Showing 9001 words to 12000 words out of 124042 words

Chapter 4 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

74

Nutsuwarsa da abinda yake kalla yaji qwarin gwiwar cigaba da yaqi da
gwagwarmaya Dan inganta rayuwarsu musamman ganin yanda takeda tsananin qawa zucinsa
kasancewarsa Mahaifinta Kuma mahaifiyarta.

Kafin tayi wayon datake dashi yanzu yasha wata irin gwagwarmayar wahalalliyar
rayuwa Dan samarda abinda zai rainar masa ita.,

Karatun jamia yake alokacin hakama bayada aikin komai face kalolin aikin wahalar
daya ringa yi Yana samarda abubuwan da kowane baby zai buqata.

Cikin wani irin tsananin hali yasamu ya kammala karatunsa yayi service yafara zuwa
yan ayyukan da zasu ringa taimaka masa Dan lalurarsa data 'yarsa.

Sana'ar gadin wani gida yafarayi tsawon watanni kafin Mai gidan yabar qasar Dole ya
nema wata aikin.

Daqyar yakuma samun aikin security a wata private hospital.

Da Wannan aikin yake rayuwa kafin raga baya yasamu aikin wankin mota yana hadawa
dashi.

Shekarar inaya uku yafara tunanin aure badan Jin dadinsaba ko Dan yanajin buqatar
hakan
Kawai dai zaiyi auren ne Dan ya samarwa 'yarsa kwanciyar hankalin samun mutum
ataredasu ko zata sake tayi rayuwa Kamar kowanne yaro,
Amma badan wai ya Samar Mata uwaba,
Har abada shine uba Kuma uwar INAYArsa,
Har abada babu mace data Isa ta zamto uwa ga INAYA,
Shine uwa Kuma uba
Ita kanta Inayah duk da qarancin shekarunta tariga ta Dan San halayen Mahaifinta
Dan haka ta daina ambatar sunan mahaifiya tuni sbd Hani da yayi mata da hakan aduk
lokacinda bakinta ya furta Mama.

Alokacinda yayi neman auren farko ga 'yar Mai Basu sallah a masallacin anguwar da
farko lafiya kalau yafara zuwa fira bawai danma yasan Mai zaiyita fadaba sbd shi
miskilin mutum ne shiyasa Bai cika shiga mutaneba,

Iyakacinsa da 'yan anguwar da mutanen gidan hayarsu gaisuwa
Itama gaisuwar sbd sanin mahimmancinta a addini ne.
Da yawa mutanen anguwar da mutanen gidansu na haya kallon me girman Kai da Rashin
mutunta mutane suke masa saidai Kuma basa iya fada gaban idanuwansa sbd kwarjinsa
da kamewar mutuncin kansa duk da kasancewarsa qaramin matashi.

ABDULMAJEED ABBI kamar yanda yarsa ke kiransa kusan hakan kowa ya sansa,
Wani irin baudadden mutum ne da babu Wanda yake iya gane inda ya dosa,
Meye ne acikin ransa?,
Meye abinda yake tunani?,
Waye shi?

Sam babu Wanda yace yataba ganin koda murmushinsa bare dariyarsa sbd
Bayan 'yarsa babu Wanda ya taba yiwa koda murmushin bare dariyar
Dan haka kusan kowa baya masa dogon shishigi
ciki kuwa harda yan saka idon anguwa da munafukan anguwa kowa ya kama kansa dashi
Zagi dai ne Idan anzauna dattijawan anguwa da Basu San su kama girmansuba sai sunyi
saka idon kullum cikin zaginsa sukeyi sunayi dashi a fakaice
Idan yawuce ta gabansu yayi musu sallama ya gaishesu haka zasu ringa washe Baki
suna amsawa suna yabonsa da yabon 'yarsa
Daya wuce zasu fara zundensa.

Aurensa da Hafsat yar liman ya lalace ne bayanda aka zuga mahaifin nata da cewar
ana zargin zafin zuciyarsa da baqar zuciya kamar kuturu ya ringa azabtarda matarsa
da duka da yunwa da wahala da baqin talauci ta gudu ta barsa da jinjirar 'ya bayan
ta haihu,

Wasu Kuma suka ringa fadar bada aure ya Haifa yarsaba Dan haka hafsatu renon 'yar
gaba da fatiha kawai zata tayi.

Wannan zugar ta lalata maganar aurensa da Hafsat wadda take tsananin sonsa Kuma shi
kansa har cikin ransa ya yaba da nutsuwarta yayi shaawar auranta ta zauna da
Inayah.

Bayan an hana masa auren hafsa bai cire raiba sbd yanzu sosai yakeda shaawar
samarwa Inayah Mai zama da ita Dan haka tunanin yin auren yashigesa sosai bawai Dan
har lokacin tunaninsa ya sauya akan Mata bane dakuma Wai Jin Yana son aure ko mace
ba,
Sam Mata bayada shaawarsu ko kadan,
Baya Kuma Jin tunaninsa da tsananin yanayinsu zai sauya a zuciyarsa har abada.

Fatima yakuma nema aure a bayan layinsu
bayan ya Dan kwana biyu Yana zuwa fira gunta daganan ya aika Mijin Yagana da Daman
shine kawai yake tsananin ganin girmansa da mutuncinsa ya nema masa aurenta.

Kamar yanda tafaru farko hakance takuma faruwa
Har anbasa auren daga baya aka fasa sbd wasu maganganun da aka Kuma kaiwa
mahaifanta itama.

Cikin qanqanin lokaci Saida ya nema aure so hudu ana hanasa daga Nan Mata suka Kuma
ficewa a Ransa kwata kwata
Musamman sbd yanda aka dauki hanyar aibata masa 'ya sai hakan yakuma tsananta
qamewar zuciyarsa akan Mata da mutane,
Bai Kuma shaawar neman kowace macen ba,
Yacire maganar aure daga ransa kwata kwata har abada bayajin zai Kuma kallon kowace
mace da sunan wani abu face sunansu na mace.

Daga Wannan lokacin burinsa ya sauyu ya karkata ga ilmantar da 'yarsa yakuma dage
ba dare ba Rana da Neman aiki da mafita dama Kuma karatu dayakeson qarawa sbd
babban burinsane Dana mahaifinsa tun Yana raye.
Aikin wahalarsa dayakeyi ya matuqar tsananta Dan kuwa bayan security na asibiti da
aikin wankin mota yanzu harda sana'ar 'dan acaba yanayi Idan yasamu abokin aikinsa
na gurin aikin security ya basa Aron mashin dinsa yayi.

Rayuwa Mai tsanani da wahalar gaske yake gudanarwa,
Baya samun cin abincin dazai kosar da cikinsa,
Duk Rana da dukan ruwan dayake Sha na fafatawar ayyukan wahalar dayake duk na
inganta rayuwar Inayah ne,
Ita yake siyawa Yar sitirar sakawa sbd ko sitirar arziki basudashi,
Abincinta da Shanta sune yake iya kokarin samarwa,

So da dama haka yake wuni da yunwa saidai yasha ruwa da Dan biredi haka ya kwanta
amma Inayah baya taba Bari ta nema abinci ko abin buqata ta rasa.
Ahaka yake gudanar da rayuwarsa acikin wani irin tsananin hali.

Yagana tana samun aiki a private school ta primary ya dage yayo wahalarsa yasamu ya
saka Inaya duk da kusan shekarunta sunyi qanqanci Amma haka ya sakata sbd a gida
yagana ta dena zama aikin take zuwa
Shima gashi yanzu ya sake dagewa da ayyukan wahala iri iri da yawon Neman aiki
Dan haka kullum yake kaita makarantar idan yadawo da wuri ya biya ya daukota Idan
baidawoba anan take zama tareda yagana har sai antada Yan primary kowa ya tafi sai
sudawo gida ta zauna gurin yagana harya dawo,

Yana dawowa yake tsayawa gurin yagana ya dauketa su shige Bata qara fitowa dakinsu
sai washe gari Idan zaije sallah wani lokacin yakan kaita gurin yagana yaje yadawo
Wani lokacin Kuma rufeta yake a dakin yaje yadawo sbd itama Kaman tayi gadon
mahaifin nata miskilace ta gaske batason zuwa koina tafison ta zauna gurin Abbin
nata.
Musamman sun saba rayuwarsu daga ita sai shi.

*****
Wani tsautsayi daya samesu shine dakinsu daya fara zubar ruwa ta sama Idan ana ruwa
yasa tunda damunar ta tsayu sosai yadaina baccin dare,

Zaune yake kwana yayi gadin Inayah tayi bacci sbd gudin yanayi na tsautsayi ko zai
riskesu,

Da safe kafin su fita zai kwashe ruwan daya taru a dakin ya goge musu ya gyare
dakin dako ledar qasa babu sai Rabin dakin ne kawai keda Leda Shima gurin katifar
Inayah sbd kada sanyi ya kamata.

Sauyin aiki akai masa daga security na asibiti zuwa na wani super market.

Ranar farko daya fara aiki a super market din yahadu da wani class mate dinsa a
gurin.

Da farko Nuradden ya bayyanarda mamakinsa sosai ganin A MAJEED a matsayin security
sbd sanin tsananin ilimi da kyakkawar takardun da MAJEED din yake dasu Dan haka Bai
wani boyeba ya bayyanarda mamakinsa tareda yimasa tayin wani aikin wanda yafi
Wannan.

Da farko MAJEED yaso kaucewa tayin Amma Nuradden din ya dage tareda tabbar masa ba
daga garesa bane taimakon dagaske maikatan ake nema.

Amincewa yayi washe gari ya Isa makekiyar maaikatar kasuwancin mahaifin Nuradden
din cikin saa yasamu aikin cashier na daya daga cikin manyan malls dinsu sbd
sunason fara jarabta aikinsa kafin su basa wani aikin daya kamata shima sbd
Nuradden yayita zuzuta musu ilimi da MAJEED din yakedashi
Dan hkaa ahankali cikin yardar Allah yafara aikinsa na cashier a gurin.

********
Tunda yasamu aikin cashier a taqon mall din rayuwar tafara yi masa sauki shida
yarsa harma da yagana da mijin yaganar sbd shi din mutum ne Mai alkhairi musamman
ga mutanenda suke tsananin kaunar Inayah,

Duk Mai kaunar Inayah to tabbas matsayinsa a cikin ransa Mai girma ne,
Yanda yake tsananin kaunar 'yarsa Jin yake komai zai iyayiwa duk namijin daya
aurawa ita duk ranarda ya cutatar masa da ita,

Wasu lokutan har fargabar yanda zai fara fuskantar bayar da ita aure zuwa wani
gurin yake Dan haka alqawarine Mai girma acikin ransa na zai wadatar da ita da
ilimin Mai zurfi sbd rayuwa a gidan wani tayi Mata sauki.

Majeed sam Bai damu da abun hannunsaba duk lokacinda yasamu 'yan kudade baya qyashi
haka zai kashewa Inaya sauran Kuma ya bawa su yaganah Suma tunda ba laifi suna
cikin yanayin rayuwa suma,

Basu taba haihuwaba itada mijinta wanda yake zaune baya iya fita nema sbd yanayin
Rashin lafiya dayake ciki na sugar gashi anyanke duka qafafun nasa biyu duk sbd
lalurar a keke yake rayuwa,
Dan haka shigowar Inaya da Abbin nata rayuwarsu ba qaramin taimakawa rayuwarsu
yakeyiba
Hakannema yasa duk yanda ake gulmar da zindensa babu ruwansu basa shiga sbd sukam
majeed kusan shine rufin asirinsu yanzu
Suma qarshe aka ringa binsu da zagin makwadaita Dan sungansa kalar 'yayan masu
arziki dama Kuma a wani bangaren da yawansu suna masa kallon Wanda yafito daga
zuriar masu hannu da shuni Kuma duk iya gulma da bin diddiqi ankasa sanin asalinsa
dakuma inda yafito.


***Ahankali Lokaci yaja sosai har INAYA ta kammala nursery tashiga primary hartayi
nisa tana primary 4.

Har lokacin a mall yake aiki saidai ba laifi yasamu qarin girma sosai harya zama
assistant manager,

Alhmdlh komai Yana tafiyar musu a daidai dan kuwa babu kalar Jin dadin da Inayah
Bata samu gurin mahaifinta sai Wanda baa rasaba daidai gwargwadonsa.

Yanason tashi yabar gidan ya kama haya wani gurin sbd 'yarsa datake girma gashi
gidan gidan tarone mutane iri daban daban
amma Kuma sbd rayuwar kadaici da zata iya wargaza Mata walwalarta data fara samu
sakamon girma data fara shiyasa Bai tashiba gidan har lokacin Amma zuwa lokacin
yanada halin sauyawa din tunda sunfara samun rufin asiri.

Inaya na gaf da kammala primary 4 yasamu hayar wani gidan acan hanyar gurin aikin
nasa Dan haka yafara musu shirye shiryen tashi duk da ba wani kayan suke dashiba
bayan katifar baccin Inayah sabuwa Mai dakan mutum daya,
Sai qaton bargon dayake shimfidawa qasa ya kwanta sai jakar kayansu da 'yan
abubuwan amfanin cin abinci.

yasamu su yagana da maganar tashin nasa dakuma tayin dayakeda niyar yimusu ko Allah
zaisa su amince.

A zaune ya samu malam Aminu Mijin yaganar a kofar dakinsu kan tabarma Yana Dan
sauraron radio dayake dare yayi Dan har qarfe tara takusa bugawa.
Inayah batai bacciba sbd assignment datake dashi dazai koya Mata Kaman yanda yasaba
yimata tishin karatunta na bokon Dana addini kowanne dare kafin tayi bacci Dan haka
tareda ita yaqaraso shimfidar malam Aminun Yana riqeda hannunta jikinta sanyeda
doguwar rigar bacci Mai kauri da har qasa sai qaramar hular sanyi akanta,
Hatta qafafunta suna sanye cikin safa Mara nauyi sbd Sam baya Wasa da duk abinda
zai taba masa lafiyarta shiyasa ko Yaya yaji Alamar sanyi to baya Wasa ko bacci
zatai saida socks.

A natse Kaman yanda yake koda yaushe ya zauna gefen tabarmar Yana bude Baki cikin
kamilalliyar muryarsa Mai nutsuwa yace"

Barka da dare Malam,
Yaya lafiyar jikin?
Allah yaqaro afuwa da nisan kwana.

Sosai cikin kulawa malam din ya amsa Yana kallon Inayah data zauna gefen mahaifin
nata yace"

Inayah yau bakiyi bacci da wuriba Kika biyo Abbin naki cikin sanyin Nan.

Ahankali ta kallesa tana sake Dan guntun murmushinta da qaramar muryarta tace"

Ina wuni malam?

Sake Yar dariyar kulawa da shaawar nutsuwarta data abbinta yayi Yana amsawa kafin
yace"

Ki shiga ciki gurin ummen taki yagana tana sallah ne.

Sake riqe hannun abbinta tayi tana sauke Kai Dan
Saida Abbin ya Dan kalleta da fararen idanuwansa yayi Mata alamar taje din tukuna
ta miqe ta nufi kofar dakin da sallamarta a Baki ta shige.

Cikin nutsuwa yayiwa malam din tayin zama dasu a sabon gidan hayar daya kama Mai
daukeda dakuna uku zuwa.,

Baya boye boye shi mutum ne Mai magana kai tsaye Dan haka Kai tsaye ya sanarwa da
malam din sbd yanda Inayah tayi sabo fa yagana dakuma yanda INAYArsa zata cigaba da
walwalarta cikin mutane Idan taga Basu kadaineba a gidan.

Da farko malam shiru yayi Yana nazarin al'amarin
sbd Kai tsaye suje su qarawa Abdulmajeed din nauyi Kaman Bai kamata ba tunda Shima
yanzunema ya 'dan damu walwala ta abin yi.

Amma Kuma ata wani fannin kaman yanda Abdulmajeed din yafada rayuwar Inayah kam
Idan babu mutane zata iya rasa walwalarta Duk da idan tana ganin Mahaifinta Bata
buqatan kowa Amma ai shi mutum rahama ne,
Kuma itama yaganarsa Yana so tasamu mutanenda koba ransa zasu dauka amanartaba
tunda Suma ba kowane dasuba Kaman su Abdulmajeed din.

Abdulmajeed yabarsu akan suyi shawara kafin lokacin tashin nasu yayi ahaka akabar
zancen Idan yayi shawara da yagana.

Bayan komawarsu daki tace zatai fitsari dayake yanzu tafara girma dole badan yasoba
yake barinta zuwa bandakin gidan Amma qaidane Bata Idan so nawa zata shiga bandakin
saiya wanke Mata shi dasu Izal germicide harma dasu Dettol kafin tashiga Kuma harta
Gama tafito Yana tsaye bakin bandaki Yana gadinta.

Idan Kuma baya gidane to yagana ma ta saba itace zatai Wannan aikin haka zata wanke
takuma tsaya harsai inayan ta fito.

Su hand sanitizers kuwa baya Bari suna qarewa yake siyowa sbd ita din,
Data fito toilet din kokuma tafito filin gidan tayi wani abin yake tsaftace Mata
hannaye dasu sbd shi wani irin mutum ne Mai tsananin tsaftar gaske shiyasa a wani
fannin mutanen gidan da anguwar dama Yan gurin aikinsa ke ganin kamar yana qyamar
mutane.

Yanzu dinma datace zata bandakin kayan wanke bandakin ya dauka tareda fitila mai
tsananin haske ya fice yaje ya wankesa tas tashiga Yana tsaye ta fito ya wanke Mata
qafafunta da hannayenta suka koma dakin.

Da kanta ta Kuma gyara shimfidar lafiyayyar katifarta tayi Addua ta kwanta ya gyara
mata rufarta kafin ya miqe ya dauko jakar takardunsa na karatun masters dayakeson
farawa da yardar ubangiji Idan su yagana su amince zasu zauna dashi da Inayah sbd
zaifi nutsuwar karatun idan yasan yarsa yanzu tana tareda mutane nagari zai ringa
zuwa makaranta hankali kwance yadawo yaje aiki.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
#AYSHATOUH INAYAH#
#LOVE/ROMANCE#
[9/30, 1:43 PM] MG: *_Mamuhgee 7_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Washe gari asubar fari yatada ita suka nufi bandaki tun kafin sauran jamaar gidan
su firfito,

Fara wanke bandakin yayi tas bayan ya tsayar da ita gefen wajen bayin inda ruwan
bazai taba taba.

Yana cikin wankewar jamaar gidan Yan son banza suka fara fitowa da duhun asubar sbd
su samu sauran tsaftar Albarkacin Inayah.

Baban habiba ne agaba da qatuwar butarsa ya nufi bayin yaja ya tsaya daga gefe sbd
sanin daga Inayah har Abbin nata basa rabar mutane.,

Yana tsayuwa oga Abdul Ganiyu ya iso da nasa qatoton cikin riqeda bokiti ya tsaya
shima.

Fitowa Majeed yayi daga bayin da fitilarsa Mai tsananin haske ya kallesu Dan yasaba
ganinsu kowacce asuba sune manyan Yan jiran banza a gidan sauran Basu qarasoba
tukana.

Inayah ya kalla tareda kamo hannunta ya dan janyo daga jikin bangon datake tsaye ya
miqa Mata fitilar tareda qatuwar butarsa ta roba shikuma ya daukar Mata bucket din
ruwa suka shiga ya ajiye Mata ya fito.

Tsayawa yayi bakin kofar daga nesa kadan
Sai alokacin ya Dan kalli su bbn habiban a natse ba sauti sosai ya musu barka da
asuba.

Baki washe suka karba suna masa sannu da kokari na wanke bayin.

Suna tsaye a gurin Daya bayan daya jamaar gidan masu son amfani da bayi lokacinda
yakeda tsaftarsa suka firfito sukazo suka bi layi sbd gari na Gama wayewa kowa
yafara kaida kawo cikin mintuna ashirin bayin gidan zai masifar rikicewa a lalatasa
gabaki daya sai Mai hakurin qazantane kawai zai iya Shiga
Shiyasa da yawansu Allah Allah sikeyi siga Majeed yadawo gidan zaiyi amfani da
bayin kokuma 'yarsa zatayi shiga
Take zasu fara shirin Yana fitowa su Shiga sbd tsafta.
Hankali kwance a natse tayo wankanta da sabulunta na Dettol da soso Mai taushi tayo
alwala ta fito saida ya rakata har daki ta shige kafin yadawo ya shiga yafito yayi
alwala ya fice zuwa masallaci da har an tada sallah.

Sam babu mutum daya a gidan daya yarda dashi akan 'yarsa datake 'ya mace,
Bama gidan ba kawai ko makaranta koyaushe cikin nanatawa yaganah kular masa da ita
yake,
shiyasa qafarsa qafarta duk inda zasu sai idan yaje gun aikine tana gurin yaganah
wadda itama take taka tsan tsan da Inayan ganin Mahaifinta yanda Sam baya sake ko
Wasa da al'amarinta tako Ina.

Vaseline na Dettol dake ajiye akan qaramin tebir da kayan shafarsu da wasu daga
cikin litattafan abbinta dake Kai ta dauka tareda komawa ta zauna bakin katifarta
ta fara shafawa a natse ga sauran baccin dakecin idonta Amma dayake tafara sabawa
da tashin asuba tunda tayi wayo abbin ke tada da asuba kullum shine saukinta,
Sama sama tagama shafa Vaseline din Bai wani shafu ba sbd tasaba abbinta ke Mata
makomai yanzu ne dai take su wanka da shafa Mai da kanta tareda saka Kaya duk da
hakan haryanzu wasu lokutan shine yake saka Mata wasu kayan Idan takasa sanyawa
daidai.

Qaramin body mist dinsu ta shafa kafin ta Sanya vest da qaramin zaninta na atampa
ta saka hijab tayi sallah tana gamawa tun kafin Abbin yadawo Takoma ta kwanta sbd
bacci takeji sosai Kuma Yana shigowa karatun zai sakata suyi dan haka da wuri ta
koma baccin.

Acan masallaci ana Gama sallar yayi adhkar da adduoinsa ya fito sbd da wuri yake
dawowa Idan yafita sallah idan har yasan a daki yabarta ita kadai.

Kallonta yayi Kai tsaye Yana shigowa yaga harta koma bacci
Dan haka ya kyaleta ya dauki nasa kayan wankan ya wuce gurin wanka.
Saida yakuma wanke bayin kafin ya shiga yayo wankan ya fito yadawo daki ya shirya
fes cikin blue polo shirt da baqin wando.

Qaramin gas dinsu daya siya kwanakin ya janyo ya fito dashi kofar dakin ya kunna ya
Dora ruwan zafi.

Dakin ya dawo ya dauki Yan canjinsa dake aje kan table din dakin ya fita.

Raba mutane ya ringa Yi Yana wucewa sbd kusan kowa yatashi gidan anata hada Hada,

Masu sana'a nata hidima da kokarin hada sana'arsu akan lokaci,
Masu fita aiki da hidimar yau da kullum Suma sai kaida kawon Shirin fitar sukeyi,
Masu zaman banzan gidan qalilan ne
Daga 'yan Mata biyu masu zaman kansu suna kawo mazan dasuka ga dama sai dattijuwa
iya kande dake sana'ar zaune wato saka ido da kayan Mata saikuma baban habiba da
shima baya fita nema ko sana'ar komai sai ta saka idon shima Amma bayan su duka
jamaar gidan suna fita nema da sanaa.

Shagon kofar gidan ya Isa ya tsaya daga gefe sbd mutanen dake ciki su rage.

Mintuna uku ya dauka a gurin kafin suka Dan rage ya qarasa yayiwa Mai shagon
sallama a natse.

Cikin washe Baki hafizu Mai shago ya amsa sallamar Yana cewa"

Barka da safiya Baban Inayah
Ina kwana?antashi lfy?
Ya Inayah?
A taqaice ya amsa da kalmar

"Lafiya kalau alhmdlh"

Dari Biyar ya miqa masa yace"

Bread daya zakaban da Kwai biyu.

Cikin sauri kuwa ya hada masa abinda yace din a Leda ya miqo masa tareda sauran
canjin Yana cewa"

Mu wuni lfy baban Inayah.

Amin nagode Mal hafizu.

Ciki yadawo ya fara juye ruwan zafin a cup babba ya maida sauran ruwan ya dafa Mata
indomie da dafaffen qwai ya juye a qaramar kularta ta makaranta ya saka Mata a
basket tareda cika Mata robar ruwanta mahadin kular ya jefa Mata biscuit din
digestive daya ya ajiye gefe sai alokacin ya tada ita ta fita bakin kofar dakin
nasu tayi brush ta wanke fuska sukaje tayo fitsari tadawo tayi Shirin makaranta
suka Sha tea kafin suka fito tana biye dashi Kamar cingum yanda wasu ke kiranta
akan baban nata.

Gurinsu yagana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login