Showing 42001 words to 45000 words out of 124042 words
akai Mata masu
tsananin sanyin qamshi da shiga zuciya.
Kallo daya Abbi yayi Mata yaga yanda daga ita har Abdul din suke kallon juna yaji
mamakin gaske yana kamasa ta yanda Inayah duk ta lalace har haka baida sani.
Ahankali ya dauke Kai daga kallonsu tareda gyara murya yana Kiran sunan Inayah din
a natse.
Cikin nutsuwa da girmamawa tace"
Yes,
Good morning Abbi.
Qarasowa tayi tareda dauke kallonta daga kan heart din tana Zama kusada Abbinta
tasake gaidasa.
Amsawa yayi tareda Dan kallonta yace"
Hafsat tasan kinzo Nan?
Murmushi tayi tana girgiza Kai da cewa"
Abbi Bata saniba banaso ta sani please.
Da mamaki ya Dan kalleta sbd yasan hakan bai kamataba Musamman yanzu irin yanda
yaga suna maitar kallon juna bayason ko kadan shedan ya Shiga zukatansu Koda
rungumace suyi kafin aurensu tunda daga yau ne sai gobe jibi zaa daura auren Dan
haka ya Dan kame fuska a kame yace"
Ok ku gaisa ki koma ciki zanyi magana dashi.
Bata fuska take Neman yi ta marairaicewa abbin Amma ganin ba wannan damar yasata
kallon Abdul daya Gama mutuwar zaune gurin satar kallonta ta gaishesa a gutsure.
Amsawa yayi batareda ya kalleta sosaiba tunda Abbi na gurin
Badan sun soba su duka haka ta juya Takoma Inda ta fito.
Shima Bai wani gane sauran zantukansa da Abbin ba sama sama ya gane yayi Masa
sallama ya wuce.
Jiki mace akai Mata zanen kunshin sbd rashin ganawa dakyau da heart dinta.
Sai kusan yamma daya kirata yasamu yasaka zuciyarta da ranta ya sake suka Dan zanta
a wayar kafin ta aje tashiga wanka sbd anmata dilkan yamma again.
Washe gari Koda ta tashi da murnar sauran kwana daya ta tashi hakama da damuwar
rabuwa da Abbinta Dan haka ta ringa samun sauyin yanayi aranar,
Tayi farin ciki tashiga damuwa ahaka dai yamma tayi duk saitaji tashiga damuwar
tunda gobene Zata bar gidan gashi har yamma tayi Babu abinda ya rage a wunin yawuce
sai kawai ta fashe musu da kuka.
Bata taba tunanin halinda Zata shigana ranarda Zata rabu da mahaifinta sai yau
Musamman idan ta tuna da Heart dinta Dan Adamawa ne can zasu tafi da ita bazata
sake Zama gurin Abbinta ba
Tsorone Mai girma ke Neman cika zuciyarta sbd duk Inda Zata tafi jinta safe cikin
nutsuwa da kwanciyar hankali agurin mahaifinta.
Tun su anty Hafsat na Mata dariya hardai suka fuskanci da gaske takeyi hankalinta
ya tashi matuqa a tsorace take.
Umma yaganah ma jikinta duk yayi sanyi Musamman itama datai wata irin sabo da
shaquwa da Inayah din tun jarinta.
Heart dinta hankalinsa ya tashi da kukan nata sbd kowa yayi yayi taqiyin shiru
shiyasa anty Hafsat tafada Masa kozai iya zuwa ya lallashi Inayah din
Itama umma yaganah takira Abbi tafada Masa Inayah fa tana nan tana zabga kukan
bazata iya zuwa Inda Batasan kowaba ta rabu da mahaifinta.
Cewa yayi idan yagama magana da baqinsa dasuka iso Lagos domin daurin auren goben
zai iso gidan.
Dr Abdulsamad Yana tareda mahaifiyarsa da qannan babansa biyu Mata sai 'yayan
yayyun mahaifiyar tasa biyu suma Koda anty Hafsat me Masa wannan bayanin.
Kallon umman yayi yace"
Umma Bari naje gidan Inayah ce tanata kuka wai bazata iya zuwa garinda batasan
kowaba.
Murmushi umman tayi cikeda mamakin shirme irin na Inayah
Gata ta girma dai Amma gata yasa yarinyar kasa nuna ta girma.
Wayarta dake gefenta ta dauka tana cewa"
Kaga bara natashi muje tare sbd dama yakamata da muka iso munje gidan an gaisa
kafin goben ranar biki muje gidan,
Kaga dama abinda yasa nazo da kaina kenan sbd Inayah din tasake tasan muna kaunarta
sosai
Nice zan karbeta da hannuna Inshallah cikin Amana bazamu Bari tayi kukan baro
gidaba.
Gaba yayi Yana cewa"
Okay umma saikin fito to.
Bayan fitarsa tsadadden mayafinta dake ajiye ta dauka tareda LV handbag dinta ta
nufi kofa tana cewa"
Nafisat zo muje Naga kece a shirye da alama su Asmau akwai sauran gajiya atare dasu
kaman wainda sukai tafiyar mota bayan jirgi kuka biyo.
Ficewa suke kokarin Yi yayar mahaifin Dr Abdul dake sallah tana idarwa cikin Dan
daga murya tace"
HADIZAH.
cak umman ta tsaya tareda waiwayo tace"
Na'am.
###MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/16, 3:29 PM] MG: *_26_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ku jirani a motar Bara na sauya Kaya muje Nima zan gaisa da iyayen na Inayah tunda
dai kaman yanda kikace din yakamata muje a gaisa basai gobe bayan daurin aurenba
muje.
Ok Tom muna jiranki a motar.
Juyawa tayi ta fice daga babban dakin ta ratsa palon zuwa babban palon gidan na
mijinta Wanda Sam basa Zama anan tunda aikinsa na soja ya maidasa Abuja ita saita
koma Adamawa sbd uwar gidantace a Abuja ita Kuma a Lagos to ana Masa transfer zuwa
Abuja tabar Lagos Takoma babban gidansa dake adamawa.
Tana Isa motar Haj balaraba na isowa Dan haka sai kawai suka shiga suka wuce zuwa
gidansu Inayah din.
Tafiyar mintuna sukayi suka iso lafiyayyar anguwar ta masu abun duniya.
Kai tsaye security ya budewa Abdulsamad din gate Yana daga murya da cewa"
Welcome Sir.
Yauwa thank you Bosco.
Parking yayi tareda kashe motar suka firfito su umman na sake yaba arzikinsu Inayah
din Dan kuwa gidan irin tsarin ginin turai ne komai ma kusan yanda Inayah takeso
akayisa.
Kai tsaye hanyar kofar palon cikin gida ya nufa dasu
Sbd su din Bai kamata yabi ta hanyar palon Abbi dasuba.
Suna Isa kofa Safnah na fitowa da waya a hannunta tanayi ganinsu yasata katse wayar
Dan nuna girmamawa gasu umman Abdul din dasuke manyan Mata sosai.
Cikin sakewar fuska da girmamawa tafara musu sannu da zuwa tana gaidasu.
Juyawa tayi tai musu jagora zuwa can qurya palonda kowa yake Anata fama da Inayah
din.
Tsokar Abdulsamad tayi da cewa"
Yanzu sbd heart din taka ka tado su umma da magribar fari Dan azo a rarrasheta.
Dariya yayi yana cewa"
Safnah harda ku kuka sake rudar mun da ita gskia
Amma haka kawai baby bazata fara kukan Nan ba.
Shi a palo ya zauna Yana amsa waya sukuma su umma palon ciki tayi dasu.
Su umma yaganah dasu Mimi na ganinsu cikeda farin ciki da mutuntawa suka tarbesu
suna musu sannu da zuwa a waye.
Mahaifiyar Abdulsamad hadiza babbar mace ce Mai tattare da Kamala da mutunci sosai
Kuma a bayyane ta nuna kaunarta da kulawarta ga Inayah.
Drinks da snacks zubbi da Salimat suketa aikin kawo musu Anata sake musu sannu da
zuwa.
Cikin Jin Dadi da farin cikin yanda aka karbesu hannu bibbiyu da mutuntawa suketa
amsawa suna sake yaba gatan da Inayah take dashi Dan duk Wanda is kalla yanayinsa a
gidan zaka tabbatarda yanda yake kaunarta tunda kusan duk albarkacinta kowa keci
acikinsu adai cikin gidan da rayuwar AA MAJEED.
Da 'yar Raha umma yaganah tace"
Kuna fama da gajiyar tafiya Rigimar Inayah ta fiddoku,
Shima Abdul din dabai daukokuba ai yabari Kun huta shegantaka ne kawai irin na
Inayah Zata fara kukan barin gida tun yanzu
Ai tabari har zuwa goben idan andaura aure.
Yar dariya Haj balaraba tayi tana cewa"
Ai Dole zatayi kuka tun yanzu sbd auren nesa na gida Daman sai kaji kaman shikenan
katafi.
Umma Hadiza kuwa Inayah data fito daga bedroom sanye cikin Riga da skirt na soft
embroidery Swiss Mai kyau da tsada navy blue ta zuba Mata Ido gabaki daya tana
kallonta.
Duk hotunan Inayah da vidcall dasuke ganinta idan Abdulsamad na gida basu bayyanar
Mata da kamannin Inayah ba kaman yanzu datake ganinta a gabanta.
Da farko zuciyarta harbawa tayi da kyawun fuska Dana jikin Inayah hartana Jin Anya
Abdulsamad bazai bartaba akan matarsa Inayah bayan auren
To Amma Kuma zuciyarta tarigada ta kamu da kaunar Inayah tun kafin auren sbd son da
Abdulsamad ke Mata to yanzuma data ganta saitaji kaunarta Mai nutsuwa da tsafta
takuma shigarta.
A natse Inayah ta qaraso Inda suke fuskarta duk yayi ja sbd har lokacin hawaye
takeyi sosai Musamman ganinsu umma Hadiza sai taji kaman sunzo tafiya da itane
gabaki daya zatabar gida.
Cikin farin ciki da kulawa tareda murmushi a fuska umma Hadiza ta kamo hannunta ta
zaunar da ita a gefenta tana cewa"
Zo ki zauna 'yata Inayah kinji,
Ki daina kuka sbd inshallah bazamu taba Bari kiyi kewansu umma da Abbinki ba sosai
Dan zamuyita tattalinki muma kaman yanda suke Inshallah.
Ba kunya Inayah ta dago ta kalli umma Hadiza alamar da gaske kike fada.
Da sauri umma da Anty Hafsat suka dungure Mata kan suna cewa"
Inayah wai bazakiyi hankaliba ko??
Su umma Hadiza da haj balaraba kuwa dariya suka sake atare harma dasu Neesah
Haj balaraba na cewa"
Eh Inayah Inshallah bazakiyi kukan shigowa zuriar muba da yardar Allah,
Barema wannan ja'irin Abdulsamad duk Wanda ya damar Masa Mata Inayah ai nasan
zaburewa zaiyi da rashin arziki kala kala
Shima Kinga muna kaunarsa sosai Dan haka bazamu Bari matarsa ta Shiga damuwar
dashima zai shigaba.
Washe Baki su umma yaganah suka hau Yi suna Jin dadin sirikan da Inayah tasamu masu
kaunarta.
Murya a sanyaye Inayah ta bude Baki cikin girmamawa ta gaidasu tana Dan sake goge
hawayenta.
Inayah daina kukan kinji Inshallah Baki rabu da gida ba duk lokacinda kikaso gida
zakizo ki gansu
Kuma kin manta Anan Abdulsamad din yake aiki ne?
Bawani dadewa zakuyi a Adamawanba zaku dawo Lagos mune ma zamu ringa zuwa dubaku
basaikunyi wahalar zuwanba.
Ahankali Inayah ta saki Dan siririn murmushi tana kallon su Anty Hafsat dake Mata
dariya.
Da Raha Haj balaraba tasake cewa"
Inayah akwai sauran kuruciya kam,
Gaki 'yar fari shiyasa aketa shagwaba ko?
Nikam ma menene Ma'anar sunan Inayah Dan naji sunan shima na Yan shagwaba.
Dariya sukai saidai anty Hafsat ce tace"
Ma'anar sunan Inayah shine kyauta daga Allah,
Kaman ace kyautar datazo wadda bayan Allah Babu Mai iya baka ita.
Dukkaninsu murmushi sukai ana cigaba da Dan sake maganganu cikin Raha da mutuntawa
har lokacin sallah yafara wucewa Dole suka tashi Dan gabatar da sallah.
A dakin umma yaganah aka Kai su umma Hadizan suyi sallah sai alokacin Inayah tasamu
ta Isa Palo gurin Heart dinta.
Yana ganinta ya taso a natse tareda miqa hannunsa ahankali ya kamo nata hannun suka
Isa kujera suka zauna Yana kallon fuskarta datai ja cikin damuwa da kulawa sosai
yace"
Baby sosai kikai kuka haka?
Oh my God,why baby?
Wasu hawayen takuma gangaro Masa tana sake narkar Masa da fuska tace"
Heart Dan Allah karmu dade Adamawa da yawa mudawo Lagos da wuri.
Numfashi ya sauke Yana goge mata hawayenta da tissue din dake palon cikin kulawa
kaman ya janyota ya rungumo yace"
Baby ki daina hawaye da damuwa please,
Idan Dan zakibar gidane na miki alqawarin bazamu dauki lokaciba zamu dawo okay?
Gyada Masa Kai tayi tana tsayar da hawayenta.
Lallabata yayi takoma ciki Dan yin sallah shima ya fice zuwa qaramin masallacin
dake gefen gidan yayo sallah Yana dawowa yace su umma su fito ya maidasu gida akwai
baqinsa dasuka iso daga Adamawa yau Dan daurin aure zai samesu a hotels din dasuka
sassauka su gaisa friends dinsane sosai.
Yana harabar gidan jikin motarsa Yana jiransu saiga motar Abbi tashigo yadawo
shima.
Su umma Hadizan ne suka fito tareda su Anty Hafsat da Mimi dasuka rakosu harma da
Inayah dake maqale gefen Haj balaraba tana sake rarrashinta cikin kauna da kulawa.
Cikin maroon luxury motar Bentley bentayga yadawo gidan Dan haka suna ganin motar
duk suka tsaya Dan gaidashi dakuma su umma Hadizan ma su gaisa tunda yariga yadawo.
Cikin wani Sky blue tsadaddiyar soft Italian cashmere a jikinsa ya fito
Fuskarsa fresh a kamile.
Kyakkyawar fuskarsa ya juyo da ita ya kalli Inda suke gabaki dayansu sun tsaya suna
jiran fitowarsa daga motar a girmame.
Hasken fatarsa da dogon hancin zuwa haiba da kwarjini Mai yawa da Allah yayi Masa
yasa dukkaninsu Babu Mai iya Masa kallon quru quru saidai a gaisa kana Dan sauke
Kai a mutunce.
Inayah ce tabar gefen Haj balaraba ta nufesa tana kallonsa cikin kulawa tace"
Abbi barka da dawowa.
Wani nutsatsen murmushi ya sakar Mata Yana amsawa Kai tsaye da kallon fuskarta
datai ja sbd kuka a natse cikin lafazinsa masu nutsuwa yace"
Duk kukan da kikaita yine wannan?
Bata fuska tayi zatai magana anty have ta Dan qaraso kadan tana Masa sannu da zuwa
cikin girmamawa tace"
Sirikan Inayah dinne wato mahaifiyar Abdulsamad sukazo tareda yayar mahaifinsa zasu
tafi ko zaku gaisa.
Ok ba damuwa"
Ya furta tareda qarasa tahowa cikin nutsuwa Inayah din na gefensa kaman Zata maqale
Masa.
Tunda suka doso su kowa ya sake Dan kame kansa suna rage kallonsu akansa sbd kam
badai cika Ido da zallar haiba ba.
Umma Hadiza datai Masa kallo daya taga fuskar kaman wadda ta sani Dan haka ita bata
dauke idonta akansaba taci gaba da bude idanuwanta dakyau akansa.
Dan juyawa kanta yayi kadan sbd toshewar Dan qwaqwalwanta ke Neman Yi gabaki daya
da kamannin nasa.
Baya wani kallon Mata Musamman su din dayaga ba laifi dattijai ne Dan haka a
mutunce ya gaisa dasu ya kalli Abdulsamad dake nuna umma Hadiza yace"
Sir wannan itace mahaifiyar tawa.
Dan sake fuska Abbin yayi kadan tareda kallon umma Hadizan a natse yace"
Barka da zuwa Haj,
Ya hanya?
Allah ya hutarda gajiya......
Tsit yayi bayan yasamu yakai qarshen gaisuwar a Dan rarrabe.
Kallon fuskarta yakeyi dakyau cikin Dan basarwa sbd danne duk wani Abu dayake
yunquro Masa cikin Rai.
Mummunan bugawa Mai qarfi zuciyarsa tayi wadda bayajin yataba samun wannan bugawar.
Sam Bai nuna halinda yashigaba saima juyawa da yayi ya wuce ciki Yana musu a sauka
lafiya.
Mutuwar tsayece da daukewar hankali na daqiqu agurin ya Kama Hadiza Saida Haj
balaraba ta Dan girgizata tana ambatar sunanta.
Kasa motsi tayi sai kawai sukaga tana neman zubewa sbd duhun dayake Neman rufe
idonta da qyar ta iya bude Baki murya a hargitse ta furta"
BP Dina ya hau sosai please ku kaini gida Nasha magani bana gani sosai.
Hankali tashe Haj balaraba da Abdulsamad din suka kamata ta shiga mota dukkanin
jikinta na rawa a rude sukabar gidan.
Da tausayin umma Hadizan su Inayah suka koma cikin gida Bata tsaya komaiba ta nufi
sashen mahaifinta.
Zaune yake numfashinsa na Dan fita da sauri
Qananun zufa na tsatsafo Masa a goshi da alama Yana Jan numfashi ne dake Neman
qwace Masa da qyar.
Da gudu tayo kansa tana Kiran sunansa hankali tashe da firgici Dan Bata taba
ganinsa hakaba.
Bai dago ya kalletaba ya karba tissue din datake goge Masa zufa
Ya Dan kame kansa Yana kokarin basarwa a hankali yace"
Ya Isa haka, I'm okay kije
Kawai.
No Abbi bakada lfy
Kana gumi fa.
Ahankali ya furta"
I think my BP dropped.
Wat?" Tafada da sauri tana kallon yanayinsa.
Juyawa tayi da sauri tana cewa"
Bara naduba.
BP monitoring machine harma dasu sphygmomanometer ta dauko da sauri tadawo cikin
damuwa sosai.
A tsaye ta taddasa kaman ba Wanda tabari Yana Dan hada gumi ba da jajayen Ido.
Da mamaki ta tsaya da Kaya a hannunta tana kallonsa cikin mamaki da kulawa tace"
Abbi?
Magana zatai ya Dan waiwayo ya kalleta a Dan kame yace"
Kibarshi kawai ya wuce
Zanyi baqi yanzu ki koma ciki.
Kallonsa tayi a marairaice da fuska Zata Kira sunansa da 'dan daga murya yace"
Nace kije Inayah.
Hawayen tashin hankali da tsoro taji suna Shirin gangaro Mata sbd yaune karon farko
da Abbi yayi Mata tsawa tunda dai ta girma tasan kanta.
##MAMUH#
#AYSHATOUH MRS AA MAJEED
#LOVE/ROMANCE/MARRIAGE
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/16, 5:48 PM] MG: *_27_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Kasa riqe hawayenta tayi suka gangaro Mata ta juya a sanyaye tana Satan kallonsa
Zata fice ya sauke wani boyayyan numfashi tareda ajiyar zuciya Mai tafe da hucin
zafin da Kai da kirjinsa suka dauka a natse Yana sake kame kansa da basar da
yanayin dayake ciki ya bude Baki yakira sunanta a natse.
Da sauri ta juyo ta dawo Dan dama bason tafiyar takeyiba ta kallesa tana share
hawayenta tace"
Na'am Abbi.
Sake sauke ajiyar zuciya yayi wannan karon kansa na qara daukan zafi Mai tsanani
kawai dannewa yakeyi Yana basarwa kada hankalin 'yarsa ya tashi babban burinsa a
yanzu ya karkata akan baya kauna ko kadan bare fatan wani illa yazo ya gifta a
cikin auren Nan da zaa daura gobe dan kuwa wannan karon aka fasa auren 'yarsa Allah
ne kawai zai Raya Masa ita sbd gargadin da likitanta yabasu akan sake shigarta
tashin hankali.,
Komai zai iya faruwa da ita idan takuma shiga wani mummunan shock na tashin
hankali,
Ganin wannan matar ya girgiza kansa da tun tsawon shekaru masu tsayi kan ya bushe,
Ganin mahaifiyar Abdulsamad babbar masiface tabbas Zata bayyana Dan kuwa idan itace
mahaifiyar Abdulsamad akwai gagarumar matsala.
Meyake Shirin faruwa da 'yarsa idan komai ya lalace a daidai wannan gabar?
Sake Kiran sunansa Inayah tayi cikin sanyin murya ganin yanda yayi shiru kaman Yana
nazarin wani abun.
Waiwayowa yayi ya kalleta da fuskar kulawa yace"
Kukan barin gidan ya isa haka Inayah,
Idan kina wannan kukan zan daga auren zuwa nxt month saiki sake cire kewan gida da
kyau.
Murmushi tayi tana share hawayenta tace"
Na Dena kukan Abbi.
Wani murmushin Dole ya saki Yana sake boye damuwarsa yayi maga Yan maganganun
dasuka sanyata sakewa sai gata tana dariya Wanda shikuma hakan yasake caza kansa
akan abinda zai iya zuwa ya komo.
Lokacin sallar ishai dayayine yasanta ficewa daga palon Abbin Takoma.
Tana fita ya sauke wata nutsatsiyar ajiyar zuciya idanuwansa na neman sauyawa.
Miqewa yayi ya fice zuwa masallacin gidansa sallar ishai.
Ana Gama sallar yadawo ya rufe sashensa ya zauna Dan tattara abinda yake yawo cikin
kansa Yana Neman juyawa.
Dafe gashi yayi Yana Jin gaban kansa kaman zaiyi bindiga tsabar nauyi da zafin daya
dauka.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Meyesa wannan matar da Baya fatan sake ganin fuskarta har abada Zata bayyana
rayuwarsa da 'yarsa a daidai wannan lokacin Kuma ta bullo ta mabulla mafi firgici
da tashin hankali.
Tun a shekarun baya tsanarta ta ginu cikin ransa tsanarda tasa ya rufe shafinta ruf
daga rayuwarsa gabaki daya Dan ko a kamanni baya fatan sake ganin Mai kamarta,
Shin ita dince ma kuwa wadda yake tunani kokuwa?
Bazai taba manta kamannintaba sbd itace ta taka mahimmiyar rawa gurin ruguza
rayuwarsa a karon farko,
Itace wadda ta wargaza buri da gatansa na zama cikin iyaye da 'yan uwansa tasakashi
a matsatsen hali mafi matsuwa da Muni.
Kamanninta Zane suke da baqin alqalami a idanuwansa,
'yarsa Inayah da girman mahimmancinta da qauna Mai tsanani ta uba da 'ya dayake
Mata yasa ya yafewa matar Nan Amma Kuma har abada bayajin zai iya cire tsanarta Mai
girma a ransa bare kallonta da daraja ko qima.
Haduwarsu ta farko da ita Bata Zama Alkhairi ba Dan hakan ko yanzu yasan
bayyanuwarta rayuwarsa ba Alkhairi bane a rayuwarsa data 'yarsa Dan haka Dole
yanason Jin amsa biyu rak daga bakinta daga ya samu amsoshinsu bazata Kuma
ganinsaba dagashi har 'yarsa har abada.
Shi idan Yana cikin damuwa ko tashin hankali Sam baa wani ganewa sbd alokacin
nutsuwarsa da kamewarsa take fin yawa,
Shiru yakeyi Yana nazari batareda buqatan hayaniya ko katse Masa nazariba shiyasa
su Inayah dasun gansa irin yanayin suke yin tsit gidan duk da dama ba hayaniya ce
dasuba gidansu.
*******Qarfe goma da mintuna Ashirin ya fito harabar gidan sanye da black hoodie
Thom Browne Riga da wando masu kauri ya nufa White jaguar motarsa ya bude ya shiga
tareda tada motar ya nufi gate dama tuni Bosco yaga fitowarsa da sauri ya bude Masa
gate ya fice.
Yana fitowa daga street din gidansa motar Abdulsamad Tasha hanasa tareda danno Masa
full light.
Wani banzan numfashi ya saki tareda Dan juyar da kansa cikin takaici da baqin ciki
ahankali yace"
Wannan matar tabbas zatasan waye AA MAJEED.
Babu tantama yasan itace a motar Abdulsamad din
Itama Babu