Showing 168001 words to 171000 words out of 321711 words

Chapter 57 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

kai yana kallon
Ummi amma bai ce komai ba, Ummi ta tabe baki tace "Ni a iya sanina warce ta xauna kafin ita ai ba
matsayin mata ka dauketa ba a lokacin ko? Wannan kuma matarka ce ta sunna...." Shi dai bai ce komai ba,
Ummi ta ci gaba tace "Don haka sai kayi hakuri da duk abinda ka gani, da yanda ka gani, na farko dai ba
wani ya nemo maka yarinyar nan yace ka nemeta ka aura ba..." Ya marairaice mata yace "Ummi to ai ni da
muka hadu da ita da farko ba wai soyayya muke ba, kuma ni ban ta6a tunanin xan ma aureta ba, kawai dai
ta kan kirani mu gaisa ne time to time, sai kuma WhatsApp chat, a airport din Abuja muka hadu taje gun
uncle dinta, ni kuma mun sauke jirgi, and she requested my digit na bata kawai don ban iya walakanci ba,
sai kuma coincidentally na dawo wani weekend na ganta a gidan nan ta xo gun Aunty da aunt dinta ashe
Mum dinta close frnd din Aunty ce" Ummi dake ta kallonsa tace "Sai aka yi yaya? Sai aka ce ka so ta dole
har ka aureta?" Yace "Aa Ummi but Aunty ce ai..." Sai kuma yayi shiru, Ummi ta tabe baki tace "Kaga Aliyu
rabani da wannan labarin da na sani, yanxu dai kawai kayi hakuri ka nema mata house help, da xata dinga
tsaftace maka gidan ka, sai kuma ka ci gaba da hakuri da sauran halayen nata tunda dai auren soyayya ku
ka yi ba auren kiyayya ba" Bai iya yace komai ba, Ummi dai sai kallonsa take, amma can kasan xuciyarta
tausayinsa take, she understands what he is going through, barin shi da yayi detesting kazanta with
passion, ita har ta mance rabon da ya shigo dakinta balle har ya dade haka yana xance da ita kai tsaye, Ya
d'an ja tsaki underneath his breathe yace "Karamar yarinya ma da ta kusa doubling age dinta warce ta
tashi a ghetto bata irin abinda take yi na kazanta wllh, tun daga balcony nake jiyo kamshi lkcn da yarinyar
ke gidan idan na dawo gida, for once ban ta6a shiga kitchen naga dirty utensils ko daya ba, ni har kunyar
wani nawa nake ya xo gidana yanxu, dama a garin nake sai in dinga gyarawa ni kullum, kawai ita abinda ta
sani sai tayi wanka ta fesa turare ta xauna tana danna waya, sai tara kawaye a gida" Ummi tace "Toh wai ita
kuma wannan karamar yarinyar da kake sa wa a baki kake comparing da matarka meye hadinka da ita ne,
why don't u face ur life ka daina mentioning dinta a lamarin ka, did she have anything to do with u again
xaka sa ta a bakin duniya" Ya kalli Ummi amma bai ce komai ba, Ummi tace "Ni ka tashi kaje ka same
matarka ka bata hakuri ka dauketa ku tafi gida, Allah ya ci gaba da daidaita ku, ba ruwana da matsalar cikin
gidanku, it's something u should have known before marrying her" Abuturrab yace "But how mum,
kullum fa fes fes xaka ganta a titi, waye xai san xata yi haka?" Ummi tace "Allah ya kyauta" Ya kwanta
saman gadonta yace "Ni sai na ci abinci Ummi, kuma ba yanxu xan tafi ba sai after isha, kullum fa sai nayi
takeaway din abinci bata girki" Sharesa Ummi tayi ta mike ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta kawo masa abinci
dakin, tana ajiyewa ta juya ta fita, shi kam ko kallonta bai yi ba, can ya mike ya sauka kasa ya dau plate ya
fara dibar abincin. Aunty ce tsaye bedroom dinta tare da Aneesah dake xaune gefen gado tana kallonta,
bata dade da dawowa gidan ba tun fitar da tayi bayan Hajja ta tarwatsa meeting din daxu, Aunty ta xuge
jakarta bayan ta dau abinda xata dauka a ciki sannan ta dawo kusa da Aneesah ta xauna ta ajiye mata
kwalaban turarruka uku a gabanta tace "kinga wannan, sai bayan mun koma asibiti ko xuwa gobe sun kara
tabbatar maki babu wata matsala sannan bayan kin koma gida sai kiyi amfani da su" Aneesah tace "Aa
kawai gwara ayi sabon dinkin Aunty, ni ina ji a jikina ba dai dai nake ba" Da mamaki Aunty tace "Kamar
yaya?" Aneesah tace "Ni dai kawai ayi hakan, ko nawa ne xan biya ai" Aunty ta tabe baki tace "Toh shkkn,
amma wllh Aliyu yayi mugun raina maki wayo, sannan ni banga laifinsa ba kece babbar wawuyar da kika
yarda wai yana da matsala, a gidan ubanwa yake da matsalar mutumin da har gidansa kin sha xuwa ki
kwana? Ko ke duk xuwan da kike gidansa a Abuja kin ga alamar yana da matsala?" Aneesah ta tabe baki
tace "Ban ta6a ganin haka ba wllh, kawai shi dai baxai yi intercourse ba sbda gudun sa6on Allah amma ba
don bashi da lafiya ba ko wani abu, amma babu abinda baya min ai, ce min yayi of recent ya samu
matsalar" Aunty tace "Wllh ni ban yarda da kanwar uwar nan tasa ba don ita ma waye bai san tana shige
shige ba kilan taje ta hango aikinmu ne tasa aka lalata, shine yake ta maki hanya hanya..." Aneesah tace
"Toh ai da kin tambaya inda kika je daxu" Aunty tace "Wllh na manta shaff ban tambayi mutumin ba,
amma akwai wani da xan kira anjima a benue, xai sanar da ni komai, yanxu kuma sai ki kirgo dubu talatin
na turaren nan ki bada" Aneesah tace "Ina na gansu Aunty, har yau fa nace maki kudin nan da kika ce in
tambayesa sai min yawo da hankali yake, yace yau yace gobe" Aunty tace "Rabu da shi don ubansa, xa
muyi maganinsa nan ba da dadewa ba, muna nan dake sai account dinsa ya dawo hannunki gaba daya"
Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty ta jawo pillow ta ture kananun kwalaban turaren a karkashi da sauri,
Aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama kansa a kasa, Hade rai Aunty tayi ta mike ta dau Hijab dinta
ta saka ta shimfida darduma ta hau sallahn isha, Aneesah dai sai wani cika take tana batsewa tana danna
waya, ya ja stool ya xauna ya fiddo nasa wayar yana dannawa, yana ta xaune har Aunty ta idar da sallah,
sannan ya kalleta yace "Ina yini Aunty" a takaice Aunty tace "Lafiya lau, sai yanxu ka ga damar shigowa
bayan ina ganin sanda ka shigo gidan tun kafin magrib?" Yana kallonta yace "Dakin Ummi nake ai" Aunty
tace "Toh yayi kyau, ai da baka fito ba ka dauwama a can din" Shi dai bai ce mata komai ba, ta dau carbinta
tana ja, bayan few seconds yace "Dama xuwa nayi in baku hakuri Aunty a kan abinda ya faru, ni bana nan
lkcn da Aneesah suka samu matsala da Hajja, ban ma san me ya faru ba har yanxu, na kuma bata hakuri
tun a daren jiyan amma taki saurarata tayi wucewarta" Aneesah ta katse sa a fusace tace "Wllh karya ne
Aunty, da bakinsa ya umarce ni da in tafi" Kallonta Abuturrab ya dinga yi yace "Ni nake maki karya?" Tace
"Toh tunda baka ji kunyar yin karyan ba nice xan ji kunyar karyata ka Aliyu" Aunty na kallon Abuturrab tace
"Ni tambayar da xan fara yi maka a nan shine me wancan dabbar taje yi gidan ka tare da Hajja?" Da
mamaki yace "Dabba kuma, ai Allah ma bai ce a siffanta mutum da dabba ba Aunty, dabba fa kika ce"
Aunty tace "Ohh ni xaka ma wa'axi? To nace mata dabbar sai kayi yanda xaka yi yanxu, kanwar uwarka ce
ita din ko ta ubanka?? Ko uban meye hadinka da ita xaka ce kar in kirata da dabba? Ka bani amsar
tambayata uban me ya kaita gidanka Aliyu?" Cikin tsawa ta kare maganar, Ya sauke idonsa kasa yace "Nima
ganinta kawai nayi tare da Hajja i don't know how" Aunty ta mike tana tafe hannu tace "Toh tayi xuwan
farko tayi na karshe, duk ranan da kauyancinta da gidadancinta ya sake kadata ta bi wani ma ba Hajja ba
xuwa gidanka dama nace tana shigowa Aneesah ta kirani, xan kuma dau makullin mota in fita inje gidan sai
kuma nayi mata abinda har ta koma ga Allah baxata manta ba don ubanta, duk ranan da ta sake gigin xuwa
gidan Aneesah wllh wllh sai na lahira ya fi ta jin dadi, sai na walakantata walakanci mafi muni, sai na mata
toxarcin da har jikokinta sai ta ba labari wllh" Abuturrab kallon Aunty kawai yake ko kiftawa babu, can dai
ya dauke kansa, Cikin bacin rai Aunty ta ci gaba tana cewa "Idan ba kwadayi da jakanci ba uban me xai sa
tayi sha'awar komawa gidan da aka saketa ta fito, me xai kai ta?? To wllh ta kiyayeni bani da kyau, idan ta ci
gaba da shiga gonata sai na sa ta bi duniya ni ba imani ne dani ba al-qur'an, su Ramlah yan iyayi da suka ga
xa su iya riketa su ci gaba da riketa din, amma duk ranan da gidadancinta ya fada mata karya ya kaita
gidanka to kuwa ranan xata yi da ta sanin haifota da matsiyatan iyayenta suka yi" mikewa Abuturrab yyi ya
nufi kofa Aunty tace "Gidan ubanwa xaka ina magana Aliyu?? Aliyu ba da kai nake ba??" bude kofar yayi ya
fice ya bar masu a bude ko kullewa bai yi ba, Aunty ta bi sa da kallo baki bude har ya fita kofar parlor gaba
daya. Abuturrab na fita bangaren Ummi ya koma, Ummi na kallonsa tace "Kaje ka bata hakurin?" Kasa ce
mata komai yayi saboda yanda xuciyarsa ke tafarfasa, Ummi ta lura da yanayinsa ta ci gaba da aikinta da
take yi kawai, bayan kusan minti uku yace "Ummi ki kira Aneesah kice ta sameni a mota, idan kuwa bata
fito ba xan yi wucewata" Ummi tace "Ka kira uwar dakin taka ka gaya mata mana, ba ita tafi kusa da
Aneesar ba, sannan ina ce ma a bangarenta take" Abuturrab ya mike yace "Next weekend idan na dawo
xan xo in dauketa in sha Allah, sai da safe" daga haka ya nufi kofa Ummi tace "Aliyu" tsayawa yayi, sai
kuma ya juyo tace "Tell me what happened" Yace "Ummi kawai ni bana son abinda Aunty take yi ina raga
mata ne kawai saboda Abba but idan ta ci gaba da shiga gonata i can go to d extent i am not suppose to,
she is getting me pissed off" Ummi ta rike ha6a tana kallonsa da mamaki a ranta kuwa cewa tayi yau
kuma?? Can ta d'an yi murmushi tace "Toh me ya hadaka da uwar dakin taka, dama ana jin kanku ashe"
Abuturrab yace "She should just stay away from my personal life nd issues, that's all, xan jira a mota ki kira
ki gaya masu idan kuma bata fito ba wucewata xanyi, sai da safe" Daga haka ya fice daga dakin Ummi ta bi
sa da kallo, daukar wayarta tayi ta shiga kiran Aunty, Aunty na dagawa tace "Hafsah ki turo min Aneesah"
Aunty ta wani kyabe baki tace "Aneesah kuma?" Ummi tayi shiru bata ce komai ba, Can Aunty tace "Toh
dama sallah take bari ta idar" Ummi ta katse wayarta, sai bayan minti shidda Aneesah ta shigo parlon
Ummi ta xauna saman kujera ta gaida Ummi, Ummi ta amsa tace "Ki je ki saka hijab dinki ki dau jakarki
mijinki na jiranki a mota, sai kuma ayi ta hakuri, shi dama xaman aure d'an hakuri ne, kowa hakuri yake, ke
kuma sai ki gyara duk abinda baya so, shima xai gyara in sha Allah, Hajja kuma ba lallai xaki sake ganinta a
gidan ba ma, kiyi hakuri ki bi mijinki ku tafi kin ji" Aneesah tayi kasa da kanta, bayan wani d'an lokaci tace
"Toh" sannan ta mike ta nufi kofa, Ummi ta bi ta da kallo har ta fita, tana komawa ta sanar ma Aunty yanda
suka yi da Ummi tana tabe baki, Aunty ta ja wani dogon tsaki tace "Toh baxa ki je ba wllh, ita a wa xata
tsomo baki cikin lamarin nan? Ina ruwanta! A cikin kayan miya wacece ita a lamarin Aliyu??" Aneesah dai
sai ta6e baki take, can tace "Kinsan me Aunty tunda har kirana tayi ta min magana ki bari kawai inje kar ta
saka ni a baki" Aunty tace "Ta saka 'ya yanta a baki dai ba ke ba wlh, kamar tana wani tabuka abun kirki a
kan lamarin Aliyun da xata wani tsomo baki a wannan case din, ta ma ji da mugun abinda ke cinta kullum a
xuciya mana da shiru shirun da take na algungumanci" Aneesah ta mike tace "Ko kayana ma baxan dauka
ba Aunty xan dai tafi da turarrukan cikin hand bag" Aunty tace "Toh ya xancen xuwa asibitin gobe, ni fa
dalilin da yasa nace baxa ki tafi yau din ba kenan" Aneesah tace "Sai in taho idan ya koma aiki gobe da safe,
nasan da sassafe xai wuce kano ai, yawanci yanxu haka yake yi, ni bana son wancan matar tace nayi
disrespecting dinta ne amma da sai in tsaya" Aunty ta ja tsaki ta xauna gefen gado tace "Dama goben ki xo
da wuri, Kinga dai dai kenan kafin ya dawo wani weekend din anyi duk abinda xa ayi an wuce wajen"
Aneesah ta saka hijab dinta ta xuba duk turarrukan a jaka sannan tayi ma Aunty sai da safe ta fita. Har suka
isa gida Abuturrab bai ce ma Aneesah komai ba ita ma haka, banda danna wayarta babu abinda take, ta
sauka motar ta bi bayansa xuwa cikin gidan, xaunawa parlor yyi yana kara regretting furnitures da aka xuba
ma Aneesah a bangarensa, ko kallonsa bata yi ba ta haye sama ta wuce bangaren nasa, kwafa yyi ya mike
ya haura sama ya bude dakin da su Hajja suka sauka ya shiga ciki, tsaf Hajja ta gyara dakin kafin su fita
neman jiddah daxu da safe, don cewa tayi babu inda xata tafi bata gyara dakin ba haka kawai ta shiga
hakkin tsafta, har bandaki sai da ta wanke, banda kamshi kuma babu abinda dakin yake, cire kayansa yayi
ya shiga bandaki dake cikin dakin, bayan yayi wanka ya jima xaune dakin kafin ya sauka downstairs ya shiga
kitchen, har sannan kitchen din fess tun gyaran da Jiddah tayi masa, ya dinga bin kitchen din da kallo kafin
ya dau mug ya tafasa ruwan xafi ya hada shayi ya fito, a parlor ya sha shayin, yana ta xaune har kusan sha
daya kafin ya mike ya wuce sama, babu yanda ya iya ya nufi bangarensa don daukar jallabiyarsa, Aneesah
ce durkushe dakin hannunta rike da karamin towel tana goge turarrukan da suka fashe da sauri, har wani
rawa hannunta yake, jakarta ta dauka xata ciro charger bata san a bude yake ba duk kayan ciki suka jirkice
ciki har da turarrukan da aunty ta bata daxu wanda nan take biyu suka fashe wani kamshi ya gauraye
dakin, tana ganinsa ta mike da sauri ta wuce bandaki da towel din, ya bi ta da kallo....


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


Makulli Aneesah ta sa a kofar bandakin bayan ta shiga gabanta na faduwa, ta ajiye towel din a karamin
bucket ta tara ruwa ta dau sabulu ta fara wanke hannunta ba ji ba gani... Karasawa Abuturrab yyi yana jan
kafa ya xauna gefen gado, har bayan minti sha biyar Aneesah bata fito daga toilet din ba, mikewa yyi ya
dau jallabiyarsa ya fita dakin, sai da Aneesah ta tabbatar hannunta baya kamshin turaren sannan ta bude
kofar bayin a hankali tana leko dakin, ganin baya nan ta sauke wani ajiyar xuciya ta fito, dama kayan bacci
ne jikinta ta dau wayarta tayi plugging sannan ta kashe wutan dakin tayi kwanciyarta.... Har karfe daya
saura Abuturrab bai yi bacci ba yana dai kwance da abinda ya damesa, idan ya juya ta daya side din gadon
sae ya sake komawa daya side din, lkci daya ya mike xaune ya dafe kansa, sae kuma ya sauka saman gadon
ya bude kofa ya fita ya sauka downstairs ya wuce kitchen ya jona ruwa a kettle, yana ta tsaye yana kallon
kettle din sae kawai ya kashe socket din ya wuce sama, bangarensa ya nufa bayan ya shiga parlon ya karasa
ya bude bedroom dinsa, hannu ya kai jikin bango ya kunna switch din dakin, bacci take hankali kwance ya
kashe switch din ya karasa gun gadon ya hau, cikin bacci Aneesah taji kamar hannu a jikinta ta bude ido a
hankali, lkci daya ta mike tace "Meye haka Captain?" Xaro ido tayi tana kokarin turasa ganin abinda yake
shirin yi tace "Wai meye ne Captain, what is this u are doing" Rungumeta yayi jikinsa underneath his
breathe yace "I need you today...." Sosai gabanta ya fadi ta fara turasa da duk karfinta tana cewa "You
need me when i am on my period Captain?" Gani tayi kamar yana son confirming din abinda ta fada, bata
san lkcn da ta fashe masa da kuka ba tana turjewa tace "Don Allah ka bari captain, meye xaka wani taho
min kamar wata akuya bayan ni ban...." Bai bata privilege din ci gaba da magana ba, da farko gani take
kamar xata iya kwatar kanta gunsa amma ya gwada mata ba karfinsu daya ba, hakan yasa ta fara masa
magiya tana basa hakuri hankali tashe tana ce masa she is not in d mood amma kamar bai ma jin abinda
take cewa, Aneesah bata ta6a shiga tashin hankali da firgicin da ta shiga a lkcn ba, banda rawa babu abinda
jikinta yake tana hadasa da Allah ya bari, cikin not less than 10 mins komai ya faru... Tunda ya koma
gefenta take satan kallonsa tana shessheka tana kukan tsoro, ga xuciyarta da take ji kamar xai fado don
bugawa, gashi ita ba ganin fuskarsa take ba balle taga expression dinsa, Ita dai har ta gaji da satan kallonsa
tana kuka ganin kamar ma bacci yake don ko motsawa bai yi ba balle ya kalli inda take, ta lallaba ta matsa
kusa da shi xata ta6asa, sauka taga yayi daga saman gadon tun kan ta ta6asa ya nufi kofa, ta bi sa da kallo
gabanta na ci gaba da bugawa sai da ya fita ta fashe da kukan gaske na tashin hankali... Abuturrab na
komawa dakin da ya fito ya sa makulli ya shiga bandaki da sauri jin cikinsa ya hautsine.... Har kusan asuba
Abuturrab bai yi bacci ba duk da sallah da ya dau lkci yana yi, after subhi prayer yana xaune parlor deeply
in thought, sai kuma ya dau wayarsa yayi dialing number Ahmad, Ahmad ya shigo daki kenan dawowarsa
daga masallaci ya nufi wayarsa da mamakin wanda ke kiransa by this time, ganin Abuturrab


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login