Showing 12001 words to 15000 words out of 124042 words

Chapter 5 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

76

suka nufa Dan gaisawa dasu kafin ya wuce Dan haryanzu baya Bari
yagana ta wuce masa da ita kullum safiya saiya kaita yake wucewa aikinsa saidai suk
hade can.

Cikin yanayi suka samu su yaganar sbd jikin malam din daya tashi jikin dare da
zazzabi ya kwana Mai qarfi.

Cikin kulawa yai masa ya jiki kafin ya ciro dubu daya ya miqa Mata yace"

Yaganah ki kokarta asamo adaidaita saiki kaisa asibitin Zan Kai INAYAH makaranta
daga can Zan biya gurin aikin saina bada uzurinda Zan sameku asibitin muga abinda
Allah zaiyi.

Karba tayi cikeda godia jikinta duk a mace da yanayin malam din sbd ko magana
bayason yi Kai kawai yake gyadawa Majeed din alamar godiya.

Fita sukayi Yana riqeda hannun Inayar suka nufi makaranta Saida suka qarasa bakin
kofar makarantar ta juyo tana kallonsa fuska a Dan shagwabe ta bude madaidaicin
bakinta tace"

Abbi Idan kaje asibiti taredasu Umma yaganah waye zaizo ya tafi Dani Idan an tashi?
Na tafi na da kaina abbi Zan iya.

Fararen idanuwansa ya saukar Mata a 'dan bude yace"

Koba yau ba duk ranar Dana samu kin fita kinbi hanya da kanki zakisan Hukuncin
dazan dauka akanki,

Kina kina?
Gyada Kai tayi tareda sake cewa"

To Abbi na zaunane nayita jira har kazo?
Umma yagana Bata makaranta Idan antashi zanji tsoro aka barni,
Kazo da wuri kaji Abbi???
Gyara Mata zaman hijabinta yayi Yana gyada Kai cikeda kulawa yace"

Kidai jirani kinji abinda na fada,
Wuce karkiyi latti,
Allah ya bada saa.

Amin Abbi.

Juyawa tayi ta shige ciki shikuma ya juya ya tara mashin ya hau ya nufi gurin aiki
Kai tsaye.

Bai wani jimaba gurin aikin ya bayyanarwa da manager uzurinsa ya fito ya kama
hanyar asibiti sbd Yagana ta sanar masa suna Isa anbasu gado.

Koda ya Isa asibitin jikin malam din yaqara tsanani sosai Kamar Kar a iso dan haka
ya karba takardun magani da abubuwan da aka rubutan.

Ba wasu kudaden ne dashiba shima Amma haka ya tafi gurin siyan maganin Dan yaji ko
nawane kudin.

Ana Gama duba takardar a pharmacy aka miqo masa kudin a rubuce.

Dubu talatin harda shida da wata dari takwas akai yagani rubuce.

Ajiyar zuciya tareda numfashi ya sauke a hankali tareda kallon Mai shagon a hankali
ya furta"

Nagode" ya juya ya wuce yabar gurin.

Bayada ko dubu goma a halin yanzu Dan kuwa duka duka dubu shida ce a account dinsa
Kuma koshi kansa baya tabata Dan na siyayyar Inayah ne na abincin zuwa makaranta
daya kusa qarewa.

Kallo takardar ya Kuma yi tareda sake lumshe fararen idanuwansa cikin tsananin
tausayin malam din da yaganah.

A iya fahimta da Dan sanin da yayi musu yasan basuda kowa sai junansu,
Yasan dai Yan asalin jahar borno ne suna cikin Wainda sukayo gudun hijira tunda
dadewa dangi da sauran Yan uwa duk sun mutu wasu Kuma Suma sun fada wata duniyar
suna ganin garari.

Fuskarsa ya shafa ahankali kafin ya juya ya nufa titi Dan hawa mashin yakoma gurin
aikinsa ya gwada rokon manager albashinsa na Wannan watan idan zai samu yanzu koba
komai saura sati daya watan ya qare.

Kokarin tare mashin yake Yar qaramar wayarsa ta Itel ta ringa vibrating sbd ya
kashe qararta bayaso.

Ciro wayar yayi daga aljihu yaga sunan yaganah ya dauka Yana cewa"

Assalamualaikum" cikin nutsuwar muryarsa Kamar kodayaushe.

Wata sanyayyar ajiyar zuciya Mai zafi tareda mutuwar jiki yaganan ta sauke kafin
tace"

Abdulmajeed kadawo kawai malam yariga ya tafi lokaci yayi...
Wani irin kuka Mai sanyi ta fashe dashi tareda kashe wayar sbd sai alokacin kukan
ya zo Mata.
Innalillahi wainna ilayhirrajiun" ya furta Yana maida wayar aljihu ya tsallaka
titin yakoma cikin asibitin Yana jinjina Kai cikin jimamin mutuwar.

Kuka sosai Yaganah keyi daqyar ya iya furta Mata kalmomin ban hakuri da tawakkali
dazai iya furtawa shima.

Basuda wani jamaa dagashi har ita yaganar har malam din Dan haka babu maganar
tsayawa Jan lokacin jana'iza
Asibiti na Gama nasu aikin suka Basu gawar suka dawo gida da ita.

Sosai jamaar gidan Dana anguwa suka nuna alhininsu akai masa sitira aka kaisa.

Bai samu zuwa maqabarta ba sbd gabaki daya hankalinsa daya rabu biyu Yana kan
Inayah da aka tadasu makaranta lokacin Dan haka makarantar ya wuce Kai tsaye ya
daukota suka dawo gidan yabarta gurin yagana yabi sauran Wainda zasu maqabartar
suka wuce.

Babu wani zaman karban gaisuwa dasukai saidai Wanda yazo yaje har kofar dakin
yagana yayi Mata gaisuwa ya wuce sun daiyi Mata tasu karar sun zauna ranar daya
rasun daga ranar saidai masu zuwa jefi jefi har akai sati biyu.

Tunda akai rasuwar babu ranarda Inayah Bata fashin makaranta zai kaita da kansa ya
wuce aiki
Idan lokacin tashi yayi zai Baro gurin aikinsa ya rakota gida kafin ya koma.

Wani sabon Nauyin ne yakuma hawa kansa na Yaganah sbd kallok uwa dayake Mata gakuma
tausayin halinda take ciki din na Rashin miji,Dan uwa,abokin fira,abokin rayuwa
Wanda suke tare tun kuruciya gashi ko tashin hankalin daya sakosu gudun hijira Bai
rabasuba sai yanzu da Mai gaba daya tazo wato mutuwa.

Sbd matsayin Yaganah agun Inayah yasa Dole ya dauki nauyinta ya ratayawa kansa Dan
haka yanzu komai nasu tareda ita yake siya sbd ko aikin ta daina zuwa Dole sbd
takaba,

Ta wani bangaren Kuma mutuwar ta tabata sosai Dan komai ya fice Mata arai
Daqyar Inayah ke samu tana dan sakata magana wasu lokutan.

Rasuwar tasa Dole yakoma ya saki gidan daya kama ya karba kudinsa kafin Yaganah ta
Gama zaman takaba zai nema musu wani Mai Yar damar Inshallah.
Dan haka kudin saiya tattara ya hada ya siya musu abinci isasshe da siyayyar
makarantar Inayah suka shiga jss 1.

Watan malam din shida cif da rasuwa sukabar gidan suka koma sabon qaramin gidan
daya kama din Wanda yamafi na farkon kusa da gurin aikin nasa,

Dakuna biyu ne a gidan da qaramin toilet harda broken tiles dinsa.

Daki daya ya dauka
Dayan Kuma haka Dole dai yaganah da Inayah suka zauna daki daya Amma wasu kayan
nata na dakin baban nata sbd sabo.

Katifar Inayah ta farko ya dauka sai ya siya musu wata Yar katifar Mai Dan girma
tareda zanin gado da pillow sbd sanin Inayah da bacci da pillow.

Labulai ma ba laifi ya Samar musu iya daidai nasu sai kayan aikin abinci da kusan
duk nasun ne na da.

Ahaka cikin Dan rufin asirinsu suka fara gudanar da rayuwarsu a sabon guri cikin
nutsuwa.
Bayan tarewarsu anguwar Basu wani dauki dogon lokaci sosaiba Yan anguwar Suma suka
gane halayensa na Rashin shiga mutane da kamewar Kai dan haka suke mutuntasa duk da
zamansa matashi ba wani babba ba.

Kwarjinsa hadi da Kamun kansa da Rashin shigewa al'amuran jamaa musamman wainda
Basu shafesaba yasa duk inda ya zauna ake mutuntasa sbd shi kamilin mutum girmamasa
akeyi Koda baida wasu manyan shekaru.

Islamiyar dake cikin anguwar ya sakata tareda sauya Mata makarantar bokonma sbd
waccan din tayi nisa Dan haka gabaki daya yanzu komai nasu ya Dan sauya,

Yagana ke girkin abinci da tsaftace koina na gidan ta sakewarta Takoma tamkar yanda
take a da dinta,

Sosai take kulawa da Inayah tamkar jikarta data Haifa uwarta,
Shi kansa Baban Inayar yana cikin kulawar yaganan Dan kuwa abincinsa baa Wasa
dashi,
Musamman data fahimci shi Mai tsananin tsaftar gaske ne sai baa Wasa da qazanta a
gidan ko kadan.

Yan anguwama ganin irin kauna da kulawa Mai girma dake tsananinsu yasa suke daukar
yaganar a matsayin mahaifiyarsa.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE#
#INAYAH#AYSHATOUH#
#ZAFAFA BIYAR

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[9/30, 1:51 PM] MG: *_Mamuhgee 8_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Farkon zaman yaganah dasu duk wata Yana fidda kudin Albashinta na zama da kulawa da
Inayah,

Lokacinda ya fara Bata kudin sosai ta nuna masa Rashin Jin dadinta sbd sune suka
taimaketa bawai itace take taimakonsu ba,

Kai tsaye ta nuna masa Karya Kuma nuna mata kudi da sunan biyanta akan zaman datake
da Inayah harma dashi..

Ganin ta nuna Rashin Jin dadin hakan sosai yasa Bai Kuma tinanin Bata dinba Amma
Kuma bayajin ya nutsu da Rashin Bata Wannan haqqin nata Dan haka cikin dabara ya
jata banki ya bude Mata account batareda ya sanar da ita asalin dalilin hakan
ba,duk wata Yana Sanya Mata 3k a account sbd shi mutum ne da bayason haqqin kowa
akansa,
Bayason Alfarmar mutane sbd Rashin yarda da kowa musamman akan sha'anin da duk ya
shafi Inayah duk da yaganah ta musamman ce a rayuwarsu yanzu,
Tsananin qauna da shaquwar dake tsakaninta da Inayah yasa tasamu matsayi Mai girma
a idonsa harma da wani bangare mai girma na zuciyarsa.

Haryanzu dasuke rayuwa da Umma yaganah shine maiyiwa Inayah wasu abubuwan Kaman
koyaushe Idan zata Sanya Kaya tafi zuwa gurinsa ya zabar Mata Wanda zata saka,
Shine suke Cin abinci tare kaman yanda tasaba hakama bacci a dakinsa Saida Umma
Yaganah tayi da gaske kafin suka samu ta daina kwana gurinsa sbd wani irin Sabone
datayi da hakan tun tana jinjira tareda Mahaifinta take bacci harta Wannan girman
shiyasa takasa sabawa da rayuwa ba gurinsaba.

Shi kansa duk dare ya ringa haske haske fitilar wayarsa Yana leqowa dayaji motsi
sbd duk inda yake bayajin cikakkiyar nutsuwa Koda rana Koda dare Idan baya ganinsa
guri daya da ita,

Allah ya sanyosa cikin irin iyayenda sukeda wata irin taka tsantsan akan tarbiya da
safety na rayuwar 'yayansu,
Sam Sam bayada yarda ko nutsuwa akan komai indai gameda 'yarsa ne Cikinma ahakan
yasamu nutsuwa sosai dakuma yarda matuqar sosai da Umma yaganah.

Umma yaganah tun Bata iya rayuwar Majeed dinba harta iya ta karance komai nasa
musamman tsaftarsa dake wahalar da ita farko Amma daga baya ta saba shiyasa yanzu
take tsananin Jin dadin rayuwarta dasu hankali kwance su ci Mai kyau da lafiya su
Sha Mai kyau da lafiya.

Kullum safiyar fari yana dawowa masallaci yake ficewa morning jogging (gudun safe),
Koda yake dawowa Inayah tagama Shirin makaranta zai rakata makarantar yadawo yayi
wanka wata ran ya tsaya yaci abinci kafin yafita wataran baya tsayawa sbd kaucewa
lattin Isa gurin aiki,

Baida wani Abu dake gabansa bayan jajirwa tuquru akan aikinsa sai kulawa da
gidansa,
Bayada aboki ko daya a yanzu,
Baya doguwar mu'amala da kowa data wuce ta aiki saita gaisawa da Yan gajerun
abubuwan da baa rasaba na mu'amalantar mutanen.


**
Ansamu cigaba ta bangarora da dama na rayuwarsu Wanda ciki ya hada da sauyawar
gidan dasuke ciki zuwa mai kyau da yalwa da tsari sbd yanzu Inayah nada nata dakin,
Shima Abbin yasake zama magidancinsa sbd yazama baban matashiyar budurwa ga Kuma
tarin aiki da masters dinsa dayake kammalawa takardun kawai suka rage masa Kuma da
yardar Allah Yana karba zasu bar Nan sbd komai nasu yagama kammala.

Daga Boko Inayah Umma yaganah ce ke zuwa su dawo tare yanzu sbd shi aikinsa baya
barinsa dawowa ya rakota gida shiyasa umman ke zuwa yanzu,
Inayar tayita fushi tana nuna batason ana zuwa dawowa da ita Amma Abbin yaqi daina
rakata hakama yaqi Bari Umma yaganah ta daina zuwa dawowa da ita duk da ta girma
sosai suna kiris da shiga SS 2
Qawayenta har dariya suke Mata suna kiranta da 'yar Abbi da Umma yaganah,
Wasunsu Kuma burgesu abin yake sbd ganin yanda da girmanta ma Mahaifinta Bai daina
ji da itaba ko Dan batada qanne ne wata kila,
Gashi baya Bata kudi ko kadan duk abinda takeso ko buqata shine yake siya Mata Amma
baya Bata Kuma baya Bari ana Bata.

Lokacinda period yafara zuwar Mata yazo Mata a yanayi Mai zuwa da ciwon Mara Dan
haka hankalinsa yayi matuqar tashi musamman wata na biyu da abin zai sake zuwa
saiyafi na farkon sbd na farkon Bata wani wahalaba gashi umma yagana ma Bata tsaya
fada masa ko meneneba kawai dai ya dauka zazzabine tayi ta Kuma warke,
Amma Wannan watan dayaga yanda take zuba amai tana kukan ciwon Mara hankalinsa
tashi yayi damuwa sosai kan fuskarsa.

Asibiti ya dauketa suka kaita sai acan likita ke masa bayanin menene ciwon,

Da farko Bai Gama ganewaba sai daga baya Umma yaganah tasake masa budadden bayani
akan jinin haila ne Inayar tafara.

Tsit yayi Yana kallon kofa da fararen idanuwansa zuciyarsa na Dan yin nauyi sbd
wani matakin girman ne Inayah takuma hawa yanzu tarbiyarta da kula da ita zaifi
hatsari.,

Shi gabaki dayama Banda Umma yaganah tai masa bayani baiwani San yayane Mata ke
wannan al'amarin,
Sam bayada sani ko kadan akan Mata da yanda suke su irin wannna din duk kuwa da
yanada ilimin addininsa daidai gwargwadonsa Amma Sam baida sani anan, a ilimance a
al'adance a rayuwance ma Dan haka Koda suka dawo gida gurin aiki yakoma
dazai dawo yazo Mata dasu pads daga gurin aikinsa,
Dazai siya dinma Dole cikin ma'aikatansu Mata wata ta zabar masu masu kyan ya siya
yazo dasu yabawa Umma yaganah,
Su panties Bai siyaba sbd yasan koyaushe cikin siya Mata undies sababbi yake sbd
kiyayewa da tsaftarta.

Tun daga Wannan lokacin duk wata haka ake fama da ita har aka samu ta saba ta iya
danne ciwonta idan lokacin period din yayi tadawo ma bamai sanin lokaci yyai tayi
ta gamawarta sabanin farkon da duk wata Abbin yasan lokacinda takeyi sbd yanayinta
da wuyar datake Sha.



********
Shekara daya da Gama masters dinsa komai nasu yagama sauyawa tako Ina,

shekaru sun qaru sun fara zama manyanci,
Arziki ya fara zaunuwa ta hannu ta banki,
Hakama rayuwa ta sake budewa tako wane fannin sbd tuni yabar mall a asalin kamfanin
yake aiki kuma a babban matsayi yafara zama sbd qualification dinsa da zurfin Aiki
da iliminsa dayakeda.

Da farko sosai Yaso samun matsala sbd Yan hassadar zuwansa da finsu matsayi da yayi
Hakan ya haifar masa da matsala sosai har yaji yafara gajiya da gurin aikin
musamman sbd bayason Al'amarin damuwa da tashin hankali.


Ta wani bangaren yanata samun invitation na offern aiki daga guraren dayayita neman
aiki dasu tun wancan lokacin
Yanzu sai babban matsayi Mai kyau suke masa tayi Amma dai sbd halacci ya zabi ya
zauna Nan din Amma al'amarin Yana neman gagara.

A gida sbd lokaci girma sosai dayazo masa yasa yanzu akwai qarin ganin girman juna
sosai fiyeda da tsakaninsa da Umma yaganah sbd yanzu yafara wuce matsayin matashi
Dan haka ganin girman tsakaninsu yafara qaruwa Amma dai ita sakewa har lokacin
akwaita sosai tsakaninsu Bata sauyaba.

Inayah kuwa haryanzu shaquwarta da abbinta saima abinda ya qaru sbd yanzu ma kusan
itace ke gyara bagarensa duk da sunada Mai aiki dake zuwa tayi aiki Takoma gida sbd
Abbin dayace Umma yaganah tasa asamo sbd Inayah karatu take bayason tana tsayawa
aiki,
Hakama itama Umma yaganar yakamata ta huta a rayuwa yanzu tunda an bautu iya
bautuwa yanzu hutu yazo ahuta tunda Allah yakawo damar.

Daga Umma yaganah sai Inayah ne kawai suka San abinda yakeso dakuma abinda yafi
buqata Dan haka acikin akwai Mai aikin gidan har lokacin Umma ce kawai ke girkin
dayake ci hakama Inayah ce yanzu ta karbar Mata gyaran palonsa zuwa dakinsa duk da
dama can bedroom dinsa ne kawai Umma yaganah bata shiga Inayah ce kawai Mai shiga
shima Idan bayanan datai girma yanzu.

Yanzu yanada arzikin siyan mota Amma har lokacin Bai siyaba sbd yanke shawarar
komawa Lagos a reshensu na aiki dake can sbd Nan din fitinar tafara yawa yadda
abubuwan aikin nan din sun fara rushewa Dan kuwa maha'intar kamfanin sun fidda
zalamarsu a fili take komai yafara rushewa.

Yana ganin hakan ya rubuta takardar aje aiki yafara aikawa Nuradden dake Lagos ta
email.

Da farko hankalin Nuradden yatashi da barin aikin na A Majeed sbd sun riga dama
suna kokarin rasa reshensu na can Idan A Majeed yabar aiki zasuyi Rashin babban
gifted Dan haka da wuri ya sanar fa mahaifinsa dake Singapore halinda ake ciki.



***Kwana biyu Yana hutawa sosai a gida cikin iyalinsa hankali kwance musamman daya
kasance dama baya wani yawo sosai daga aiki sai gida sai wasu guraren qalilan sai
Kuma makarantar Inayah da har lokacin Yana zuwa kaita.

Ganin Abbinta gida kwana biyu kuwa Inayah sai takejin Dadi sosai sbd Dana aikinsa
Yana riqesa sosai Lokacin Kuma yake gida itama Kuma makarantar yamma Dan gaka
yawanci sai dare suke samun lokacin zama dashi.

Satinsa biyu a gida Yana hutu ana ukun ya shirya zuwa wani aikin da akeson daukarsa
saiga sakon Amb Ibrahim Dikko mahaifin Nuradden daga Singapore.

Sabuwar offer ce na aiki dasu a Singapore.

Kai tsaye farko dakatar da offer din yayi sbd bayajin zai iya barin qasar yaje wata
qasar aiki yabarsu Inayah anan su kadai Dan haka Kai tsaye bayan kwana biyu yayi
rejecting offer din.

Wancan aikin ya karba harya fara Amma Nuradden suka kasa barinsa sunata bibiyarsa.

Sake sabon nazari yayi akan aikin sai kawai ya amince bayan an amince masa da zuwa
dawu Inayah Amma Lagos zasu zauna tsawon lokaci kafin.

Lokaci qanqani suka dauka kafin suka tattara suka koma Lagos gabaki daya acan suka
dasa sabuwar rayuwa.

Da farko sunsha wahalar rayuwar garin kafin suka saba saidai kam makaranta da Dole
da qarfin hali Umma yagana ce aka koyawa mota Kuma Allah yasa ta iya tunda ba wani
manyata tayiba dan haka ya siya musu mota itace take kaita tana daukota,
Koda minti daya Bata taba Bari tayi lattin Isa makarantar daukan Inayah ba sbd
maimaicin dokar hakan daga gurin mahaifinta.

Aiki yamasa yawa sosai yanzu dan haka sosai baya wani zama,
Haha tafiye tafiyen garuruwa harma da 'yan wasu qasashen daya fara sbd aikin nasa
shiyasa yanzu Dole tarbiyar Inayah tadawo hannun Umma yaganah gaba daya saidai
koyaushe cikin Kira da maimaita akula yake nanata musu.

Inayah na kammala secondary school bada jimawaba ya tattarasu suka koma Singapore
sbd hankalinsa daya rabu biyu.

Rayuwarsu a Hougang Singapore wata sabuwar wayayyar rayuwace ta hutu da Jin Dadi
sbd arziki daya zaunawa Abbin.

Watansu tara a Hougang suka dawo cikin asalin Singapore Singapore,

Bayan aikin kamfani wani karatu yasake jonawa cikin shekara biyu ya kammala tareda
samun wani babban aiki a Australia suka bar Singapore.

Bayan barowarsa Nigeria ko shekara hudu Bai gama rufawaba kamfanin gabaki ya rushe
akai gwanjonsa Wanda shine tashin farko ya siye kamfanin da malls malls din na can
Nigeria harma Dana Singapore ya damqawa Nuradden da mahaifinsa Wanda manyanci yasa
shima yace abawa Nuradden din yaci gaba da kularwa da A Majeed din dasu tunda yanzu
komai ya zama mallakinsa ne
Amma hallacinsa yasa yabar kamfanin a hannunsu suci gaba da kulawa.
Sun sallami dukkanin ma'aikatan dasuke zargi da ha'incin Daya kaisu ga rushewa suka
rasa komai aka Kuma zuba sabbin ma'aikata bayan ansake gyara companies din da malls
malls dinsu.
*_BAYAN WASU SHEKARU....._*
#MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
#A.A MAJEED#
#INAYAH#
#AYSHATOUH#
#RIBABIYU#

*_Dan samun cigaban labarin follow me @Mamuhgee at arewabooks_*
*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[9/30, 1:57 PM] MG: *_Mamuhgee 9_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


_A.A MAJEED's_
_659 Melrose victoria mosmon,_
_SYDNEY,AUSTRALIA._
A hankali ta qarasa zare navy blue turkian doguwar rigar dake jikinta ta jefar kan
brown Chiara Andreatti sofa dake babban bedroom din nata.

Kyakkawar fuskarta datai ja ta Dan kalla ta cikin mirror tana Dan yamutsa fuska
kafin takai hannunta akan fuskar ta shafa gefen damarta da wani Dan qaramin pimple
ya fito mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login