Showing 51001 words to 54000 words out of 124042 words

Chapter 18 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

71

*_31_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Sake Shan jinin jikinsu dukkaninsu sukayi Jin cm yace sufito atafi gida Nan suka
sake tabbatarda ba lafiyaba
Amma Kuma bilyamin qanin Anty Hafsat ya tabbatar musu da an daura aure,
To Kuma menene matsalar?
Sudai koma menene suna ganin da sauki idan har andaura auren Inayah da Dr Abdul
dinta.

Ita kanta Inayah data dawo hayyacinta tuntuni zaune take tana jiran ta Inda labarin
halinda aurenta yake ciki zai bullo.

Lokacinda bilyamin ya sanar dasu cewa andaura auren wani irin Al'amari taji
atattare da ita shi ba farin cikiba hakama ba baqin cikiba
Tadaisan jikinta ya mutune kawai Dan haka daqyar ta iya sauya Kaya kaman yanda su
Anty Hafsat suka takura Mata sbd Ango na tafe da jama'arsa suyi hotuna takuma gaisa
da abokansa da zasu bi jirgi a ranar su koma.

Tafiyar su Anty Hafsat shine ya fara daga hankalin umma yaganah harma da Inayah Dan
haka da kanta ta Kira cm din a waya tace Inayah tace Dan Allah abar Mata Hafsat da
Safnah har zuwa anjima.

Bai Musa ba yabar Anty Hafsat da Safnah Dan haka gidan yayi tsit daga umma yaganah
sai Anty Hafsat da Safnah da Neesah
Dr farhat ma ta tafi gida sai zaa wuce da Inayah din tace akirata.

Babu Mai wata doguwar walwala acikinsu sbd sudai anbarsu a duhu basusan meyake
faruwaba sai jiran tsammanin zuwan Ango da jama'arsa suke Amma basuga alamar hakan
Zata faruba ga wayarsa da Inayah ke Kira kaman zata zare Amma batama shiga kwata
kwata.
Sanin Abbi yadawo yasa ta miqe jiki mace ta nufa gefensa tana sake trying din
Abdul.

Kodata Isa knocking daya tayi tabude kofar tashiga daukeda sallama Mara sauti
sosai.

Baya Palo da alama Yana bedroom dinsa Dan haka ta zauna kan kujera tana sake trying
din Abdul.

Tunanin Kiran ummansane ya shigota ta nema numbern umman aikuwa tafara ringing.

Harta katse baa dagaba Dan haka ta fara rubutawa Abdul text.

Kofar bedroom dinsace ta bude Dan haka ta dakata rubutun tareda dagowa tana kallon
kofar.

Sanye yake da ash Lululemon wears navy blue dasuka fidda hasken fatarsa sosai da
alama wanka yayi ya shiryo cikin kayan Dan samun nutsuwa,
Qamshinsane ya gauraye palon take ya qaraso da yimata kallo daya yanajin wata
qululuwar damuwar auren da aka daura Yana dawo Masa.

Cikin boye damuwarta da Yar sakakiyar murya tace"

Abbi kadawo Ashe tun dazu?
Abbi Ina Heart ya....kasa qarasawa tanajin nauyin qarasa zancen sbd ita wani
lokacin mantawa takeyi da kunyar fadan wani zancen.

Dan juyowa yayi kadan ya kalleta ganin damuwa a tattare da ita cikin dan yanayin
kawar da zancen Kai tsaye yace"

Abdul na asibiti ya Dan samu attack ne aka wuce dashi asibiti.

Zaro ido tayi cikin tashin hankali da firgici Amma ganin ba fuskar Kuma wata
tambayar agurin Abbi yasata miqewa ta silale Takoma.

Koda ta Isa a tsattsaye ta taddasu kowanne ba acikin cikakken hayyacinsaba,
Tashin hankali da firgicin data gani ataredasu duka yasata bude Baki da qarfi cikin
firgici tace"

Badai Heart wani abun yasamaba kuma daga asibiti???

Umma yaganah kanta yakasa daukan abinda CM yafadawa Hafsat a taqaice na cewa A
MAJEED shine mijin da aka daurawa Inayah aure dashi yau.

Wani irin zufa takeyi tanajin kaman iskar dake gurin Bata isarta Dan haka da sauri
Neesah ma dake cikin tsananin shock ta Kama umma yaganah sukai daki taqara Mata AC
tareda bude suka windows tana cewa"

breath, just breath kada ki Bari Jan numfashi ya tsaya Miki kiyi kokari kijasa.

Kasawa umma yaganah tayi Saida Inayah tashigo dakin tana kallonsu a haukace tana
cewa"

Dan Allah ku fadan abinda yake faruwa,
Wane tashin hankali ne zaisaka umma wannan halin?
Anty Hafsat is crying,
Kema Neesah sai zare Ido kikeyi Kun kasa fadamun komai,

Kuka ta fashe dashi tana cewa"
Idan Heart ne ya rasu Dan Allah ku fadamun.

Kasa riqe maganar bakinta Neesah tayi cikin mamaki da qin yarda da abinda sukaji
tace"

Inayah Abbi ne fa ya aureki,
Dashi aka daura auren wai,
Shine mijinki yanzu,
Dama akwai aure tsakanin uba da 'ya??....

A jere take Watso kalaman sbd takai kololuwar kasa danne mamakin firgicin dake
ransu ita nata kalaman ne suka Riga na kowa fitowa a hargitse.

Kallon rashin fahimta Inayah ke Mata kafin ta kalli umma yaganah da duk tayi wani
iri Dan kuwa CM bazai musu qaryaba,
hakama tafi kowa sanin MAJEED ba jahili bane bakuma mahaukaci bane da iliminsa
Idan harya auri Inayah hakan na nufin bashine ya haifetaba kenan tun asali....to
wannan wane irin masifa ce Zata sakasa auran yarinyarda take matsayin 'yarsa Koda
ba shine ya haifeta ba tasan Dole ba auran dadin Rai ne yayiwa Inayah ba.

Anty Hafsat ce tashigo tana sake samun tabbaci daga uban mijinta Alhaji babbah cewa
Inayah dai ba 'yar MAJEED bace Kuma shine dai mijin daya aureta yau Dan haka suyi
kokarin ganin sun tausar da ita batareda taqara Masa tension ba akan Wanda yake
ciki yanzu.

Da rikitaccen yanayi Inayah ta maida kallonta kan Anty Hafsat data shigo dakin
cikin kosawa tace"

Anty Hafsat meke faruwa dan Allah?Bazan iya daukan wannan shirun da kowa kemun ba,
Maganar Neesah ma Ni Sam bangane itama me take nufiba.

Ahankali Anty Hafsat takama hannunta suka nufi Inda umma yaganah take ta zaunar da
ita itama ta zauna suka sakata tsakiya itada umma yaganah ahankali ta kalleta cikin
sanyin murya tafara cewa"

Inayah bamusan komai dayasaba kokuma yazama sanadi komai for now Amma dai abinda
yake gaskiyar zance shine aurenki da Abdulsamad Bai yiyuba Amma aure kam kaman
yanda aka sanar Mana tabbas andaura Miki aure da...

Dan shiru tayi tareda kallon umma yaganah dake saurarenta itama Dan Hafsat din
tafisu sani da fahimtar komai da kyau tunda itace tayi waya da mijinta yayi Mata
bayanin komai hakama Alhaji babbah yayi Mata bayanin komai qarshema yanzu driver na
hanyar zuwa daukansu su duka zuwa gurin Alhaji babbah din Dan shine kadai zai iya
yiwa Inayah bayaninda kila Zata fahimta.

Kaman daga sama sukaji Inayah din tace"

Da aka fasa aurena da heart sai aka daura mun da Abbi???
Right?
Shine abinda kikeson fada mun?

Shigowar zubbi da sakon isowar driver daga can family house yasa Anty Hafsat dojewa
amsa tambayar Inayah din Dan haka ba Bata lokaci takama hannun Inayah din Umma ba
Bata jira komaiba ta sauko gadon tareda miqewa ta zari mayafi suka fito Dan kowa
matse yake da a wayar Masa da Kai akan wannan sauyin lamari Mai wuyar ganewa.

Koda suka Isa gidan Alhaji babbah na masallaci sallar la'asar Dan haka Saida suka
jira ya dawo a babban Palo Haj mama na sake yimusu nasiha a fakaice Dan ita saima
taji tafi jin dadin MAJEED daya aure Inayah Dan kuwa da tun farkoma sun San bashine
ya haifetaba baida alaqar Jini tako Ina da ita da tuni sun matsanta Masa ya aureta
yafi fashe fashen aurenta da akaita Yi shima Kuma ga lokaci yaja Bai taba aureba
ace haryanzu matsayin saurayi yake Dan haka Kai tsaye ya bayyanarda farin cikinta
ana fada saidai Kuma ta tausayawa Inayah sosai ta yanda Rana tsaka Zata karbi
zamanta ba 'yar mahaifintaba datake tsananin so da kauna amatsayin ubanta ita daya.

Kusan Banda Inayah data kasa fahimta bare yarda har lokacin
Sun Gama fahimtar dai Abbi bashine ya Haifa Inayah ba Kuma shine mijinta a yanzu.

Duk sun gane wannan abinda basu ganeba shine meya Hana a daura auren da Abdulsamad.

Alhaji babbah na dawowa daga masallaci suka dunguma palonsa lokacin har CM ma ya
iso Yana gidan.

Zama kowa yayi jiki a sanyaye Musamman Inayah da kusan komai Bata ganewa Takoma
kaman wata mutum mutumi.

Ita Alhaji babbah yafara kalla cikeda tausayawa da kulawa kafin ya maida kallonsa
kan umma yaganah datake Babba zatafin fahimtar komai Kuma idan ta fahimta komai
zaifi tafiya daidai Dan itace Zata ringa dorata a hanya akan auren da haqqoqinsa
tunda tare suke rayuwa gida daya.

Gaisawa suka fara Yi kafin ya Dora da fadar"

Haj yaganah ya fama da hidima da jama'a?
Allah yasa angama lafiya yakuma sanya Alkhairi.
To wani babban Al'amari yafaru tsakanin shekaran jiya zuwa jiya da Kuma yau din
kafin daurin aure Wanda yasa aka samu sauyi cikin qurarren lokaci.,

Shi aure nufine na Allah Dan haka kada kuyi Wani mamaki da Al'amarin ubangiji,
Inayah dai kaman yanda a da MAJEED shine jigonta yanzuma shine jigonta Kuma
ma'ishinta Dan kuwa shine mijinta haryanzu yafi kowa iko akanta.

Basai an tsaya tone toneba anan ko dogon bayani Wanda Zata samu daga baya idan
ansamu komai ya lafa
MAJEED dai bashine mahaifinta ba Kuma yada alaqar Jini tako Ina da ita bamu kadaiba
duniyama Bata taba sanin da hakanba sbd riqon Amana da Gaskia da yayi Mata da
zuciya daya Kuma a wannan duniyar abune Mai wuya samun irinsa Dan kuwa ko 'dan
jininka baka riqewa ba Amana irin hakan Amma shi ya riqeta ya reneta da Amana da
kauna bai taba barin tasan bashine mahaifinta ba idanba yanzu da hakan ta bullo ba
Rana tsaka shima Kuma hakan da yayi yayine duk akanta sbd har gobe itace kulawarsa.

Shi Dr Abdul dai anfasa aurensane sbd uwarsa daya ubansa daya da Inayah Wanda shi
wannan bayanin ba hurumin shigata bane
Dan hakan Ina fatan Kun fahimci yanayin da aka shiga dakuma wandama zaa Shiga Nan
gaba sbd Koda Wasa karnaji anyi wata fitina kokuma tashin hankali akan wannan
auren,
Shima MAJEED din danasan yafi kowa shiga mugun yanayi akan wannan auren nai Masa
nasiha Kuma Inshallah Ina fatan ya dauka.

Dan hakan Haj yaganah sai anyi kokari gurin fahimtar dasu wasu abubuwan aure ya
wuce mutum yayi Masa daukan dayaga dama,
Allah ya sanyawa auren albarka,

Suma can Allah yabasu ikon warware komai lafiya.

Waiwayowa yayi zaiwa Inayah nasiha akan itama saita dauki qaddara sbd da tashin
hankali samun kanka irin wannan yanayin sai ganin sukai tana Jan numfashi alamar
attack Zata samu
Kafin suyi wani yunqurin tasamu attack take Dan haka a rikice suka dauketa zuwa
cikin gida.

Allah yasa akwai likita taredasu Neesah taredasu Amma bada ita akaje palon Alhaji
babbah ba
itace tayi gaggawar fara taimakawa Inayah din wadda takejin kaman zata rasa ranta
sbd yanda numfashinta ke Neman yankewa Neesah na taimaka Mata gurin janyosa da
karfi.

Ganin kaman Al'amarin zaiyi girma sosai Dole suka Kira Dr farhat wadda kafin ta iso
suka dunguma da Inayah din zuwa asibiti sbd tuni umma yaganah takira Abbi ya sanar
Masa yace su wuce asibiti gashinan zuwa asibitin.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biyaπŸ‘‡
07040727902

MTN cardπŸ‘‡
09134848107
[10/20, 1:34 PM] MG: *_32_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Private hospital din dake anguwarsu Alhaji babbah aka kaita sbd kafin suce sunje AA
specialist wato private hospital dinsu akwai nisa daganan da hakan suka tsaya tanan
kusa.

Cikin gagawa suka karba Inayah din
Neesah ma bata barmusu aikinba su kadai da ita sukayi Dan sunada fahimta tana sanar
dasu itama likitace suka barta ta taimaka musu tunda dama itace kusan tasaba
taimakawa Inayah idan irin hakan ta taso.

Umma yaganah gabaki daya kanta neman sake cakewa yakeyi da wannan Al'amuran daketa
faruwa daga wannan sai wannan,

Har cikin ranta takejin kauna Mai tsafta da tsanani akan MAJEED da Inayah sbd sune
danginta itace danginsu Dan lokuta da dama sukan mantama basuda alaqar jini da
juna.

Badan a yanda yanayin komai ya fallasa kansa ba lokaci daya ba zato ba tsammani da
Babu Wanda zai kaita murnar Auren MAJEED datake addua da fatar gani tsawon shekaru.

Hakama auren Inayah wani babban burinta ne shima datake fatan Allah ya nuna Mata ya
cika a yau din
sai gashi Allah yacika Mata burin Auren dukansu a yanayinda Babu wanda yataba
tsammata,

Ku kansu basuma San farin ciki zasuyiba ko damuwar sanin ba Abbi ne ya haifi Inayah
ba.

Anty Hafsat ma zuciyarta kusan Kashi Kashi take kasuwa tana rarraba Mata tunani sbd
ayanzu Bayan Jin bayanin yanda Al'amarin yake daga bakin Alhaji babbah taji
zuciyarta na farin ciki da auren Dan kuwa Inayah Allah yayimata kyakkyawan sauyin
dayafi duka tarin mazan data rasa abaya sbd Abbinta yakai kowanne level da ake
kwadayin namiji yakai badan tashin hankalin halinda Inayah tashigaba da a fili Zata
fara bayyanarda farin cikinta akan wannan tsintar damu akala da Inayarsu tayi Dan
kuwa Abbi kam Masha Allah.

Sbd wadda tasaba ji da matsalarta na kusa yasa ma'aikatan asibitin Basu Sha wuyar
taro yanayinta ba tadawo hayyacinta saidai take bacci ya dauketa sbd kusan wannan
attack din yafi wainda tasaba samu abaya.

Kwantawa hankalinsu yayi ganin tadawo daidai tasamu bacci Amma kallo daya zakawa
fuskarta ka gano baccin na tattareda yanayin firgici data shiga.

Suna zaune a dakin datake anty Hafsat na kokarin daidaita ACn dakin da yayi yawa
umma yaganah Kuma na zaune tana kokarin amsa wayarta da Mimi ke Kira saigashi ya
iso yashiga dakin cikin nutsuwa sanyeda Lululemon wears har lokacin da alama Bai
tsaya sauyawaba zuwa wasu manyan kayan.

Fresh skin dinsa daya bayyana sosai cikin kayan anty Hafsat da Neesah suka kalla
suna sake tabbatarda kyau da tsarin da Allah yayiwa Abbin
Take suka sake Jin tabbas ta wannan fannin Inayah Dinsu tagama dacen miji illa
kawai baqin cikin dazata Shiga sanin Abbinta datafi so fiyeda komai baida alaqan
Jini da ita
Tsintar yayi,kyautarta akai Masa kokuma tayaya ya sameta Allah ne kawai yasani
saishi da umman Abdul din.

Cikin girmamawa anty Hafsat da Neesah sukai Masa sannu da isowa

Da qaramin sauti ya amsa Yana dan kallon Inayar kafin ya kalli anty Hafsat sbd umma
yaganah na waya yace"

Doctors din sungama dubata ne?

Neesah ya nisan yanayin nata?

Firgici ne kawai data shiga ya daketa sosai Amma Inshallah lafiyanta kalau yanzu
anmata allura ne sbd tayi baccinda kanta zai Dan warware ya rage Mata tashin
hankalin.

Gyada Kai yayi ahankali tareda sake kallon Inayah datai wani iri cikin lokaci
qanqani.

Dan gajeran numfashi ya sauke tareda juyawa yafita zuwa ganin likita Dan bayason ta
kwana a asibitin gida zasu koma tunda suna tareda qwararrun likitoci a gidan.

Fitarsa da mintuna biyar sai gasu Mimi sun iso asibitin a gigice sbd tashin hankali
biyu,
Na farko Jin auren MAJEED da Inayah dakuma Jin uwarsu daya ubansu daya itada Dr
Abdul ga qarin halinda Inayar tashiga.

Jigum jigum sukai a dakin wasunsu na sake Dan jajanta wannan alamari da masu godewa
Allah da baa Riga an daura aurenta da Dr Abdul dinba dan da abin yafi lalacewa.

Umma dai bayan taga Inayah ta tashi babu abinda take fata Dan ita kanta yanzu
tanajin dacin da Inayah Zata Shiga,.

A sanin dataiwa Inayah kuka da baqin cikin dazata Shiga na zaman Abbi ba
mahaifintaba zaifi Mata ciwo da radadi fiyeda auren Dan kuwa tafi buqatan ace
alaqar jini suka hada Bata auratayyaba.

Har yamma lis suna asibitin Inayah Bata farkaba sai magriba.

Tana farkawa takasa kallon kowa a dakin sbd yanda duk sukai jigum jigum yabata
tabbacin abinda yafaru kafin zuwanta asibitin Gaskia ne haqiqanin Gaskia Kuma Dan
haka Batasan ta Ina Zata fara bayyanarda babban abinda takeji tokare da zuciyarta
da maqoshinta.

Cikin kulawa da sanyin jikin yanayin da Inayah din ta nuna umma yaganah da Anty
Hafsat suka fara kokarin magana saiga shigowar Abbi Wanda Yana shigowa qamshinsa ya
gauraya dakin suka tsit suna jiran abinda zai faru Kuma ga Inayah din ga Abbi a
amatsayin ma'aurata.

Yanayinsu yasashi basarwa tareda Dan kamewa ya kalli Inayah data dago ta zuba Masa
Ido tana Neman fashewa da kuka yace"

Kina farkawa Kuma Zaki fara wani kuka agurin.

Neesah dake gefenta ya Dan kalla yace"

Ku shirya gida zaa koma da ita yanzu.

To" Neesah tace tana kallon Inayah din dake kokarin fashewa da kuka Amma takasa sbd
abun datakeji ya girma qwaqwalwarta.

Juyawa yayi ya fice suka biyo bayansa.

Anty Hafsat motar CM zatabi itada Mimi da Safnah
Su Kuma su Inayah din motar Abbi zasubi Dan haka suka nufa motar Kai tsaye umma
yaganah na riqe da hannun Inayah dake kokarin zubewa sbd tangadin datake na Bata
cikin cikakkiyar nutsuwarta.

Kaman yanda suka Saba fitarsu da Abbin idan takama Inayah ce a gaba Dan haka yau
dinma itace agaba sai umma da Neesah a baya.

Bayan sanyin Ac na motar da qamshinsa daya cika motar Yana zagayawa Babu Mai ko
motsi acikinsu kaman ba kowa a motar kowa da tunanin daya shiga Banda Inayah da har
lokacin qwaqwalwarta Bata fara aiki daidai ba dif take Bata ji Bata gane komai
yanzu.

Suna Isa gida Dole Neesah ce ta kamota suka nufi ciki tana kokarin kaita bedroom
dinta ta qwace Takoma Palo tana kokarin bin bayan Abbi cikin dimauta tana cewa"

Abbi ne kawai zaifadamun Gaskia na yarda da abinda duk ake fada,
Abbina ne kawai zan yarda da maganarsa.

Da sauri umma yaganah ta riqota tana cewa"

Ki nutsu Mana Inayah,
Me zakije kice Masa yanzu?
Bakiji anfada Miki yanzu mijinki bane,
Qarya zamu taru mu Miki ne?
Alhaji babbah zai Miki qaryane?
MAJEED din dakikeson saiya fada Miki komai Yana cikin damuwa sosai bakya gani?
Zaki sake daga Masa hankali da kukan Nan nakine idan kikace rikicewa zakiyi.

Rikitaccen Kuka ta fashe dashi Mai tsananin qunci tana cewa"

Ni bazan yardaba wlh abbin ne mahaifina,
Banason kowa a mahaifi sai Abbi,
Har umman Abdul din banaso amatsayin uwa Ni Abbi ne kawai uwa Kuma ubana...

Da sauri umma ta rufe Mata Baki jikinta na rawa sbd jikinta daya fara sanyi itama
da irin kukan da Inayah din fasawa Wanda tunda take Bata taba yin irinsaba sai yau.

Rirriqeta sukai ta zube qasa tana sake tsananta kukanta zuciyarta na Mata wani irin
zafi da radadi...

Idan ba abbine mahaifinta ba ai ita asaran duniya da baqin cikin duniya tana cikin
cikinsa da wannan mummunan labarin da gwara ayita fasa aurenta har abada akan
wannan labari...

Bazata taba yarda da maganar kowaba sai taji daga Abbinta cewa gaske bashine ya
haifetaba.


Dukkanin sautin kukan datake yanajinsu Amma Bai iya zuwa Inda suke dinba Dan kusan
yafita baqin ciki da wannan bankadar,
Dan yaso ya tsaya a ubanta na har abada saidai qaddara Bata bar hakan ba Dan kuwa
Koda warware auren Nan akayi har abada ita zaa Kira da matarsa ta farko wadda
tafara daukan igiyoyin aurensa haka itama har abada shi zaa Kira da mijinta na
farko daya fara riqe martabar aurenta.

Kuka Inayah da tashin hankali sosai tashiga lokaci daya Wanda ya gigita umma
yaganah da Neesah harma dasu zubbi da Salimat sun Shiga tashin hankali da damuwa
sosai ganin halinda Inayah din ke ciki

Ta bangare daya shi kansa Mai gidan babu Wanda yakuma ganinsa har washe gari,

Abincin gidan ranar haka aka daukesa aka fitarwa Bosco ya rarrabawa securities din
anguwar abokanansa sbd Babu Mai nutsuwar cin wani abinci.

Da zazzabi Mai zafi Inayah ta kwana Dan kaman yarinya qarama Takoma musu daqyar
baccin wahala ya daukeda jikinta da mugun zazzabi.
MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biyaπŸ‘‡
07040727902

MTN cardπŸ‘‡
09134848107
[10/20, 10:13 PM] MG: *_33_*
*_Arewabook@Mamuhgee_*
Da zazzabin ta tashi da safe Dan haka sallah kawai ta iya Yi Takoma ta kwanta sbd
tsananin ciwon Kai Dana kirji,

Ana Gama breakfast umma yaganah ta sallami baqinta aka kaisu aka sanya mota tareda
Dan abin arziki gidan yasake daukan tsit.

Su zubbi tuni suka shirya komai a dining na breakfast kaman yanda suka Saba.

Umma dai a dakinta tayi breakfast din Neesah ma bata fito dining ba Dan a daki
Tasha tea Danma sunyi sunyi Inayah ko tea din Tasha taqi.

Har lokacin bata daina tsiyayar hawayeba,
Takasa yarda da wannan qaddarar lokaci daya wai ace Abbinta shine mijinta,

Tayaya Zata fara fuskantar wannan maganar,
Har abada bazata taba iya karban Abbi amatsayin mijintaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login