Showing 57001 words to 60000 words out of 124042 words
Inayah dake kuka sosai
har hancinta Saida yayi jajir Bayan idanuwanta da fuskar gabaki daya.
Karbe wayar Neesah tayi tareda dorawa akan kunnenta cikin tausasa murya dakuma
damuwa tace"
Dr wannan kaman kuna neman butulcewa qaddarar da Allah yake jarabtarku da itane,
Inayah matar wanice yanzu daga ita har Kai kunsan me ake nufi da hakan
Badan kana matsayin muharramintaba dasai nace wanna haramun ne kuke aikatawa
mezaisa bazaku danganaba ku dauki hakan wani babban rabo daga ubangiji ku gode Masa
da kuka kasancema Jini daya qarshen kauna,
Shi Abbi Yana baqin ciki da takaicin rashin zamtowarta jininsa kaikuma data zamo
jininka kuna Neman batawa kowa da komai Dan wannan lalata komai zaku qarasa yi.
Kashe wayar tayi ta dungurar Mata gefe tareda kallonta cikin fara Dan siqewa da
yawan kukanta akan soyayyar Dr Abdul tace"
Inayah can you stop all this stupidity,
Yanzu ke kunya bakyaji ki zabi wani kinata kuka akan wani duk kin kasa tsayawama ki
duba babban abinda ya rataya akanki.
Tsoki tayi tareda juyawa tabar gurin ta fada toilet Dan yin wanka sbd ita duk sun
fara Bata haushi.
Rayuwa saukine da ita,
Ansan ba abune Mai saukin karbaba wannan yanayin dayazo Amma Kuma ba abinda zaka
daga hankalinka bane sbd abbin dai dayafi Mata komai da kowa yasake zamowa nata
dukkaninsa ba maganar kukan rabuwa dashi Amma haukan soyayyar wani na Neman rufe
Mata Ido waninma 'dan uwanta da aka tabbatar Mata da Babu aure tsakaninsu.
Inayah dake hawaye komawa tayi ta kwanta kawai batareda ta iya magana ba sbd bazata
iya cire soyayyar Dr Abdul arantaba lokaci dayaba,
Tafi tausayinta sosai akan kanta na wannan yanayin dasuka samu kansu sbd sanin
yanda yagama zurfafa da haukacewa a Sonta.
Aurenta Kuma da Abbi Bata Gama yarda dashi bane sbd tasan abbin ma bazai taba
karban aurenba sbd Babu yanda zaayi suyi rayuwa ko zaman aure Dan tamkar haramunce
garesu.
Ita maganar uwarta da akeyi Kuma batajin Zata taba iya daukanta a wani matsayin
Bayan na mahaifiyar Abdulsamad kawai
Sbd aduk matsayinda Abbi zai dauketa hakan itama Zata dauketa Mai kyau ko sabaninsa
sbd har abada Abbinta shine komai nata Kuma maganarsa zataci gaba Dabi har qarshen
rayuwarta.
Koda Neesah tafito har lokacin Inayah din takasa daina hawaye sbd yanzu kukan
rashin sanin kanta takeyi.
Shin marainiyace ita kokuwa 'yar gaba da fatihan dagaskeΒΏ
Yarasa tayaya uwarta Zata jefar da ita kokuma guduwa tabarta kokuma kaita gidan
marayu tun jarinta,
Tayaya ta fada hannun Abbinta,
Wace irin tsana uwarta Tai Mata da Zata jefar da ita tana jaririya
ta dauki Abdul daya girmeta Amma ita ta jefar da ita.
Ganin kukan datakeyi yayi yawa Kuma akwai tsananin damuwar abin da quncinsa a
bayyane da Inayahn yasa Neesah tahowa ta zauna gefen Inayah din tareda Dan
rungumota batareda tace komaiba Dan kada ta katse Mata damuwar datakeson ragewa ta
hanyar kukan da tunanin.
Sun jima a hakan kafin Inayah ta janye jikinta tareda zamewa ta kwanta kan gadon
tana rufe idanuwanta.
Shiryawa Neesah tayi itama cikin kayan bacci masu gajeran wando tazo ta kwanta
gefen Inayah sbd tana period bare tayi sallar ishai.
Tanajin yanda jikin Inayah yayi zafi sosai alaman yauma da zazzabin atareda ita Dan
haka ta miqe tadauko Mata magani tabata Tasha suka kwanta tanajin jikinta duk
yakuma sanyi.
Washe gari ma Bata fito breakfast shima Abbin Bai fitoba su kadai sukayi daga umma
yaganah sai Neesah.
Bayan sun Gama umma yaganah da kanta takai breakfast din abbin palonsa ta jiye ta
fito.
Neesah Kuma tayi Shirin na Inayah takai Mata daki itama.
Zazzabinta ya tsananta Dan haka hankalinsu ya tashi Amma dai duk da hakan umma Bata
sanarwa Abbin ba sbd kada damuwar suyi yawa Dan haka suka samu suka Dan lallabata
Neesah Tai Mata allura bayan awa biyu jikin nata ya Dan saki tasamu qwarinsa tasamu
tayi wanka tayi sallar azahar.
Tana idarwa ta zare kayan sallar ta miqe ahankali ta zura slippers ta fito dakin
sbd tasan Abbinta baisan batada lafiyaba tunda Bai nemetaba Dan haka Kai tsaye tana
fitowa Bata nufi koinaba sai hanyar palonsa jikinta ba qwari tafiyarma ahankali
takeyi.
Tsit taji gidan duk da dama basuda wani manyan motsi a gidan Amma tsit taji da
alama kaman umma yaganah basa gidan.
A dining yake zaune yana Shan ruwan yakasa cin abincin dake jere gabansa
idanuwansa sun sauya sosai sbd yau wani irin daci ne da quncin zuciya tareda
damuwar shekaru suke tasowa suna komawa sababbi fal Kaman yanda komai yafaru
alokacin bayan...,
Baitaba sanin zai Kuma fuskantar maimaicin abinda yafaru dashiba alokacinda yake
cikin radadi da zafin maraicinsa abayaba.
Rintse idanuwansa yayi cikeda daci Mai tsanani dayake sake cika maqoshinsa...
Qamshin Turaren Inayah duk da Bata wani sakaba da yawaba yasashi bude idanuwansa
dasukai jajir Yana kokarin basarda yanayinsa sbd kada tagani ta daga hankali da
tambayarsa abinda yake damunsa.
Jin takunta ya nufi wani direction din yasashi waiwayowa ahankali ya kalli hanyar.
Riga da wandone ajikinta na masu Fadi sosai Amma basuda nauyi ko kadan sai suke
saka kirjinta da bra rawa qaramar hular kayan ce kawai akanta Bata Gama rufe baqin
gashintaba da akaiwa gyaran aure Amma auren baiyiyuba.
Dauke kansa yayi daga kallon gurin tareda miqewa ya nufito ganin hanyar palon
dazatakl kaita gurinsa ta nufa Kuma yasan su Alhaji babbah da dangin Hadiza da
Hadizan suna ciki sbd maganganun da zaayi...
Shigarta hakan gurin zai iya bayyanarda raunin tarbiyarta ga Hadiza da danginta
dake gurin harma da Dr Abdul Wanda zai Mata kallon da zai iya Zama laifi ga
ubangiji.
Qaramin palon daya rabasu da palon Abbin ta Isa Zata shige taji anriqo hannunta ta
baya.
Batada qarfin razana Amma duk da hakan a tsorace ta waiwayo sbd riqon bana mace
bane hakama tasan basuda namiji a gidan dazai shigo har nan bayan Abbinta.
Tana juyowa acikin idon Abbin idonta yafara fadawa akaron farko dataji tsoro da
fargaban kallon idon Abbin...
Da sauri ta maida kallonta kansa tana bayyanarda tsoronta da damuwarta tace"
Abbi..
Kasa magana tayi sbd idanuwanta dake kokarin cikowa da hawayen da batamasan na
menene ba ita dai tasan Abbinta shagwabarta akansa ta qare Dan haka yanzuma tasan
bazata iya dainawa sbd kallonsa kawai nasa taji duniyarta alhmdllh sbd samun
tsayayyen uba kamansa sai Mai saa irinta.
Matsowa tayi tana sake riqe hannunsa cikin hawaye tace"
Abbi Dan Allah kayi hakuri idan fushi kakeyi sbd na nace Akan zuwa asibiti dubo
heart...
Tun jiya Banda lafiya sosai abbi baka..
Saketa yayi tareda zare hannunta daga riqon datai Masa
Tabisa da kallo tana jin sabon kuka na zuwar Mata sbd ganin kaman fushi yake da ita
sbd ta saba riqe hannun mahaifinta ko bayan ta girma Bata daina riqe hannunsa Amma
yau din ya zare batareda ya kalletaba.
Juyawa yayi Yana komawa palon ya zauna Yana cewa"
Akwai baqi aciki koma ciki anjima zansa Dr farhat tazo ta dubaki.
Kuka ya fashi dashi tareda zuwa gabansa ta durqusa tana hawaye masu gudu tace"
Abbi Dan Allah kayi hkr idan nayi laifi,
Kamun hukuncin laifin ma
Amma Dan Allah kada kabari a rabani da Heart Abbi.....
#MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biyaπ
07040727902
MTN cardπ
09134848107
[10/25, 8:35 PM] MG: *_36_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ahankali ya waiwayo ya kalleta
Ganin irin kukan datakeyi yasashi Dan sauke ajiyar zuciya Yana nazarin halinda
tashiga duk tabi ta sauya sbd kuka da damuwa da tashin hankali lokaci kankani.
Dr Abdulsamad ne ya sulale daga palon batareda sanin kowaba ya shigo ciki Yana Jin
idan ba ganin Inayahn yayiba bazai fahimci dukkanin abinda akeson fadaba a zaman.
Umma yaganah data lura da fitarsa ta miqe ta biyo bayansa sbd fargabar abinda
shedan zai iya sawa su aikata shida Inayahn idan sun hadu,
Itakuma yanzu Kam tunda aka daura auren INAYAH da MAJEED batajin tanada abinda
yakai Mata wannan auren mahimmanci sbd dai basuda yanda zasuyi aure an daura Dan
haka kowa hakuri zaiyi a runguma wannan qaddarar gabaki daya.
Shigowar Dr Abdul yasa Inayah dakatawa daga rokon datakeyiwa Abbi ta zubawa Dr
Abdul din idanuwanta tanajin kaunarsa na sake karyar Mata da zuciya..
Meyesa ummansa Bata tashi bayyanaba sai alokacinda zasu mallaki junansu.
Dr Abdul ma kasa riqe hawayensa yayi dukda zamtowarsa namiji agabanta.
Qarasowa yayi ya durqusa gaban Abbin shima tareda sunkuyar da Kai Yana tsiyayar
hawaye cikin yanayi na damuwa Mai tsanani da quncin dake cinsa cikin zuciya yace"
Sir Dan Allah kada ka rabani da Inayah idan ta haramta aguna matsayin Mata Dan
Allah kabani ita matsayin 'yar uwa tunda hakan Bai haramtaba.
Kukan tausayin Dr Abdul din yakuma zuwarwa Inayah ta kalli abbin dayaqi ko kallonsu
yayi shiru cikin nasa nazarin.
Idanuwansu sun rufe suna roqonsa
Inayah roqonsa takeyi akan ya warware auren da aka daura sbd har abada bazata iya
karban Abbinta amatsayin mijiba.
Irin kukan datakeyi shine yake Sosa ransa ba girman kalaman datake fadaba,
Har cikin ranta take bayyanarda quncinta na auren,
Bazata iya karban wannan aurenba,
Ta zabi yaci gaba da Zama ubanta har qarshen rayuwarta...
Umma yaganah dataga irin kuka da Inayah keyi ya daga hankalinta sosai Musamman
ganin shima MAJEED din yanda idanuwansa suka sauya sosai batareda ya juyo ya kalli
su Inayahn ba.
Miqewa yayi tsaye ahankali ganin tana neman shaqewa sbd kuka numfashinta Yana
hardewa alamar wani attack dinne Zata Kuma samu...
Idanuwansa ya juyo ya zuba Mata Yana kallon yanda numfashinta ke kokarin rabuwa da
kirjinta duk akan aurensa daya rataya akanta,
Meyesa tun farko ya aminta da auren sbd tunanin shine mafitar da Zata Hana kowa
karban Inayah daga hannunsa...
A zuciyarsa kusan yafi kowa Jin kunci da shiga matsananci hali akan wannan yanayin
dahar yakai ga wannan auren Wanda shima yasan yin auren kawai akai bazai taba
kallon 'yarsa amatsayin maceba bare matar da....kasa qarasa tunanin yayi sbd nauyin
da dacin kalaman.
Da gudu umma taqaraso tana kokarin kamo Inayah
Inayahn ta miqe da sauri tana sake rarrafawa gaban Abbi tana roqonsa numfashinta
ko fita daidai bayayi.
Cikin tashin hankali umma yaganah ta sake tarota tana miqar da ita tsaye tace"
INAYAH kinada hankali kuwa?
Kinsan me kike fada?
Wane auren kikeda qwarin gwuwar cewa araba?
Cikin kuka tace"
Umma yaganah wlh bazan iyaba,
Bazan iyaba,
Rayuwar auren da akeson ayi tsakanin ma'aurata bazan iya yinta da Abbi ba wlh,
Rayuwar auren dazanyi bazan taba yinta da Abbi ba,
Umma bazan iya kwanciya gado......
Suka umma yaganah takaiwa bakin tanajin baqin ciki da takaici harma da tashin
hankali sbd yanayin MAJEED duk kannewarsa Yana bayyanarda bacin Rai da griman
tasirin da maganganunta keyi a ransa.
Ajiyar zuciya Mai sanyi abbin ya sake Yana kallon yanda numfashinta ke kokawa da
Isa yasake sauke numfashi Yana Dan dauke idonsa daga kallon kirjinta dake harbawa
sosai sbd halinda take ciki.
Fuskarta ya kalla ahankali cikeda kulawa ya kalleta tareda riqo hannunta daga jikin
Umma yaganah ya zaunar kan kujera tareda kallonta Yana nazarin kalamanta dasuke
bayyanarda haqiqanin Gaskiar abinda yake ranta.
Cikin nutsuwa da sautin muryarsa Mai nutsuwa da kamewa yace"
Inayah!!!!!
Kasa dagowa tayi ta kallesa sai hawayenta dake gara gangarowa daga Idanuwanta
dasukai mummunan kumbura.
Kukan dakikeyi Zaki jawa kanki ciwo akan wannan unnecessary Al'amarin,
Auren ne yasaki wannan halin right?
Gyada Kai tayi wasu zafafan hawaye na Kuma ganganro Mata.
Kai tsaye Bai tsaya komaiba yace"
namiki alqawarin sauke Miki wannan auren daga lokacinda kika yarda da qaddara kika
San aure tsakaninki da Abdul ya haramta,
Zan sauke Miki auren ki koma hannun mahaifiyarki da Abdulsamad kimun alqawarin
bazaki Bari shedan ya Shiga zuciyarkiba kiyi watsi da tarbiyar Dana Baki.
Dago jajayen idanuwanta tayi da basa iya budewa sosai ta kallesa Jin Zata bar
hannunsa Wanda ita Batasan wannan yarenba kwata kwata bazata taba barinsa Koda Zata
rasa kowa a duniya.
Juyawa yayi ya kalli umma yaganah zaiyi magana
umma yaganah tayi saurin zubewa qasa tana neman fashe Masa da kuka tace"
Dan girman Allah MAJEED kada ka furta kalma daya data danganci rabuwar wannan
auren.....
Rintse idanuwansa yayi Yana sake hadiye yanayin dayake ciki ya kalli Inayah dake
kallonsa Ido na tsiyayar hawaye tana jiran kalamansa da zasu warware auren su koma
matsayinsu na uba da 'ya.
Tunda umma yaganah take Bata dukan Inayah ba bare ma agaban Abbi sai yau dataji
kaman tayiwa Inayah din duka tashi Kisha ruwan gishiri Dan haka Batasan lokacinda
ta ringa dukan Inayahn da mayafin Jikintaba tareda damqar hannunta tayi ciki da ita
bayan ta kalli cikin tsakiyar idanuwan Dr Abdul dake zubarda hawaye shime ta buga
Masa wani irin mummunan gargadin dayasa shi kallon Abbi Wanda yakasa cewa komai sbd
kansa daya toshe Yana sake daukan zafi.
Wucewa yayi yabar Dr Abdul din a tsaye gurin Yana bin hanyoyin dasuka bi da idanuwa
cikin tashin hankali sbd Koda yasan bazai taba auren Dan Inayah ba zaifi samun
nutsuwa da sauki idan yasan ba auren kowa kanta.
Umma na shiga daki da Inayah tayi wurgi da ita tsakiyar dakin tareda kallonta cikin
tsananin takaici da bacin Rai tarasa wane irin duka zataiwa bakin Inayahn,
Cikin kuka Inayah ta cusa kanta cikin tsakiyar qafafunta tana jin hankalinta Kuma
na tashi da kalman Abbi na miqata ga matarda ake Kira da mahaifiyarta wadda
haryanzu basu sake haduwaba tun ranarda tazo gidan komai ya lalace.
Daqyar umma yaganah ta samu danne zuciyarta Takoma palon Wanda dama MAJEED ake
jiran yazo afara maganar da zaayi.
Koda Isa palon zaman taron yaqara yamutsewa sbd Dr Abdul da jikinsa ya rikice Dole
suka bar gidan.
Umma Hadiza kaman zata Dora hannu akai tayita rusa ihu takeji sbd wannan masifar
dake Neman dawo Mata,
'danta daya Wanda take ganin ta Kama qwaqwalwarsa na Neman juyewa sbd son 'yar
uwarsa
Gashi tana neman rasashi batareda wannan datake ganin tasamoba Bayan shekaru tazo
hannuntaba.
Bataso tafiyaba saita hadu da Inayah Amma MAJEED ya hanata ganin 'yarta sbd yaqara
nuna Mata ikonsa akanta.
Bayan barinsu gidan umma yaganah qin zuwa Inda Inayah take tayi sbd wannan karon
tayi mummunan Kona Mata Rai.
Matuqar auren MAJEED yabar kanta Bata tunanin Inayah Zata samu mijinda zai kaisa
agurin kulawa da ita Dan haka zatai iya kokarinta gurin ganin wannan auren baitaba
rabuwaba Koda hakan na nufin da qarfin hali ta cusa Inayah gun MAJEED ya dirka Mata
ciki taga yanda auren zai rabu kowama ya huta har Hadizan da 'dan su huta dasu akan
raba auren.
Ranar gidan ko abincin dare Babu Wanda ya fito ci sai Neesah kawai data fito itama
snacks kawai taci takoma daki ta kwanta.
Acikin daren Abbi yayi booking ticket na zuwa Abuja akwai Wanda zai gani daga can
zai wucewarsa Dan Yana buqatan kansa ya sake.
Washe gari qarfe 8 na safe yayiwa umma yaganah txt driver ya wuce dashi airport
jirginsu ya tashi qarfe Tara.
Koda INAYAH ta tashi da safe jiki a mace tasan Bata kyautaba Musamman da umma
yaganah ta matse fuska sosai Bata wani sake Mata ba
Duk saitaji tasake Shiga damuwa dan haka ko wanka bataiba da Riga da wandon bacci
masu tsantsi ta wuce palon Abbinta Dan basa hakuri sbd Bata iya juran fushinsa
akanta ko kadan,
Kuma ta wani bangaren gaskiyarta ce tafada bazata iya rayuwar aure da Abbinba sbd
asalin life takeso arayuwar aurenta wanda Zata iya nuna soyayyar mijinta agaban
kowa Kuma shima zai iya nunawa agaban kowa Dan haka Babu ta Inda Zata iya wannan
rayuwar da Abbi Wanda takewa kallon ubanta Kuma uwarta.
Shine ya koyar da ita yakuma Bata tarbiyar fadar Gaskia komai dacin dazata kawo
shiyasa koyaushe ake ganin wautarta Dan ita tasaba gaskiyarta take fada daga zuciya
ba boye boye ko munafurci.
Kayan jikinta umma yaganah ta kalla lokacinda ta gaisheta tareda juyawa Zata nufa
sashen Abbin.
Floral pyjamas ne na bacci ajikinta masu santsi farare,
Babu bra ajikinta Dan haka kirjinta dasuke tsaye qyam suna bayyanarda basa cikin
bra din.
Ko hips dinta sosai suka fito a wandon kayan sbd santsin kayan yasa suka Dan lafe a
jikinta.
Da adah ne umma yaganah hanata zuwa takeyi gaban Abbinta da kayan bacci sbd kusan
rayuwar Inayah din babu ruwanta kusan koyaya tana iya zuwa gaban mahaifinta da
towel ne kawai Bata iya zuwa gabansa sai guntayen Kaya Amma Dan kayan bacci dasu
leggings duk ba komai bane agunta.
Umman na sane Sarai ta qyaleta ta Kama hanyar palon nasa batareda tace Mata taje ta
sauyaba kokuma sanya wani Abu akai.
Ja'irar yarinya Allah ya nunan ranarda wannan bakin naki zai mutu yayi hankali.
Shima MAJEED din da haryanzu yake biye Miki yaqi bude Baki ya magantu dakyau ki
dawo hankalinki.
Inayah nakaiwa kofa massage din MAJEED nashigowa wayar umma na cewan yayi tafiya.
Sanyi jikinta yayi tanajin tausayin MAJEED din sbd abubuwan sun Masa yawa gashi
wannan Yar banzar na Neman qara zafafa Masa kai da haukarta.
Cikin gatse tace"
Hajiya saiki dawo MAJEED din yayi tafiya yace
Saiki dawo kici gaba da kuka tunda Baki aura Dan rayuwar dakike burin samun aureba.
Maganar umma na cewan abbin yayi tafiya yasa hankalinta sake tashi saidai Bata
nunaba sbd umman karta cigaba da Mata wannan fadan na baqar magana Dan haka ta juya
jiki mace Takoma dakinta.
Tana shiga daki ta zauna tareda daukan wayarta Kai tsaye tasaka kiransa tana sake
Shiga damuwa Mai tsanani,
Abbinta akaron farko dasuka kwana suka wuni basuyi wayaba basuyi maganar arzikiba,
Yanzu Kuma yayi tafiya batama saniba hakama umma yaganah kawai ya fadawa.
Hawaye taji idanuwanta na cikowa dasu indai kuwa akan Abdulsamad Abbinta zaiyi irin
wannan fushin da ita Zata hakura dashi...
Tama hakura dashi
Zata bawa Abbi hakuri bazata sake ko maganar Abdul dinba barema ummansa.
Kiran wayarsa tahau yi Amma takasa samu Dan haka taji kaman wani zazzabin na neman
kamata Dan haka ta silala tayo wanka ta shirya cikin doguwar Riga breakfast dinma
Dan Dole ta fito taci tana qarfafawa kanta sbd Abbi yadawo anjima ya taddata ta
sake zaifi saurin yafe Mata sbd fushin Abbi shine abinda Bata taba dauka da wasaba.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biyaπ
07040727902
MTN cardπ
09134848107
[10/25, 9:56 PM] MG: *_37_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Sukuku ta wuni ranar zuciyarta ba Dadi hakama umma har lokacin ta fuske Mata ga
Neesah nata shirye shiryen tafiyarta ga abbin sai Kira takeyi takasa samunsa duk
saitaji kaman tayita rusa kuka
Gashi umma na fushi ko tayi kukan tasan ba rarrashinta umman zataiba.
Har qarfe biyar na yamma tana jiran dawowar abbin sbd Bata tunanin tafiyarsa Mai
nisace kokuma kwana bare barin qasa dazai tafi Bata saniba tana matsayin 'yarsa
daya tal......
Shiru tayi daga wannan tunanin sbd tunowa da auren da har lokacin Batajin ta sauko
ta karba auren,
Ta hakura da Dr Abdul sbd kaucewa fushin abbin Amma ita maganar aurenta dashi
batajin Zata taba karban wannan.
Ganin zaman Yana neman Cinna Mata hauka yasa ta fito Palo tana kokarin nufar hanyar
dakin umma yaganah saiga qarar akwai baqi a kofa.
Duk da tasan ba Abbi bane Amma sbd tana buqatan ganinsa yasa taje da sauri ta bude
tana adduar Allah yasa shi dinne.
Anty Hafsat tagani da CM da sauri ta rungume anty Hafsat tana Jin hawaye na ciko
idonta kawai sbd Daman tana neman Wanda Zata fadawa kukanta.
Cikin kulawa Anty Hafsat ta dago bayan ta zare jikinta tace"
Muna tareda baqi Inayah behave yourself idan mun nutsu mayi magana.
Fuskarta still da sauran hawaye ta juyo ta kalli baqin.
CM tafara kallo cikin nutsuwa tace"
Daddy Ina wuni?
Murmushi yayi cikin kulawa shima yace"
Lfy kalau Inayah,
Yaya umma yaganah?
Ki gaidata idan Kun shiga bazan tsayaba sauri nake saidai idan nadawo.
Anty Hafsat ya kalla yace"
zanje na dauko Alhaji babbah sbd suma su Haj Hadizan suna hanyar qarasowa nan din
kafin su iso akai su hajiya suyi sallah su huta sun biyo hanya.
Juyawa yayi ya kalli farar dattijuwar