Showing 81001 words to 84000 words out of 124042 words

Chapter 28 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

68

Kira.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/3, 11:50 AM] MG: *_50_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ringing biyu wayar tayi anty Hafsat ta dauka tana cewa"

Dr Inayah majeed Yar gatan Abbinta Kuma amaryar Abbinta.."" ta qarasa zancen da Yar
dariya.

Sanyi jikin Inayah yayi tana Jin dadin kirarin Amma Kuma duk wannan yanason
kauduwa.

A sanyaye tace"

Anty Hafsat Yaya gida?
Ina my sweet Siyama?

Lfy kalau Inayah,
Ya kike?
Yasu umma yaganah da hajiya?
Ya abbin naki Kuma?

Bata tsaya amsa gaisuwar yasu umma ba tace"

Anty Hafsat Abbina ya canja sosai zuwan Haj umma
Kuma umma yaganah ta Hana nayi magana
Ni gaba daya Abbina yafara Zama kaman na nawaba.

Umman Dr Abdul tace na sauya bangaren Mata
Ni banganeba Anty Hafsat kizo gidan kigan yanda muke yanzu duk ba Dadi,

Ga Haj umma komai nayi saitace shiriritata da shirme kawai na iya.

Yanzu itace Mai kulawa da Abbi fa,
Umma yaganah ma yanzu Takoma Yar kallo abinci kawai take Masa.

Nidai anty Hafsat wlh bazan iyaba
Ina kallo Abbina ya Dena ji Dani kaman da
Bayan umman Abdul tace kamata yayi matsayina ya ninku tunda matsayina biyu
agurinsa.

Numfashi anty Hafsat ta sauke tana jinjina zantukan Dan duk da kusan a shagwabe da
damuwa Inayah ke fadan zancen idan ta fahimta Haj umma batai na'am ba haryanzu da
Inayah a rayuwar AA MAJEED barema ta dauki auren da mahimmanci.

Wani numfashi takuma sakewa tana ajiye ruwan data kawowa CM ta juya ta fice daga
palonsu zuwa dakinta Dan bazataso yaji zancen nasuba.

Tana Shiga daki ta zauna bakin gado tana cewa"

To kodai kina Mata abinda baimata bane Inayah?
A sanyaye tace"

Wlh anty Hafsat bana Mata komai
Kuma Ni bandamu data kaunaceniba
Nidai Abbina nakeson ya koma yanda yake kada ya rage ji dani.

Inayah duk wannan abin na tabbata Koda qwayar zarra kaunarki da matsayinki a
zuciyar Abbinki Bata raguba
Bama Zata taba raguwaba qaruwa zatayi sbd har Koda yaushe kece kaman strength
dinsa.

Kawai dai inaga aurenku ne Bata aminta dashiba sbd ganin kaman bazaki iya kalawa da
AA MAJEED dinba kinyi qanqanta....

Aikuwa wlh Ni inason auren yanzu bazaa rabani da Abbi ba,
Ko shima Ni Zan fada Masa inason aurena bazan rabu dashiba.

Da mamaki anty Hafsat tace"

Yanzu Kuma kinason auren kenan?
To kinason auren yanzu harzaki tsaya kina kallo auren na Neman fara rawan tun
baigama tsayuwa ba,

Wannan rashin amintar da Haj umma tayi kome zai iya faruwa
Dan kuwa ko auren be rabuba MAJEED Kam zai iya samun matar dazata kular Mata
dashi....

Wani mummunan faduwa gaban Inayah yayi ta tashi zaune ahankali dakyau tana cewa"

Sai tasashi yayi wani auren anty Hafsat?
Shima abbin sai yayi wani auren?

Wani mugun sanyi taji Yana shiga qafafunta tayi shiru tana jiran amsar anty Hafsat
wadda taji rashin kamatan yin zancen da Inayah Dan haka ta Dan gyara murya cikin
nutsuwa da kulawa da rarrashi tace"

Idan kika tsaya shirme nake fada Miki hakan kila zai iya faruwa,
Dan haka yanzu ki nutsu kema ki ringa kulawa da Abbin kaman matarsa sbd wannan
right dinki ne dake Zaki bawa kanki.

Kasa cewa komai tayi sbd jikinta daya Gama mutuwa da wani irin tsoro dan kuwa tana
fama da zuciyarta akan Haj umma idan Abbi ya auro wata Batasan ya Zata iya dauka.

Ganin ta Dena gane abinda take fada yasa Anty Hafsat yimata sallama da cewan Zata
shigo gobe Inshallah.

Aje wayar tayi hannuwanta na Dan rawar data kasa gane Kota menene.

Kasa qarasa cin abincinta tayi ta miqe tareda daukan tray din ta fita zuwa kitchen.

Tana ajiye kayan data kawo kitchen kasa juyawa tayi ta tsaya agurin tana shiga
tunani
Ita gabaki daya kanta ma ya toshe takasa gane komai,

Ita Abbinta kawai takeso ita kadai.

Juyawa tayi ta fito tana kokarin Isa hanyar bedroom dinta taji Qamshin Boadicea ta
dakata sbd tasan Abbinta ne yadawo.
Juyowa tayi tadawo palon daidai Yana shigowa sanyeda kaftan
Navy blue best kalar dayafi amfani da ita.

Ganinsa yasa idanuwanta cikowa da hawaye tanajin wani irin nauyi a zuciyarta da
abinda anty Hafsat ta fada dazu.

Kallonta ya qaraso yanayi zuciyarsa na tabuwa da kallonda take Masa idanuwanta da
Hawaye Wanda yasan na kewansa ne.

Ahankali ya bude Baki zaiyi magana ta fada jikinsa ta qanqamesa tana sako
hawayenta.

Shiru yayi Yana kokarin daidaita kansa sbd ba zatan datai Masa.

Qamshin Turarenta na black opium ya shiga hancinsa da kyau
Take yaji kansa ya Sara ya bude idanuwansa akanta tareda daga hannuwansa zai zareta
daga jikinsa Amma ta ture hannunsa tana sake shigewa jikinsa hawayenta na sake gudu
zuciyarta na bugawa da zancen anty Hafsat har lokacin.

Maqoshinsa yaji Yana Neman bushewa sbd yanayin yayi Masa nauyi Musamman Haj umma ko
umma yaganah wani zai iya samunsu ahakan.

Numfashi ya sauke ahankali tareda Dan nutsuwa cikin kulawa yace"

Me kikeyi Inayah?
Lafiya?
Akwai abinda ke damunkine?
Taso naji matsalar...

Girgiza Kai tayi tana qin sakinsa tace"

Abbi Dan Allah karka rabu Dani Ni inason auren....

Wani irin duka zancenta yayiwa zuciyarsa har baisan lokacinda ya rintse Ido
ahankali ba tareda budewa zuciyarsa na Neman yin sanyi sbd a bazata yaji zancen.

Ahankali ya daga hannuwansa Yakai kan hannuwanta Yana kokarin janyeta kenan saiga
Haj umma da umma yaganah kusan atare sun shigo palon kaman aike....

Da sauri Haj umma ta dakata tana kallon ikon Allah lokaci daya tana dauke idonta
Kuma.

Umma yaganah kuwa juyawa tayi abinta batareda ta tsayaba tana jinjina sangantar
Inayah sbd tasan itace me wannan aikin ba Abbin ba.

Ganin Haj umma yasa duk yaji yana sake shiga wani yanayi na sanyin jiki ya janye
Inayah din zaiyi magana ta sake komawa ta maqalesa tana cewa"

Abbi Dan Allah kabarni da aurena zanyi biyayya akan da....

Salati haj umma ta sake tana maido da kallonta kan Inayah dataqi Kota kan idonta
tabi.

Ba Shiri Haj umma ta kamo hannunta tana janyota gefenta tace"

Yaushe zakiyi nutsuwa nikam 'yar nan?
Yanzu uban naki kike damuqa haka gaban mutane kina maganar aure.
Tashi cikin turawa haukane akace Miki?

Maza wuce daki kisan abinda kikeyi
Mace da kunya da kamun Kai aka santa.

Haj umma idan na Kama kaina to Abbi zai iya auren wata yabarni da wannan auren..

Daga Haj umma har abbin kasa magana sukai sbd zancenta ya mugun Basu mamaki
Ya dago ya zuba Mata indanuwansa dasuka sake kashe Mata jiki tanajin kaman
zuciyarta Zata fashe akan kishin hada sunansa da wata takuma rabarsa.

Haj umma kuwa sake sallamawa Inayah tayi sai takasa cewa komai ta qwalawa umma
yagana Kira.

Umma yaganah najin Kiran tasan zaa Rina Indai akan MAJEED ne Inayah Bataji hakama
Haj umma da alama itama tanada aiki tunda tana cikin uwaye masu kishin yayansu.

Umma yaganah na fitowa Abbin na wucewa batareda ya tsayaba Dan baisan mezai iya
tsayawa saurara ba kuma.

Yaganah meyasa Inayah bakinta baya tauna zance ne?
Kunga illar rashin kwabarta
Gashinan sai zantuka takeyi marasa kan gado.

Cikin nutsuwa da umma yaganah tace"

Ya aka iya sai hakuri da addua Haj
Inayah din ce akwai kuruciya sosai atareda ita.

Fada Haj umma tafara Yi umma yaganah na Bata hakuri aka dai kashe maganar taja
Inayah zuwa daki.

Bataiwa Inayah fadaba sbd itama zuwa yanzu tafara ganin rashin kyautawar Haj umma
saidai Kuma bazata nuna hakan gaban Inayah ba sbd kada taci da ganin rashin
kyautawar Haj umma din.

Batace komaiba Dan batada abin cewar Dan haka ta juya ta fice Takoma aikin datakeyi
kitchen.

AA MAJEED na Isa bedroom dinsa zaunawa yayi kan sofa ahankali tareda Dan rintse Ido
Yana dafe goshinsa sbd Dan juyawar da kansa keyi.

motsawan da zaiyi Qamshin black opium ya Shiga hancinsa daga kayansa na Inayah Dan
haka ya miqe ahankali ya zare ya janyo towel maroon ya daura a qugunsa ya nufi
toilet Yana Dan sake dafe goshinsa.

Wanka yayo yafito ya shirya cikin Kelvin Klein sweatset yana qamshi Mai sanyi ya
fito ya nufi masallaci sallar magriba.

Tunda tadawo daki haka kawai takasa samun nutsuwa da sukuni tayita hawayenta tagama
ta tashi itama tayi alwawala tayi sallar magrib tana idarwa ta dauki wayar Neesah
daketa faman kiranta.

Sun jima suna waya tana Bata hakuri da qarfafa Mata gwiwa akan aurenta kafin suka
kashe.

Wanka ta tashi tayi sbd batai niyar fita cin abinci ba tana fitowa ta saka Riga da
wandon Balenciaga masu kauri tana kokarin hayewa kujera chatting ta tuna gargadin
Abbinta na rashin fitowa cin abinci Dan haka ta miqe da wayarta a hannu tareda zira
slippers ta fito tana qamshin black opium Mai sanyi.

Tana fitowa ta nufi dakin Haj umma ta Bata hakuri suka fito kusan tare zuwa dining
din haj umma na sake nanata Mata ta Dena sakawa ranta banzayen tunani akan MAJEED
sbd ubane agunta.

Batace komaiba har suka Isa suna Zama saiga Abbin ya shigo cikin nutsuwarsa da
kwarjini sai qamshinsa yakeyi komai nasa a kame da nutsuwa.

Zama yayi Yan gaidasu umma kafin ya kalli Inayah dake kallonsa cikin sanyi da
alaman ban hakuri.

Shikenan ya Isa"
kawai yace Mata ahankali cikin kulawa.

Murmushi tasake tana maida kanta ga abincin da aka dafa tuwon shinkafa da miyar
ganye masu lafiya da Naman kaza da kifi.

Bata fuska ta danyi sbd Bata cikason tuwoba Dan Haka kadan ta zuba tuwon tanaci da
spoon ahankali..

Shima abbin da spoon yakecin tuwon a natse.

Wayar Inayah din ce tayi ringing sunan Dr farhat ya bayyana akai ta saki siririn
numfashi tareda daukan wayar a gundure tace"

Dr farhat I will call you muna cin abinci.

Kashe wayar tayi Bata jira amsartaba ta ajiye.

Jin Dr farhat ce yasa Bayan ajiye wayar haj umma Dan kallon MAJEED fuska asake
tace"

Dr farhat nada kokari jiya ta hadani da mahaifiyarta mun gaisa sunada karamci
sosai....

Shiru kowa yayi harshi abbin.

Jin yanda Haj umma ke yabon Dr farhat yasa Inayah kasa shiru tace"

Haj umma Ni kullum fada kikemun Amma kinata yabon Dr farhat,
Bayan nice jikarki Kuma....

Da idon umma yaganah tai Mata tsawa tana hanata qarasawa.

Murmushi Haj umman tayi tace"

Ke dince su yagana sun sangartaki da yawa kin kasa sanin kin girma,
Bakisan abinda kikesoba da Wanda bakyaso komai fada kike...

Ni yanzu Abbi kawai nakeso bayanshi banason koma....

Qwarewa abbin yayi da abincin dake bakinsa yafara tari ahankali.

Da sauri ta dauki ruwan ta taso ta kawo Masa tana cewa"

Sorry Abbi,sannu...

Matsesa tayi gurin basa ruwan
Turarenta yaringa Shiga hancinsa take ruwan suma suka fara kokarin qwaresa ya ajiye
cup din Yana daidaita nutsuwarsa yace"

Thank you.

Kasa magana Haj umma tayi bakinta take ya mutu har aka Gama Babu Wanda yakuma
magana acikinsu.
##MAMUH#
#HOTLOVE/ROMANCE




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/3, 5:38 PM] MG: *_51_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Qin wucewa tayi bedroom dinta tabi bayan Abbi Wanda baisan tana bayansa ba Saida
yashiga palonsa taji mutum a bayansa Yana juyowa suka hade Saura kadan ta Fadi ya
tarota ta dawo jininsa.

Shiru tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa dayake kokarin hanawa karban kowane
yanayi.

Cikin nutsuwa ya zareta Yana cewa"

Meyake damunki ne kwanakin Nan Inayah?

Murmushi tasake tana kamo hannunsa bayan ya zauna itama ta zauna gefensa tareda
shige Masa sosai tana cewa"

Abbi Ni bansaniba ko nayi lefi yanzu ka daina ji Dani kaman da,.

Ko Dan Haj umma Bata Sona ne?....

Wani kallo ya juyo yayi Mata da idanuwansa dasuka Dan sauya cikin Dan fada yace"

Karki Kuma cewa haka,
Ki Dena hada matsayinki Dana ummana kowa matsayinsa daban...karna sake Jin hakan a
bakinki.

Ahankali tace"

Sorry Abbi na dena
Amma Abbi ai zaka barni a matsayin matarka ko?????.....

Rintse idanuwansa yayi da wani irin yanayi na mamaki da fara kosawa da zancen
Yaushe Inayah ta Zama haka akan aurene Bai saniba?
Bude idanuwan yayi tareda juyowa ya zuba Mata su gabaki daya Yana kallon bakinta da
yayi maganar zuwa kirjinta dake harbawa da sama sbd fargabar zancenta Mara control
daya sake fitowa bakinta ba Shiri.

Farare idanuwanta dake kallonsa cikeda kauna Mai girma ya maida NASA idanuwan Yana
kalla....

Hannunsa dake cikin nata takuma kamawa tana kallonsa a sanyaye.

Kasa cewa komai yayi Yana kokawa da tunanika dake yawo akansa Yana kokarin
kwantarda kansa.

Ahankali ta furta sunansa cikin wata kasalalliyar murya wadda ta sanya tsigar
jikinsa tashi sbd numfashi Mai dumi data furzo a fuskarsa bayan Kiran sunan nasa.

Ganin har lokacin baice komaiba sai idanuwansa Daya dauke ahankali daga kanta Yana
maidawa kan tv Dake kunne.

Ahankali cikin seta murya yace"

Haryanzu maganar aure Bata fita bakinkiba Inayah.

Yanda yayi magana da wata shaqaqqiyar murya yasa jikinta mutuwa itama ta kwantar da
kanta a kan hannunsa tana cewa"

Abbi Ni naka auren kawai nakeso yanzu ai.

Sake danne numfashinsa yayi Yana basarwa.

Sosai tayita yimasa fira wadda duka yawanci shagwabane ta ringa zuba Masa wadda
tagama take neman lalata kamewarsa da wuce tunaninsa akan yanda Inayah din take
abubuwan dabaisan a Ina tasaniba.

Tana tafiya dakinta ya miqe ya nufi toilet din bedroom dinsa Kai tsaye ya sakarwa
kansa ruwan dumi Yana lumshe idanuwansa dasuka sauya Yana sake riqe kansa da
kamewa.

Ita Kam tana komawa daki sallar ishai tayi zuciyarta cikeda farin cikin yau tayi
fira da Abbinta kaman da
Tayi Shirin bacci ta haye gado tayi kwanciyarta tana jin yanayi Mai qarfi fa girma
a zuciyarta gameda Abbinta Wanda takejin yanafin na dah.

Washe gari fes ta shirya cikin haricca long knitted skirt and blouse milk sai
vincci loafers ta fito ta wuce aiki Bayan taje ta gaida Haj umma
Umma yaganah Kuma tare sukai breakfast Abbinta Kuma Bai fitoba da alama Bai
tashiba.

Agurin aiki yau ma umma Hadiza tazo sunyi fira sosai kafin tadawo gida.

Tun a harabar gidan tasan anty Hafsat tazo sbd taga motar CM daya.

Batai tsammanin samun harda dr farhataba a gidan Dan haka duk fitarta da Anty
Hafsat Basu wani samu sinyiba gashi Haj umma ta cika kowa da kulawarta akan Dr
farhat wadda itama sosai take nuna Jin dadin hakan Dan tasan tagama samun guri a
gun AA MAJEED.

Har dare Basu samu sunyi maganaba yanda ya kamata saidai sama sama anty Hafsat din
tasake nanata Mata akan itace Zata gyara aurenta yazama kaman kowanne aure da
kanta.

Bayan tafiyar anty Hafsat da Dr farhat rasa abin kamawa tayi saidai ta shiririce
gurin waya da Neesah wadda suka qarasa shiriricewa akan firarrakinsu na Yan Mata
yanda suka Saba.

Sallar ishai tayi ta fito zuwa dakin umma yaganah sbd sunci abinci already tun dazu
taredasu Anty Hafsat.

Tana Shiga dakin zubbi tace"

Abincin Sir yazama ready zaa aje a dining ne kokuma zaa kai Masa dakin Haj umma?
Ko a palonsa zaa Kai?

Kallon Inayah umma yaganah tayi daga zaune tace"

Kije ki Kai Masa palonsa basai an jera a dining ba.

Fitowa tayi tareda zubbi batareda taje dakinta ta sauya kayaba ta dauki qaramin
tray din da tea ne akai sai faten dankali dayaSha kayan ciki da curry.

Kai tsaye palonsa ta nufa da tray din tana shakkar kada abbin yayi Mata fadan kayan
jikinsa sbd akwai sanyi gashi Riga da wandon baccine ajikinta masu santsi Kuma
wandon ba har qasa bane ko bra Babu ajikinta.

Tana shiga palon sanyin AC daya Gama gauraya da turarensa ta shaqa tareda nufan
table ta ajiye tray din tana dagowa Yana fitowa daga bedroom dinsa sanyeda pyjamas
shima
fuskarsa tayi fresh kaman baya Shiga Rana.

Akan kayan jikinta idanuwansa suka fara sauka ya dauke Kai Yana qarasowa ya zauna.

Zama tayi gabansa tana daukar tea din ta miqa Masa tana cewa"

Abbi barka da da fitowa.

Numfashi yafara saukewa ahankali kafin ya dago ya kalleta tareda sakin taqaitaccen
murmushi yace"

Barka Dr Inayah majeed.
Dadi taji sosai ta taso daga gabansa ta dawo gefensa kusa dashi sosai tareda dafa
cinyarsa Saura kadan ya qware da tea din dake bakinsa tayi saurin janye hannunta
tana kallonsa Dan itama batasan a cinyarsa ta Dora hannunba.

Daqyar ya hadiye Wanda ya kurba a bakinsa tareda juyowa ya kalleta idanuwansa na
gangarawa ga bakinta dake motsi tanason yin magana Amma takasa sbd idanuwansa dake
Neman rudar da ita.

Qamshinta ya shaqa ahankali tareda Dan rufe Ido ya bude Yana ajiye cup din hannunsa
ya juyo gabaki daya Yana kallonta
Magana yakeson yin Amma qamshinta yayi Masa yawanda yake kokawa da nutsuwarsa ya
hadiye numfashi ahankali zai bude Baki yace ta tafi tayi saurin Kai hannunta kan
bakinsa ta rufe sbd tasan korata zaiyi....

Saukar tafin hannunta Mai taushi akan bakinsa yasashi rufe idanuwansa dasuka sauya
ya bude ya watsa Mata idon numfashinta na shiga hancinsa tareda qamshinta Kai tsaye
Wanda yasa numfashinsa Dan sauyawa.

Janye hannunta yayi Kai tsaye Yana fuskewa tareda daukan cup dinsa yakai bakinsa
Yana kurba a natse yace"

Kije ki saka kayan sanyi ki kwanta akwai sanyi yau.

Zuciyarta dake bugawa da qarfi ta dafa da sauri tareda kallon gurin tana Jin yanda
bugun zuciyarta ke qaruwa.

Juyowa yayi ahankali ya kalleta Jin Bata motsaba
Yaga hannunta kan kirjinta dayaketa kaucewa kalla sbd yanayin datake ciki....

Sosai tsatsayyun kirjinta suka nuna basa batareda bra sbd yanda suke motsawa kadan
cikin santsin rigarta.

Kaman Mara lafiya ya dauke Ido daga kanta yakasa tambayarta lafiyarta data dafe
kirji sai kawai a hankali yace"

Kije ki sauya kafin sanyi ya kamaki.

Bata musaba ta miqe ta nufi kofa ta fice sbd bugawar da kirjinta yakeyi yasata
Shiga fargaba da tunanin itakuma.

Tana fitowa Palo suka hadu da Haj umma data fito daga dakin umma yaganah dubota da
ciwon kan datace tana Dan ji tun yamma.

Da boyayyan mamaki take kallon Inayah wadda ke tafiya a sanyaye hankalinta baya ma
kan Haj umma din Dan Bata lura da itaba.

Kai tsaye dakinta ta wuce tareda fadawa kan gado tana shigewa bargo ta lumshe ido
tanajin sabon feeling Mai qarfi akan Abbinta.

Daqyar tayi bacci da daren Dan haka tayi lattin tashi...

Shima Abbi ranar baisamu wani bacci ba Dan haka tunda safe ya shirya ya fice sbd
zuciyarsa dake buqatan iskan da Babu Qamshin Turaren 'yarsa ko kansa zai sake.

Da wuri Inayah ta dawo Dan kawai tasamu fira da Abbinta Amma Bai dawo da wuri ba
Qarshema ranar sai dare yadawo Bayan sunyita jiransa itada Haj umma Amma sai kusan
10 yadawo Kuma Kai tsaye yayi musu Saida safe ya shige sbd Yana tareda gajiya.

Haka Inayah taqi tafiya daki saida ta dafa tea takai Masa tareda cake Mara zaqi
sosai sbd Sam bayason zaqi ko kadan.

Haj umma na kallo Inayah taje palon nasa Kuma ta dauki mintuna sosai kafin ta fito
Wanda itakuma tsayawa tayi yafito daga bedroom Amma tayita jira Bai fitoba Dan haka
ta tahowarta ta wuce daki jikinta a sanyaye.

Washe gari haka abbin yakuma fitar safe Bai tsaya breakfast ba Kuma Bai dawoba sai
dare yauma.

Washe gari ma hakance takuma faruwa tun abin na Wasa saigashi Abbi ya rage zaman
gida Sam Baya Zama he's always busy Sam yaqi bawa kowannensu time sbd Haj umma
tafara tunkararsa da maganar Dr farhat Wanda Inayah Bata saniba batada labari
Umma yaganah ce kawai tasani Kuma taqi barin Inayah taji zancen sbd rigimarta.

Hankalin Inayah tashi yayi fiyeda komai,
Rashin lokacinsu daga Abbinta yasata sukukucewa ta daga hankalinta sbd tsoron ko
tayi wani lefin ne tunda itama tasan bataji.

Haj umma ma tashi hankalinta yayi tashiga damuwa tareda Dora lefin akan Inayah tayi
masa lefi ne shiyasa yake cikin damuwa Dan kuwa damuwa ta nuna sosai akan fuskarsa.

Jin Abbinta na cikin damuwa yasa hankalinta ninkuwa atashi Dena fita aiki sosai
tana Neman hanyar zaunawa da Abbin tabasa hakuri.

A bangare Daya pressure din da Haj umma ke basa akan ya aura Dr farhat yasa ciwon
Kai Mai tsanani kamasa qarshe ya Dena fita sbd Yana buqatan kansa ya sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login