Showing 282001 words to 285000 words out of 321711 words
wani lkcn sai in ji bana
ma son auren, gwara kawai inyi ta duniyanci na wllh" Dariya su Salmah suka yi suna hailing dinta da karfi,
Suhaila tace "Toh kar dai ki manta karfe takwas xa ki fito Aneesah, don wllh wajen da nisa sosai" Aneesah
tace "In sha Allahu takwas din kuwa..." Da haka tayi sallama da su ta dawo cikin gida cike da farin cikin
xuwansu, kawayenta ne na kut da kut tare suke watsewarsu a Abuja, lkcn da aurenta da Abuturrab ya tashi
babu irin shawaran da Rabi'ah bata 6ata ba kan kar tayi aure yanxu tana yarinyarta da ita ta fara fuskantar
matsalolin rayuwa amma Aneesah taki ji, wnn ne ma yasa Rabi'ah bata yi attending bikinta ba sae su
Fauziyya da Suhaila kawai. Jiddah na kwance daki kana ganinta kasa she is very sad, tun indomie da ta ci
shi ma ba sosai ba da safe bata sake cin komai ba har yanxu sbda tana tsoron fita parlor, yunwa take ji
sosai amma ta rasa yanda xata yi, ta mike xaune a hankali tana share hawayen da ya kawo idonta ta mike
ta isa jikin window ta tsaya wani hawayen na sauka idonta, sosai take jin kewar Abuturrab, and she wished
he is around da baxata ji yunwa ba.... Aneesah na shiga dakinta ta shiga wanka da sauri, bayan wasu
mintuna ta fito, cikin gaggawa ta mulke jikinta da turarruka iri iri snn ta fito da wani ubansun English wears
ta saka ta dau babban handbag dinta ta saka brush da maclean, sai panties biyu, ta debi turarruka kala uku
ta xuba su a jakar, Hijab dinta ta dauko har kasa ta saka sannan ta dau flat shoe dinta shi ma ta sa ta dau
dubu hudu ta xuba a jaka ta dau jakar ta nufi kofa ta fita, kulle kofarta tayi da makulli a hankali snn ta fara
sauka downstairs without making any sound, Jiddah na tsaye jikin window dinta har sannan taga Aneesah
da hijab har kasa da handbag ta nufi gate da sauri, Jiddah ta dinga kallonta har ta fita gidan. Da sauri
Jiddah ta nufi kofa ta bude ta sauka da nufin tayi duk abinda xata yi a kitchen kafin dai ta dawo, tana ta
tsaye kitchen tana tunanin me xata dafa da baxai dau lkci ba, kawai tayi deciding ta dafa jollof din pasta, ba
kifi ba nama don a tunaninta xai bata mata lkci, cikin minti ashirin ta gama don pasta din rabi tayi amfani
da ta juye a warmer ta dau ruwan gora a fridge ta fita kitchen din ta koma sama da sauri tana sauke ajiyar
xuciya.... Har aka kira magrib bata ga Aneesah ta dawo ba, aka yi isha still tana ta xuba kunnen ta ji an
bude gate an shigo amma shiru, wanka Jiddah tayi ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta
gefe, she is just missing everything about Abuturrab so much, sau da yawa sai taji kamar lips dinsa a nata
har sai ta kai hannunta bakinta, ta lumshe ido ta takure waje daya tana ta kwance har karfe goman dare, ta
mike xaune cike da mamaki don har yanxu bata ji Aneesah ta shigo ba, a haka har bacci ya dauketa wajajen
11. Da asuba tana farkawa ta fito ta sauka downstairs don haka kawai taji hankalinta ya tashi ganin har
bacci ya dauketa jiya Aneesah bata dawo ba, ta kofar parlon kadai xata san ko ta dawo ko bata dawo ba
don in har ta dawo to xata kulle kofar parlor, ga shock dinta a bude taga kofar da ta murda, alamar ba a
shigo ba balle a kulle, ta dinga kallon kofar a tsorace sai kuma ta juya a hankali ta koma sama. Gari na
wayewa karfe bakwai Jiddah ta sauko parlor don bata jin dadi taga gidan so dirty, tunda ita dai ba me
kiwiya bace, ga shi Aneesah da bakinta na jiya sun yi kaca kaca da parlon kamar yan yara, duk cake ne kan
tiles da goran drink da ruwa, tana cikin sharan parlon aka bude kofa, daga kai tayi da sauri, Aneesah na
ganinta ta hade rai taki yarda ta sake kallon inda take har ta haura sama, Jiddah ta bi ta da kallo tana ci
gaba da sharanta a hankali, bayan ta gama tayi mopping xata kai bokitin waje sai ga Aneesah ta sauko daga
sama da saurin ta again, atamfa ne a jikinta da mayafi sai handbag dinta sai xuba kamshi take, nan ma ko
kallon Jiddah bata yi ba ta fice daga parlon tana picking call dinta tace "Kai Rabi'ah gani na fito yanxu, wllh
na makara ne" Jiddah dai ta bi ta da ido don a bude ta bar kofar.... Bayan la'asar Jiddah ta fito kitchen
kenan bayan ta wanke plate din da ta ci abinci, har sannan Aneesah bata dawo gidan ba, xata tafi sama ta ji
an bude kofa ta juyo da sauri, Hajja ce ta shigo parlon ba ko sallama, Jiddah da ta ji dadin ganinta ta dawo
parlon da sauri tana murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Bari Jiddah ba wannan ne gabana
ba, Ina mijin naki?" Jiddah ta girgixa kai tace "Ya tafi aiki ai" Hajja ta rike kai tace "Kashh, wai nan na shirya
ne ya kai ni gidan kyauta ance min shi kadai ya san gidan a Barnawa tunda a lkcn da ya maida Hafsah
uwarsa da ubansa kusan duk kwana biyu sai sun je gidan da shi da ita, yanda yake xuwa gidan ma ko gidan
Ramlah bai xuwa... Amma wllh ban ji dadin wannan shegen aikin da ya tafi ba, wai fa daga na d'an
kishingida in huta yanxu kawai sae nayi mafarki an kwama ma bakina katon kwado bana um bana um um,
kuma ni kadai ke ganin kwadon babu me gani wllh, su Usman da Hauwa sun tsaya kai na suna ta hajja
lafiya, Hajja lafiya, amma ina ba baki an garkame sae kallonsu kawai nake kamar bebiye, to shi yasa ban ga
ta xama ba a xo a kaini gidan Kyauta ayi min iyaka da Hafsah, wllh da kyar idan baxan kai wannan xancen
kotu gobe ba, don ya gigita ni shiga bandakina biyar kafin in xo gidan nan, yanxu haka xancen da nake maki
sae na kara xagawa a gidan nan, ai ko dabba ba a kulle ma baki ba balle mutum" Jiddah dake ta kallonta
tace "Hajja ai ana kulle na doki" Hajja ta saki baki tace "Toh ni doki ce? Ina ruwana da doki xaki ce min ana
kulle na doki, ana maganar mutane me ya kawo na dabba kuma Jiddah? Kawai mata matsiyaciya ki nemi
garkame min baki ban maki komai ba, wllh baki ga ba ko abincin kirki ban iya ci a kan wannan xancen yau
kwana hudu kenan, kwatsam sai ga mummunan mafarkin nan daxu, kin ga kuwa ai ba lafiya, to tun kan a
cuceni a mayar dani Bebiye gwara a xo a biya min tikiti in koma Masar bakina alekum" Jiddah dai
sauraronta kawai take, Hajja tace "Shi kuma yaushe xai dawo daga gararin samaniyar tasa?" Jiddah tace
"Kilan juma'ah ko asabar, Hajja ki xauna in kawo maki ruwa" Hajja tace "Wani ruwa bayan abinci ma
wannan na kasa ci, meye kuma ruwa, naga alama kun dau wannan kess din karamin kess, wllh da a Masar
ne sai an bata kwadon gaske ace ta kulle bakin nawa a gani, Allah sai an mata zindir an xane shegiya
sannan a mika ma yara su yi ta jifa, me na mata xata min haka??" Tana kai wa nan ta nemi waje ta xauna
tana fiffita xufar da tayi da mayafinta, Jiddah ta nufi kitchen dauko mata ruwa da lemo ta ajiye gabanta,
Hajja ta dau goran ruwa daya sai da ta kwankwadesa tass, sannan ta ajiye tace "Rabona da shan ruwa tun
kan inji wannan mummunan batun" Bude kofar parlon aka yi duk suka daga kai, sosai gaban Jiddah ya fadi
ganin Abuturrab ya shigo parlon, suna hada ido ya dauke idonsa fuskar nan tasa a daure, ta sunkuyar da
kai, Hajja ta kalli Jiddah tace "Kika ce min ya tafi aiki?" Kafin Jiddah tace komai yace "Ehh daga can nake"
Hajja ta mike tace "Abinda Allah ya ga xuciyata ko daga sararin samaniyar ne ai sai a hankado min kai
kawai, wllh ina cikin garari Aliyu, gidan Kyauta yayar Hafsah xaka kai ni a Barnawa don girman Allah"
Abuturrab yace "Daga Abuja fa nake yanxu ko hutawa ban yi ba Hajja" Hajja tace "Oh oh Allah, Aliyu
mafarki nayi an kulle min baki da kwado fa? Wa xai xauna da wannan mugun mafarkin idan ba gantalalle
ba" Yace "Toh ki bari in huta na gaji, bayan nayi aiki kuma na sake shiga mota na taho kaduna" Hajja ta
koma ta xauna tace "Toh tafi ka huta ko na minti sha biyar ne, ai ni ba bakuwar xafi bace, banda Ramlah
ma bata san gidan ba ai ita nayi niyyar ta rakani don naga ita dai dai take da ko wani d'an banxa a duniya"
Abuturrab bai ce mata komai ba ya nufi sama, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja tayi kasa da murya tace "Ina
gantallaliyar abokiyar xamar ta ki?" Jiddah tace "Kila tana daki ban sani ba" Hajja tace "Atoh, ina ruwanki
da ita da xaki san inda take dama" Mikewa Jiddah tayi tace "Ina xuwa Hajja" Hajja tace "Toh ni dai kar a
shanya ni, ba ruwana da iskanci da rana tsaka" stairs Jiddah ta nufa, tana haurawa sama ta tsaya corridor
tana tunanin ta je ko kar taje side din nasa, haka kawai ta ji tana shakkarsa sosai, bayan few seconds kawai
ta nufi bangaren nasa tana tafiya a hankali, bude kofar parlon tayi kamar munafuka ta shiga ciki ta gansa
xaune, ta karasa ciki ta d'an durkusa kasa daga gefensa ta ki yarda su hada ido tace "Sannu da dawowa" Ba
tare da ya kalleta ba yace "Thank you" Kallonsa tayi a hankali, jin bai sake cewa komai ba ta mike ta nufi
kofa ta fita ta koma wajen Hajja. Bayan minti ashirin Abuturrab ya sauko parlor kafin nan sai da ya bude
kofar dakin Aneesah ya ji sa a kulle, kallon Jiddah yayi yace "Lend me ur car key" Ta mike tana kallonsa don
babu yabo babu fallasa yayi maganar, ta wuce sama ta dauko masa makullin a dakinta ta risina ta basa, ya
amsa yace "Tashi mu je Hajja" Hajja ta mike tace "Allah yayi maka albarka, mu je in ji ba'asin kulle min
bakina" Kofa ya nufa tana biye da shi ko sallama bata tuna tayi ma Jiddah ba har suka fita, Jiddah ta bi su ta
tsaya bakin kofa tana kallon Abuturrab, ya ki yarda ya kalleta, nan da nan hawaye ya kawo idonta, kamar
ance ya juya ya ga hawaye a idonta, ya jefa mata wani kallo, turo masa baki tayi ta juya ta koma parlon da
sauri. Abuturrab na ajiye Hajja kofar gidan Kyauta ya ciro dubu biyar ya mika mata yace "Hajja gashi idan
xaki koma sai ki samu adaidaita sahu, ni yanxu xan koma aiki ne, nayi mantuwa ne yasa na dawo" cike da
masifa Hajja tace "Yau naga jalala, dama ba da kai xa mu shiga ba ni kadai raina xan shiga?" Yace "Toh ni
macece da xan bi ki mu shiga Hajja, excuse na dauka wajen aiki, jirgi na can a airport din Abuja xan daga
xuwa kano" Hajja tace "Toh na fi jirgi ne? Ko ina ruwana da shegen jirgin naku? Sbda ba bakin uwarka aka
yi niyyar garkamewa ba shi sa baxa ka bi ni mu shiga ba ko??" Dariya ta basa amma ya cije yace "Toh sai in
bar aikina in shiga ayi ta xancen garkame baki da ni?" Hajja tace "Toh Allah ya isa, ai sbda kai da uwarka
aka yi niyyar kulle min bakin nawa Allah ya toni asiri, kuma wllh daga yau ko kasheku naga xa ayi kai da
uwarka shiru xanyi abina in koma gefe tunda gashi ta dalilinku aka nemi hallaka min bakin da nake salati
nake ba Allah gaskiya" Daga haka ta fixge dubu biyar din ta shige gidan tana rafka wani uban sallama,
dariya yayi ya juya kan motarsa ya dau hanyar gida. Yana komawa gida bayan ya haura sama dakin
Aneesah ya bude ya ji a kulle har sannan, ya d'an tsaya sai kuma ya nufi dakin Jiddah ya bude, kwance ya
ganta tayi kukanta ta koshi, ta mike xaune tana kallonsa ya wani hade rai, cikin sanyin murya tace "Kayi
hakuri" yace "Ban yi ba" Tura masa baki tayi ta juya masa baya, ya shafa kansa yana kallonta, sai kuma yace
"Ina Aneesah?" Ta kallesa a hankali tace "Nima ban sani ba" ya karasa dakin ya rungume hannunsa yana
kallonta, lkci daya ya dauke idonsa daga kanta, yyi kasa da murya yace "Make me a cup of tea" daga haka
ya juya ya fita, ta mike a hankali ta fita ita ma ta sauka downstairs. Bangarensa ya tafi ya dauko spare key
ya bude dakin Aneesah thinking ko kulle kanta tayi a ciki, amma babu kowa dakin haka ma bathroom din...
A ranan Abuturrab xai koma Abuja don ko awa biyu bai yi niyyar yi ba a gidan, but ya kasa tafiya yana ta
xaune parlor downstairs yana jiran ya ga sanda Aneesah xata shigo gidan, Jiddah ta fito daga kitchen tana
kallonsa tace "Na gama in xubo maka yanxu?" Ya daga kai ya kalleta yace "Tun yaushe Aneesah ta fita
gidan nan?" Ta d'an buda hannunta tace "Nima ban sani ba ina daki" Yayi shiru, ta koma kitchen ta xubo
masa girkin da tayi ta fito ta ajiye masa kusa da shi, kallon kirjinta kawai yake da ta durkusa ajiye abincin,
ya lumshe idonsa ya jinginar da kansa jikin kujera, don ba karamin nesa yake kai xuciyarsa ba a kanta tun
daxu, barin da ya shiga dakinta ya ga tana kuka he wish he can hug her tightly and tell her he isn't angry
and he is back all because of her, ta mike tana kallonsa ta wuce sama ta shiga dakinta ta xauna tana
tunanin yanda xata yi Aneesah ta san ya dawo gidan, mikewa tayi ta tafi bangarensa tana kallon wayarsa
da ya bari kan kujera, dauka tayi ta kulle kofar parlon, ta shiga call logs dinsa amma bata san yanda yayi
saving number Aneesah ba, Blossom ta gani can kasa nan da nan ta tuna ta ta6a ganin sunan a phone
dinsa da dadewa tayi dialing number, yana fara ringing aka daga.....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Jiddah tayi shiru, daga daya bangaren ta ji muryar Aneesah kasa kasa tace "Hello My captain..." ta fadi
hakan yayi sau uku, jin shiru Aneesah ta katse wayar ta sake kira, Jiddah ta dinga kallon screen din kamar
baxata daga ba, har ya kusa katsewa sai kuma ta daga a takaice tace "Dama kawai ce maki xanyi ya dawo
tun daxu..." Aneesah ta xabura lokaci daya tace "Captain din?" Jiddah bata ce mata komai ba ta katse
wayar, Ta ajiye masa kan kujera sannan ta fito ta wuce dakinta.. Abuturrab na dawowa masallaci bayan
magrib ya dinga kallon motar da yayi parking kofar gidansa, sai ga Rabi'ah ta sauko daga maxaunin driver
ta bude back seat ta riko Aneesah ta fito da ita, Banda nishi babu abinda Aneesah take tana tafiya da kyar
Rabi'ah na rirrike da ita tana mata sannu, ya dinga kallonsu sai kuma ya shige gate kawai, yana xaune
parlor suka shigo bayan minti goma irin da kyar Aneesah ke tafiya din nan, Aneesah ta kwanta saman
kujera tana sauke numfashi da kyar tace "Ka dawo ne Captain? Hope all is well?" Shiru yayi yana kallon tv,
Rabi'ah tace "Haba dai Captain, kai da ya kamata ka fara tambayar lafiya ka dawo gida baka sameta ba
kuma daga ina take? Sai kuma kayi shiru? To daga asibiti muke" Ko kallonta Abuturrab bai yi ba, Aneesah ta
mike xaune ta jingina da kujera tana nishi tace "Ban yi bacci ba kwata kwata jiya da daddare captain wani
xaxxabi me xafi ya rufeni na rasa yanda xanyi, ga shi drugs da aka min prescribing a hospital kamar shi ya
sake triggering xaxxabin da ciwon kai, na daure da sassafe na fita na kwankwasa ma matarka kofa tana ji ta
ki budewa, har ce mata nayi bani da lafiya ne, wllh sai ce min tayi ita baxata iya fitowa ba bacci take, ban
ta6a xaton haka ba wllh, na dai koma dakina ina son sake shan drugs din nawa amma ban ci komai ba, sai
na daure na sauko downstairs wajen karfe sha biyu tana xaune tana kallo tana cin abincin da ta girka, jin
kamshin girkin ya sa naji amai ya taho min, wllh captain a nan parlon na gama amai na, na gyara wajen
Jiddah ko sannu balle Allah ya sauwake, shine na koma daki nayi ta kiran layin Aunty Safara'u taki dauka
kuma nasan fushi take da ni har yanxu, da na rasa yanda xanyi kai kuma ina tunanin kana bakin aiki sai na
kira Rabi'ah ta xo ta kai ni asibiti, shine sai yanxu fa" Rabi'ah ta ajiye mata ledan magungunan hannunta
tace "Sai da safe Aneesah, Allah ya sauwake ya kara lafiya, ciwo kuma na kan kowa ai...." Daga haka ta nufi
kofa ta fita, Abuturrab ya dinga kallon Aneesah dake sauke numfashi da kyar, yace "Wani asibitin ku ka je?"
Tace "Nima ban sani ba, sai dai a tambayeta, i almost lost conscious a hanya" Bai kuma ce mata komai ba
ya mike ya wuce sama, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, ta tashi ta tafi dakinta da sauri ta kwanta ta
lulluba da bargo, bayan isha Abuturrab ya shigo dakin nata, duk da idonta biyu taki nuna hakan, ya karasa
ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "Ya jikin?" Ta bude ido da kyar tace "Da sauki" yace "Me xa ki ci?"
Tayi kasa da murya tace "Shayi kawai xan sha kar in yi amai" mikewa yayi ya sauka kasa ya shiga kitchen,
yana making cup of tea Jiddah ta shigo kitchen din, ya kalleta sau daya ya ci gaba da abinda yake, ta wanke
plate din hannunta ta ajiye xata fita ta ji yace "Me yasa da Aneesah ta ce maki bata da lafiya kika yi
shunning din ta?" Kallonsa Jiddah take with confusion, ya juya ya kalleta yana jiran amsanta, jin tayi shiru
yace "Just like that?" Tace "Ehh, haka nayi niyya" tana fadin haka ta juya ta fita ya bi ta da kallo,