Showing 48001 words to 51000 words out of 124042 words

Chapter 17 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

78

Kuma ganin
'yartaba Wanda haukar da Allah ya taqaita Mata lokacinda tayi danasani tashiga
Neman yarta to haukar zatayi yanzu matuqar takuma rasa Ayshatouh.

Hankali tashe ta fito motar da gudu ta nufosu Inayah tana Kiran sunanta.

Dakatawa umma yaganah tafarayi tana kallon Hadizan kafin Inayah itama ta dakata
suna kallonta cikeda mamaki.

Inayah kuma umman na isowa gabansu ta kalleta da kyau taga yanda idanuwanta da
fuskarta sukai jajir tashin hankali bayyane kan fuskar umma Hadizan
Wani mummunan bugawa zuciyar Inayah tayi har Saida ta dafa Neesah dake gefenta.
Muryarta na rawa itada umma yagana ma data shiga zullumin abinda zasuji Dan dagani
ba lafiyaba murya a hautsine sukace"

Umma Hadiza....

Kasa tambayar abinda ke faruwa sukai sbd tsoron abinda zasuji.

Kai tsaye Inayah taji wani jiri na Neman dibanta kafin tayi kokarin dafe kanta taji
muryar Umma Hadiza a hargitse tana cewa"

Dan Allah kadaku tafi wlh qasar zaku Bari kuna fita,
Aurenki Inayah da Abdul bazai fas....

Inayah Bata gama jiba qafafuwanta suka yanke zuciyarta na neman bugawa ta tabbatar
fasa aurenta yanzuma akai ko ake neman Yi.


Innalillahi wainnan ilaihrrjiun"
Mezan gani hakan Ni yaganah,
Innalillahi, innalillahi.

Hawayene ke kokarin gangarowa Inayah Amma tashin hankali yaqi Bari umma yaganah
dasu Neesah da duk suka shiga tension din suka fara kokarin kamata sukoma ciki da
ita

Umma Hadiza ma cikin tsananin tashin hankali da dimuwa ta ringa maimaita ba fasawa
nace anyiba Dan Allah Inayah karki shiga wani hali,
Babu fashi aurenki da Abdulsamad,
Zaa daura zamu tafi dake adamwa zan Baki duk wata soyayyar uwa da Baki samuba,
Inayah, Inayah.

Sam Inayah Bata gane kalma daya da umman Abdul din take fada sbd zuciyarta bugawa
takeyi sosai da tashin hankali da attack data samu take Dan hakan komai Bata ganewa
sai rawa da jikinta keyi.

Su umma yaganah kuwa take ta fara tunanin daqyar idan umman Abdul nada lafiyar
qwaqwalwa sbd duk tabi ta rude da Kiran Inayah da suna biyu.

Abbi da hankalinsa nakan CM dayazo daukansa su wuce daurin auren tare Bai lurada
Hadiza ce tashigo a motar Dr Abdul ba Saida yaji salatin da umma yaganah ke qwalawa
da qarfi hankalinsu duk yakoma Kai cikeda mamaki da zafin zuciya Mai qarfi ya kalli
umma Hadiza Yana kallon 'yarsa dake Neman siqewa cikin tashin hankali numfashinta
na neman gagararta.

Cikin bacin Rai Mai qarfi ya qaraso gurin tareda kallon umma yaganah yace"

Ku kaita ciki Dr farhat ta dubata da sauri.

Kan umma Hadiza dake kokarin binsu hankali tashe ya maida kallonsa idanuwansa na
Neman sauyawa yace"

Ni Zaki sama da duk abinda kikazo dashi,
Me kika fadawa Inayah yasata cikin wannan halin?

Ganin su umma yaganah Basu qarasa shigewa da Inayah ba yasashi juyawa tabiyo
bayansa tana cewa"

Dan girman Allah da manzansa kaban 'yata,
Ka sanar da ita nice mahaifiyarta,
Dan Allah kada ka cutatar da uwar dake cikin qunci tsawon shekaru ta hanyar Hana
Mata 'yarta....

Babban palonsa suka shigo ta tsaya gabansa idanuwanta na zubda hawaye sosai cikin
mawuyacin hali tafara rokonsa akan ya sanar da Inayah itace mahaifiyarta.

Mamakine ya Kama CM dake tareda A A MAJEED din tako Ina.

Idan ya fahimta Kuma yagane wannan matar Inayah take Kiran 'yartace.

Itace mahaifiyar Inayah?

MAJEED da idanuwansa ke bayyanarda tsananin bacin ransa da fushinsa ya kalla yasan
yau kam ransa yakai kololuwar baci tunda ya bayyanarda fushinsa.

Bai iya cewa umma Hadiza komaiba sbd baimasan mezai fada mataba,
Da alama tanada ciwon Kai Dan hakan tako Ina lalata Masa Al'amura zatai.

Cikin kosawa da ganinta gabansa ya bude Baki a gundure yace.

"Me kika fadawa Inayah da har kika data cikin wancan halin datake ciki?
Idan kin sanar da itane matsayinki a gunta kinyi babban kuskuren da....

Cikin sauri da bayyanarda gaskiyarta ta katsesa da cewa,

"Banfada Mata komaiba
Maganar aurenta da Abdul kawai nake fada musu.

Wani irin rufe Ido yayi ya bude cikin baqin ciki da takaici yace"

Kinsan shima hakan matsalar da Zaki haifar mata?
Kinsan halinda Zata iya Shiga akan hakan?
Meysa zakiyi kutse acikin Al'amarin da bakisan Yaya yake tafiyaba?

Numfashi Mai zafi ya sauke tareda fitarda ajiyar zuciya Dan bazai iya wannan tashin
hankalinba yanzu.
dauke kallonsa daga kanta yayi a natse yace"

Idan harkina kaunarta a matsayin uwa kaman yanda kika fada kibarta taci gaba da
rayuwarta batareda kin dandana Mata 'dacin rashin karbuwa daga uwar data haifeta
kokuma dacin hanyar da aka samar da ita.

Maganarsa ta qarshe tayi mummunan girgiza,
Kenan shima daukan yake ta hanyar banza ta samu Inayah tunda yaga ta gudu tabarta?

Wasu hawayen baqin ciki Mai tsanani ne suka gangaro Mata ta dago da jajayen
idanuwanta ta kallesa zuciyarta na quna da bacin Rai tace"

Na tsaya rokonkane ka bayyanarwa 'yata nice na haifeta sbd nabaka haqqinka
amatsayin Wanda ya reneta da Amana ba cutatarwa bawai Dan narasa damata ta uwa
agaretaba.

Kanason nuna dukiya ka rabani da 'yata rabuwar har abada Amma hakan bazai taba
karbuwaba gurina.

Wlh bazan yardaba Sharia Zata karbamun 'yata tadawo hannuna.

Mamaki tafara basa ta yanda take iya furta kalamai batareda taji kunyar kantaba na
abinda ta aikatawa 'yar a baya harma dashi.

Idan tana maganar qarfin ikone
To zai nuna Mata qarfin iko akan Inayah.

Cikin sautin bayyanarda gajiya da lamarinta yace"

Wannan shine Karo na qarshe da Zaki iya zuwa gidana ko kusantar daya daga cikin
iyalin gidana,
Zaki iya tafiya.

Kallon baqin ciki da damuwa lokaci daya take Masa tace"

Zantafi Amma kasani nice uwa dana Rena cikin Inayah nakuma haifeta har abada babu
wani ko sunan dazai sauya mun matsayi akanta,
Nice nafi kowa cikakkiyar dama da iko akanta,

Kaikuma damarka da ikonka akan Inayah ya tsayane a matsayin mariki Kuma zai tsaya
ahakan ne har abada.

'ya mace ce duk iko da isar da zaka nuna akanta saitabarka har abada sbd aure
zatayi take gidan wani Kuma a qarqashinsa Dan hakan idan kafi qarfin hukuma
bazakafi na shari'a ba,

Sharia Zata dauke inayah daga hannunka tabani 'yata,

Idanma shariar kafita ikone zamuga wannan sbd duk ikonka akanta bazaka taba
aurentaba Dan kuwa aurene kawai zai riqe 'ya mace aguri wani ikon ya kasa dauketa
dauketa
Kuma da yardar Allah Inayah bazata rufa wata a hannunkaba saina karba Yana Koda ta
hanyar kawo Mata wani mijin auren ne.

Rintse idanuwansa yayi cikin takaici da baqin cikin ganin Hadiza agabansa.

Duk shekarun mace hankalinta da tunaninta na banza ne lokuta da dama,
Sam kansu toshewa yakeyi hat basusan me suke fadaba.

Idan Hadiza na tunani haryanzu akan shari'a Zata karba Mata Inayah a hannunsa to
zai sakata a spot dinda ko shariar bazata iya dauke inayah daga hannunsaba a gurin.

Bai iya kallontaba sbd siqewa kai tsaye yace.

Kije Ina jiran shariar.

A fusace da baqin ciki ta juya tana hawaye sbd ba haka tasoba son tayi ya amince ya
hadata da 'yarta idan Tai Masa barazana da sharia sbd tasan bazai taba son duniya
tasan Inayah ba 'yarsa bace.

CM da kansa yayi matuqar daurewa da daukan zafi kusan yagama gano kan zancen shine
Inayah dai ba Amininsa neba ya haifeta Kuma wannan matar itace mahaifiyar tata.

Baisan ya zancen yafaruba Amma tabbas a wannan tsukakken yanayin yasan akwai
matsala Babba matuqar wannan Al'amarin zai shafa daurin auren yau.

Agogo A MAJEED ya kalla yaga Sha daya da rabi harta fara wucwa.

Bai iya cewa Amininsa komaiba yace su tafi kawai.

Shima CM tunda ba qaramin yaro bane yasan yanzu ba lokacinda zai tsaya tambayar
MAJEED din meyake faruwa bane saidai idan an natsa zafi da dacin ransa ya sauka.

Suna fitowa Kai tsaye yabawa Bosco odar kada akuma barin motar Abdulsamad tashigo
gidansa matuqar bashineba aciki.

Kai tsaye babban masallacin dake kusada gidan iyayen CM suka nufa Inda anan ne zaai
daurin auren dama.

Mutane ne tako Ina sun cika anguwar ga securities da jamiaan tsaro kusan tako Ina
sbd akwai manyan mutanensu dasun iso tuni Dan mintuna goma Sha takwas suka rage ga
daurin auren.

Wani irin zafi da 'dacin zuciya yakeji ganin tarin jama'ar dasukazo Dan sheda
daurin auren ga dangin Abdul ma da dama sun iso shi kansa Abdulsamad din ya iso
gurin cikin shigar alfarma ta angon dake cikin tsananin farin ciki.

Qarfe goma Sha biyu daidai aka nutsu aka fara daurin auren Wanda CM ne da kansa
yayi wakilcin Amarya mahaifinsa Alhaji babbah yayi wakilcin Ango sauyin daya faru
tsananinsu take agurin.

Kafin iyayen Abdulsamad su Ankara sukaji ana shelar an daura auren ABDULMAJEED
ABDALLAH da INAYAH A MAJEED.
#MAMUH#
#AFADA ALKHAIRI KO AYI SHIRU/#MASU YI DANI A BAYANA.



*_ZAFAFA BIYAR_*

*_INAYAH_*
_Mamuhgee_

*_GURBIN IDO_*
_Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/18, 10:01 PM] MG: *_30_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Kusan da yawan jama'ar gurin Basu fahimci wane ABDULMAJEED din ake nufiba sai Amin
kawai suke amsawa da ita suna qarawa da adduar zaman lafiya da albarkar aure sbd
sunan Abdul din da aka ambata cikin sunan basu wani bambamceba tunda dai kowa yasan
sunan Ango Abdul.

Iyayen Abdulsamad Wakilansa sune suka saki Ido da Baki cikin zallar mamaki da
firgici Jin andaura da wani Abdul din daba nasuba Dan Babu Wanda ya tsaya kawo wani
rubabben tunanin AA MAJEED mahaifinta ake nufi.

Shi kansa Abdulsamad kasa tantance meyake faruwa yayi saiyafara tunanin ko matsalar
fadan sunan aka samu Mai fadar be kila ya rude ya fada sunan mahaifin Inayah a
matsayin uba Kuma yadawo ya fada amatsayin Miki Wanda aka daura auren dashi.

Jin zuciyarsa dai takasa yarda sai tsinkewa data farayi yasashi kokarin baro Inda
yake Dan zuwa gaban wakilan daurin auren yaji wane rudadden ne Mai sanarwar dazai
saka kansa kuncewa da zancensa.

Kusan dai jama'a tsakani da Allah duk Basu ganeba idan ba wainda suke Yan uwan
Abdulsamad ba sbd suka Sarai sunji ba sunan angonsu aka fadaba
Sauran jama'a da Basu ganeba tunda ba hankali mutane ke badawa sosaiba gurin daurin
aure sai an daura zu amsa da Amin da fatan Alkhairi su tafi Dan haka aka ringa
gaggaisawa ana Allah sanya Alkhairi ana neman fara watsewa.

Ciki mamaki Mai tsanani da kokarin danne bacin Rai yayan Marigayi salisu ya kalli
CM da Alhaji babbah kafin ya maida kallonsa kan AA yace"

Alhaji MAJEED mufa bamu gane abinda yake faruwaba anan,
Auren da zaa daura biyu ne Daman kokuwa dai Wanda zamu daura dinne aka daura da
wani 'dan ba namuba?
Dan idan naji daidai sunan yarinyar dai shine wadda zaa daurawa danmu da ita.

Duk Inda damuwa da 'dacin Rai Dana zuciya suke sune a dabaibaye da A MAJEED,
Bai taba samun kansa a yanayi Mai 'daci da qaqa nikayiba irin wannan Rana,
Ko a wancan lokacin daya hadu da qaddarar samun Inayah baishiga damuwa da quncin
dayake cikiba yanzu.

Me zaiyi da auren 'yarsa ta kansa?
Wace mummunar masifa Hadiza ta sakasa daya qare qarshe a auren Inayah 'yarsa??

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Yau shima yahadu da qaddarar Sharrin shedan Dana zafi da yanke hukunci cikin fushi.

Duniyama idan taji shine ya aura 'yarsa zai anyi Allah wadai da tunaninsa.

Gashi garin yanke hukunci kada Hadiza ta ra'bi Inayah har Inayah tasan bashine
mahaifinta ba yaje cikin fushi da bacin Rai yayi abinda ba iya Inayah kadaiba da
bayason ta taba sanin bashine ya haifetaba duniyama kowa zai sani yanzu Wanda harga
Allah yaso riqeta amatsayin ya har abada batareda kowane Dan Adam yasan bashine ya
haifetaba sbd daga lokacinda mahaifiyarsa datafi kowa saninsa da tarbiyarsa ta
tuhumesa tareda yarda da zai iya aikata Zina harma ya Haihu a hanyar Zina yasaka a
ransa ya karbi Inayah amatsayin 'ya dabazai taba barin wani yasan bashine ya
haifetaba ciki kuwa harda mahaifiyarsa saigashi Rana tsaka Hadiza ta sakasa a
mummunan tarko.

Hadiza itace masifar rayuwarsa yau ya tabbatarda hakan sbd akaro na biyu takuma
sakasa masifar da kusan tafi ta baya yaqare da rataya igiyoyinsa na aure a wuyan
'yarsa baisan wane mummunan Al'amarin Zata Kuma kawo masaba a gaba Dan yasa zaifi
wainnan zauta Kai da qwaqwalwa.

CM ne yayi saurin kallonsu Alhaji buhari ganin ransu yafara baci sosai sunason Jin
bayanin abinda yake faruwa Dan haryanzu sunkasa yarda da auren matar 'dansu aka
daura da wani sbd har lokacin Babu Wanda yakawo da AA MAJEED aka daura auren tunda
ba abune Mai yiyuwaba uba ya aura 'yarsa Dan hakan kaf gurin Babu Wanda yakawo
ABDULMAJEED mahaifinta ake nufi suma su CM da Alhaji babbah sunqi barinma agane
wane ABDULMAJEED Dadi da qari kusan duniya da AA MAJEED tasansa bada cikakken
sunansaba ABDULMAJEED ABDALLAH.

Cikin qarfin hali Abbin yataso Yana sallama da mutanensa dake wucewa suna Masa
Allah ya sanyawa auren 'yarsa albarka Yana amsawa da amin.

Kaurewa da gurin yayi da jiniyar motocin 'yan sanda da civil defense ga yawan
jama'a kowa nata kokarin miqa barkarsa ya wuce shiya taimakawa su CM gurin Jan su
Alhaji buhari zuwa cikin gida palon Alhaji babbah Wanda shine da kansa ya iya fara
tankwafarsu sbd fadan tozarci dasukagani qarara dasuka fara yi.

Alhaji buhari ne mai iya dan danne tsananin bacin ran dasuke ciki su Alhaji kabiru
'yan Nan Hadiza kuwa kasa dannewa sukai suka fara zuba masifar tashin hankali Dan
duk Inda ake wulaqantawa an wulaqantasu ankuma tozartasu sun debo jiki tun daga
adamawa sunzo Lagos daurin aure ace suna zaune suna kallo kaman wasu gumaka
andaurawa amaryar aure da wani koma Dan uban waye ai Basu cancanta wannan
tozarcinba.

Abdulsamad a rikice cikin tashin hankalin daya zaburo Masa tako Ina ya ringa kutsa
jama'a Yana neman iyayensa maza dasune wakilan Amma Bai gansuba Dan haka ba Shiri
ya zare hular kansa Yana Jin akwai gagarumar matsala Mai tsananin girman gaske
kuwa.

Saida mutane suka rake sosai aka fara Ankara da abinda yafaru ganin rudewa da
tashin hankali da Abdulsamad yake ciki da yawa wainda suka dauka sune basuji sunan
daidaiba suka fahimci cewan daidai sukaji Ashe auren ne dai bada Dr Abdulsamad aka
dauraba.

Take kurar hayaniya tafara kaurewa daga gurin
Ganin Abdulsamad na Neman zarewa yasa Abbi daya Gama sallamar baqinsa ya Kama
hannunsa sukai cikin babban gidan na Alhaji babbah.

Qanin CM Professor Ibrahim shine ya tsaya yaqarasa sallamar sauran jama'ar aka
watse wasu nata sake sawa auren albarka wasu Kuma na shiga mamaki da son Jin yanda
wannan mugun Al'amarin yafaru hakama wasu take suka ringa maimaitawa wainda
basujiba cewan sunan fa AA MAJEED ne aka daura dashi.
Mamaki da firgici wasu suka Kuma shiga Jin sunan Wanda aka daura dashi din aikuwa
take tun anan suka fara shigar da gulmar Internet.

An watse tsaf ba kowa Dan hakan Alhaji babbah ya kalli su Alhaji buhari dake cikin
mummunan yanayi na bacin Rai da fushi.

Cikin sanyi da taushin murya ga Wanda baa kyautawaba yace"

Alhaji buhari kuyi hakuri nasan baa kyauta mukuba tako Ina Musamman da baa sanar
daku komaiba ko fahimtar daku komaiba Saida kukazo cikin baynar jama'a hakan
tafaru.

Dr Abdulsamad dake tsiyayar wasu ruwan zufan tashin hankali da fita hayyaci ya
kalla duk saiyaji jikinsa yayi sanyi da tausayin Abdulsamad din sbd duk Wanda ya
kallesa yasan yana tsananin son Inayah so Mai tsanani,
Tayaya Za'a kallesa ace Masa uwarsu daya,
Uban ne kawai Basu saniba ko dayane tunda A MAJEED cewa yayi uwar kawai yasani
itama a bisaga qaddara.

Shi kansa Dr Abdul idanuwansa duka da hankalinsa suna kan Alhaji babbah sbd ya
fahimci agurinsa zasuji abinda suke buqatan ji Wanda zuciyarsa ayau harbawar datake
yasan ta wuce kowane irin tsari da akeson zuciyar Dan Adam ta buga.

Babu wani yaren dazai gane ayanzu idanba na maganar aurensa da Inayah bane.

Dan jinjina maganar dake bakinsa Alhaji babbah yiyi tareda dauke idanuwansa daga
Abdul ya maida kan su Alhaji buhari dasuke manya zasu fahimtarsa a natse yace"

Ita wannan yarinya Inayah wadda mahaifiyar Abdulsamad ke Kira da Ayshatouh 'yar
mahaifiyar Abdulsamad ce wadda ta jima da Bata tun jarinta Wanda A jiyan bayan
haduwar mahaifin Inayah Wanda yanzu zance mijinta da ita mahaifiyar tasa suka
tabbatarda Dr Abdulsamad da Inayah uwa dayace ta haifesu,

Dr Abdulsamad da Inayah uwarsu daya Kuma kaman yanda duk muka sani Babu aure
tsakaninsu,

Sauyin Wanda aka daura dashi Kuma wannan nine Nan na tayasa yanke wannan hukuncin
sbd kaman barazana da ita mahaifiyar yarinyar takeson tayiwa MAJEED Dan hakan muka
yanke hukuncin ya aureta.

Dan haka a taqaice ABDULMAJEED shine ya aura AYSHATOUH INAYAH,
Shine mijinta ayanzu,
Sauran bayanin Inda ita mahaifiyar Dr ta samo yarinyar har suka Zama uwa daya da Dr
wannan saidai aji daga gareta.

Wani mummunan shock da matsiyacin zufane ya fesowa Alhaji kabiru zuciyarsa na
harbawa da mamaki ya juya ya kalli malam Umar Dan uwansa Wanda harya fisa jiqewa
jagab da zufa.

Alhaji buhari daya Gama samun qullewar Kai da mamaki da Yar rudewa yace'

Inayah kuma Yar Hadiza?
Tayaya?
Garin Yaya?
Yaushe?

Shaqewa muryar Alhaji kabiru tayi a Rikice murya na yankewa yace"

Inayah itace AYSHATOUH????
'yar da Hadiza ta Haifa ranarda mahaifiyarmu ta rasu??

Da tashin hankali malam Umar ya karba da cewa"

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun
Tabbas Hadiza ta haifi 'ya takuma saka Mata Ayshatouh.,
Idan har ya tabbatarda Hadiza ce dimun wadda tabar Masa 'ya to tabbas kuwa wannan
'yar ta Hadiza ce halak malak sbd ranarda ta haifeta ranar tabar gida.

Sai alokacin zufa ta karyowa Alhaji buhari Jin dai ta tabbata Hadiza haihuwa tayi
ba aure bayan rasuwar salisu.

Da sauri malam Umar daya fahimci tunanin dake zuciyar Alhaji buharin yace"

'yar Hadiza 'yar halak ce
'yar sunna Dan kuwa cikinda salisu yabarta dashine muma sai daga baya muka Ankara
da hakan Dan haka 'ya 'yar halak ce
Uwarsu daya ubansu daya da Abdulsamad gashinan zaun....." Ya qarasa fada Yana
waiwayawa Inda Abdulsamad ke zaune sai kawai sukagansa zube baya numfashi da alama
ya jima da sumewa Basu saniba sbd tashin hankalin da kowa yake ciki.

Arikice Alhaji buhari yayi kansa shida malam Umar suna Kiran sunansa Amma da alama
ba sumar kadai yayiba kaman harda attack yasamu.

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun""Alhaji buhari yake fada Yana kamo Abdulsamad din
da qarfinsa
Ba arziki Dole zaman bayanin yaqare sukai asibiti dashi hankali tashe.

Bayan fitarsu kallon Abbi Alhaji babbah yayi yana nazarin halin tsananin damuwar
dayake ciki da rashin ta Ina zai Kama wannan rakitaccen Al'amarin.

Tausayinsa ne Dana Abdulsamad ma dayafi kowa tausayi yanzu Dan yasan Al'amarin zai
daki yaron sosai sudai dama saukinsu da hamdalar dasuke shine da baa daura aurenba
da komai yafi lalacewa uwa daya uba daya.

Bayason qarawa MAJEED damuwa da wasu zantukan Dan haka ya taqaita da cemasa,

"MAJEED kaje gida kasamu ka nutsa kanka ya sake kafin shima Abdulsamad asamu
lafiyarsa saiku zauna duka kuyi taron fahimtar juna,

Itama yarinyar kada kace zaka kasa karban wannan qaddarar sbd ko ahakan Allah
ikonsa ne ya nuna,
Haisawa sukace matar mutum kabarinsa
Allah yayi itace matarka shiyasa Bai baka ikon aureba tun kuruciya har gashi
manyanci nason zuwa hakama rabon zamtowarta matarka ya hadaka da mahaifiyarta harta
dawo hannunka dan ka tarbiyantar da matarka da kanka Dan haka shi Allah Babu
ruwansa idan ya jarabta mutum to akwai tanadin dayayiwa wannan bawan idan har yayi
tawakkali yacinye wannan jarabawar.

Allah yasa mudace,
Allah Kuma yabaku zaman lafiya yasawa wannan auren albarka.

"Amin" CM ya amsa adduar ta Alhaji babbah Yana cewa"

Allah yaqara girma.

A natse MAJEED shima yayiwa Alhaji babban godia kafin suka fito.

Dayake da lafiyayyar Lexus din CM sukazo Dole shine ya maidasa gida.

Suna Isa gidan Yana ajiyesa harabar gidan yakira matansa yace kowaccensu ta fito su
koma gida sbd yasan ba qaramar rigima zaayiba idan zancen auren ya Isa cikin gidan
tunda duk matane bare ita kanta Inayah din
Gwara idan zatai Rigimar ya Zama ba kowa a gidan.
##MAMUH#
#LOVE/MARRIAGE/ROMANCE#




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/19, 9:15 AM] MG:

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login