibiti
tana daga tsaye tana demonstrating har karshe... Tana huci tace "Yanxu duk xan kwasheku mu tafi gidan
Ramlah ku ga yanda yarinyar ta mayar da Jiddan, to kuwa tunda yar daba ce har shi Aliyun wataran sai tayi
masa jina jina ai, ni ko ina xa mu jira wannan ranan, oh oh ba matar xama bace wllh" Hajja ta kalli Ummi
tace "Kema don haka Aliyu ya xo ki tisa shi gaba ya sallami yarinyar ko ya canxa uwa, duk nuna masu xa mu
yi mu en banxa ne" cike da isa Umma tace "Kuma kin manta baki kara masu da cewa na kai ita matar
Aliyun police station ba, yanxu haka tana can a kulle" Hajja ta kalleta da sauri tace "Auuu, kun ji abun
arxiki, kai amma Allah ya maki albarka Ramlah, ka ga mace me kamar maza, yo ai da dani kika tafi gidan
yan sandan in basu bayanin komai da yanda komai ya faru xa su fi daukar abun da muhimmanci" Gaba
daya brothers din Abba kallon Umma kawai suke amma sun ki cewa komai sbda Hajja, Hajja ta koma ta
xauna ta sharce xufar goshinta tace "Ko ni ko Hafsah yau" Aunty dai idan hankalinta yayi dubu ya tashi a
lokacin, Alhaji Lawal ya d'an yi gyaran murya yace "Kina ji na Hajja" Hajja ta jefa masa wani kallo tace "Kai
saurara Malam, ba na kiraku don ku kawo taku shawaran bane, ni fa umarni kawai na bada a nan ba wani
abu ba, nayi kiranku ne don ku taho ku ba d'an uwanku shawaran yayi duk yanda xai yi kada in sakar masa
bakina ya tagayyara, wllh wllh...." Sai kuma ta fashe da kuka sosai tace "Na fi shekara hamsin ban xubda
hawaye ba sai gashi yau wai Usman xai sani inyi ta xubarwa kamar er banxa" Abba ya kalleta a karo na
farko yace "Hajja kiyi hakuri, wannan abun wllh duk bai kai..." Wani tsawa tayi tace "Ya kai, har ya wuce...
Wllh sai ka saketa" Duk aka kasa cewa komai a parlon Umma dai sai kallon tv da aka rage magana har
karshe take bbu ko digon tausayin Aunty a ranta, Aunty taga fa da gaske Hajja take, ta mike ta isa gabanta
ta fashe da kuka ta durkusa ta rike kafarta tace "Don Allah kiyi hakuri Hajja, idan ma wani laifin na maki kiyi
hakuri kar ki kashe min aure...." Hajja ta janye kafarta tace "Kun ga muguwa wai inyi hakuri kar in kashe
mata aure, halinki ne xai kashe maki aure ba ni ba, kuma ai Hauwa ya kamata ki tafi ki kama kafarta ki bata
hakuri kafin ki bar gidan idan kuwa ba haka ba sai hakkinta ya kama ki wllh, wato kin cuceta ainun, kin
shiga tsakaninta da mijinta kin raba su, walakancin da take hadiya ko kurma da bata jin magana baxa ta iya
hadiyewa ba, duk wanda ya kalleta ya san cikin damuwa take babu kwanciyar hankalin xaman aure, hakan
kuma bai isheki ba sai da kika nemo ma d'anta er dabar Habuja kika aura masa neman kashe masa uwar
gidansa Jiddah, don kuwa duk ke kika koya mata abinda xata yi idan ta xo asibitin" Kuka kawai Aunty take
cikin tashin hankali tana cewa "Hajja idan wani abun nayi ayi min hakuri don Allah" Hajja ta mike tana
kallon Abba da kyau tace "Tashi ka dauko takardan da ka adana kake sa wa ayi sake sake ba tsoron Allah"
Abba ya kalleta cikin kwantar da murya yace "Hajja..." Ta dakatar da shi a fusace tace "Wllh kar ka bari
xuciya ta kwasheni in fada maka ba dai dai ba Usmanu" Ummi na son cewa ayi hakuri amma ta rasa ta ya
don bata san yanda Hajja xata dau hakurin nata ba, ita dai duk jikinta yayi sanyi kuma har ranta bata son
Abba yayi wnn sakin, mikewa Abba yayi ya tafi parlonsa, Alhaji Kabir ya mike ya bi bayansa, bayan sun
shiga parlon yace "Hajja baxa ta saurari kowa ba a wannan lokacin Usman gudun matsala da kuma fushin
uwa, ka rubuta ma Hafsah saki daya hakan shine kadai mafita" Abba dai bai ce komai ba ya dau takardan
da biro suka fito parlon, Aunty na ganin takardan da biro ta kara rudewa tace "Usman yanxu sai ka iya saki
na?? Takarda fa ka dauko Usman, yanxu baxa ka bata hakuri ba Usman" Hajja ta mike sai safa da marwa
take fuskar nan nata a murtuke take cewa "Wllh baxan hakura ba kar ma a bani" Abba babu yanda ya iya
haka ya rubuta takardan yana kallon Aunty xai ajiye a gabanta Hajja ta fixge ta kai ma Umma tace "Karanta
min Ramlah" Umma ta amsa tana kallon takardan tace "Na sake ki saki daya" Sai da gaban Ummi ya fadi
sosai ta dinga kallon Abba, Hajja tace "Shkkn haka ya sa?? To uban wa ya saka?" Umma tace "Haka aka sa"
Hajja ta mayar masa tace "Rubuta Hafsah a gaba" Abba ya amsa ya rubuta sannan ya mika mata, kin amsa
tayi tace "Aa bata da hannunka ba ruwana kar ta kai ni gaba tace ai ni na mika mata takardan ma" Abba ya
ajiye ma Aunty takardan yana kallonta, ta dauka tana dubawa, wani murmushi tayi tana gyada kai ta goge
idonta ta kalli Ummi da Umma sannan ta mike fuuu ta wuce bangarenta sunan Jiddah na mata yawo a
kai...., Hajja tace "Sai a tafi a fara harhada kaya kuma a koma benue, Allah ubangiji ya saka ma Hauwa duk
cutarta da kika yi" Mikewa Abba yayi xai bar parlon Hajja tace "Dawo malam" ya dawo kuwa, tana tafe
hannu tana kallonsa da kyau tace "Aliyu kuma da ka sa a baki sai ya saki baiwar Allah har da rantse rantse
to ka cire ido a kansa, rantsuwan da kayi kuma daga gobe ka fara daukan axumi don Aliyu ba shi da matar
kirki da ta wuce Jiddah ita din alkhairinsa ce, yo kayi axumi sittin ma ranan da ka hallaka wani bawan Allah
da mota a hanyar Abuja balle uku kacal? To tun wuri ka fara axuminka bakin ka alekum, ita kuma wannan
mata ta Aliyu Nanisa take ko wa?? ni da Ramlah kadai muka san yanda xa ayi da ita wllh, yanxu ma police
station din xan bi ta mu tafi" tana kai wa nan Abba ya mike ya bar parlon ta bi sa da wani shegen kallo, snn
ta kalli su Alhaji Lawal tace "Duk na sallameku, a nemi me rufe mana taro ku koma garin ku"




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Ina mata ma'abuta gyaran jiki kuzu ga supplement na gyaran jiki kala muna da supplement masu sa haske
da laushin fata da gyaran jiki da maganin sanyi da masu kashe kuraje da tanbo ku Wani kalar supplement
muna da cikin sauki da rahusa kadan Daga cikin su

Lady capsule
Royal jelly
Sugar wanita
Khusus
Vitamin e
Cantik ayyu
Puspa ayyu
Dara
Rapit wanita
Maca capsule
Reload
Papaya
Collagen snail
Flat tummy
Sliming capsule

Da sauran su domin neman Karin bayani atuntube wanna number 08066726866 mmn mujaheed



Umma bata kara ko minti daya a gidan ba ta yi wucewarta gidanta ranta fess, bata ta6a jin Hajja ta burgeta
irin yau ba, tana xaune parlonta bayan ta idar da magrib kenan Ahmad ya shigo tare da Abuturrab, tayi
masu kallo daya ta ci gaba da jan carbinta, Ahmad ya xauna saman carpet yana shafa kansa, Abuturrab ya
xauna saman kujera yana kallonta, Jin duk sun ki cewa komai ta kallesu tace "Wai ya aka yi ku ka xauna min
jigum jigum a gabana? Lafiya" Ahmad ya sauke kansa a hankali yace "Umma don Allah kiyi hakuri ayi
abinda ya kamata, Umma all this...." Umma ta katse sa tace "Inyi hakuri ayi me?" Ahmad yayi shiru,
Abuturrab dai sai kallonta yake, ta girgixa kai tace "Kun ga ku fita harkata wllh, ku fita harkata kar in maku
rashin mutunci, ku kun isa ku gaya min abinda ya kamata inyi?" Sallama aka yi bakin kofa, Ahmad ya juya,
Nafisah ta shigo parlon ta karaso ta xauna ta gaida Umma sannan tace "Umma wai kawu Lawal xa su yi
magana da ke a waje" Umma ta ta6e baki kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Toh sai su shigo"
Nafisah ta mike ta fita, Bayan few minutes Alhaji Lawal da Alhaji Umar suka shigo parlon, xaunawa suka yi
saman kujera Ahmad ya gaishesu, Abuturrab ma ya gaida su ya mike ya tafi bedroom din Ahmad, Ahmad
ya mike ya bi bayansa, Hakuri Alhaji Lawal suka dinga ba Umma tayi hakuri ta janye case din da ta kai
police station na Aneesah, Umma ta saki baki tace "Wato dai ana nufin banxa kawai ta doka kenan?" Alhaji
Umar yace "Aa bata doki banxa ba, amma ta ci darajan masu daraja, sannan shi Aliyun dole xai dau
matakin da ya kamata a kanta, ba ido xa a xuba mata ba...." Umma ta kasa ce masu komai don tana jin
nauyinsu ainun, ita dai ta san da Abba ne bai isa ya sa ta janye case din nan ba, ganin ita suke saurara ta
sauke ajiyar xuciya tace "Toh a gaskiya sai ta xo har gidan nan ta ba Jiddah hakuri, sannan sai ta rubuta
statement a station cewar ko kallon banxa baxai kara hadata da Jiddah ba" Alhaji Umar yace "Ai wannan ko
baki fada ba doka ce, dole yan sanda sai sun sa ta rubuta statement din" Mikewa Umma tayi ta wuce
dakinta ta dauko jaka da wayarta, ta fito ta shiga dakin Ahmad tana kallonsu tace "Ka fito ka wuce da mu
station Aliyu" Ahmad ya kalleta yace "Umma kin manta patient ne shi?" Umma tace "Eh ban manta ba
amma ya taso ya kama gabansa, kai kuma ka xo kayi driving dina" Daga haka ta juya ta fita, Ahmad ya d'an
yi murmushi ya mike ya nufi kofa, Abuturrab ya tashi shi ma ya fita, Su Alhaji Lawal suka fara fita parlon
Umma ma ta fita, Abuturrab dai na tsaye, Ahmad ya gane dakinsu Maimoon yake son shiga, shi dai bai ce
masa komai ba ya nufi kofa, Abuturrab ya shafa kansa yana bin sa da kallo, Har Ahmad ya fita ya juyo da
sauri ya kalli Abuturrab yace "Umma.. she is coming back" Ko rufe baki bai yi ba Abuturrab ya bi sa shi
ma... A motar Umma suka tafi police station din, su Alhaji Umar kuma na tasu motar. Abuturrab ya kulle
kofar parlon bayan ya shigo yana kallon Aneesah da ta wuce sama fuuuu kamar xata tashi sama, Calmly
yace "Hey you, listen to me!!!" Kamar jira take ta dawo da sauri ta nufesa ta cakumo kwalarsa tana xaro
ido tace "Me xaka ce min Aliyu?? Gaya min me xaka ce min?? Nace me xaka ce min??" Sai kuma tayi wani
murmushin takaici tace "Ni kayi ma kishiya, kishiyar ma me tallan awara a hayin rigasa? Ni Aliyu? Hakan
kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login