Showing 12001 words to 15000 words out of 321711 words
share hawayen idonta tayi ta leka ledan taga dari biyar sababbi dal a rafe, sosai gabanta
ya fadi, ta kasa kwakkwaran motsi, wani almajiri ne yace "Awaran ki na konewa" Da sauri ta juya ta sauke
awaran, ta xauna xuciyarta na bugawa da karfi, muryar Hansai taji a bayanta, Hansai ta ajiye bokitin wani
awaran tana cewa "Ta dari biyar ce wnn, gaba daya ya kama dubu biyar da dari biyar...." ganin awara ya
kone a mai tayi tsit tana xare ido, lkci daya ta saki salati da karfi tace "Na shiga uku awaran kika kona min
Jiddah???" A mugun tsorace Jiddah ta mika mata ledan kudin tace "Baabarmu wllh wani ne ya xo ya kawo
min wnn wai in kai maki kar mu sake fitowa sai bayan kwana biyu...." Hansai ta karbi ledan tana duba ciki
da sauri, xaro ido tayi tana kallon tulin kudin cikin ledan, lkci daya ta dinga bin anguwan da kallo, murya
can kasa tace "Daga ina yake?" Jiddah ta buda hannu har sannan jikinta na rawa tace "Wllh ban sani ba"
Hansai tace "Dauko jarkar man da roban awaran mu wuce gida ai ya kare ma" A haka Jiddah ta kwashi
kayan awaran ta bi bayan Hansai dake tafiya da sauri da sauri, A bakin kofar dakin Hansai Jiddah ta makale
tana kallonta tana ta faman kirgan kudi duk ta hada xufa, har ta gama kirgen tana xaro ido tace "Dubu dari
a wannan marran ni Hansatu, Allah yyi ma bawan Allahn nan albarka, yanda ya taimaki marayu Allah ya
taimakesa haka shi ma, kaiii a duniyar nan ma dai xaman wasu toshe hanyar alkhairi kawai yake, banda
haka daga rasuwan Isuhu kamar daga sama Allah ya jefo bawan Allah ya bamu dubu dari cif cif, yaushe
rabon inga dubu ashirin da idona ni Hansatu" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta xuciyarta na mata xafi bata
ce komai ba, Hansai tace "Maxa ki sa ruwa kiyi wanka kema ko kya ji dadin jikin ki, kinga dai mutuwar nan
alkhairi ne garemu sai kiga Allah yyi ta bude mana hanyoyi iri iri, aa ni dai wllh gwara da ya bamu hanya
mu san me muke ciki a duniyar, to da ya baki kudin sai yace maki me?" Cikin sanyin murya tace "Yace kar in
sake fitowa sae bayan kwana biyu" Hansai ta fashe da kuka tace "To dama banda talauci me xai sa mijina
ya mutu in fara awara a ranan da aka yi sadakan uku, ai sai dai talaucin dama" Ta kara rushewa da kuka
tana matsar kwalla da bakin xaninta, juyawa jiddah tayi a hankali ta bar bakin kofar tana dada jin mutuwar
mahaifinta kamar a mafarki wanda hakan yasa hawaye kawowa idonta.
*Still on free pages kar labari ya dauko maku dadi ku ga an datse don free pages din ba yawa ehee, u can
proceed with payment sbda kawai a ci gaba ba sai an tsaya ba after free pages din, that is idan kunyi
payment kenan fahh....*👌🏻
Tunda dai littafin me sunana ne wannan kunsan baxan gantalar da littafin ba, don haka kar kuyi fargaban
komai ku ma baxan gantalar da xuciyoyin ku ba a gaskiya😹😹
Ping 07087865788 for payment details.
💖💖 Jiddatul Khair💖💖
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
5.....
Alhaji Usman ne xaune parlonsa tare da Hajiya Hauwa, ya ajiye wayar hannunsa yace "Toh ke ya kika ga
Madam?" Ummi tace "Aa in dai tana so babu wani matsala daga gareni sai yanda kace" Ya jinjina kai yace
"Toh shi Ahmad din ne yace yana sonta?" Ummi tayi murmushi tace "Toh wannan kuma gaskiya i can't say
Alhaji" Abba yace "Toh sai na fara magana da shi Ahmad din da Ramlah, don ke da kanwar nan taki na lura
kanku kadai ku ka sani" Yana murmushi ya kare maganar, tayi 'yar dariya tace "Aa ai baxa ayi masu dole ba
dama" Yace "Toh Allah yayi xabi mafi alkhairi dai" Ta amsa da Ameen. Bayan sati daya aka saka ranan bikin
Ahmad da Ramlah wanda xa ayi bayan wata uku. Abuturrab na gidansa na Abuja tare da Ahmad da
shigowarsa gidan kenan, banda kamshi bbu abinda ke tashi a gidan, ko ina so very neat and tidy kai kace
da mace a gidan, Ahmad ya fito daga kitchen rike da cup din coffee yana juyawa da spoon yace "Matar
gidan bata iso ba har yanxu kenan" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa, Ahmad yyi wani dariya yace "Ka
gama yaudaran yar mutane daga karshe ka samu yar sweet sixteen ka aura abun ka" Abuturrab yace "Sai
ince na auri me? Ashe xaka sha mamaki kenan idan kaga na auri Aneesah" Ahmad yace "Gaskiya don ban
ta6a sawa a rai cewar xaka auri Aneesan nan ba, ku dai gama holewan ku tayi auren ta kayi naka"
Abuturrab bai kuma ce masa komai ba ya maida hankalinsa kan TV dake aiki, Ahmad ya nemi kujera ya
xauna yace "To in har da gaske sonta kake da aure kayi magana mana a saka mana rana daya gaba daya"
Abuturrab that is already getting pissed up yace "You dont have to tell me what to do with my life dude..."
Dariya Ahmad yyi yace "Of course, especially in a case like this" Tsaki Abuturrab yayi ya mike ya dau
wayarsa ya wuce daki ya bar masa parlon... Ahmad na gama shan coffee din ya mike ya bisa xuwa dakin,
xaune ya samesa da wayarsa yana magana alamar video call yake, Abuturrab ya kallesa sannan yace "Toh
gashi nan ya shigo sai ku gaisa" Ahmad yace "Waye?" Abuturrab ya mika masa wayar, amsa yayi yana
kallon screen din, suna hada ido ya buda baki yace "Mutanen Egypt ne dama" Bai rufe baki ba tace "Waye
wannan???" Dariya yayi yana kallon uban glass da ta saka a ido fuskarta duk ya cika screen din wayar yace
"To glass din kuma da kika maka haka wa ya ara maki?" Ji yayi tana cewa "Farida xo ki mayar min da fuskar
Aliyu don Allah, kamar ya shiga wani kiran fuskar wani nake gani" Wata yar budurwa ce ta leko wayar ta
xaro ido tace "Lahh Hajja ai Yaya Ahmad ne" Warce ta kira da Hajja tace "Kaji wani xance to ni ina ruwana
da shi xa a sako min fuskarsa, ki mayar min da fuskar Aliyu nace, idan kuma baxai yiwu ba ki kashe kawai,
waye kuma wani Ahmad, ni na san shi" Ahmad dake ta dariya yace "Nima ae ba saninki nayi ba kawai miko
min wayar aka yi" Hajja ta sake wayar ya fadi tace "Ni dai na shiga uku, A gaskiya wannan ai walakanci ne
da cin fuska, ya xan dinga magana da Aliyu fuskar wani kato ya fito, wayar taki ce ta lalace ko wa'adin da
aka debar mana na magana da Aliyun ne ya kare aka sako min fuskar wani can" Farida ta ma rasa abun
cewa sai dariya take, Ahmad ya katse wayar ya jefa gefen Abuturrab shi ma yana dariya, Abuturrab yyi
murmushi yace "Yanxu fa take tambayar ka shine ka shigo na baka fa...."
Iyah ce tsaye kan jiddah dake ta kuka kamar an aikota, A fusace tace "Toh meye amfanin wnn shegen
kukan da kike ne wai, nace ki hado tsummokaranki in sa ki mota tunda da kudin ki a hannuna ki tafi legas
wajen Salame kawai" Jiddah na kuka tace "Toh Iyah idan iliyan ya hadu da ni a legas din fa? Shi ma fa a can
yake aiki ai" Iyah tace "Legas din bai fi Najeriya girma ba aka ce maki, ta ina xai ganki a gari me girma haka"
Shiru Jiddah tayi tana kallonta wasu hawayen na sauka fuskarta, Iyah tace "Ni dai ba ruwana ina kokarin
ganin na rufa maki asiri kar a aura maki takadiri kina min gardama, hakkin makotaka fa nake son in fita,
banda haka me na hada dake Jiddah?? Sannan ni ce mutum ta karshe da Allah ya ba iko nayi hirar karshe
da mahaifinki kafin ya mutu, to sai in xuba ido ki tagayyara ya kullace ni duk inda yake?" Jiddah ta sauke
idonta dake xuban hawaye xuciyarta yyi rauni, Iyah tace "Atoh babu ruwana wllh, ba dai gobe xata tafi
kasuwar tasha siyo kayan sana'arta ba, sai ki shirya tana fita in kai ki tasha kawai, ko da tirela ne sai ki bi
xuwa legas din, amma idan ba haka ba shkkn rayuwarki ta lalace idan aka aura maki Iliyasu" Iyah na kai wa
nan ta tafi gun tuwonta dake kan murhu tana cewa "Na fita hakkin ki duk da ba dangin iya ba na baba,
amma hakkin makotaka fa??" Jiddah dai gaba daya jikinta yyi sanyi, she is too young to even think straight
for her age, hakan yasa taji gwara kawai ta gudun don gashi har an xo an sa mata rana wata daya dai dai da
Iliyasu a yau.
Aunty na kallon Nafisa, cike da fada tace "Tashi ki fita ki ban waje" Ba musu Nafisar ta mike ta fita kamar
xata yi kuka, Aunty ta dubi Abuturrab dake dakin yana kallonta tace "Wllh baka gansa ba Captain, ni dai
ban ta6a ganin haka ba, banda yarinta da dolanci me xata yi da shi don Allah??" Abuturrab na cin Apple
din hannunsa yace "Meye da shi wai Aunty?" Cike da takaici Aunty tace "Don dai sai da yamma ka dawo
jiya da ka gane ma idonka...." Yace "Aa ni a garin nan ma nayi sllhn juma'ah, private jet muka biyo daga
kano, sha biyu da rabi ina kaduna..." tace "To a ina ka tsaya sai bayan la'asar ka dawo gida?" Yace "Muna
tare da wasu abokanmu" Aunty tace "Shi yasa, ai da ka gansa wllh... Muna xaune fa jiya da safe kamar
abun arxiki tace mana wai Salis yace xai xo bayan an sakko juma'ah mu gaisa, na xata abun arxiki ne har da
sa masu aiki su tayata yi masa snacks iri iri wai ashe gantalalle xata kawo mana..." Abuturrab dake ta
kallonta yace "Toh meye da shi baki fada min ba har yanxu" Tace "Toh kaga Captain tun daga bakin titi da
kafa ya tako har nan, ashe ko motar ma bashi da, sai kaga wani yakunannen yadin da ya sa bbu gugan
arxiki, kana ganinsa dai kaga 'ya yan ya ku bayi, ni ko a raina nace ko ina wannan yarinyar ta samo mutumin
nan haka, ni wllh a bakin stairs na tsaya amsa gaisuwarsa ban yarda na karaso parlon ba" Abuturrab yyi
murmushi ya kai Apple dinsa baki yace "Wani sana'a yake yi?" Wani kallo ta jefa masa tace "Sana'a, wa ke
ta wani sana'arsa banda abun ka, ko ka mance da wannan saying din that goes thus... The way u dress will
be the way u will be addressed??" Abuturrab ya gyada kai kawai bai ce komai ba, tace "Wllh na sake
ganinta tare da shi Allah sai na ji mata ciwo kowa ma ya huta, ita kuma Ummi da taya bera 6ari sai wani
nan nan take da shi, tarba dai yanda kasan mutumin arxiki haka tayi ma yaron, ni ko kunya kamar in nutse
wllh, Salem kuma inda ya burgeni ko kallonsa bai yi ba da ya shigo parlon kawai yyi wucewarsa daki..."
Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta...." Tace "Ameen sai ka kirata and talk sense
into her head... Ba ni xata kwaso ma abun kunya ba" Mikewa yayi, tayi saurin cewa "Captain ban kai ka
kaje kaga filin da na siya ba ae" Yace "Xuwa gobe in sha Allah" tace "Lahadin xaka koma aikin?" Yace "Idan
Allah ya yarda" Tace "Wancan satin kasa nayi maka tamarind drink baka dawo ba..." Ya shafa kansa yace
"Wlh daya daga pilot din da xai yi piloting jirgi daga lagos xuwa port Harcourt bai ji dadi ba shine ni nayi,
wnn satin ma ban yi niyyar dawowa ba coz i was so stressed out during the week" Tace "Gashi ko ka xo
kadunan ba wani hutawa kake ba tunda ba xama kake gida ba" yyi murmushi kawai, tace "Sai kaji an sa
ranan Ahmad da Ramlatu" Yace "So Abba told me" Tace "Atoh bai fi mata ba, yar uwarta ta tsaya kula ya
ku bayin garin nan, Ahmad ai d'an gayu ne d'an boko ga hankali da nutsuwa duk da dai ni ba wani shiri
muke da shi ba, though auren xumunci ne ma ai amma gwara hakan, Nafisa ma tace min ai tasan tsohuwar
Budurwarsa Maryam islamiyyar su daya kafin ta canxa islamiyyan" Abuturrab ya nufi kofa yace "To Allah ya
kyauta" Tace "Bayan an gama da na Ramlah sae a dawo naka da Aneesah ko?" Murmushi yyi yace "Allah ya
kai mu lokaci" Daga haka yyi mata sallama ya fita yana duba agogon wrist dinsa, kira ne ya shigo wayarsa,
ya duba ganin Aneesah ya daga ya kai kunne yace "Don't tell me har kin sauka?" Tace "God!!! Nima Don't
tell me baka fito ba Captain" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ban dade da shigowa gida ba... But in few
mins time xan karaso I'm sorry" Bai jira me xata ce ba ya katse wayar ya fita ya hau motarsa.... Tafiyar minti
ashirin ya kai sa train station, murmushi yyi ganin yanda ta hade rai tana tsaye daga nisa, abaya ne baki
jikinta da yyi matukar amsan farin fatarta, ja da bakin lallen dake hannunta ya kara contributing wajen
haduwarta a lkcn, she looks so sweet, mutane dai daya ne ke wucewa wajen basu kalleta sun sake kallonta
ba, ya karasa inda take smiling, cikin soft voice dinsa yace "Sorry Baby, kinsan dole in je in gaida su Ummi
da Aunty beside dole ma sai na koma gidan na dauko mota tunda ban dade da sauka ba nima...." Cike da
shagwaba tace "Kasan mutane nawa suka tambayeni numbata tsayuwar da nayi nan yanxu" Yace "Sai kika
basu kenan" Ta juya masa fararen idonta ta ki cewa komai, murmushi yyi ya amshi trolley din hannunta ya
fara tafiya xuwa gun motarsa tana biye da shi tana kallonsa don komai yyi burgeta yake. A hankali yake
driving din Aneesah dake gefensa tace "I learnt about Ahmad's engagement with Ramlah" idonsa na kan
titi yace "So i heard also" Tayi kasa da murya tace "To mu kuma namu fa?" Still bai kalleta ba yace "Xa ayi"
Tace "Yaushe??" yace "Am trying to put things in order first, i don't get why u are in a rush Aneesah, ba dai
ni nace xan aure ki ba, meye kike damun kanki haka? Do i look like a liar or do my words sounds
deceptive?" Ta kai hannunta kan nasa cikin sanyin murya tace "I just can't imagine loosing u My Captain, i
just can't...." Yace "Keep ur mind at rest Neesah, i am all urs and urs alone" Yana fadin haka ya sakar mata
murmushinsa dake kara narkar da xuciyarta, dai dai nan kuma ya kai layinsu Jiddah, yau bata awara a bakin
titin don babu alamar ma ta fito, sai dai mutane ne cike fal a d'an layin nasu, a hankali yake driving din
yana kallon cikin layin, Aneesah dake kallon direction din ita ma tace "What's happening there, ko anyi
rasuwa ne?" kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ko in sauke journalist taje ta gano mana???" Dariya
tayi tace "Oops a wnn local area din xanyi journalism dina Captain? Haba this is so disgusting..." Tana
magana tana yamutse fuska, shi dai bai ce komai ba yana ci gaba da driving dinsa, can gidan Kanwar
babanta ya ajiyeta a unguwar sarki, bayan ya yi mata few shopping na kayan ciye ciye, ta sauka motar
bayan yyi parking tana kallonsa, shi ma ya sauko ya fiddo mata da trolley dinta ya kai bakin gate din ya
ajiye, ta dau ledan shopping din da yyi mata tana kallonsa bayan ya dawo cikin sanyin muryarta tace
"Thank you My Captain, plss ka daure ka xo anjima da daddare mu yi hira..." Ya kashe mata ido yace "Ohk
babe...." Daga haka ya shiga motarsa yyi reverse ta bi sa da kallo har ya fita layin tana sake jin wutan sonsa
na ruruwa a xuciyarta. Abuturrab na komawa gida yyi parking nan kofar gidansu ya shiga ciki yyi alwala snn
ya fito ya shiga masallaci don ana ta kiran magrib, bayan an idar ya fito masallacin ya shiga motarsa ya
xauna yana danna wayarsa, ajiye wayan yyi yana kallon flowers dake xagaye kofar gidan nasu trying to
imagine the meaning of the crowd they saw earlier a layin yarinyar nan me awara, did someone die again,
tunanin hakan ya sa ya tada motarsa ya bar layin, yana isa yyi parking bakin titi ya dau nose mask dinsa a
motar ya saka snn ya bude motar ya sauka, ashe da daddare sana'a ake yi sosai bakin titin layin, just like
sauran layukan anguwan gaba daya, daga me soya wancan sai me soya wannan, masu siyar da gyada, rake,
abubuwan ci na gargajiya dai yawa... A hankali yake tafiya cikin layin yana yatsine fuska, he is even afraid
kada allergy ya je ya kamasa cos he is so sensitive to anything Filth,... har dai ya kai dai dai kofar gidan da
yaron nan ya ta6a kai sa a matsayin gidansu yarinyar, tsaye yyi yana bin duk wajen da kallo, ginin block ne
sai dai ko plaster babu, sannan gidan karami ne sosai, duk gidajen layin haka suke, banda gida daya da ya
d'an darasu girma shi ma da kadan wato gidan Iyah, wata yarinya ce ke tafe ko takalmi bbu a kafarta, ya bi
ta da kallo yace "Baby...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Xo in aike ki cikin gidan nan" Yarinyar da baxata
wuce shekara shidda ba ta dawo tace "Gidansu Bibalo?" Yace "Ehh, shiga kice ana kiran me awara a ciki"
Da gudu yarinyar ta shiga, babu kowa tsakar gidan don Hansai ko minti biyar ba ayi da fitarta ba, ta shiga
makota, Bibalo kuma tun la'asar rabonta da gidan, yarinyar ta kutsa kai cikin dakin su Bibalo tana kallon
Jiddah dake kwance ta takure waje daya kan yakunannen katifarsu da Bibalo, tace "Wai ana sallama a
waje" Da sauri Jiddah ta mike xaune da idanuwanta da suka yi jajir, duk da tasan Hansai ta fita gidan don
sai da ta bar mata sallahun bakar magana ma kafin ta fita amma hakan bai hana xuciyarta dinga bugawa ba
jin abinda yarinyar tace, A tunaninta saurayinta ne Usman ya xo, kilan ya ji abinda ke faruwa ne, da kyar dai
ta lallaba ta mike ta cire Hijab din jikinta ta dau wankakke dake a linke ta saka, sanyi take ji sosai don
xaxxabi ne jikinta, ta fito dakin ta sa takalminta tana tafiya kamar iska xai kadeta ta fito kofar gidan, babu
haske sosai wajen hakan yasa ta dinga kallon mutumin dake tsaye da fararen kaya ya juya baya, gani tayi ba
Usman bane don wnn yafi Usman tsayi, ta bi layin da kallo tana kara tsoron kada Hansai ta dawo ta tarda
ita a waje