Showing 15001 words to 18000 words out of 124042 words

Chapter 6 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

58

qwaya daya tal daya hanata fita koina tun shekaran jiya.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda zare fararen undies dake jikinta ta nufi toilet dasu
a hannu tana shige ta jefa cikin laundry ball dake gurin ta nufi inda brushes dinta
suke ta dauka daya tareda diban Toothpaste tafara brush tana kallon fuskarta jikin
mirror tana sake Jin damuwar kurjin fuskar tata,

Tana gamawa jacuzzi ta nufi ta shige tareda sakarwa kanta ruwan dumi tana Dan
lumshe ido sbd damuwarta ta Dan saketa.

Mintuna qalilan ta dauka tana wankan kafin ta fito daure da brown towel kanta ma
daure da brown towel din qarami
fatar jikin qyalli takeyi tana bayyanarda tsananin hutu,Jin Dadi da tsadaddiyar
kular datake samu ta hanyar amfani da skin products masu tsananin kyau da tsada.

Kai tsaye gaban madubin dakinta ta nufa ta zauna tareda kunna hand dryer tafara
busar da gashin kanta data kunce bobmarley braids (kitso/kalban Bob Marley) jiya da
yamma.

Doguwar malaysian riga ta saka har qasa Mara nauyi ash kala ta zira Burberry
slippers ta fito daga bedroom din nata hannunta riqeda wayarta tana kokarin saka
Kira.

Qamshin turarenta na Versace(Bright crystal) ne yafara bayyanarda fitowarta daga
bedroom dinta zuwa babban yalwataccen palon gidan dake.

Zubbi Mai aikinsu tun a Singapore Yar Amana wadda Alhaji Nuradden Aminin Abbi ya
Aiko musu daga Nigeria itace ta dago daga kunna qatuwar Humidifier dake palon bayan
tagama gyare koina na gidan ta tsaftace ta kalli hanyar da Inayah ta fito tana
kallon kyakkawar fuskarta ta saki dan gajeran murmushi tana cewa"

Good morning Inayah.

Kallonta Inayah tayi da fararen idanuwanta tana amsawa Kai tsaye da cewa"

Morning zubbi.

Hanyar bedroom din Umma yaganah ta kalla tana cewa"

Umma yaganah ta tashi?

Yes ma" zubbi tafada tana qarasowa Dan shiryawa Inayah breakfast dinta kan dining
ta nufi babban Australian kitchen dinsu ta shige.

Kai tsaye ta murda kofar dakin ta shige tana qaramar sallama da cewa"

Umma yaganah yauma bazan fita koinaba fuskana ta sake kumbura da ja...

Zaune umman take kan wata tattausar sofa kalar ash na komai dakin dayake ash Mai
haske,

Farin glass ne a idonta tana karanta wani Arabic hisnul Muslim
Jikinta sanyeda doguwar rigar plain cotton Swiss Mai tsada light pink.

Dagowa tayi tana kallon Inayah cikin kulawa da tsananin bayyananniyar kaunar Inayah
data Dade da shiga jininta ta ajiye littafin gefe kan table tareda maida hankalinta
kan Inayan gaba daya tace"

Yau kam saikin fita Inayah,
Meyesa kike Wasa da karatunki ne yanzu?
So kike abbinki ya dawo yasan kwana biyu bakya zuwa makaranta?
Karatun likitanci fa kikeyi karki manta,
Ahakan zakiyi wani abin arziki kullum cikin shiriritar Gayu ya hanaki Wannan da
wancan?

Akan pimples bazakice kindaina fitaba sai kin warke Dan haka
Ki Gama breakfast kije kiyi Shirin zuwa makaranta.
Zama Inayah tayi gefen umman tareda yamutsa fuska tana kokarin yin magana umman ta
katseta tana cewa"

Abbinki kinfi kowa sanin fadan bacin ran dazai nuna Idan yasan kina skipping
ranakun zuwa school,
Banason bacin ransa akan Rashin dalilinki.

Kai Umma yaganah Abbi fa idan yaji abinda ya hanani zuwa bazaiyi fada ba.

Inayah please Mana,
Ki daure ki cire Rashin son makaranta a ranki bayan kinsan Abbinki yanada riqaqqen
raayi akan son karatunki.

Bari sai Akira likita tazo ta sake duba fuskar taki,ok?

Gyada Kai tayi tareda miqewa tana kokarin barin dakin tace"

Good morning,ban gaishekiba Dana shigo.

Wani qayataccen murmushi Umma yaganah ta sake tana kallon fatar wuyan Inayar dake
bayyane tana sheqi sbd yanayin rigarta cikin Yar dariya tace"

Barkanki da safiya kema Inayah Majeed.

waiwayowa tayi ta kalli Umman tana Yar murmushi sbd friends dinta ne masu Kiranta
Kai tsaye hakan Amma ko umman sau tari hakan take kiranta itama.

Dining ta nufa ta zauna hankali kwance Tasha black tea da toasted bread biyu da
kwai ta tashi tabar gurin ta nufi dakinta tana sake Danna Kiran Mahaifinta dataketa
Kira tun dazu takasa samunsa sai yanzu Kiran yashiga.

***Zaune yake a palon madaidaicin duplex dinsa dake Singapore tareda CM Nuradden
Aminin huldodinsa suna meeting akan aikin da zaaiwa sabon kamfaninsa da aka bude
reshensa a portharcourt Nigeria.

Kan couch Mai zaman mutum biyu yake zaune sanyeda sky blue English kaftans masu
tsananin taushi da tsadar dake bayyane.

Wayarsa dake gefensa ajiye ya waiwaya a natse ya kalla ganin hasken data kawo
alamar shigowar Kira ko saqo.,
Fararen idanuwansa yafara Dan juyowa ya kalla CM Nuradden dasu Ahankali cikin
nutsuwa yace"

One minute.

Hannunsa yakai ya dauki wayar kai tsaye tareda kaiwa kunnensa cikin nutsuwar murya
da Allah yayi masa Mai tattareda kamewa saidai kasancewar 'yarsa ce tilo datafi
masa kowa da komai daya mallaka a duniya ahakan muryar tasa a bayyane take da kauna
da kulawa
Kai tsaye ya furta"

Yes,INAYAH.

wata ajiyar zuciya ta sake tana zama bakin gadon dakinta cikin tsananin kauna da
kewan mahaifin nata tace"

Good morning Abbi.
Ahankali ya dago fararen idanuwansa ya kalli agogon _Patek Philippe_ dake daure a
hannunsu ya maida idanuwanta ya dan kalli CM Nuradden
yasan Inayah zataci lokacin magana dashi sosai Dan Kuma CM flight zaibi yakoma
Nigeria zuwa 11 dan haka Kai tsaye cikin nutsuwa da kulawa yace"

Morning Inayah,
Kintashi lfy?

Lfy kalau,
Abbi haryanzu kana Singapore?
Yaya aiki?
When are you coming back?

Cikin nutsuwa ya amsa ta da cewa"

Inayah Ina magana da CM yanzu,
Anjima I will you back,ok?
Ki kula,Ki gaida Umma yaganah.

Ok Abbi sai anjima.
I miss you.

Kashe wayar yayi tareda ajewa gefensa kafin ya dago ya kalli CM dake jiransa dan
harya fara shiga yanayi na damuwa sbd sanin wayar Inayah ga mahaifin nata sai tasa
a rasa meetings masu mahimmanci dazasu kawo manyan dukiya da dama Dan ansaba
Indai akan Inayah ne AA MAJEED nada raunin duba al'amura da dama masu mahimmanci
Kuma hakn wani al'amarine da kusan duk wnada yake hulda ko mu'amala dashi yasani,

'yarsa Inayah itace Rauninsa da kowa yakasa sani duniya akansa sai Aminin nasa Cm
Nuradden sai Kuma Umma yaganah sbd sune sukeda cikakkiyar shaidar yanda 'yarsa take
a Ransa fiyeda duk abinda yakeda,

Hakama 'yarsa Inayar itace qarfin Rayuwarsa,
Duk Wannan arzikin da dukiya Mai yawan daya Tara basukai masa mahimmancin farin
cikin yarsa na wuni daya ba,

Inayah da kanta tasan itace hasken rayuwar Mahaifinta kaman yanda itama kowa
yasanta yasan Mahaifinta shine abinda Bata iya hada girma da tsananin kaunarsa da
komai,
Shine Abbinta,shine mahaifi Uba Kuma mahaifi UWA.

Numfashi CM ya sauke ya sauke yana kallon A MAJEED din sbd ya dauka zaman jiran
yagama wayar ya samesa ne saigashi Allah yasa yau A MAJEED din ya taqaita.

A MAJEED ya fahimci zullumin da CM ya shiga dan haka ya taqaita wayar
Cikin nutsuwa ya dauki takardun da zai saka hannu akai yafara signing Yana cewa"

Sauran takardun na AIA sa hannun Inayah zaa saka a takardun Amma ba yanzuba saita
kammala karatunta tukuna so agama aikin kawai kafin lokacin.

Alright Inshallah.

Sai 10 suka rabu da CM bayan daya daga cikin ma'aikatansu yakaisa airport ya wuce.

11:30 shima yabi jirgi tareda secretary dinsa suka bar Singapore zuwa Australia.

****Badan tasoba haka tayi Shirin makaranta ta fice daga gidan zuwa school bayan
tayi waya da qawarta da itama duk sunne ba wani son karatun sukeba sunfi ganewa
Gayu da rayuwa kawai irin ta 'yayan gata masu abin duniya.
Duk da Bata wani son karatun sosai bashi yasaka Bata maida hankali ga karatunba
idan taje,
Wuyarta dama dai taje din sbd idan taje sosai take maida hankali ga karatun Kuma
Allah ya taimaketa tanada qwaqwalwar daukan karatun sosai Dan ahakan Bata taba
failing ba
Koyaushe tana samun grades masu kyau,
Kawai dai Allah Bai saka Mata wani son karatun bane
Abinda Allah yasaka Mata so shine Tanada shaawar yin aure kawai sbd ta daina zuwa
makaranta tayi rayuwarta yanda taga dama daga shopping sai zuwa beauty parlor dasu
spa sai yawan qasashen dataga dama.,

Ko yanzu kusan rayuwarta hakanne,
Batada wani aikin bayan yawon shoppings da zuwa su spa day guraren gyaran jiki sbd
Bata hada gyaran jikinta da komaiba Wanda kusan hakanne yasa koyaushe fatarta da
jikinta koina yake sheqin hutu da lafiya cikakkiya da zallar gyara na musamman,

Yawon qasashene Bata wani Yi sbd duk qasashen datake zuwa tareda Abbin take zuwa
kokuma zuwa umrah ko Hajj tareda Umma yaganah Dan haka Bata wani samu tana yawon
yanda takeso sbd haryanzu dasuka samu sauyin rayuwa mai tsananin nisa Abbinta baya
barinta tana yawo yanda takeso duk da kuwa ba wani zama yakeyiba Amma dokarsa na
aiki a gidan duk inda yake kuwa.

Hakan yasa takeson aure fiyeda karatu musamman ma auren irin na wayayye irinta
dazai barta tayi rayuwar datakeso ta Rashin takura da damuwa kawai suyita soyayya
suna shaqatawa sbd love na cikin abubuwan datake yiwa kanta shaawar samun kanta
aciki hakanne ma yasa bayan abbinta da yaganah to Babu Wanda takeso sama da
saurayinta Zaid.

Soyayyar Zaid tayi wani irin nisa a ranta Kaman yanda shima yake tsananin son
Inayan,
Kusan yanayin rayuwarsu daya sbd shima iyayensa masu arzikine sosai Amma suna
Nigeria Dan asalin portharcourt ne karatu yake a qasar,
Kaman yanda take wayayyar Yar gata girman turai hakan yake shima sbd tun Yana yaro
shima kusan a qasahen turawan ya tashi tareda iyayensa sai daga baya Suka koma gida
sukabarsa Yana karatu.

Dan haka da rayuwar Zaid tayi daidai da tata sai soyayyarsu takeda wani irin qarfi
da shaquwa.

Abbinta yasan raayinta na Rashin maida hankali kan karatu yakuma san aurene takeso
fiyeda karatun Amma yaqi nuna Mata ya sanin sbd karta sake samun damar nuna batason
karatun,
Shikuma raayinsane riqaqqe dakuma buri akan bazatai mata aureba saita Gama karatun.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
#AA MAJEED#
#AYSHATOUH INAYAH#
#LOVE
#ROMANCE
#MARRIAGE

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[9/30, 1:58 PM] MG: *_Mamuhgee 10_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Karfe uku na yamma ta dawo daga makaranta tareda qawarta neesah wadda kusan
ra'ayoyi da halayensu suke duk iri daya,

Neesah Bata kaunar karatu kusan fiyeda Inayah ma Kuma itama tanada qwaqwalwar
daukan karatun Amma tamafi nisa Rashin maida hankali kan karatun sbd ita iyayenta
basa takura Mata ko Bata wata doka da Oda duk kuwa da kasancewarsu musulmai Kuma
hausawa kamansu Inayah,

Iyayenta ita har tafiye tafiyen wasu guraren suna barinta Amma qawancenta da Inayah
yasa Bata tafiyar koina itama sbd tare suke komai to Inayah Kuma abbinta baya Wasa
Sam Sam bare sake fuska ga irin Wannan shashancin Duk da kuwa ko ita neesar tana
fada son da iyayenta ke Mata itada takeda uwa da uba wasane akan Wanda Abbin Inayah
yakewa Yar tasa Amma duk da Wannan tsananin kaunar A.A MAJEED bai taba bada fuska
ko daga qafaba akan tarbiyar 'yarsa,

Kaman yanda yake tsayayye akan dukkanin huldodinsa magana daya yakeyi baya sauyi to
kusan hakanne akan Inayah,
Dokarsa tun tana qanqanuwa haryanzu Bata daina aikiba sbd a gurinsa har yau har
gobe Inayah jinjira ce agabansa.

Taren Inayah da neesah yasa akan Dole itama neesah din yau da gobe Ahankali ta
sauya bangarori da dama dan tana samun tarbiyar Inayah na shafarta sbd dukkanin
kiyayewa da dokokin Abbin akan Dole itama ta koya binsu tunda Inayah Bata
tsallakesu Dan haka itama tunda tana kaunar Qawar tata Dole ta ringa bin tarbiyar,

Ahakan sai rayuwarta taqara Mata Dadi sbd Ashe tarbiyar da tsawatarwar tanada Dadi
sosai musamman Idan Umma yaganah ta zauna tana musu fadan wani abin idan sunyi sai
su gyara ko basa so ahakan sai suga ba illa bane kuwa gyaran.,

Ko sallah da bawani sosai neesah takeyiba sbd Rashin ilimin addini da tarbiya sosai
duk sanadin tarenta da Inayah yanzu babu sallar datake tsallakewa saidai wata ayita
ba acikin lokaciba Amma komai dare idan batayiba saita rankasu take kwanciya.

Bangaren saka sitira ne dai haryanzu sai ahankali bawani sitirar Daya kamata take
sakawaba shima sbd itama Inayan tana saka qananun kayan sosai ne sai Suka hade Amma
Kuma ita Inayah wasu lokutan tamafi saka dogayen riguna irinsu Turkish ko Kuwait
abayas fiyeda qananun kayan.

Iyayen neesah kuwa Suma Dadi suka ringa ji sosai ba kunya har Kiran Umma yaganah
suke suna godiya akan tarbiyar dasu Suka kasa bawa yarsu suna son Kiran Abbin
Inayah amma AA MAJEED ba gurinda zasuyiwa dogon shishigi bane bare shima su ringa
Kiran suna godiya Amma a hakan dai dad din neesah Bai daina cusa kansaba sbd dama
dalilin dazai hada hulda da A MAJEED din yake nema tuni.

Tare Suka jero kai tsaye suna shigowa cikin yalwataccen palon dake farko na cikin
babban gidan nasu,

Inayah sanye take cikin free Malaysian Abaya ash kala da Adon black beads sai black
silky scarf dayake kanta daure hasken fatarta ya fito sosai sbd black kalar dake
jikinta,
Neesah Kuma Kaman dai yanda kusan aka saba turtle neck Balenciaga top ce a jikinta
brown da Alvn straight skirt shima brown.

Zubbi ce data fito daga hanyar kitchen daukeda tray da drink akai da cup ta nufi
inda zata ajiye ta aje ta qaraso gurinsu cikin girmamawa da sakewa ta karba handbag
din Fendi dake hannun Inayah tana cewa"

Sannu da dawowa Inayah.

Kallon neesah tayi tana cewa"

Welcome Ms Neesah.

Thank you" Suka furta Mata kusan state suna qarasowa tsakiyar palon.

A hankali idanuwan Inayah Suka sauka kan kyakkawar fuskar dake zaune palon ta Dr
Farhat Ahmed
Kwararriyar likitar Mata dake amatsayin likitarsu wadda itace ta saka kanta hakan
sbd tsananin kaunar A MAJEED dake dawainiya da rayuwarta,
Taqi aure har shekarunta sunja sosai sbd qwallafa ranta datayi akan Abbin Inayah
shikuma duk dubaru da dadin Baki da komai da Inayah da Umma yaganah sukeyi Akan ya
aura Dr Farhat din Sam babu haske qarshema sosai sukaga bacin ransa akan hakan daga
lokacin Basu sake Shiga hurumin maganar yayi aurenba,

Inayah da Umma yaganah sunsan cewa bazai taba aureba sai Lokacinda ya aurar da
Inayah Wannan Kaman wani raayine nasa wanda yaketa damun Umma da Inayah din
sakamakon hakanne shaawar yin aure tashiga Inayah sosai sbd tayi aure da wuri kodan
sbd Abbinta yayi aure tunda bazaiyiba sai ya aurar da ita din.

Wannan sanadin ne yasa takeda buri da kaunar aure batareda ta tsaya dogon karatu
ba,
Saigashi raayinta ya kama qawarta itama aure takeson yi ba karatunba,
Dr Farhat tun kafin Bayyanar A MAJEED da 'yarsa rayuwarta batada wani Mai nemanta
da aure ga shekarunta sun Dan fara ja Dan haka tana ganinsa taji Aurensa shine
qarshen abinda takeso a duniya dan haka ba Wasa ta maqale tanata fama da wahalarta
ita kadai Amma yanda Inayah ta shaqu da ita tayi Mata alqawarin tsaya Mata sai
abbinta ya aureta.

Cikin sakewar fuska da farin cikin ganinta Inayah yaqaraso tana cewa"

Yanzu kika zo ko tintini Dr Farhat?

Miqewa tsaye Dr Farhat tayi tana Dan rumgume Inayan tana cewa"

Just 3 min kenan da shigowana,

Ok,sannu da zuwa,
Umma yaganah Bata Nan ne?

Zama sukayi cikin nuna damuwa Dr Farhat ke kallon fuskar Inayah tana cewa"

Umma takirani kina fama da Rashin lafiya a fuska
Hankalina yatashi so I had to come
Banma dauka kin fita school ba.

Dan kwabe fuska tayi tana cewa,

"Nafita Amma gaskia dama Ina buqatan ganin likita.

Ba wani sauran Bata lokaci suka miqe suka dunguma zuwa gurin umma yaganah suka
sanar mata zasu asibiti.

Ficewa sukai a motar Dr farhat din suka nufa asibiti gurin likitan fatar dashine
zai duba Inayah din.

Sai yamma sosai suka dawo gida ta ajeta ta wuceda Neesah ta kaita gida itama.

Dakinta ta wuce direct ta tube tayi wanka tareda alwala tayi sallar magrib
Tana idarwa taga time din ishai yayi dan haka ta miqe ta yi sallar tana gamawa tayi
adhkar tagama ta miqe ta sanya riga da wando na bacci masu Dan kauri da safa sai
hular dake hade da rigar sanjin jikinta data rufawa kanta ta zira slippers din
Gucci.

Fitowa tayi daga dakinta Tana amsa wayar zaid cikin wani irin yanayi sanyin jiki da
sakewa dakuma taushin murya kaman yanda tasaba waya dashi saidai Kuma sanyin jikin
na rashin ganin Abbi ne gabaki daya tunda yayi tafiya ya dawo.,

Hanyar dazata kaita palon abbin ta nufa Kai tsaye Tana cigaba da wayar hankalinta
na Dan rabuwa biyu sbd kaman yanda abbinta baya hada komai da 'yarsa itama kam
tamafi sa Dan kuwa ita batamasan komai da kowaba dake gaban mahaifinta tunda shi
kadai ta taso da sani.

Abbin yasan da soyayyarta da Zaid duk da irin tsananin dokokin dake gidan gameda
tarbiyarta Amma Sam Bata tsaya nuqu nuqu ko Bata lokaciba ta fada Masa Zaid din Dan
tasaba Bata iya boyewa mahaifinta komai Kuma kusanma shine yabata tarbiyar hakan
yayi mata sabo sosai da rashin boye Masa komai sai tsananin gata da wayayyar
rayuwar turai dasuke ciki ta qara shigar da ita hakan Sam Batasan wani dogon boye
boyeba.

Farko Bai wani bawa lamarin nasu mahimmanciba sbd yasan ba maganar aure akanta
yanzu tasani ita kanta saita Gama karatu Amma daga baya ganin yanda ta dauki Zaid
din da tsananin mahimmanci da so Mai tsanani yasa dole yashiga lamarin sbd Inayar
nada raunin zuciya bazaiso soyayya ya taba masa raunintaba,rayuwarta Zata iya
juyewa Takoma wata kalar daban idan raunin zuciyartata ya tabu.

Hakan yasa ya sakarwa Zaid din dama yasansa sosai yasan iyayensa Dan kuwa cikin
kwanaki qalilan aka Gama binciko Masa asalinsa da iyayensa dama karatu da aiki
dayakeyi anan din.

Ba laifi ya yaba da dukkanin abinda aka binciko Masa akansa daga Nan yabasa damar
fara Neman inayah din
Aikuwa Dadi da farin cikinta sosai ta nunawa abbin duk da sosai yasaka Ido akansu
din Dan bayason Zaid din yaqarasa hargitsa Masa tunanin 'ya dason aure Dan
shigowarsa rayuwar inayah din yasa soyayyarta da aure ta qaru sosai,
Damar daya basu din yasa yanzu suke soyayyarsu hankali kwance,

Yanda take tsananin son Zaid din yasa Shima yakejin kaman zai zaune idan ba auren
Inayar yayi tazama tasaba Dan kuwa bayajin zai iya rasata Bai zauceba Dan haka duka
su biyun suka zaqu suyi su qarasa karatun suyi aure,

Shi yamaso ya gabatar da maganar ayi auren su kammala karatun a gidansu Amma Sam ba
fuska ko damar hakan koda wasa sbd tsananin kwarjinin Abbi kesa idan yayi magana
daya babu Mai kuzarin iya sake wata daban Dan haka suka barta ahakan suna
soyayyarsu tunda sun samuma ya bada wannan damar.

Umma yaganah ma sosai take son ace anyiwa Inayah aure tun da qananun shekarunta
zatafi morewa auren hakama A MAJEED idan ba aurarda ita yayiba yaga tafara aje Masa
jikoki bazai taba tunanin yin aurenba,

Saukinsu da jin dadinsu daya dasuke godewa Allah akansa itada Inayah shine da Allah
yayisa wani qaqqarfan namiji Mai siffar gaske,
Sam babu alamar manyanci ko shekaru masu yawa sosai a bayyane dashi sbd kyan jiki
dakuma wani irin geamin dayake hakama tun farko haihuwace kawai ta wuri da Allah
yakawo Masa bawai Dan yanada wasu shekarunba badan duniya tasan shine ya Haifa
Inayah ba da bazaka dauka shine mahaifintaba,

Yanada wata irin siffar manyan matasan dasukai saurin aure da haihuwa Dan kuwa
yanzu yake cikin 40s dinsa,
Idan ba kamanninsa da 'yar tasa ka kallaba zaka dauka babban 'yayanta me irin Wanda
yabata tazarar Nan sosai da sosai Amma yanayin kamannin dogayen hancinsu da hasken
fatarsu da Shima yafita hasken sosai yasa kallo daya zakai musu kaga yanayi irin na
uba da 'ya.

Inayah dai kusan sbd mahaifinta buri da shaawar aure suka shigeta a farko sbd ji
daga umma yaganah akan abbinta Aqidarsace dadaddiya bazaiyi aureba saiya aurar da
ita sbd yanda abubuwa suka faru dashi acan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login