Showing 84001 words to 87000 words out of 124042 words
sosai.
Ga Inayah duk yanda taso ta kusantoshi bayaso yanzu sbd matsalar da hakan ke basa
Itakuma ganin hakan saita rikice da damuwa sbd bayason tana zuwa gurinsa sosai.
Dr farhat ce tazo daga gidansu ta dubasa sbd ciwon kan ya tsananta Masa.
Rashin bacci ne da damuwa yake damunsa abinda yafadawa Haj umma.
Hakan kuwa yasa Haj umma yanke shawaran aurawa majeed din Dr farhat Kai tsaye sbd
yasamu Mai kulawa dashi,
'danta yana buqatan kulawar mace
Wadda Zata sakasa farin ciki tabasa kwanciyar hankali Kuma bataga hakan atareda
Inayah ba wadda bayan shagwaba datake zuba Masa Babu abinda Zata iya Dan haka
bazata zuba Ido 'danta ya mutu abanzaba ko jikiki Bata samuba.
Anty juwairiyyah takira tanayiwa wannan bayanin akan harta Kira qanin abbansu
MAJEED din zaa saka lokaci a je Neman auren.
Umma yaganah damuwa da nata tashin hankalin tashiga Jin hukuncin Haj umma din Wanda
Kuma Babu Mai iya takesa tunda itace uwar MAJEED Bayan shi Babu Mai iya tsallake
wannan zartarwar.
Hafsat takira a waya tace tazo tana nemanta sbd Dole sufara shawarar yanda Inayah
zataji wannan mugun labarin.
Abinda Bata saniba shine MAJEED din ya amince kokuwa? sbd batai maganar dashiba
Kuma shima baizo yamataba.
Inayah na asibiti anty Hafsat tazo cikeda damuwa sbd umman tafara Mata bayani a
waya shiyasa batazoba Saida ta tabbarda Inayah na asibiti.
Tagumi suka rafka dukkaninsu biyun cikin dakin umma Bayan umma yaganah tagama
yimata bayanin abinda yake faruwa ta Dora da cewa"
Hafsat ki kokarta ki sake nutsar da ita tasan abinda takeyi Dan kuwa kishiya da
qananun shekarun Nan nata da sangantar datake basune zasu fiddataba Duk kuwa da
tsananin son da MAJEED ke Mata idan ya auri wata macen yasamu nutsuwa a gurinta
bazata sake gane komaiba.
Numfashi anty Hafsat ta sauke cikin takaici da damuwar maganar tace"
Umma Inshallah Inayah bazata taba wulaqanta a hannun AA ba saidai Zan dage na sake
lurar da ita abinda yake gabanta..Amma dai yanzu inaga kada abari tasan Abbin aure
zaiyi kusa.......
Inayah dake bakin kofar shigowa dasuka Bari a bude Zata shigo
A Rikice qafafunta na rawa tace"
Aure Kuma?
##MAMUH#
#HOT/LOVE/ROMANCE
#MAJEED& INAYAH
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/4, 8:32 AM] MG: *_52_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Da sauri suka kallo kofar lokaci daya atare cikin mamaki da fargaba.
Anty Hafsat ce tayi saurin tasowa tana kokarin riqo hannunta su qaraso ciki tana
cewa"
Yaushe kika dawo Inayah?
Bata amsa tambayar ba sbd batama wani gane me Anty Hafsan ta fadaba qafafuwanta na
rawa zuciyarta na bugawa da qarfi tace"
Anty Hafsat abbi ne naji kuna maganar zaiyi aure fa?
Kinga Inayah zauna muyi maganar a natse ba abinda kikaji din bane wata maganar
muke......
Kasa Zama tayi ta tsaya tana kallon umma yaganah da duk tayi wani iri sbd damuwa
wadda take bayyane qarara a kan fuskarta
Take taji wani mugun tashin hankali da 'daci na cika maqoshinta zuwa bakinta da
qyar ta tattaro yawu tace"
Anty Hafsat fuskar umma yaganah ta nuna tana cikin damuwa
Karki wani boyemin ku fadamun Gaskia idan aure Abbi zaiyi Ni insani..
Yanayin yanda tayi maganar muryarta a harde da tashin hankali da firgici yasa umma
yaganah sauke numfashi tana dagowa ta kelleta dakyau cikin sanyi ta janyo hannunta
tana cewa"
Zo ki zauna Kuma ki nutsu hafsat Tai Miki bayanin komai banason hayaniya ko tashin
hankali iya maganace kawai tunda ba auren aka Riga anyiba.
Wani nauyi kirjinta ya qara Mai tsanani hartaji numfashinta na Neman toshewa daqyar
Anty Hafsat ta zaunar da ita suka kalleta su duka atare cikeda damuwa.
Umma yaganah ce taci gaba da cewa"
Kofa nutsu karki jawowa kanki ciwo nafada Miki bakomai bane Dan yaqara auren tunda
dama ai kinsan koba yanzu ba Dole MAJEED zaiyi aure wata Rana tunda ke naki auren
bawani daukansa aure kukaiba kinata shirmen sagarta da shagwaba kin kasa tsayawa
kisan me kikeyi
Mahaifiyarsa kuma ba tsayawa zatayi tana kallonsa Yana garariba Babu aure ga
manyanci na Neman cimmasa.
Anty Hafsat ce ya karbi zancen da cewa"
Ko ahaka dai ba komai bane Inayah
Kishiya kaman Dr farhat ai ba Zaki daga hankalinki ba tunda kinsan halinta tasan
naki Kuma kaman yanda umma yaganah tace baa dauraba karki saka damuwa tun
yanzu........
Kasa riqe numfashinta dake kokawar toshewa tayi sbd maganganunsu dake fasa
zuciyarta tako Ina take idanuwanta suka ringa ganar Mata duhu suna neman rufewa.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Ke Inayah,
Inayah?
Innalillahi..
Kanta sukayi suna tarota ganin numfashinta na Neman daukewa.
Hankali tashe suka ringa kiran sunanta a rikice suna rasa abinyi Dan kowa bayason
Kiran Dr farhat Musamman yanzu da Inayah din tasan abinda ke Shirin faruwa.
Waya umma yaganah ta dauka Kai tsaye takira Dr Abdul tareda sanar dashi suna zuwa
asibiti yanzu da Inayah.
Cikin tashin hankalin abinda sukace yace su Kira gashinan zuwa gidan ya dubata.
Lokacinda sukai wayar Yana gida tareda mahaifiyarsa dataqi komawa tayi zamanta a
Lagos dama tuntuni MJ Muhammed yafison zamanta a Lagos itace taqi Amma yanzu tunda
'yarta na garin ta zabi Zama anan su Inna kawai ya rage ataho Mata dasu idan Abdul
yaje.
Tareda umma Hadizan suka iso gidan saidai Kuma bayan sun iso suka rasa yanda zasu
bawa Abdul Daman shiga har dakin umma duba Inayah gashi abbin yau ya Dan samu sauki
ya fita sbd tafiya yakeson Yi ma kwanakin.
Haka dai sukai shahada tunda muharraminta ne suka basa Daman shigowa yaje ya duba
Inayah din wadda sosai take neman shidewa da attack din data samu.
Dan taimakon dazai Bata yayi tafara Dan dawowa daidai saidai sbd tashin hankalin
data sakawa kanta numfashinta yaqi dawowa daidai haka ya fito ya wuce sbd bazai iya
ganinta a wannan hakinba Kuma yasan Inayah Bata samun attack saita Shiga wani
mummunan shock na tashin hankali
Koma me akai Mata ya tabbata ya danganci Abbi sbd abinda ya shafesa ne kawai yake
saka Inayah cikin tashin hankali Amma Babu abinda yake damunta harta saka arai sbd
koyaushe shine kadai Mai mahimmanci agunta.
Yana tafiya Dole Dr farhat suka Kira bayan hankalinsu yakuma tashi da hawayen
datake Babu kakkautawa cikin yanayi na daukewan numfashin.
Dama yanzu a gidan Kira kawai Dr farhat ke jira Dan haka ana kiranta jiki na rawa
ta taho tana nuna damuwa a fili sosai akan meya samu Inayah din Amma Babu wanda ya
fada Mata.
Zuwa Dr farhat yasa Inayah Jin wani sabon ciwo a zuciyarta tafara bori batason a
dubata abarta ta mutu
Ita mutuwarma takeso ta huta...
Da mamaki suke kokarin tausarta Amma ta tibure ta dinga zuba kuka tana qin Bari ko
tabata Dr farhat tayi.
Basu umma yaganah ba ita kanta Dr farhat hankalinta tashi yayi sosai tafara tunanin
ko kwakwalwar Inayah tasamu matsalane?
Haj umma da batasan meyake faruwa ihu da tashin hankalin faman da akeyi da Inayah
yasata fitowa bedroom dinta cikin fargaba ta iso dakin umma yaganah da aketa zuba
tashin hankalin tana cewa"
Innalillahi,
Lafiya?
Meyake faruwa da ita?
Iska ne akanta?
Dama tanada iska ne kome?
Kasa magana anty Hafsat tayi sai umma yaganah ce tace"
Batada iskan komai
Kawai ciwo take takuma qi Bari a dubata sai rigima takeyi....
Mamaki sabone ya Kama Haj umma
Yanzu akan ciwo da batason a dubata take zuba wannan tashin hankalin?
Dr farhat da abin yafara Bata tsoro ganin sosai Inayah ke kuka tana daga musu
hankali tace"
Kodai zaa Kira AA ne sai awuce da ita asibiti can zaa iya fin karfinta a dubata sbd
tana kokawa da numfashinta dakeson daukewa Amma taqi barin na taimaka Mata.
Hankali tashe umma yaganah ta dauko wayarta ta saka Kiran MAJEED sbd ganin
numfashinta yafara sama sama.
A natse ya dauki wayar tareda sallama a hankali.
Cikin kokarin daidaita muryarta ta Dan boye tashin hankalin ta sanar dashi Inayar
batada lafiya sosai Kuma takasa Bari Dr farhat ta dubata numfashinta na......
Bata qarasaba taji dib alamar ya kashe ne kokuma network ne batasaniba.
Kokarin sake saka kiransa tayi taji Amma Sam Bai dagaba cikin sabon tashin hankali
tace"
Inaga network nada matsalar muje da ita asibitin kawai.
Ko asibitin ma win yarda tayi atafi sbd ganin Dr farhat kawai tsananta toshe
numfashinta yakeyi
Gashi zuwa lokacin ta matuqar galabaita Dan haka cikin fada sosai umma yaganah take
tirsasata tashi.
Koda umman ke fada batama San me take cewaba sbd idanuwanta dake kokarin
rufewa...saiga Abbin ya shigo Kai tsaye zuwa dakin umma yaganah din.
Da sauri duka suka juya suna kallonsa baka gane komai a fuskarsa Amma dukkaninsu
suna iya hasaso tsananin damuwar dake ransa na ganinta hakan.
Yana shigowa Kai tsaye gurin ya nufa anty Hafsat na Kira sunanta kada ta rufe
idonta.
Tana ganinsa ta maida idanuwanta akansa tana Jan numfashi cikin zafi..
Hannuwansa biyu yasa ya tallafota Kai tsaye daga kan kujera zuwa jikinsa Yana Kiran
sunanta cikin yanayi na kulawa sosai da damuwar meya sameta.
Daqyar taja numfashi tana tsiyayar hawaye ta bude Baki ahankali tace"
Abbi aure zakayi????
Bata fuska yayi cikeda mamakin yanda taji zancen take ransa yayi mummunan baci Amma
dayake bakowa ke gane yanayinsa ba duk Basu ganeba.
Ruwan da umma yaganah ke miqowa ya karba ya Kai Mata abaki cikin sanyi yace"
Relax and breath,
Just breath,
Yawwa deep breath,
Sake Jan numfashin...
Yanda yace tayi takeyi ahankali numfashin nata na daidaituwa ahankali ahankali.
Sam taqi dagowa ta kalli kowa dakin sbd haushi da zafin kowa takeji hardasu umma
yagananta.
Ganin tadan dawo hayyacinta yasashi juyowa ya kalli Dr farhat dake kallon ikon
Allah Dan tasan Inayah itace mafi so da kauna a rayuwar Abbinta Kuma tasan sangarta
da shagwaban Inayahn Amma Batasan yaushe tafara boriba haka kokuwa Dan Bata taba
rigima bane gabanta?
Qatuwar budurwa na irin wannan tashin hankalin Amma mahaifinta ko damuwa yayi Mata
ko 'yar tsawa baiyiba saima kokarin dawo da ita daidai yakeyi cikin sanyi da
nutsuwa tareda boye tashin hankalinsa na ganinta hakan.
Haj umma dake tsaye sake da Baki cikin mamakin dayafi na kullum ya Dan kalla Yana
danne yanayinsa kafin ya kuma maida kallonsa kan Dr farhat Kai tsaye yace"
Dr zaki iya tafiya I can handle this,
Thank you.
Juyawa tayi ta kalli Inayah cikin kulawa ta nufeta zatai Mata magana
Inayah tayi saurin fara kokarin miqewa tana kokarin janyewa anty Hafsat ta dafeta
tana kokarin tausarta kafin takuma borewa.
Ganin hakan yasa Dr farhat dakatawa tana kallon MAJEED Daya dauke Kai ba annuri ko
daya a fuskarsa da duka abinda kowa yayi agidan.
Murmushin yaqe tasaki tareda yimusu sallama ta yiwa Inayah fatan samun sauki ta
wuce.
Shiru ya danyi tareda sake hadiye 'dacin ransa ya juyo ya kalli Inayah dake hawaye
sosai har lokacin ta dago ta kallesa take taji wani sabon 'daci da qunci na cika
ranta matuqar Abbinta zai auri wata mace....
Tasowa tana sakin sabon kuka Zata bar dakin umma yaganah ta riqeta tana cewa"
Zan mareki idan bazaki nutsuba
Ba'ason hauka kinji ko??
Sabon kuka Mai qarfi ta saki tana cewa"
Umma yaganah bazan iya nutsuwaba Ni kubarni natafi banason ganin kowa....
Aurenma banayi na fasa bazan zauna da kowaba da Abbina.....
Sai alokacin Haj umma ta fahimci duk wannan tashin hankalin akan meye,
Takaici ne da mamaki suka tarar Mata wato duk wanna daga hankalin jama'ar gida da
borin kaman me tashin iska da asthma duk akan ance MAJEED zaiyi aure ne?
Wannan halin na Inayah na shashanci Yana Bata takaici da damuwa Dan haka cikin
siqewa tace"
Yanzu dama duk wannan ihun da tashin hankali dakikeyi kika daga hankalin kowa duk
akan majeed zaiyi aure ne?
To so kike gabaki daya ya qare rayuwarsa gurin tattali da renonki shi Kuma bazai
Gina tasa rayuwarba?
Da Ina tareda shi tunima dayayi auren Dan bazai zauna saidai yaga 'yaya wasu na
tarawaba shine zakizo kina shirmen ihun kuka da......
Cikin kuka Inayah tace"
Ni nace bazan Tara Masa 'yayan bane?
Ai Nima Zan Haifa Masa idan kika barmu...
Fiddo idanuwa Haj umma tayi cikeda mamaki,
Su umma yaganah da Anty Hafsat ma tsit sukai yau ciwon bakin Inayah yayi musu Dadi
duk da duk kunya ta kamasu da sauri umma yaganah ta buge Mata bakin sbd karta
qarasa.
Shi kansa abbin kasa magana yayi sbd mamakin bakin Inayah Daya Gama wuce tunaninsa
hakama da bacin ran zancen dasuka sanar Mata da wani abin yasameta ayau acikinsu
babu Mai abin fada masa sun kashe Masa 'ya ko me??
Numfashi ya sauke a boye Yana sake kawar da bacin ransa ya kalli Haj umma dake
kallonsa jiran abinda zai fada sbd duk suna iya hango zallar bacin ransa duk da
boyewar dayake kuwa.
Daidaita kalamansa yayi cikin nutsuwa yace"
Umma Ina dauka maganar auren Dr farhat bamu gama meyasa zaku dagawa Inayah hankali
da zancen bayan bawai Kai karshen maganar akayiba.
Umma yaganah da Anty Hafsat ya kalla suma yace"
Meyasa zaku sanar da ita umma tunda kinsan halinta
Yanzu gashi tana neman illata kanta akan hakan,
Maganar aurena da Dr farhat Kar akuma tadasa a gabanta sbd ba........
Maganarsa tasa Inayah fashewa da sabon kuka tareda juyawa da gudu tabar wajen tana
cewa"
Kenan yin auren zaiyi da Dr farhat.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/4, 3:04 PM] MG: *_53_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Rintse idanuwansa dasuka Dan sauya yayi tareda juyawa yabar gurin shima Yana kansa
na Kuma sarawa dama gashi kwana biyun Yana fama da ciwon kan.
Yana barin gurin umma yaganah Haj umma suka kalla itada anty Hafsat sukaga yanda
tayi zuru da mamaki dashiga tunanin agaban kowa MAJEED zaiyi mata magana Mai Kama
da fada kaman shine uban nata.
Juyawa tayi jiki a sanyaye ta koma bedroom dinta tanaji wayarta na ringing
juwairiyyah na Kira takasa dauka sbd ranta ba Dadi ko kadan bazata iya wani bacin
ranba sbd yanzu juwairiyyah Zata sake dorata akan abinda zai quntata ranta.
Anty Hafsat Kuma bayan Inayah tabi zuwa dakinta Dan tausarta Amma rarrashinta
duniya tayi Inayah din Taki Dena kuka.
Har bayan magriba suna fama da Inayah din Haj umma dake dakinta tana Dan jiyo yawon
umma yaganah da Anty Hafsat gurin rarrashin Inayah din sama sama
tayi banza dasu sbd gabaki daya ganin takeyi su suka Gama lalata Inayah din da
bakinta baya tauna magana sam Sam.
Ana gap da ishai haka anty Hafsat ta hakura ta tafi gida tabar umma itama tayi nata
rarrashin ta hakura ta zubawa sarautar Allah Ido.
Abincin dare ma kusan daga ita sai Haj umma ne sukaci Inayah taqi fitowa shima
MAJEED din baizoba Koda Haj umma takirasa shayi kawai yace akai Masa.
Zubbi ce takai ta ajiye Masa a palonsa ta fito ta dauki da Inayah ma da umma tace
ahada Mata takai mata Amma ko motsawa Inayah batayiba tana kwance.
Duk dubara da rarrashin umma yaganah Inayah kin Shan ko tea tayi Dan haka jiki a
mace umman ta barta taje ta kwanta.
Zafi da ciwo zuciyarta ke Mata sosai bayan hawaye Babu abinda takeyi sbd bazata
taba iya kwatanta Abbinta da wata macen ba,
Wannan zafin datakeji har abbin ma takejin zafinsa akan lamarin.
Kwana tayi da ciwo a Rai da damuwa me tsanani Dan haka Koda garin ya waye da wani
zazzafan zazzabi ta tashi Mai qarfi.
Zubbi da umma yaganah ne akanta hankali tashe umma na rage Mata zafin gashinta da
farin qaramin towel
Zubbi kuwa chocolate custard me zafi ta hado Mata da farin soyayyan qwai Mara komai
aciki.
Kasa Shan komai tayi Saida umma yaganah ta nuna Mata rauninta na itama Zata iya
kuka idan Inayahn bataciba kafin Tasha custard din aikuwa ko Gama Sha bataitaba
amai ya taso Mata da sauri zubbi ta kamata takaita toilet ta ringa Aman cikin
wahala sbd rashin qarfin jiki.
Bayan tagama ruwan zafi zubbi ta hada Mata tayi wanka ta fito umma ta dauko Mata
wata qaramar Riga Mara tsayi Mai taushi ta saka Takoma ta kwanta jikinta na
tsananta zafi.
Wanke toilet zubbi tayi ta gyare dakin tsaf ta kashe Mata AC ta kunna humidifier
bayan tazuba wasu turaruka cika masu dadi suka fice daga dakin har umma.
Umma na barin dakin tana Isa nata ta dauki wayarta ta saka Kiran MAJEED.
Ta jima tana ringin kafin ya daga murya ahankali yace"
Barka da yau umma.
Barka MAJEED,
Yau baka fitoba Allah yasa lfy dai ko?
A natse Yana danne yanayinsa yace"
Lafiya kalau alhmdllh,
Yaya Inayah?
Tana Nan tana Rigimar ko?
Numfashi ta sauke a sanyaye tace"
Tanata rigima tun jiyan gashi yanzu ciwo yashigo ciki sbd zazzabi Mai qarfi takeyi
custard ma datakeso Tasha tayi amansa,
Bansaniba ko Dr farhat din zaa Kira tazo ta dubata Amma Kuma wata sabuwar rigamat
zatayi tana ganin Dr farhat din.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda cewa"
Ganinan zuwa zanfara dubata kafin Akira likitan.
Kashe wayar umma tayi tareda ajiyewa gefe tana Zama kan kujera tana cewa"
Allah yasa ta tsaya taji maganarka.
Kwance take tanajin zazzabin sosai bacci na Dan daukanta Yana sakinta duk da hakan
tunanin Abbinta da aurensa na maqale cikin ranta.
Turo kofar dakin yayi Kai tsaye tareda shigowa a natse sbd shima ciwon Kaine atare
dashi.
Fararen Fendi wears ne ajikinsa
yau Qamshin nasa ma ahankali yake tashi daga jikinsa sbd Bai wani saka turareba
Qamshin na jikinsane daya dade da Kama Turaren Mai sunyin Dadi.
Cikin nutsuwa ya tako har bakin gadon ya tsaya Yana kallonta ahankali cikin nutsuwa
ya lumshe fararen idanuwansa Yana budesu akanta cikeda kaunarta Mara sirki da qarfi
wadda take gine cikin ransa shiyasa Sam Baya son bacin ranta ko damuwarta Amma
tacika rigima yanzu duk akan aurensa dake kanta data dauka ta saka arai.
Bude idanuwanta dasukai nauyi da sauyawa sbd zafin zazzabi Jin mutum akanta tasan
Abbin ne sbd qamshinsa daya shiga hancinta.
Maida idanuwanta tayi ta rufe tanajin nauyin kirjinta na qaruwa sai kawai hawaye
suka fara gangaro Mata.
Yana ganin hawayen nata yaji jikinsa yaqara sanyi ya zauna ahankali bakin gadon
nata tareda Kai hannunsa dakeda sanyin ACn Daya fito ya taba goshin yaji zafinsa
sosai
Da kulawa sosai yace"
Da wannan zazzabin naki ajikinki kike sake wani kukan Inayah??
Kinason ciwo ya kwantar dake ne?
Meyasa bazaki Dena kukanba haka?
Juyar da kanta tayi tana sake sakin kuka Mara sauti a wahalce batareda tace Masa
komaiba.
Shigowar Haj umma ne tareda Salimat data kawo wasu ruwan da towel Zata rage Mata
zafin jikinta da umma yaganah tace zubbi takuma Yi Amma zubin na aikin gyaran Haj
umma Dan haka ita takawo.
Haj umma kuwa duba Inayah din tazo yi sbd rashin lafiyarta yasa gidan kaman anyi
mutuwa kowa tsit ba walwala tunda princess din gidan ba lafiya.
Salimat na ganin Abbi a dakin ta ajiye ruwan kan bedside drawer ta juya ta fice.
Haj umma ma da 'yar kulawa kadan tace"
Yaya jikin nata?
Allah yabata lafiya
Amma saita sakawa kanta salama
Wannan kukan Babu abinda zai qara Mata sai ciwon.
Amin"MAJEED ya amsa a taqaice Yana sake taba gashin Inayah din daya zafinsa yaji
duk ya daga Masa hankali harya Dena Jin nasa ciwon kan.
Cikin kulawa yace"
Ina Ms Salimat take tazo ta rage Mata zafin jikin kafin Dr farhat tazo ta dubata..
Fadan sunan Dr farhat kawai yayi yasata sake tsananta hawayenta saiga umma yaganah
ta bude kofa itama ta shigo da tea me zafi a tray tazo ta ajiye.
Umma yaganah ki rage Mata zafin jikin Nan yayi yawa kafin likita tazo ta dubata
jikin nata Yana tsananta zafi sosai...
Cikin kuka ta tashi zaune daga kan gadon tana cewa"
Ni banason Dr farhat ta dubani
A Kira Dr Abdul....
Satar kallon Abbi umma yaganah tayi tana matsowa gurin gadon Zata dauki qaramin
towel din Fadi tas
Cikin kuka Inayah tasake cewa"
Ni har rage zafin banason tunda ba zafin danakeji a zuciyata zaa rageba,
Wlh abbi idan kayi wani auren zuciyata bugawa zatayi nidai