Showing 72001 words to 75000 words out of 321711 words
Ramlah da abinci wanda Umma ta basu su kawo ma Jiddar, sosai
Jiddah ta sake da su don ba kadan suke debe mata kewa ba, Ramlah ta dinga mamaki kamar yanda Ahmad
yyi ganin ashe dai Jiddah na magana haka, ga dariya kamar me, xuwan su ya sa har ta samu confidence din
fita suka xaga cikin gidan gaba daya tare da su, a nan ne ma tasan da mai gadi da matarsa a gidan, sai
bayan magrib Umma ta aika driver ya je ya daukosu, Jiddah ranta fess ta ci sauran abincin da suka rage
sannan tayi wanka tayi isha ta shirya ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Karfe tara saura Abuturrab
dake xaune hotel room dinsa a kano yyi dialing number nata, har ya gama ring bata daga ba, da mamaki ya
dinga kallon wayar, ya sake kira nan ma no answer, sake kira yyi ya sake ringing ya gama ba a daga ba, da
yamma ma ya kira sau biyu no answer, a lkcn kuma Jiddah na can compound tare da su Ramlah, ajiye
wayar yyi, can ya mike ya shirya within few minutes ya dau makullin motarsa da jakar laptop dinsa ya fita
dakin, abinda bai ta6a yi ba xai yi ranan, wato driving to kaduna at night, dama da asuba yyi niyyar
komawa kaduna sbda throughout gobe ba shi da duty, amma yanxu yyi deciding din tafiya kawai, sai kusan
sha biyu da wani abu Abuturrab ya shiga gida yyi parking mai gadi ya taho da sauri yyi masa sannu da
xuwa, amsawa yyi ya wuce ciki, makulli ya ciro ya bude kofar dake a kulle, Jiddah bata mance warning din
Ahmad na cewar duk wanda ya xo kar ta mance kulle gidan da makulli bayan ya tafi ba sannan ta boye
makullin, bin parlon ya dinga yi da kallo, ya kashe wutan dake a kunne ya wuce sama, kofar dakinta ya
bude, kwance ya ganta tana bacci cikin nutsuwa, karasawa cikin dakin yyi still looking at her da wani
expression can ya juya ya fice daga dakin ya tafi bangarensa. Washegari da safe bayan Jiddah tayi wanka ta
shirya ta fito daga dakinta, cak ta tsaya jin kamar tana jin murya a can daya part din, to ko tv ne a kunne,
ko ma ita ce ta ta6a abu da ya kunna tvn ranan da ta shiga dakin bata sani ba, gabanta na faduwa ta fara
tafiya xuwa can din a hankali, har ta isa sannan ta bude kofa cikin nutsuwa tana lekan parlon, babu wani tv
dake a kunne ta dinga bin parlon da kallo, sai taji ba tv bane karatun qur'ani ne, har xata juya ta d'an yi jim
kamar me shakkar shiga ciki, can dai ta karasa ciki tana kallon kofar bedroom din da ba a rufe ba gaba
daya, tunani ta dinga yi ko ita ta bar kofar haka jiya, a hankali ta kutsa kai ciki, wani kara tayi a tsorace
ganin mutum kwance with short and singlet yana bacci, ta juya da sauri ashe ta mayar da kofar ta ci karo
da kofar, wani ihun ta kuma yi ta dafe forehead dinta....
Don Allah no Reader should come and ask me of complete document na Jiddatul Khair plss, naga dai ba
tsohon book bane da xaku dinga cewa sae an baku document xaku biya, snn shi page guda guda da ku ke
karantawa ae ba kyauta bane shi ma, to don hka ko wacce ta ji da bashin dari biyat din mutane😏
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Bude ido Abuturrab yyi ya tashi xaune yana kallonta da mamaki, ta mike tsaye hannunta a goshinta, ko ina
na jikinta rawa yake, duk ta daburce, xata bude kofar cikin tsawa yace "Me ya kawo ki nan??" Kin juyowa
tayi hannunta na rawa ta bude kofar xata fita, wani tsawan ya kuma yi mata yace "Kar ki kuskura ki tsallaka
bakin kofar nan" fashewa tayi da kuka amma taki juyowa kuma bata fita dakin ba, ya sauka daga saman
gadon ya dau jallabiyansa ya saka sannnan ya nufeta, tana jin alamar ya sauka gadon ta juyo da sauri,
ganinsa tayi tsaye gabanta, fuska daure yace "Me ya kawo ki bangarena?" Cikin rawan murya ta durkusa
tace "Wllh kara naji shine na xo in ga meye, ban san ka dawo ba Allah" Ya rungume hannunsa yace "Wato
har nan kike shigowa kenan idan bana nan kenan?" Ta fashe da matsanancin kuka tana girgixa kai tace "Aa
bana shigowa, ni ba shigowa nake ba wllh" Yace "Toh ina ruwanki da koma me kika ji da xaki shigo min
daki?" Hawayen dake makale idonta ya sakko ta girgixa masa kai kawai bata ce komai ba, yace "Toh tafi ki
dauko abun shara, ki share tun daga cikin dakin har parlor sannan ki goge, ki wanke bandakin...." Ta
sunkuyar da kanta don har ta ji hankalinta ya kwanta xatonta har marinta sai yyi yau, kofar balcony din
dakin ya nufa ya bude yana nuna mata yace "Har nan xaki share kiyi mopping" Gyada masa kai kawai tayi,
ya dau wayarsa har ya nufi kofa ya tsaya, ya juyo yana kallonta yace "Kar ki ga na kyaleki yau, billah idan
kika sake shigo min bangarena ko da wasa xaki sha mamaki" Kai kawai ta gyada masa a sanyaye, ya juya ya
fita, sai da ya fita parlon gaba daya sannan ta juya a hankali ta fita ita ma, downstairs ta sauka ta gansa
xaune parlor ya kunna TV, ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, abun sharan ta dauko da mopping bucket tare
da mop with duster sannan ta wuce sama, aikin ta shiga yi babu ganda, har xanin gadon sai da ta sake
shimfidawa, bayan ta gama da bedroom din ta tafi balcony, kallon inda taga mutumin ranan tayi duk da
babu kowa wajen sai kujera amma sai take ganin kamar shi a wajen, ta fi minti biyu tsaye tana ta kallon
wajen kafin ta fara share balcony din ta yi mopping ta dawo dakin ta kulle kofa, parlor ta tafi nan ma ta
share ko ina ta goge har kayan kallon, tana gamawa ta koma bedroom din ta bude kofar da take tunani
bandaki ne, kallon bracelet din hannunta me kyau tayi wanda yau ya kai kwana uku da ta saka shi, ta tafi
gaban mirror dinsa ta cire sannan ta ajiye tana kallon turarrukan da ke gaban madubin, kwalabensu ne ya
burgeta sosai, they look so unique, ta dau daya daga ciki ta bude ta kai hanci, rufe ido tayi sannan ta bude,
da wannan kamshin ta sansa, babu kuma abinda ya fado mata sai lkcn da yake xuwa can wajenta a Hayin
rigasa, ta dau murfin xata rufe turaren ya subuce daga hannunta duk kokarin ganin ta kama turaren kan ya
kai kasa hakan ya faskara don tuni yayi landing kan tiles sbda irin faduwan da yayi kuma lkci daya ya
tarwatse, a tsorace ta ja baya ta dafe kirjinta da ya hau bugawa, lkci daya ta fara yarfe hannu murya can
kasa tace "Na shiga uku" hankali tashe take kallon turaren, ta ma rasa abun yi, can ta nufi kofa sai a sannan
ta fashe da kuka ta fita part din, downstairs ta sauka ta makale jikin bango tana kallonsa gabanta na
faduwa, jin footstep kuma bai ji ta karaso cikin parlon ba ya sa ya juya, sunkuyar da kanta tayi, ya mike
yana kallonta ganin hawaye a idonta, satan kallonsa tayi ganin kallon da yake mata ta fashe masa da kuka
tace "Don Allah kayi hakuri" kasa daina kallonta yyi, can yace "Me kika min a sama?" Ta kara rushe masa
da kuka tace "Don Allah kayi hakuri nace" Ya wani hade rai yace "Me kika yi nace?" Kin cewa komai tayi, ya
nufeta, da gudu ta bar wajen ta wuce sama, ya bi bayanta, tuni ta shige dakinta ta rufe kofan da karfi, part
dinsa ya nufa tun bai shiga parlon ba ya soma jin kamshin turarensa, ya shiga parlon sannan ya bude kofar
dakin, tsaye yayi bakin kofa ya rungume hannunsa yana kallon tsadadden turaren nasa a kasa, Jiddah dai
sai zare ido take tana jiran jin ya shigo dakin amma bai shigo ba har sha daya na safe, sai a sannan ta fara
jin yunwan da ya dameta, lamo tayi kan gado kamar xata yi kuka tana tsoron fita, tana nan a haka har
kusan sha biyu, mikewa tayi daga karshe ta nufi kofarta ta bude a hankali, cikin sanda ta sauka downstairs
bayan ta tabbatar baya kasa sannan ta wuce kitchen, indomie ta dauka ta fara dafawa a kitchen din, ko
kadan bata yrda tayi making noise da xai sa a san tana kitchen din ba, yanda taga Ramlah ta dafa masu
indomie jiya take yi, with ingredients, tana duba indomie da har ya dahu kamar ance ta juya ta gansa tsaye
bakin kofa, sake murfin tukunyar tayi a rikice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" end din kitchen din ta
tafi ta tsaya tana kallonsa a tsorace kamar xata yi kuka, ya karasa gun gas din ya kashe na indomien, da
kuma na kwai dake tafasa, tana ganin haka xata fita kitchen din da gudu, ya tare hanyar, hade hannunta
tayi waje daya ta marairaice tace "Don Allah kayi hakuri" yana mata wani kallo yace "Laifi nawa kenan kika
yi yau a gidan nan?" Ta hadiye abu da kyar tace "Biyu" yace "Wanne da wanne?" Tayi narai narai da ido ta
ki cewa komai, ya hade rai yace "Ina jin ki" Cikin rawar murya tace "Na fasa maka turare" yace "Ehen, sai
me?" Tace "Na ji kamar radio na magana shine naje sashinka ka kamani" Ya gyada kai yace "Good, kinsan
nawa turaren nan da kika fasa min?" Ta bude ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, yace "Toh ki sani
cewar tara ki nake, turaren nan kuma sai kin biyani duk yanda za ki yi ba ruwana" a hankali tace "Toh ae ni
bani da kudi" yace "Ehh nemosu xa kiyi duk inda xa ki nemo su" ta sauke idonta kasa, kallonta yake daga
sama har kasa, ya sauke idonsa kan fingers dinta yaga babu farce alamar tana cirewa a kai kai, ya kalli
fararen toes dinta, kallon fuskarta yyi yaga har sannan kasa take kallo, yace "Cire hular ki" sae a sannan ta
daga kai ta kallesa amma taki cirewa, ya hade rai yace "Magana nake maki" a hankali ta xame hular, ya
dinga kallon bakin gashin nata wanda sak na Fulani, amma duk ya takure waje daya duk da da ribbon ta
dauresa a tsakiya ya sauka kasan wuyarta, tun gyaran gashin da Umma tayi mata har ranan bata ta6a
gashin ba, ya yamutsa fuska yace "Meye wannan din?" Ta kallesa bata ce komai ba, ya mata tsawa yace
"Ba tambayar ki nake ba" Cikin sanyin murya tace "Gashina ne" Yace "Ke kaxamar wace gari ce, gashin ki
ne kika bari haka kamar na mahaukaciya?" Ita dai bata ce komai ba, ya koma baya yana sake kare ma
gashin kallo da mamaki, satan kallonsa tayi ya mata wani shegen kallo yace "Sae na tsokale idonki kika sake
kallona, kina mace da ke dubi ynda gashin ki ya koma kamar gashin jikin tinkiya?? What nonsense" Lkci
daya hawaye ya kawo idonta, strictly yace "Ki gama cin abincin kiyi sllh ki jirani a parlor" Bata ce komai ba
ya juya ya fice daga kitchen din, Jiddah bata wani ci abincin ba sae hawaye, daga karshe ta mayar kitchen
ta rufe taje sama ta wanke bakinta ta dau gogaggen hijab dinta ta saka ta dawo parlor ta xauna fuskarta
babu walwala, sae da ya dawo sallahn Juma'ah sannan ya dau makullin motarsa, ya isa bakin kofar fita
sannan ya kalleta yace "In xo in dauko ki ne" mikewa tayi a sanyaye ta bi bayansa, gaban motar ta xauna
don bata mance abinda yace mata ba last time da ta xauna a baya, wani saloon ya kai ta, yana xaune mota
ya jira har aka gama sannan daya daga workers din ta fito ta sanar masa an gama ko xa ayi mata lalle, yace
"Aa, nawa ne kudin gyaran gashin naku?" Ta fada masa ya ciro kudin ya mika mata tayi masa godiya ta
koma ciki, ba a dau lkci ba sai ga Jiddah ta fito daga saloon din, walking slowly ta iso gun motar har sannan
fuskarta babu walwala, ta bude gaban motar ta shiga, ta rufe bata ce komai ba, kallonta kawai yake da
mamaki, gani yake kamar da kyar ta iya rabuwa da halin gidadanci, ya daga kafada don yasan yana magana
xata fara hawaye abinda bai shirya gani ba kenan, ya tada motarsa ya bar saloon din, suna tsaye traffic
ganin yanda take kallon me tallan Apple a bakin glass din motar yace "Xa ki ci ne?" Sauke idonta tayi bata
ce komai, yace "Ba magana nake maki ba?" Ta girgixa masa kai fuskarta a tamke tace "Baxan ci ba" hade rai
yyi yace "Keee" Juyawa tayi ta kallesa tace "Nace A'a" Wani mugun kallo ya dinga mata ta dauke kanta, har
suka isa gida bata sake kallon inda yake ba, yana gama parking ta sauka amma tana tsoron ta fara tafiya yyi
mata masifa, Matar Mai gadi ce tsakar gidan daga kofarsu ganin Jiddah tace "Sannunku da dawowa Hajiya,
Ina wuni...., duk yau shiru baki fito ba" gaban jiddah ya fadi sosai, Abuturrab ya dinga kallonta, Jiddah ta yi
murmushin karfin hali tana kallon matar tace "Ina yini" daga haka ta fara tafiya da sauri, bin bayanta
Abuturrab yyi, sai da ya shiga parlor ganin har ta isa stairs xata wuce sama yace "Dawo nan" juyowa tayi
sannan ta dawo gabanta na faduwa, yace "Ta ina kike fita har take ce maki yau baki fito ba?" Ta xaro ido
tace "Ai kofar a rufe kake barinsa, ni bana fita ko ina, ban ta6a ganinta ba ni sai yau" kallonta kawai yake ta
Sunkuyar da kanta, ya xauna saman kujera, ita dai bata yadda ta sake kallonsa ba, yace "Ina gyaran gashin
da aka maki?" Cire Hijab din jikinta tayi sannan ta sauke hular tana kallonsa, da mamaki yace "Daga nan
xan gani" A hankali ta duka kasa ta matsa kusa da kujeran da yake xaune ta juya masa kan nata, kallon
bakin gashin dake ta sheki yake, yace "Ta haka xan ga gyaran an daure gashin?" Ta juya ta kallesa sannan ta
xame ribbon din gashin ya sauka kasa, bayan few seconds jin bai ce komai ba ta juya ta kallesa suka hada
ido, hade rai yyi yace "Tashi ki tafi" Tashi tayi ta mayar da hulan sannan ta wuce sama dakinta. Mikewa yayi
ya dau makulli ya fita don xuwa can gida ya gaida su Ummi, Tana jin an bude gate ta mike ta isa bakin
window ta tsaya tana lekan compound din har ya fita da mota, turo baki tayi ta koma bakin gado ta xauna,
can ta kalli wrist dinta sai kuma ta mike ta fita dakin ta tafi can bangarensa da sauri, a hankali ta bude kofar
parlon ta shiga ta karasa bedroom da sauri ta isa gaban madubin tana duba bracelet dinta bata gani ba, bin
dakin ta shiga yi da kallo bata ga alamarsa, juyawa tayi ta fita ta koma dakinta ta kulle kofa ta kwanta. Da
daddare Abuturrab na bedroom dinsa yana operating laptop wayarsa ya fara ring, dauka yyi ganin me
kiransa ya katse ya kirata, daga daya bangaren tace "Hi ya Abuu, Grandma want to vid call with u, na kira
naga baka online" Yace "Ohk, how about zoom?" Tace "Aa ta WhatsApp dai" katse wayar yyi ya bude
datansa ya hau online sannan ya kirata vid call din, Hajja ta hakikance gaban screen da katon eye glass
dinta, yyi dariya yace "Ina wuni Hajja" Tace "Aa ba ruwana, meye kuma ina wuni, kai baka kiran mutane sai
dai a kiraka kawai don kana matukin jirgin sama, baka da wani bambanci fa da me jan motar haya wllh,
naga kamar wani jin kanka kake, ga Saleem kullum sai ya kira Farida ya ga fuskata, haka ma Bashir, ko daxu
sai da Bashir ya kira muka ga fuskar juna, to kawai don bana kasar sai kayi watsi da ni, sai kace ba ni nayi
wahala da kai ba, ko uwarka ce tace ka fita harkata, don dai har yau bamu san xuciyar matar nan ba"
Abuturrab na shafa kansa yana murmushi yace "Ya gidan Hajja" Tace "To lafiya lau, ai naji Baban farida xai
taho Nigeria ni dai nace tare xa mu taho don na gaji, babu wani abinci a nan banda gurasar alkama, to ina
dalili duk na kanjale na xata wajen arxiki ne ashe ba haka ba, basu da komai sai alkama da madara"
Abuturrab yace "Yaushe xa ku taho kenan?" Tace "Aa ni dai kawai ji nayi xai taho, amma ban san yaushe
ba" Yace "Toh Allah ya kai mu" Tace "Kana nan kana tukin jirgin har yanxu dai ko? Don duk na sanar ma
abokan arxiki da nayi a kasar nan cewar jikana tukin jirgin sama yake, bbu kamarsa duk Nigeria" Abuturrab
yyi murmushi kawai, tace "Aa ba batun murmushi ba, ko sun koreka a aikin ne nake nan nake ta tsuga
karya?" Yace "Ke fata kike a koreni" kiran Aneesah ne ya shigo wayar, hkn yasa vid call din yyi still, ya daga
kiran, daga daya bangaren cike da fara'a Aneesah tace "Guess what My captain?" Ya jawo pillow ya kwanta
ya lumshe ido cikin calm voice dinsa yace "I am not a good guesser u know...."
Hansai ce xaune kan takalmanta da kawarta Zulai da ita ma ta xauna kan takalman nata a karkashin
bishiyar wani tsakar gida, Mata ne sun fi talatin a d'an tsakar gidan, ko wacce da hijabinta yarkace yarkace,
wasu da goyo wasu da ciki, Hansai tace "Anya Zulai xa mu samu ganin mutumin nan yau kuwa, ni d'an
cinikin awaran yau ma nake ji, don wllh Bibalo ba yi xata yi ba ta