Showing 33001 words to 36000 words out of 124042 words

Chapter 12 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

358

bada himma ki nutsu kisamo wani
Natsatsen mijin ayi Miki aure ki Haifa 'yayanki irin Siyama din,
Abbinki ma Kinga kin Haifa Masa jikoki acikinsu zai darje amaryarsa dal a leda.""

Da dariya ta qarasa zancen
Itama Inayah dariyar tayi tana kwatanta ranarda Zata Haifa nata 'yayan,

Irin qaunar da Abbinta ke mata zatawa nata 'yayan
Suma tasan Abbinta zai sosu tunda 'yayan Inayarsa ne.

Haka kawai burin ganin hakan shima ya shigeta a fili ta tace"

Idan na haihu shikenan Abbi ka Zama grandfather?

Dariya yasake ahankali Yana cewa"

Inayahn Abbi ma shikenan ta Zama uwa ko?

Dariya tasake tana sake cewa"

Abbi zanji kunya idan kana fada da kanka fa.

Ok ya Isa haka Time to sleep,
Umma yaganah taje ta kwanta Inshallah zuwa gobe Zata fara fita asibiti.

Ok Tom Allah ya kaimu Saida safe."" Cewar umma yaganah daya fadawa maganar.

Amin, goodnight Abbi.

Goodnight Inayah.

Suna Gama wayar Inayah ta saka numbern Neesah ta Kira.

Neesah ma tana ganin numbern Nigeria tasan Inayah ce Dan haka da sauri ta dauka
tana cewa"

Meyesa kika dauka lokaci kafin ki Kira??

Dariya Inayah tasake tana miqewa daga palon ta nufa dakinta Dan tasan doguwar Hira
zasuyi da Aminiyar tata.

Aikuwa sabuwar Hira suka dasa Dan tunda suka hadu basu taba tafiya Mai tsayin data
rabasu ba irin wannan.

Sai dare sosai ta Gama wayoyinta ta miqe ta nufa toilet tayo wanka tazo ta kwanta.
Washe gari wuni tayi a daki tana dube dube a waya da laptop sbd asibiti da Zata
fara zuwa,

Abbinta yafison tafara aiki a asibitin gwamnati kafin taci gaba dayi a asibitin
kudi sbd shi qwarewarta yakeso a aiki bawai samun ilimin abuba kawai aiki dashi
yafi buqata.

Kasancewar Bata Gama hada emails dinta aka fidda ba dama sauran uzurirrika yasa
dole a satin Bata fara zuwaba Saida sukai kwana goma Sha biyu da Zuwa Nigeria din
tafara fita.
##MAMUH#
#A MAJEED/INAYAH
#LOVE/MARRIAGE



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/12, 8:26 PM] MG: *_20_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ranarda tafara fita aiki tareda Safnah sukaje sbd driving din Nan Sam batajin Zata
iya,

Driver ne yakaisu babban Lagos State general hospital.

Dr Abdulsamad salees ne likitan da CM yayiwa magana Musamman Dan ya ringa kulawa da
aikin Inayah din dakuma guiding nata sbd yanayin asibitin Nan da can Inda tayo
karatunta dabam.
Dr Abdulsamad kallo daya yayiwa Inayah ya fahimci hankalinta ya 'dan tashi da
asibitin sbd yanayin hargitsinta,

Shima ba wani jimawa zaiyi a asibitin ba shekara daya zaiyi yakoma Abuja can
asibitin dayake aiki,
Yanzu watanninsa hudu anan din.

Qayataccen murmushi ya sake Mata Yana kallon yanda hankalinta yake Neman sake tashi
duk da yasan tasan duk Mai aikin ceton Rai da lafiya Baya kasancewa Mai tsananin
qyanqyami sbd aikinsu Bai gadar musu da hakan ba.

INAYAH" yakira sunanta cikin kulawa da sakewa fuskarsa daukeda murmushi.

Kallonsa tayi da idanuwanta a natse itama ta amsa da"

Yes Doctor.

Muje afara shigarda isowarki da fara aikinki.

Wucewa sukayi a jere Yana sake Jan hankalinta gameda wasu abubuwa da yanayin
asibitin.

Gyada Masa Kai takeyi tana saurarensa a natse har suka Isa sukai abinda zasuyi suka
fito.

Safnah Bata tsaya jirantaba sbd dama iya rakiyarce tata Dan haka tareda driver suka
koma gida sukabar Inayah din.


Har qarfe biyu suna tareda Dr Abdul suna fama da patients,

Ba laifi taji dan dadin aiki dashi Dan kuwa sosai ya Bata kulawa da tattali
Gashi ya kware sosai akan aikinsa.

Sai kusan karfe 3 tadawo gida a matuqar gajiye.

Wanka tafara yi tareda wanke jikinta sosai Dan kayan data dawo dasuma daga Palo ta
ciresu tabawa zubbi akai laundry dasu.

Sallar la'asar da aka Gama tayi Dan tayi azahar acan.

Tana idarwa Bata nema abinciba kwantawa tayi tayi baccin awa daya da rabi kafin ta
tashi Takoma toilet tayo brush ta wanko fuskarta ta fito tana duba wayarta dake
silent.

Miscalls din Abbinta ne guda biyu saina Neesah ma kusan hudu saina Mimi mahaifiyar
Safnah 'daya.

Dakin umma yaganah ta nufa tana Kiran wayar Abbi.

Bai dagaba tasan dama zaiyi wuya ya daga waya lokacin Dan haka Bata sake Kiran
kowaba ta ajiye wayar tana Zama gefen umma yaganah dake kallonta cikin kulawa tace"

Umma yaganah yunwa zai kasheni.

Murmushi umman tayi tana cewa"

Ahakan Zaki Zama yanda Abbinki keson ki Zama?
Bana gane wannan yanzu umma yunwa nakeji sosai fa,
Banci komaiba a asibitin
Bazan iya Shan koda ruwaba a asibitin Gaskia,
Dr Abdul yaso muje restaurant naci abinci Amma bazan iya cin komaiba batareda nazo
na cire kayan jikina nayi wankaba.

Zubbi ta qwalawa Kira da muryarta Mai sanyi ta gajiya.

Zubbin a kusa take dama Dan tana Palo tana gyaran yamma shiyasa taji Kiran tazo.

Yes Ma gani.

Zubbi ki kawon abinci.

Ok.

Juyawa tayi ta fice tareda nufar hanyar kitchen.

Brown rice da chilled chicken akai su Kuma aka zubo Mata sai ruwa Mara sanyi sosai.

Taci abincin sosai ba laifi kafin Tasha ruwa ta bawa zubbi kayan ta maida.

Sai alokacin tadawo daidai dan haka takuma daukan wayarta tafara Kiran Neesah.

Maganganunsu sukaita Yi tsayin lokaci kafin suka Gama wayar.

Bata Kira Mimi ba sai bayan sallar magrib shima sbd ta sake kirantane.

Gaisawa sukai a mutunce sai Mimin data ringa tambayarta aiki cikin nuna kulawa.

Sosai taji dadin yanda Mimin ta nuna kulawarta harma ta ringa janta hira.

Sun jima suna wayar kafin suka Gama bayan ta Bata Safnah sun sake gaisawa itama Tai
Mata sannu da gajiyar yau.

Sbd tasan Zata fita ko goben yasata kwanciya da wuri bayan tayi sallar ishai.

Abbinta ma saidai Tai Masa text ta tura Masa ta kwanta.

Washe gari akan lokaci ta shirya ta fito cikin blue skinny jeans da farar laced
chiffon top Mai Fadi sosai.

Black Prada strap sandals ne a qafarta sai black Prada handbag.

Ko data fito driver na jiranta Dan haka tea da cake kawai taci ta fice.

A hanya tayi waya da Abbinta harsuka Kai tana waya dashi
Saidata Isa office din Dr Abdul ta kashe wayar.

Cikeda nutsuwa tayi knocking tareda bude kofar ta shiga da sallama tana kallonsa
Yana zaune Yana waya da mahaifiyarsa.

Ahankali bude Baki tayi cikin nutsuwa tace"

Good morning Dr.

Murmushi ya sakar Mata Yana cewa"

Morning Dr INAYAH.
Murmushi kawai tayi tana nufar gurin Zama ta zauna itama tana duba tata wayar.

Tanajin yanda yake waya da mahaifiyarsa cikin nutsuwa da tsananin so da kauna.

Yana gamawa basu wani Bata lokaciba suka fita zuwa aikinsu.

Yauma kaman jiya sai 3 suka baro asibitin.

Yau ko firar Bata samu damar tsayawa Yi da umma ba suna sallar ishai tashige ta
kwanta Dan yau din hartafi jiya Shan wahala.


Cikin kwanaki kadan tafara sabawa da rayuwar fita aiki kan lokaci da Kuma sabo da
shiga jama'a sosai sbd a asibiti Dr Abdul likitan jamaa ne yanada farin Jini da
mutunci sosai a idon mutane Musamman patients dinsa,

Sam baida qyama ko kasalar aiki
Sosai yake sakewa da marasa lafiya ya dubasu yanda Yakamata.

Ita kanta zuwa lokacin tayi wani irin sabo dashi hakama itama sbd aiki tareda a
qarqashinsa yasa ta koya sabawa da patients tana Dan sake musu haka.

Yanayinta da yanayin rayuwarta yasa kusan da yawa asibitin suka santa duk da tana
sabuwar zuwa,

Yanda take gudanar da rayuwarta yasa kusan duk akasan ba anan tayi zamaba a waje,

Gashi batada wasu shekaru masu yawa Amma har ta kammala karatunta hakama ba laifi a
iya Yan 'daidaikun dasukasan mahaifinta sunsan ita kadaice 'ya gurin mahaifin nata,

Batada wulaqanta mutane Amma tanada Dan wuyar sabo sbd rayuwar gata da shagwabar da
ita da mahaifinta yayi
Duk da hakan Dr Abdul yana taimakawa sosai gurin koyar da ita yanda zatai hulda da
jama'a Musamman patients sbd yanda zatai hulda da jama'a kam Abbinta Bai koyar da
itaba sbd ko jama'ar Bata wani shiga sai yanzu da rayuwarta ta Zama ta jamaa cikin
lokaci qanqani.

Dr Abdulsamad kyakkyawan matashin likita ne Dan asalin Adamawa,
Qwararre ne akan aikinsa haka Kuma yasamu nasarori da cigaban rayuwa ta fanni da
dama sbd aikinsa.

Aikine kawai yakeyi a Lagos din Amma ba anan yake zaune ba tun farko.

Baida Mata Kuma Bai taba aureba hakama baida wata tsayayya dayake nema
Hasalima Bai taba Jin soyayyar mace sai akan Inayah wadda ganin farko da yayi Mata
yakamu da
Love at first sight.

Ganin yanayin rayuwar Inayar yasa Bai nuna mataba Kuma Bai sanar Mata ba sbd Dan
sanin dayayiwa mahaifinta na career dinta yakeson fara tsayar Mata kafin komai
Dan hakan shima ya tsaya akanta yaga komai ya tafi daidai.


A bangaren gida kuwa da qarfi da yaji su Mimi sun Zama iyayenta sbd wata irin
kulawa da kaunar dasuke nuna mata daga Mimi har daddyn harma da anty Hafsat.

Tafi Shiri sosai da anty Hafsat akan Mimi sbd ita Mimi uwa ta dauketa anty Hafsat
din Kuma tamkar babbar yayarta ta dauketa,
Shirinta da anty Hafsat Yana Dan Kona ran Mimi Amma dai idan ta duba kusanci da
INAYAH din tasamu da Safnah sai tanajin sanyi sanyi.


Cikin yardar Allah Saida sukai wata uku harda kwanaki kafin Abbi ya diro qasar.

Tana gurin aiki ya iso Dan haka a kaqe take data dawo gida tagansa.
#MAMUH#
SORRY SHORT CHAPTER###AMUN UZURI PLEASE.



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/13, 3:15 PM] MG: *_21_*
*_Arewabook@Mamuhgee_*
Tana isowa gidan tun a compound tasan Abbi yadawo gida sbd ganin sabuwar motarsa da
tunda sukazo take a gefe rufe ruf Amma gatanan a fake gefe da alama da ita aka
daukosa daga airport.

Kofar palonsu ta dosa tana warware nadin qaramin gyalen dake kanta tun daga hanya
Tana isa ta bude kofar Kai tsaye ta shige.

Bakowa a palon sai Qamshin RoseNight da Sanyin AC daya Gama cike palon
Saikuma qatuwar tv dake aiki ba murya sosai.

Su zubbi da Salimat tuni suka Gama aikinsu suka nufi bangarensu tunda Mai gidan na
gari Dan haka idan ba aiki ba Babu abinda zai Kuma shigowa dasu saikuma idan
kiransu akai.

Dakinta ta nufa direct ta tube tafada toilet tayi wanka ta fito daureda towel.

Kiran Dr ne yashigo wayarta da sauri sauri ta dauka tace Masa"

I'm kinda busy
I will call you.

Aje wayar tayi tareda nufar gaban madubi ta shafa Neutrogena oil dinta ta fesa
spray kawai ta koma gurin kayanta ta saka wata chiffon wide neck gown Mara nauyi ta
ziro slippers ta fito ko wayarta Bata daukoba.

Kai tsaye hanyar palon Abbi ta nufa tana tunanin yanda ya shammaceta Saida yadawo
ya fada Mata da ba lallai ta jima gurin aikinba ayau.

Da farin ciki bayyane kan kyakkyawar fuskarta tayi knocking kofar harso biyu kafin
taji muryarsa daga ciki a natse ya furta"

Yes Inayah,
You can cm in.

Shigowa tayi da sallamar dake bayyanarda farin cikinta na ganinsa ta qaraso har
gefensa ta zauna tana cewa"

Abbi kana tunawa danima kuwa?
You look more than cool and calm.

Wani qayataccen murmushi Mara sauti ya sake Yana kallon yanda itama tayi Yar rama
ta yanayin aikin data samu kanta aciki da cikakkiyar kulawa yace"

Dr INAYAH A MAJEED ko gaisuwa babu tukuna kafin complains su biyo baya.

Cikin murnarta tace'

Abbinah barka da dawowa
Munyi kewarka
Kagani har Rama nayi sbd ban saba dadewa hakaba bakanan,
Ga stress na aiki.

Yar dariya kadan yayi Yana cewa"

Duk kokarin Dr Abdul akanki menene da stress acikin aikin?

Dr Abdul yana fadamun irin kokarin da kike keep it up okay.
Tun yanzu Ina alfahari da 'yata Zata Zama babbar likita wata ran.

Taji dadin kalmomin nasa Dan babu abinda yafi komai faranta ranta kaman ta faranta
ran mahaifinta harya bayyanarda hakan.

Firar familyn CM tafarai Masa tana sanar dashi irin kulawa da kaunar dasuke Mata
harma da umma yaganah.

Sosai yaji dadin hakan Kuma a gaban nata yakira Cm yayi Masa godia a gajarce na
yanda iyalansa suka karbi nasa iyalin da hannu babbiyu.

Daganan firar Dr Abdul suka koma wadda kusan duk Rabin firar itace taketa fadar
halayen Dr Abdul din dakuma yanda take kulawa da tattalinta.
Abbinta saurarenta kawai yakeyi Yana nazarin irin shaquwar data samu da Dr Abdul
din lokaci daya,

Yana fatan alaqar da tsaya iya ta aiki sbd irin wannan yabo da Inayah ke Masa baya
fatan tasake shiga wata soyayyar yanzu Musamman ko Dan yanayin weak heart nata
Duk da wani bangaren Dr Abdulsamad ya kwanta Masa sosai a Rai.

Sai dare tabaro gurin Abbin Dan abincima acan palonsa sukaci tare sbd shi kansa
yariga yashige ne bazai fitoba sai gobe shiyasa shima Bai fito main hall ba cin
abincin dare.

Tana baro palon Abbin gurin umma taje sukai Saida safe ta wuce daki ta kwanta bayan
tayi waya sama sama da Dr Abdul akan daga gobe a
Shift din dare zasu sake komawa.


Washe gari da safe batada zuwa asibiti Dan haka baccin safe tayi sosai sai 11 ta
fito lokacin Abbi baya gida ya fita.

Sanye da Riga da skirt na atampa ta fito tana waya da Neesah.

Breakfast tayi ita kadai sbd tasan ko umma ta jima da yin nata.

Tana gamawa ta nufi dakin umma yaganah acan tayi kwanciyarta tana chatting sama
sama saiga su Mimi sun taho gidan dukkaninsu yiwa Abbi barka da zuwa aikuwa take
gida ya kaure da hayaniya.

Mimi harda tsarabar wasu kayan atampopin tayiwa Inayah aikuwa umma ta gode Mata
sosai itama Inayah din tanajin dadin kayan Dan haka ta gode mata.

Dakinta suka koma itada Safnah suna firarsu ta matasan 'yan mata,

Fira suke akan anty Hafsat da Bata isoba sun biya sun ajeta gidan yayar mijin
qanwarta dasuke tsananin mutunci sosai, daga can zaa kawota Nan din.

Saida suka gama cin abincin Rana kusan karfe biyu da mintuna kafin Anty Hafsat ta
iso gidan.

Da farin cikin ganin siyama Inayah tarbota tun daga harabar gidan.

Faruk Ismail shine Wanda yakawo anth Hafsat daga gidansu.

Kallo daya yayiwa Inayah yaji Tai Masa sbd shima tunda yayo karatu a Malaysia
yadawo yakasa ganin macen datai Masa gashi dama iyeyensa sun takurasa akan aure.

Ganin dayayiwa Inayah da yanayin gidan nasu yasa Kai tsaye ya 'dan fahimci wayayyu
ne jama'ar gidan,
Da alama sun danyi nasu yawon bude Ido wata qasar.

Inayah gabaki daya batama wani lura dashiba sbd hankalinta dake anty Hafsat da
Siyama tana murmushi dukkanin kyanta na Kuma bayyana.

Anty Hafsat ce ta juyo ta kallesa tana cewa"

Ok faruk nagode sosai
Ka Isa gida lafiya.

Gyada Kai kawai yayi tareda tada motarsa yabar harabar gidan ya fice Yana ayyanawa
aransa shikam yaga matar aure irin class dinsa dayakeso.
Inayah kam Anata bangaren ko kula batai dashiba Dan a daukarta driver nema yakawo
antyn.

A gidan suka wuni Anata fira da hayaniya sai yamma da Abbin yadawo aka kaisu
palonsa suka gaisa a matuqar mutunce da girmamawa.

Sai dare suka tafi bayan Abbi yayi musu kyautar kudi na Musamman ga Yara.

Inayah Jin tayi kaman kada su tafi sbd yanzu da qarfi da yaji tafara sabo da
rayuwar hayaniya Dan duk Wanda zai Yi rayuwa a Lagos dolensa ya koya daukan
hayaniya duk da sukam anguwarsu batada abinda ya hadata da hayaniyar ko hayaniyar
ma Kai securities basa Bari magana suke maka sbd gudun shiga haqqin wasu.

Suna tafiya itama wanka da sallar ishai kawai tayi ta shirya cikin Riga da wandon
Adidas sai qaramar veilhijab da jakar Nike data goyo ta fito tana qamshi Mai sanyi.

Umma yaganah ce ta rakota har kofa ta fito tana saka wayarta silent.

Abbinta ne da kansa zai kaita Dan haka gaban motar tashiga suka fice ta waiwayo ta
kallesa cikin Yar shagwaba tace'

Abbi kaman karnaje Allah
Yau ban wani hutaba sbd baqi da akai.

Murmushi kawai yayi Mata yana cewa"

Zaki Saba Inayah.

Tura Baki kadan tayi tana lafewa jikin kujera.

Suna Isa asibitin Dr Abdul ma na isowa da 'yar qaramar motarsa.

Ganin Alhaji MAJEED dinne dakansa yakawo Inayah yasa Dr Abdul qarasowa cikin
nutsuwa da tsananin girmamawa ya gaida Abbin Yana cewa"

Barka da zuwa Sir.

Kallon Abdul din yayi da kyau cikin sake karantar nutsuwarsa ya gyada Kai shima a
natse ya amsa da cewa"

Thank you Dr,
Ya aiki?
Ya fama patients da Inayah?

Murmushi yayi Yana Dan sake kallon Inayah dake kallonsa fuska asake
Ya kasa maida kallonsa sosai akan AA MAJEED din sbd tsananin kwarjini da cika Masa
idon da yayi uwa uba ga wata irin nutsuwa da kamewa atare dashi,

Shima Adidas dinne a jikinsa black masu hade da hula yayi fresh acikinsu sosai
tamkar sabon saurayi Mai tashen samartaka Dan kuwa shi Yama kasa yarda da shine ya
Haifa zuqeqiyar budurwar 'ya kaman Inayah.

A hankali yace"

Lfy kalau alhmdllh Sir.

Ok Tom Allah ya taimaka
Thank you ko.
U're welcome Sir.

Jan motar Abbi yayi yabar gurin
Suma suka dunguma zuwa ciki.

Washe gari qarfe 8 tadawo gida wanka kawai tayi ta shige bargo sai bacci.

Bata farkaba sai 1 na Rana shima Kiran Anty Hafsat ne ya tadada.

Saidatai wanka tayi sallah taci abinci kafin ta Kira anty Hafsat din wadda tuni
takira umma yaganah ta sanar mata 'dan Yar uwarta yaga Inayah din ya rikice musu
tun jiya.

Umma yaganah Bata wani dauki zancen da mahimmanci ba saidai tace musu ya nema
Inayah din da kansa idan sun daidaita ai shikenan haka akeso.

Kasancewar Inayah din batada wani saurayi ko daya yasa bata wani damuba tabawa anty
Hafsat damar gabatar dashi din.

Ranar farko daya fara zuwa gidan Abbinta bayanan yayi tafiya zuwa Kano da CM Dan
haka basu wani samu damuwaba ko fargaba daga ita har umma yaganah.


Faruk Ismail kyakkyawa ne ba laifi Kuma Dan boko da gayun gaske,
Ya waye sbd Yana ganin yayi karatu a Malaysia saidai Kuma daya Gama sanin
cikakkiyar waye Inayah da mahaifinta sai ya Dan sassauto daga 'dagawar dayake Yi na
shi baa Nigeria yayi karatu ba,

Shi karatun kawai yaje yayo yadawo ita kuwa acan taqarasa girma acan tayi karatu.

Ranar Ashe Bai yiwa Inayahn kallon tsaf ba sai yau din daya Gama kallonta a natse
Yaga irin kyan siffa data fuska dama sanyin halaye so innocent take yaji ya mutu
akanta.

Cikin sanyi da sakewa irinta wayayyu take komai uwa uba ga shagwaba data Zama kamar
halinta sbd tasowarta a shagwaben Dan haka tasaba komai Kai tsaye da gaskiyarta
take yinsa.


At first Bata tsaya ta karanta Faruk ba sai daga baya daya Gama karantar shikam ya
dauki duk wata hanyar mallakar zuciyarta,

Tsananin kulawa da kauna Mai girma yake nuna Mata tareda wata irin soyayya.

Shikansa yayi mamakin daya iya soyayya lokaci kankani sbd Bai taba soyayyar ba.

Halayensa na kulawa da zallar soyayya yasa tuni itama tafada soyayyarsa Mai qarfi
taqarasa mantawa da Zaid gabaki daya da babinsa.

Soyayya Mai qarfin gaske sukewa junansa cikin watanni kadan
Ga Dr Abdul dayake fama da tsananin Sonta Amma haka yabawa kansa hakuri ya danne
tunda anriga ansha gabansa.

Abbinta Bai damuba sbd tako Ina ya bincika iyaye da familynsu faruk din basuda illa
Kuma tunda tagama karatu yanzu baida damuwa da aurenta koba komai auren ne next
dama Dan haka yabawa faruk din Daman neman Inayah din.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
#MAJEED/INAYAH/MARRIAGE



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/13, 5:45 PM] MG: *_22_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Lokaci ya tafi sosai dan tuni maganar aurenta da Faruk ta Gama kammaluwa aka saka
lokacin biki hankalinta Dana faruk din ya kwanta sbd wata irin soyayya ce sukeyi
Mai zurfi da qulafucin juna.

Shi kansa Abbin hankalinsa yafi kwantawa sosai da aurenta da Faruk akan can baya da
Zaid.

Ba maganar komawarsu Australia saidai idan sunje hutu saikuma Abbin da shikam zai
ringa zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login