Showing 1 words to 3000 words out of 124042 words

Chapter 1 - INAYAH Riba by Mamuhgee

Mamuhgee   

08 May 2026

4

[9/30, 1:34 PM] MG: *_INAYAH_*
_(Riba Biyu)_

_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*

1
_BismillahirRahmanirRaheem_
Tasowa tayi ahankali tana takowa zuwa tsakar gidansu datake jiyo maganar
mahaifiyarta da yayyunta maza tareda kishiyar mahaifiyartata suna magana duk a
jujjuye sbd hankalinsa daya tashi lokaci daya cikin mummanan yanayi da tashin
hankalin mugun labarin dayazo musu yanzu yanzun.

Ita kanta hankalinta baa kwance yakeba dama can sbd halinda take ciki na jinyar
mijinta dake kwance asibiti Yana jinyar accident dasukai kwana biyu dasuka wuce a
hanyarsa ta dawowa daga gurin daurin auren qaninsa dasuke uwa daya uba daya,

Kaman a fizge kunnuwanta suka jiyo mata abinda babban yayanta Umar ke fada saidai
Sam takasa fahimtar abinda yafada din zahirance Dan haka tana buqatan jinsa da
kyau,

Ta qaraso jikin kofar ta yaye labule ta fito tana kallonsu daya bayan daya fararen
idanuwanta dasuka jima da shigewa ciki ciki sbd damuwar datake ciki kwanakin,

Suma ita suke kallo Kaman yanda take binsu da kallo kowannensu fuskarsa cike dauke
da alhini dakuma tausayinta Dan kuwa Rashin miji a irin shekarunta abin tausayi
Ga Kuma 'da da ciki dake jikinta.

Kallon mahaifiyarta tayi taga yanda tayi qasa da Kai cikin yanayi na hawayen dasuke
Neman saukar mata takasa kallon Yar Tata

Dan haka ta kalli kishiyar mahaifiyarta kai tsaye tace"

Inna Menene duk kukai wani iri haka?
Lafiya kuwa?
Wani abin yakuma faruwa ne?

Maida kallonta tayi kan yayyunta dake tsaye suna kallonta tace"

Yaya Umar,Yaya kabiru?
Lafiya duk kukai shiru haka?
Jikin Abban Abdul ya tashi ne?

Ajiyar zuciya Yaya kabirun ya sauke tareda gyara tsayuwarsa ya kalleta da Dan
alhininsa irin na maza masu taurin zuciya Kai tsaye yace"

Khadija bayan barowarki asibiti yanzu Allah yayiwa Salisu cikawa........

Bai qarasa ba ta waiwayo gefensa tana kallonsa cikeda zallan mamaki da faduwar gaba
muryarta na gwamutsuwa tace"

Yanzu fa na Barosa Yana barci,
Wanka fa kawai zanyi nakoma asibitin shine zaace ya rasu????
Yanzu yanzu fa?

Da sauri innar ta riqota cikin tausayawa tace"

Hadiza karkiyiwa ubangijin haka,
Tawakkali zakiyi tunda kinsan dai baa wasan mutuwa...
Idonta na sauya zuwa ja da hawayen dake kokarin cikowa saidai taurin zuciyarta ya
hanasu fitowa
ta katse innar da cewa"

Inna bacci nabarosa yanayi fa,
Yaji sauki sosai yau,
Rasuwa fa akace,
Mutuwa fa kenan, ya tafi ba dawowa har abada,
Ta Yaya zanyi.......

Cikin Dan daga murya Yaya kabirun yace"

Ke Khadija Menene hakan?
Rasuwa fa akace Miki salisun yayi,
Ki nutsu ki fahimci ita rasuwa babu ruwanta da yanzu yanzun dakike fada,
Kiyi gaggawar bude hankalinki ki fahimci abinda yafaru dake,
Salisu ya rasu bazai taba tashiba......

Bakinsa take kalla kanta na juyawa
Zuciyarta na harbawa da mugun qarfi Kaman zata faso kirjinta,

Mamarta ta kalla idanuwanta na qafewa taga alamar gskiyar zancensa akan fuskan
mamar,

Ta waiwaya ta kalli Yaya kabiru Shima hakan tagani.

Wani busasshen yawu ta hadiye wanda har yankan maqoshinta yake
Ta juya kai tsaye Takoma dakin mama ta dauki doguwar hijabinta data cire bayan
shigowarta gidan ta zira ko waya da kudin adaidaita Bata daukaba ta fito ta zira
slippers din mamarta daya Da nata takalmun daya batareda ta luraba ta nufi kofa
tana jefa ka kawai dan bata cikin hayyacin kallon gaban nata
asibitin take buqatan isa kawai.

Inna ce tayi saurin janyo nata hijabin tabi bayanta tana Kiran sunanta,

Mamarta kuwa kallon Yaya Umar tayi tana cewa"

Bisu kabasu kudin adaidata ban Saka ran kowannensu ya daukaba.

Juyawa yayi ya bisu
A titi yayi saurin taddasu ya ciro 1000 ya miqawa Inna Yana cewa"

Ga kudin adaidata Inna
Ki lura da ita Inna kartaje asibiti tayita wainnan maganganun
Tawakkali akeyi kifada mata Inna.

Da sauri innar ta qarasa gurin hadizar daketa zuba sauri tana tafiya ta riqota ta
riqe hannunta gam tana kokarin Kiran sunanta saiga adaidata gabansu ba Bata lokaci
suka fada ciki
innarce tafada masa asibitin da zasu
Khadijan kuwa Banda rawa babu abinda qafafunta da hannuwanta keyi.

Isarsu asibitin ko Gama tsayuwa baiyiba Khadija ta sauka tareda wucewa da sauri ta
nufi hanyar Emergency ward da har lokacin Salisu anan yake.,

Tun daga nesa Yan uwan Salisu din maza da mata suka hangota tana tahowa a gigice ko
ganin gabanta batayi
Hankalinsu yakuma tashi da tsananin tausayinta dan haka da yawansu suka qara
fashewa da sabon kukan Rashin Dan uwansu.

Tana qarasowa da kallo tabisu daya baya daya taga yanda mahaifiyar salisun ke rusa
kuka take taji Rabin jikinta na neman mutuwa ta qarasa dakin tashige da gudu ta
nufi gadonsa da gawarsa kawai ta tadda a rufe da zanin gadon data zo masa dashi
yau da safen.

Tsawonsa ta kalla tareda hannuwansa da aka miqar,

Kasa gasgatawa tayi Saida takai hannu ta yaye zanin tayi arba da kyakkawar fuskarsa
ta asalin fulanin Yola....

Mummanan bugawa zuciyarta tayi ba tsammani idonta yarufe tana kokarin zubewa Inna
tayi saurin tarota tana Kiran sunanta Amma Sam batajinta sai neman somewa takeyi.

Da sauri hajiyarsu salisun ta qaraso tana cewa"

Ku koma gida da ita karta shiga wani Mummanan halin ga juna biyu a jikinta.

Qwacewa takeson yi Dan Bata tunanin zata bar gawar salisun ta tafi koina Amma
batada qarfin motsawa bare magana Dan bakinta take ya manne Kaman an Saka mata
glue.

Tana kallon gawar mijinta Salisu aka jata aka fice da ita har waje aka kuma sakata
napep tareda Inna da qanwar salisun suka nufi can gidan iyayen salisun.

Suna isa ko tsakar gidan Bata qarasa shigaba ta yanke jiki ta fadi jini nabin
qafafunta.

Hankali tashe sukai kanta tareda ciccibarta zuwa dakin hajiyarsu salisun Inna na
Kiran sunanta hankali tashe.

Jini sosai take zubarwa Wanda ya tabbar musu da cikin zubewa ne yayi babu tantama
Dan haka basuyi wani yunqurin maidata asibiti ba haka Inna da dattijuwar gidan
qanwar mahaifinsu suka taimaka mata gurin ganin jinin yagama zuba ta Dan gyara.

Kururuwar koke koken da gidan ya dauka ne ya tabbatar musu da isowar gawar Salisu
gida
Tana jin hakan ta rintse idonta cikin tsananin azaba sauran abin dake cikin nata ya
qarasa zubowa sai alokacin wani irin gunjin kuka Mai tafe da radadin zuciya ya
kufce mata.

Inna dake kanta ta qara matsowa tana dafata cikin tausayawa jin irin girman kukan
datake,

Kuka takeyi sosai zuciyarta na radadin Rashin mijinta uban 'danta dakuma wannan
cikin daya qwallafa ransa akansa,
Ashe tareda cikin zasu bar duniya Rana daya shiyasa Allah ya saka masa tsananin
kaunar cikin abokin tafiyarsa ne kenan.

Bata damu da yanayin datake ciki ba
Haka ta dafa ta miqe tsaye tareda qarasawa tsakiyar bayin dakin hajiyar ta wanke
jikinta daqyar sbd tsananin rawar da hannuwanta da qafafunta keyi.

Fitowa tayi Kai tsaye ta karba zanin da inna ke miqo mata ta daura wani irin
tsananin jiri da ciwon mara Mai tsananin gaske Yana nukurkusarta Amma taqi yarda
tazauna Kai tsaye ta fito tsakar gidan sanyeda hijabinta tanajin yanda tako ina
gidan ke amsa amon kukan Yan uwan Salisu.
Gawarsa dake shimfide a dakin da zaai masa wanka ta nufa ta zube gabansa tafara
rero wani irin gunjin kuka tana Kiran sunansa.

Duk yanda akaso janyeta kasawa akai sbd kuka takeyi sosai zuciyarta na tsananin
qunar Rashin mijinta datake tsananin so da kauna yau gashi ya tafi yabarta cikin
duniyar da kowa babu abinda yasani sai kansa,

Ina zata da 'danta Abdul Wanda tasan babu Wanda zai daki kirji a cikin danginta
Kona salisun ya tallafi rayuwarsu.

Lokacinda za ai masa wanka da sirita aka samu aka janyeta daga dakin musamman da
itama wani irin gagarumin zazzabi ya rufeta lokaci daya dakuma sabon jinin daya
Kuma balle mata sai alokacinma kowa ya San da Bari tayi.

Baa kaita asibiti ba a dakinta dake gidan aka kwantar da ita kasancewar a gidan
suke zaune tareda iyayen salisun tunda dagasu har iyayen ba masu hali ban Dan hakan
nema sukeda daki daya tal da Dan qaramin palo da bandaki acikin palon,
Tana daki ana fama da ita har aka tafi da gawar makwancinsa,

Iya fatu aka kirawo makociyarsu Mai karban haihuwa ita tazo ta duba hadizan ta
tabbar musu da cikin yagama zubewa
Nan aka shiga wani jimamin aka fara kulawa da hadizan.

Sbd yanayin jikinta dakuma zaman gaisuwar da ake gidan yasa dole Inna ta zauna
tareda ita tadawo da kwana gidan tunda maman hadizan bazatazo ta zauna ba.

Sosai take fama da jinyar kanta bayan kwana biyu da rasuwar sbd takasa daina kukan
mutuwar Salisu,

Salisu mijine ma gari Kuma uba nagari hakama 'da na gari gun iyayensa.

Cikin kwana biyu duk tabi ta yamutse da tsananin damuwa dakuma ciwo dake damunta na
tsananin ciwon mara na barin datai.

Angama zaman gaisuwar har anyi sati biyu babu wani Abu daya sauya daga gareta saima
sabon ciwon damuwa daya kamata Sam takasa fita daga halin damuwar Rashin mijinta,

Inna na tareda ita har lokacin Kuma dai ita zata zauna da itan har tsawon watannin
dazata Gama takabarta kafin sukoma gida tare.

Abdul Yana gurin mama dama tun tana zaman jinyar abbansa asibitin kafin rasuwar
tasa Dan haka kullum a daki suke wuni daga ita sai Inna,

Abincinta Wanda yake kicin dinsu tun Wanda salisun ya siya shi Inna ke dafa musu
yana qarewa babu Wanda yakawo musu wani saidai aka ringa Basu daga cikin gidan Idan
an dafa,

Wanda ake basun baya wani isarsu itada innar dan haka so da yawa innar Idan taci na
safe yafe mata na ranar take ita taci,

Itakuma Idan anbasu na daren saitace ta koshi saita barwa innar taci.

Tun daga Nan yanayin yafara kulle musu
Da innar dai taga daga ita har hadizan sunfara dogayen wuyan yunwa Kamar Yan gudun
hijira dole taje gida ta sanarwa mamar hadizan sukai shawara akaiwa Umar da kabiru
magana akan su taimakawa hadizan da abinci
shine suka Dan fara taimakawar duk bayan kwana biyu suna Bata dubu daddaya ko dari
Biyar Biyar.
Tun suna Bata tana samun na siyan abinci da Kamar su sabulun wanki hardai Suma ana
Jan lokaci suka daina sbd Suma da nauyin nasu iyalan akansu dan haka suka koma Yar
gidan jiya.

Watan salisun uku da satittika da rasuwa gabaki daya rayuwarta ta juya mata upside
down sbd hajiyarsa itama ta kanta takeyi Dan dama shine kawai Mai tausayi da
tallafa mata acikin yayanta shiyasa itama bazata iya daukan nauyin hadizarba Dan
haka kowa tasa ta fisshesa akeyi a gidan.

Hadizar ta rame ta hargitse ta sauya kamanni sosai bayan dogon wuya da dogon hanci
sai ido dasuka fito kaman me Neman allura a duhu haka Takoma dama ita Inna sun saba
da talaucinsu Dan haka masifar quncin Rashin ba wani damunta tayiba Kaman dai yanda
tausayin rayuwar hadizan tafi damunta sbd tasan wani sabon gararin ne zata tadda
gida koda tagama zaman takabar sunkoma.

Ta bangare daya tunda tayi barin cikinta lokacin rasuwar Salisu har yanzu takasa
ganewa lafiyaarta sbd ciwon mararta yi yakeyi Yana tasan mata,
Wani lokacin idan yatasar mata Kaman zata rasa ranta haka take fama dashi Amma Bata
taba zuwa asibiti ba Dan babu hali,

Ko innar dasuke tare Bata sanarwaba Dan karta daga mata hankali bayan daga ita har
mamarta tada hankali kawai zasuyi basuda wata mafitar.

Cikin wani irin tsanani da matsuwar Rashi da tarin damuwa tagama zaman takabarta
suka fara Shirin tattarawarta komawarta gidansu.

Hajiyar Salisu tayi sabon kukan mutuwarsa lokacinda hadizan zata tafi,
Tanajin inama tanada halin cigaba da kulawa da matar salisunta da 'dansa data
riqesu
Amma batada Wannan halin,
Ko Abdul dinma tana tsananin kaunarsa saidai bazata iya riqonsaba shiyasa batamayi
maganar karbarsaba,
Da mahaifinsu salisun Shima Yana raye tasan bazai taba barin hadiza da Abdul din su
tafi ba.

Ita kanta hadizan ta San cewa Rashin halin ne yasa hajiyar batai yunkurin cewa a
bar mata abdul ba Dan tunda salisun ya rasu itama yanzu abincinta neman gagarta
yake
Gwara tabarwa hadizar 'danta tasan duk tsanani zata nema ta kula dashi.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
[9/30, 1:36 PM] MG: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


2
Dawowarta gidansu dole dakin Inna ta tare tareda innar tunda babu wani extra daki
dazata zauna a gidan bayan nan,

Duka duka dakuna biyu ne gidan sai bandaki dake tsakar gida,
Daki daya na mama daya na innar,

Ko acan dah da mahaifinsu na raye zagayen dakuna yake,
Ita Kuma Idan Yana kwana dakin mama saita kwana a dakin Inna,

Idan a dakin Inna zai kwana saita kwana a dakin mama
Ahaka ta girma harya rasu itama akai mata aure.
Dawowarta gida wata sabuwar rayuwar zullumin kullum tashiga acikinta,

Daga Inna har mama babu Mai wata qwaqwarar sana'a,
Mamace ke Saida lallen hausa
Inna Kuma tana saida su kanwa da borkono
To tundama ta tafi taya hadizan zaman takaba sana'ar ta tafi sbd jarin ba wani Mai
yawa bane dakuma hardashi suka hada duk suka cinye a can gurin zaman tunda sun
shiga tsanani,
Dan haka sana'ar innace kawai yanzu take Dan taimakawa ta wani bangaren Amma kam
suna cikin gararin yanayi sbd Suma dama can salisun ne yake dauke da nauyin nasu
tunda nasu yayan basa taimakonsu kansu da matayensu da yayansu kawai suka sani.

Ita Inna Bata taba haihuwaba shiyasa tun take riqon hadiza tun tana yarinya gashi
Kuma hadizar ce kawai mace acikin yayan mama dukansu mazane su uku,
Malam Nafi'u Wanda Allah yayi rasuwa watannin baya,
Sai Kabiru da Umar dasu kuma ayanzu kownanensu yakeda mata daddaya da yara kusan
Biyar biyar,

Sai ita autarsu Khadija wadda Rashin tsayayyan manemi yasa batai auren wuriba sai
data dan girma a gida sosai takai kusan shekara ashirin da takwas kafin tasamu
salisunta dasuke tsananin so da kaunar juna sukai aure ya dauke nauyin tallafawa su
Inna daidai gwargwadonsa.

Daga Yaya Umar har Yaya kabiru babu Wanda ya dauke lalaurar kula dasu mama,
Saidai idan an kwana biyu su samu Kamar dubu daddaya su Basu ko 500 Wanda sukam
suke ganin kokarinsu a hakan suyita saka musu albarka duk da innar tasan basa
kyautawa suna kallo Salisu ke ciyar dasu bayan Shima ba wani karfin yake dashiba
kawai zuciyar alkhairi yafisu.

Yya Kabiru koyarwa yakeyi a secondary school din gwamnati dake kusa da anguwar
dayake da iyalinsa
Kusan shekara goma kenan Yana aikin koyarwar Amma babu wani cigaba kullum Yana Nan
a yanda yake.

Yaya Umar kuwa sanaa kowacce yi yakeyi baida tsayayya guda daya Amma dai yafi yin
ta dillancin harkar Saida filaye da gidaje Dan Yana samu sosai acikinta shiyasa
yafi yya Kabiru rufin asiri,
Qarshema dai fadawa yayi siyasa sbd uban gidansa dayasashi fitowa Dan samun kudin
jam'iyyar da zasu fito ta karkashinta tunda sunsan dai ba ci zasuyiba Amma sunsan
jam'iyyar zata Basu kudi sosai Dan haka gadan gadan yafada siyasa baji ba gani,

Yaya kabiru daya fahimci akwai samu sosai a harkar take ya marawa Umar din Baya Dan
Shima ya samma masa Idan ta 'bulle.

Itakam hadiza ganin zaman baida wata mafita
Ga Abdul ya isa sakawa makaranta tuni
Sbd abbansa koda ya rasu yanada burin sakasa makaranta alokacin,

Yanzu komai ya juye musu Kuma tanada burin bawa Abdul din ilimi Dan ya anfana
rayuwarsa,

Gasu Inna da mama kullum cikin dubaru ake
Yau aci kwadon kwaki,
Gobe aci kwadon qanzo,

sai ankwana hudu ko Biyar Daqyar ake hada cinikin da zaai musu tuwon gari da miya.

Dole hadiza ta tashi ta Saida katifarta da ita kadai ta dawo da ita sai tarkacen
kayan kitchen ta kwashesu takai kasuwar Yan kayan hannu ta saida ta tattaro kan
kudin taraba biyu ta siyo musu abinci da kayan abincin tadawo gida.

Sana'ar kosan safe dakuma awarar Rana tafara da sauran kudin yafara juyuwa.

Kasancewar ita Inna da sauran karfinta sai tana taya hadizar aikin sana'ar musamman
awarar datafi wuyar sha'ani.

Cikin ikon Allah lokaci qanqani saigashi sana'ar ta samu karbuwa sosai duk da farko
taci tsananin wuyar wuta da Rashin jamaa masu siya tunda baa saniba,

Babu ranarda Bata konewa shiyasa kusan koina tagama kokkonewa hannuwa da qafafu
Har fuska ma wani lokacin idan Mai yayi watsi.

Ba laifi yanzu basa neman komai a gurin kowa Wanda dai zasuci saidai Dan abinda baa
rasaba.

Inna ma tuni dole suke komai tare sbd aikin yanawa hadizan yawa ga koko dasuke
hadawa dashi yanzu da safe,
Da Rana ma yanzu ba awarar kawai sukeba harda dankalin hausa da wainar rogo.

Dole dai yanzu innace take aikin kosai da kokon safe ita Kuma tana awarar da
sauransu da Rana sbd dukkaninsu aikin yayi mutsu tsananin wuya musamman tunda aikin
wuta ne,

Mama ba cikakkiyar lafiyayyaceba shiyasa Basu taba barin ta shiga sana'ar ba,

Tunda mahaifinsu ya rasu haka take yau lafiya gobe ciwo,
Hawan jini da ciwon sugar ke tsananin damunta Dan haka lallabawa kawai takeyi tana
rayuwar.

Ahaka hadiza ta samu ta sanya Abdul a makarantar gwamnati yafara zuwa
Kullum ita ke rakasa da qafa tadawo
Idan antashi haka take komawa ta dawo dashi sbd akwai Dan nisa sosai.

Hutun farko na makarantar tabi taqarasa hargitsewa sbd yanda kullum saita kaisa ta
daukosa ga lattin fara sanaarta datakeyi Idan taje daukosa,

Dole Inna ce take fara yimata kafin ta dawo daukosa ganin mutane sun fara janyewa
ansamu wata Yar baqin cikin ta fara sana'ar a makwaftansu.

Ganin Inna ma wahalar duniya tafara sakota gaba sbd ayyukan sun mata yawa ko baccin
arziki bata samu sosai dole mama ta ringa karba tanayi sbd Suma su ringa samun
sassaauci tunda Allah yasa yanzu da aikin suka dogara kacokam.

Tsawon lokaci rayuwar tana yanda take garesu ba wani dogon sauyi saima ciwo daya
kwantar da mama Dan haka suka sake zagewa da Sanaa ga Inna itama karfinta yayi
qasa,
Ga Abdul yanzu karatun nasa yafara nisa tunda Yana aji biyu yanzu.

Ita kanta lafiyarta wani lokacin qaranci take mata sbd ciwon mararta har lokacin
Yana taso mata akai akai gashi wani babban ikon Allah dayake kamata shine tunda
tayi Bari lokacin rasuwar Salisu har yau Bata taba yin wani al'adar ba,

Tayiwa Inna maganar innar tace mata wasu matan na hakan musamman Idan suntaba samun
matsala ta Bari Dan haka ko jinin Al'adar zai koma ya ringa zuwa daidai sai tayi
wani auren kilan.

Da Wannan zancen ta tattara maganar Rashin zuwan Al'adar ta watsar tafara neman
wata sana'ar sbd wannan din ta daina tafiya sosai sbd kusan anguwar ganin ana samu
duk sun fara sana'ar shiyasa yanzu ba mutane sosai.

Ganin wata sana'ar taki samuwane
Duk Wanda tafara Bata karbuwa gashi jarin nata tafiya gurin hidimar gidan yasa dole
tafara zuwa aiki wani gida acan GRA da mama Indo qanwar Inna ta Samar mata.

Fara aikinta sai rayuwa kuwa ta sauya musu Dan yanzu da albashin suke komai.

Bata wani jimaba da fara aikin saigashi hajiyar suka tattara suka bar qasar itada
'yayanta dole tadawo zaman gida ba wani aikin.

Jin bazata iya zaman ba aikin komaiba yasa takuma zuwa tasamu mama inda dake shirye
shiryen tafiya Lagos itama aikin Sanaa tace takuma samar mata wani aikin.

"Babu wani gidan aiki Idan ba Lagos Zaki shirya ki bini ba kya ringa musu aike daga
can kokuma abaki Aron kudi ki bar musu Idan munje can kya ringa biyana da kudin
aikinki??"

Haka mama indo ta sanar mata Dan haka batada wani sauran zabi bayan amincewarta sbd
suna cikin tsananin halin nema gskia.

Ko data sanar dasu Inna farko sunso hanawa Amma ganin yanda mama Indo tai musu
bayanin aikine kawai a wani babban restaurant na masu kudi da aka bude Kuma sunada
masauki Mai kyau da restaurant din suka tanadarwa ma'aikatansu a tsaftace cikin
kwanciyar hankali.

Hakan yasa suka amince tareda bawa mama Indon Amanar kula da hadizar duk da ba
yarinya bace.

Kudi sosai hadiza ta karba gurin mama Indo ta siyawa su mama abinci Mai Dan yawa
tareda dinkawa Abdul uniforms har kala biyu da sabbin takarman zuwa makaranta da
slippers harma da sababbin litattafai.

Sauran kudin taje takuma siyo musu sabulan wanka da omon wanki dasu lalle da kanwar
dazasu ringa saidawa daga zaune cikin gida ta damqawa Inna sauran kudaden a
hannunta.

Daga Yaya Umar har Yaya kabiru babu Wanda yayi yunqurin hanata tafiya sbd su yanzu
siyasar gabansu ta ishesu shi Yaya kabiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login