Showing 6001 words to 9000 words out of 124042 words

Chapter 3 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

73

yabi takan qafafuwanta ynaa neman tattakawa a fusace yace"

Uban waye Zaki fadawa akai mama asibiti? Lokacinda kike zubarda mutuncinki kinyi
tunanin halinda zata shiga Idan taganki da wanna abun.

Kukanta qafewa yayi alokacin sbd a yanzu mahaifiyarta kawai takeson yiwa bayanin
gaskiyarta,
Mahaifiyarta dake cikin mawuyacin hali takeson tabbatarwa Bata lalaceba Kaman ynada
suke tunani.

Gurin Inna ta rarrafa tana roqonta akan subarta taga mama Dan Allah.,

Wallahi tallahi Inna ban taba aikata abinda kuke tunaniba,
Inna ku yarda Dani Dan Allah,
Wlh Inna cikina kwanci yayi sai yanzu yatashi,

Inna wlh cikin Salisu ne,Dan Allah inna ke ki yarda Dani.......kuka ta fashe dashi
Mai tsananin ciwo tana sauke kanta sbd babu sassauci ko alamar yarda da ita atareda
kowa.

Tashin hankalin data samu kanta dawowarta bata dauka zata tadda hakanba.

Duk wani sauki da rahama Bata samu daga yayyunta har innar ba qarshema haka ciwo ya
tasar Mata Wanda tabbatar naqudace Amma tashin hankali yakasa barinta tanema guri
ta nutsu ko haihuwarce zatazo.

Irin wulaqanci da tozarcin da yayunta sukai Mata bazai taba barin tasamu sassaucin
nauyin zuciyarta ba har abada,
Sunkuma tabbatar Mata da wallahi bazata taba rainon cikinba a gidan bare
haihuwarsa,
Idanma ta haifesa koko zasusa abasa yasha ya mutu su sun huta itama ta huta da
renon 'dan da babu uba hakama shi kansa Dan ya huta da girma a duniya yatashi cikin
gori da wulaqanci.

Masiface da tozarci Wanda ya haddasawa maqota sanin abinda tadawo dashi daga Lagos
din suka ringa zuba Mata cikin fushi da bacin Rai,

Da yawa wasu sunshigo da sunan duba Inna Dan su tabbatarwa da idonsu cikin shege
tayo daga zuwa Lagos....

Bata taba kukan Rashin mahaifintaba da Rashin Salisu kamar ayau datai wunin
tsananin baqin ciki da danasanin tafiyarta Lagos sbd da agaban iyayenta cikin ya
farfado da babu Wanda zaiyi Mata Wannan yankan qaunar.

Idanuwanta sunyi wani irin kumburi da Bata iya gani sosai.

Daddafawa tayi bayan tasamu dare yayi su Yaya Umar sunbar gidan ta shigo dakin da
mahaifiyarta take ta zube gabanta Daqyar sbd tsananin azabar naquda.

Hawaye ne suka gangaro Mata takai hanunta dake rawa ahankali ta dafa na
mahaifiyarta tareda rintse ido wasu hawayen na tsananta Mata gudu.

Kuka takeson yi ganin yanda mahaifiyarta ke numfashi ahankali alamar samun sauki
saidai bazata kukanba Dan naqudarta tagama zuwa kusa,ta gyara zamanta da qyar tana
hada wani irin zufan gaske tako Ina jikinta azababbiyar azaba takeji Dan haka ta
damqe hannun mahaifiyarta da qarfi tana sake wani irin gurnanin Nishi tana Kiran
sunayen Allah a azabance.

Inna na dakinta kwance zazzabi Mai tsananin gske ya kwantar da ita da wannan babbar
masifar data kunno musu Kai Dan haka batasan meyake faruwa da hadizan ba.

Naquda Mai tsananin wuya da azaba takeyi gadan gadan
Tagama jiqewa sharkaf da zufa
hakama mama tuni tafara bude idanuwanta cikin tsananin ciwo,

Tanajin 'yarta na nakuda Kuma Mai wuya da azaba Amma babu abinda zata iya yimata
hakama babu Wanda zai taimaka Mata...

Hawaye da 'dacin tausayin 'yartane ya gangaro gefen idonta
ta Dan motsa hanunta dana hadizan yake Kai ta kama hannun hadizar ahankali
idanuwanta na zubowa da wasu hawayen masu zafin gaske.

Hadiza taji mamar Amma bazata iya magana ba ko juyowa takalleta saima wani
wahalllen Nishin datake fitarwa tana fidda Rai ga rayuwa,.

Jin take da zata mutu agurin wannan naqudar data godewa Allah ta huta da Wannan
rayuwar da babu komai acikinta sai qunci da damuwa.

Wani qaqqarfan Nishi ne yafara zuwar Mata Idanuwanta sukai jajir gumin na sake
jiqota tako Ina...

Cikin dauriya da azaba tafara Addua sbd sanin adduar mace Mai naquda karbabbiyace
inshallah.

"Ya Allah kaine masanin gaskiyata nida abinda zan Haifa,

Ya Allah ka albarki rayuwarsa ko rayuwarta Idan mace ce,

Allah ka tallafi rayuwar abinda zan Haifa ka datar dashi kyakkawar rayuwar
kwanciyar hankali da nutsuwa.

Mahaifiyarta da 'danta Abdul take kokarin yiwa Addua Amma Ina mamar kawai tasamu
damar rokarwa Allah sauki jariri ya kunno Kai Kuma adaidai lokacin mama Allah
yabata ikon riqe hannunta kyau Dan sassauta Mata radadin datake ciki na kutsowar
'da ya fito ta jikinka.

Gabaki daya jaririn ya fado tareda sake lafiyayyan kukan jarirai ba kakkautawa.

Wani irin numfashi take saukewa da a wahalce tana Kai hannu inda jaririn yake ta
dauko ta Dora jikinta.

Daqyar ta bude idonta dakyau ta Dan daga kafar jaririn taga 'ya mace ce
Take wasu hawayen suka gangaro Mata masu dumi,

Duk da hakan ta godewa Allah daya Bata abinda ta haifar Amma taso namijine sbd
zaifi samun qwarin zuciyar fuskantar zunde da qalubalan maganar da zaa ringa binsa
dasu na Kalmar 'da Mara uba.

Kukan jaririyar ne ya karade gida tako Ina
A gigice Inna ta taso ta fado dakin tana Kiran sunan hadiza.

Da mamaki da tausayi take kallon hadizar tana cewa"

Hadiza ke kadai Kika haihu acikin wannan halin?

Komawa tayi da hanzari ta dauko sabuwar Reza a dakinta tazo ta yanke cibin
jaririyar tana kallon fuskar Yar da fitilar hannunta.

Bata iya cewa komaiba sbd batasan Mai zata fada ba,
Rayuwarsu cikin Rana daya Allah ya juya musu akalarta inda yaso dan haka take fatar
Allah yabasu ikon cinye Wannan jarabawar.

Ruwan zafi ta Dora acikin tsakar dare tazo ta karba karba Yar ta wanke tas
Ta juyewa hadizar sauran ruwan itama ta lallaba taje tayo wanka tadawo.
Sauran tafasasshen ruwan hadiza ta karba Tasha sosai sbd babu abinci babu komai.

Komawa sukayi suka zauna jigum jigum babu Mai cewa qala.

Hadizar zaune take bakin shimfidar mama Idanuwanta dake kumbure ta zubawa jaririyar
tana kallo duk da acikin duhune Bata ganin komai.

Hannu mahaifiyarta taji akan kafadarta
Ta juyo ahankali idanuwanta na Mata nauyi da radadi ta kalla maman cikin duhu ta
bude Baki jikinta matuqar sanyaye muryarta a shaqe tace"

Mama 'ya mace ce na Haifa.

Wani sanyayyan numfashin da Baya fita sosai maman tasaki tareda janye hannunta kan
hadizar ta bude Baki daqyar cikin yanayi na majinyaci Mai tsananin Jin jiki ta Kira
sunan Hadizar.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
#LOVE#
#ROMANCE#
#INAYA A MAJEED#
#AYSHATOUH#
[9/30, 1:40 PM] MG: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


5
Daqyar ta iya furta

"Hadiza Allah zai zama gatanki,
Allah zai raya Miki 'yarki cikin Aminci inshallah.

Allah ya Raya zuriarki ya sanyawa zuriarki albarka kinji¿

Hakama halima ki kula da ita tamkar uwar data dauki cikinki ta haifeki sbd dagani
harku har abada bamuda abinda zamu saka Mata dashi akan halacci da kaunarta garemu,
Batada kowa saiku ku sauke nauyin uwa mahaifiya akanta kinji hadiza.

kasa kuka tayi sbd yanda zuciyarta taso tsayawa cak daga bugawa da sanyin kalaman
mahaifiyarta,

Tunda mutuwa ta dauki mijinta Bata taba samun kyakkawar kalamiba daya taba
zuciyarta sai yau da mahaifiyarta ta furta matasu adaidai lokacinda duniya da kowa
ya juya Mata baya ana gudunta akan abinda daya sameta.

Cikin rawar murya dake son bayyanarda kukan dake kokarin yiwa kansa iso tace"

Mama kin yarda da bazan taba aikata abinda ake zargina dashiba???

Mamar Bata iya mgna ba saidai gyara kanta tayi ahankali tana rufe Idanuwanta dake
lumshewa da kansu...

Kalmar shahada take kokarin furtawa a kakkarye
Hadizar naji ta tabbatarwa da kanta rasuwa mamar zatayi
Cikin sanyi da qarfin zuciya ta Bata sauran Kalmar shahadar
Cikin saa maman ta karba ta qarasa daqyar sbd Rai dayazo gangar fita.

Wata masifar a rayuwa fin karfin wata masifar take,
Idanuwanta da zuciyarta ne suka bushe Mata alokaci daya
Saidai wani irin gagarumin nauyi daya tokale zuciyarta ya tsaya a maqoshinta.

Hannnunta na cikin na mahaifiyarta ta cika,
Rintse idanuwanta tayi ahankali tana Jin nauyin Kirjin nata na tsananta
Ta miqe tsaye ahankali tareda aje jaririyarta a gefe ta matsa gurin inna dake
qudundune gefe tana Nishin azababben zazzabi takai hannu ta tada ita tareda Kiran
sunanta ahankali cikin sanyi tace"

Inna ki tashi Allah ya karbi ran mama...

Wani mugun yunquri Inna tayi tana tashi zaune idanuwanta a waje ta kalli inda mamar
take tana qara hasken fitilarta tace"

Aishatu ta rasu kikace hadiza?

Yanzu nabarta akwance fa tana numfashi.

Miqewa tsaye tayi ta nufi maman hankali tashe tana cewa"

Ya akai kikasan ta rasu ne tunda ba ganewa zakiyiba.

Gaban gawar maman ta tsaya tana Kiran sunanta muryarta na rawa cikin firgici.

Data tabbatarda Aishatun ta rasu ficewa tayi daga dakin ta zauna tsakar gida tana
rusa wani irin kuka Mai rauni.

Tun tanada shekara goma Sha uku Malam ya aurota daga qauyensu kasancewarta
marainiya itada qanwarta Indo yazo ya kawosu Mama lokacin itama batafi shekara goma
Sha biyarba ya hadasu suka zauna lafiya harya aurar da Indo itama.

Lafiya kalau sukai rayuwa da mama tamkar yaya da qanwa haka suka zauna harsukai
wayo mamar ta hayayyafa su kabiru har manyanci da tsufa yakamasu suna zaune lafiya,

Basu qara kaunar juna na mutunta junaba saida malam ya rasu ya barsu
Ita Inna Batada kowa sai mama da 'yayan mamar da itace tayi renon kowannensu harya
girma.

Yau aishatu ta tafi tabarta da tsananin kewa da kadaici adaidai lokacinda 'yayanta
suke tsaka da rikicin da zai rabasu har abada Idan ba Allah ne ya kawo dauki ba.

Koda aka fito sallar asuba tuni su Yaya Umar da malam kabiru suka iso sbd Inna ta
buga musu da 'yar qaramar wayarsu da hadiza ta siya musu tun kafin zuwanta Lagos
wadda da ita take waya dasu.

Hadiza na zaune gefe cikin dakin da jaririyarta a dunqule suka shigo babu Wanda ya
kalla inda take sukaiwa gawar mahaifiyarsu Addua suka fice Dan fara shirye shiryen
jana'izarta da sauransu.

Jaririyarta data Kira da sunan AYSHATUH daidai bayan rasuwar mahaifiyarta sai
baccinta takeyi sanyeda kayan sanyi farare tas data zakulo daga kayanta data Bari
Nan gida tun kafin tafiyarta,
Kayan tun na Abdul ne Dan haka sun Mata yawa sosai amma tunda babu wani kayan haka
ta Sanya Mata su.

Jamaar anguwa da koina sunji labarin rasuwar Mama Dan haka mutane sukaita shigowa
cikeda alhini.
Tana dakin itadai Bata fitoba da jaririyarta sbd mutane zasu iya zunde duk da
rasuwar da akai mata tasani

Dan haka ta kame kanta a daki Bata fitoba har akaiwa mamar wanka da sitira ta matso
tayi Mata Addua aka
Dauketa aka tafi da ita.

Duk yanda taso kuka takasa zuciyarta ta bushe ta kafe da tsagwaron qunci da baqin
ciki.

Saida Yan gaisuwa suka rage tana daki tafito taje tayi wanka da tafasasshen ruwan
da Inna ta Dora Mata tana gurin wankan jaririyarta tayita kuka
Nan take Yan zaman gaisuwar suka fara yi da ita.

Haka tafito bandaki Takoma daki Bata Kuma fitowaba,
Wankanba itace tayiwa jaririyar da kanta sbd inna na cikin Yan gaisuwa.

Har dare Bata fitoba tana daki
Saidai taci abinci data fidda kudi tabawa innar aka siyo musu sukaci da daddare.

Washe gari take anguwa da jamaa suka dauka cewar haihuwar cikin shegen datai shine
ya kashe mama da baqin ciki
Dan haka Take masifar gidan takuma tashi da daddare harta kwanta su malam kabiru
suka shiga shida Yaya Umar sukace wlh saita bar gidan da 'yarta bazata rena 'yar
datai sanadin mutuwar mahaifiyarsuba adakin mahaifiyar tasu.

Tunda mama ta rasu zuciyarta ta kafe Dan haka ta tashi ta hau tattara kayanta.

Kallonta Inna tayi tana cewa

"Ina Zaki ki barni hadiza?

Wasu siraren hawayen tsananin tausayin Inna ne suka gangaro Mata.

Inna abar tausayice tako Ina sbd barinta tamkar watsar da itane ga duniya Dan kuwa
su Yaya Umar Basu tallafi mahaifiyarsu data kawosu duniyaba tanada Rai tayaya zasu
iya tallafar rayuwar Inna da batada kowa batada komai...

To Amma ya zatai tunda ankoreta ita kanta,
Kuma ita kanta zataso tafiyar sbd yanda ake zundenta da qyamatarta da yarta tareda
jifanta da alkaba'i daban daban akan itace tayi sanadin mutuwar mahaifiyarta.

Tana kuka ta tattara kayanta tabar gidan cikeda baqin ciki da quncin Rashin ganinta
Abdul daya koma hannun hajiyarsu Salisu sbd jinyar da mama keyi Inna Batada lokacin
kulawa dashi.

Inna kam itama kukanta daukewa yayi bayan tafiyar hadizar da sunaji suna gani su
malam Umar ana gaman zaman gaisuwa ya Roshe dakin mama ya hade da wanda yafara
ginawa cikin gidan ya fake da sunan zai kawowa Inna abokiyar zamane sbd kadaici.

Barin Hadiza gida ya rusa rayuwar Inna da ita kanta hadizar wadda batasan Ina ta
nufaba.
ALLAH YA ZAMA GATAN MARAYA A DUK INDA YAKE..AMIN

**************
_March 2002_
_7:26am_

Kokarin saka Mata pink safa a qananun qafafunta yakeyi Yana dan sake waiwayawa yana
kallon wajen dakin nasu dan duba yanayin garin dakeda hadari sosai Wanda tun bayan
sallar asuba yaketa haduwa.

Ganin yanda duk tabi ta lafe masa tamkar Mara lfy yasashi dagowa ya kalli kyakkawar
qaramar fuskarta dake kallonsa da idanuwanta dako yaushe zai kaita makarantar raino
sai tayi wannna qyuyar wadda tun batai wayo hakaba takeda ita.

Batasan kowaba bayan mahaifin nata da a duniya batada kowa bayanshi Kuma Bata yarda
da kowa sai shi din sai uwar renonta yagana wadda take kira da Ummey.

Cikin idanuwanta dasuka Dan Yi Kaman zatai hawaye ya kalla ya saki ajiyar zuciya
ahankali Yana janyota jikinsa cikin lallausan muryarsa me zallan nutsuwa ya furta

_"INAYA.._

Hawayene suka fara gangaro Mata ta girgiza kai ahankali cikin Rashin budewar
harshenta sosai tace"

_ABBI..._

cikin kulawa ya hanata fadar abinda yasan rigimace kawai zatayi sbd batason zuwa
Kuma ya saba da hakan tunda yafara kaita kullum saitai masa wannna rigimar.

Share Mata hawayenta yayi tareda miqewa tsaye ya dauki Yar jakar takardar dayake
saka Mata robar ruwan pure daya dayake juye Mata a empty robar Coke sai fanke da
kosan matar kofar gidansu daake soyawa na siyarwa.

Daukarta yayi ya riqe jakar a dayan hannunsa suka fito ya janyo kofar dakin tareda
Sanya padlock dinsa ya rufe kofar dakin nasa ya juya ya nufi hanyar kofar ficewa.

Dukkanin jamaar gidan hayar dasuke gidan kusan kowa yafito Yana hada hadarsa a
qatoton tsakar.

Da damarsu dasukaci karo da fitowarsa da mugun kallo suka bisa
Wasu Kuma dai tabe Baki sukai suka dauke Kai Suma.

Maman habiba ce dai da Bata gajiya da cusa kai tana ganinsa ta taso tana washe baki
da cewa"

Aa su INAYAN Abbinta ce anfito zaa tafi makaranta?
Zo mu gaisa kinji?

Hannu ta miqa Dan karbanta
Inayar ta sake maqalewa Mahaifinta tana lafewa tareda rintse ido batamason kallon
maman habiba din.

Yar dariya tasake tana cewa

"Inaya haryanzu dai qyuya ko?
To adawo lfy.

Amin kawai ya iya bude bakinsa ya furta ahankali kafin ya ra6a maman habiban ya
wuce tana bin bayansa da kallo.

Mijintane ya qaraso ta bayanta Yana kallon Wanda takebin da kallo yace"

Zuwaira bazaki daina shiga sha'anin Wannan Mai shegen girman kan da miskilanciba
ko?
Sam Dan iskan yaro a naqushe cikin talauci Amma baya ganin girman kowa
Baya daraja kowa
a duniyarsa babu abinda yasani sai wannan aljanar 'yar tasa Mai kama da 'yar
Rake,

Kullum Yana tafe Yana kame kansa Kaman dan kwalisar daya sauko daga jirgi.,
Ke Kuma sai naci da shishigi kike masa akan yabaki renon Yar tasa kina samun 'yan
kudin da yagana ke samu gurinsa.

Juyowa tayi tana fuskantar mijin nata tace"

Baban habiba laifine Dan na nace masa akan yaban renon Nima naringa samun Yan
qananun canjin da yagana ke samu?
Inace Idan nasamu kudin Kai zan rufawa asiri na ringa Dan samun ciyar da yarana
tunda Kai zuciyarka ta jima da mutuwa bazaka iya fita kayi ko aikin wahalar dashi
yakeyi Dan ya kula da 'yarsa kasamoba...

Cikin masifa Yana jefanta da mugun kallo yace"

Idan zuciyata mutuwa tayi ke taki konewa tayi ko?
Sbd Naga alamar son abin duniyarki Neman yake ya rufe Miki ido yaro Dan qarami
Wanda kikai qani dashi Zaki zauna Yana wulaqantaki tunda ko kallonki bantaba ganin
yayiba duk wannna shishigin da kike masa akan 'yarsa dako qafarta baya barin ta
taka tsakar gidan Nan Kamar akansa aka fara haihuwa
mu duka 'yayanmu ba 'Yaya bane sai tasa 'yar ce kawai 'ya,

Yasan Yana tsananin jinta kamar ransa ubanwa yace ya rabu da uwarta?

Cikin takaici maman habiba tace

"Ina ruwanka da Idan sakin uwarta yayi idanma mutuwa tayi,meye naka?

Bbn habiba ka fita fa idona na rufe kabarni nasamu nacusa kaina a gurin nasa nasamu
abinda nakeso.

Inaya dai inshallah sai ka ganni Ina renonta
Ina laifin dari Biyar duk sati?wlh zanyi kokari nasamu tunda Kai din ba nemowa
kakeyiba sai shegen gulma da sa ido.

Qaramin tsaki ta sake tana juyawa ta wucewarta tabarsa tsaye Yana binta da hararar
mugun rainin datai masa Bata kunyar fada masa magana kowace iri tunda taga ita ke
nomowa ta ciyar dashi.

Suna fitowa gida Kai tsaye hanyar titi ya nufa Bai Kuma sauketaba har lokacin sbd
karta Bata qafafunta da takarminta da daudar hanya tunda lokacin damuna ne.
Barema koba lokacin damuna bane baya ajeta koyaushe daukarta yakeyi daga cikin gida
har inda yake kaita,
Bai cika barin ta fitoba tayi tafiyaba koyaushe daukar 'yarsa yakeyi shiyasa tayi
wani irin mugun sabo da abbin nata Bata yarda da kowa saishi Bata iya zama da kowa
sai shi,

Wani irin qawa zucin Mahaifinta Allah ya dasa Mata acikin ranta sbd tunda tafara
wayo shine halitta mafi soyuwa a zuciya da idanuwanta,

Yagana farkoma data fara wayo qin yarda takeyi yabarta gurinta yaje gurin nema sai
ahankali tadan fara sabawa da ita Amma harya dawo daukanta Bata sakewa duk da
qananun shekarunta tasan Mahaifinta ta yanda ko sallamarsa taji daga nesa tana gane
shine.

Wata qaramar private school ya nufa da ita Kai tsaye dake anguwar.
Yana Isa dayake maigadin makarantar ya sanshi sosai sbd yanda kullum yake zuwa kawo
'yarsa tun tana jinjira har tayi shekaru hudu yanzu.

Da sakewar fuskar ya miqe tsaye Yana cewa"

*_Haji ABDUL-MAJEED_* baban Inaya sannu da qarasowa,

Inayar ya kalla yana dariya yace"

Inayar Abbi sauko to na kaiki gurin yagana.

Kallon Abbin nata tayi tana sake riqesa idanuwanta na kokarin cikowa da hawaye
Kaman yanda tasaba kullum aka kawota.

Wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta cikin kulawa tareda zareta daga
jikinsa ya miqawa yagana data iso gurinsu tana Kiran sunanta cikin kulawa da kauna.

A natse da kamilalliyar murya yace"

Barka da safiya yagana,
Mun tashi lfy?

Lfy kalau Baban Inaya,
Ya Inaya?antashi lfy?

Alhmdlh" ya furta a taqaice Yana maida kallonsa kan inayar datake kallonsa ya sakar
Mata wani taqaitaccen murmushin da duk duniya ita kadaice yakewa murmushi da
tattausan lafazi ya furta

"INAYA"
Karkiyi kuka zandawo da wuri inshallah kinji??

Gyada Kai tayi ahankali tana cewa"

Abbi...

Kallon yagana yayi yana ciro 500 ya miqa Mata tareda jakar inayar Yana cewa"

Ku shige zan koma daga Nan.

Juyawa sukai yaganar tayi ciki da ita tana Mata wasa.

200 yaciro ya miqawa Jamilu Mai gadin Shima kafin ya juya ya wuce yanajin yanda
yake jero godiya Yana adduar Allah ya Raya musu Inaya.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR
#AYSHATOUH INAYA#
#A MAJEED#
#LOVE/ROMANCE#
[9/30, 1:41 PM] MG: *_Mamuhgee 6_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Yagana aiki takeyi a qaramar private school din dake kusa da anguwar tasu amatsayin
nanny Mai kula da yara Amma gidansu na haya 'daya da ABDULMAJEED din da yarsa
Inayah,

Tun 'yarsa na jaririya shi kadai ke dawainiya da lalurar kulawa da ita sai yaganar
wadda Rana daya suka tare gidan hayar itama tazo tareda mijinta da kusan yake
kwance ba lafiyayyeba,
Da farko sbd babu yanda zaiyi ne yasa ya amince yaganar datai masa tayin taimaka
masa da rainon 'yar tasa da Kai tsaye ya sanar Mata da ya rabu da mahaifiyarta.

Yagana itace tayi rainon Inaya hartai wayo ta girma tasan Mahaifinta har takewa
yaganar qyuya akansa shiyasa daga baya Takoma gurin Mahaifinta gabaki daya saidai
idan zai fita takaita gurin yaganar Amma daya dawo yake zuwa ya taho da ita
Da haka harsuka koma rayuwarsu su kadai,
a dakinsa yake Mata wanka cikin qatuwar robar wankanta daya siyo
Zata tsaya aciki kokuma ta zauna aciki yayi Mata wankanta tas ya shiryata.

Rayuwarsa da 'yarsa wata irin rayuwace dasuke abarsu su kadai dagashi sai ita sai
yagana data Dan shigo ciki,

Duk duniyarsa babu wani buri ko abinda yake gabansa bayan 'yarsa INAYA dayake
iyayin komai dabai sabawa shariah ba Dan inganta rayuwarta da Bata wadatacciyar
tarbiya da nutsuwar rayuwa,

Bayan INAYA babu wani Abu dayake so da kauna a duniyarsa,
Ita kadaice abinda yakeda,
Ita kadaice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login