Showing 36001 words to 39000 words out of 321711 words

Chapter 13 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

yayi ya koma
bathroom ya wanke bakinsa ya fito ya dau pray mat ya shimfida ya hau sannan ya tada sllh, ko da Aunty ta
dawo dakin ganin yana sallah ta koma dakinta, ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike a hankali
ya dauke darduman ya koma kan gado, mayar da ruwan yyi ya kashe wuta ya kwanta ya lullube jikinsa
yana jin kamar wani sabon xaxxabin xai sake rufesa. Da asuba duk yanda Abuturrab ya so tashi yin sllh
kasawa yyi, Karfe shidda da yan mintuna Aunty ta shigo dakin, ta kunna wuta ta karasa gun gadon ta cire
duvet din da ya rufe har kansa da shi, bude ido yyi a hankali, tace "Ka samu kayi sallah kuwa?" Girgixa mata
kai yayi, tace "Da ka daure ka tashi, amma how are you feeling now?" A hankali yace "Alhamdulillah"
mikewa yyi xaune, tace "Let me get u something to take sai ka sha magungunan idan ka idar da sallahn"
Fita tayi dakin, yayi karfin halin tashi ya cire ruwan da ya rage kiris ya kare sannan ya shiga bandaki, yana
sallah ta dawo dakin, ta ajiye masa cup din shayi da ledan drugs din ta nemi waje ta xauna har ya idar da
sallahn sannan ta sa ya dau shayin da ta hada masa ya sha.... Karfe goma na safen Abuturrab na bedroom
dinsa hannunsa rike da bowl din pepper soup, Ummi ce tsaye dakin tana kallonsa, ko minti biyar ba ayi da
fitan family Dr dinsu daga dakin ba, bayan few minutes ya d'an kalli Ummin tasa, ji yayi gabansa ya fadi
sosai, a hankali yace "Why don't u sit Ummi?" Ummi tace "Am okay here" Ba tare da ya kalleta ba yace
"Aunty fa?" Tace "She is in the kitchen" Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din
hannunsa a hankali, Ummi tace "Kun yi magana da Abban naka? Ya kira kana bacci daxu" Ya gyada kai yace
"Ehh Aunty ta bani mun yi waya" Tace "Ohk" Juyawa tayi ta fita dakin ya bi ta da kallo, lkci daya jikinsa yyi
sanyi, ya ajiye bowl din hannunsa ya jingina da gadon da yake xaune, he needs someone to talk to about
this unfavorable issue, he needs to share this with someone that's understandable, who will this be, rike
kansa yayi yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.... Xuwa yamma Abuturrab ya d'an samu saukin
ciwon kan dake damunsa, ya fito wanka kenan yana goge kansa da karamin towel din hannunsa aka bude
kofar dakin, Ahmad ne ya shigo dakin hade da sallama, ganin Abuturrab a tsaye, ya tsaya daga bakin kofar
ya rike waist dinsa yace "This is better, and I'm glad i saw u this way" Abuturrab bai ce masa komai ba,
Ahmad ya d'an yi murmushi yace "Medical report dae ya xama na gaske yanxu kenan" Abuturrab ya kallesa
yace "Ka taho min dashi?" Ahmad ya karasa ya xauna gefen gado yace "How are you feeling now?"
Abuturrab ya nufi gaban mirror a hankali yace "Alhamdulillah" Ahmad yace "But dama baka jin dadi ne,
coz naga sickness din yyi striking dinka so hard, you look lean...." Ta madubi Abuturrab ke kallonsa bai ce
komai ba, Ahmad yace "Ba shiru xaka min ba, i left my work for ur sake na biyo train" Abuturrab yace "Da
baka dawo ba ma ni xan kiraka ka dawo, i have been expecting you" Ahmad yace "Hope you are feeling
much better now?" A hankali Abuturrab yace "Not at all.... We need to talk Ahmad" Keenly Ahmad ke
kallonsa cause he can see how worried and confuse he looks, Mikewa Ahmad yyi ya karasa kusa da shi
yace "Tell me what's wrong Captain?" Kasa ce masa komai Abuturrab yayi, Ahmad ya koma ya xauna yace
"To ka gama shiryawa mu yi magana" Yana kallon Abuturrab har ya gama shiryawa ya dawo ya xauna gefen
gadon shi ma, Ahmad yace "Me ke faruwa tell me" Abuturrab ya shafa kansa a hankali kamar me tunanin
ta inda xai fara, bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo rike da bowl din fruit salad biyu, murmushi tayi
ganin Abuturrab tace "Alhmdlh, son jiki yayi kyau, you are looking much much better and healthier now"
Abuturrab yyi murmushin karfin hali bai dai ce komai ba, ta karasa ta mika masa Bowl daya na fruit salad
din tace "I made this for u" Amsa yayi yace "Thank you Aunty" Kujeran dakin ta xauna tana shan fruit salad
din daya bowl din hannunta tace "Abbanku ma ya kara kira yanxu nace da sauki, shi ma duk ya damu"
Ahmad da ya d'an hade rai yace "Ina yini..." Ba tare da ta kallesa ba tace "Lafiya lau" magana ta ci gaba da
yi da Abuturrab dake shan fruit din hannunsa, Ahmad ya mike yace "Alright Captain, sai ka xo can gidan
namu, i will be leaving now" Abuturrab ya kallesa da sauri, ta gefen ido Aunty ta harari Ahmad tana ci gaba
da shan fruits salad dinta, Abuturrab yace "Ai nace maka nima xan fita Ina son in sha iskan waje" Ahmad
yace "Okay ka sameni mota idan ka gama, i will wait" daga haka yace ma Aunty "Sai anjima" ko tankasa
bata yi ba har ya fita ya kulle kofar dakin, Aunty tace "Yaushe har ka farfado xaka wani fita Abuturrab? Shi
Ahmad din bashi da hankali ne ko don ya xo lkcn da jikinka yayi kyau, kana fama da kanka ina wani fita idan
ba neman magana ba?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Aunty na gaji da xaman gidan ne, ni nace masa mu
fita, ba shi ba" Ta tabe baki tace "Toh ai shkkn...." Bayan kusan minti ashirin Abuturrab ya fita xuwa gun
Ahmad bayan ya sanar ma Ummi xai je gidansu Ahmad din, Sbda yanda idonsa ya fada yasa shi saka bak'in
spec dinsa, kananun kaya ne jikinsa wani sanyayyen kamshi na tashi jikinsa, kana ganinsa kasan he is still
recovering, he still looks weak, Kallonsa kawai Ahmad yake yi har ya karaso ya shiga front seat, Ahmad na
kallonsa da d'an damuwa yace "Wai malaria ne ya kamaka haka Captain, ka rame fa, kamar wanda yayi sati
a kwance" Captain bai ce masa komai ba, Ahmad ya tada motar suka bar layin. Karfe biyar da few minutes
suka isa gidansu Ahmad, Abuturrab yace "Ka bar motar a waje ba dadewa xan yi ba xaka maida ni gida
ynxu" Hakan yasa Ahmad yyi parking a waje, Abuturrab ya bude motar ya sauka ya nufi cikin compound
din, Ahmad ma ya sauka ya rufe motarsa ya bi bayansa, sosai gaban Abuturrab ya fadi bayan ya shiga
compound din sun yi ido hudu da Jiddah dake tsaye ta jingina da bango a bakin tap din dake cikin
compound din ta tara bucket.....

Abuturrab ya dauke idonsa hade da daure fuska yana tafiya, murya can kasa Jiddah tace "Ina yini" Bai kara
kallon inda take ba balle ya tanka ta, tafiyarsa kawai yake kamar bai ji ta ba, Ta kalli Ahmad da ya shigo
compound din shi ma, ta sauke idonta tace "Ina yini?" Murmushi yayi yace "Lafiya lau, sannu da aiki"
Juyawa tayi tana kallon ruwan da take jiran ya cika, Ahmad ya bi bayan Abuturrab da har ya kusa main
entrance din gidan, babu kowa parlon da Ahmad ya shiga sai kamshin girki dake tashi alamar ana girki a
kitchen, bedroom dinsa ya nufa ya tadda Abuturrab a kwance idonsa a lumshe, ya karasa ciki ya kulle kofar
yana kallonsa yace "Are you alright?" A hankali Abuturrab ya bude idon sae dai bai ce komai ba, cike da
karfin hali ya mike xaune looking so dumbfounded, Ahmad ya xauna yana facing dinsa with seriousness
yace "Tell me what is happening Captain, you look disturbed" Abuturrab ya shafa kansa ya lumshe ido
wishing all this nonsense would turn out to be a dream, kara bude ido yyi, gathering much courage yace "I
am in trouble Ahmad" Tuni yanayin Ahmad ya sauya, ya kafe sa da ido, can yace "Tell me what is it, me ya
faru??" Cikin sanyi Abuturrab yace "Yes i will, amma kuma mafita nake nema a wajenka don Allah, and this
should be a secret between just i and you for now plsss" Shi dai Ahmad kallonsa kawai yake waiting to
here what is this that's weighing down his frnd har haka, Abuturrab yayi kasa da murya da kyar ya fara
magna yace "Yarinyar da kake siyan awara wajenta a hayi, u remember her right?" Bude ido Ahmad yyi
sosai yana kallonsa yana jiran jin abinda ya sameta, A hankali Abuturrab ya shiga basa labarin tun daga
xuwansa siya ma Umma awara sanda bata da lafiya, abinda ya faru a ranan, har ixuwa yanxu da suke xaune
tare da Ahmad a daki, Abuturrab ya share xufan goshinsa yana kallon Ahmad da ya bude baki for almost
five minutes now ya kasa rufewa, Abuturrab ya hade rai yace "Don Allah ka daina kallona haka Ahmad ka
bani mafita, find a way out for me, i am stuck, ban ta6a shiga rudani iya rayuwata kamar na wannan
lokacin ba, what have i done to my self daga taimako??" Sae a sannan Ahmad ya kulle bakin da sauri, wato
kawai sae yake ganin labarin da Abuturrab ya basa kamar tatsuniya, or is he dreaming?? Ya kifta ido kusan
sau hudu sannan ya kafe Abuturrab da ido, he is finding it hard to believe all what Abuturrab said now, as if
counting his words yace "Wait Captain... Wllh kamar fa ban fahimce wannan gajeran labarin nan naka ba, i
am confus...." Captain yyi tapping dinsa on a serious note yace "You just have to believe all what i said, duk
abinda na gaya maka hakan yake stop confusing ur self" Ahmad na nunasa da yatsa cikin wani expression
yace "Are you for real Aliyu??" Abuturrab ya kafe sa da ido regretting everything from the start, Ahmad ya
buda ido sosai yana kara digesting din lamarin with shock, he knows Abuturrab have a soft heart, a very
soft heart kuwa, yana damuwa sosai da matsalan da ba tasa ba, he prioritized damuwar wasu kan nasa,
but he never thought ya kai wannan extent din, bai ta6a tunanin Abuturrab can go this deep ba, what is
baffling him more is yanda this time around taimakon nasa yyi sa ga talaka sosai, don Ahmad bai ta6a
ganin yayi stressing kan lamarin local people ba, tsakaninsa da su sadaka if the need arize, babu wani
magana me tsayi dake hadasa da su, Abuturrab ya hade rai ganin irin kallon da Ahmad ke masa yace "Nayi
kuskuren gaya maka damuwata ne da ya sa ka min shiru Ahmad? Don't u have anything to say to me pls?"
Lkci daya yanayin Abuturrab ya kara sauyawa gaba daya, sai yake jin wani sabon xaxxabi xai rufesa, da kyar
Ahmad na nunasa yace "You mean you are married now without our knowledge Captain??" Cakumosa
Abuturrab yyi a fusace yana huci yace "Wannan kake kira da aure? Haka ake auren dama? Mahaukaci ne ni
da xan amince nayi aure yanxu" Ahmad yyi iya kokarin ganin bai yi dariyar da ya taho masa ba ganin how
furious Abuturrab was, Turasa Abuturrab yyi ya mike yana jin xufa na keto masa yace "Ka gaya min meye
abun yi ynxu, i have never been this confused all my life, what have i done to my self, taimako fa kawai nayi
kokarin yi...." Lkci daya idonsa ya kada ya dawo ya xauna ya rike kansa, Wani tausayinsa Ahmad ya ji har
ransa, hakan yasa kawai ya kawar da dariyar dake cin sa gaba daya a xuciyarsa, ya kwantar da murya yace
"let's talk brother" Abuturrab ya dago da idanuwansa da suka yi ja yana kallonsa, Ahmad yyi shiru yana
tunanin yanda Abuturrab yayi making fool out of him, ko da wasa bai ta6a gaya masa abinda yake yi ba sai
da abu ya 6aci, har da raina masa wayo wai shu murhu yake gani a hayi, wani boyayyen ajiyar xuciya ya
sauke yyi kasa da murya yace "before i say anything just tell me what u have in mind now about this
issue?" A hankali Abuturrab ya kai hannu aljihunsa ya fiddo farar takarda da biro yana kallon Ahmad,
Ahmad ya buda ido sosai, lkci daya ya girgixa kai yace "Nooo.... This isn't a solution, idan ka rubuta
takardan nan dole gida xata koma ga axxalumar step mum dinta, kaga anyi ba ayi ba kenan, and at the end
wannan mahaukacin kilan yace sae ya aureta..." Abuturrab yace "But I can't sleep in peace again today in
har ina tuna auren warce ke kaina, baxan ta6a samun nutsuwa ba matsawar ban aiwatar da haka ba, me of
all people fa?? Where will i start from with that girl, me xanyi da ita a rayuwata?? Ko a mai aiki wllh wllh
wllh baxan yi employ dinta ba, baxan bata aiki ba a gida na dai, western education zero, islamic education
zero, wayewa zero, tsafta zero, mu'amalat zero, kyau zero.... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ahmad dake
ta kallonsa bbu ko kiftawa ya girgixa kai yana d'an murmushi yace "A bangaren kyau kuma ka so kanka
Captain...." a mugun fusace Abuturrab ya fixgosa yace "What the heck.... Kyau xan ci?? Tsaftar fa?? Ilimin
fa?? Wait wai kai Ahmad kana tunanin no matter what xan iya xama da local yarinyar nan a matsayin
matata? Noo plss... God forbid, this is more like an abomination to me, idan na sake kwana da auren
yarinyar nan a kaina yau wllh nasan gobe xan iya xarewa a wuce dani psychiatry" Ahmad ya lumshe ido ya
bude yace "Duk na fahimce ka, amma idan ka saketa ynxu Captain ka gaya min meye makomarta? Ina kake
son taje? Kasan xamanta tare da maigadin gidan nan da matarsa ba abu bane da xai ja lkci coz daki daya ne
da su" Abuturrab ya lumshe ido ya bude yace "I don't care anymore, saninta da tausayinta ne duk ya ja min
plight da nake ciki ynxu..." Ahmad yace "Ohk Now tell me, after the divorce what next, ya xa kayi da
lamarinta? Kaga tamkar ka lalata aikin ladan da kayi ne daga farko har karshe" Abuturrab na masa wani
kallo yace "What are you insinuating now? Kar in saketa kake nufi ko me?" Ahmad ya daga hannu da sauri
yace "Aa ni bance haka ba" Abuturrab ya ja wani tsaki yace "Xan saketa, kuma xan ci gaba da mata
taimakon da nayi niyya" Ahmad yace "Good, ta yaya?" Abuturrab yace "Under my roof" Ahmad yace
"Elaborate plss" Abuturrab yace "I'm thinking i will have no choice but to explain everything that
transpired to my Dad, xan ma Abbana bayanin komai, xan kuma kai sa har gun me anguwan, i don't want
to look foolish, you get? Then he can explain everything to Ummi coz ni baxan iya ba...." Ahmad ya katse
sa yace "You are confusing me, kai da kake da intention sakinta yanxu me xai kai magana kuma kunnen
Abba?" Abuturrab yace "Don nace xan saketa ba yana nufin ai baxan yi duk abinda nayi niyya a kanta ba,
wllh xan saketa without anyone's knowledge, daga ni sai kai ne xa mu san babu aure tsakanina da ita,
amma she will be under my care xan kula da ita har sanda xata samu me aurenta" Ahmad da ke ta kallonsa
baki bude yace "Under ur care as how?? a gidanku xaka ajiyeta kenan?" Abuturrab ya girgixa kai yace "A
gidana dai" Wani tsaki Ahmad ya ja yace "See the way u are talking like an illiterate plss, ba matarka ba ba
komai ba xaka ajiye a gidanka kuna rayuwa tare Captain, ko dai nine ban fahimce abinda kake nufi ba, ka
min bayani yanda xan gane" Abuturrab ya masa wani kallo yace "Toh me xamanta a gidana xai kara ko xai
rage? Did i look like someone that have anything to do with that girl? Haba Ahmad, don dai ta kwana ta
tashi tayi girki ta ci abinci ta tafi boko ko islamiyya, xamanta a gidan nan da rashin xamanta duk daya to
me, Monday to Friday ina gun aiki, na dawo sunday and Saturday, wait tell me what u have in mind first"
Ahmad yace "Gaskiya baxan yarda da wannan rashin tunanin ba, kana cikakken namiji ka xauna gida daya
da mace...." Mikewa Abuturrab yyi looking super angry yace "Amma ka gama da ni Ahmad, mace me tsafta
iya tsafta ina xulumi da tunanin yanda xanyi tarayya da ita balle wannan, haba.. haba wannan xagina kayi
wllh, ta ina xan fara abinda kake tunani, did you know who i am kuwa Ahmad, me xanyi da warce tayi
tsaftar yarinyar nan sau biyar ma balle ita" wani kallo kawai Ahmad ke yi masa Abuturrab yace "You just
insulted me wllh, and i am seriously not happy about it" Ahmad ya tabe baki ya ki basa amsa, Abuturrab
yace "Sabida wannan kaddaran da ya fada min ma dole nan da lkci ba mai tsayi ba in auri Aneesah" Ahmad
yace "Sai ka ajiye su gida daya kenan?" Abuturrab yace "Yes, kaga Aneesah ta samu me taimakonta aikace
aikace kenan" Ahmad yace "Gaskiya ne wannan, to yanxu abinda nake son sani shine, idan ka rubuta
takardan ba yarinyar xaka yi kenan ko ko ya xaka yi?" Abuturrab yace "I will do the rightful thing, giving her
or not giving her" Ahmad yace "To su kuma can iyayen nata xaka bari su san tana wajenka?" Abuturrab
yace "There is no need, idan ta samu 'yan cin kanta xata je garesu watarana" Ahmad ya sauke ajiyar xuciya.
Karasawa Abuturrab yyi jikin window yana kallon waje, Ahmad dai sae kallonsa yake, shi har sannan ganin
lamarin yake kamar a film, abinda ya fi daure masa kai yanda Abuturrab ya boye masa komai from
beginning sae ynxu da abu ya baci, murmushi yyi yana gyada kai yana tunanin irin dariya da tsokanar da
xae fara yi ma Abuturrab idan hankalinsa ya kwanta, sae dae deep down him he is so Happy for this young
girl don yasan Abuturrab baxae ta6a cutarta ba, with him her future is super bright, komai na rayuwa baxai
ji kyashin yi mata ba, maganar sakin da Abuturrab yyi ne kadai bai ji dadi ba har cikin ransa. Ana kiran
magrib suka fita tare xuwa masallaci bayan sun yi alwala, Jiddah ce kadai xaune tsakar gida da buta a
gabanta, tunda ta hangosu daga nisa tayi kasa da kanta tana alwalanta,, Kallonta kawai Ahmad ke yi yana
mamakin yanda ita da gogan suka iya pretending, ko da wasa bata ta6a nuna masa ta san sa ba, murmushi
kawai yake yi yana kara jinjina wannan lamari me abun mamaki, Abuturrab dai ko kallon inda take bai yi ba
har ya fita gate din, Ahmad yyi murmushi ya bi bayansa, shi dai ya san ko giyar wake Abuturrab ya sha
baxai yi accepting yarinyar nan matsayin matarsa ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login