Showing 84001 words to 87000 words out of 321711 words

Chapter 29 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

kada ki sake sa irin kayan nan a gidan nan ba?" Ta kallesa tace "Ai daxu ka gaya min, ina ce daga yau
kace.." Bai kuma cewa komai ba ta koma inda take ta bude ruwan, sai da ta sha ruwan sannan ya juya ya
fita dakin, tsaye ya ga El-Basheer a parlor hannunsa rike da kwalin lemon chivita yana sha, Abuturrab ya
xauna yace "What will u be taking for lunch?" Xaunawa El-Basheer yayi yace "Naaah... I'm full, i just need
rest" Abuturrab yace "Okay mu je sama" Mikewa yayi ya fara tafiya sama, El-Basheer ya mike ya bi bayansa
rike da lemonsa, Abuturrab ya kai sa part dinsa, xaunawa El-Basheer yayi gefen gado cikin bedroom din
bayan ya rufe lemon hannunsa ya ajiye yace "Tsarin gidan yayi sosai, the Architecture is really good" yana
fadin haka ya kwanta, Abuturrab dai na tsaye gaban madubi yana kallonsa ta madubin, can dai yace "Xan
je in dawo yanxu!!!" El-Basheer ya dago yace "Ina xa ka?" Yace "To get lunch" daga haka ya nufi kofa ya
fita, yana isa kofar Jiddah ya bude, ya d'an hade rai yace "Dauko Jilbab dinki, ki sameni waje" Daga haka ya
wuce, yana cikin mota Jiddah ta fito da Hijab har kasa, sai da ta shiga gaban motar sannan yayi horn, mai
gadi ya hau bude gate din, jan motar yayi suka fita gidan, wani babban eatry ya tafi, ya siya ma shi da El-
Basheer fried rice and chicken, Jiddah dae na xaune kan kujeran da ya nuna mata cikin eatry din, sai bin
mutanen wajen take da kallo, baka ta6a cewa tare suke da Abuturrab don bai ko sake kallon inda take ba,
wani mutumi ne ta ga ya ja daya daga kujeran table din da take ya xauna, ya daga face cap dinsa yana
kallonta, ta saci kallon Abuturrab da ke xaune wani table can yana jiran order din da yayi, ta sake kallon
mutumin, ya sakar mata murmushinsa me kyau, ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Hello, how are u
doing, are u waiting for ur order?" Ta saci kallon Abuturrab taga kallon direction dinsu yake ko kiftawa
babu, sosai gabanta ya fadi, cikin rawan murya tace "Yayana na nan fa" Mutumin ya bi eatry din da kallo,
kawai gani yayi Abuturrab ya nufosu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Abuturrab na isowa yana kallon
mutumin babu yabo babu fallasa yace "Didn't she tell u she is married?" Mutumin ya mike yace "Ooh i am
sorry plss" Abuturrab bai tankasa ba ya ja wani kujeran ya xauna facing her directly, mutumin ya kara basa
hakuri, nan ma yaki amsawa har mutumin ya bar wajen, Jiddah ta saci kallonsa suka hada ido, ya jefa mata
wani kallo yace "Ko tausayin rayuwarki baki ji har xaki fara kula maxa ko?" A hankali tace "Ni bani na kirasa
ba kawai xuwa yayi" Yace "Toh bari kiji har sai kin gama jami'a kin fara aiki, kafin ki kalli ko wani namiji balle
har ki kulasa" Ta gyada masa kai kawai, ya ci gaba da danna wayarsa har aka kawo masa order da yyi a
takeaway, without looking at her yace "Me xa ki ci?" ta sunkuyar da kanta tace "Ko meye" tsaki yyi ya mike
ya bar wajen, jollof rice yayi mata order da kazar ita ma sannan suka bar eatry din, tana rike da ledan nata
ta wuce dakinta bayan sun isa gida, Abuturrab na shiga bedroom dinsa ya tadda El-Basheer a kwance
yanda ya bar sa idonsa lumshe, parlonsa ya koma ya xauna.

Bayan la'asar Abuturrab ya sauko downstairs ya samu El-Basheer dake xaune yana jiransa, El-Basheer yace
"Plss idan baxa kaje ba ni in tafi mana, i have many places to go yau din nan, i will be leaving probably
tomorrow in sha Allah" Abuturrab ya mika masa wayar hannunsa yace "Aneesah..." amsar wayar El-
Basheer yyi ya kai kunne, Abuturrab ya ajiye makullin motarsa sannan ya koma sama, El-Basheer ya amsa
gaisuwar Aneesah yace "Ya kwana biyu?" Aneesah tace "Alhmdlh, he is just telling me kuna tare yanxu" El-
Basheer ya d'an yi murmushi yace "Yea daxu na shigo kaduna and am at his resident now" tace "Oh ohk,
ya su Ummi?" Yace "Ban je ba" Aneesah tace "Ayya, to ya garin?" El-Basheer yace "Cool, i have a question
for you Aneesah, nasan baxa ki boye min ba" kafin ta ce komai yace "Tell me.... is Aliyu saying the truth na
cewar ya saki yarinyar nan??" Aneesah ta yi shiru da fari, can kuma cike da confusion tace "Yarinya? Wacce
yarinyar? Kuma sakin me?" Shiru El-Basheer yyi, can yace "Ohk then, i will pick a call right away...." Daga
haka ya katse wayar ganin from all indication she knows nothing about what he is saying now, sake kira
tayi ya ajiye wayar gefensa ya jingina da kujera, Abuturrab na tsaye dakin Jiddah dake rakube jikin gado,
yana kallonta strictly yake cewa "In har muka shigo gidan nan kika wani sakko wai xaki dau wani abu xaki
sha mamaki na, duk abinda xa kiyi kiyi ki gama yanxu kafin mu dawo" ta gyada masa kai kawai, kamar
wanda ya tuna abu ya juya da sauri yana kallon kofa, lkci daya ya fice daga dakin ya sauka downstairs yana
kallon El-Basheer da manyan idanuwansa yace "Hope... Hope you didn't say anything apart from greeting
to Aneesah???" El-Basheer yace "Of course baka ce min haka ba, na tambayeta ko gaskiya ne ka saki
yarinyar nan kamar yanda ka fada, and from d way she sounds, bata san komai kan maganar ba ma"
Abuturrab ya xaro ido yace "Ohh my God... Me yasa xaka yi mata wannan maganan El-Basheer?? We are
still hiding it from her" Mikewa El-Basheer yyi ya dau makullin motar Abuturrab yace "Ni kace min bata
sani bane, ga ta nan tana ta kira, pick and find what to say to her" daga haka ya nufi kofa ya fita, Abuturrab
ya bi sa da kallo xuciyarsa na tafarfasa. Daukar wayarsa yyi yaga calls din Aneesah har biyar yayi silencing
wayar ya bi bayan El-Basheer.... Bangaren Aunty suka fara shiga suka gaisheta bayan sun isa gidan, Aunty
na kallon El-Basheer tace "Har ka iya xuwa wai gidansa El-Basheer, ni fa na tattare lamarin Abuturrab na
watsar a gefe, i see no reason da xai dinga boye boyen cewar ya saki yarinyar nan, ko meye fa'idan xama
gida daya da ita bayan ya saketa, who is he deceiving?? To wllh I've made up my mind cewar Abbansa na
dawowa sati me xuwa xan sanar masa komai, wannan ae iskanci ne, to ko minti biyar ba ayi da muka gama
waya da mahaifiyar Aneesah ba, labari ya je masu, kana tunanin xaka iya ci gaba da boye masu ne dama??
Wllh yanxu haka duk hankalina a tashe yake, nayi kokarin fahimtar da su ba auren amma ya faskara...."
Kallonta kawai Abuturrab yake yi, shi na Aneesan ma bai damesa ba kamar na Abba da tace xata sanar ma
ya saki Jiddah kuma yana xaune tare da ita, gaba daya yaji hankalinsa yyi mugun tashi, Waje ya nema ya
xauna jin har kansa ya fara juya masa, El-Basheer yace "Ni banga abun boye boye a nan ba, let this be
known to everyone that she is no longer ur wife, kana xaune gida daya da macen da ba muharramarka ba,
who does that??" Abuturrab ya kalli Aunty da ta ci gaba da abinda take bbu fara'a fuskarta, yyi kasa da
murya yace "Amma Aunty kinsan Abba won't be happy idan yaji na saketa, he will be highly disappointed
at me, kuma ni sbda bana son bacin ranki ya sa na saketa wllh, idan kika gaya ma Abba cewar nayi hakan
yanxu he won't take it likely with me, i am just confuse Aunty" Aunty ta juyo a fusace tace "Ni kuma dole in
sanar masa duk abinda xae faru ya faru ba, are u this happy being with the girl da yasa ka daina dawowa
weekend gidan nan sae dai ka sauka gidanka ka karashi weekend dinka ka wuce, haka xaman naka da ita
yayi dadi duk da ba matarka bace ashe?? To kuwa xaka sha mamakina kuwa wllh" Ya girgixa kai yace
"Aunty ni weekend din ma gaba daya na daina dawowa fa, Jiya ne kawai na dawo sbda El-Basheer yace
min yana hanya" Aunty tace "Wato ita kadae ke yanda ta so a katon gidan? Ka sakar mata babban gida
haka ta ci karenta ba babbaka, to baxai yiwu ba ne wllh" Shiru yyi bai ce komai ba, Aunty tace "Don kuwa
da ta ci gaba da xaman gidan nan naka gwara ka dawo da ita nan, dama mai aiki xata tafi garinsu jibi, kaga
ba wani xai ce ta bar nan gidan ba wataran..." Kallonta kawai Abuturrab ke yi gabansa na bugawa, tayi
masa tsawa tace "Kallon ne amsan ka? Ko baxa kayi abinda nace bane??" Ya girgixa kai yace "Aunty can din
ma ina assuring dinki ba sae wani yace ta tafi ba xata tafi, wllh ita kadai ce bbu kowa" Aunty ta kara masa
wani tsawa tace "Nace ka dawo da ita gidan nan, ko ban isa ba??" Ya sunkuyar da kansa lkci daya jikinsa yyi
sanyi, can ya kalleta cikin sanyi yace "Toh" Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da harara tana huci, El-
Basheer ya d'an yi murmushi yace "But how can a normal human being do what Abuturrab did?" Cike da
bacin rai Aunty tace "Atoh... Isn't this irritating Bash?? Wllh da lamarin nan nake kwana nake tashi a raina,
ya ce ya saketa quite alright he did that, na sani, to kuma xaman me suke tare idan anyi magana yace
Abbansa, ance masa da Abban nasa ya san ya saketa xae barsa ya ci gaba da xama gida daya da ita, ga
yarinyar ido a bude, to xaman iskanci yake son fara yi da ita ko me, don dai shi ma ba saiti garesa ba kuma
ba jin magana yake ba, ka sani, na sani, shi yasa bai dauki xaman da yake under same roof with her wani
abu ba" El-Basheer ya mike yace "Allah ya kyauta" daga haka ya fita. Ko bangaren Ummi Abuturrab bai
shiga ba ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya jinginar da kansa da kujera yana jiran El-Basheer, dalilin da
yasa bai son xuwa gidan kenan idan ya dawo weekend, ganin har bayan minti sha biyar El-Basheer bai fito
ba Abuturrab yyi dialing numbersa, El-Basheer na dagawa, a fusace yace "Inyi tafiyata ne?" El-Basheer yyi
murmushi ya katse wayar, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi, sai ga text ya shigo masa, bude content din
yyi, "C'mon wani irin gaisuwa kake son inyi ma Ummi, gaisuwan minti goma? Tunda kai kaki shigowa
gaisheta ni baxan iya ba" Abuturrab ya mayar masa reply yace "Ka sameni a gida then" daga haka ya ajiye
wayar ya tada motarsa ya bar anguwar. Yana parking ya shiga parlor ya xauna kujera ya jinginar da kansa ya
lumshe ido yana jin ransa ba dadi, text ne ya shigo wayarsa ya bude ido a hankali ganin Aneesah ce tayi
text din ya bude content din, "Abinda ka min was the least i expected from you Aliyu, ban yi xaton haka ko
a mafarki ba, amma ka sani ka cuceni, ka ci amanata, ka yaudareni, ka ruguza min rayuwa, i gave u all my
trust but u ended up betraying me, why Aliyu, did i deserve this harsh treatment from you?" Ko gama
karanta text din bai yi ba yayi mata reply kamar haka "Since you never expect this from me... Then u
consider me... Aure kuma sai idan kece kika ce baxa kiyi da ni ba, as for me you will be my first and last
wife in sha Allah.... i will call u in 5 hours time in sha Allah" daga haka ya tura mata text din ya ajiye wayar
ya mike ya wuce sama. Har bayan Magrib El-Basheer bai shigo gidan ba, hakan ya sa Abuturrab yyi dialing
number sa, yana fara ring El-Basheer ya daga yace "Gobe xan shigo before leaving, Ummi tace i should
spend the night here" Abuturrab yace "Ohk" daga haka ya katse wayar. Mikewa yyi ya wuce sama ya bude
kofar dakin Jiddah, tun da ya dawo ko motsinta bai ji ba, tana xaune gaban mirror tana ma gashinta kitson
kalaba, ganinsa ta dau hulanta ta saka, yana tsaye bakin kofa yace "Meye hakan kike yi?" Tace "Aa ina
kitson gashin ne, yana karyewa idan ban yi kitso ba" Yace "Sai anyi kitson ne baxai karye ba?" Ta gyada
masa kai, yace "Toh kwance wannan abinda kika yi, tunda a garinku ne aka ce maki xai karye idan ba ayi
kitso ba, a tsefe xaki bar gashin, haka nake so" Ta kallesa da sauri, that was when he realized what he just
said, lkci daya ya hade rai yace "Ko kina ganin kitso a gashin su Ramlah, mu a nan ba a kitso" Cikin sanyin
murya tace "Toh" ta fara tsife dogon gashin nata da ta kitsa, har ta gama tsefe daya bata ji ya tafi ba, hakan
yasa ta leko sa ta cikin gashinta da ya rufe mata fuskarta gaba daya, suna hada ido ya juya ya fita dakin.
Ana kiran isha ta gama parking din dogon gashin nata ta kitse jelan sannan ta sa hularta. Karfe tara saura
wayar da Abuturrab ya bata ya fara ring a gaban madubi, karasawa tayi ta dauka tana kallon number jikin
screen din sannan tayi picking ta kai kunne, muryarsa taji yace "Ina jiranki a parlor" Daga haka ya katse
wayar, ajiye wayar tayi ta sa Hijab dinta ta fita, shi kadae ne xaune parlon ta durkusa jikin kujera a hankali
tace "Gani" Yace "Me kika ci?" Ta sunkuyar da kanta tace "Taliya na dafa" ya nuna mata ledan dake gefensa
yace "dauka" mikewa tayi ta isa kusa da shi ta duka ta dau ledan, ya rike numfashinsa sbda wani kamshi na
daban da ya doki hancinsa, ganin kwalin lemo a cikin ledan ta cire xata ajiye, ya saki breath dinsa ya hade
rai yace "Har da shi xa ki tafi" Innocently tace "Ban iya sha ba" Yace "Haka xa ki je ki koyi sha yau, tunda ke
yar kauye ce" Bata ce komai ba ta mayar da kwalin cikin ledan sannan ta mike ta nufi stairs, bin ta yyi da
kallo tana isa stairs ta juyo suka hada ido, da sauri ya dauke idonsa, tace "Nagode" sannan ta wuce sama,
jinginar da kansa yayi a hankali da kujera yana jin damuwa iri iri a ransa, gasasshiyar kaza ce da yaji Jiddah
ta bude a dakinta, sai kamshi kazan yake, ta kalli kwalin hollandia din sannan ta bude ta d'an sha kadan, ji
tayi yayi mata dadi a baki sbda gardinsa, ta lumshe ido ta kara sha sannan ta ajiye ta fara cin naman a
hankali, lkci daya rayuwar da tayi a gidansu ya fado mata, tura kazan tayi tuna Babarsu da tayi.
Abuturrab na kwance wajajen sha daya a parlor, waya na kare kunnensa, he felt relieved bayan yayi
convincing Aneesah a kan kaddara ce ya sa shi auren jiddah sannan kuma bashi da aurenta a kansa yanxu,
daga daya bangaren cikin sanyin murya tace "Amma why is she still at ur resident My captain??" Yace "Ina
kike son in kai ta yanxu?" Tace "Ni ko gidanmu ma ka kawota su Mummy baxa su ce Aa ba wllh, ni nasan
karyar da xan masu, ka barta ta dawo gidanmu plss" Bai san lkcn da yyi wani murmushi ba, a hankali yace
"Koh?" Ta marairaice tace "Sure dear" yace "I will think about that, xuwa nan da short period of time" tace
"Do so fast plss Captain" daga kai yyi jin footstep a stairs, lkci daya yace "I call you in some minutes time"
bai jira cewarta ba ya katse wayar, yayi kasa da idonsa kamar me bacci, A hankali Jiddah ke tafiya duk
xatonta bacci yake hannunta rike da ledan kazan da ko yanka uku bata ci ba, to bata saba da shi ba shi yasa
bata iya ci sosai ba, drink din ne ma ta d'an sha ba laifi, kitchen ta tafi ta ajiye ledan kazan a fridge ta ajiye
lemon ma sannan ta fito, a hankali take tafiyar ta nufi stairs ya bi ta da kallo, nighty ne jikinta wanda ya
wuce kneels dinta da hularta a kanta, sai da ta isa stairs ta juyo ta kallesa suka hada ido, sosai ta tsorata,
yyi saurin mikewa xaune pretending to be awake at that moment yace "Me kike yi a nan" ta nuna masa
kitchen tace "Na kai abu na ajiye" yace "Je ki dauko abinda kika ajiye" Tayi narai narai da ido ta ki motsawa
daga inda take, ya hade rai yace "Baki ji abinda nace ba?" Da gudu ta wuce sama, ya mike tsaye da mamaki
yana bin ta da kallo, har ta shige dakinta.


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Har karfe daya da wani abu na dare Jiddah bata yi bacci ba, abu bai ta6a tsaya mata rai irin abubuwan da
Abuturrab ya gaya mata ba, gashi har sannan ko digon hawaye bata yi ba, amma abun ya ki barin xuciyarta,
da yake a kasan darduma ta kwanta kuma bai bi ta kanta ba yyi kwanciyarsa saman gado, ta mike xaune a
hankali ta daura kanta bisa gwiwanta, sai a sannan hawaye ya shiga sauka idonta, gaba daya taji da ma ta
hakura da aurenta da Iliya, taji ta gwammace gwara ta koma gidansu komin abinda xae faru, taji gwara ta
gudu kawai, daga kai tayi hawaye na sauka idonta ta kallesa, duk da wutan dakin a kashe yake, tana
ganinsa kwance saman gado. Da safe bayan ya gama shirinsa haka ya fita ba tare da yace mata komai ba,
tun bayan da ta gaishesa bata ma san ko ya amsa ba har ya fita bata kalli inda yake ba ita ma, sae dai bata
ga ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login