Showing 81001 words to 84000 words out of 321711 words
Ta sunkuyar da kanta bata
ce komai ba, on a serious note without bothering ko ta gane turancin nasa ko bata gane ba yace "Naga
kina neman fara wuce boundaries din ki a gidan nan, to bari kiji, daga yau, i mean daga yanxu da kike tsaye
nan kada ki sake shigo min parlor idan ina gidan nan, idan kin tashi da asuba kafin in fito da safe dama ki
girka duk abinda xaki girka na safe da rana ki kai dakin ki, karfe biyar na yamma ina sama, sai kiyi amfani da
wannan opportunity din ki sakko ki dafa abinda xa ki ci da daddare, kafin shidda ki tabbatar kina dakin ki....
Am i clear?" Ita dai kanta na kasa, ya mata wani tsawa yace "Baki ji na ne?" Ta dago kanta hawaye cike
idonta tace "Toh" Yace "Get out.. Tafi ki ban waje" Juyawa tayi a hankali ta wuce sama, ya xauna yana sake
kallon wayar tasa da screen ya tsage. Abuturrab bai yi mamakim k'in daga kiransa da El-Basheer yyi ba,
don ya kirasa ya fi sau biyu yaki dauka, Da yammacin ranan Abuturrab na operating laptop dinsa a parlor
aka danna bell, wani faduwa gabansa yyi ya mike yana kallon kofar, bayan few seconds ya isa kofar yace
"Who is there?" Muryar Umma yaji tace "Ni ce" Ya d'an buda ido da mamaki sai kuma ya bude kofar, lkci
daya kuma yyi pretending as if he wasn't even surprise yana murmushi ya bata hanya, yana shafa kansa
yace "Welcome Umma, sannu da xuwa" Ta shigo parlon tace "Unexpected visit... Ban ce xan xo ba ko?"
Yace "Ai ba sai kin ce min ba Umma, ya hanya?" Ta xauna saman kujera tace "Alhmdlh, ina jiddar?" Ya d'an
kalli sama sannan yace "Tana sama" daga haka ya wuce sama, calmly ya bude kofar dakinta, xaune ya
ganta can karshen gado ta takure waje daya, tana ganinsa ta sauke kafarta ba tare da ta yarda ta sake
kallonsa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja yyi, kana ganinta kasan kuka tayi sosai, ya hade rai yace "Wani
abu aka maki da kika xauna kike kuka?" Ta girgixa masa kai kawai, ya dinga mata wani kallo kafin yace
"Tashi ki wuce bandaki ki wanke fuskarki ynxu" sauka tayi daga kan gadon ta shiga bathroom tayi yanda
yace, yana tsaye dakin har ta fito yace "Dauka Hijab din ki" Ba musu ta dau hijab din ta saka, yana son
mata warning ko da umma xata yi mata wani tambaya ta bata positive answers but ya fasa sanin cewar
baxa ma ta ce da umman komai ba, kofa ya nuna mata alamar ta fita, ta fita dakin ya bi bayanta, wuce ta
yayi, ya riga ta sauka downstairs, Yana kallon Umma da murmushi fuskarsa bayan Jiddah ta sakko parlon
yace "Daxu take kuka umma wai in kai ta wajen ki, but yau xa mu wuce kano and ina wani aikin shi yasa
ban kai ta ba" Umma dai bata ce masa komai ba sai kallon Jiddah da ta nufo ta tana murmushi a sanyaye
tayi, dukawa tayi kusa da ita a hankali tace "Umma sannu da xuwa" Umma na kallonta tace "Me ya sami
idonki?" Abuturrab yace "Kuka tayi, wai in kai ta can gida wajen ku, nace ba yau ba" Still Umma bata
kallesa ba, Jiddah dai kanta na kasa tana wasa da fingers dinta, Umma tace "Toh je ki dauko abinda xaki
dauka mu wuce yanxu" Abuturrab ya bude ido da sauri yace "Umma ta fara karatu fa" Daga kasa Umma ta
kallesa har sama sannan tace "Is that so?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh Umma, tare xa mu koma kano da
ita" Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah tana kallonsa, Umma tace "Toh shkkn, Allah ya taimaka, dama
anguwan na shigo shine nace bari in karaso mu gaisa, i will take my leave now, tunda na same ku lafiya
Alhmdlh" Yace "Umma da wuri haka, ki bari after magrib...." Ta katse sa tace "Ohk da magariban xa ku dau
hanyan kanon kenan?" Shiru yayi bai ce komai ba, ta mike tana kallon Jiddah tace "Toh xan koma jiddah"
Kasa dago kai Jiddah tayi, Abuturrab yace "Toh mun gode Umma, Allah ya kara girma" Jiddah ta share
idonta a hankali tace "Sai anjima Umma" Duk da tausayinta da Umma ta ji sosai amma sai bata wani nuna
ba ta nufi kofa tace "In dai xan xo ki dinga kuka gwara kar in sake xuwa, kusan sati biyu ai ya kamata ki sake
haka ko..." Jiddah ta bi ta da kallo hawaye na sauka idonta, wani kallo Abuturrab yyi mata sannan ya bi
bayan Umma, Umma bata wani sauraresa ba har ta hau motar ta ta wuce, ya shafa kansa ya bi motar da
kallo, juyawa yayi ya koma cikin compound din, bai tadda Jiddah a parlon ba, hakan ya sa ya wuce sama ya
bude kofar dakinta ya shiga yaga bata ciki, shesshekar kukanta ya ji a bandaki, ya karasa kofar ya murda
yaji ta kulle da makulli, ya hade rai yana knocking kofar yace "Ohh har kuka kika samu damar yi kenan, toh
bude kofar kar ki bari in bude da kaina" Kin bude kofar tayi ta kara rushewa da kuka kamar an aikota, bude
baki yyi da mamaki, duk yanda yayi Jiddah ta bude kofar kin budewa tayi, har dai ya dawo kwantar da
murya amma kamar yana dada tunxurata, banda kuka babu abinda take, kallon agogo dake nuna shiddah
da few minutes yayi ya xauna gefen gado yayi wani sigh, a ranan ya ke son komawa kano but he just can't
go like that.... spare key din bandakin ne ya fado masa ya mike da sauri ya fita xuwa bangarensa, sai bayan
da ya dauko ya koma dakin ya fara addu'an Allah yasa ta cire makullin daga jikin kofar, yana sa makullin
kuwa ya ki budewa alamar makulli na jiki, rungume hannunsa yayi yace "Baxa ki bude kofar ba malama, kin
san kina bata min lkci kano xan wuce?" Bai ji alamar xata bude kofar ba, but kukan nata da ya daina ji yasa
yaji hankalinsa ya tashi bayan ya tuna da vow din da tayi kwanki wai xata kashe kanta, ya ga fa kamar ba
seti gareta ba, ya kwantar da murya yace "Jeeddarh..." Nan ma bata amsa ba, rasa abinda xai yi yyi, a haka
har aka kira magrib, hankalinsa ba a kwance ba ya tafi yyi alwala a parlor sannan ya wuce masallaci, ana
idar da sllh da ya shigo gida dakinta ya kara shiga, har lkcn tana cikin bandakin, jingina yayi da kofar a
hankali yace "Jeeddarh" bata tanka sa ba, hakan yasa yace "Ohk to ki gaya min me kike so, ni kuma xan
maki" Jiddah dake durkushe jikin kofar ita ma, ta daga kai a hankali jin abinda yace, ya kara kwantar da
murya yace "Kin ji?" Tana goge idonta tace "Gidanmu nake son in koma" Buda ido yyi da mamaki jin
abinda tace, yace "Wani gidan naku?" Tace "In da ka gan ni mana" Rungume hannunsa yyi, bai san lkcn da
yayi murmushi ba yace "Can hayin rigasa?" Tace "Ehh" yace "Kin tabbatar?" Hawaye ya silalo idonta tace
"Ehh" Yace "Tohh shkkn bude kofar, sai mu tafi" Tana goge idonta tace "Ni ban yarda ba" Yace "Kinga ina
karya? Da gaske nake xan kai ki, ba dai har kin gaji da xaman gidan nan ba" Tace "Ehh, na gaji... Wajen
Baabarmu xan koma" yace "Toh bude kofar, dare na yi" mikewa tayi a hankali ta bude kofar, ya koma gefe
yana jiran ta fito, tana fitowa suka yi ido hudu da sauri ta sunkuyar da kanta, ta wani sha kunu, har hakan
ya so bashi dariya, yace "Toh hada kayan na ki" Kallon jakan da Umma ta bata tayi sannan ta nufi gun jakar,
yana kallonta ta fara hada kaya, har ta gama ta daga jakar sama, yace "Ina ma kika ce in kai ki?" Tace
"Gidanmu nace" yace "Toh tafi parlor da jakar ki jirani" Jan trolley din ta fara yi ta nufi kofa ya bi ta da ido
har ta fita sannan shi ma ya fita ya tafi bangarensa, Jiddah na parlor ta xauna kasa tana jiransa, banda wasa
da yatsunta babu abinda take har ya sakko rike da makullin motarsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Mu je"
mikewa tayi tana jan trolley din ta bi bayansa, bakin motarsa ta tsaya ganin ya bude Booth ta saka trolley
din a ciki, sannan ta tafi ta bude gaban motar ta shiga, ya tada motar suka bar gidan. Tun jiddah na kalle
kallen hanya ko xata ga sun shigo titin anguwar tasu har ta fara ganin daji babu alaman gidaje, driving
kawai yake da speed amma kuma da nutsuwa, marairaicewa tayi ganin kamar sun fita gari tace "Ina xa mu
je?" Ko tanka ta bai yi ba hakan yasa bata sake ce masa komai ba, sai hawaye, duk da baccin da ta dinga ji
har suka shigo garin kano wajajen karfe sha daya bata yi baccin ba, hotel din da ya ke sauka ya tafi yayi
lodging yayi ordering abinci, bin sa kawai take yana tafiya har suka isa dakin da aka basa, tana shiga dakin
ta jingina da bango ya kulle kofar ta dinga bin dakin da kallo, ya ajiye makullin motarsa da wayoyinsa gefen
gado ya shiga bandaki ya dauro alwala ya fito, ita dai tana ta tsaye, ya shimfida darduma yayi sllhn isha,
bayan ya idar da sllh aka yi knocking kofar, mikewa yayi ya isa kofar ya bude, ya amshi abincin da aka kawo
sannan ya kulle kofar, shayi ya sha, sai pepper soup din hanta bai bude takeaway din shinkafar ba ya mike
ya dau wayarsa yayi dialing number Aneesah don tun yana hanya take ta kiransa, fita yyi dakin ya kulle
daga waje, Jiddah ta bi sa da kallo, xaunawa kasa tayi hawaye na taruwa idonta bayan kusan minti sha
biyar ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito tayi magrib da isha, kwanciya tayi kan darduman
nan da nan bacci ya dauketa. Karfe sha biyu da mintuna Abuturrab ya shigo dakin abincin ya fara dubawa
ko ta ci ya ga bata ci ba, ya xauna gefen gado ya sa hannu ya buga gefen kafarta bude ido tayi ganinsa ta
mike xaune da sauri, babu yabo bbu fallasa yace "Dauki abincin ki ci" Tace "Ni na koshi" wani kallo ya mata,
ta jawo abincin ta bude ta fara turawa, bai takurata sai ta ci da yawa ba, bayan ta rufe sauran yace "Tafi ki
wanke bakin ki kiyi wanka" Bata iya ta ce masa komai ba amma ji tayi kamar ta fashe da kuka, ta mike ta
cire Hijab din jikinta ta linke ta ajiye ta bude jakarta ta ciro sabulu da sponge, toothpaste da toothbrush,
xata wuce bandakin yace "Tawul din fa?" Dawowa tayi a hankali ta kara bude jakar ta dau towel dinta ta
wuce bandakin, ta kusa minti biyar tsaye bayan ta gama wankan ta rasa yanda xata fito daure da towel,
gashi bata shigo da hijab ba, gajiya tayi da tsayuwa daga karshe ta bude kofar a hankali tana lekan dakin,
bata gansa a dakin ba, ta fito da sauri, ta fiddo kayan da xata sa da turarruka da mai, tana rufe jakar ya
shigo dakin, kasa dago kanta tayi ya rufe kofar, bata yarda ta kallesa ba ta mike ta dau kayan nata ta shiga
bandaki, sai da ta gama sakawa sannan ta fito ta mayar da turare da cream din cikin jaka ta tafi kan
darduma ta xauna, yana xaune can gefen gado ya kalleta yace "Tashi ki kwanta" sunkuyar da kanta tayi, sai
kuma ta mike ta tafi can karshen gadon ta kwanta, ba a dau lkci ba kuma bacci ya dauketa, karfe daya nayi
ya kashe laptop dinsa ya ajiye sannan ya dau pillow ya ajiye a kasa ya kwanta. Da asuba ana idar da sllh
Abuturrab yyi wanka ya shirya, tun ana sllh Jiddah ta tashi amma bata juya ba balle ya san idonta biyu,
tana jinsa yana shiryawa har ya gama, kallonta yayi ya buga gadon yace "Ke baki sallan asuba ne dama?"
Mikewa xaune tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta wuce bandaki, kwance ta gansa da ta fito idonsa a
lumshe ta tada sllh bayan ta idar ta kwanta kan darduma, karfe bakwai da few minutes Abuturrab ya tashi,
tashinta yyi ta mike xaune da sauri, yace "Anjima idan anyi knocking ki bude kofa ki karbi abinda aka kawo,
apart from that ban ce ko bakin kofar ki je ba, kin ji me nace maki??" A hankali tace "Toh" Sai da ya fara
kunna TV dake dakin ya kai tashar hausa sannan ya dau jakarsa ya nufi kofa ta bi sa da kallo har xai fita ya
juyo, da sauri ta dauke idonta daga kallonsa, yace "Saura ki bude kofar a haka baki sa hijab ba idan aka
kwankwasa" bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, mikewa tayi ta hau saman gado ta ci gaba da
baccinta. Karfe takwas taji an kwankwasa kofa, mikewa tayi har ta nufi kofar haka ta dawo da sauri ta dau
hijab da ta daura kan riga da wandon jikinta na bacci, sannan ta nufi kofar ta bude, abinci aka kawo mata
ta amsa tare da godiya ta juya ta koma cikin dakin, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta yi breakfast din da
aka kawo mata. Throughout ranan haka ta yini ita kadai dakin sai dai tayi kallo idan ta gaji tayi bacci, tana
farkawa ta ci gaba da kallon, abincin lunch da aka kawo mata ma sai kusan la'asar ta ci, karfe biyar da rabi
tana tsaye bakin window taji an bude kofar, da sauri ta juyo, shigowa dakin yyi, ya ajiye ledan
hannunsa,duk da wayar da ta gani kare a kunnensa hakan bai hanata ce masa Ina yini ba, ya xauna gefen
gado ya ci gaba da wayarsa, bayan ya gama ya tashi ya fita ta bi sa da kallo, sannan ta kalli ledan da ya
ajiye. Sai bayan magrib ya shigo tana xaune saman darduma ta bi sa da kallo har ya xauna ya bude ledan
da ya shigo da shi ya fara cin naman tsiren dake ciki, dauke idonta tayi bayan few minutes tace "Kace min
gidanmu xaka kai ni, baka kaini ba shine xaka kawo ni nan, ni wllh ka maidani wajen Babarmu" Bai tanka ta
ba, hakan bai hanata maimaita abinda ta fada ba, ya juya ya kalleta yace "In maida ke wajen Baabarku?"
Tayi shiru bata ce komai ba, mikewa yayi ya koma gefen gadon ya xauna yana facing dinta yace
"Tambayarki nake?" Ta sunkuyar da kanta tace "Ehh kai kaini wajenta" Yace "Ohkk... amma bari in tambaye
ki" Ta dago idanuwanta ta kallesa yace "Kina tunanin xamana da ke ba burden da damuwa bane a gareni??
Ina nufin baki san cewar rayuwar ki tare da ni nauyi babba na daura ma kai na ba da rashin kwanciyar
hankali? Do you think ko matata ba iyakar abinda xan mata nake maki ba? What's so important about
staying under same roof with you? Kina tunanin ni ajin ki ne da nake kula ki nake kula al'amuranki? Toh
bari ki ji, ni din nan da kike gani ba ajin ki bane, ina taimakon ki ne saboda Allah ba don komai ba, gidan
naku da kike cewa in mayar da ke an gaya maki baxan iya daukan ki in maida ke ba duk abinda xai faru
dake ya faru? Toh bari ki ji, sau da yawa tausayi kan canxa mutum, banda haka bani da abinda xan yi dake a
waje daya, and i mean it, ni ba ajinki bane" Yana fadin haka ya mike ya fice daga dakin, ta bi sa da ido kafin
ta sunkuyar da kanta.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow mu
Abuturrab ya dau throw pillow dake gefensa ya jefa ma El-Basheer da ya bi Jiddah da ido, sae a sannan El-
Basheer ya dauke idonsa, sai kuma ya daga kafada as if counting his words yace "Ita ce.... Ex-wife din
taka?" Abuturrab na kallonsa da wani expression yace "Does that warrant u to stare at her that way??" El-
Basheer yyi shiru yana danna wayarsa kamar baxai ce masa komai ba, sai kuma ya kallesa yace "Naga
kamar ganinta ya fi jin ta ne, ita ce yar hayin rigasar?" Abuturrab ya masa wani kallo ya dau remote yana
canxa channel, El-Basheer yace "Ko dai a gidanka ne ta samu transformation din nan, she's got a beautiful
shape" Abuturrab ya mike, sounding fed up yace "Stop this plss El-Basheer... U r sounding lousy" El-
Basheer yana shafa gashinsa yace "Lousy? Ohk sorry about that" Abuturrab ya dinga kallonsa da wani
expression that is expressing how really angry he is, ya koma ya xauna yana canje canjen channel, El-
Basheer ya bi parlor din da kallo yace "I need something cold to take now, haka kake treating visitors?"
Mikewa Abuturrab yyi ya wuce kitchen, El-Basheer ya bi sa da kallo, fridge ya bude ya dau bottle water
daya sannan ya fito, sama ya wuce yana cewa "In dai ni xan kawo maka ruwa xaka dade baka sha ba" El-
Basheer ya bi sa da kallo yana d'an murmushi, can ya girgixa kai, bude kofar dakin Jiddah Abuturrab yayi ya
shiga.... xaune ya ganta ta takure waje daya, tana ganinsa ta gyara xamanta tayi narai narai da ido tana
kallonsa, ya ajiye ruwan gaban mirror ya juyo fuska a tamke yace "Me nace maki daxu?" Shiru tayi, yace
"Ba ce maki nayi kar ki fito ba all through?" Hawaye ya cika idonta tace "Ruwa ai naje in dauka, ba ce min
kayi in daina shan na bandaki ba" Yace "Me ya hanaki dauka daxu da kika sakko" shiru tayi bata ce komai
ba, yace "Xo ki dauka" mikewa tayi ta tafi gun madubin ta dau goran ruwa, yana kallonta yace "Sannan ba
nace