Showing 261001 words to 264000 words out of 321711 words
or 07067210195
Call:08064532391
Available in Kano and Kaduna
We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166
Serious buyers only please,
Inamasu bukukuwa😍
Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu
Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195
Cika alkawari shine takenmu🤝
Thank you
Mutuwar tsaye Aneesah tayi jikin window tana kallonsu gaba daya, ta kasa kwakkwaran motsi, lkci daya
taji xaxxabin da take ji tun safe ya sake dawo mata, Muryar Maimoon a compound din gidan kuwa ba a
magana, sai ka rantse ita aka siya ma mota duk da abun nata har da gayya, Hotuna ta dinga ma Abuturrab
da Jiddah tana masu video da wayarta, Jiddah dai taki bude idonta gaba daya kunya ya rufeta, tayi kokarin
xame jikinta daga na Abuturrab amma ya ki saketa, duk kunyan kawayen Maimoon dake tsaye ya cikata,
Aneesah ta dauke idonta ta juya ma window din baya kirjinta na wani heaving kamar xai fito, mota??
Tambayar da tayi ma kanta kenan a fili, da hannu biyu ta dafe kirjinta tana jin wani abu da bata ta6a ji ba,
da gudu ta nufi kitchen kamar wata ta6a66iya.... shigowar Mai gadi compound din ya sa Abuturrab ya sake
Jiddah ta juya masa baya da sauri, Maimoon ta tafi ta rungumeta cike da farin ciki take cewa
"Congratulations Jiddah, i am really happy for u sis, Allah ya sanya alkhairi" Jiddah dai ta kasa cewa komai
suna rungume da juna, Mai gadi ya nufo Abuturrab da sauri duk da bala'in da ya sha a bakin gate, da
ladabi yace "Ranka shi dade anyi baki ne, xa a shigo da mota.. nace bari in fara sanar da kai" Abuturrab
yace "Ohk ka bude gate din" komawa yayi da sauri xai bude sai ga Hajja ta shigo compound din rataye da
katon jakanta wanda babu komai ciki, Cike da fitina take kallon mai gadin tace "Wllh Allah ya isa ban yafe
maka ba..." Abuturrab ya nufeta yace "Me ya faru Hajja?" Kamar xata yi kuka tace "Wllh su a Masar in xa
su dau mai gadi sai an fara kai sa asibitin kwakwalwa an binciki kwakwalwarsa ciki da bai, basa daukan
masu gadi kansu tsaye, banda haka har wannan tsukakken mutumin xai ce bai ta6a ganina ba a gidan nan?
Idan ma bai ta6a ganina ba xai ce bai ga kamanni ba? To ni dai Allah ya isa wllh, ya min axabbabben
walakanci bakin gate din nan wanda da a Masar ne titi xa a mika ma yara shi suyi ta jifan d'an banxa, ai ba
a ma tsofaffi haka a Masar, sun san mutuncin tsoho, to idan ma ni bai ga kamannina da kai ba xai ce bai ga
kamannin Hauwa tare da kai ba, tare da ita fa muke, nace yau wllh ko taki ko ta so sai mun taho gidanka
tare tunda bata ta6a xuwa ba, amma mutumi kawai ya walakanta mu a bakin gate yace mana daga ina?
Allah ya saka min wllh, ita kuma Hauwa ta wani ja6e a mota tayi shiru maimakon tace kai don uwarka
gidan d'a na ne ni na haifesa wannan tsohuwar kuma ta haifi ubansa, to wllh bata yi haka ba sai ta ja
bakinta tayi gum, mata kawai matsoraciya malam" Dai dai nan driver ya shigo compound din da motar yayi
parking Ummi ta bude motar ta sauka, rungumeta Maimoon ta tafi tayi tana murmushi tace "Sannu da
xuwa Ummi" Abuturrab kam sai kallon Ummin nasa yake don ko hanyar gidansa kam bata ta6a xuwa ba sai
yau, ya kuma yi farin ciki har ransa da xuwan nata, Jiddah ma ta nufi Ummi ta gaisheta da ladabi, Ummi ta
sakar mata murmushi tace "Ya ku ke Jiddah, ya gida?" jiddah tace "Lafiya lau Ummi" sauran kawayen
Maimoon ma duk suka gaishe da Ummi, Hajja dai taki hakura sai tsine ma mai gadi take tana nuna sa da
d'an yatsa wai shi ma sai an masa abinda ya mata a bakin gate, Abuturrab sai danne dariyarsa yake don
kawai tsayawa mai gadin yayi yana kallonta kamar ya ga sabon kamu, Abuturrab yyi kasa da murya yace "Yi
hakuri Hajjaj xa a canxa sa in sha Allah, wanda kuma xa a canxo xa a duba kwakwalwarsa" Yasan hakan
kadai ne xai sa ta hakura, Hajja ta wani sauke ajiyar xuciya tace "To ko da na ji, amma wllh ba a ta6a ci min
mutunci irin na yau ba, har kuka sai da nayi a xuciyata, to wannan fitina da axababben walakancin har ina"
dariya Abuturrab yayi ya nufi Umminsa yayi mata side hug a hankali yace "Welcome Ummi" ta hade rai tayi
masa kallon gefen ido tace "Meye haka?" Dariya Maimoon ta dinga yi, Jiddah dai ta nufi Hajja ta gaisheta
cikin sanyin muryarta, Maimoon na washe hakora tace "Hajja ga motar Jiddah, yaya ya siya mata..." Hajja
ta juya da sauri ta kalli motar, ta kai minti daya tana bin motar da kallo, sai kuma ta saki wani kabbara tace
"Shi Abuntural din ya siya ma Jiddah wannan xukekiyar mota?" Cike da farin ciki Maimoon tace "Wllh kuwa
Hajja, yanxun nan aka kawo motar" Ummi dai sai kallon Abuturrab take da mamaki but deep down she is
so happy for Jiddah, Hajja ta rike kanta ta kuma sakin wani kabbara tace "Wayyo wayyo, to ko dai na
kyautan budurci ne wannan xukekiyar mota ba mu sani ba? Banda haka me yasa bai siya ma Nanisa
kazama ba duk xamansu tare, to ko a bazawara ya aureta bamu da labari...." Ummi dai tayi hanyar
entrance din gidan bakinta alekum, Maimoon ta bi bayanta da sauri tana kunshe dariyarta, Hajja na kallon
Jiddah da ta kasa dago kanta tace "Toh wllh wlh ki kama mijinki ki rike gam yana sonki so ba na wasa ba, da
kyar ake samun miji irin Aliyu a wannan xamanin na yan banxa da en iska, ki rikesa ya xama uwarki da
ubanki, shine gatanki a nan duniya dai, kishiyarki kuma...." Shiru Hajja tayi jin tarwatsewan abu a cikin
gidan, duk suka kalli entrance din gidan, Hajja na gwale ido tace "Ruwa xa ayi ne ba hadari, naji kamar
tsawa" Wani tsawan glass din suka kuma ji, Abuturrab ya nufi cikin gidan da sauri... Upstairs Abuturrab ya
dinga jin tarwatsewan glasses, Ummi da Maimoon dai na tsaye parlon suna kallon sama su ma, haurawa
yayi Maimoon ta bi sa da sauri, Hajja na xare ido ta labe daga balcony tana leko parlon, Jiddah ma dae na
tsaye gefen Hajja gabanta sae faduwa yake, kawayen Maimoon dai dama gate suka nufa gaba daya, still
Abuturrab yayi bakin room din Jiddah with mouth agape yana kallon Aneesah da tayi kwatsa kwatsa da
mirror ta tarwatse duk kwalaben gaban mirror din a kasan tiles, sannan press din dakin ma tayi kaca kaca
da madubin jiki, ko ina a kasan tiles din dakin glass ne a kwance da drop din jini, furniture din gadon ma
duk ta mummuka masu katon ta6aryan hannunta, daga hannun nata har kafanta jini ne ke diga kasa,
gashin kanta duk a baje kamar sabon kamu sae wani huci take, da gudu Maimoon ta sauka kasa tana cewa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Ummi da hankalinta yayi mugun tashi tace "Me ke faruwa haka??
What's happening?" Maimoon bata tsaya ba Ummi amsa ba ta nufi kitchen da gudu ta dubo wani
tabaryan, ko ta kan Ummi bata bi ba balle Hajja ta haura sama tayi hanyar dakin Aneesah, sae dae kash taji
dakin a kulle an sa makulli... Abuturrab yayi ma Aneesah tsawa for d second time kamar Zaki yace "Nace
me kika aikata haka Aneesah?? Are you mad??" Ta juya tana kallonsa da idanuwanta da suka koma kamar
garwashi tana huci, sae kuma ta fashe da wani dariya tace "Dakin amaryarka na tarwatsa kaga nima sae ka
tarwatsa ni... babu fetur ne da wllh wuta nayi niyyar cinna ma dakin without minding ko da ita a ciki ko
babu, Aliyu shigo ka kasheni shine hukunci mafi ma'ana da ya kamata ka yi mani ka huce, nayi hakan ne
don ka kasheni kawai, ba dai dakin Jiddarka na mayar haka ba, come in and take revenge, nace shigo ka
dau fansa..." Tana fadin haka ta nufesa a guje jini na xuba jikinta ta cakumosa tayi wani ihu kamar xata
tsaga gidan tace "Ka dau fansa nace Aliyu, dakin matar so fa na mayar haka, wai ma uban wa ya haifeka da
xaka ke walakanta ni don ka auri warce aka yi ma like like aka kawo maka, har ni xan xama abar walakancin
ka?? me matsiyaciyar ta fi ni da shi banda rashin asali da kauyanci????" Bata gama rufe baki ba ya dauketa
da wani wawan mari ya shaketa sannan ya bugata da bango ya kuma kai mata wani marin, tayi taga taga
xata fadi har sannan jini na xuba sosai daga jikinta, duk jirin da take gani haka ta dinga kunduma masa xagi
da shi da Jiddan tana ci gaba da fashe fashe a dakin, juyawa yayi ya nufi bangarensa direct kamar xai tashi
sama, Maimoon ta hauro sama tare da Hajja da jikinta ke bari, Hajja na leka dakin Jiddah suka yi ido hudu
da Aneesah dake huci, ta fasa wani ihu a gigice ta sauka kasa ta nufi kofar fita parlor tana cewa "Huhuhu....
Idan nayi magana sae a dinga min kallon er ta'adda, idan nayi magana sae a maidani salubabbiya hotiho,
wayyo Allah!!! Wato tun daga ranan da nayi arba da Aneesah a gidan Usman tana amarya nasan ba
lafiyayya bace a kwakwalwa, ni nasan sabuwar kamu ce, wllh tun daga ranan nasan ta6a66iya Aliyu ya auro
na dai ja bakina ne nayi shiru, to duk ba wannan ba don bai dameni ba.... amma me??? kai kana ganin
kazantarta kasan da ta6in hankali a tare da ita, don me lafiya baxae yi wannan kazanta da take yi ba, to yau
dai hauka muraran ya ta66ata a gidan Aliyu, wayyoo jama'a, babu dawanau ne a kaduna stey? Duk girman
kaduna babu dawanau ne?" Fita tayi parlon tana kwala ihu tana cewa "Masu gadi ku kawo dauki, jama'an
anguwa ku kawo dauki, masu gidaje a anguwan nan ku taimake mu ku kawo dauki, jikana ya auri
mahaukaciya bamu sani ba...." Mai gadi ya ja gefe da sauri yana kallon Hajja baki bude, wata mota taga ke
tahowa ta sa hannu bibbiyu tana tsayar da motar cikin daga murya tana cewa "Wayyo ku kawo mana
dauki, ni daga Masar nake ban san wani gidan mahaukata a kaduna ba wllh" motar ta tsaya, aka sauke
glass din baya da gaba, wata mata da baxata wuce shekaru hamsin da biyar ba ta bude motar ta sauko da
sauri tace "Lafiya kaka, me ke faruwa?" Tana magana ne tana kallon gidan don a xaton ta gobara ne, Hajja
ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Wllh matar jikana ce ta haukace mu kuma bamu san dawanan
Kaduna ba" Matar ta xaro ido tace "Subhanallah, a nan gidan take?" Hajja na kuka tace "Wllh kuwa, daga
Masar nake ban san dawanan garin ba" Wanda ke driving din motar ya sauko shi ma jin abinda Hajja ke
cewa yana kallonta da mamaki, dattijuwar matar tace "Toh me gidan fa?" Hajja tace "Wani me gida?? Ai
yana ciki ya rasa yanda xai yi da ita duk ta rotsa kaf kayan gidan tayi kwatsa kwatsa da shi har kayan kallo"
Guy din da ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan Hajja ta bi bayansa da gudu tana cewa "Ku taimakemu
mu daureta kafin a mika ta gidan mahaukatan" Matar ma ta bi bayansu xuwa cikin gidan, Basu tadda kowa
parlon ba, Hajja ta nuna masa hanyar stairs tace "Suna can sama, ka lallaba ka haura" Mahaifiyarsa dai na
tsaye ya juya ya kalleta tace "Be very Careful Aliyu" Hajja tace "Ehh wllh gidan Aliyu ne ashe kun san sa, ai
jikana ne, ni na haifi ubansa, ko ba wani matukin jirgin sama ba" Wanda aka kira da Aliyu dai ya haura
sama bai tsaya ba Hajja amsa ba, Hajja ta bi sa da sauri jikinta na rawa, Ummi ce tsaye corridor ta amshi
takarda da biron hannun Abuturrab cikin fushi take cewa "Baka da hankali ne ina magana kana magana
Aliyu? Ban isa da kai bane kake son ka nuna min" Abuturrab ya juya kawai ya nufi bangarensa xuciyarsa na
tafarfasa, Hajja na kallon Ummi kamar yanda Ali da mahaifiyarsa da suka hauro sama suka tsaya suna
kallonta, a hankali Hajja tace "Ya dauretan ne?" Bata jira me Ummi xata ce ba ta leka dakin taga Aneesah
tsaye sai huci take har sannan tana rike da tabarya, Jiddah da Maimoon suna can karshen corridor din sai
kallon Ali dake tsaye da mum dinsa Jiddah take sai dai shi bai ganta ba, meanwhile ita kuma mahaifiyar
Alin sai kallon Jiddah take, Ummi ta tsaya kofar dakin tana kallon Aneesah tace "Ajiye abun nan na
hannunki ki fito" Jefar da tabaryan Aneesah tayi ta fito dakin, bata kalli kowa a cikinsu ba ta nufi dakinta
kamar xata tashi sama, cikin daga murya Hajja ta dinga cewa "Allah ya tsine maki albarka shegiya, in sha
Allahu karshenki ya xo a gidan nan tunda kika ta6a kayan Jiddah, biliyoyi aka kashe kafin ayi mata wannan
kayan, don haka ko waye ubanki a Habuja yau sai an kai ni wajensa idan ma bara xai fara ya fara don kaf
dukiyarsa basu kai su siya kayan dakin Jiddah ba..." Ko kallonta Aneesah bata yi ba ta ciro makullin dakinta
da ta tusa a kirjinta ta bude kofar ta shige sannan ta kulle dakin da key, Mahaifiyar Ali da mamaki ya cikata
tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, menene amfanin haka?? Me mata suke son mayar da rayuwarsu a
wannan xamanin?" Hajja dake ta xufa tace "yan iska mana... to wllh karshenta ya xo a gidan nan, in har
xata iya ma kayan dakin da basu ji ba basu gani ba wannan tijaran to wllh tsaf xata kashe mutum da
ta6aryar hannunta, ga fa yar mitsitsiyar kishiyar tata can, warce a haihuwan kaji tayi jika da ita kai har
tattaba kunne, da er cikinta fa take kishi don bala'i har da lalata mata daki haka, toh Allah ya tsine maki
Nanisa" Ali ya kalli Jiddah da Hajja ta nuna, kallonta ya dinga yi da mamaki ko kiftawa babu, Mum dinsa ma
kallon Jiddah take har sannan, Jiddah ta sunkuyar da kanta, Hajja ta kalli Ummi tace "Huhuhu.... da na san
abinda xai faru gidan nan kenan yau wllh da Ramlah xan taho asirina a rufe ba ke ba, a kira min ita yanxun
ma ta xo taga abinda aka yi ma kayan yar ta, maxa kira min ita Maimoon ba mu ga ta shiru ba ai" a hankali
mahaifiyar Ali tace "Toh Allah ya kiyaye, Allah ya kyauta, but this is so bad wannan wani irin bakin kishi ne
haka ni Amina?" Hajja ta karbi wayar da Maimoon ke mika mata bayan ta kira Umma, Umma na daga kiran
Hajja ta fashe da kuka tace "Ramlah ki taho gidan Aliyu yanxun nan ba lafiya babu dalilinta, ki saka
hijabinki ko ba kaya ki taho kawai Ramlah" tana gama fadin haka ta mika ma Maimoon wayarta, Hajja ta
kalli su Ali tace "Ku kuma da ku ka saurareni har ku ka shigo ku ka gane ma idonku wannan abun al'ajabin
Allah ya maku albarka, kun dai ga me rayuwa ke ciki yanxu, kishi ne ake yi irin na tsinannun bayi, gashi nan
dai sbda kishi ta hallaka kayan dakin kishiyarta har lahira, to karshen aurenta ne kawai ya xo ba mu sani
ba" Ummi ta sauka downstairs ta xauna tana al-ajabin wannan abun da ya faru, tare Hajja ta sauko da Ali
da mum dinsa, sai a sannan suka gaisa da Ummi, Hajja na nuna Ummi tace "Ita ce uwar mai gidan fa,
amma kun ga babu wani hukunci da ta dauka, gata dai da takarda a hannu kamar malamar makaranta bata
ta6uka komai ba, ai samun uwa tsayayyiya ma wani abu ne a rayuwan nan wllh, tirrrr" Hajiya Amina na
kallon Ummi tace "Can we talk outside pls" Mikewa Ummi tayi ta bi bayanta suka fita compound, Ali na
kallon Hajja yace "Duk matansa ne kenan kaka?" Hajja tace "Ehh wllh, ita warcan yar farar yarinyar da ka
gani a rakube kamar mage sai gwale ido take to kayan dakinta aka yi ma wannan cin mutuncin da tijara,
kuma gobe satinta ke cika daya da tarewa a gidan, ita kuma me k'irar yan da6a warce tayi aika aikan ta kai
wata shidda ko shekara daya ina ga a gidan yanxu, toh kai in kai ne Aliyu don Allah wani hukunci xaka
dauka bawan Allah?" Ya sauke ajiyar xuciya yace "Sai kawai in sallami ita wannan me 6arnan don da alama
baxa ta bari a xauna lafiya ba" Hajja tace "Allah ya maka albarka, don kuwa wataran kashe Jiddar xata yi
har lahira ko??" Ali dai yayi shiru, Hajja tace "Xa ma ka san me gidan idan kana shige shigen jirgi sbda
matukin jirgin Najeriya ne, kuma ance shi kadai ne bakin fata" Murmushi yyi yana shafa kansa yace "Allah
sarki" Bayan wani lkci Ummi ta shigo parlon ta kalli Maimoon dake saukowa tace "Kira min Aliyu" Mikewa
Hajja tayi tace "A kira maki shi kiyi masa me?? Idan kina da wani amfani wllh shegiya nake Hauwa, ke da
xaki sa sai ya rabu da matsiyaciyar yarinyar yau amma kinyi shiru kin ja gefe kamar dai kin samu fim din
hausa kina kallo" Ummi bata ko kalli Hajja ba tace "Maimoon daga nan ku sauko har da Jiddah driver ya kai
ku can gida yanxu" Ali ya sauke ajiyar xuciya don fa gaba daya case din nan ya daure masa kai, yace "Allah
ya rufa asiri, Allah ya tsare gaba Kaka" Hajja tace "Wllh sai Aliyu ya saketa baxai xauna da yar da6a ba a
gaskiya da raina, don daga wnn abun da ta aikata xaka san tana hulda da rikakkun yan daba" Ba a dau lkci
ba Abuturrab ya sauko downstairs, har sannan fuskarsa a daure yake xuciyarsa na tafarfasa, Hajja tace "Ba
daure fuska xaka yi ba kamar wawa, mataki xaka dauka yanxun nan, ni abinda ya tsaida ni kenan don da na
tafi tuntuni, da fa a Masar ne har ni xa a kwashe idan yan sanda suka xo gidan nn wllh, sbda kamata yayi
tun farkon lamarin a kai masu rahotu, to wannan sai Ramlah kuma tace tana hanya" Abuturrab ya nufi Ali
yana kallonsa ya mika masa hannu, Ali yace "You just have to be calm and take things easy, do not make
conclusion while angry" A hankali Abuturrab yace "In sha Allah" Ali ya mike yace "Toh kaka Allah ya tsare
gaba" Hajja tace "Toh ina xaka kuma? Uban wa xa mu nuna a matsayin shaidun mu idan ka tafi?" Yayi
murmushi yace "Ai gidanmu na kusa da wannan Kaka" Hajja