Showing 39001 words to 42000 words out of 124042 words

Chapter 14 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

83

kulawarsa harma da alqawuransa yasamu yashiga
zuciyar Inayah din.

Wannan karonma ba Bata lokaci ya aiko iyayensa da maganar aure.

Abbin yaso su saurara Kar ayi rushing din Al'amarin Amma Dr sadeeq din ya dage da
iyayensa har abbin ya yarda.

Dr Abdulsamad kusan zaucewa yayi da wannan maganar auren Kuma Saida kusan kowa
yakusa gane halinda yashiga,

Kasa hakuri yayi sbd zuciyarsa bazata iya daukaba yabi ta qarqashin qasa ya lalata
auren ta hanyar tona asalin waye Dr Sadeeq Kuma can ma gidansu anty Hafsat akai
fitinar ta hada 'dan uwanta da 'yar gaban fatiha tunda ba uwarsu dayaba.

Wannan karon har asibiti Inayah ta kwanta ciwo sosai sbd zuciyarta tafara kasa
dauka
Abubuwan sun fara tabata sosai.

Hankalin umma yaganah da mahaifinta ya tashi sosai sbd Saida suka dangana da zuwa
Australia taga likita acan tayi jinya
Ta huta kanta ya Dan sake kafin suka dawo.

Ciwonta ba ita kadai ya taba ba harda Dr Abdul Wanda shima hankalin mahaifiyarsa
yafara tashi da wannan mummunan masifar dake tunkarota 'dan ta namiji guda datake
alfahari dashi Yana Neman samun tabin qaqwalwa akan son mace.
##MAMUH#
#AA MAJEED#
#AYSHATOUH INAYAH#
#DR ABDUL SALEES/HADIZA



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biyaπŸ‘‡
07040727902

MTN cardπŸ‘‡
09134848107
[10/15, 2:11 PM] MG: *_24_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Alaqarta da Anty Hafsat Bata taba girgiza ba sbd fashin auren da aka samu akaro na
biyu saima tausayin juna dasuke,

Su suna ganin qoqarinta da tausayinta akan yanda taketa kokarin hada Alkhairi Amma
Alamuran na lalacewa,

Itama tausayin Inayah takeji sosai sbd yanda Inayah duk tabi ta sukurkurce akaro na
uku da fashin auren.

Alqawari tayi bazata qara kawo kowaba ya nema auren Inayah tun basu fara tsanartaba
Amma duk mijinta Inayah Zata aura alqawarine ta dauka itace Zata jajirce su tsaya
sosai da umma yaganah suyiwa Inayah gyaran gaske da duk wainda sukaiwa kansu
hasarar rashin aurenta sai sunyi kukan baqin ciki da Dana sani.

Yanzu sosai take tsoron kula mazama kwata kwata basa ranta sunma fice Mata Rai sbd
a matsayin da raunin zuciyarta yakai aka Kuma samun matsalar rashin aurenta komai
zai iya faruwa da ita Dan haka tayi nesa da duk wata alaqar dazata Kuma jefata
soyayya.

Abbinta ma sosai yake data da taka tsantsan akan Wanda Zata Kuma samu yaanzu sbd
kaucewa hadari da damuwa,
Duk aka Kuma samun irin wannan matsalar likita ya fada Masa zuciyarta ba lallai
takuma daukan wani mummunan tashin hankalinba.

A yanayin weak heart irin na Inayah shi baimasan me zatayi da soyayya ba sbd duk
wani disappointment Yana cikin soyayya yake gani.

Haka suketa lallabawa da tunanin ta Inda wani manemin auren zai bullo mata.,

Ita dai umma yaganah fargabarta da babbar damuwarta kada Inayah din itama auren
yafita ranta kwata kwata kaman mahaifinta,

Shi namijine bazaiyi tsufa a aurenba Nan kusa barema kusan yanzu ne yake cikin
shekarun da neman aure agurinsa abune Mai saukin gaske,

Ita Kuma yanzu tanada sauran kuruciya ayanzu ne auren ya kamaceta kaman yanda take
buri da tsananin kaunar yin auren
Dan haka ta ninka roqonta gurin ubangiji Allah yakawo musu abokanan rayuwa masu
albarka suyi auren.


***Familyn Dr Abdul hankalinsu yafara tashi akan yanda ya dauko hanyar tabarbarewa
akan mace,

Duk Wanda yake Dan uwansa yasan INAYAH A MAJEED a rayuwar Dr wata babbar
jarabawace,
Abin haushi da baqin cikin shine duk yabi ya lalace akanta Amma wai Bata saniba
hakama iyayenta suna gani sunyi kaman basu ganiba,
Hakan yasa kusan duk wasu Yan uwansa sukaji basa kaunar Inayah din sbd Dan uwansu
daya Zama gwanin tausayi baida zance sai nata.

Ana cikin hakan Inayah ta hadu da wani yayan abokin Safnah.

Mimi da gudu ta ringa Jin Dadi sbd yanzu mijin ta bangarensu ya bullo Dan haka ta
zaqe tanata sake cusa zancen Ahmed din gurin Inayah da umma yaganah saidai Inayah
Sam hankalinta Bai kwanta takuma sakewa sosai akan soyayyaba Dan har yanzu akwai
sauran son faruk maqale acikin ranta.

A karon farko da zancen ya Isa kunnen Dr Abdul sanyi jikinsa yayi ya silale ya
zaune Yana sauraren Inayah din dake fada Masa da kanta.

Bai iya ce Mata komaiba saima kasa kallonta da yayi sbd kada taga yanayinda yake
ciki Dan kuwa Zata girgiza da ganin idanuwansa dasukai jajir.

Bai iya tsayawa yin aiki ba ranar sulalewa yayi ya koma gida sbd ciwon Kai Mai
tsananin gaske daya taso Masa.

Itama haka Takoma gida jiki amace sbd yanayin Dr Abdul din daya sakata damuwa.

Baiyi bacci ba ranar haka ya kwana Yana juye juyen ciwon Kai Mai tsananin gaske da
azaba,

Yasani matuqar Mai samu Inayah ba wlh zai iya haukacewa
Hauka tuburan ta gaske,
INAYAH tazamar Masa jarabawa Kuma qaddara.

Hawayene suka gangaro Masa masu zafin gaske ya miqe zaune tareda nade jikinsa waje
daya Yana fashewa da kuka Mai tausayin gaske.

Washe gari Bai iya fita aikiba sbd ciwo ya kwantar dashi
Haka Inayah tazo tareda Dr Emma ya dubasa.

Ciwon kansa Mai tsanani ne Dan haka yayi requesting suje asibiti ya dubasa acan
Amma yace AA ba buqatan hakan Inshallah maganin ma zaiyi Masa.

INAYAH ce tasaka aka kawo maganin daga asibiti yasha ya shige ya kwanta itama
Takoma gida jiki duk amace.


Kwanansa biyu a kwance kafin ya Dan warware yaci gaba da fita aiki.

Babban abinda ya bawa Inayah tsoro itada umma yaganah da Anty Hafsat shine tun
ba'aje koinaba akan maganarta da Ahmed Al'amarin ya lalace ta hanyar Kama Ahmed a
drugs case.

Haka kawai hankalin Inayah yaqara tashi sbd ta tabbatar yanzu kam koma menene yake
lalata aurenta daga gareta ne sbd shaidu da komai sun nuna Ahmed gskia mutumin
kirkine baya hulda da drugs tako Ina Dan haka akafi tunanin sharri akai Masa.

Kan kace me mutane suka fara canfa daga Inayah ne duk Wanda yazo aurenta to masifu
kala kala na zuwa garesa.

Hankalinta ya tashi sosai da wannan mugun Al'amarin har abin yaso tabata,

Abbinta kuwa take yafara Dana sanin dawo dasu Nigeria,
Da suna can duk da kila Canfi da wasu abubuwan rashin wayewa basu faruba,

A qasar waje da qabilu daban daban anan dinma basu damu da auren Wanda aka Haifa
bada aureba sbd idanma hakane shi ai ba laifinsa bane,
A taqaicema shi abin tausayi ne Musamman ga Wanda hakan ta kasance dashi Yana
musulmi.

Amma duk Anbi an hargitsa Masa rayuwa da tunanin 'ya Bayan duk tattalinsa da
kulawarsa sun qare akan 'yarsa tilo guda.

Fara tunanin maidasu Australia yayi Nan Kuma hankalin umma yaganah yafara tashi sbd
har ga Allah tafison zaman Nigeria sbd kana cikin qasarka kafi nutsuwa da kwanciyar
hankali idan ba su dasuke Yan boko ba sunfi son rayuwar turai din.

Dama shi Abbin yafi kaunar zamansu acan ne sbd nesanta Inayah da irin wainnan
maganganun dayasan matuqar suna Nigeria yau da gobe sai Mutane sunfara maganganun
dazasu saka Mata wasi wasin asalinsu akanta.

Ya zabi barinsu zaman wata qasar ne da nesantata da bude Baki wataran ta tambayesa
mahaifiyarta kokuma asalinsu,kokuma labarin yanda mahaifiyarta ta tafi tabarsu.

Gashi tun ba'aje koinaba anfara rikita Masa kanta da wainnan fitintinun,

Auren data sakawa ranta ta nace gashinan Bata samu 'dan amanar dazai iya aurenta
dan Allah ba,
Daga Wanda keson aurenta Dan dukiyar mahaifinta sai Mai son wani bangare na jikinta
sai masu aibata zuwanta duniya.
Dan hakan yanke shawaran maidasu kawai su koma sai Kuma gaba idan Allah yakawo
dalilin dawowar.


Labarin barinsu Nigeria shine ya fidda asalin ciwon dake damun Dr Abdul akan Inayah
Dan kuwa har Saida yayi Dana sanin lalata aurenta da Ahmed tunda wuri.,

Kusan zaucewa yayi Dan kuwa baimasan lokacinda yakai kansa gurin Abbinta ba Yana
kuka da idanuwansa akan yabasa aurenta shi zai aureta sbd Babu Wanda yakaisa sonta.

Dama yasan za'ai hakan to Amma shi kam soyayyar Dr Abdul din shakku take sakasa,

Son yayi yawa,
Bai taba ganin irin hakan ba,
Basa Inayah din kaman yanada hadari sosai sbd irin wannan ya wuce so ya zama
possession.

Amma Kuma ta wani bangaren tausayi Mai zurfi Abdulsamad din yake basa sbd mutum ne
Mai nutsuwa da Kamala tareda ilimi sosai Amma sbd soyayya shima duk hakan na Neman
gagararsa,
He is loosing everything slowly.

Ta wani bangaren yasan samun Inayah ce warakar Dr Abdul din haka zalika badan tabin
kan son dake Neman yawaba yasan Dr Abdul zai Zama Miji nagari Mai kula da kauna ga
Inayah.

Dan haka ko yanzu Bai cire ran Dr Abdul din zai kasa kula da Inayah ba,
Yana saka ran idan yasamu Inayah din bazai Bari haukarsa ya cutatar da itaba Dan
haka yace yabasa dama ya nema Inayah din idan ta amince shikenan,
Amma da sharadin zai bisu can qasar zai Samar Masa aiki a one of the best hospitals
dake qasar
Yaci gaba da aikinsa acan da matarsa.
Baiga abinda zai tsaya tunaniba matuqar zaa basa auren Inayah din Dan haka Kai
tsaye ya amince,
Dan koba komai kusan qaruwarsa ce zuwa wata qasar aiki.

A natse abbin ya girgiza Masa Kai Yana cewa"

No Kar kayi rushing abubuwan
Zaje kayi shawara da iyayenka da mahaifiyarka dakace,
Sbd kaman abune da bazaka iya yankewa Kai dayaba Dole kana buqatan iyayenka aciki.

Shidai farin cikinsa ya hanama ya tsaya dogon zance ya amsa da cewa"

Inshallah zan tafi cikin satin Nan na sanar da ita komai Umman tawa.

Allah ya taimaka yasa hakan shine mafi Alkhairi.

Amin, thank you sir,
Ngd sosai Allah yaqara girma da rufa asiri.

Amin.



******Abbi ne da kansa ya sanarda umma yaganah da Inayah buqatan Dr Abdul na abasa
damar neman auren Inayah din Kuma yabasa damar Amma sai idan ta amince.

Umma yaganah ba Bata lokaci ta bayyanarda farin cikinta sbd ta jima tana yiwa
Inayah shaawar auren Dr Abdul din Dan nutsuwarsa da kamalarsa,
Gashi kyakkyawa shima da Dan arzikinsa ba laifi.

Shi kansa Abbi gskia Dr Abdul din ya kwanta Masa fiyeda duka maneman da Inayah din
tayi a baya Amma Kuma yafison tayi zabi akan Dr Abdul din da kanta.

Wani iri taji Al'amarin a farko Dan haka batace komaiba.

Neesah tafara fadawa a waya
Aikuwa Neesah ta ringa tsallen Murna sbd tasan Dr Abdul tako Ina yayi gskia,
Ita da harta fara yiwa kanta sha'awar aurensa Amma ganin basa qasa daya yasa bata
zurfafawa kantaba dakuma hango tsagwaron son Inayah a idonsa.

Safnah ma tsallen murna ta ringa Yi tana cewa"

Wlh dama nasan zaai hakan sbd Dr Abdul ya dade da mutuwa akan sonki Naga alama.

Anty Hafsat ma a nata bangaren hamdala da godewa Allah tayita yi sbd dukkaninsu sun
yaba da mutuncin Dr Abdul dakuma shedar irin son dayake Mata bazai taba gudunta ba
Dan duk wani abunda zaa fada.

Itadai Inayah tanajin 'yar shakkar Al'amarin sbd girman matsayin Dr Abdul a ranta
idan sanadin auren Nan suka rabu tasan Zata shiga mummunan hali fiyeda lokutan baya
sbd matsayin Dr Abdul a ranta jinsa take yafi Mata duk wata soyayyar datake abaya,

Kaunarsa takeyi sosai cikin ranta tana jinsa tamkar wani jininta,
Tasha gwada yimasa kallon wani bangare na rayuwarta sbd mahimmancin mutuncin dasuke
da juna.

Umma yaganah, Neesah,anty Hafsat da Safnah ne suka taru suka ringa azalzala Mata
soyayyarsa da nacin nusar da ita irin yanda yake Sonta.
Tun tana jin Al'amarin wani iri sbd Bata taba tunani ko kawo kwatancin soyayya
harda aure zai shiga tsakaninta da Dr Abdul dinba har tazo nacinsu da kulawarsa
daya soyayyarsa da yanzu yagama bayyanar Mata suka sauya matsayi da kaunarsa cikin
ranta zuwa tsaftatacciyar soyayya Mai nutsuwa.
##MAMUH#
#RIBA BIYU
#AA MAJEED ABBI/AYSHATOUH INAYAH




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biyaπŸ‘‡
07040727902

MTN cardπŸ‘‡
09134848107
[10/15, 11:47 PM] MG: *_25_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ganin hankalinta ya kwanta akan auran Dr Abdul din sai kowa yaqara bada himma gurin
qarfafa Mata gwiwa da sake kwantar Mata da Al'amarin cikin zuciyarta,

Bata sake sakankancewa ta budewa Dr Abdulsamad zuciyarta ba Saida Abbinta ya nuna
Mata goyan bayansa akan auren Abdulsamad
Dan haka ta budewa Dr Abdul dukkanin zuciyarta ta karba soyayyarsa.


Abdulsamad tamkar a mafarki yakejin rayuwarsa yanzu dazai mallaki Inayah amatsayin
matarsa halak malak batareda shamakin kowaba.,

Sosai kowa ke mamakin yanda duk yabi ya kasa sukuni ya rude Yana bayyanarda farin
cikinsa koina.
Tamkar wani zautacce yakomawa Inayah soyayya yake nuna Mata kamar ba Dr Abdul din
data saniba tuntuni.

Ita tausayinsama takeji Mai qarfi dayake qarawa soyayyarsa girma cikin ranta sbd
Batasan haka yake tsananin sontaba da bazata taba tsayawa kula kowaba da tuni ta
amince dashi anyi aurensu.

Mahaifiyar Abdulsamad kam sosai take qaunar Inayah sbd yanda 'danta ke tsananin
sonta,
Da farko hankalinta yaso tashi sbd tunanin Bazaa bawa Abdul dinta auren Inayah ba
duba da matsayinsu na wainda sukafi na Abdulsamad din kudi sosai sai gashi anyi
halin girma anbasa aurenta Dan haka take kaunar Inayah har ranta duk da iyakacinsu
waya haryanzu Allah Bai saka sun hadu a zahiri ba wata kila sai lokacin bikin
Auren.


***Ansaka lokacin bikin Wata biyu masu zuwa Dan haka ko wannan karon su umma
yaganah da Anty Hafsat da wuri suka fara shirya 'yarsu Inayah tako wane fanni.

Gyaranta akeyi sosai Dan kuwa Abbi ya sakar musu kudi suna yanda suke so dasu gurin
harkar shirye shiryen bikin.

Wannan karon baiyi wani gayyataba sosai sbd kaucewa hayaniya albarka auren akeso ba
taronba,
CM ne ma dai dayafi A MAJEED din shiga mutane sosai ya dauka nauyin gayyatar ta
hanyar aikawa manyan mutanen dasuke taredasu special invitations na auren.

Anty Hafsat ta haukace tsima Inayah kawai takeyi tako Ina da abubuwa masu kyau da
inganci nasu na manyan mata.

Umma yaganah Kuma masu gyaran jiki takuma sakawa aka kawo matasu daga maiduguri
harma da 'yan uwanta biyu dasuka zo bikin auren Dan haka tako Ina families din guda
uku nasu na A MAJEEDs,da iyalan gidan CM saina dangin ango dasuke Adamwa hidimar
biki akeyi gadan gadan ta kowane bangare.

Inayah tana cikin wani irin farin ciki Mara misali sbd jikinta da dukkanin imaninta
yabata wannan karon Zata auru Inshallah bazaa fasa aurentaba Dan haka taketa Jin
farin cikin igiyoyin auren Abdulsamad dintane zasu hau kanta bana kowaba.

Shikan oga Dr Abdulsamad fadar irin farin cikin dayake cikima wasane Dan kuwa jin
yake Kamar zai take kan jariri dama uwar jaririn ya wuce sbd zumudi da farin ciki.


Lafiyayyan lefen aure dangin Abdulsamad din suka kawo ana Saura kwana biyar afara
bikin Wanda su umma yaganah sun yaba sosai da irin kokari dakuma uwar dukiyar dasu
Abdul din suka kashe.

Neesah sai a ranarda aka kawo lefen itama tasamu isowa daga Australia tareda Dr
farhat wadda ita ta sauka a gidan Mahaifiyarta dake aure a Lagos din Dan haka tana
zuwa suka sake hautsinewa da Murna.

Safnah ma tuni tadawo gidan da kwana sai angama biki so gabaki daya gidan dai a
kacame yake da jama'ar biki duk da ba wasu masu irin yawa dinnan bane.


Inayah gabaki daya ta sauya Takoma tamkar wata jaririyar da aka Haifa acikin watan
sbd tsananin kyau da taushi da fatarta tayi,
Gyara da rashin fita tareda tsananin hutu da kwanciyar hankalin datake ciki a
watannin yasa tayi wani irin zallar fresh sai sheqin fata takeyi.

Tunda Dr Abdul yazo yaga irin kyau data qara da sheqin amarci datake tun yanzu yasa
yaqarasa rikicewa akanta duk da soyayyarsa Bata shaawa bace Amma tuni kyanta ya
qarasa rikita Dan sauran nutsuwar dayake da ita akan Sonta daya zaburesa.

Ganin yanda yabi ya rude hakuri na Neman gagararsa yasa Anty Hafsat ta hanasu
haduwa sosai tace sai lokacin bikin Dan haka yanzu a waya suke koyaushe ba sakat
Kamar wasu hanta sa jini.

Abbi kam sosai Al'amarin nasu ke Dan basa mamaki da dariya kawai sbd yanda Inayah
tasan ta iya soyayya sosai irin haka Dan shi haryanzu a jaririyar 'yarsa yake
kallonta gashi zatai aure takoma qarqashin ikon wani.

Yau sosai take amatuqar gajiye sbd saka lalle da akai ayau din can gidan CM Dan
haka sosai take amatuqar gajiya Koda suka dawo gida zare tsadadden lace din dake
jikinta tayi Mara nauyi ko kadan ta nufi toilet tashige.

Gaban mirror ta tsaya tafara goge fuskarta tas da Neutrogena makeup remover wipes.

Wanka tayo da ruwan dumi kafin tafito daureda towel tana kallon Neesah ma dake
jiran ta fito wankan itama tashiga tayo Dan duk makeup din fuskokinsu damunsu
yakeyi sbd basa wani makeup dama can
Iyakacinsu Liner da mascara sai lipstick masu tsadan gaske dake zaunawa da kyau
abakinsu idan sun saka.

Sama sama ta shafa Mai tareda spray dasu khumrahs masu sanyin qamshi da akayo
Musamman masu tsada daga maiduguri.

Riga da wango tasaka masu kauri sbd sanyi sanyi datake ji.

Sallolin dake kanta tafara Yi kafin ta miqe ta fito tana waya da Dr Abdul dinta ta
nufi dining tana cewa"

Heart yunwa fa nakeji sosai yau banwani ci abinci ba
Zaa ramar maka Ni da yunwar biki.

Cikin kulawa sa so Mai tsanani ya karyar da murya yana cewa"

Ni zasu illata gskia bazan dauka ba,
Kyakkyawar amaryar tawa ce zaa Bari da yunwa
Gskia bazan yardaba
Laifin anty Hafsat ne data hanamu haduwa yanda muka saba kewanki is driving me
crazy
Gobe da safe zanzo na ganki kafin su Umma su iso sbd itama tana zuwa Zata qarawa
anty Hafsat qwarin gwuwar hanamu ganin juna sai ranar Daurin auren.

Murmushi tasake Mai kyau tana cewa"

Dan Allah kazo goben da wuri Nima nayi kewanka fa sosai.

Zama tayi a dining daidai lokacinda Abbi ke isowa dining room din a kasalance ta
ajiye wayar sbd bataso Gama waya da Heart dinta ba Amma Kuma girman Abbinta na
daban ne akan komai.

Kallon abbin tayi Yana sanye da Fararen hoodie graffiti print sweatset.

Sanyin qamshinsa ne yake neman danne na Lafiyayyan abincin dake jere kan dining din
yayi fresh Kamar ba baban amaryar ba Batasan lokacinda ta sake qaramar dariyaba
tana cewa"

Abbi barka da fitowa.

Da Dan silent murmushi ya kalleta yana amsawa da cewa"

Barka Amaryan Dr Abdulsamad.

Dariya tasake tana kallonsa tace"

Abbi Naga kamanma ka matsu natafi nabar gida,
Kullum saikace mun amaryar,
Nidai kunya nakeji Gaskia.

Wani qayataccen murmushi ya sake daidai lokacinda Neesah da umma yaganah suka iso
dining din cin abinci yace"

Inayah kinsan kunya dama?
Inace you don't know the name kunya,
Kin manta a gabana kike zuwa kina kukan soyayya da Kiran sunan zayyan ne sunan koma
fahat ne I can't recall
And now kinata tsalle da murnan zakiyi aure shine kike fadamun kunya
Rashin kunya plus lie ko??

Dariya umma da Neesah sukai umma na saka musu Baki da cewa"

Inayah kam ai indai anan cikin gidane Babu Wanda take kunya saidai mutane waje take
kunya.

Kai umma yaganah please karki sake batan suna gurin Abbi Kinga zaifi kowa kewata fa
idan natafi ko Abbi?

Abincin data Gama zuba Masa yafara ci yana Dan gyada Mata Kai ahankali.

Bayan sun Gama cin abincin bin Abbinta tayi palonsa suka cigaba da maganganunsu na
tsakanin uba da 'ya sai kusan after 9 tafito ta nufi daki ta kwanta bayan tasake
goge fuskarta da face cleanser.

Washe gari shine zaai Mata lalle Kuma tasan heart dinta yace zaizo Dan haka da wuri
ta tashi tayi wanka ta shirya cikin Riga da skirt na maroon super exclusive wax da
qaramin Marron veil ta fito a sace sbd yaca Mata ya iso Yana palon Abbi.

Tana shiga palon Abbin Yana zaune tareda Abbi suna magana cikin nutsuwa.

Bude kofar tareda sallamarta a sirance tasaka su waiwayowa kallon kofar atare take
zuciyar Abdul yakusa bugawa.

Ya salam ya furta a fili batareda yasan ya furta hakan agaban Abbin ba.

Qamshintane ya doshi hanyar mamaye palon gabaki daya sbd wasu irin qamshine kala
kala na designer turarukanta masu tsada da turarukan khumrahs da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login