Showing 168001 words to 171000 words out of 196133 words

Chapter 57 - IDAN BA KE by Nimcyluv sarauta

09 Jun 2026

121

kuma yana shafa mata tare da hura mata iska a kunne, tayi luff
tana riƙe shi gam!.
Numfashinta mai zafi ya fara sauka a ƙirjinsa alamar tayi barci cikin nutsuwa ya
zameta ya gyara mata kwanciya, tare da ja mata duvet ya sumbaci goshinta tare da
cikinta data ɗora hannu akai, bai san ya ya yake ji game da ita, ya kuma kasa
fahimtar yadda zai fasalta ko bayyana al'amarin, kalmar Ina son ki tayi ƙanƙanta a
gareta, sam! Ta shige hakan, kawai abu ɗaya ya sani aikatawa a bayyane kamar yadda
ta zama wani sashe da sashin jikinsa.
Ya shafa kanta ganin ta tura baki tare da marairaice fuska kamar ƴar tsana she
looks like takeaway. Ya fita bayan yabi kusurwar ɗakin da addu'a kana yaja mata
ƙofa ya nufi part ɗin Zahrah yana riƙe kansa tare da kame fuska ya dawo Yaa Sheikh
Aliyu haydar Aliyu ya fita daga Yaa Sheikh ko kuma malamin Danejo Rome.
Zahrah na zaune ta riƙe Jikinta sbd magungunan data sha, gabaɗaya a sama ta sha ga
wani magani goran tula mai saukar da ni'ima sai duk ta birkici, ƙamshin turaren
Roja ya ruga sallamar Yaa Sheikh zuwa wacce ya yi a kamalance tana ganinsa ta miƙe
tsaye fuskarta ɗauke da murmushi ta rungome shi ta ce
"Wlcm Sweetheart, har na fara tunanin zuwa gareka" Ya jinjina kai tare da zareta a
jikinsa a hankali ya ce "kizo part ɗina" yana faɗin haka ya juya ya fita, sbd
turaren dake hautsina kansa amma bai nuna ba, ta ce "Ok I'll be there"
Ta ƙara fesa perfume ta shan magani wanda ya sa duk ta lalata kanta, yana zaune ya
sauya kaya zuwa na barci ash colour hannunsa riƙe da coffee daya samu an ajjiye
masa, ta faɗo ba sallama yaƙi kulata da kanta ta miƙe ta fita ta sake shigowa ɗauke
da sallama ya amsa yana miƙewa zuwa bathroom ya yi brush da alwala ta kariya, ya
sameta kwance ya kwanta yana kashe hasken ɗakin.
Zahrah ta ce "Me ya kake samun Halisa har part ɗinta, amma ni sai nazo naka akwai
fa'ida hakan ne?" Bai kalleta ba cikin gajiyawa ya ce
"Banda hayaniya please"
Ta jawo Jikinta zuwa nasa ta riƙe shi tare da ƙoƙarin haɗe kissing nasa, ya yi
saurin zame fuska yana sakar mata murmushi tare da kissing goshinta.
Zahrah ta ce sam bata san Wannan ba, ta birkice masa, gabaɗaya gangar jikinsa ta
kasa amsar saƙon da take tura masa, yana da biye da ita gudun saɓawa mahalicci da
gaske tana tsananin buƙatarsa da kulawarsa gareta, ya yi yaƙi da zuciyarsa bada
wasa ba yana kiran sunan Allah a haka ya samu sassauci ya fara kyautata mata, amma
sam ya kasa yarda yaji bakinta a nasa. Yaa Sheikh na fita Halisa ta buɗe ido,
zuciyarta na bugawa ta riƙe kawai domin wannan daren tabbas zai shiga cikin kundin
lissafin ajjiye muhimman abubuwa, zai zama dare mafi tsayi da muni a tare da ita
duk wani mai sonta dole ya tausayawa mata, yau Abbanta ne zai kwana tare da wata?
Ɗaki ɗaya,gado ɗaya? Maybe na jiki ɗaya. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un" ta
furta tana fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ko cikakken abinci ta kasa ci
yau, taji a ranta idan akwai abinda zai bata matsala acikin aurenta bai shige
kishin da take dashi akan Abbanta Yaa Sheikh ba, tayi kuka sosai daga ƙarshe ta
miƙe tayi Alwala tare da ɗaukan Alkur'ani sai dai sam bata ganewa kuma bata
fahimta, gudun kada tayi saɓo ta ajjiye ta fita zuwa main parlour barci tuni ya
ƙauracewa Idanunta, ta zauna a kujera tana kuka ƙasa-ƙasa.
Zahrah taga Yaa Sheikh ya tsaya cak bai taɓa ganin abin al'ajabi da almara haka ba,
ki da can baya da yake riƙe kansa lafiyayye ne shi, amma yanzu daya nufi hanyar
samawa Zahrah nutsuwa sai maɗaukan suka daina ɗaukan sati ta zama tamkar ruwan da
tsumma ya jiƙa tare da kwanciya tayi barci irin barcin nan da zakai zaton namiji
nakashasshe ne...



Sorry For the shortly👏🏽
[2/6, 7:58 AM] Abk: *Follow my Facebook page👇🏾*
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL

Ta shi Yaa Sheikh ya yi sbd tsananin kunyar Zahrah daya lulluɓe shi, bai san yadda
zata ɗauki al'amarin ba, ya nufi bathroom ɗin shi tare da sakarwa kansa shower,
idanunsa lumshe yana kiran sunan Allah maɗaukakin sarki, wanda ya samar da sammai
da kassai bakwai, ya wanzar da sirrai a cikinta, ya samar da ƙasa, wacce muke
tafiya a kanta, ya halicci mutane da dabbobi da dukkan abin dake da rai. Ya sauke
numfashi wannan abu shi ne mafi tsayuwa a ranshi, yana ganin abin al'amara amma
wannan ya banbanta, ya kai duban shi ganin yadda yanzu komai ya daidaita kamar ba
yanzu ne maɗaukan suke barci ba, ya ƙara sakin ruwa sosai tare da ɗaura alwala ya
sanya bathrobe ya fito jikinsa na zubar da ruwa. Zahrah ta dube shi Idanunta cike
da hawaye sosai ta ce "Na sani, ba zaka iya ba amma daka sani da baka fara mini
abinda zai sanya na samu matsala da tunani na ba, ina jin kamar Allah ya ɗauki
raina kafin cikar lokacin da Dr ya faɗa"
Ya dubeta lokacin da yake taje gemunsa mai tsafta, kaifin idanunsa a kanta ya sanya
ta kasa cewa komai sai kawai ta fashe da kuka na baƙin ciki tana rufe fuskarta.
Bai ƙoƙarin hanata ba, yasan da zaifi hakan ga ko wacce mace musamman ita da ga
yadda al'amarin ya kasance, zata iya zargin wani abu, duk da zato zunubi ne.
Ya shimfiɗa prayer mat bayan ya sanya farar jallabiya tare da tayar da sallah, ya
jima yana Sallah tare da addu'ar Allah ya nuna masa manufar sabon wannan al'amarin
a cikin maɗaukan shi ya yin barci, kamar yadda ya saba yin gamo da sabbin al'amura
cikin rayuwar shi. Har lokacin daya idar kuka take ya dubi agogo a hankali da sauri
kuma ya rufe idanu ganin 2 da wani na dare, gently ya miƙe tare da nufar kan gadon
ya zauna cikin laushin murya da gajiya da jin kukan nata ya ce
"Zahrah" ta ɗago kai ta kalle shi ya numfasa ya ce "Kuka? Name?"
"Kafi kowa sanin kukana Yaa Sheikh wallahi...,"
Ta kasa ƙarasa maganar tana fashewa da kuka sbd ita kaɗai tasan ciwon da mararta
yake mata, ya jawota ya rungometa jikinsa ya shafa kanta ya ce
"It's okay, ki barwa Allah komai cikin lamuranki, ban san yaya ne ba, ban san
matsalar ba kiyi addu'a just pray" ta riƙe shi gam! Numfashinta na fita da ƙyar
raɓuwa da take a jikinsa wani tsananin a zaba take ji sbd wutar abinda ke cinta ta
ce.
"Kayi mini al'ƙawarin farin ciki, ina son samun baby dakai kafin Ubangiji ya ɗauki
raina" ya girgiza kai yana ɗan faɗaɗa fuskarsa wacce hakan ya sanya gemunsa motsawa
yana gogar fuskarta ya ce.
"Idan kina son rahamar Ubangiji da kuma farin ciki ga rayuwarki da mijinki, You
should stop lying" kukanta ya tsaya tayi saurin kallonsa ta ce
"Ƙarya?" Ya jinjina kai ya ce "Eh, idan za kayi ƙarya don ka samu wani abu, sai
Ubangiji ya baka abin kuma ya barka kai da shi daga ƙarshe ya zamana abin bai
amfana maka da komai ba" ya numfasa cikin gajiyawa amma ya zama dole ya fahimtar da
ita abinda bata sani ba, domin ya lura Empty head ce ya gyara zama cikin tarin
nutsuwar shi ya ce "Kin ya ƙarya kina da Cancer, kin manta ni likita ne?" Bakinta
na rawa Zahrah ta ce
"Ni... Ni.. yaushe?" Ya tsareta da idanunsa masu kaifi wanda ya tilasta mata yin
shiru ya ce "Kada Kiyi musu, kowa da baiwar da Ubangiji ya yi masa, haka kowa da
naƙasun da yake da shi a rayuwa, na sani na sani, i knew everything da ki ke
harding, ban aure don naji tausayinki ba, ban kuma aurenki don ina son ki ba, haka
ban aureki don inci zarafin ki ba ni da kai na bani da dalilin aurenki, amma na bar
hakan matsayin ƙaddara wacce take zama zanan dutse, duk wayonka, da iliminka, duk
na gartar da Ubangiji ya baka sai ya jarabce ka da ƙaddarori masu zafi domin ya
gwada imaninka, idan kayi haƙuri ka miƙa lamarin ga Ubangiji sai Allah ya duba ka
kuma ya sanya hannu cikin al'amarinka, ke ƙaddara ta ce ke kuma soyayyar da ki ke
mini ita ce ƙaddararki"
Idanunta ya cika da hawaye kunya ta kamata, Allah da kansa ya ce fazakkir fa'innàl
zikkira tamfa'ul mu'uminun. Yaa Sheikh ya ƙara samun ƙarfin gwiwar fahimtar da
Zahrah ya tallafo haɓarta yana bin fuskarta da shekaru ya ce "Kin san za a haifeki?
Kin san zaki karatu mai zurfi? Kin san zaki haɗu da Father? Kin san zaki samu ciki
har huɗu? Kin san zaki haɗu da Saif-wazir? Kin san saki aureni? Kin san zaki haifi
Muhammad?" Ta girgiza kai jiki duk a mace ta ce
"Ban sani ba" a taushashe yana sakin fuskarta ya ce
"Allah ya sani, tun kafin haihuwar ki ya rubuta hakan jikin allon lauhil-mahfuz,
allon da baya ƙarya bawa baya shige ƙaddarar shi, baki san ina jin tsananin nauyi
da kunyar kai na na auri wacce tayi hulɗa da wanda nake kallo matsayin Uba? Na
kanji sauƙi idan na tuna babu haramci, ba ke ba ko Mother zan iya aura idan hakan
ya zama ƙaddarar Aliyu!" Ya miƙe tsaye ganin kamar lokacin kiran sallar farko ya yi
ya ce "One thing da zan faɗa miki, ki dai na yarda da mutum akwai wanda suna zaune
da kai domin su samu abin faɗa akan ka acikin mutane, akwai wanda zasu ya beka bisa
raɗin kansu a baya su zageka, akwai wanda su da kansu basu dalilin daya sanya suke
tare da kai ba, zaka birgesu har zuciya amma zasu zageka, masu yin hakan kuma
Ubangiji ya tana dar musu makoma domin laifin bawa akan bawa saɓo ne mai girma da
zunubi, ki tsarkake harshenki daga cin naman mutane ko cin mutuncin su"
Ya ƙara sauke numfashi gajiya duk ta bayyana a jikinsa ya ce "Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: lokacin da aka yi Mi'iraji dani, muka hau sama
sai naga wasu mutane da baƙaƙen farata suna yage fuskokinsu da ƙirjinsu, na tsorata
da hakan nace Ya ɗan uwana Jibrilu su waye wannan?" Sai ya ce mini "Su ne wanda
suke cin naman mutane da cin mutuncinsu su" Anas bin Malik
(RA) . Yaa Sheikh bai gushe ba sai daya ƙara bata fatawa da faɗin Ibn Abu Shaiba
ya ruwaito shi a cikin
Musnaf ɗin sa ya ce Manzon Allah
(SAW) yana cewa:
“Wanda ya ci mutuncin
ɗan uwansa za a yi
masa suturar wuta (a
Lahira), idan mutum ya yi ba daidai ba kira shi ka sanar masa da kuskuren shi domin
ya gyara”.
Zahrah Jikinta ya ƙara sanyi sosai gabaɗaya bata san Wannan ba, musamman daya
kasance kaf zuri'arsu ilimin ya hudu ya yi musu gurbi a zuciya, Zahrah kuma tazo ta
fisu ilimin daman kuma ace abin cikin kwan yafi kwan daɗi, kyan ɗa ya gaji ubansa,
kuma ko wanne tsuntsu kukan gidansu yake. Taji ta tsani kanta,kuma ta tsani komai
zafin iyayenta da basu kyakkyawan ilimin addini ba ya shigeta. Ta kalli Yaa Sheikh
cikin kuka ta ce
"Da gaske baka so na?"
Bai iya ƙarya ba, kuma baya son farata ba zan faɗa mata gaibu domin taji daɗi ba,
sbd yasan babu hakan a ran shi ya ce "Eh, ban san me gaba zata haifar ba kiyi
addu'a" ta miƙe tare da faɗawa jikinsa ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi,
soyayya masifa ce, musamman Allah ya haɗaka da wanda baya son ka kuma jarrabawa ce,
ita kam zata iya cewa Soyayyar Yaa Sheikh ita ce girbin abin data shuka na saɓon
Ubangiji tun a duniya. Ya ɗan rarrasheta kana ya koma Bathroom ya wanke jikinsa
domin a jininsa yake jin ta ɓata shi ga ɗan abin da ya yi mata.
Da sauri ta nufi steps na benen zata yi downstairs ganin Halisa zaune ta riƙe kanta
tana kuka ƙasa ƙasa ya sanya Zahrah taka tawa. _"Zahrah think, Kada ki zama abar
gori wajan kishiya"_
Zuciyarta ta faɗa mata haka, tayi saurin komawa da baya tare da laɓewa ta kurma ihu
ta ce.
"Wayyo Allah Yaa Sheikh zan mutu, ka bari wallahi ban saba ba, zaka ka sheni na
tuba nayi ladama wayyo bayana Wayyo marata I love you so much sweetheart" Halisa ta
firgita tare da miƙewa ta saka hannu ta toshe kunnenta.
Ɗan cikinta ya juya ya daki mararta ta fara gani dishi dishi zuciyarta kuma tayi
wani kyakkyawan bugawa. Zahrah ta leƙo ganin Halisa cikin wannan yanayin ya sanya
ta ƙara sakin wani ihu ta ce.
"Yaa Sheikh da gaske kake faɗa mini Halisa bata daɗi? Bata iya komai ba, ka daina
faɗa kada taji babu daɗi" ta ƙara yin shiru ta ce
"Na gode sosai ban taɓa sanin cewa kafi so na fiye da yadda ka ke son Halisa ba sai
yanzu, na gode da kyautar fili da kuma kamfani wayyo i love You so much" Halisa ta
gigice ta dinga kiran sunan Allah da karfi tana dafe cikinta, iya tsorata da
firgita tayi sosai tun tana kiran sunan Allah daya kawo mata ɗauki har tari yaci
ƙarfinta ta kifa tare da buga kanta da jikin kujera.
Zahrah was happy ganin Halisa cikin wannan yanayin, and she don't feel anything
data aikata, ta juya zuwa bedroom ɗin Yaa Sheikh ta same shi tsaye a gaban mirror
ya kafe waje guda tare da riƙe kansa da hannu ɗaya, she hope ace bai ji abinda ta
faɗa ba. Ta ƙarasa tare da tafa kafaɗar shi ta ce.
"Sweetheart" Ya juya ya kalleta taga idanunsa jajir tayi murmushi sai shi shima ya
yi murmushi, gabanta ya faɗi ganin haƙuri guda ɗaya dal a tsakiyar bakinsa, ta juya
ta kalli mirrow bata san lokacin da fitsari ya fara zuba daga Jikinta ba, ta cikin
madubin taga Rabi jikin aljani rabi jikin Yaa Sheikh ya koma wata suffa mai munin
gaske, taji ya taɓa ta ya ce
"Fitsari a nan Zahrah?"
Ta kasa kallon shi domin ba fitsari ba, wallahi hatta kashi zata iya a wajan ta
ƙara kallo cikin madubin, wani razannan ihu! Ta fasa ganin wani narkeken maciji
yana yawo, babu addu'a ta fara ihu tana faɗin.
"Asstagafirullah no no, what's is that..." Dum! Aka kashe hasken ɗakin ya zama
baƙiƙƙirin sululuu kuma taji abu yana ratsawa ta cikin rigarta tare da shigewa
cikin wandon jikinta ta ƙara yin wani ihun tana faɗin "Dad, Mimi help wayyo Ya zama
Aljani wallahi aljani someone please help me"
Sai kuma hasken ɗakin ya dawo ta haɗa zufa Jikinta banda ɓari babu abinda yake. Ta
juya taga Yaa Sheikh tsaye a kanta ta girgiza kai sai ya wangale mata haƙuri ɗaya
ta miƙewa tana layi zata kifa kafin ta faɗi sai taga babu komai a wajan ganinta ya
ɗauke. Yaa Sheikh dake bathroom ya kifa kansa a sick kamar an dasa shi Jikinsa ya
jiƙe sosai da zufa sai karkarwa naman jikinsa yake, kamar a mafarki yaji Zahrah ta
fasa ihu ya ɗago kansa dake sara masa sosai ya dafe da hannu ɗaya tare da murɗa
handle ya bita daga bathroom ɗin, Ya she ya samu Zahrah kanta ya bugu sosai ya
ɗagota yana ɗan bubbuga kumatunta domin jin jikinsa yake kamar an masa dokan tsiya,
ya ce "Fatymerh?" Ya daɗe kafin ta saki numfashi ta buɗe idanu tana arba da shi ta
saka ihu zata gudu ya riƙeta da kyau ya fara mata addu'a ya lura kamar tsoran shi
take ko an firgita ta ohhu!?
Da taimakon addu'ar ta ɗan dawo hayyacinta sai ta fashe da kuka ta ce
"Wallahi gidanmu zani, kashe ni za'ai" da mmki ya ce "kisa? Akan me" tana kuka
sosai ta ce
"Kawai zani, amma akwai Aljanu a gidanka" ya ɗan yi jim! Sai kuma ya yi ɓoyayyen
murmushi ya ce "Gidan Malam guda da Aljanu? Sai dai idan Malam ɗin ne Aljani da kan
shi, Kinga tashi muhimmancin addu'a kenan" ta miƙe tana riƙe da shi amma ta kasa
kallonsa gani take kamar zata wawulon shi mai haƙuri ɗaya ya ce
"Sallah" da sauri ta ce
"Nima sallah zan yi" mmki duk ya addabe shi ya yi mata kallon tsaf! Ya ce "La
sallah Ala, ban janabati sai kinyi wankan sarki" ta ce "Mene wankan tsarki?....


Afuwa my Special kunji shiru, ku tayani da addu'a kawai Please... Kwana biyu sai a
hankali.
[2/7, 8:12 PM] Abk: *_Arewabooks@Nimcyluv 73_*
Yaa Sheikh was speechless ya lura da Zahrah bata da ilimi na addini, everything and
anything babu, Ilimin addini zero, kula da miji zero, girki zero, shagwaɓa zero,
ƙirji zero that's too much to her.
Bai ƙara ce mata komai ya ɗauki hiraminsa ya naɗa as asual, kai tsaye downstairs ya
nufa bakinsa ɗauke da tasbihi gabaɗaya bai lura da Halisa dake durƙoshe a main
parlour ba, walking slowly cike da nutsuwa ya nufi part ɗinta, ganin ƙofar buɗe ya
sanya ya shiga bakinsa ɗauke da sallama cikin murya mai tsananin taushi.
Babu ita a bedroom ɗin, he was thinking ko tana bathroom tunda daman sallah bata
shigeta, daman kuma hakƙinsa zai sauke a matsayinsa na miji. Ya juya tare da buɗe
ƙofar da zata fitar da shi daga Main parlour ya nufi compound zuwa masjid. Tun a
yanayin tafiyar shi Halisa tasan shi ne kafin kuma ƙamshin turaren shi ya biyo
bayan, da ƙyar ta iya ɗago kanta tabi bayansa da kallo zuciyarta babu daɗi Banda
duhu babu abinda take gani cikin ƙwayar Idanunta, kuka ya yi mata hijira bata taɓa
sanin yinsa Rahma bane sai yanzu. Ta miƙe da ƙyar tana ambaton Allah tasan wayonta
bazai fitar da ita, daman kuma ance komai yayi zafi maganinsa Allah. Tana shiga
bedroom ɗinta taja ta rufe tare da murza key, bata iya wankan data saba duk Subhi
ba, alwala tayi ta sauya duguwar rigar Jikinta zuwa Jallabiya.
Bayan ta idar ta jima tana addu'ar samun kusanci da mijinta, duk wani abun sharri
mugun ji da mugun gani ya ɗauke idanun abin daga kansu, daga ƙarshe ta nemi
Ubangiji ya sassauta mata zafin kishin da take dashi akan Abbanta Yaa Sheikh.
Wani irin zafin Yaa Sheikh taji wanda bata san dalili ba, amma maganganun da Zahrah
ta faɗa ya tsaya mata suna ta kokawa da ƙarya da gaskiyar dake son gasgata batun
nata, tana nan zaune taji ana knocking ƙofar babu mai yin hakan sai shi, taƙi
motsawa can cikin taushin murya taji ya ce
"Zawja" tayi banza da shi su take ta barshi shi da Zahrah taga inda iya al'amarin
nasu zai tsaya, Yaa Sheikh dake tsaye hannunsa riƙe da Casbawa bai jima a Masjid
ɗin ba, domin hankalinsa na kan Halisa da abinda yake cikinta, tun a jiya ya
fahimci kamar ba daidai take ba, shi ya sa 6:00 daidai ya fito tare da dawowa zuwa
duba halin da gabaɗaya matayen nasa suke, Yaa Sheikh ya gyara tsaiwa idanunsa na
lumshewa ya ƙara lanƙwasa harshe ya ce
"Are you ok Zawja"
Still batai magana ba, hakan yasa ya kasa samun nutsuwa ya juya zuwa bedroom ɗin
nasa yana shiga ya ɗaga fararen idanunsa suna haɗa idanu da Zahrah ta fasa ihu da
sauri muryarsa na harɗewa ya ce "La'ilaha illallah Muhammadur Rasulullah s.a.w" Ya
riƙe kansa daga kallonta ya nufi gaban mirrow tare da ɗaukan key ya nufi waje tabi
bayansa da sauri suna sauka tayi part ɗinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login