Showing 171001 words to 174000 words out of 321711 words
ne ya daga ya
kai kunne, daga daya bangaren Abuturrab yace "Good morning" Ahmad yace "Morning..." Abuturrab ya
d'an shafa kansa yace "Dama ina son maka tambaya ne" Ahmad yace "Alright i am all ears" Abuturrab yace
"I want to know more about Virginity, what it is, and how it is" Buda ido Ahmad yayi sosai yace "Tohhh" sai
kuma ya kalli Ramlah dake xaune saman darduma, kofa ya nufa yace "Ban gane tambayar ka ba" Abuturrab
yace "Meye baka gane ba a ciki?" Ahmad na fitowa parlor ya nemi kujera ya xauna, Abuturrab yace "I'm
serious Ahmad, ka bani amsar tambayata don Allah" Ahmad yace "No ina mamakin hadin Pilot da
tambayar ne... But anyway virginity da Hausa shi ake ce ma budurci, kuma idan aka ce Virgin ana nufin
wanda bai ta6a intercourse ba, weather a male or a female..." Abuturrab yace "To ya ake gane someone
that is a virgin?" Ahmad yace "Mace ko namiji?" Abuturrab yace "Both" Murmushi Ahmad yyi yace "Ita
mace akwai wani thin membrane lining da ake kira da hymen a jikinta, and it will seem a bit difficult to
penetrate in her, don dole sai anyi breaking hymen din, and in some cases they will be shedding of a little
blood, mind u in some cases nace, wasu matan kuma ba sai ta hanyar intercourse kadai hymen dinsu ke
breaking ba, d'aga abu me karfi, tsalle tsalle, hawan bishiya ko keke, and many stuffs like that, yana sa suyi
loosing hymen dinsu, but duk da haka ba wai xa a ji su kamar sun ta6a samun affairs bane idan an kusance
su, don't quote me wrong... sae dai kawai baxa su yi shedding blood din nan ba, infact masu hymen din ma
ba ko wacce ne ke fitar da jini ba...." Katse sa Abuturrab yayi yace "Amma kuma ya ake gane warce ta sa6a
sex da warce bata ta6a ba?" Ahmad yace "That's so easy, warce bata ta6a ba u neva find it easy to
penetrate in, they are alot of struggles, and u ur self will know u just need to be extra gentle on her...."
Katse sa Abuturrab yyi yace "Alright thank you, sai anjima" Ahmad yace "But why all this questions?"
Abuturrab yace "Karin ilimi" D'an murmushi Ahmad yyi yace "Ohk that's great" Abuturrab yace "Sai
anjima" daga haka ya katse wayar, ya jefar a gefensa ya jinginar da kansa da kujera. Sae kusan karfe shidda
ya tashi ya wuce dakin da ya kwana yyi wanka, xaune yyi gefen gado thinking of how to get his cloth from
his room without seeing Aneesah, ganin lkci na ta wucewa kuma driving xae yi xuwa kano ya mike ya wuce
can bangarensa kawai, Aneesah na kwance kan gado ta dunkunkune cikin bargo tunani iri iri a ranta, bata
san ya encounter dinta da Abuturrab xai kasance ba yau, ko wani hukuncin xai dauka a kanta oho, to amma
taya ma xai gane ita ba virgin bace bayan tana da tabbacin bai ta6a sex ba balle ace yayi da wata har ya
banbance, sannan ma duk da rashin virginity din nata sai da taji axabarsa, kenan dai a matsen take, kuma
ba lallai ya ma gane ba virgin bace ita, ita dai kadai take ta tunani kala kala, kana ganinta kasan she is so
tense and disturb, duk irin burin da ta ci na yanda haduwarta da shi xai kasance ya wargaje, ko armashi
abun babu banda axaba, tsoro da tashin hankalin me xai biyo baya, to amma duk da haka ita tasan tana da
taste dinta kamar yanda ake yawan gaya mata, shi dai kawai ba ya gamsu ba ina ruwansa da yanda ya
sameta, kilan ma bai gane komai ba ita ce ke ta damun kanta, ta ina xai wani san virgin da warce ba virgin
ba abinda bai ta6a yi ba, Abuturrab bai ko kalli saman gadon da take ba ya wuce gun kayansa, ta bisa da
ido tana tunanin abinda ma xata ce masa, lkci daya ta fara shesshekan kuka, ya dau kayansa da jakar laptop
dinsa ba tare da ya kalleta ba still, ganin xai fita cikin rawar murya tace "Naka tukuicin kenan after
deflowering ur wife Captain?" Tsayawa yyi ya juya ya kalleta yace "Did u say deflower?" Shiru tayi gabanta
na mugun bugawa tana kallonsa daga kwancen da take kamar er mage, yayi wani murmushi yace "I wished
so Aneesah, but my trust got betrayed by u, i regret doing what i did yesterday...." Cike da karfin hali ta
mike xaune ta dake tace "Ur trust got betrayed?? How Captain?? Wannan wani irin magana ne?" Sai kuma
ta fashe da matsanancin kuka ta girgixa kai tace "Amma ka bani mamaki, yanxu so kake kace min maxa
nake bi ko me?? Dama ashe baka fi kowa sanin halina ba Captain? Bayan kai ka ga alamar akwai wani
wanda nake kulawa har muka yi aure?" Sai kuma ta kara rushewa da matsanancin kuka tace "Tunda nake
ban ta6a zina da wani d'a namiji ba Allah shaida, idan ina yi kai ma da ka sani ai don irin wannan abun
baxai boyu ba, bani da wanda nake kulawa da ya wuce kai, me na maka xaka saka min da haka a ranan da
ka kusance ni..." Abuturrab bai ce mata komai ba ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da kallo tana hadiye
abu da kyar. Bayan ya shirya ko sallama bai mata ba ya fice daga gidan cikin motarsa, yana driving ya kara
dialing number Ahmad, bayan Ahmad ya daga yace "Ahmad i still have more questions" Ahmad yace
"Alright go on" Abuturrab yace "Kace not everyone ke shedding blood due to reasons u listed.... haka ko?"
Ahmad yace "Yes" Abuturrab yace "But how about if u just find ur self in without any stress, me hakan ke
nufi, or ana samun irin wannan cases din gun warce bata ta6a sex ba?" Ahmad yace "Noo!! if u should go
in freely, to ko ma wacece ta ta6a sex wllh, continuously ma kuwa, and probably for long take abunta shi sa
ma kayi noticing hakan lkci daya...." Abuturrab dai yayi shiru yana sauraronsa, Ahmad yace "And let me tell
u something, in dai mace ta sa6a sex before marriage to memory din wanda ta sa6a da shi din will remain
in her brain, da kyar ta iya rabuwa da shi duk da fa ga mijinta, yawancinsu basa iya tsayawa a matrimonial
home dinsu without following men outside, it's just like a curse, ko da sun dau vow din repenting to ina
gaya maka na yan shekaru ne... xa su koma idan ba Allah ne ya so su da Rahama ba" Shi dai Abuturrab bai
ce komai ba, Ahmad yace "Are u okay now?" Abuturrab yace "Sure nagode, i am on my way to kano, thank
you... Sai anjima" Ahmad yace "Alright safe trip" Katse wayar yayi ya ci gaba da tukinsa. Tun da Aneesah
taji fitar motarsa a gidan ta hau kiran Aunty, Aunty na dagawa ta fashe da kuka tace "Aunty na shiga uku..."
Aunty dake kwance kan gadonta ta mike xaune da sauri tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Wllh kawai
daren jiya Aliyu ya far min, duk yanda nayi kokarin stopping dinsa hakan bai yiwu ba har sae da yayi" Aunty
ta bude baki tace "Yayi?? To sai aka yi yaya ynxu?" Tana kuka tace "Tun jiyan ya ki kulani bai ma kwana
dakin ba, sae yau da safe ya xo daukan kaya yake ce min i betrayed his trust, kinga wllh ynxu ma haka ya
tafi kano ko sallama bai min ba" Aunty ta saki salati tace "To garin yaya hakan ya faru, garin yaya kika yarda
kinsan halin da kike ciki Aneesah?" Kuka kawai take tace "Wllh he forced him self in me Aunty, nayi kokarin
preventing hakan amma ni ba karfinmu daya ba" Aunty tace "Tabdi, to ni yanxu me xance??" Aneesah ta
dinga goge idonta ko da wasa bata ce ma Aunty turaren da ta bata ne ya fashe ba, Aunty tace "Toh abinda
xai faru duk inda xaki nemo kudi ki nemo a samu a rufe bakinsa kawai" Aneesah tace "Sai in dau zinarina in
siyar, I can't imagine Aliyu yace xai rabu dani sabida haka, wllh ina sonsa sosai Aunty" Aunty tace "Ya rabu
da ke?? Ji wani mugun alkaba'i, ke fata kike ya rabu dake ma kenan? Akan wannan d'an abun xai rabu dake
kamar warce ta kashe mutum? Mata nawa ne aka aurar bbu budurcinsu kuma suna xaune qlau da
mazajensu? Rabu da d'an iska xai ma sakko ne, ke dai kawai ki siyar da zinarin ki turo min kudin a tura
benue" Aneesah tace "Toh Aunty, ynxu xan fita kasuwa in siyar sae in tura maki kudin" Aunty tace "To yi
maxa, kar ki wani damu abunki, ubansa ma yayi hakuri da hakan balle shi gantalalle, shaff mancewa xai yi
idan na sa ayi aikin..." Aneesah tace "Toh nagode Aunty, bari inje, xan kiraki" Aunty tace "To yi maxa" daga
haka ta katse wayar, ko wanka Aneesah bata yi ba tun daren jiyan balle aje ga sallah, ta saka doguwar rigar
atamfa ta xumbula hijab dinta sannan ta saka zinarin a jaka ta fita daga gidan. A ranan Ahmad ya kai Jiddah
makaranta kamar yanda ya ce da Umma, Tunda yyi duk registration din da komai ya tafi ya barta kawai ta
fara karatu Monday din... Da yamma karfe hudu da kansa yaje daukota daga school din, amma sanin halin
Ummarsa sae ya wuce da ita can gida kawai, Umma tayi farin cikin fara makarantar Jiddah sosai, ita dai
Jiddah na xaune kasa kan carpet tana murmushi, Umma tace "Toh tashi kiyi sallah ki ci abinci" mikewa tayi
ta wuce dakinsu, Ahmad ya kalli Umma yace "Kince daga nan xata dinga tafiya ko Umma?" Umma tace "Eh
xata dinga xuwa daga nan" Yyi murmushi yace "Ga dai sauki amma ke baki so Umma" Umma tace "Saukin
me?" Yace "Kashe transport" Umma tace "Kai yanxu ka bada shawarar a bar kamarta da Ramlah a gida kai
kana can gun aiki, to wa xai dinga gaya masu gaskiya ko ya sa su kan hanya, shiririta kenan kawai" Yace
"Kema dai kinsan Ramlah bata da shiririta Umma, sannan Jiddah ma na da hankali da nutsuwa sosai, kinga
from monday to Friday idan taje schl sae ta xo nan Friday din da yamma ta maki weekend, ina ga xae fi
wllh" Umma tace "Shkkn kuma babu me sa mata ido kan karatun?" Yace "A nan ma kinsan bbu me sa mata
ido amma take yin karatunta wholeheartedly" Umma ta ta6e baki tace "Toh ae shkkn, sae ta tafi can din,
amma friday ta dawo nan tayi weekend" Yace "In sha Allah Umma" Sae kusan biyar da rabi suka bar gidan
suka koma gidan Ahmad, a hanya yake bata hakuri kan gidan Iya da bai kai ta ba tunda ta koma schl, Jiddah
tayi murmushi kawai tace "Toh Allah ya kai mu wani lkcn" Ranan friday Abuturrab na shigowa garin kaduna
gidan Umma ya nufa direct, yana parking a kofar gida ya shiga cikin gidan, Umma ce xaune parlor suna hira
da Huraira, yayi sallama ya shiga parlorn, sanye yake da fararen shadda da suka amshesa sosai, sae da
Huraira ta gaishesa sannan ta bar parlon, Ya xauna saman kujera yana kallon Umma yace "Ina yini" Umma
na kallonsa tace "Lafiya lau, daga ina haka?" Yace "Daga gida" Tace "Madallah, ya kwana biyu?" Yace
"Alhmdlh..." Sallama aka yi bakin kofar Umma ta daga kai tare da amsa sallaman, ta shigo parlon sanye da
hijab dinta gogagge har kasa da jakarta a hannu, ta gefen ido yake kallonta har ta karaso cikin parlon ta
nufi Umma ta durkusa nan kasa kusa da ita a hankali tace "Umma ina yini" Umma tayi murmushi tace
"Lafiya lau Jiddah ya karatun?" Ta sunkuyar da kanta tace "Alhmdlh Umma" Abuturrab dai kallonta kawai
yake, Umma tace "Ya su Ramlar" Jiddah na wasa da fingers dinta tace "Tana gaisheku..." Umma tace
"Ahmad din ya shigo ne?" Jiddah ta girgixa mata kai tace "Aa" tunda ta lura da cewar Abuturrab ne xaune
parlon duk da ba wai kallonsa tayi ba taki yarda ta dago kanta gaba daya, Umma tace "Toh yayi kyau, kije ki
xuba abinci ki ci" Tace "Umma na ci abinci" Umma tace "Ohk to kice ma Huraira ta kawo ma Aliyu ruwa"
Mikewa Jiddah tayi still bata yarda ta kalli direction din da yake ba ta wuce kitchen din, satan kallonta yake
har ta shiga kitchen din, sai kuma ya kalli Umma yaga wani kallo da take masa...
*Sorry for the late night update*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat
tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging,
Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for
wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028
Abuturrab ya dauke kansa, Umma tace "A hado maka da abinci ne?" Girgixa kai yayi yace "Aa" Jiddah na ba
Huraira sakon Umma ta fito ta wuce dakinsu, Huraira ta fito da ruwan ta ajiye ma Abuturrab, knocking aka
yi bakin kofa Huraira ta karasa bakin kofar ganin driver ne ta kalli Umma tace "Umma Musan ya dawo"
Umma tace "Ohk to ya jirani" Huraira ta koma ta gaya ma drivern abinda Umma tace, Abuturrab ya dau
bottle water ya bude yana kallon Umma yace "Umma fita xa ki yi?" Umma tace "Ehh yanxu kuwa" Tana
fadin haka ta mike ta wuce dakinta ta dau hijab da purse dinta, tana fitowa parlon shi dai bin ta kawai yake
da kallo, ta xauna saman kujera ta kira Huraira, Huraira na xuwa tace "Kira min Jiddah" kallonta kawai
Abuturrab yake, Huraira ta wuce daki sai ga ta sun fito tare da Jiddah, Umma tace "Dauko Hijab dinki ki
rakani" Jiddah tace "Toh" sannan ta juya, Abuturrab dai sai kallon small mum din tasa yake, banda danna
wayarta babu abinda take, Can ya shafa kansa a hankali yace "Umma ina xa ku?" Tace "Kwana biyu banje
na gaida Yaya ba, can xanje yanxu" Yace "Nima can, xan tafi na dai fara xuwa nan in gaisheki ne" Umma
tace "Allah sarki, ai ka kyauta" Yace "Toh in ajiye ku can din?" Umma tace "Idan ka ajiye mu wa xai maido
mu, gwara mu tafi da driver ko awa nawa xanyi xai jira in gama sannan ya maido mu gida" Abuturrab yace
"Ae xan kai har bayan isha a can, duk sanda xa ku dawo sai in dawo da ku sannan in wuce gidana" Umma
tace "Toh ai shkkn idan ba takura" Umma ta mike ta wuce kitchen don juye pepper soup din da tayi ma
Ummi, Jiddah ta fito daki sanye da hijab din da ta xo da shi, hada ido suka yi da shi, ta juya da sauri ta wuce
kitchen, babu 6ata lkci Umma ta fito kitchen Jiddah na biye da ita rike da warmer din pepper soup,
Abuturrab ya mike yace "Ina jira a mota Umma" Umma tace "Eh yanxu xa mu fito" Umma ta gama ba
Huraira instructions din da xata bata sannan suka fito parlon da Jiddah, driver dake tsaye parking space
Umma ta nufa tace "Musa kawai kayi tafiyarka na samu ma wanda xai ajiye ni can gidan" cike da ladabi
Musa yace "Toh shkkn Hajiya, Allah ya tsare" Umma tace "Ameen, sai gobe kenan" Daga haka ta nufi gate
Jiddah na biye da ita a baya being very careful kar ta 6ata hijab dinta da abinda ke cikin warmer din
hannunta, back seat Umma ta bude ta shiga, Jiddah ta shiga bayan ita ma ta kulle motar, Umma na
kallonsa tace "Idan ka samu wajen siyar da fruits a hanya" Yace "Ohk" daga haka ya tada motar ya bar
layin. Dai dai wajen masu siyar da fruits yayi parking kamar yanda Umma ta umarcesa, Umma ta ciro kudi
ta mika masa tace "Apples kawai sai grapes" Ya kalli kudin ya sauka motar yace "Akwai kudi a jikina" daga
haka ya kulle motar ya tafi gun masu fruits din, bayan some minutes ya dawo, ya bude back seat yana mika
ma Umma ledan amma Jiddah yake kallo, Umma ta kallesa tace "To ita kake ba ledan ko ni Aliyu? idan ita
ce sai ka xaga ta can mana" Tana fadin haka ta amshe ledan xata rufo door din motar, shi dai bai ce komai
ba ya koma driver seat, Jiddah dai na makale at the far end of d car don bata ma son su hada ido
mistakenly ta madubi. A kofar gidansu yayi parking, Umma ta sauka, Jiddah ma ta sauka rike da warmer
din ta bi bayan Umma da sauri, Direct bangaren Ummi suka tafi, Jiddah dai na xaune kasa bayan sun gaisa
da Ummi da ta fito daga daki, Ummi tace "Toh ki xauna kujera mana Jiddah" Murmushi kawai Jiddah tayi
bata ce komai ba, Umma tace "Ko a gida ma kafin ta xauna a kujera sau daya tayi xamanta a carpet ya fi a
kirga" Ummi tace "Ikon Allah, to ina su Maimoon?" Umma tace "Suna dawowa boko suka tafi gidan Hajiya
Zainab" Ummi tace "Haba, tana garin nan dama?" Umma tace "Aa last week ta shigo" Ummi tace "Allah
sarki" Umma tace "Jiddah kuma ai nace maki tana gidan Ramlah ta fara karatu ko?" Ummi tace "Ehh haka
kika ce, Allah ya bada ilimi me albarka da amfani" Umma tace "Ameen, Hajiya Hajja fa? Kwana biyu ba a je
min ba" Ummi tayi murmushi tace "Shekaranjiya ta tada rigiman a kai ta gombe wajen mai martaba,
amma yau kuma wai sai naji suna hanya kilan ma sun kusa, mun yi magana da El-Basheer din da safe"
Umma ta tabe baki tace "Toh Allah ya kyauta, meye amfanin tafiya me nisan da ko kwana uku baxa ayi ba"
Dariya kawai Ummi tayi, aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama, xaunawa yayi ya gaida Umminsa,
Ummi ta amsa tana kallonsa, Umma tace "Shi ya kawo mu, yaje can gida gaisheni shine yace bari ya ajiye
mu tunda nan xa mu xo" Ummi tace "Maa sha Allah, Ina matar taka??" Yace "Tana gida" Ummi tace "Toh
yayi kyau, shekaranjiya ma ai ina jin ta xo nan wajen Hafsah, amma ni dai ban ganta ba su Nafisah ke gaya
min" Abuturrab dai yyi shiru bai ce komai ba, Umma dai ta ta6e baki tana kallon Tv, Ya kalli Ummi yace
"Ummi akwai abinci?" Umma ta wani kallesa tace "Amma da nayi maka magana a can gidan me ka ce
min?" Murmushi kawai yayi, Ummi ta kalli Jiddah tace "Akwai abinci kitchen ki dibar masa Jiddah" Sosai
gaban Jiddah ya fadi ta kalli Ummi,