Showing 273001 words to 276000 words out of 321711 words

Chapter 92 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

har yaje dakinta ya dauko mata drugs dinta, ya
bata ta sha sannan ta kwanta, ya gama abinda xai yi a laptop dinsa ya mike ya kulle kofar dakin ya dawo ya
kwanta kusa da ita, ganin kamar tayi bacci don idonta a lumshe suke ya kwanta side dinta not wanting to
disturb her yana shakan kamshinta me dadi da saka nutsuwa, Lumshe ido yayi shi ma, yana tunanin da ya
tafka asara babba in har ya rasa Jiddah, kasa daurewa yayi, yayi wrapping dinta jikinsa, lkci daya ya ga ta
juyo ta rufe fuskarta a kirjinsa a hankali tace "I really appreciate the car, Allah ya kara budi da daukaka,
Allah ya kare ka ya tsare ka duk inda xaka shiga, Allah ya bani ikon kyautata maka kamar yanda ka yi min
tun daga watanni sha daya da suka wuce har xuwa yanxu, i know I can't pay u, i.... " Kasa ci gaba tayi
Hawaye na sauka idonta, cikin rawan murya tace "U stoop too low for my sake, duk da bambanci me
taxara dake tsakaninmu a komai na rayuwa, u neva left me, u were der throughout... Ur sacrifice will for
ever remain in my memory, how can i ever pay for this?"




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada
wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan
kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun
fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan
wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan
link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697


Abuturrab was Speechless.... ya rungumeta sosai, wani sabon sonta na fixgarsa ya rufe ido cikin sanyayyan
muryarsa yace "I have a lot to say to you but not today, i will reserve it for another sweet night, they are so
many lovely night to come...." Ita dai bata bude idonta ba tana sauke numfashi a hankali. Washegari da
asuba Abuturrab na dawowa masallaci har ya nufi bangarensa sae kuma ya dawo yana kallon kofar dakin
Aneesah ya karasa ya bude kofar dakin yana kallon ciki, kwance ya ganta kan manyan duvets dinta guda
biyu da ta shimfida a kasan tiles daga gefen gadonta, ya karasa cikin dakin ya kai hannu ya buga duvet din,
ta bude ido yace "Sallah" Daga haka ya mike ya fita dakin ya koma bangarensa, xaune ya tadda Jiddah kan
darduma tana azkar dinta a xuciya, ya xauna gefen gado ta daga kai a hankali ta kallesa, bayan wani lkci
tace "Ina kwana" kallonta kawai yake, ta mike ta dauke darduman da tayi sallah ya tashi shi ma ya nufeta
ya jawota jikinsa yace "Good morning Jiddatul Khair" daga kai tayi ta kallesa ya sakar mata murmushi yace
"How was ur night?" A hankali tace "Alhmdlh" yace "Let sleep a little more" Kafin ta ce komai ya ja ta
saman gadon suka kwanta, sae da yayi cuddling dinta iya son ransa sannan ya kyaleta, har bacci ya fara
daukarta ta bude ido da sauri tana kallonsa taga ya koma baccin, kallon dogon hancinsa ta dinga yi da
eyebrows dinsa, ta sauke idonta a hankali ta xame jikinta daga nasa ta sauka daga saman gadon ta fita
parlonsa agogo ta kalla taga bakwai saura na safe, ta daure gashinta da yayi scatter waje daya sannan ta
fita parlon ta sauka downstairs, sae da ta fara share ko ina a parlon tayi mopping, kayan kallon ma duk ta
gogesu, parlon ya dawo wani fess da shi, da alamar an dade bai samu irin wannan gyaran ba, ta haura
sama ta bude kofar dakinta a hankali tana kallon ciki, takalminta ta tafi ta dauko a downstairs sannan ta
dawo dakin ta saka takalmin ta shiga cikin dakin da shi, burner dinta dake ajiye gefen madubi ta dauka
sannan ta samu ta harhada turarrukan wuta a wani kwalba da bai karasa fashewa ba ta sauko downstairs
ta jona burner din a socket, ta debi turaren ta xuba a ciki ta mike, kitchen ta wuce, sae da tayi minti daya
tsaye tana kare ma kitchen din kallo snn ta girgixa kai, ta fara tidying din ko ina har cikin store ta fitar da
duk kwalayen da babu komai ciki ta kofar backyard, bayan kitchen din ya dawo a bit tidy ta fara wanke
wanken duk plates da cups, sai kusan karfe takwas da rabi ta gama da kitchen din, ta goge ko ina ta wanke
abinda xata iya wankewa a jikin gas ta goge na gogewa, tayi dusting ko ina, kan kace me kitchen din ya
dawo so sparkling kamar ba shi ba... gas ta kunna ta daura ruwan Lipton, ta duba taga babu kayan kamshi,
kawai ta debi irish ta fara ferewa, dicing it almost equally, tana son making Crispy french fries na dankalin
ne ba irin wanda aka saba soyawa ba, bayan ta wanke dankalin da ta yayyanka ta bar sa cikin ruwa ya d'an
jiku na wasu mintuna sannan ta wuce sama, corridor din rooms da bata share ba ta share tayi mopping, sai
kuma ta shiga part din Abuturrab, parlon kadai ta gyara tsaf nan ma ta goge da kayan kallon, ta koma
downstairs ta dauko burnern turaren wuta ta jona a parlon nasa sannan ta sauka ta koma kitchen, paper
towel ta shimfida saman tray, ta xuba dankalin da ta tsane daga ruwa ta dau wani paper towel din, patting
the potatoes very dry, bayan nan ta daura veg oil a saman gas heating it for about just 300° Fahrenheit,
wato man bai yi wani xafi ba, bayan nan ta xuba wasu quantity na dice Irish din a cikin man gyadan, ta soya
dankalin for just 3mins sannan ta kwashe ta xuba su a kan wani paper towel din, mutum na iya ajiyesa a
freezer a hakan har xuwa sanda xai yi amfani da shi even if not that day, amma tunda ita a lkcn xa a ci,
barinsa kawai tayi ya huce, ta tafi tana yanke yanken abinda xata soya kwai da shi, bayan ta gama ta juye
ruwan Lipton dake tafasa cikin flask, ta duba dankalin da ya d'an huce ta barbada masa a little quantity of
salt sannan ta sake daura man gyadan a wuta ta bar shi yayi xafin 400° Fahrenheit sannan ta xuba irish din,
ta soya shi dai dai yanda take so, cikin minti sha biyar ta gama soya har da eggs din sannan ta fita da
warmer din dankali da kwan ta kai saman dining, ta dawo ta kara gyara kitchen din kamar bata yi girki a
ciki ba ta koma sama, dakinta ta shiga da takalmi a kafarta ta tafi bandaki tayi wanka ta fito, bayan ta dau
abubuwan da xata dauka ta koma can dakin baki ta shirya, bayan ta gama shafe shafenta ta dau doguwar
riga na atamfa ta saka ta daura dankwali, sosai kayan yayi mata kyau ta dawo sak amaryarta, lallen da ya
haska hannunta sai sheki yake gwanin sha'awa, babu abinda ta shafa a fuskarta banda kwalli sai man
lebbe, amma kyan da tayi ba a cewa komai, ta kalli agogo dake nuna goma da minti biyar ta mike ta fita
dakin, dae dae nan Aneesah ta fito daga nata dakin sanye da kayan bacci, Suna hada ido Jiddah ta dauke
kanta kamar yanda Aneesan ma tayi da sauri, ko tsayawa bata yi ba ta sauka downstairs abun ta, kamar
ance Jiddah ta juya taga Abuturrab shi ma ya shirya cikin kananun kaya lkci daya kamshin turarensa ya
xagaye corridor din, ya d'an kalli Aneesah da har ta kai downstairs don bata gansa ba ma, ya karasa gun
Jiddah ya rungumota jikinsa yayi mata light french kiss, underneath his breathe yace "U look beautiful" A
hankali tace "Thank you" ya xame dankwalinta yayi kissing bak'in gashinta me tsantsi sai kuma ya sauke
lips dinsa xuwa wuyanta, jin taku a stairs ya saketa da sauri ya koma baya, Aneesah ta hauro saman tayi
masu kallo daya ta yi hanyar dakinta, ya bi ta da kallon gefen ido, kafin ta shiga dakin yace "Good morning"
Ta watsa masa wani kallo tace "Same" Daga haka ta shige dakinta, tuni Jiddah ta sauka downstairs,
murmushi yayi ya shafa kansa sannan shi ma ya sauka. Ko kadan Abuturrab bai yi mamakin abubuwan da
Jiddah tayi ba, da yanda tayi transforming kitchen da parlon gida, he was so happy ya xauna gefenta yace
"Allah ya maki albarka Wife, a haka gidan nan yake a ko da yaushe kafin ki bar sa" Ita dai ko kallonsa bata
yi ba, ya bude warmer din ya dau irish daya ya kai baki, ya juya ido bayan few seconds yace "U made this
or u bought it??" Still ta ki cewa komai, sauka kasa yayi ya xauna saman carpet ya tankwash kafa ya bude
kwan ya dau spoon ya deba ya kai baki, lumshe ido yayi yace "umm.... So Yummy" mikewa tayi ta durkusa
kusa da abincin ta dau plate ta dibar masa, sannan ta fara hada masa shayi, shi dai kallonta kawai yake
babu ko kiftawa, komai tayi burgesa yake, ba kuma yau ya fara jin hakan ba, for long ya ke ji hakan... bayan
ta hada shayin ta dauka ta ajiye masa a gabansa a hankali tana kallonsa, kissing lips dinta yayi ya lumshe
ido yace "Thank you MPG💖" ita dai kallonsa kawai take da manyan idanuwanta, under neath his breathe
yace "My Precious Gift 💖" Ta sauke idonta amma har ranta taji dadin words din nasa, yace "kiyi serving
kanki sannan ki dibar ma Aneesah ma, i will be back soon" Daga haka ya mike ya wuce sama, ta bi sa da
kallo. Yana shiga dakin Aneesah ya tar da ita xaune can karshen dakin ko tunanin me take oho, ta d'an
kallesa yace "Taso mu yi breakfast" Shiru tayi yace "I am talking to you" a takaice tace "Aa ku dai ku ci, ai
kune masu gidan yanxu" Ya karaso cikin dakin yace "U admitted kina son xama da ni as ur husband
Aneesah, and for peace to continue reigning in our midst duk abinda na fada just adhere and obey that's
all, nace ki taso mu yi breakfast, i wasn't expecting you to decline that" Bayan few seconds ta mike ta dau
mayafinta ta yafa sannan ta nufosa ya bi ta da kallo har ta fita, fitowa yayi ya kulle kofar dakin sannan ya bi
bayanta downstairs din, Can gefe jikin kujera ta samu ta xauna, ya dau dankali da kwan da Jiddah ta debar
mata ya ajiye gabanta, sannan ya hada mata shayi ya ajiye mata, Jiddah dai ko kallonsu bata yi ba, a
hankali take shan shayin hannunta, Ya dau fork din dake plate din potatoes da Jiddah ta debar masa yana
kallonsu both yace "Kun gaisa yau?" Babu wanda yace komai cikinsu, ya kalli Jiddah sannan ya kalli
Aneesar duk babu wanda ya kallesa, yace "I am talking" Jiddah ta ajiye shayin hannunta ta mike, ya daga
kai ya kalleta yace "Ina xa ki?" Without looking at him tace "I want to ease ny self" daga haka tayi
wucewarta sama, Aneesah ta dau fork ta fara cin abincin gabanta, shi dai Abuturrab bai ce komai ba,
bayan mintuna kadan ya kalli Aneesah yace "You met her downstairs, sannan she made this meal and
tidied the whole house, why not even tell her weldone" Aneesah ta kallesa tace "Ni ban taso a gidanmu
naga Babba na gaida yaro ba, ai darajar girmanta da nayi ya ci ace ta gaisheni kafin ni kuma in ce mata
sannu da aiki, but tana jira ni in gaisheta, na san kuma na bata at least 7 good years, autarmu ma ta
girmeta" Abuturrab yace "Amma sai ki yi mata sannu da aiki ki ga ko xata gaisheki ko baxata gaisheki ba,
balle u met her ba ita ta xo ta sameki ba" Aneesah tayi wani murmushi tace "I am not surprise u are always
supporting her, to ta dawo ta xauna sai in gaisheta i know i won't loose" Abuturrab bai ce mata komai ba,
bayan some minutes yace "U asked for something few weeks ago, do u still need it?" Ta ajiye fork din
hannunta tace "Bana bukatarsa, kawai yanxu cikon kudi xaka bani a kawo min wasu furnitures din, kudin
da xa a turo min baxa su isa ba...." Ya girgixa kai yace "Bani da kudin furnitures because i didn't budget for
it this month... anjima xan saka maki abinda kika tambaya 2 weeks ago" Bata dai ce masa komai ba, yace
"And ki shirya before 12 xa mu shiga gidan neighbors dinmu a gaisa, so we can know each other more"
Tace "Aa ni baxan je ba, ku je dai da matarka..." Calmly yace "Ni kuma nace ki shirya mu je" Bata ce masa
komai ba, hakan ya sa ya mike ya koma saman kujera ya dau wayarsa dake vibrate, kallonsa take har ya
gama wayar sannan ta sunkuyar da kanta tace "Captain i think i have to go to do hospital don jikina baya
min dadi, ina yawan jin jiri da kasala sannan i don't have appetite na cin abinci...." yace "Ohk, Allah ya
sauwake" tace "Ameen, i need to see a doctor" kwashe duk kwanukan tayi da plate ta wuce kitchen da su
ya bi ta da kallo. Mikewa yayi ya wuce sama, bangarensa ya tafi hoping to see Jiddah there, ganin bata nan
ya dawo dakin baki, kwance ya ganta saman gado idonta rufe, ya xauna gefenta yayi kasa da murya yace
"Jiddah" Kin bude idon tayi ya dagota ta 6ata fuska tace "Ni bacci nake ji" Yace "Me yasa kika ki cin
abincin?" Ta bude ido tace "Saboda na koshi" Yace "Amma baki ci komai ba" shiru tayi masa, yace "Or are
u angry at anything?" Tace "Not at all" Ya kamo hannunta yayi lowering voice dinsa yace "U know what?" A
hankali ta daga ido ta kallesa, yace "For the sake of ta girmeki ku dinga gaisawa da safe pls idan kin
ganta..." Ta xame hannunta daga nasa tace "It's not necessary" da mamaki yake kallonta, can dai yace
"Why?" Tace "That's just my stand on it" yayi kasa da murya yace "No Jiddah ina son ku xauna lafiya kamar
yaya da kanwa pls, nasan in sha Allah Aneesah ta canxa halinta xa ku xauna lafiya without any problem"
Murmushi kawai Jiddah tayi tace "Ae da kai ya kamata ta xauna lafiya ba ni ba, ni ina ruwana da ita tunda
ba xamana take ba" Mamakin furucin dake fitowa bakinta upon her age ya dinga yi, and he saw nothing
other than sheer jealousy a idanuwanta, ta mike tayi shigewarta bandaki ta bar sa a xaune, shafa kansa
yayi thinking of where to start from, can ya mike ya sauka downstairs yana ta xaune parlon har kusan 12 jin
footstep a sama ya daga kai, Aneesah ce ta sauko cikin English dressing da veil dinta ta karaso parlon ta
xauna ba tare da ta kallesa ba tace "Na shirya" kallon agogo yayi sai kuma yace "Ohkk" ya mike ya tafi
sama, dakin Jiddah ya shiga, ya sameta xaune da wani littafi a hannunta, yace "Xa mu shiga gidan
neighbors dinmu mu gaisa yanxu, are u ready?" Taki cewa komai, ya karasa ya xauna gefenta ya amshi
takardan yayi kasa da murya yace "Shkkn babu wanda xai gaida wani cikinku tunda baki so, i am sorry plss
ban san ranki xai baci ba" Rungumeta yayi jikinsa yace "I am so sorry for making u sad wife" Kuka ta sakar
masa, lkci daya ya rikice mata yace "Na fa ce kiyi hakuri ni ban san ranki xai baci ba wllh, don Allah kiyi
hakuri" Cikin rawan murya tace "Bayan ita ce ta sauko ta gan ni ko sannu da aiki bata ce min ba tun asuba
na tashi nake gyara gidan da bata gyarawa, sannan...." Bai bari ta ci gaba ba ya fara kissing dinta. Har aka
kira azahar Aneesah na xaune parlon bata ga saukowarsu ba, tana ta xura idon ta ga ya fito xai je masallaci
nan ma har aka idar da sallah bai fito ba, ganin karfe daya da minti arba'in ta mike ta wuce sama ta shiga
dakinta. Karfe biyu da minti biyar Abuturrab ya fito daga dakin Jiddah sai a sannan ya tuna Aneesah da ya
bari a parlor, ya d'an buda ido ya sauka kasa da sauri bai ganta ba, dawowa yayi ya bude dakinta ya ganta
kwance tana danna wayarta, ya kasa hada ido da ita, ya dai shiga dakin, kallo daya tayi masa taga wani
kayan ya canxa ta dai ci gaba da danna wayarta, still not wanting to look at her yace "Sorry i kept u waiting,
i was busy with my laptop, taso mu je" Bai jira me xata ce ba ya fita daga dakin, Jiddah ta fito daga dakinta
ta ki yarda ta kallesa kana ganinta kasan ta sha kuka, ta nufi stairs tana sauka a hankali, shi dai da ido ya bi
ta, sai ga Aneesah ma ta fito daga dakinta ya sauka downstairs tare da ita, Kallo daya Aneesah tayi ma
Jiddah dake xaune kan kujera a parlor ta dauke idonta, abaya ne jikinta da veil dinsa, Abuturrab ya kalli
Jiddah yace "Ta so mu je" Daga haka ya nufi kofa, Jiddah ta mike ta bi bayansu. Abuturrab ya xauna a wajen
shan isa bayan sun shiga compound din gidan, Aneesah ta danna bell din parlon aka bude kofar wata
warce da alamar mai aikin gidan ce ta gaishesu, Jiddah dai ko kusa da kofar bata je ba sbda Aneesah dake
tsaye, mai aikin tayi masu Bismillah, Aneesah ta fara shiga parlon sannan Jiddah ta shiga, wata matashiya
da baxata wuce shekara talatin da biyar ba dake xaune parlon ta shiga welcoming dinsu tana kallon Jiddah,
mai aikin gidan ta tafi ta kawo masu ruwa da lemo, Matashiyar matar dai tana jiran su fadi daga inda suke,
Aneesah na wasa da xobunan hannunta tace "Nan makota ne, gidan da yake kusa da naku" Matar tace
"Ayya sannunku da xuwa, ai kam


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login