Showing 78001 words to 81000 words out of 124042 words
sosai sbd ko kadan bazata so a shiga haqqin AA MAJEED ba bayan datasan girmansa
da sadaukarwarsa akan Inayah,
Ayanzu ko ita data Haifa Inayah din tayi alqawarin dakatar da kanta daga zuwa gunta
matuqar ba MAJEED din ya Basu Daman hakanba.
Yauma kaman baqi haka suka gaisa da juna saidai har umma Hadizan ta fice Inayah na
zaune cikin mota tana kallonta.
Fitowa tayi ta nufi ciki tana saka wayarta silent tareda sakawa cikin jaka.
Kaman yanda suka Saba kusan tareda Dr Abdul tayi aikin wunin ranar na duba patients
Dan haka tafara Jin sakewa dashi kaman yanda suke can farko.
Sai yamma sosai yau tadawo Dan haka Bata tsaya koinaba sai bedroom dinta tafada
wanka.
Tana fitowa sallar magriba tayi tareda saka kayan bacci tayi kwanciyarta a daki
tana Jin ciwon Kai na Dan damunta na gajiya.
Ta Bangare Daya jinta takeyi wani sukuku sbd gabaki daya wunin batai magana da
Abbinta ba abinda baitaba Kuma baya faruwa a rayuwarta,
Abbinta shine abokin firarta akoda yaushe kusan da safe da Rana kusanma dai time to
time suke waya idan har baya gari
Idan Yana gari kuwa tunda safe saitaga Abbinta take fita hakama kafin tadawo Zata
kirasa da darema tare sukecin abinci a dining Kuma tabisa palonsa kafin taje ta
kwanta Amma yanzu komai Yana neman canjawa duk sbd auren Nan dakuma zuwan Haj umma.
Da zaaci abincin dare Bayan kowa ya zauna zasu fara baiga tafito Kuma yau duk
baijitaba shima.
A natse ya dago ya 'dan kalli umma yaganah yace"
Inayah Bata dawo daga asibiti bane?
Tadawo,
Batajin dadine kanta na ciwo tun dazu.
Baice komaiba ya ajiye tissue din hannunsa tareda miqewa tsaye zai wuce Haj umma ta
riqe hannunsa ahankali cikin kulawa tace"
Ka zauna,
Ina zaka bakaci abincinba?
Bari a kuma kiranta.
Dan shiru yayi tareda Dan juyowa gefen zubbi dake kokarin ajiye juice data kawo
yace"
Ki kirata ta fito taci abinci.
Idan jikin yana damunta sosai Dr farhat zatazo yanzu ta dubata.
Yes Sir" zubbi tace tareda juyawa ta nufi dakin Inayah din.
Tana zuwa ta taddata kwance idanuwanta a rufe saidai ba bacci takeyiba waya takeyi
da Neesah ahankali sbd batako son doguwar magana yau.
Magana sukeyi da Neesah akan damuwarta na abinda yake sauyawa daga rayuwanta da
Abbi.
Cikin kulawa zubbi tace"
Abbinki yace a kiraki kifito kuci abinci.
Ajiyar zuciya Inayah sauke ahankali zatai magana Neesha tace"
Babes kice bakida lafiya sosai bazaki iya fitaba kodan abbin yanuna Miki kulawansa
dakika rasa kwana biyun.
Shiru Inayah tayi tana nazarin maganar,
Bata yiwa Abbinta Karya sbd Bai koyar da itaba Amma Kuma tanason kulawansa datake
neman rasa sbd zuwan Haj umma Dan haka ta amsa shawarar Kai tsaye tace"
Babes saimunyi mgn.
Kashe wayar tayi tareda ajiyewa gefe ta kalli zubbi a kasalance tace"
Zubbi bazan iya fitowaba kaina na ciwo sosai na koshi da abincin.
Juyawa zubbi tayi abinta ta isarda sakon ta juya ta koma kitchen.
Shiru kowa yayi
Haj umma na jiran ganin idan tashi zaiyi.
Umma yaganah ma jiran take taga abinda zaiyi.
Ajiye spoon din hannunsa yayi yanason miqewa Amma Kuma Haj umma da kanta tayi
serving dinsa cikin tsananin kulawa da kauna da maimaicin yaci abincin.
Katse shirun Haj umma tayi da cewa"
Yaganah Akira likitan dazata dubata Mana tun kafin dare yayi Amma nafisa ran stress
ne na aiki kawai may be idan tayi bacci zuwa safe Zata wartsake.
Dan yakamata ta saba da duka irin wannan stress din tunda likitace,
Kun sangartata shiyasa komai qanqantan Abu take maidasa Babba,
Saiga kuna rufe Ido kuna koyar da ita wani bangare na rayuwar
Ba'a sangarta da shiririta rayuwar Zata qareba
Aure zatayi Batasan kalan rayuwar dazata tadda b......
Tissue din daya goge Baki ya ajiye tareda miqewa Yana musu Saida safe gabaki daya.
Umma yaganah ma kasa shiru tayi cikin 'yar Wasa tace"
Aure Kam ai tariga tayi saidai ta muyita fama ta nutsu tasake sanin abinda takeyi,
Inayah kam dama ai akwai shiririta taqi girma indai tana gaban MAJEED.
Aikuwa Dole tasan ta girma tunda majeed din ba zauna zaiyiba zaman jiran tayi
hankali,
Aure yakamata yasan yayi Dan shekarunsa yanzu yakamata ace yafara Tara Yara Amma
gashinan aurenma baisan yayiba Dan shirmen Inayah,
Idanma batai hankaliba ai shikam bazai zauna jiran ranarda Zata hankaltuba aure
zaiyi manyanta yakeyi ba saurayi yake sake zamaba.
Tsit umma yaganah tayi tana sauraron abinda Haj umman ke fada cikeda mamaki da
shakka,
Me kuma yakawo maganar MAJEED da wani auren yanzu ana zaune kalau,
Auren dake kansa yanzuma baigama samun mazauniba a rayuwarsa ake maganar wani auren
yanzu?
Kenan Haj umma Bata dauki auren Inayah din da majeed aureba sai hanyar dakatar da
Hadiza kawai.
Jin tayi jikinta yayi sanyi bakuma gurin sauran gurin shigan abinci acikinta sbd
maganar Haj umma Dan haka ta Dan saki yaqen murmushi tana yiwa Haj umma din Saida
safe ta tashi.
Itama Haj umma tagama Dan haka ta miqe ta nufi dakinta Kai tsaye tana sanarda
Salimat ta hado ruwan zafin gasa Mata qafafunta.
Inayah dake daki tana jiran zuwan Abbinta dubata taji shiru Babu Wanda yazo tsawon
mintuna.
Sanyi jikinta da zuciyarta ke kokarin Yi matuqar Abbinta baizo dubataba to tabbas
yanzu ba kaman dah bane kenan,
A sanyaye ta zame ta qarasa kwanciya tana Jan bargo ta rufa.
Shigowar umma yaganah ce ta sanyata dagowa a sanyaye ta kalleta.
Itama umman jikinta a mace yake Amma Bata Bari Inayah din taganeba ta qaraso tareda
Zama gefenta tana cewa"
Yaya kan?
Ya rage ciwo?
Dago kanta tayi daga kan pillow ta kwantar kan cinyar umma yaganah tana lumshe
idanuwanta.
Ahankali tace"
Umma yaganah Ina Abbi?
Yana gurin Haj umma ne?
Numfashi umma yaganah ta sauke tareda dafa kan Inayahn cikin nutsuwa da kulawa
tace"
Inayah kina buqatan cire duka wani tunanin MAJEED kada ya kusantu da kowa bayan ke,
Haj umma mahaifiyarsa ce wadda duk duniya Babu Wanda yakaita matsayi agunsa,
Duk yanda yake tsananin kaunarki idan kina nuna Jin zafi ko kishin kusancinsa da
Haj umma Zaki iya jawa kanki matsala,
Ki cire tunanin komai ki maida hankali kan aurensa dake kanki Dan yanzu duk wani
shashanci ki ajiyesa ki fara sanin aurene akanki.
Kuma ki koyi hadiye Abu Dan Allah Inayah sbd banson afara samun damuwa tunda wuri
tsakaninki da mahaifiyarsa tunda dai ba zaunawa zatai har abada ananba dole wataran
Zata tafi,
Nima zuwa gaba kuna fara taramun 'yan jikoki Zan barku ayita kaimun renonsu..koba
haka ba?
Ko har shirin auren da kukai keda Neesah ya wargaje sbd Abbi ne mijin ba'a aura
masu rawar Kai ba..
Da 'yar tsokana ta qarasa zancen tana shafa kan Inayah sbd ta sake Dan tasan Zata
iya kwana da damuwa aranta.
Murmushi kawai Inayah tayi tana safe lafewa tace"
Umma yaganah ai Abbi ma kila ya manta da cewa nifa yanzu matarsace..
Nidai umma yaganah kiyi Masa tuni nifa yanzu ba 'yarsaceba kawai Ni matarsace Dan
Allah ya......
Buge bakin umma yaganah tayi tana cewa"
Zaki fara ko?
Ba nace ki ringa Kama bakinkiba idan bakisan me Zaki fadaba.
Umma yaganah fa kinaga ko Dan kallon mace bayamun saina 'yar baby Inayah wadda
ta.......
Bazakiyi shirunba kenan?
Shiru tayi tana hadiye sauran zancen Dan ita idan matsayin Mata zaisa kulawan
Abbinta yadawo Mata Zata zabi hakan da sauri.
Zubbi ce tayi knocking kofar dakin tashigo tareda Dr farhat wadda taketa zuba
qamshi Mai Dadi da adonta na doguwar Kuwait Abaya red fes da ita kaman ba dareneba.
Abbi ne yakirata ta taho duba Inayah,
Qarasowa tayi fuskarta daukeda murmushi da kulawa tana gaida umma yaganah kafin ta
zauna gefen Inayah tana cewa"
Oh my baby meke damunki?
Abbinki yakira hankalina ya tashi na dauka sosai ne jikin naki,
Meye matsalar?
Tashi zaune Inayah tayi daga kwancen ta zauna tana cewa"
Ciwon Kai ne kawai due to stress na aiki I think,
So Inaga dana samu nayi isashen bacci I will be ok by morning.
Duk da hakan Bari nai checking pulse naki,
Duka wannnan Zaki Saba ahankali ok?
Ki ringa samun bacci da hutu sosai.
Tea da cake Mai laushi akasa zubbi ta kawo Mata Tasha suna Dan fira sama sama kafin
sukai sallama Dr farhat ta fito.
Umma yaganah ce takaita har dakin Haj umma ta gaidata.
Da mamaki sosai Dr farhat ke sake gaida Haj umma dakyau tana mamakin ba umma
yaganah ceba Ashe ta Haifa AA MAJEED.
Haj umma itama sosai ta saki fuska suka gaisa da Dr farhat din Dan yanda Dr farhat
ta ringa gaidata cikin Jin kunya da girmamawa sosai yasa taga mutuncin Dr farhat
din sosai.
Bayan tafiyar Dr umma yaganah itama wucewa tayi dakinta ta kwanta.
Har Inayah tayi bacci cikin sanyi tana Jin damuwar rashin ganin Abbi.
Da safe haka taqi fita aiki da wuri Saida tayi breakfast da kowa.
A dining tana zuwa da Abbi tafara hada Ido Yana zaune cikin Navy blue Ralph Lauren
suit dasukai masifar yimasa kyau tareda fidda hasken lafiyayyar fatarsa dake cikin
hutu.
Gabaki daya Qamshinsa ya hadu Dana English breakfast din dake jere a dining ya
sauya gurin.
Cikin nutsuwa da kulawa da sanyin murya tace"
Good morning Abbi.
Idanuwanta ya kalla kafin ya dauke idonsa akai anatse Yana cewa"
Morning,
Yaya jikinki?
Complain zatayi umma yaganah ta katseta da cewa"
Yaya jikin Inayah?
Naji sauki umma,
Haj umma Ina kwana?
Umma yaganah good morning.
Zaunawa tayi tana kokarin fara cin abinci Haj umma tace"
Yaya kan?
Yayi sauki ko?
Eh naji sauki alhmdllh.
Fara cin toasted bread tayi tana daukan tea tafarasha.
Itace tafara gamawa ta miqe ta Zata fice Abbinta yace tajira zai ajeta asibitin.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/3, 1:04 AM] MG: *_49_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Bai dauki wasu mintinaba ya Gama shima ya goge bakinsa da tissue tareda miqewa
yabar dining din
A natse cikin sautin Mara qarfi yace"
Saina dawo umma.
Umma yaganah ya dan kalla itama yace"
Saina dawo.
Kusan atare sukai Masa adduar adawo lfy.
Zaune Inayah take tana chatting sama sama da Neesah dake son Jin labari daga gareta
tana ganin ya nufota tafara kokarin saka wayar cikin aljihun skinny jeans din dake
jikinta da farar doguwar Riga Mara nauyi wadda gefenta yake yanke daga qasa har
gurin qugunta.
Cinyoyinta da wandon ya lafewa ya Dan kalla Yana dauke kai kafin ya dakata daga
shiga motar ya juyo cikin fada yace"
Kije kisa native wear.
Kallonsa tayi da sauri tana kallon kayan jikinta....
Me Kuma kayanta yayi?
Sake dagowa tayi ta kallesa taga harya shige motar Yana zaune
Batace komaiba ta juya Takoma cikin gida ta sauya kayanta zuwa Riga da skirt na
atampa dark green da qaramin medium chantley veil ta fito riqeda qaramar Chanel
handbag.
Gaban motar ta bude tashiga suka wuce.
Suna fara tafiya ahankali ta juyo ta kallesa tareda marairaice fuska ta dafa dayan
hannunsa dake gefen datake cikin wata sanyayyar muryar shagwabar data Saba yimasa
tace"
Abbi idan nayi lefi Dan Allah kayi hakuri bazan sakeba.
Dan juyowa yayi ahankali ya kalleta da idanuwansa dake sake Jin hawayen shagwaba,
Tace please Abbi Dan Allah bazan sakeba.
Hannunta ta qarasa dorawa kan hannunsa
Ya Dan sake kallonta
Tana ganin ya kalleta ta gangaro da hawayen data Tara a Ido tana qara marairaice
Masa.
Rintse idanuwa yayi ya bude ahankali Yana dauke kai daga kallonta....
Besan yaushe Inayah ta iya wainnan abubuwanba na saurin kuka yanzu Musamman idan
tanason Abu daga garesa sbd tasan kukanta shine abu na karshe dazai so a duniya.
Ahankali ya sauke boyayyan numfashi cikin kulawa da sanyin lafazinsa yace"
Meyasa kike Wasa da abinci?
Kina aikin lfy kice bakisan ciwo da dama suna shigaba ta hanyar yunwa?
Karna kumajin zaaci abinci kinbada different story daga yau.
Okay?
Gyada Masa Kai tayi tana sake riqe hannunsa cikin nata.
Zare hannun zaiyi tasake riqewa tana cewa"
Nacefa bazan sakeba Abbi,
Ahaka zamu qarasa ai ni matarkace yanzu Ab....
Wani mummunan burki yaja dasu akan hanya Saura kiris motar bayansu ta dakesu.
Kallonsa takeyi da mamaki batareda ta damu da abinda tafadaba cikin kulawa tace"
Are you okay Abbi?
Juyowa kadan yayi Yana zuba Mata manyan fararen idanuwansa dasuka sata Jin gabanta
faduwa a Karo na farko sbd Abbin nata Bai taba zuba Mata idoba sosai Yana kallonta.
Koyaushe kallonsa akanta taqaitaccene duk da tsananin kaunar da son dayake Mata
amatsayin ubanta.
Sunkuyar da kanta tayi ahankali Jin kallon yayi Mata nauyi da karfi ahankali tace"
Sorry Abbi.
Hannunsa dake cikin nata ya janye ahankali batareda yace komaiba ya ja motar suka
wuce.
Shiru bakinta yayi sbd tasan ta zaro zancen da umma ke cewa idan batada abin fada
ta ringa yin shiru Dan haka tayi shiru Amma Kuma ai Dagaske shi mijintane kodai
Abbinta baya Sonta kenan da auren???
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun" ta furta a fili tareda dagowa ta kallesa tana Jin
kaman hankalinta zai tashi da wannan tunanin.
Har suka Isa asibitin Babu Wanda yasake magana
Yana parking motar Dr Abdul na shigowa harabar asibitin.
Fitowa Inayah tayi tana kallon motar Dr Abdul din kafin tadawo da kallonta kan
Abbinta.
Bai lurada Hadiza ba dake cikin motar ya sauke glass din motarsa Yana amsa gaisuwar
Dr Abdul daya iso cikin girmamawa kaman da can Yana gaidasa.
Ba tsammani sai ganin hadiza yayi tana qarasowa gurinsa.
Inayah ya juya ya kalla itama shi take kallo batareda ta kalli Inda Hadiza ke
tahowaba.
Hadiza na isowa cikin Jin kunya da nauyinsa Mai tsanani ta Dan kallesa a sanyaye
tace"
Ina kwana Abbin Inayah.
Daga ita data fada har su duka dake gurin tsit sukai cikin jujjuya zancen.
Batareda ya kalletaba cikin nutsuwa ya amsa a taqaice da cewa"
Muntashi lfy¿
A natse Inayah ta gaidata tareda kallon Abbin tace"
Abbi to waye zaizo daukana idan natashi tunda banzo da motaba?
Tada motarsa yayi ya dago ya kalleta cikin kulawarsa da kaunarsa yace"
Dr Abdul nasan zai Zama busy
May be mamansa idan Bata komai Zata iya maidaki gida,
Amma karki biya koina daga asibiti gida direct Zaki koma.
Jan motar yayi yabarsu tsaye Inayah nabin motarsa da kallo
Umma Hadiza kuwa wanin zallar farin ciki da mamakin MAJEED ne yacikata kenan majeed
din ya yarda takai Inayah gida sbd kawai ta zanta da 'yarta....
Tasan bazai iya yafe Mata ko kulata lokaci dayaba Amma ko ahakan ta gode da
karamcin.
Inayah rasa abin cewa tayi ta kalli umma Hadiza da farin cikinta Bai boyuba tace"
Zan dauki drop kokuma na Kira Charles idan natashi sbd Zaki wahala zuwa daukana
Kuma ki kaini har gida.
No Ayshatouh please kibari nazo na daukeki da kaina
Muna buqatan sanin juna
Damace Abbinki yabani please.
Dan murmushin yaqe tayi tana cewa"
Ok Zan tashi 2 yau Inshallah.
Zanzo kafin 2 Inshallah.
Juyawa tayi ta wuce dama Dr Abdul Bai tsayaba ya wucewarsa.
Bayansu umma Hadizan tabi da kallo tana jin farin ciki Mai tsanani ganin yayanta
dukasu biyun likitoci ne.
Duk da Inayah Bata Gama Zama qwararriyaba Amma zuwa gaba itama tasan Zata Zama abin
alfahari gurin marasa lfy dasu iyayenta.
Data tuna mahaifiyarta zatazo daukanta saitaji wani iri Amma Kuma ita kanta
tanason sanin umman Abdul din.
Qarfe daya da arbain kuwa saiga Hadiza ta iso asibitin Dan haka Inayah ta tattara
ta fito suka wuce gida.
A hanya umma Hadizan keta Jan Inayah din da fira da tambayoyi akan rayuwarta Wanda
komai ta tambaya sunan abbine amsar,
Anan tasake saddaqarwa MAJEED sbd yariga yayi ginuwar da Babu abinda zai girgizasa
Aran Inayah,
Shine ciki da Bai din rayuwarta Dan kuwa da ace wani mijin ta aura bashiba zaiyi
wuya mijinta baiyi kishinsaba duk da Yana matsayin ubanta sbd kaunar tayi karfi.
Kaman daga sama ta jeho Mata tambayar
"Ya maganar aurenki da Abbin naki?...
Shiru Inayah tayi cikin rausayar dakai tace"
Bansaniba,
Amma dai Ni aguna tanan bazan taba rabuwa da Abbi ba ko bayason auren nidai inaso
yanzu....
Kallon mamaki Hadiza tayiwa Inayar tana tauna zancen,
Lallai majeed yagama shagwaba Inayah ta yanda Babu ruwanta duk maganar datazo Mata
fada takeyi.
Tayaya zakiso auren idan shi baisoba ai Babu au......
Karki min Baki a auren please,
Ni inaso Kuma tunda inaso Abbi ma zaiso.
Murmushi Hadiza tayi aranta tana cewa"
Hmm wanna abbin naki Mai taurin Rai bazai taba kallonki mace ba bare matarda zai
iya kwanciyar aure da ita.
Suna Isa gida a gate ta ajiyeta batareda tashiga gidanba ta juya ta komawarta.
Inayah na shigowa gida a Palo ta tadda Dr farhat tazo sunata fira da Haj umma
Umma yaganah Kuma tana kitchen yau da ita ake aikin abincin sbd kwana biyu bataiwa
MAJEED abinci da kantaba.
Da mamaki Inayah ke kallon yanda har suka Saba a wuni daya daga zuwan Dr farhat
din.
Gaisawa sukai tana tambayar Dr farhat dalilin zuwanta tace Haj umma tasake zuwa
gaidawa da Rana sbd jiya darene Basu gaisa da kyauba.
Dakinta ta wuce tayi tube tayi wanka da sallah ta fito sanyeda doguwar chiffon gown
Mara nauyi kanta daure da silk scarf.
Tunda ta fito itama kitchen ta nufa gurin umma yaganah acan Tasha cornflakes sbd
bata iya cin birabisco ba shi sukai da Rana.
Da ita aka qarasa aikin tasaka hannu duk da bawani aikin ta iyaba bayan wanke
plates da cups sai dafa tea shima Dan Abbinta Nasha sosai yasa ta iya Dole.
Daki Takoma ta sauya kayanta sbd batason kamshin girkin dasukeyi.
Har dare Dr farhat na gidan da ita sukai dinner tareda Abbi dashima ya danyi
mamakin sabonta da ummansa daga zuwa.
Gurin cin abincinma haka dai umma yaganah da Inayah suka Zama Yan kallo har aka
gama kowa ya tashi.
Da Dr farhat Zata tafi har mota ta rakata ta wuce sai yabon Haj umma takeyi itadai
Inayah batace Mata komaiba akan aurenta da Kuma Dr farhat din Bata saniba hakama
Haj umma Bata Sanar mataba.
Kasa bacci tayi Saida ta fadawa Neesah zuwan Dr farhat sukaita maganar kafin ta
kwanta.
Washe gari Abbi Bai tashi da wuriba Dan haka ta wuce
Kuma acan ta tadda umma Hadiza Saida suka gaisa kafin ta wuce.
Yauma tana dawowa Dr farhat na gidan yau Kuma wai BP din Haj umma dinne yahau tazo
dubowa.
Haka takuma wuni dasu sai dare ta wuce.
Ahankali ahankali Dr farhat ta maida gidan nasu gurin zuwa fiyeda yanda take zuwa
adah,
Tayi sabo da Haj umma sosai ba laifi Dan kuwa Haj umma najin dadin yanda take zuwa
duba BP dinta akai akai Wanda Kuma a Yan kwanakin tagano irin son da Dr farhat kewa
MAJEED sbd hatta kulawar datakewa Inayah Mai girmace duk sbd MAJEED
Shikuma baimasan tanayiba.
Ta bangare Daya Inayah kwata kwata yanzu Bata wani gane kan Abbinta sbd dukkanin
kulawansa Takoma kan Haj umma sbd kwana biyun batajin dadin BP dinta sai hawa yake
Yana sauka.
Tun suna mamaki itada umma yaganah harsun koma Yan kallo Danma umma yaganah tana
kokari sosai gurin dannarta da hanata magana,.
Duk tabi Takoma sukuku batada walwala koyaushe a sanyaye take Dan yanzu koyaushe
idan dai Abbi na gida to Yana tareda Haj umma wadda yanzune tasan tana tareda
kaunar danta tunda ya maida hankali sosai akanta.
Ganin hakan yasa Inayah ke dadewa gurin aiki sosai sbd gidan ba Dadi tunda Abbinta
baida lokaci sosai.
Hadiza kuwa ganin tana samun ganin Inayah a asibiti yasa kusan duk bayan kwana daya
saitaje gurin Inayah asibitin su jima suna magana
Da hakan tafara sabuwa da 'yarta tunda dama Inayah bamai hayaniya ko riqe Abu bace
Ba jimawa tayi sabo da mutum sbd sanyin halinta.
Ahankali umma Hadiza ta fahimci abinda ke damun inayah na kishin Abbinta da kowa
karya fita kusanci dashi
Hakama Sam wannan auren nasu tasan idan akabi ta MAJEED kila ahaka zasu qare
amatsayin uba da 'ya.
Cikin dubara ta bawa Inayah shawaran ta fadawa antynta Hafsat abinda yake faruwa.
Dayake anty Hafsat tayi tafiya jiya tadawo aikuwa da farin ciki ta karbi shawarar.
Tana dawowa gida wanka kawai tayi tayi sallar la'asar tayi zamanta adaki zubbi
takawo Mata noodles data saka ta dafa Mata da sausage.
Wayarta ta fidda ta Nemo numbern anty Hafsat ta saka Mata