Showing 3001 words to 6000 words out of 124042 words

Chapter 2 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

373

harda tattara aikinsa yayi ya ajiye sbd
ganin sun fara samu ba laifi.

_LAGOS_
Da farko tafara Shan wuyar rayuwar garin data aikin dasukeyi sbd wani sabon hotel
ne da aka bude aka daukesu aikin Dan haka wainda basajin turanci bangaren
restaurant aka ajesu gurin harkar abinci.,

Farko ganin baa bacci kwana akeyi aiki yasa tafarajin zuciyarta tayi sanyi da
rayuwar,
Amma ana Bata albashin farko taga irin yawan kudin sai kawai ta tattara kyuya da
damuwar komai ta watsar ta zage da aiki gadan gadan.

Kasancewarta mai tsananin kokarin aiki da Amana da ladabi yasa cikin wainda aka
daukesu tare watansu biyu aka qara mata matsayi tareda dauketa daga kitchen aka
maida bangaren tsafta,
Ma'ana bangaren masu Kai abinci dakunan manyan Idan sunyi odar abinci Dan haka
kusan yanzu hutawa takeyi sosai sai anyi odar abinci taje takai.

Gidan dasuke cikin kudinsu na albashi ake Dan tsakura duk wata ana biyan haya Dan
haka hankalinta ya kwanta sosai gashi ahakan duk wata take turawa su Inna Yan canji
ta hanyar Mai pos din kusada gidan nasu data baro.

Kwanciyar hankali da hutu da Kuma nutsuwar datake samu yasa tafara sauyawa sosai
sbd abinci Mai kyau na hotel din sukeci,
Nama da kayan Dadi kala kala haka suke ci dan haka tafara sauyawa sosai,

Mama indo dai ita a bangaren abinci take har lokacin Kuma babu ranar sauyata daga
gurin sbd yanda ta iya wata irin lallausan sakwara da Amala,Eba,semo
duka dai kalolin swallow babu Wanda mama Indo Bata qwareba shiyasa saka barta
agurin Kuma itama ahakan ba qananun kudi take samuba sbd yanda suke tsananin son
aikinta.

Hutu da nutsuwar da kwanciyar hankalin data samu tareda abinci mai kyau yasa tafara
sauyawa jikinta yafara budewa da wata irin kiba,

Hasken fatarta daya jima da dafewa saigashi yafara washewa Yana dawowa,

Da farko tayi mamakin hakan Amma ganin rayuwar nutsuwar datake yasa Bata damuba
saima Jin dadin hakan datai sbd tasan inshallah yanzu zata iya samun miji tayi aure
tunda tayi kyan gani.

Ba laifi cikin qanqanin lokaci tasan mutane dakuma Yan tsirarrakun areas da streets
sbd tana fita Yar siyayyarta
Yanzu har maganin gargajiya take siya daga nan ta aikawa mama da koyaushe take fama
da jiki duk da ana cemata taji sauki din saidai yanayin muryar maman yasa ta
fahimci suna fadane kawai Dan kwantar mata da hankali.
Hakama Abdul tana Dan yimasa siyayya idan zatai Aiken ta aika musu.

Tana gab da cike shekara a sabuwar rayuwarta ta Lagos ta fahimci wani babban
alamari Mai tsananin ban tsoro da firgitarwa a tareda ita.

Bata tabbatarba Dan haka ta saka lokacin zuwa wani qaramin asibiti dake kusada
anguwar dasuke,

Ana albashi da kwana biyu ta kwasa ta nufi asibiti a dubata sbd tabbas Idan tanaji
Kuma tana fahimtar daidai motsin ciki takeji a cikinta Wanda girman daya fara yasa
ta dauka kibar datayi ce Kuma hakan Wainda take taredasu suke fada tayi qiba tayi
tumbi.

To me take Shirin ji ne?
Tsakanin kwanaki Biyar zuwa yanzu take Jin motsin sosai da juyi Wanda ta tabbarda
cikin haihuwane kawai yake Wannan motsin.
#MAMUH#
#LOVE#
#ROMANCE#
#ZAFAFABIYAR#
[9/30, 1:37 PM] MG: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


3
InnalillahiWainna ilayhirrajiun"

Shine abinda zuciyarta tafada lokacinda take zaune cikin jerin layin ganin likita
data buga sammakon zuwa.

Gyara zamanta tayi a karo na Bata lissafi sbd gabaki daya takasa nutsuwa ta aje
jikinta guri daya,
A tsananin matse take datasan asalin Menene ajikinta,

Shin wani ciwon ne yasameta?
kokuwa wata lalurarce Wannan da batasan da itaba?

Itadai a yanzu koma menene gata agaban dakin ganin likita Allah yasa taji abinda
zuciyarta zata iya dauka sbd koma wane irin ciwone atareda ita Bata tunanin Mai
saukine sbd girman motsin datake ji.

Dago Kai tayi ta Dan bude manyan fararen idanuwanta dasukai jajir da tsantsar
damuwa da fargabar fake gamutse cikin ranta da kanta
Ta kalla inyamurar data fito daga ganin likitar wadda daga ita mutum biyune ya rage
layin yazo kanta.

Bin bayan wadda ta shiga tayi harta shige kafin ta dauke kanta tana sunkuyar da
kanta gefe tareda rufe idanuwanta tana sake Jin motsin da akeyi acikin cikin nata.

Haka ta muskuta tana cigaba da zaman jira zuciyarta na cigaba da cika ta koina da
damuwa da fargabar abinda zaije yadawo har tsawon mintuna ashirin kafin aka kirata
ta miqe tareda gyara zaman qaramar Jakarta dake rataye kafadarta ta nufi kofar
dakin ganin likitan tashige tana kokarin samarwa kanta nutsuwa sbd tayiwa likita
bayanin yanayinta a matse.

Dr Adebayo A Aziz tagani rubuce a gaban farar Lab coat din dake jikinsa

Ta qaraso ta zauna jiki a sanyaye sbd taso tasamu likita Mai Jin hausa koda Yar
kadan ce sbd tasamu ya fahimci zancenta dakyau hakama itama ta fahimci abinda zai
sanar da ita da kyau.

Tanajin dan pidgin dinta data koya a zaman garin Lagos din saidai bazai isheta suyi
magana da kyauba Dan haka sai kawai jikinta yakuma sanyi ta gyara zamanta ahankali
tana dagowa ta kallesa lokacinda ya bude Baki Yana kallonta Kai tsaye yace"

Yes, what's the problem madam?

Dan rage kallonta akansa tayi cikin sanyin jiki ta bude Baki tana Kai hannu kan
cikinta da yayi tauri cikin kwanakin ta nuna masa tana harhada turancin da qyar
cikin gwamutsawa tace"

Something is moving inside my here" ta qarasa fada tana nuna masa cikinta da
hannuwanta biyu.

Is moving very very much,
But no pains,
No fever,
No anything only the movement inside here.

Idanuwansa ya Dan zuba mata tareda sakin murmushin bayanin nata.

Ya kalli cikin dakyau Yana cewa ta janye hannunta ya gani.

You said no any pains or fever?

Gyada Kai tayi tana kallon fuskarsa.

Rubuce rubuce yayi cikin file dinta kafin ya aje ya miqe tsaye.

Gadon dake dakin ya nuna mata Yana cewa tahau ta janye rigarta ya duba cikin.
Ajiye Jakarta tayi gefe tareda moqewa ta nufi gadon tahau zuciyarta na cigaba da
tsalle cikin rudani da fargaba.

Tana janye rigarta tun kafin yakai hannunsa kan cikin idanuwansa suka tabbatar masa
da cikine a jikinta Kuma tabbas inshallah zai Kai wata Biyar zuwa shida haka.

Hannu yakai yafara Danna cikin da Dan qarfi Yana examining nata aikuwa saiga cikin
Yana sake motsawa.

Kallonta yayi Yana zare Safar hannunsa yace"

Madam ciki wata nawa???

Kallonsa tayi da sauri tana kokarin Jan rigarta ta rufe cikin ta tashi zaune tana
Kuma kallonsa Kaman Bata gama fahimtar abinda yafadaba tace"

Eh??

Komawa yayi ya zauna gurin daya tashi Yana kallonta bayan itama tadawo ta zauna
yace"

Madma ciki naka wata nawa??

Girgiza Kai tayi tana kokarin Hana kanta shiga firgici sbd zancen nasa buga
kirjinta yake.

Ganin halinda take ciki take ya fahimci batasan da cikinba kokuma cikin Bata shirya
daukarsaba kokuma ma batada tabbacin na waye acikin mazan datake taredasu dan haka
rubuce rubucensa yayi yagama ya kalleta tareda miqa mata takarda yace"

Madam you are pregnant,
I mean kanada ciki zai Kai like 5mnth
Take this kaje kayi scanning ka kawo.

Wata takardar yakuma miqa mata yace"

And this one,test ne go lab zasu dauka blood naka ayi test na ciki da shauransu,
then you'll come back on Monday and bring the results to me.

Hannuwanta dake tsananin rawa takai ta karba takardun tareda miqewa tsaye ta fice
zuciyarta na wani irin azabar bugawa da nauyin gaske.

Kasa barin asibitin tayi Kai tsaye ta nufi bangaren da ake scanning ta biya ta
shiga akayo mata cikin mintuna qalilan saigata da result din ciki a hannu.

Rufewa idanuwanta sukai da wani irin tsananin duhu,

da daddafawa ta samu wata kujerar plastic dake hanyar fita asibitin ta securities
ta zube zaune hannuwanta da qafafunta sosai suka dauki wata Mummanan rawa zuciyarta
na qafewa da zallar tashin hankalin da Bata taba shigaba ko alokacin mutuwar
Salisu.

Takardar dake damqe hannunta ta Kuma dagowa ta kalla kafin takuma budewa hannuwanta
na rawa tafara bin rubutun dake ciki daki daki da idanuwanta dake mata zallar yajin
radadin Neman hawaye Amma Sam babu alamar zuwansu.

Daya bayan daya take bin kalmomin tana karantawa da 'Dan ilimin bokon datake dashi
na iya secondary.
Hawaye ne taji suna ciko idanuwanta take data Gama duba takardar,

Ko ba Dan ta karanta ba Wannan takardar da abinda ke cikinta ya tabbatar mata da
zancen likitan sbd Zak irinta wannan bayanin ne na ciki ajikin takardar dasukai
scanning tareda Salisu wancan lokacin cikin Abdul.,

Kenan da gaske ta tabbata cikine ajikinta?

Tayaya?

A Ina ya fito tunda tasani Kuma Allahn da yayita shine mafi sanin Bata taba aikata
komaiba a duniya da wani da namijin bayan salisunta.

Dama Ace shekarar data gabata ne da saitace cikintane da Salisu ya barta dashi Bai
bare ba.... InnalillahiWainna ilayhirrajiun,,

Ni hadiza wane irin Mummanan haline Wannan nashiga Wanda bansan meyake faruwaba.

Sai alokacin tafashe da wani irin Mummanan kukan mawuyacin halin datake ciki
Ga cikin sai sake motsawa yakeyi alamar Yana cikin cikakkiyar koshin lafiyarsa data
sanyashi kwanci tsawon shekara biyu sai yanzu daya samu tashi.

Kukan fitar hankali tayi tsawon lokacinda Bata saniba agurin har Saida taji
idanuwanta da fuskarta sun kumbura kafin ta iya miqewa ta kama hanyar komawa gida.

Isarta gida Bata Bari kowa ya gantaba ta shige daki ta aje Jakarta ta fito tayi
alwala Takoma dakin sallah kawai tayi ta fara rokon Allah mafita tana hawaye
Ahaka ta Gama ta miqe Takoma ta kwanta Bata Kuma fitowaba sai washer gari.

Gurin aikima datazo nokewa kawai taketa faman yi tana kame kame sbd ganin Kamar
kowa zai fahimci cikin jikinta Dan haka duk tabi tayita Jin kanta a muzance.

Tana tashi aiki Bata koma gidaba Kai tsaye gurin wani gurin scanning din daban ta
nufa takuma yi,
Shima result daya tasamu na akwai ciki.

Wani gurin takuma zuwa Shima duk daya,

Haka tayita yawon guraren scanning ana Bata result daya
Ta tattara tadawo gida hankalinta zuwa lokacin yagama barin jikinta,

Tashin hankali da tsananin tsoro takeji yanzu sbd ta tabbata takuma shaidar kanta
Idan har Wannan cikin na haihuwane bana aljanuba to wlh cikin Salisu ne ajikinta
Wanda yabarta dashi tunda tasan Bata taba ko tunanin 'da namiji ba bayan rasuwar
salisunta.

A daren kwana tayi wani irin kuka da quncin zuciya mai nauyin gaske.

Tayaya zata fuskanci duniya da ciki a jikinta?
Cikin da bai tashi fitowa ya bayyana kansaba sai data baro gaban iyayenta tazo
Lagos,
To tace me akan cikin?
Zaa yarda da itane?

Cikin qanqanin lokaci damuwa da kunci sukaiwa rayuwarta mugun baibayi,
Sam tarasa walwala da kwanciyar hankali da nutsuwarta,

Kullum cikin zullumi da tashin hankali take tashi takuma wuni acikinsa sbd ciki dai
yanzu gadan gadan fitowa yakeyi Yana girma ahankali Kaman yanda kowanne lafiyayyan
cikin keyi.

Lokaci na Ja tadain shiga mutune Sam yanzu Takoma tamkar mujiya sbd yanda cikin
yagama fitowa kowa ya ganta Kai tsaye zai shaida cikine a jikinta,

Hankalin mama Indo yayi Mummanan tashi da girman mamakin ganin Wannan alamari,

Tashin farko Bata yardaba da anata gulmar cikin Hadizar sai data tinkareta ta
ganarwa idonta ta tabbatar musamman yanda hadizar takasa hada ido da ita sai
hawayen baiqin ciki takeyi.

Babu kalar diban albarka da Rashin mutuncin da mama Indo batai mata tareda gori da
zagi kala kala karshe ma haka ta tara mata jamaa agabansu tai mata Mummanan
wulaqanci har Wanda baima Gama sanin halinda take cikiba yasani,
Take gurin aikin dama gidansu aka fara zundenta,
Masu zaginta da masu tausayinta dama wainda suke ganin ba komai bane Dan tayi
cikin,

Haka aka ringa yi da ita tun tana daurewa zuciyarta harta fara gazawa sbd babu inda
take Jin Dadi ko sassaunci alamarin duniya yataru yayi duhu,

Babbar fargabarta da tashin hankalinta Kar mama inda ta sanarwa su mama da Inna
halinda take ciki
Dan haka duk tabi ta daga hankalinta wata sabuwar damuwar da tashin hankali yakuma
shigarta.

Ahankali Ahankali lokaci yakuma tafiya Amma a rayuwar hadiza kullum da'da zurfafa
take cikin tashin hankali da damuwa da qunci take sbd rayuwa tayi mata tsanani
sosai sbd ciki kam ya tsufa sosai kowanne lokaci zata iya haihuwa,

Kullum adduarta Allah yasa ta Haifa abunda yake cikin yazo ba rai ta huta ta
tattara Takoma gida sbd bazata iya zuwa gaban iyayenta da Wannan cikin ko abinda
zata haifa barema yayyunta data San basuda imanin karbanta da abinda zataje dashi,
barinma yanzu dasuke siyasa bazasu yarda da abinda zai taba qimarsu dasuke tunanin
sunada ita a manyansu.

Wani sabon tashin hankalin ta shiga Rana tsaka da gurin aikin suka sallameta
bataredama sun jira watan yaqare anbata albashintaba.

Lokacinda taringa roqar Manager tana basa hakurin yabarta zata iya aikinta koda
cikin Amma ya rufe ido ya sallameta tareda Bata awanni akan ta tattara tabar gidan
kamfani tunda gurin aikinne suke Basu gurin zaman Dan haka Kai tsaye gida Takoma
bayan tagama ganin tonan asiri da tozarci iri iri daga gurin abokan aikinta da
jamaar hotel din.

Kuka zuwa Wannan lokacin ya 'dauke mata zuciyarta bayan radadi da tsananin qunci
babu abinda take Mata
Dan haka ta tattara kayanta da duka abubuwanta ta fito Kai tsaye ta nufi inda zata
shiga motar dazata kaita tashar da zata siya ticket din motar komawa Adamawa.

Tunda tashiga mota zuciyarta tai Mata nauyinda Bata ko iya kuka sbd dole dai Takoma
gida ta fuskanci Wannan sabuwar qaddarar data zo Mata.
Har motarsu tayi wuni guda a Tasha tana zaune guri daya sallah kawai ke tada ita
har dare yayi suna tashar Basu tashiba sai tsakiyar dare motocinsu suka tashi aka
dauki hanya.

A hanya asuba tai musu,Rana tayi musu,yamma tayi sunata Dukan hanya har wani daren
yakuma yi suka kwana ahanya sai ana gabanin asuba suka iso cikin garin Adamawa kowa
ya sauka.

Lokacin har anfara Kiran sallar asuba a masallatai da dama Dan haka dole da yawansu
suka tsaya anan tashar sukai sallar asuba ciki harda ita sbd batasan abinda zata
tadda a gidan ba gwara tayi sallar ta nema sassauci daga ubangiji dayake jarabtarta
da Wannan rayuwar.

Qarfe 5:24 mashin ya sauketa bakin kofar gidansu datai mamakin ganinsa bude lokacin
ta sauka daga kan mashin din tana miqa masa kudin data fidda daga jaka tun a hanya
sbd daga ta saka ya miqa masa ta shige gida batareda ta tsaya jamaar anguwa sun
gantaba.

babu kowa tsit anguwar sbd garin da Bai Gama haske ba
ta kinkimi qatuwar Jakarta da akwatinta harma da wasu ledojin ta nufi cikin gidan
zuciyarta na tsananta bugu duk da tayi imanin da iyayenta bazasuyi Mata zargin Zina
ba tunda sune suke tarbiyanceta Kuma sunsan halinta da abinda zata iya dama wanda
bazata iyaba koda kuwa inda yafi Lagos taje.

Ganin Sabon mashin fil a soron gidan yasata kallon kofar cikin gidan zuciyarta na
neman karaya sbd fahimtar tabbas kodai Yaya kabiru kokuma Yaya Umar ne acikin
gidan.

Siririyar shaqurarriyar sallama ta saki lokacinda ta shigo tsakiyar gidan daukeda
kayanta kamar sabuwar bokanyar datayo gudun hijira.
##MAMUH#
#LOVE#
#ROMANCE#
##INAYA A MAJEED ABBI#
[9/30, 1:38 PM] MG: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


4
Inna ce dake kokarin fitowa bandaki riqeda mama ta amsa sallamar Kai tsaye batareda
ta Gama tantance waye me sallamar sbd hankalinta gaba daya dake kan Mama data riqo
wadda ko tsayuwa Bata iya yi Dan jikinta matuqar sosai yayi tsanani a kwanakin.

Sai data fito tsakar gidan da kyau ta dago tana sake amsa sallamar da hadizar
takuma tana kallon mahaifiyarta data sauya kamanni gabaki daya sbd tsanani da
azabar ciwo.

Hawayene suka ciko idanuwanta da sukai zurfin Rama da irin kukan rayuwar datake
ciki ta dago qafafuwanta dasukai Mata sanyi da nauyi ta tunkarosu tana Dan kasa
kallon cikin idanuwansu da suka zuba Mata dukkaninsu.

Inna da qafafunta suka kusa sakewa sbd tsananin mamaki da faduwar gaba
A 'dan rude muryarta na gwamutsuwa tace"

Hadiza kece Wannan a tsaye???

Jin hakan yasa mama da Bata gane kowa sosai ta Dan sake riqe hannun innar tana bude
idanuwanta ko zata sake ganinta da kyau

Sai idanuwanta suka sauka kan tsohon cikin gaban hadizar
Ta Dan motsa kadan tana bude Baki cikin sanyin ciwo tace"

Lami?
Kasa amsawa Inna tayi sbd idanuwanta data kasa daukewa kan tsohon cikin Hadizar.

Lami?
Wace hadizar Kika ambata?
Hadizata ce tadawo?
Itace Wannan a tsaye?

wani busasshen yawu Inna ta hadiye tareda sake riqo mamar da kyau sbd hannuwanta
dataji suna sanyi da daukar rawar tashin hankali mugun ganin datai safiyar fari.

Dakyar ta qarasa da maman kofar dakinta tana kokarin kwantarwa kan shimfidar datai
Mata a wajen
Maman ta Dan janye tana waiwayowa ta kalli hadiza da har lokacin take tsaye a inda
take cikin mutuwar jiki da qamewar zuciya.

Hadiza?
Hadiza kece agurin tsaye?

Sai alokacin ta daqo qafafunta ta janyo jiki ta qaraso gaban mamar ta zube tareda
fashewa da wani irin kuka dukkanin zuciyarta na Mata wani irin radadin qunci da
damuwa da baqin ciki.

Kukanta ya tabbatarwa da maman tabbas hadiza ce kuma cikine ajikinta ta samo ta
dawo dashi.

Cikin rawar murya ta firgici Inna tace"

Hadiza cikine ajikinki?

Ba musu ba Jan dogon yanayi ta dago jajayen idanuwanta ta kasa kallon innar ta bude
Baki murya a shaqe tace"

Eh.

Hadiza Ina nufin ciki fa na haihuwa?

Kuma amsawa tayi da "eh..

Hadiza daga Lagos fa kikaxo da Wannan cikin.,

Aure kikai acan bamu saniba?

Girgiza kai tayi ahankali tareda cewa"

Aa inna,Amma wallahi tallahi......

Zubewar innace da sautin salatin Yaya Umar Mai qarfine yasa maganarta yankewa
hankali tashe ta dago tana kallonsa idanuwanta jajir.

Inna gurin mama ta nufa tana Kiran sunanta,

Aishatu?
Aishatu? Aishatu Dan Allah karki kashe kanki sbd wannan mugun abun kunyar da hadiza
tadauko,

Innalillahi Aishatu Dan Allah karki tafi ki barni banida kowa,
Malam ya tafi ya barmu ke kadai Kika rage karki tafi ki barni.

Kuka Inna ta fashe dashi tana Kiran sunan inna data jima da somewa.
Sabon tashin hankali hadiza tasamu kanta aciki
Da sauri tayi kan maman itama tana kiran sunanta cikin mummunan mawuyacin hali sbd
ita kanta tanaji batada lafiya.

Wani Mummanan Marin Rashin Imani da baqin ciki Umar ya sauke Mata lokaci daya Yana
kallonta a qazance ransa a matuqar bace yace"

Karki kuskura ki tabata,
Shekara kusan biyu kena bakya gida
Bakizo musu da kudin dakikaje nemaba sai tsohon cikin banza¿

Gashinan Zaki kasheta lokaci daya da baqin ciki,

Tashi na daina ganinki wlh kafin na illataki daga ke har abin banzan da kike dauke
dashi.

Yanda yayi maganar a tsananin fushi da bacin Rai har Yana sake yowa Kanta yasata
Jan jiki tayi can gefe tana wani irin kukan zuci Mara sauti.

Kwasar mamar sukayi sukai cikin daki da ita sai firfita Inna ke Mata tana kuka
Wanda yake na firgici da tsoron halinda Aishatun zata shiga dakuma zallar baqin
cikin al'amarin da hadizar take tafe dashi.

Duk dubarunsu da ruwa dasuka ringa shafa Mata Bai saka ta farfafo saima qarasa
rikicewa sosai da jikin yayi gabaki daya.

Hankalinsu duka yatashi Dan haka dole Yaya Umar din ya fidda waya yakira Yaya
kabiru,
Shima rabon zaai gabansa ne yasashi zuwa gidan tunda asuba sbd ruwan da aka kwana
ana zubawa yasashi tunanin gininsa da akeyi acikin gidan da baa kammalaba Wanda
yasa ai masa daki daya da bandaki
amarya yakeson yi to anan zai kawota ya gwamutsa cikinsu innar.

Koda Yaya kabirun ya iso tuni innar tayi nisa Amma basuyi yunqurin kaita asibiti ba
saima wani sabon tashin hankalin daya barke tsakaninsu sbd ganin hadiza ce silar
koma meya samu mamar.

Kabiru buga rantsuwa yayi akan wallahi saita bar gidan da cikin,
Bazasu taba barinta ta zaunaba a gidan baqin cikin rainon ciki da goyon shege ya
kashesu mama
hakama bazasu yarda ta Bata musu sunan dasukai gwagwarmayar samarwa kansuba
lokacinda take Lagos tana zubarda mutuncinta da qimartaba.

Yaya Umar dinma bayan kabirun yabi akan Takoma inda tafito da cikin.

Rokonsu takeyi tana wani irin kukan tausayi da tsananin quncin datake ciki akan su
yarda da ita Bata taba aikata Zina ba Amma Sam babu Wanda ya saurareta saima qara
harzuqa dasukeyi da tsananin fushi da bacin rai,Yaya Umar Dukan mutuwa yakeson yi
Mata Amma Inna dake kuka sosai ta Hana ta riqesa tana bayyanarda nata fishin itama.

Riqonsu tadawo yi akan su fito da mama akaita asibiti
Nan ne Umar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login