Showing 45001 words to 48000 words out of 124042 words
tantama dama tasan yau komai dare saiya fito nemanta sbd dukkanin Susan
amsar tambaya daddaya dake zukatansu kafin daurin auren gobe Dan kuwa amsoshin
tambayar dake ran kowannensu itace future din yayansu da zaa daurawa aure gobe Dan
haka a wahalce ta saci jiki ta fito bayan tasa Abdul yabar musu motarsa incase idan
ciwonta zai tashi da dare su wuce asibiti ya samesu acan.
Batada lafiya sbd jininta yakai kololuwar hawa ko tsayuwa Bata iyawa sosai Amma
bazata iya kwana ayauba batareda tayi magana da mahaifin Inayah ba,
Zuciyarta bugawa zatai da sake sake da fargaba harma da tashin hankali matuqar yau
batai magana dashiba taji abinda takeson ji.
Da wani irin speed ya fizgi motarsa yabi ta gefen motarta ya wuce Yana Jin tsohon
tabon baqin cikin daya dade Yana dannewa yana taso Masa.
Ribas tayi ta rufa Masa da gudu itama duk da qarfin haline kawai takeyi Dan sosai
takejin kaman zuciyarta Zata fashe,
Tsohon famin baqin ciki da quncin da tarin Dana sanin gaske datake dannewa shekaru
masu yawa ne suke birkito Mata tako Ina tanajin zuciyarta na azabar zafi da qunci.
Baisan tasan Lagos ba sosai Dan haka ya ringa ratsa manyan anguwannin dazai bacewa
ganinta saidai sosai ta nace tana binsa idanuwanta ma tuni suka fara tsiyayar
hawaye Dan kuwa hakan ya tabbatar Mata da tunaninta Gaskia ne akansa shine Wanda ta
gudu tabarwa Jaririyarta AYSHATOUH.
A daidai gaban ma'aikatarsa ya faka motarsa tareda qin fitowa zuciyarsa na qara
daukan wani irin zafi da bacin Rai da baqin ciki Mai zafin gaske.
Baya kaunar ganin fuskarta sbd ganin fuskarta na tunatar dashi kowace daqiqa na
lokacinda ya rabu da gatansa da iyayensa harma da farin cikinsa akanta.
Jajir idanuwansa suka kada sosai sbd tsananin zafi da zuciyarsa ke dauka.
Bude motar tayi ya fito ya wuce zuwa ciki tabi bayansa da sauri itama hawayenta na
tsananta gudu kaman yanda bugun zuciyarta da tashin hankalinta ke tsananta.
Cak suka tsaya a tsakiyar office dinsa koina tsit ba kowa sai securities din
ma'aikatarsa.
Zubewa tayi agabansa tareda fashewa kawai da kuka Mai tsanani da taba zuciya sbd
Batasan me Zata fara fadaba ko tambaya.
Kukanta sake zafafa ransa yakeyi Musamman wannan sautin kukan shine ta ringa Yi
Masa a wancan lokacin batareda da duba girmewar datai masaba ta lalata rayuwar 'dan
matashin dake tsakiyar karatunsa cikin kwanciyar hankali da kulawar iyaye.
Wani mummunan 'daci da qunci Mai nauyi ya hadiye ta wuyansa tareda juyowa ya
kalleta da idanuwansa dasukai jajir Kai tsaye Yana danne fushinsa da nutsuwa yace"
Bansankiba ko wancan lokacin hakama bansakinba a yanzu,
Banda alaqa kowace iri dake bayan wadda zamu qulla a goben ta auren 'yayanmu Kuma
itama zan bar 'danki ne kawai ya auri 'yata sbd farin cikinta dakuma kaucewa abinda
zai sameta idan akai fashin auren Dan haka ki amsa mun tambaya daya rak itama sbd
kaucewa Mummunan Al'amari.
Kuka takeyi sosai sbd tasan Babu abinda daga ita harshi sukewa tsoro kaman alaqar
'yayansu
Saidai kafin komai yabiyo baya na abinda ya faru a baya shine susan makomar alaqar
dake Shirin qulluwa goben wadda tuna abinda zai biyo batama tashin hankali ne da
wata babbar masifar.
Cikeda baqin ciki yakuma kallonta Jin batada niyar amsawa sai kukan datake Yi kaman
zata shide.,
Zafi da quna ransa ke qarawa Dan haka ya juya yanajin kansa na sake yamutsewa da
babban tashin hankalin da Inayah Zata iya Shiga akan wannan matar...
Yanada zafin zuciyan gaske Mai tsanani Amma tunda rayuwarsa ta sauya ya iya boyewa
da dannewa Babu Mai gane yanayinsa duk kafiyarka Amma yau zafin zuciyan tasa ya
gagara dannuwa a zafafe ya buga glass table din dake gefensa take ya tarwatse da
qara Mai tsanani
Saida Hadizan ta firgita tana dagowa da jajayen idanuwanta dasuka rine take sbd
tashin hankali Mai tsanani da kuka.
Miqewa tsaye tayi hawayenta har lokakacin basu tsayaba Dan ba tsayawar zasuyiba
muryarta na rawa tace"
Ina AYSHATOUH???
Wani matsiyacin kallon baqin ciki da takaici yayi Mata yanajin duk duniya Babu
Wanda yakai Hadiza sonkai
Ya dauke Kai Yana kokarin danne kansa daga zafin fushin dake taso Masa Kai tsaye
yace"
Idan kece kika haifi Abdulsamad menene alaqarki da 'yar da kika Yar????
Gangaro Mata hawayen daci da danasani sukai muryarta a dashe tace"
'yatace nice na haifeta da ita da Abdulsamad duk nice na haifesu Kuma mahaifinsu
daya idan Inayah itace AYSHATOUH to uwarsu daya ubansu daya da
Abdulsamad.......""da kuka ta qarasa zancen Dan kuwa babbar masifa ta diro ta
sameta a zazzafan tabon ciwon qunci..
Idan Abdul Mai samu Inayah ba haukacewa zaiyi"" innalillahi wainnan ilaihrrjiun
Na shiga uku Ni Hadiza rayuwata tasake shiga wata babbar jarabawar Mai nauyi...
Mutuwar tsayece ta samu AA MAJEED Dan kuwa yayi fargabar Jin hakan Amma Bai yarda
da zaiji tabbatar hakan daga bakintaba.
Qarasa rikidewa idanuwansa sukai jajir yanajin wani gumin zafi da babban tashin
hankali na shigarsa.
Abinda yakeson tabbatarwa kenan daga bakinta dan shakku da fargaban daya shigesa na
iya yiyiwar hakan Kuma ta tabbatar Masa Dan haka baida sauran buqata da ganinta
kona second daya Dan a Karo na biyu ta sake wargaza rayuwar 'yarsa.
Juyawa yayi Yanayinsa na ninkuwa ada sauti Mai 'dacin gaske yace"
Zaki iya komawa ki sanar da danki dagani har 'yata yanzu bamuda alaqa daku Auren
anfasa.
Juyawa yayi zai fice Dan hankalinsa gabaki daya yagama yamutsewa qarshe kaman kansa
zai buga
Inayah yakejin tashin hankalin yanda Zata karba kaddarar rashin auren Abdulsamad
sbd bazai taba fada Mata dalilinba Dan kuwa bazai taba barin Hadiza ta kusantar
Masa 'ya ba.
Da saurin Hadiza Tasha gabansa tana rokonsa cikeda tarin nadama tace"
Dan Allah kafadamun idan Inayah ce Ayshatouh na,
Har abada nasan bazan taba samun yafita a zuciyarkaba Amma Dan Allah kada ka hanani
Ayshatouh Inayah,
Wlh nayi Dana sani nayi nadama.....
Sauraronta tafasashi sukeyi tako Ina Dan shi kansa komai ya kunce Masa a yanzu.
Wucewa yayi Yana daga wayarsa zuciyarsa a quntace ya saka kirana Mr Al-amen Yana
dauka Kai tsaye yace"
Ai Mana booking tickets da komai na tafiya nida familyna gobe kafin 12 zamu bar
qasar....
##MAMUH
##MARRIAGE/LOVE
##AYSHATOUH INAYAH AA MAJEED
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/17, 11:03 AM] MG: *_28_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tashin hankali Hadiza tashiga Jin abinda ya fada a firgice Tasha gabansa tana
rokonsa cikin mummunan hali na kuka tana rokon ya hadata da 'yarta Ayshatouh
Inayah.
Numfashi ya sauke a hankali tareda ajiyar zuciya Mai dumi kafin ya Dan dago ya
kalleta kadan cikin nutsuwa kaman Wanda zuciyarsa ba tsananin quna takeba da 'daci
takeba yace"
Babban taimakon da zakiyiwa kanki da Abdulsamad shine ki cirewa ranki da kanki
tunanin sanin mahaifin Inayah bare ita Inayah din,
Inayah 'yatace Kuma Babu Wanda zaizo Rana tsaka yacemun shine ya haifeta,
Bansankiba Baku nada alaqan komai dake..
Ki nema yarki a Inda kikasan son zuciya yasa kin barta.
Zafi maganganunsa suka farai Mata sbd duk yanda tayi aikin son zuciya abaya Inayah
dai yartace Kuma tayi danasani daga ranar data gudu ta barta.
Wlh bazata yardaba taga yarta sannan ya dauketa su bar qasar tasan bazata Kuma
ganintaba har abada Dan haka cikin rashin tunani da tauna zancen abinda yafada
matan tace"
Har abada saidai ka Kira kanka matsayin mariqinta uban daya raineta Amma bazaka
taba sauyata daga nice wadda na dauka cikintaba na haifeta.
Bai tsaya saurarentaba ya fito Kai tsaye yashiga motarsa Yana cewa security a rufe
Masa koina.
Cikin zafi ga figi motarsa da matsiyacin speed yabar gurin batareda yajira ganin
fitowartaba.
Ikon Allah ne kawai da nutsuwa dayayita kokarin sakawa kansa sbd kada su Inayah su
gano halinda yake ciki yakaisa gida lfy.
Yana parking ya fito ya nufi kofar dazata kaisa palonsa na farko direct batareda
yabi kofar dazata bi dashi ta palon su Inayah ba kafin ya Isa nasa palon.
Yana Shiga palonsa Kai tsaye hanyar bedroom dinsa ya nufa ya shige tareda Zama kan
luxury italian sofa dake dakin ya rintse idanuwansa dasukai jajir.
Ajiyar zuciya yafara jerowa da numfashi Mai zafi yanajin damuwa da tashin hankali
Mai tsananin wannan auren da Allah yasa baa dauraba da tako Ina masifun da tashin
hankalin bullowa zaiyi,
To Amma babban tashin hankalin da damuwar shine ta yanda Inayah Zata karbi fashin
aurenta akaro kusan na hudu.
Tayaya zai iya taro matsalar da Zata iya samunta?
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun.
Miqewa yayi ya nufa toilet ya sakarwa kansa daya dauki tsananin zafi ruwa yanajin
zafin kan na tsananta.
Da ruwan dumi yayi wanka ya fito ya saka blue pyjamas sai sanyayyan Chanel na jiki
ya kashe wayarsa tareda jefarwa gefe ya hau gado zauna Dan yasan yau koda qyaftawar
Ido bazai rintsaba sbd fitina da tashin hankalin dayake jiransu da safe.
Umma Hadiza ma cikin masifaffen tashin hankali da tsoron AA MAJEED yabar qasar da
inayah ta iso gida jikinta Babu Inda baya kakkarwa ta silale tashige dakinta
batareda kowa yasan fitarta da dawowartaba ta rufe daki tareda zubewa qasa tafara
kuka Mara sauti tana cewa"
Ya Allah kagani rashin mafita da madafa da Sharrin shedan ya hanani tawakkali na
gudu nabar 'yata badan bana tsananin sontaba ya Allah nayi shekaru cikin qunci da
damuwa da tawakkali ya Allah kada kabari wannan bawa naka ya tafi da 'yata wata
qasarda bazan Kuma jinsu ko ganinsu.,,ya Allah ka duba maraicina ka hadani da
'yata,
Allah ka kawo Mana sassaucin wannan masifar data kunne Kai da tashin hankalin dazai
biyo goben sanadin fashin auren yaran Nan.
Kuka takeyi sosai tana rokon Allah sassauci da mafita.
****Daga AA MAJEED har umma Hadizan Babu Wanda ya rintsa yanda sukaga Rana haka
sukaga dare da safiya.
A gidan A MAJEED da zallar farin ciki iyalan gidan suka tashi Dan ko su Anty Hafsat
duk a gidan takwana da yaranta gasu Safnah da Neesah dasu Daman tuni suka tare sai
Yan uwan umma yaganah guda biyu dasuka zo bikin Dan tayata Murna dakuma samun abun
arziki.
Dr farhat dasu Mimi ma tunda safe suka iso gidan kaman dasu aka kwana.
Kowa farin cikinsa bayyananne ne sbd duka aurarrakinta da ake fasawa Babu Wanda
yazo ranar Daurin auren sai wannan yau gashi Allah yayi anzo daurin auren a wanni
kadan ne suka rage tazamata cikakkiyar matar Heart dinta Abdulsamad salees halak
malak.
Cikin kayan baccin data kwana dasu Riga sa wando masu santsi tafito da hula akanta
fuskarta da dukkanin fatar jikinta sunyi fresh sai sheqin kyau da gyara sukeyi
gashi yanayin data fito din kaman wata qaramar yarinya.
Kai tsaye dining ta nufa tana cewa"
Yunwa nakeji zubbi kawon tea nafara sha.
Tea da doughnuts masu laushi guda uku zubbi takawo Mata tana cewa"
Mint tea din Sir is ready
Zaa shirya Masa ne a dining kokuwa?
Tana Shan tea dinta tace"
No ki shirya zan Kai Masa palonsa yau da mutane a gidan bazai shigo ciki ba,
Harda dessert din kin kammala hada Masa?
Yes Ma.
Ok kije ki hado zan Kai Masa.
Ok Ma.
Juyawa tayi ta koma kitchen din Dan hadowa takawo Mata.
Wayarta ta daga tana kokarin Nemo numbern Heart sai gashi kiransa yashigo wayarta
da farin ciki bayyane kan fuskar ta dauka da Yar muryarta Mai shagwaba tace"
Good morning Heart.
Wani sanyin farin cikine yakuma cika ransa sbd ranar yau din daqyar yaga garin ya
waye
Cikin wani irin girmammen farin ciki yake Mai nutsuwa,
Allah yau yacika Masa burinsa na mallakar Inayah amatsayin matarsa dazata Zama uwar
yayansa.
Ji yayima farin cikin yasaka jikinsa sanyi Musamman data Kuma kiran sunansa da
HEART.
Muryarsa a sanyaye yace"
Morning baby,
Kin tashi lfy?
Yaya shirye shiryen da hayaniyar su Anty Hafsat?
Murmushi kawai tayi Tana cewa"
Idan anty Hafsat tajika Zata sa a 'daga tafiyan Amarya yau sai wani satin.
Wat? aikuwa Dana tare a gidan Abbi Nima.
Dariya tayi tana cewa"
Zan kaiwa Abbi breakfast zankiraka idan nafito
Kisses.
Murmushi kawai yayi Yana kashe wayar gabaki daya muryarta ta kashe Masa jiki yayi
sanyi sosai,
Jin yayi har zuciyarsa na yin sanyi.
Daukeda tray ta nufi hanyar palon Abbi tana murmushin wayar data Gama da Heart.
Knocking kofar tayi ahankali tareda budewa ta shigo da sallama tana kallon palon da
Babu kowa sai Sanyin AC dake aiki da Qamshin turarensa daya Gama Kama koina na
palon.
Hanyar bedroom dinsa ta kalla tana ajiye tray din kan table.
Tabaro wayarta bare takirasa ta sanar Masa tana Palo Dan haka tana ajiyewa ta juya
ta fice.
Breakfast ta tadda duka kowa nayi wasu a dining wasu a dakin umma yaganah Dan haka
tayi joining Dinsu itama tana cin Doyan da aka soya kadan.
Har qarfe Tara ta buga da mintuna Abbi Bai fitoba sbd baisan ta Yaya zaifara cewa
su Inayah su shiryaba zasu bar qasar ayau datake ganin ranar Daurin aurentane.
Yarasa ta Ina zai fara,
Ta Ina zai tarbo wannan rikitaccen matsatsen yanayin.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun.
Gashi jama'a da dama manyan tunanensu sai kiransa akeyi ana tayasa Murna wainda
bazasu samu damar zuwaba basa qasar dama wainda suna qasar uzuri bazai basu Daman
halartaba.
Kansa Neman bugawa yakeyi,
Duk wannan masifar damuwarsa da tashin hankalinsa na Inayah ne da Zata shiga
mummunan hali daga lokacinda aka Kuma fasa aurenta dakuma wannan mummunan labarin
da har abada baya kaunar tajisa cewan bashine mahaifinta Wanda ya haifetaba,ko
alaqan Jini basuda a taqaicema baisan mahaifinta da mahaifiyarta ba Dan zuciyarsama
badan ya tattabar akansaba cewa uwa na iya yafe danta da bama zai yarda da cewan
Hadiza ce ta Haifa Inayah ba Dan uwa Bata iya Yar da 'danta
To Amma hakan tafaru dashi sbd tasa uwar ta yafesa sbd zarginsa na aikata abinda
Bai aikataba bayajin ma zai taba iya aikatawa.
Tayaya zai Bari Inayah tasan wannan 'datacciyar Gaskiar?
Baya fatan ko kadan ta 'dandana 'daci Mai kaifin gaske da ciwon uwa mahaifiyarka ta
gujeka sbd wani dalilin banza Wanda Koda bakada uba tunda qaddara ta Samar da Kai
baka cancanta hakanba.
****Hadiza Koda safiyar ta waye tagama fita nutsuwa da hayyacinta,
Bata ji Bata gani matuqar ba 'yarta Ayshatouh AA MAJEED yadawo Mata da itaba,
Tayi gangancin rabuwa da yarta shekarun baya Amma yanzu ko zaisa a daureta asibitin
mahaukata sbd arzikinsa wlh bazata yardaba saiya Bata yarta tadawo hannunta ciki
kuwa harda Koda Zata qaryata kanta agurinsa da cewa ba itace ta Haifa Abdulsamad ba
idan yaso a daura auren su tafi da Inayah Adamawa suna zuwa can ta fada Gaskia a
Raba auren 'yarta dai tadawo hannunta.
Wannan rubabben tunanin shedan ya qissima Mata ta tashi hankali tashe Musamman
ganin lokaci na tafiya tasan rasai AA MAJEED din zai bar qasar da inayah kafin
lokacin daurin aure Dan haka a rikice ta iya watsa ruwa ta kimtsa kanta sbd kada
Wanda yagano halinda take ciki na firgici da tashin hankali.
Da mamaki su Haj balaraba suke kallonta lokacinda ta fito dakinta a shirye tsaf
harda gilashin fuska sbd kada a gano tsananin kumburin da idanuwanta sukai
Gashi iyaye maza yanne da qannen mahaifinsu Abdulsamad din sun iso yanzu da safen
daga Adamawa suna hanyar isowa gidan kafin lokacin daurin auren yaqarasa Amma ta
fito tana cewa zataje karbo saqo tadawo.
Kafin Haj balaraba data saki bakin kallonta tayi mgn umma Hadizan ta wuce
hannuwanta na rawa sosai keys din motar ma daqyar ta iya damqesu suka tsaya a
hannunta ta Isa motar ta bude ta shige da gudu tabar gidan tana kallon agogo.
A daidai wannan lokacin Abbi yagama yanke shawarar tura Inayah da umma yaganah su
fara wucewa qarfe goma Sha daya jirginsu zai tashi shikuma zai tsaya ya bawa
mutanensa dasuka zozzo hakurin fashin auren batareda Inayah tasan fashin auren
akaiba idan yaso Bayan kwana biyu zai samesu acan yasan yanda zai rarrasheta ya
fahimtar da ita fashin auren ta wata hanyar.
Dan hakan Kai tsaye yakira umma yaganah a waya ya sanar da ita ta shirya itada
Inayah akwai Inda zasu qarfe Sha daya kafin lokacin daurin aure.
Yana fadan hakan ya kashe wayarsa sbd kada tayi Masa tambayar komai.
Agogo ya kalla yaga qarfe goma da kusan rabi Dan haka ya miqe ya nufi toilet yayo
wanka cikin nutsuwa.
Daure da Brown towel mai kauri a qugunsa ya fito farar fatarsa sai tsiyayar ruwan
wanka takeyi so freaking fresh.
Gaban mirror ya nufa ya tsaya ahankali Dan baya Zama gaban mirror kaman mace saidai
ya tsaya a tsaye yayi komai.
Lumin body moisture ya shafa tareda fesa spray din Paco Rabanne
Yayi brushing sumar kansa tareda sauran Shirin daya saba yagama ya wuce closet din
tarin kayansa.
##MAMUH#
##MARRIAGE/INAYAH.
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/18, 8:13 AM] MG: *_29_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Qarfe goma da minti arbain su Umma yaganah da Inayah suka fito tana shirye cikin
Tsadadden red Australian lace mara nauyi dinkin fitted gown daya zauna jikinta da
kyau
Shafaffen cikinta zuwa hips dinta dake Dan baje sun fito da kyau cikin kayan ta
yafo 3D veil dinta kayan touches na lace din.
Zallan qamshi Mai sanyi da nutsuwa take fitarwa
Kyakkyawar fuskarta sai sheqin farin cikin dake ranta take fitarwa.
Suna fitowa harabar gidan Abbi ma na fitowa Sanye cikin wata fitinanniyar farar
shadda Mai tsadar gaske da laushi.
Basu taba ganinsa da babbar rigaba sai yau shima sbd Inayah data nace abbin saiya
saka Kaya masu babban Riga a aurenta sbd kada mutane da dangin mijinta su ringa
cewa babanta Bai manyantaba sosai.
Qamshinsa ne ya gauraya iskar gurin suka zuba Masa Ido dukkaninsu Musamman Inayah
dake washe bakin farin ciki tana cewa Abbinta na Musamman ne aduk Inda yaje.
Neesah kuwa dasu Safnah take kowaccensu taji da Abbi matsayin yayan Inayah ne ba
mahaifiba Babu abinda zai hanasu aurensa.
Umma yaganah ma cikin kulawa da farin cikin ganinsa cikin Shiri da adon auren
Inayah a hankali tace"
Masha Allah laquwata.
Allah yaqaro girma da 'daukaka
Yabaka tsari da kariya
Yayi maka albarka tareda kawo dawamammen farin ciki rayuwarka data zuriarka.
Amin"
Su Safnah dasuka jita suka amsa suna dauke idonsu daga kallonsa sbd grima da
kwarjininsa.
Ahankali ya kalli fuskar Inayah ganin farin cikin dake tattareda kowane irin
yanayinta,
Ta Bangare daya baisan tayaya zai Samar dasuba qasar zasu Bari yau.
A natse fuskarta daukeda murmushi tace"
Abbi you look handsome,
and...
Katseta yayi a nutse da cewa"
Inayah kuje karkuyi latti Inda zaa kaiku.
Kallonsa tayi a natse tana cewa
"Abbi Ina zamuje?
Dan rufe idonsa yayi ya bude tareda kallonta cikin tsananin kulawa yace,
"Idan kunje Zaki gani.
Da murmushi akan fuskarta tace"
Okay.
Umma yaganah ya kalla sukai gaisuwar safe d basuyiba tunda ba haduwa sukaiba.
Su Neesah ma da Safnah cikin girmamawa sosai suka Masa Ina kwana kafin ya kalli
umma yagana a natse cikin Dan takaita magana yace"
Idan kunje komai na hannun Ahmed zai damqa miki komai
Zanzo daga baya.
Tsit suka Dan Yi da mamaki suna kallonsa duk da basu gane komaiba akan Inda zasuje
sai jikin umma yagana yayi sanyi taji zuciyarta na Neman shiga wasi wasi.
Inayah ma jikin nata taji yafara sanyi take ta kalli abbin da rauni Amma batace
komaiba.
Juyawa yayi yana kokarin Isa motarsa aka bude gate motar CM tashigo ko qarasa rufe
gate baayiba motar Dr Abdul ta Sako Kai itama.
Umma Hadiza ce aciki Kuma tanayin parking idonta ya sauka kan Ayshatunta take taji
wasu hawayen da tsananin kaunar yarta suna finciko Mata tako Ina,
Kaunace Mai tsananin gaske wadda uwa kewa 'danta Bayan tacire ran samu ko ganinsa
har abada.
Hawaye takeyi sosai tana kallon Inayah din tanajin tamkar taje ta rungumota tayita
kissing dinta tana fada Mata yanda take kaunarta da qaddarar datashiga akan
cikinta.
Wani zafi da tirnikin bacin Rai da tashin hankali ne ya taso Mata ganin suna
kokarin shiga mota tasan wlh qasar zasu Bari suna fita gidan yau bazata