Showing 1 words to 3000 words out of 121650 words

Chapter 1 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

127

MACE A YAU
Written by Shatuuu
The story of Sulaim and Khulthum, the two besties and bussoms.
Completed
Shatuuu095@wattpad
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
[6/16, 10:31 PM] Anty Fauzar: 💄💅💖
👜👠💖
*MACE A YAU!*
💄💅💖
👜👠💖

01

✍️Shatuuu ♥️

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION



This page completely, wholly goes to Anty Sumayya...... I hail you

"Abu daya zan fada miki shi ne yanzu kin girma kin mallaki hankalin kanki, Kinsan
daidai da wanda ba daidai ba, Kinsan idan akace *budurci* ko virginity Kinsan me
hakan yake nufi, nasan Kinsan shi ne Abinda ya zaunar damu gidan mazajenmu har
yanzu, idan kika Bari ya kubce miki I'm so sorry to say bana tunanin zakiyi darajar
da wadda ta kaishi gidanta zatayi, inason Kiyi tattalin shi don kuwa shi zai fadi
tarbiyya da kika samu. Kada wani ya baki abu ki karba Kici, Kada wani ya kaiki
alley ko wani isolated area, Kawaye kisan wacece kawarki da kuma wa kike mu'ammula
dasu .... Abu na karshe ki kula da addininki sannna kiyi hakuri shi ne rayuwa! "

Se lokacin Mami tayi shiru yayinda Baki daya Sulaim tayi shirun tana sauraren
mahaifiyar ta, dago kanta tayi muryar ta Cikeda rauni tace

Inshaaa Allah Mami, bazan Baki kunya ba, zan zame miki abin alfahari!

Kai Mami ta gyada tace

"Allah yayi miki albarka, idan kikayi haka kin gama mana komai"

"Amin" Sulaim ta furta kafin Mami tace

Kije ki shirya da munyi La'asar Zamu fita, make sure kin saka dan kunne da sarka.

Murmushi Sulaim tayi wanda ya fito da dimple dinta hakan yasa tayi kyau sosae dukda
maganganun Mami taba ta suke ga kuma kewar gida da ta Fara ji Tun kafin lokacin
tafiyar. Mikewa tayi jiki a sanyaye 1 Don komawa dakinta, dakin yana facing wanda
ta fito Daga ciki, tura kofar tayi nan take komai na ciki ya bayyana, oil paint ne
jikin bangon dakin purple colour wanda yasa dakin yayi dan duhu kadan, gadonta Irin
silver poster bed dark purple, se wata resting chair a gefe, Daga Dayan barin akwai
study table da kujerar shi sannan walk in closet da kuma toilet, akwai stickers a
mammane jikin bangon dakin hakan yasa dakin ya zama very girly.

Tana ta jan kafa ta fada gadon tayi rub da ciki, hakan ya kasance aladar ta duk
lokacin da take son tayi tunani ko kuma ta zama emotional haka nan. Ta jima a
Wannan yanayin kafin kiran sallar laasar ya tashe ta, mikewa tayi ta shiga toilet
wanda komai na ciki yake light blue ta daura Alwala, wani lungu ta isa a dakin ta
shimfida sallaya ta Bada farali, Tana idarwa taji ana knocking hakan yasa tace

Yes... Come in please

Yarinya ce wadda shekarunta bazasu wuce sha uku ba ta shigo tace

Anty Mami tace ki shirya.

Kai kawai ta gyada hakan yasa yarinyar ficewa ita kuma ta isa gaban dressing mirror
dinta ta Fara assessing kanta, atamfa ce jikinta turquoise green se circle pattern
pink, dinkin skirt da Riga ne, kasancewar batada kiba yasa kayan sukai mata cas a
jikinta, powder ta shafa ta gyara daurin dankwali ta feshe jikinta da turare sannan
ta yafa pink veil ta dauki jaka tayi hanyar fita, kafin ta kai ga bude kofar ta
dawo da sauri ta janyo drawer ta dakko dankunne da bracelet sanin matsawar ta fita
haka se Mami ta dawo da ita, saboda Mami mutum ce da ta dauki abubuwan mata da
muhimmanci.

Tare suka fito Daga dakunan su, seda Mami ta gama assessing Sulaim kafin ta gyada
Kai Tace

"ko ke fa gashi kinyi kyau abinki kin fito a mace"

Murmushi kawai tayi saboda ita din ba Mai yawan magana bace, batada surutu ko kadan
wanda hakan yake fito da gentility dinta. Jakar Mami ta karba ta rufo dakunan kafin
suka sakko downstairs, gidan ya hadu karshe duk yadda zuciya zata kai ga hasashe to
abin ya wuce haka. Suna isowa tsakiyar falon sega wani matashin saurayi ya turo
main kofar parlour Sanye da kananan kaya wanda sukai masa kyau suka fito da
tsantsar yarintar shi, da murmushi saman fuskarsa ya karaso har inda suka ja tunga,

Mami ina zaku je da yammar nan?

Ya tambaya Yana maida dubansa kan Sulaim wadda Ke kallonshi fuska dauke da
murmushi,

Inda Jawad ubana ya aikeni.

Baki daya suka saki dariya Don karan Mami da Jawad babu wasa, fuska ya bata yace

Haba mana Mami daga tambaya,

Kallon Sulaim tayi tace

Leka kice dasu Iya Abu mun tafi.

To Mami" ta amsa mata kafin ta rabe Jawad ta nufi wata kofa, Baifi 5 minutes ta
dawo suka fita duka su ukun banda tsokana babu Abinda Jawad kewa Mami ka rantse da
Allah Kace Mami din kakar shi ce, a haka suka isa bakin wata bakar Prado se kyalli
take, suna isa wani daga cikin sojojin dake bakin gate ya iso tareda saluting Mami,
kanta ta gyada alamun ta karba tace

Babu damuwa, da jawad zamu fita.

Kanshi ya gyada yace

OK Ma'am

Jawad ya amsa key din ya shiga Mami ta kame a baya yayinda Sulaim ke gefen Jawad,
suna tafe suna hirarraki gwanin shaawa.
A gaban wani katon mall yayi parking suka fito, cikin nitsuwa suka taka ciki inda
babu bata Lokaci suka Fara shopping yawanci cosmetics ne, toiletries se suka fada
boutique din inda Mami ta dinga dibar kaya yawancinsu Abayas ne se kuma suit suit
na mata. Sun kusa 2hours a ciki kafin akai musu packaging aka kai har mota Jawad se
cin magani yake Don babu Abinda Mami ta siya mishi, daya isheta da mita se cewa
tayi

Jawad kudinka ne ko nawa?

Itakam Sulaim murmushi kawai take a haka har suka je gida.

Bayan kwanaki biyar aka gama dukkan shirin tafiyar Sulaim BUK inda anan ta samu
admission into Law, kullum zancen Mami daya ne Sulaim ta kula da wayanda take
mu'ammula dasu da kuma addininta, sanin son da Sulaim ke yiwa Law batada matsala
hakan yasa Bata taba ce mata tayi karatu ba don tasan zatayi.

Mami is very caring kuma Bata wasa da yayanta especially akan Sulaim wadda gani
take amana ce Allah ya bata kuma duk idanun duniya na kansu, da zarar wata baraka
ta auku zasui dariya tareda Allah ya kara..... This is the world we live in! Da
kanta ta hada mata kaya duk Abinda tasan zata bukata seda ta saka mata tareda sake
jadadda mata kula da kanta da addininta.

Kasancewar early February ne garin na Kano yayi lum shi babu Rana kuma haka babu
zafi se guntun sanyi da bai gama wucewa ba. Cikin bakar Benz Ja'afar ke driving
Wanda shi ne male version na Mami saboda yadda kamannin Mami suke prominent akan
Fuskarshi, babu yabo babu fallasa haka yake murza steeree Cikeda kwarewa yayinda a
gefenshi Sulaim Ke Zaune tana cikin abaya wadda stones suka kawata ta, fuskarta
tayi fayau se idanunta da ta boye su cikin dark shade hakan ya bayyanar da pointed
nose dinta. Itama fuskarta tayi kyau sede she looks pale. A baya kuma Mami ce Tana
rikeda newspaper itama tayi kwalliyarta da yake ita mutum ce me kwalliya. Gefenta
Dan gidanta ne Jawad Hannunsa rike da waya Yana ta danne danne ga uban headphone ya
saka hakan yasa gaba daya hankalinsa baya cikin motar. Wayarta dake hannun Sulaim
ce ta Fara ringing, ba tareda ta duba ba ta mika mata se ji sukai tana fadin

Soja marmari daga nesa, I salute you

Baki daya dariya suka saki Don sunsan Jabir ne his father's inherent the thug of
war..... A tsanake yace

Mami barka da warhaka

Barka dae, ya aiki dasu Imratu?

Gaba daya suna lapiya? Kun tafi Kano din.

Kai Mami ta gyada kamar yana gabanta tace

Gamu a BUK road, mun kusa gidan.

Dan tsaki yayi yace

Mami place me on speaker

Haka kuwa akai Sega muryarshi ta cika motar Baki daya, duka suka gaisheahi yana
fadin

Sulaim Duk Abinda Subay'a tayi miki just call me kinji?

Murmushin nan dai shi tayi tace
Angama Yaya JB

Se kuma ya koma kan Ja'afar yace

Mutumin make sure you strictly warn Subay'a cewar autar Mami ce Sulaim Kada tayi
wani Gigi....

Kafin ya bashi amsa Mami tace

Bakuda kirki matar yayan naku kuke yiwa haka, kanada digit dinsa call him but not
through my phone.

Daga haka kit ta kashe wayar aikuwa suka saki dariya kafin suka koma yadda suke.

A unguwar rijiyar zaki dake gefe daga tsakiyar birnin na Kano anan gidan babban
yaya Junaid yake inda a tsarin Baba da Mami nan ne gidan da Sulaim zata zauna Zuwa
lokacin da Allah yayi. Horn yayi take aka wangale gate din inda farfajiyar gidan ta
bayyana, Cikeda kwarewa ya danna motar ciki ya samu gefe yayi parking motar wanda
hakan ya janyo hankulan mutane dake cikin gidan. Yara biyu ne suka fito a guje baki
daya bazasu wuce shekaru shida da uku ba, gurin Mami suka Fara isa suka dane ta
saboda lokacin kowa ya fito, itama hannunsu ta rike baki daya suka nufi kofar
parlour, seda sukai sallama aka amsa kafin suka shiga baki dayansu, babu kowa se
Nanny din yaran da take tattare toys din da Ahmad yayi wasa dasu, suna zama Sega
wata farar mata ta fito wadda shekarunta bazasu wuce 25 ba, kyakyawa ce Irin
shouting beauty hakanan take irinsu masu manyan kyau kuma as kana Zaune dasu time
zaka gane cewar ba wani mashahurin kyau bane ba haka Subay'a take mace daya tak
wajen Junaid uwa ga Muhammad da Ahmad. Kujera daya ta samu ta xauna fuskar ta babu
annuri ko daya tace

Mami sannu da zuwa

Inda sabo kowa ya saba da halin subay'a, babu Wanda taki jinin gani sama da 'yan
uwan Junaid hakan yake tsoratar Dani Irin zaman da xa'ayi tsakaninta da innocent
Sulaim.

Lapiya lau Subay'a ya yaran.

Lapiya.

Daga haka babu Wanda ta kara yiwa magana se Sulaim da Jawad suka gaisheta suma tana
ta cika da batsewa ta amsa, dama Ja'afar tasan karya take tayi tunanin zaiyi mata
magana Don ya fita zafin kai. Ko ruwa bata basu ba suma babu Wanda ya nema cikinsu
se su Muhammad ne Ke ta faman basu labarai yawanci na school da islamiyya.

Har wajen Mintina sha biyar suka shude Bata ce musu Kala ba haka suma, se Mami tace

Subay'a Junaid baya nan ne?

Dago idonta tayi daga Kan wayarta data Ke dannawa tace

Ahmad go call your Papa.

Baki daya tsananin mamaki ya mamaye su kada ma Sulaim taji labari don tasan yadda
Matar Yaya Jabir take musu yadda kukasan ta hadiye su Don Imratu is one among
millions, unlike Subay'a wadda ita dole yaki ke tsakaninta da dangin miji. Ja'afar
ne ya bude Baki yace

Amma ke anyi.......
Sabr! Sabr!! Ja'afar

Mami ta katse shi kanta ta sake girgizawa tace

Don't do that, allow her.

Shiru parlour ya ratsa, Sulaim na kara girmama hakurin Mami cikin ranta, is not
like tunda tazo duniya take tareda Mami amma shekaru hudu da tayi tareda su Bata
tunanin akwai rana daya da taga wata baraka daga gurin Mamin ko alamun rashin
hakuri ko fada she's the best woman she have ever seen a rayuwarta, Shiyasa Mami is
her role model.

A hankali Cikeda nutsuwa da tsantsenin inda kyakyawar kafarshi zata taka ya fito
Daga wata karamar kofa, dogo ne Yana da tsayi, jikinshi a murmure yake babu alamar
rama ko daya, shi ba fari bane haka zalika baya cikin layin bakake, yana Sanye da
jallabiya brown me short sleeve, kanshi babu komai banda suma wadda batada yawa
kasancewar shi ma'abocin aski, ko cikin mata aka samu mutum me tsaftar Junaid
lallai se ayi barka.

Bakinshi dauke da sallama ya iso parlon sede ganin Mami da ahalimta yasa yaja ya
tsaya kafin ya maida dubansa kan Subay'a wadda gaba daya hankalinta yana kan
wayarta,

Mami kada kice min tun dazu kukazo? Subay'a me yasa baki kirani ba se yanzu? Sulaim
ya banga an kawo muku komai ba?

Duka cikin seconds yayi maganar ko nace tambayar, baki daya kallonshi suke da
tausayi Don Yana son yan uwanshi musamman Mami da Sulaim. Murmushi Mami tayi tace

Relax Junaid, yanxun nan muka zo, zauna a gaisa ko.

Kasa ya tsugunna yana sauke ajiyar zuciya ya gaida Mami sannan ya samu cushion ya
zauna, nan sauran suka gaishesu se kuma hira ta balle, can Sega Subay'a da abinci
da drinks itada masu aikinta. Babu Wanda ya kalli abincin bare suci se Jawad ne
dake food monger ne baya wasa da abinci.

Subay'a.

Mami ta kira sunanta lokacinda suka Mike don tafiya, dagowa tayi batareda ta amsa
ba itama Mamin she wasn't expecting such don haka ta cigaba da fadin

Ga Sulaim na kawo gidanku zata zauna, ban taba rokarki abu ba amma yau na roke ki
da Allah ki kulamin da amanata kamar yadda kike kula da Ahmad da Muhammad. Kinsan
wacece ita idan kika cuce ta Keda Allah!

Tana gama fadar haka ta nufi kofar fita, duka suka mara mata baya Harda Sulaim
wadda ta Fara sharar kwalla.

Shatuuu ♥️
[6/17, 7:38 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU!*

02

✍️Shatuuu ♥️

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
Fitowarta kenan daga daki, fuskarta dau tayi wani Irin haske kamar fitila Sede
babu digon kwalliya a fuskar hakan yasa fuskar ta kumbura saboda rashin kwalliyar
Don ba sabon Khulthum bane zama babu make up, Duk bala'i Duk masifa Bata taba fita
se tayi kwalliya hakan yasa matsawar ta fita batai kwaliyya ba to se ta koma tamkar
Marar lapiya.

Gidan karami ne Wanda dakuna kwatakwata biyu ne a ciki kanana wanda Bana tunanin
zai cinye gado da wardrobe amma hakan bai hana mazauna gidan alfahari dashi ba. Se
Bandaki a gefe da ko kofa babu se buhu, Daga gefe akwai langa langa (zinc) da aka
gewaye Dan karamin guri da ya bada kitchen wanda duk ranar da ruwa ya taso bansan a
ina matar gidan zatayi girki ba.

Tunda ta fito baki daya babu annuri ko digo saman fuskarta, tana sanye da bakar
riga wadda tayi dabbare dabbare, tabarma ta shimfida sannan ta dubi yan matan dake
tsaye kikam tace

Bismillah.

Babu musu suka zauna ita kuma ta koma ciki, dakin wata yan kwananniyar katifa ce a
shimfide a mata shimfidawa bedsheet, Daga gefe na hangi akwatuna wajen biyar a
jibge ga kuma katuwar Ghana must go a Cike taf da kaya, daga gefe kwanuka ne cikin
kwando, daidai Bayan kofa ta tsaya inda buhun Lalle yake a jingine ta diba sannan
ta tsugunna ta kwaba da sinadaranta, seda ta gama tsaf sannan ta fito inda yan mata
biyun ke jiranta, seda suka gaisa kafin ta Fara da wadda nake tunanin Itace babba,
Tunda suka Fara bata ce dasu uffan ba se waya da take abinta.

A hankali yara suka Fara dawowa daga islamiyya, biyu Maza se uku mata, ko sallama
basui ba suka shigo hakan yasa Khulthum tace

Dan ubanku ku fita a gidannan kuyi sallama.

Babu Wanda ya kalleta cikinsu sema dakin dake gefen nata da suka shige, tsaki tayi
ta cigaba da kunshin sega Amira ta fito ta zo inda ake kunshin ta tsaya Don babu
Abinda take so irin yadda Khulthum ke designing kafafun mutane Amma Khulthum taki
barinta ta koya.

Uban me kike Yiwa mutane Akansu? Dallah bar gurinnan.

Sumsum ta wuce, ta samu dan nesa da gurin ta zauna don Tana hangowa, amma ganin
haka yasa Khulthum daukar mafici ta wulla mata tareda fadin

Ke mayyar Inace ne, dallah tashi kafin na karya ki.

Mamaki sosae ya kama yan matan har daya a ciki tace

'Yar President dan Allah ki Bari ta gani mana.

Dake duk wanda yasan Khulthum da 'Yar President ya Santa saboda idan kuka hadu a
waje karya kake Kace daga wannan gidan take, sede kayi tunanin Irin yar wani shegen
ce baka taba tunanin Wannan kufan ne gidansu ba.

Rabu da ita, wanke wanke zatayi tasan aikinta ai.

Turo Baki Amirar tayi tace

Ki bayar a siyo OMO Kinsan babu.

Batace komai ba ta cigaba da kunshin har ta gama Sega sallamar wata dattijuwar mace
ta shigo da kuma alamun Matar gidan ce saboda yadda suke kiranta da Mama. Bakin
kofa ta zauna, yanmatan suka gaisheta Khulthum tayi mata sannu da zuwa sannan ta
koma gefe tana waya.

Amira maghariba ta kawo Kai ace har yanxu ba ayi wankewanke ba.

Mama to babu OMO a gidan ya kare.

Tsaki Mama ta danyi ta dubi inda Khulthum ke Zaune tace

Ummu bayar a siyo OMO Kada dare yayi.

Kafin Khulthum ta bada ansa A'isha ta fito tace

A hada da kudin ashana da gishiri saboda suma sun Kare.

Wai gidan ubanwa ake kai kayan gidannan ne? saboda ba ubanku ke bada kudin ba yasa
kuke almubazarranci. Ni na gaji Wallahi.

Gaba daya babu Wanda ya tanka hatta Maman se ta kunce bakin zaninta ta ciro hamsin
tace

Gata nan canjin da na dawo dashi Maza kiyi sauri ki sayo a tsallake.

Karbar kudin tayi ta fice, yayinda Khulthum ta Fara kiran Amir, amsawa yayi tace

Je ka karbo min kayan guga kasan gobe zan fita.

To

Ya fada ya cigaba da tsayuwa, tasan Abinda yake so amma se ta share shi ta cigaba
da Abinda take, ganin da gaske bazai je ba ta ciro 200 ta mika masa, murmushi yayi
yace

Yanzu kika Yi magana hajiyata.

Daga haka ya fice.

Ana Idar da sallar isha'i yayi daidai da gama shirin Khulthum, tayi wani Irin
fittinnan kyau, babu kuma abinda Ke tashi Daga jikinta banda wani kamshi me dadi.
Gyara zaman mayafinta tayi ta fito Daga daki, tabarma ce a shimfide inda duka yaran
Ke Zaune se A'isha da take bakin murhu tana karasa abincin dare, babu Wanda tace wa
Kala tayi hanyar zaure se Mama ce tace

Kulthum ina zakije.

Tsayawa tayi batare da ta juyo ba tace

Ashir ne a waje Yana jirana.

Daga haka tayi waje ta bar su da kamshinta, a kofar gidan Ashir na tsaye gefen
Lifan dinshi ya durkufar da kanshi yayinda wani magidanci ke tsaye wanda ya
tabbatar min cewar shi ne mahaifinki Khulthum saboda fuzgar kama da suke da Amir,
matsowa tayi tace

Baba sannu da zuwa

Juyowa yayi yace
Sannu dai khaltume, kin barshi Yana ta faman jiranki.

Kanta ta sunkuyar ba tareda tace komai ba amma tana takaaicin sunan da Baba ke
kiranta dashi Se Kace lokacin jahilliya zai dinga kiranta da khaltume, wucewa Baban
yayi nan suka gaisa itada Ashir wanda bakinshi ya kasa rufuwa tamkar gonar auduga
shidai Allah ya Dora masa zazzafan son Khulthum yarinyar tayi masa, kallonta yayi
yaga Baki daya hankalinta yana kan machine kafin ya kai ga magana tace

Wai se Yaushe ne zaka siya mota? Ni na fara gajiya da ganin ka da Lifan dinnan.

Dan dariya yayi yace

Rai dai Khulthum kuma ma banda abinki nida ba aiki nake ba ina zan samu kudin mota.

Tsaki tayi tace

Maganar kenan kullum, sa'oinka nawa ne suke da mota?

Kanshi ya dafe yace

Khulthum Haba mana, stop comparing me to others, ni daban sauran daban kowa yadda
Allah ya tsara mishi daban.

Kara bata rai tayi zatayi magana yayi saurin beating dinta yace

Don't suffocate the environment please, kinga yadda kikayi kyau...... Bana tunanin
duk duniya akwai Wanda yayi Saar Irin tawa.

For the first time Tunda ta fito ta saki murmushi wanda yake na gaske daga
karkashin zuciyarta tace

Kaima kayi kyau.

Kanshi ya gyada yace

Not as beautiful as you, so gobe zaki fara lecture

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login