Showing 72001 words to 75000 words out of 78821 words

Chapter 25 - FURAR DANKO COMPLETE BY BILLYN ABDUL

02 Jun 2026

68

Baya yay cikin wani salon da ta samu iska shuuu, ya Wago yana murmushi tare da kashe mata ido Waya, sai kuma ya nuna fuskar tasa da yatsa yana Wan sake matsota harda ranwafowa kaWan.  Duk randa wannan hannun ya sauka kan wannan fuskar da sunan mari to kisa a ranki MAZA sun faWi, faWuwa"

irin ta MUTUWA. dan itace kawai damar da YANWA zata iya samun yin birgima a gaban ZAKI yanda

"take so . Ya ara kashe mata ido Waya yana Waga mata yatsu biyu da faWin,  Bye *MATAR ILLITERATE* ."

Yay gaba abinsa.

"Yuuuuu!! Lulu ta dinga jin hajijiya na neman kwasarta, wato itace ma yanwar yake nufi. Dariya sosai"

"Uncle Yousuf da ke cikin motar dake a kusa da su batare da sun san akwai mutum a ciki ba ke tuntsurawa harda walla. Ashe zaton da yakema yaron nan ya wuce nan. Kai jama'a har ya fara tausayin ar tasa gaskiya. Dan tabbas akwai babban wasa a wannan tafiya yanzu ne kuma za'a fara. Ganin yanda ta wuce tana haWa hanya ga hawaye sun wanke mata fuska ya sashi daina dariyar ya buWe motar ya fito, sai dai duk yanda yake son binta ya haura dan lokacin sallah yayi. Ya kai dubansa ga su Smart da ke"

alwala sai kawai ya nufesu yana gyara yanayinsa kamar bashi ya gama kwasar dariya ba a mota...

Bayan an idar da salla kusan a tare suka fito. Uncle Yousuf ya dakatar da Smart da ke sallama da su

"maigadi akan ya jira su wuce tare. Kamar zai ce a'a sai kuma dai yay shiru dan kiran da Abba yay masa suna oarin shiga massalaci akan idan ya dawo gida ya sameshi falonsa yanzun nan. Yasan maganace da Abban, shi kuma da yayi niyyar bama masu bin san nan a baya dama dan ya tabbatar ba haura sukai ba su kamashi dan yana son yin magana da koma waye ya turosun. Babu yanda ya iya dole yabi Uncle Yousuf Win, shiko ya aunaci ALLAH ya kaisa har gida yau. Tunda suka fito kuma yaga motar nan sai dai ba napep Win yanzu, motar dai ce ke cigaba da binsu yanzu ma. Suna isowa titin anguwarsu yaga sun dakata cikin takaici direban motar na kaina sitiyari duka alamar ba haka sukaso ba. Sai dai kuma abinda"

bai sani ba shima Uncle Yousuf ya san da su shiyyasa ma ya Wakkosa ya kawo har gidan.

" Alhaji yau na saka ka aiki, Nagode sosai ."

"Murmushi Uncle Yousuf da idonsa ke kan mirror yana kallon mutanen nan ya saki, tare da faWin,  Har"

yanzu dai ina a Alhaji na? A tunani na na zama Uncle yanzu tunda a zan bayar duk da auren wucin gadi

"ne . Yanda Uncle Yousuf Win ya are maganar ne ya saka Smart kallonsa, sai kuma ya Wauke kansa yana sakin murmushi ya ce,  To ayi hauri Uncle ."

" Shike nan na haura, dan dama ba'a san iyaye da fushi da aansu ba. Ina fatan zaka samu Abba da"

maganar yau ko? .

 Da wuri haka? .

Smart ya faWa da mamaki yana kallon Uncle Yousuf Win.

" Dole ne muyi da wurin, dan Wazun Baba ya sake kirana akan zuwan M Atik Kumo shima yana"

"nemawa Wansa aurenta, sannan Alhaji Sulaiman da Wansa sun gama ulla matakin da zasu Wauka a gobe idan ALLAH ya kaimu  tsaf ya zayyane masa komai shima. Mamaki ne ya sake lulluSe Smart, yayinda a"

"asan zuciyarsa yake ta lissafi akan yanda zai canja salon wasan a yanzu tsakaninsa da Alh. Sulaiman. Kafin yanzu shi bai wani Wauki zancen da muhimmanci ba, dan har ya gama ulla yanda zai kuSuce wa al'amarin, sai dai a yanzun nan ya canja sabuwar shawara. Duk da bai san minene dalilin Alh. Sulaiman Win ba ya kamata ace ya nuna masa shima tsageran kansa ne a wannan gaSar. Bai damu da zancen MM"

Atik Kumo ba.....

 Aliyu kayi shiru!

Uncle Yousuf ya katse masa tunani. Iska ya Wan furzar kaWan sai kuma ya fuskanci Uncle Yousuf Win.

"Cikin sake furzar da wata iskar ya ce,  Please Uncle kozan iya sanin yaya kuke da shi Alh. Sulaiman Win? ."

 Yerh babu damuwa Aliyu. Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko Wane ga Alhaji Sufi Ado Garko. Sannan Yaya

"ga mahaifiyar Mawaddat uwa Waya uba Waya. A shekarun baya Wan uwana mahaifin Mawaddat abokai ne da Alh. Sulaiman na ut-da-ut, dan sun haWu ne tunkan ya auri mahaifiyar Mawaddat Win adalilin shi Baba da ya ja Yayana jikinsa. Sai dai a yanzu ba haka bane, dan bamu san minene ya shiga tsakanin wannan amintaka ba abokan biyu suka zama maiyan juna ta yanda ko inuwa Waya basa sha. Iya tambaya na yima Yaya amma yai faWa min komai. Shi iyakarsa fita harkar Sulaiman, amma shi Sulaiman a bayyane yake nuna tsanarsa garesa da mu ma ahalinsa gaba Waya shiyyasa Yayana yay ruwa yay tsaki wajen hana aure tsakanin Tajuddeen da Mawaddat dan yace akwai manufa. Wannan shine iya abinda na"

sani gaskiya .

Kai Smart yake jinjina wa cike da gamsuwa. Sai da Uncle Yousuf yay shiru sannan shima ya bashi

"labarin kamasan da Alh. Sulaiman Win yayi a randa yazo shi da Ahmad suka roesa ya koma aiki, ya kuma"

sanar masa aikin da yace ya koma yay masa tare da nuna masa motar yaran Alh. Sulaiman da ke tsaye a

bakin layinsu kasancewar suna iya hango su da ga nan ofar gidan su Smart Win da ke a bakin titin.

"Sosai al'amarin ya girgiza Uncle Yousuf Win, ya kuma tabbatar masa da shima dalilinsa na kawoshi"

"gida yanzun. Dan tunda suka kammala waya da Baba yaji a ranasa Alh. Sulaiman zai iya Waukar mataki kowane iri ne akan Smart shine ya saka wani Wan sanda zuwa office Win Lulu ya saka masa ido, Wan sandan ne ma a Napep ashe, sai ko gashi bayan tahowarsu gida Wan sandan ya tabbatar masa ana binsu...  Wato Aliyu idan na fahimta tun fara aikinka da mu Alh. Sulaiman na biye da lamarinka kenan? Kuma bana raba Wayan biyu a wajen Tajuddeen ya sani. Lallai ya kamata musan dalilinsa danni zuwa yanzu har"

Tajuddeen Win ma na saka masa alamar tambaya .

" Sanin dalilinsa abunne mai saui Alhaji, yanzu dai barshi na fara masa duka a ciki, bayan cikin ya"

"ulle zai amayar da duk abinda ke a ransa da kansa. Sannan Tajuddeen bai zama lallai yasan komai ba, zata iya yiwuwa amfani uban keyi da shi batare da shi ma ya sani ba ."

"Murmushi Uncle Yousuf yayi tare da bubbuga kafaWar Smart, dan tsaf ya fahimci inda zaurancen nasa"

"ya nufa game da duka a ciki. Murmushi shima Uncle Smart Win yayi tare da buWe motar yay masa godiya ya shige gida, shi kuma yaja motar yana ara jin aunar yaron har tsakkiyar ransa. A rayuwa yana matuar auna da son jarumin mutum. Musamman ma matashi irin Smart mai tsayyar zuciya. Wannan nagartar tasa ya fara hanga a filin wallo ya shige masa zuciya, faruwar addarar data nema dakushesa da ga cikar burinsa ta fara sakashi jin tausayinsa da laluben hanyar da zai iya taimaka masa. Bayan yin dogon nazari ya yanke shawarar kusantosa gefensa domin ara tabbatar da halayensa kafin ya ja hannunsa hanyar da ya gama shiryawa domin kaisa ga cikar burin nasa. Sai kuma ga al'amarin ar Wan uwansa ya gitta a cikin labarin tamkar bakangizo a tsakiyyar gagarumin hadarin da ke gab da zubda ruwa. Fatansa kawai ta kasance bakangizo mai amayar da ruwan da ta shanye bamai haWiyewa ba har"

abada.

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

"*KINSAN SUNAN LABARAN?,. GASU KAMAR HAKA*"

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR  KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay at

1487616276

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan

09033181070

VIP

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*

Zafafa

5525)5"5'5

 5A5P5M5<5M 5?5<5I5F'5J.....!!

5i5؊5؍5ؚ5؏ 5h5؃5؅5ؖ5؍5؍ 5؄5؆

5j5؉5؂5ؑ5ؕ5؆5ؓ

.......Bai samu ganawa da Abba ba sai bayan sallar isha'i ya samesa a falonsa. Bayan sun gaisa cikin

"dakewa Abban ya ce,  Aliy! ."

Ya amsa da  Na'am Abba .

 Aliy!

Ya sake ambata. Shima sake amsa masan yayi kamar farko. Malam Mika'il bai gajiya ba ya sake kiransa a

karo na uku shi kuma ya amsa masan dai kamar yanda yay na farko da na biyu.

 Na kiraka sau uku ko? .

Kai ya gyaWa masa alamar eh.

" Na kiraka badan tisa maka sunan da ni na saka maka ba ne, na kiraka ne domin a yau zan tabbatar"

maka da magana ta arshe ne akan aurenka. Dan duk maganganun da Yahanasu ta faWa Wazun akanka sun sosama mahaifiyar ka da nima kaina zuciya. Kuma mun Wauki alawarin bazaka sake rufa wata anan

"gidan babu matar aure ba. Dan haka a yanzu ina son jin ta bakinka, idan kana da wadda kake so sai ka"

"faWeta, idan kuma babu mahaifiyarka ta maka mata, nima kuma na maka sai ka zaSi guda a ciki. "

"Sai da ya Wan rumtse idanunsa da jan numfashi, sannan ya Wago a hankali ya kalli mahaifin nasa. Sai"

"kuma ya sake maida kansa ya duar.  Kuyi hauri Abba duk ni ne na ja muku, amma insha ALLAH komai yazo arshe, ba sai kun nemomin mata ba ni da kaina ma na samota ."

"Wata irin ajiyar zuciya Abba ya sauke a hankali, sai dai cikin dakewar san nan ya ce,  Wacece? ar"

wanene? A ina kuma ta ke? .

"Duk da yawan tambayoyin bai gazaba wajen amsasu ga mahaifin nasa. Ya ce,  Yarinyar da nake"

aiki gidansu. iya ga Alhaji Isma'il Jiamshi. A yau suma kuma suka buaci na turo iyayena dama in har

na shirya .

 Alhamdullahi. Aliyu Hydar ka daWe baka faranta min rai irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Ya yaye

maka dukkan damuwarka. Ya Wauraka akan maiyanka. Ya kawo maka mafita ga al'amuranka. Na amshi

"zaSinka badan ta kasance Wiyar Alhaji Isma'il Jiamshi ba, ko dan yana da kuWi, sai dai dan nasan kai nagartaccen mutum ne da bazai taba yin zaSen tumun dare ba. "

(Abba ka gafarceni wannan dai kam zaSen tumun asubace ma arewar dare) ya faWa a zuciyarsa. A

"zahiri kam murmushi kawai yayi da faWin,  Nagode Abba. ALLAH ya ara lafiya da nisan kwana mai"

amfani. Ku gafarceni akan dukkan abinda nai muku ba dai-dai ba kuma insha ALLAHU zan cigaba da zama

a fiye da yanda kuke buata .

"Sosai Abba yay murmushin jin daWi, Aliyu na cikin aan da yafi auna a cikin aansa, sai dai shi"

"kansa a wasu lokutan bai san mike danne soyayyar ba yayta kyararsa da hantararsa a dalilin addarar da wani bai isa ya canjata ba. Albarka sosai ya saka masa sannan ya sallamesa. Koda yabar wajen Abba cikin gida ya shiga, sai dai kai tsaye Wakin Ammah ya shige yau bai gaida kowa ba a matan gidan. Ya samu tana shirin fitowa kaima Abba abinci dan yau itace da shi. Ya fahimci tana cikin damuwar da ya san babu makawa akan abinda ya faru Wazune tsakaninta da Umma. annensa kansu yau basa cikin walwala. Suna gama gaisawa Ammah ta fice, annan ne Hawwah ke bashi labarin faWan da akai sosai ne ai yau Win kuma duk a sanadinta ne. Da ga arshe aka are da musu goron halin da yake a ciki. Sosai ya ara jin zuciyarsa"

ta Zafafa. Sai dai komai bai ce ba yay musu sallama ya tafi makwancinsa......

*_WASHE GARI_*

Washe gari batare da sanin kowa ba Abba da tawagarsa suka nufi gidan Alhaji Isma'il Jiamshi

nemawa Aliyu Hydar auren Mawaddat Isma'il Jiamshi. Sun sami tarba ta mutunci dan har Baba ma yazo gidan shima. Abinda zai birgeka babu yama ko hantara irin ta mai kuWi ga talakawansa. Abin farin ciki da mamaki ashema Alh. Sufi Ado Garko school mate Win Abba ne ma a secondary school. A take hira ta kaure a tsakaninsu har zuwa kan abinda ya tarasu. Sai dai kuma bayanin da shi Baba yazo da shi ya

girgiza su a wajen. Dan a ganinsu babu wani shiri ai tare da su game da haka. Baba ya kwantar musu da

hankali tare da tabbatar musu da dalilansa masu warin gaske ta yanda su duka suka gamsu da hakan.

Sun Wan ara tattaunawa sannan sukai musu sallama cike da jin daWin karramawar da suka samu suka suka taho akan sai anjima idan sun haWu Win....

&&......

Sam Smart bai san mima ake ciki ba. Dan hatta zuwan nasu Abba bai san da shi ba saboda yau bai ma

fita aiki ba. Tunda ita tace ta koresa da kanta a ganinsa babu amfanin ya koma su sake raba hali. Dan haka ya zaSi yin kwanciyarsa a Waki yayta buga game Winsa hankali kwance har lokacin sallar juma'a ya gabato. Yana shirin shiga wanka Ahmad yazo gidan. Zuwan Ahmad gidan ba sabon abu bane garesa dan haka bai damu ba. Haka koda ya bashi shadda sabuwa fil yace ita zai saka bai kawo komai a ransa ba dan

"Ahmad Win ya sha musu Winki irin hakan, haka shima kansa yasha yi musu Winki a taren."

"Bai wani Sata lokaci ba ya fito a wankan, Ahmad na zaune har ya kammala shirinsa. Yayi yau matua"

"kamar ka sacesa ka gudu. Ahmad ya wani shiga masa ruwan turare. Warce turaren Smart yay yana hararsa da faWin,  Kaifa a duniya kamar baka san wahalar kayan duniyar nan ba. Anata wannan yanayin zaka aramin turare haka dan neman hanyar talautani ."

Dariya kawai Ahmad yay masa da kashe ido Waya ya furta  Am sorry Zakin zaki .

Shima dariyar yay a karo na farko. Dan duk sanda ya kira shi da Zakin zaki yana nufin shi Win na Coach

Hameed kenan yayansa. Cikin nishaWi da farin cikin tsokanar juna da suke na kiran tuzurai suka fita. Jan Ahmad yay suka shiga ciki gaida Ammah. Ta saka masu albarka tare da addu'a data so tsayama Smart a rai. Amma sai ya danne ta a asan rai da tunanin Ammah tayi addu'ar ne kawai domin gabansa. Daga haka suka taso suka fita acewarsu zasuje sallar juma'a su dawo nan suci biranuskon da Amma keyi

matsayin abincin rana...

 Wai wane massalaci zaka akaimu haka ne? .

Cewar Smart yana kallon Ahmad dake drivering a nutse. Murmushi Ahmad yay masa idonsa a titi ya

"bashi amsa da  Mi kakeci na baka na zuba? Zaka gani ai . Baki Smart ya Wan taSe da cigaba da game Winsa a waya. A haka suka cigaba da ar hirarsu har suka iso massalacin juma'ar. Zamansu babu jimawa aka fara khuWuba, dan haka suka nutsu wajen saurare har aka kammala. Ana oarin tada salla ya hango Uncle Yousuf da Coach da ke isowa yanzu, da alama sun makara ne. Baice komai ba ya gyara tsaiwarsa aka tada salla. Kasancewar bayan idar da sallar juma'a yin Waure-Wauren aure a massalacin normal ne yasa bai kawo komai a ransa ba. Sai dai haka kawai yake jin sa wani iri yau kamar wani abu na shirin faruwa da shi. Ga kansa da ke ciwo asa-asa amma dai sai ya daure tunda bawai ya matsa masa da"

yawa bane. Wani irin harbawa da dokawar irji ce ta samesa a lokaci guda a dalilin jin sunansa matsayin

angon da aka Waurama aure da amarya mai suna Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiamshi. Shi al'ajabi ne ma

"ko ruWani yama rasa ganewa. Ya dubi Ahmad da ke kallonsa yana dariya,  Kai nifa ban ganeba wlhy, wai waye haka mai irin sunana komai da komai fa ."

Sake tuntsirewa da dariya Ahmad yayi har da rie ciki. Sai da yaga Smart ya turSune fuska har yana

"harararsa sannan ya Wan sassauta. Sai dai maimakon amsa masa sai ya mie dan yau dama Waurin auren biyu ne kawai ma, bayan an Waura na farko da ya kasance Smart da Lulu na biyun kuma aka fahimci shima dai da amaryar farko ne da wani angon, dan kuwa dai Alh. Sulaiman ne ya ulla, abin mamaki kuma babu shi a massalacin sai Tajuddeen kawai da gayyar abokansa. Yana jin kuma an Waura auren Lulu da Smart ya yanke jiki a wajen ya faWi. Su dai mutane basu fahimci minene matsalar ba, haka ma su Abba magabatan Smart dan sai da aka tashi idonsa ya gane masa mahaifin nasa da tawagar dattijan anguwarsu. Sagade kawai yay yana kallonsu kamar television. Abba da ke kallonsa da murmushi ya ce,"

" an nema daina kallona ni, ko duk murnar ce ta saka sumar tsaye ."

Dariya dattijan suka sanya har da Baba. Uncle Yousuf da ke jin ALLAH ya gama masa komai a yau ya

"matso ya kama hannun Smart cikin nasa ya jasa ya rungume.  FATAN ALKAIRI SURUKINA . ya faWa cikin kunnensa. Kamar wanda aka farkar a barci Smart ya ja nannauyar ajiyar zuciya. Cikin marairaice fuska alamar yaya haka.. yake kallon Uncle Yousuf. Shiko ya sake faWaWa dariyarsa da Wan Wage kafaWa alamar nima ban sani ba. Coach ma rungumesa yayi yana mai jera masa addu'oi. Shi gaba Waya ma ya kasa iya furta komai. Sai da Ahmad yaja hannunsa gaban su Baba sannan ya motsa gaSSansa da yar. Rissinawa sukai suka gaida Baba da ke zagaye da manyan mutane ciki harda gwamna. Abin zai baka mamakin yanda har aka iya haWa mutanen bayan auren babu wani shiri a cikinsa. Koda yake ba abin mamaki bane idan akai dubi da girman Alh. Sufi Garko Win da arfin ikon da yake da shi wajen manyan jihar. Sosai manyan mutanen nan suka dinga saka masa albarka kowa na jansa jiki ganin yanda Baba ya dame hannunsa cikin nashi shima. Daddy ma sun gaisa yana ar fara'arsa dai. Daga haka suka ringuWa zuwa government house. Dan sakamako gwamna ne ya bada auren Mawaddat matsayin waliyyi yasa shi shirya liyafar cin abinci bayan Waurin auren. Smart dai ya zama kamar wani butun butumi. Komai Waukarsa yake kamar a mafarki. Ga kansa dake ara nauyi matua har idanunsa na Wan rinjayar ganinsa. Amma dai yanata dakewa kodan fidda mahaifinsa kunya. Dan duk da Malam Mika'il Idris Mawashi ba mai tarin dukiya bane. Dattijo ne nagartacce mai cikar kamalar da masu kuWun dole suga girmansa da jin shakkar kawo masa raini.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login