Showing 72001 words to 75000 words out of 124042 words
cewa afadawa Abbinki kin daina rashin jiba?
Dawo zauna kici abinci.
Zubbi da sauri tasake matsowa cikin kulawa tana kokarin zuba Mata wani abincin sbd
wannan ya huce
Inayah din tace"
Barshi zubbi zanci wannan din ahaka.
Dawowa tayi badan tasoba ta zauna tana tura abincin.
Kasa riqe mamaki anty juwairiyyah tayi tana Satan kallon Haj umma cikin ranta tana
cewa"
Akwai matsala kuwa babba Dan haj umma tazo qarshen kishin 'danta kila Dan wannan
yariyar da alama tagama nisa a tabara Mai lasisi gurin MAJEED.
Koda aka gama cin abincin Saida umma yaganah tasa aka hada fruit salad takaiwa Haj
umma daki da kanta harya zauna sukai Dan fira duk da bawani fuska sosai gurin Haj
umma din.
Danta MAJEED kawai take buqatan yadawo ta rungumi abinta tashafa kansa ta tsiyayar
da hawayenta na shakarun rashinsa dake qasan zuciyarta.
Inayah kuwa hankalinta tashi yayi sosai Dan hakan Bata taba faruwa da itaba na
rashin Jin Abbi Kuma Bai sanar da itaba Ina yatafi Dan haka hankalinta yayi masifan
tashi daqyar taga safiya.
Duk Wanda yake gidan tun qarfe 6 na safe ta tadasu bacci da tashin hankali harsuma
duk saitasa hankalin kowa yatashi sbd kowa yakira wayarsa baya samu
Kosu Haj umma dake basuda numbernsa anbasu kowa yayita Kira baa samu.
Kuka da tashin hankali Babu wanda Inayah bata shigaba ba shiri aka nema CM suka
Samar dashi.
Baiso sanar musu tafiya AA din yayiba Saida yaga yanda Inayah ta dagawa kowa
hankali tukuna ya kwantar musu da hankalin tafiya majeed din yayi Kuma wayarsa da
basa samu sbd layin baya Aiki acan ne.
Hankalinsu ya Dan kwanta anty juwairiyyah Saida tayita fadan yanda Inayah ta dagawa
mutane hankali Batasan Haj umma nada hawan jini bane Zata kashe musu ita tunda
batada asara.
Itadai Inayah batace komaiba sai Haj umman dataje tabawa hakurin daga Mata hankali
datai taqara da cewa bazata sake ba.
Har dare ma still abbin bai kirasu ba haka jiki amace Inayah ta kwana,
Washe gari neesah Zata wuce Dan haka itace da kanta takaita airport tareda Safnah
suka rakata ta wuce.
Daga airport gidan anty Hafsat suka wuce.
Acanma anty Hafsat rarrashinta tayi tareda Bata qwarin gwiwa akan auren a fakaici
Dan kuwa suma basusan yaushe wannan auren zai Zama cikakke ga ma'auratanba Amma dai
kam Zata dage gurin ganin ta ingiza Inayah tako Ina tunda baruwan Inayah din ba
doguwar Noke Noke ta iyaba
Babbar matsalar da fargaban na gurin AA MAJEED Wanda kwata kwata matan ne basa
gabansa bare Inayah dayakewa kallon 'yar cikinsa.
Sai yamma tadawo gida bayan umma yaganah tayita kiranta tadawo gidan hakanan.
Koda ta dawo anyi sallar magriba Dan haka daki ta wuce Kai tsaye tayi alwawala tayi
sallar magriba ta zauna tana sake gwada kiransa Dana Neesah Amm duka Bata samesuba.
Ajiye wayar tayi ta nufi dakin Haj umma ta gaidata kafin ta fito ta wuce dakin umm
yaganah ta taddata tana waya da Yan uwanta dake maiduguri.
Zama tayi gefenta tan saurarenta harta Gama tukuna tace"
Umma yaganah ke kisake gwada Kiran Abbi ko zaa samesa.
Bara mugani to"
Nemo numbernsa tayi tasaka Kira Amma Bata shigaba Dole suka hakura.
Fira umman kewa Inayah Mai Kama da nasiha saiga Kiran Hadiza yashigo wayat umman ta
kalli Inayah tace"
Ga mahaifiyarki Nan nakirana.
Dauka tayi da sallama suka gaisa Hadizan ta tambaya ko AA MAJEED din yadawo daga
tafiya umma ta sanar Mata Bai dawoba.
Inayah ta tambaya cikin sanyin murya da jiki.
Kallon Inayah umma tayi kafin tace"
Lafiyanta kalau gatanan zaune Bata nabata ki gaisa.....
Aa,aa kyaleta tunda naji lafiyartama ya Isa zanci gaba da jira har AA din yadawo
kaman yanda nayi alqawari Inshallah Zan jira sai ranarda ya yafemun ya hadani da
ita Dan kansa Zan tunkareta.
Tausayin Hadizan yasa umma Dan rintse Ido tana cewa"
MAJEED baida matsala Inshallah idan Anbi komai a hankali zakiga da kansa zai
hadaku.
Godiya Hadiza tayi kafin sukai sallama suka aje wayar.
Inayah shiru tayi batace komaiba
Itama umman tana aje wayar batacewa Inayahn komaiba.
Tashi sukai Sakai sallar ishai suna gamawa Inayah tayi dakinta jikinta a mace
tanajin wata irin damuwa da tashin hankalin rashin ji daga Abbinta.
Wanka tayi tana fitowa ta sanya D&D off-white Riga da wando masu Dan kauri Amma
guntaye Dan wandon Bai Gama kaiwa gwiwarta ba Amma yanda Fadi sosai
Rigar kuwa daidai jikinta ce saidai yau tasaka condom bra.
Kanta farar qaramar wulace akanta data bayyanarda kusan Rabin gashinta dayake
sauran gyaran aurenta har lokacin.
Slippersta ziro ta fito qamshinta Mai dadi Yana tashi daga jikinta ahankali.
Tun kan ta iso palon anty juwairiyyah tajiyo Dan qamshinta Dan haka ta waiwayo tana
tallon hanyar kofar dakin Inayah din.
Dukkaninsu me zaune a palon har Haj umma da umma yaganah sun Dan zatawa sama sama.
Zuwansa yasa Haj umma kallonta ta dan dauke kai sbd kayan Inayah din kullum Babu na
arziki tasaba da rayuwar turai da sakewa a gida ba ruwanta.
Umma yaganah data lura da yanayin haj umma da Anty juwairiyyah dakewa Inayah kallon
mamaki
Saita miqe a Dan fuske ta kalli Inayah zatai Mata magana aka bude kofar palon Kai
tsaye Wanda yasasu juyawa duk su dukan sbd Babu mai shigowa Kai tsaye batareda
Danna doorbell ba idanba Mai gidanba dakansa.
Cikin nutsuwa kuwa yashigo sanyeda black Armani's fuskarsa fes tana daukan idon
kwarjini Mai tsanani,
Take qamshinsa ya doke Wanda Inayah tacikasu dashi.
Cak kowa ya miqe suna kallonsa dukkaninsu shima cak din ya tsaya yana
kallonsu.......
Inayah data Gama kallonsa cikin tsananin farin cikin ganinsa da Murna taje a guje
ta fada jikinsa ta maqalqalesa da wata irin kyakkyawar rungumar datasashi dafa
kofa.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/1, 11:02 AM] MG: *_45_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Kofa ya dafa da kyau sbd ba zato yaji ta jikin nasa....
Yaune Karo na farko data rungumesa tunda tayi girma tazama budurwa sosai,
Kuma yau shine Karo na farko da mace ta taba rungumarsa har kirjinsa dana mace ya
hadu.
Saurin janyeta yayi daga jikinsa Yana kallonta cikin yanayi na Dan kame yanayin da
dan fada kadan yace"
Ki nutsu mana,
Bakya girma ne haryanzu Inayah.
Bata fuska tayi idanuwanta nacikowa da hawayen dabatasan Kona menenba ta sake riqo
hannunsa tana riqewa sosai tace"
Abbi kasan yanda hankalina yatashi da tafiyar Nan taka?
Kowa anan yadamu Amma nafisu damuwa sbd baka taba fushi Dani irin hakaba...
Tafin hannunta ta sake sakawa cikin nasa tafin hannun ta riqe tana cewa"
Dan Allah kayi hkr Abbi bazan sakeba.
Dagowa yayi Yana kokarin janye hannunsa duk da tasaba riqe hannunsa sosai ko bayan
girman nata Amma yau din akwai mutane.
Kasa amsa Inayah din yayi idanuwansa nakan matarda yake son tabbarda idan
mahaifiyarsa ce daya rasa shekaru masu yawa,
Ummansa da Babu lakacinda zaizo qasar baije ya bincika lafiyartaba yaji yanda take
agurin Mai gadin gidan Wanda ya tabbatar Masa da Karya taba fadawa kowa zuwan nasa.
Anty juwairiyyah da ita mamaki da takaicin duniya yayi Mata yawa na Inayah ya kalla
ya tabbatarda itace take ya yarda da ummansa ce agabansa cikin gidansa Yaka gani.
Sukuwa dukkaninsu mamaki rashin kunyar Inayah sukeyi Mai girma Banda umma yaganah
datasan halin kayarta tasaba da hakan Amman yau abin yayi wani irine sbd agaban
hajiyar MAJEED dinne da yayarsa Wanda data kusada Inayah yashigo riqeta zatayi
bazata Bari tajeba koba komai ga kayan dake jikinta dasuka Santa su hajiyar mamaki
tun farko Dan su komai Inayah tayi haryanzu a mazaunin rashin kunya da da'a suke
sanyashi duk da sunada wayewa suma sunyi yawon qasashen Amma dai na Inayah ciwo
yakewa Haj sbd kishin kusanci da gata Mai tsanani da MAJEED yayiwa Inayah.
A hankali cikin nutsuwa da yanayin na mamaki da bayyanarda rauni sosai Wanda su
Inayah Basu taba ganinsa dashiba ya tako ya nufi gurin hajiya umma Yana sake danne
zuciyarsa ga raunin dayake bayyanarwa sbd baisan dalilinsu na Neman Inda sukeba
sukazo...ko haryanzu fushi ummansa keyi dashi.
Haj umma data fara hawayen ganin 'danta daya rabu da ita Yana matashinsa yazama
tamkar babban mutum,
Yazamar Mata wani kamilallan Alhaji komai nasa ya rikida Yakoma tamkar mahaifinsa
lokacinda yake daidai shekarunsa.
Kasa jiran ya Isa gabanta tayi sbd sanyin jikin daya nuna na shakkar fushinta
akansa
ta tako ta qaraso gurinsa itama da sauri ta rungume abinta tana fashewa da kukan
farin cikin ganinsa da jinsa.
Akaro na farko tun Bayan barinsa gida Yana dan matashinsa daya zubarda hawaye daga
idanuwansa.
Mahaifiyarsa dayake tsananin kauna a duniyarsa ta yafe masa,
Ta sauka daga fushinta na shekaru,
Yau itace agabansa tana kukan farin cikin ganinsa.
Daqyar hajiyar ta sakesa ta dago tana kallon fuskarsa da shima ita yake kalla
muryarsa a sanyaye yace"
Umma..kin yafemun?
Gyada Kai tayi da sauri tana hawaye tana murmushi duka alokaci daya tace"
Na yafe maka MAJEED,
Na yafe maka,
Nice nayi kuskuren bakaiba..
'dana yadawo gareni ya Allah nagode maka.
Ahankali ya Dan sunkuyar dakai Yana hadiye hawayensa cikin nutsuwa da farin ciki
Mai yalwa shima yake yiwa Allah godia,.
Kuma dagowa yayi ya kalli anty juwairiyyah dake tsaye itama tana kallonsa duk
tunanin duniya ya ninku akanta sbd ganinsa ya tabbatar Mata da arzikin dasuka gani
ma kenan Wasa ne,
Majeed din yakoma wani hakimtaccen namiji Mai zallar kwarjini da cika ido,
Ita kanta datake yayarsa Jin tayi tana Neman kasa hada Ido dashi Saida tayi da
gaske Bata Ankara ba taji bakinta na furta"
Sannu da dawowa MAJEED.
Qayataccen murmushinsa yasake cikin nuna farin cikin ganinta itama ya miqa mata
hannunsa daya Yana cewa"
Ina farin cikin dawowarku rayuwata kema anty juwairiyyah.
Dayake sun saba da shaking hannuwa tun suna Dan kaunar juna Dan haka ta miqa hannu
takama nasa tana bayyanarda farin cikinta na ganinsa itama.
Hannunsa cikin na hajiya da Anty juwairiyyah ya juyo ya kalli umma yaganah da
Inayah dake tsaye tana kallonsa da idanuwanta dasuka Dan sauya da yanayi Dan Jin
wani iri Abbinta zai Zama ba nata Ida kadaiba yanzu tunda family dinsa zunzo Bayan
tasaba da Baya hadata da kowa bare komai.
Kasa sakinsa hajiyarsa tayi Dole anan suka zauna duk da gajiyar tafiyarsa ta sakesa
take sbd farin cikin ganin mahaifiyarsa.
Cikin nutsuwa da sanyinsa yace"
Umma yaushe kukazo?
Waye yakawo?
Ya kukasan Nan?
Cikin farin ciki tace"
Majeed bazan taba iya rabuwa dakaiba yanzu sbd haryanzu Bayan ganinka ciwon da
zuciyata take na rashinka Bai dainaba..
Alhaji babbah da kansa yayi aikin mutum har gida aka taho damu Bayan Kiran waya
dayayita yimun..
Banda zabi Bayan zuwa din sbd Nima Ina Neman 'dana Ido rufe,
Meyasa katafi baka dawo gareniba MAJEED?
Meyasa baka taba waiwayataba majeed?
Kuka ta fashe dashi tana bayyanarda tsananin radadin da zuciyarta tashiga na
rashinsa duk tsawon lokacin.
Anty juwairiyyah ce dashi suka ringa rarrashinta Yana sake Bata hakuri akan
kuskuren rashin komawa dakuma kuskuren zaban tafiya yabarta,
Bai tsaya Jan tado zancenba ya yarda da suka shine mai lefin yabata hakuri tareda
alqawarin insha hakan bazata Kuma faruwaba.
Umma yaganah ma ta Dan saka baki tasake bawa hajiyan hakuri da adduar Allah ya
tsare gaba.
Inayah data matsu sugama tayi magana da Abbin ta matso tareda Zama gefensa daya
tana kallonsa cikin yanayin son magana zatai magana ya Dan saci kallon hajiyarsa
Dan yasan idan ba yanzu ta sauyaba zataji damuwar shigewar da Inayah Tai Masa Dan
haka cikin Dan kulawa da nutsuwa ya kalli Inayah din yace"
Inayah kina gaida hajiya yanda yakamata tunda tazo kuwa?
Kallon hajiyar tayi tace"
Eh Abbi kullum safe da yamma har dare ma wani lokacin.
Kuma tare muke cin abinci a dining.
Dan murmushi yayi Yana cewa"
Kin kyauta to.
Jeki ki saka kayan sanyi
Ana wannan sanyin Zaki fito haka?
Umma yaganah ya kalla yace"
Da mutane a gida shine take yawo hakan?
Kallon Inayah tayi tace"
Kasan Inayah ba Jin maganata takeyi sosaiba.
Abbi banajin sanyi fa,
Nidai Zan sauya Kaya Amma saika yafemun kadaina fushi Dani,
Abbi Dan Allah kayi hakuri ka daina fushi Dani wlh nafadawa umma yaganah nayi
alqawari ko sunan Heart bazan Kuma ambataba,
Ni har aurenmu ma na karba zanyi
Amma Dan Allah Abbi ka yafemun.....
Hawaye tafara tana riqeda hannunsa cikin yanayi da dana sanin lefin data aikatadin
duk da batasan takamaimai akwan wanne daga cikin lefin take fushi da itaba.
Nauyin mahaifiyarsa mai tsanani yakeji Musamman ganin duk sunyi zuru suna kallon
ikon Allah Dan Inayah dinnan tafara wuce tunaninsu
Gashi kaman majeed din biye Mata yake da alama shiyasa tabarar tata take yawa.
Zame hannunsa yayi Yana kallon umma yaganah yace"
Kuje ciki zamuyi magana gobe idan na nutsu.
Gangarowa hawayen Inayah sukayi tace"
Abbi gobe?
Nidai bazan iya bacci ba idan baka dena fushi daniba ka yafemun.
A natse ya juyo ya kalli fuskarta cikin kulawa yace"
Bana Hana wannan kukan ba?
Kije ki saka kayan sanyi
Anjima zamuyi mgn.
Ok Abbi" tace muryarta a sanyaye.
Tashi tayi ta wuce umma yaganah tabita suka Basu guri yabisu da kallo kadan sbd
yasan Inayah saitayi kukan idan suka Isa daki.
Baki sake Haj umma suke kallonsa
Ya dawo da kallonsa kanta Yana sake Jin farin ciki.
Bata Bari Inayah tashiga damuwarta akan danta ba sbd tasan Babu Wanda zai taba
samun matsayi irin nata a zuciya da rayuwar 'danta.
Anty juwairiyyah Kuma mamaki da tunanin zaman da Haj tace zatai a gurin 'danta
takeyi Dan kuwa akwai matsala.
Haj na kishin 'danta
Inayah ma da alama batason kowa ya rabi Abbinta sbd ta taso da kaunarsa da
kulawarsa akanta ita kadai Bai taba hada kaunarta da kulawarta da komaiba Dan haka
a take tagano Inayah ma zatai kishin wani ya rabi Abbin nata Wanda yake mijinta
yanzu duk da ba mijin ta daukaba haryanzu a Abbinta yake.
Hmmmnn""ta sauke ajiyar zuciya a fili.
Sun dade a palon sosai suna magana kafin yasamu ya nufi dakinsa.
Akwatinsa daya dawo da ita yafara ajewa closet kafin ya tube ya fada toilet.
Wanka yayi tareda alwala yafito sanyeda bathrobe fara ya nufi gaban mirror yafara
tsane jikinsa.
Bawani dogon shiri yayiba yagama ya tada sallar magriba da ishai dake kansa.
Inayah kuwa suna Isa daki ta zauna kan sofa tana kokarin tsaida hawayenta,
Umma yaganah Bata zaunaba tana kallonya daga tsaye tace"
Ki nutsu Inayah kisan yanzu bamu kadai bane a gidan akwai mutane,
Mahaifiyar majeed ake magana bazance kakarkiba yanzu saidai nace uwar mijinki ce,
Bakowane shiga zakina yiba yanzu sbd Bai kamataba,
Dacan dakikeyi baa hanakiba sbd mune kadai a gidan Kuma Kinga wancan lokacin
Abbinki mahaifinda ya haifeki muke mgn Amma yanzu hakan zai iya saka wani abin
daban Musamman agaban hajiyarsa sbd yanzu Kam mahimmancinta yafi na kowa da komai a
gunsa...
Shiru Inayah tayi Jin abinda umman tafada Kuma ya taba zuciyarta sosai dahar take
sake Jin zafi da ciwon rashin zamanta jinin Abbin.
Har umma yaganah ta fice shiru take tana kokawa da 'dacin ranta na cewan yanzu
akwai Wanda yafita matsayi gun Abbinta.
Hawaye taji suna neman cika idonta na kishin hakan itama,
Saidai duk matsayin hajiya agunsa batajin nata matsayin itama zai sauka sbd Abbinta
ai yanzu harda mijinta ya Zama Dan haka itama matsayinta biyu akansa bazata yarda a
qwace Mata matsayinta na Yar gatan Abbinta ba Kuma ai itace sanyin idaniyansa kaman
yanda kowa yasani Dole itama Haj umma tayarda da itace Yar lelen Abbi.
Ranta a cunkushe ta dauki wayarta dake ringing taga sunan anty Hafsat ta dauka tana
farawa da cewa"
Anty Hafsat Abbi yadawo,
Amma yanzu Haj umma ce.....
Tareta anty Hafsat tayi da cewa"
Ashe tashin hankali yaqare tunda yadawo
Kuma ya tadda hajiyarsa
Fatan dai Kun taru Kun tayasa Murna?
Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa"
Eh mun Masa Murna sosai ai tun baima dawoba kinsani.
Sanyi jikinta yayi ahankali tace,
Yanzu anty Hafsat Abbi zaifi son Haj umma akaina ko?
Murmushi Anty Hafsat tayi tana tausasa murya tace"
Inayah mahaifiyarsa cefa,
Tayaya bazaifi Sonta akan kowaba?
Ai uwa ba Wasa bace,
Kema Taki uwar duk abinda tayi haka zakiyi hakuri ki rungumeta sbd itama shedan ne
kawai yashiga zuciyarta bawai Dan bata sonkiba.
Banajin haushin umma Hadiza anty Hafsat Amma dai zuciyata tafi kaunar Abbi haryanzu
akanta sbd bansantaba,
Bantashi da kauna ko soyayyar uwaba saita uba Wanda kaunarsa ta ginu araina shi
kadai tun ina qanqanuwa,
Abbina Ni kadaice tasa Amma yanzu da hajiyarsa tadawo yafi Sonta akaina.
Kasa cigaba da magana tayi Tai sallama da Anty Hafsat din ta jefar da wayar.
Zubbi ce tai knockin tashigo dakin cikin kulawa tace"
Umma yaganah tace kifito zakuci abincin kowa yafito.
Gyada Mata Kai kawai tayi a gundure tace"
Kije am coming.
Bayan fitar zubbi Saida ta dauki mintuna tana danne damuwar zuciyarta kafin ta miqe
ta nufi closet dinta ta dauko dogon wandon Burberry kawai ta saka batareda ta sauya
rigaba ta fita.
##MAMUH#
##LOVE/ROMANCE/A&I
*_ZAFAFA BIYAR_*
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/1, 11:33 PM] MG: *_46_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tana fitowa Kai tsaye dining room ta nufa jikinta sanyaye da sabuwar damuwar data
saukar mata arai.
Da kallo suka bita data iso sbd ganin Bata sauya kayanba kawai dogon wando ta Sako
ta suturta dogayen qafafuwanta dake bude a fili dazu.
Zama tayi ahankali batareda tace komaiba.
Drink din da Umma yaganah tazo dashi daga kitchen ta ajiye kan table tana cewa"
Inayah kije ki sanarda MAJEED table yazama ready.
Tanajin haka ta miqe har lokacin jikinta a sanyaye ta juya Zata tafi saiga
qamshinsa yafara isowa take tasan yana hanyar shigowa ta dakata tana kallon kofar.
Reebok hoodie wears ne ajikinsa farare sai black Valentino slippers.
Fuskarsa fresh as usual kaman sabon saurayi ba damuwan komai saidai nutsuwa da
sanyinsa daya Riga ya kama rayuwarsa tun barinsa gida Dan haka wannan walwalar da
faran faran ba lallai yadawoba.
Inayah ya kalla da fararen idanuwansa take yagano sanyinta.
Ajiyar zuciya ya sauke a Dan takaice kafin ya kalli qafafunta yaga ba safa ga
kayanta dai ba wani na arziki bane.
Da kulawa yace"
Menene Kuma yanzu kike Bata fuska?
Ba nace abar kukan hakaba?
Biyosa tayi tana sake marairaice murya tace"
Abbi ni haryanzu Banga ka yafemun bane ai to.
Da nutsuwa yace"
Saikin Dena yawan kukan Nan da Kuma Jin maganar umma yaganah.
Zama sukai a dining Haj umma na kallon 'danta tana Masa adduar kariya daga mugun
Ido da mugun Baki sbd 'dan nata tubarkallah yakoma Mata tamkar ba itace ta
haifesaba fes kaman Dan baqaqen larabawa.
Cikin girmamawa ya sake gaidasu Haj umma kafin suka fara cin abincin.
Inayah ta zuba Masa abincin iya yanda tasan yanaci sai gashi ko farawa baiyiba Haj
umma tace"
Majeed ko abinci bakaci sosai kenan yanzu?
Murmushi yasake ahankali Yana diban brown rice din yakai bakinsa yace"
Kusan komaiba ya canja umma ai.
Murmushi tayi itama tana cewa"
Duk da hakan Bai kamata kana Wasa da abincinba duk busy din dazaka Zama kuwa,
Yaganah haka kuna kallo yake Wasa da abinci?
Wani rolling da Ido Inayah tayi cikeda mamakin zancen hajiyan tace"
Abbi da daddare ne bayacin abinci sosai Amma ba ranarda Zan bar Abbina da yunwa tun
dama can....
Dangwalar cinyarta umma yaganah tayi alaman tayi shiru Amma hakan kawai takejin
bazata Bari Haj umma ta nuna tafiya son Abbinta ba.
Cikin nutsuwa da kulawa Abbi yace"
Keep quiet Inayah.
Ba abinci kike ciba har kike tsayawa zance.
Bakin nata ne ai Ni Naga gabaki daya kaman bakwa kwabarta,
Kaida yaganah Kun taru Kun sangartata qatuwar budurwa kaman wannan da ta Isa ace
tuni tana gidan miji Amma tana zaune ka Gama tabarar da ita magana daya biyu sai
kuka,
Wannan ma banajin likitar gaske ce Dan ko kanta Bata Gama saniba bare marasa
lafiya.
Shiru dukkaninsu sukayi suna sauraron jininin hajiyar wadda sangartar Inayah tafara
isarta Dan kaman MAJEED din yagama shiriricewa akan 'yar Sam Baya wani tsawatarta.
Inayah kuwa raurau tayi da Ido tareda kallon Abbin zatai magana da fararen
idanuwansa yayi Mata alaman tayi shiru kartayi magana.
Hadiye maganarta tayi tareda kokarin miqewa Zata