Showing 147001 words to 150000 words out of 196133 words

Chapter 50 - IDAN BA KE by Nimcyluv sarauta

09 Jun 2026

109

Allah"
Tunda ta fara magana Halisa ke kuka ta ce
"Ya zan yi Dada? Ban taɓa ganin mahaifata ba, ban zauna tare da mahaifina ba ko sau
ɗaya ba, ban san ƴan-uwana ba, shi ya fara ɗorani a hanya har naji zan iya masa
komai ya gaji ya kai ni" ta saki kuka ta ce "kuma fa baya so na, wai Zahrah zai
aura ina laifin ya nemi auren wacce ban sani ba ya san na tsaneta ba, kuma ya yi
mini al'ƙawarin ba zai auri kowa ba.....,"
Dada ta katse ta da faɗin
"Tunda shi bashi da hankali kamar ki ko? Besty ni ya yiwa biyayya, ni na shaida
masa bana buƙatar zuwanki masarauta, sbd ban manta wahalar dana sha ba, na ce sai
naga yadda zamana ya kasance da sauyawar al'amarin zan bashi damar ya kawo ki,
umarni na ya bi, ni zaki tsana Danejo ba Abban naki ba, batun Zahrah kuma ke ki ka
bawa mijinki lasisin damar kula wata har ya aureta, ni na ji daɗin haka gobe wata
mai irin halinki ta kuma, Zahrah kuma daman son shi yake yana aurenta ki kaɗe har
ganye sai a fara lissafa miki aure tun yanzu"
"Dada don Allah zan zo wajan Mai martaba wallahi zuciyata babu daɗi" Dada dake kan
layi ta ce "Kin san Allah babu inda zaki zo, ko kinzo sai na saka Khalil ya dawo
dake ko El-bashir"
Ta haɗe rai ta ce "Ni ki daina haɗani da wani El-bashir" ran Dada ya sosu da halin
Halisa ta ce "Ɗan uwan naki ki ka tsana? Akan wanne dalili" tai shiru domin da
kunya ta ce akan Yaa Sheikh ta tsani El-bashir
"Zan zo kai lefen Besty ne zaki bayani" kafin tai magana ta kashe kiran
"Lefe?" Ta furta a fili kenan aure ya tabbata Yaa Sheikh ya kasa jure fushin zai
auri Zahrah mai yasa zai hukunta ta da hakan? Ta ce
"Na tsaneka, bana son ka" A can parlour bayan tafiyar Dr A'isha Abba Hakimi ya ce
"Koda wasa kada wani ya kuskura ya shaida mata ba saki bane, zuwa lokacin da za ta
gaji da kanta"
"Ya batun auren Zahrah gasky ne?" Ya ce
"Ba wanda zai iya tsayar da Malam, zuciyar shi ba irinta kowa bace, baya son Zahrah
amma ba zai iya bari ranta ya salwanta ba, kuma ta rantse idan bai aureta ba zata
iya kashe kanta, ya ɗauki kasadar zai yi Jahadi kuma zai riƙe Muhammad ya dawo
wajan shi, ya yi masa riƙo da zuciya ɗaya saɓanin yadda Engineer Aliyu ya riƙe shi,
zai ramawa kura anniyyarta"
"Amma ban ji daɗi ba, bai dace Yaa Sheikh ya auri wacce Engineer ya sani ba"
Murmushi kawai Abba Hakimi ya yi ya ce
"Me ya sa zaki haramta masa abin da Allah ya a halarta masa? Mata tunaninku da ban
yake" ya miƙe tare da ficewa.
Zahrah na kwance hannunta ɗaya manne da drip ɗayan kuma jini ke shiga a hankali, ta
rame tai baƙi ta fita daga cikin hayyacinta bakinta ya bushe ba kowa ake bari ya
shiga inda take ba,
Kallo ɗaya zakai mata ka zubar mata da hawayen tausayi, ko nono Muhammad baya samun
shi kullum cikin shan madara yake.
Dr ya gama duba ta ya juya yana fitowa Mimi ta ce "Dr ya ake ciki?" Ya sauke
numfashi ya ce
"Kuyi mata addu'a, zuwa lokacin da Allah ya nufa zata tashi idan mai tsayin rai ce"
Ta juya ta kalli Alhaji Farouk cikin kuka ta ce
"Alhaji kwanakin ka biyu da zuwa Kano, amma babu Yaa Sheikh ba alamar shi, don
Allah kayi wani abu kada Zahrah ta mutu akan Soyayya wacce irin Masifaffiyar
soyayya ce wannan? Wlh ko a film da labarai na littafai ban taɓa ji ba, Allah ka
dubi idanuna kada ka hukunta mini Zahrah da soyayya"
"Allah zai shiga lamarin In sha Allah" Mimi na ƙoƙarin magana suka ji ƙamshin
turaren Roja ya mamaye wlrd ɗin da suke zaune. Ta ɗago da sauri Idanunta ya sauka
akan Yaa Sheikh da Umar-khan sai wani kyakkyawan Bafullatani da kuma Surry.
Wai, dole Zahrah ta so Yaa Sheikh mutum bai nagarta da tsantsan addini da nutsuwa
da kamewa har haka
Sai bazan ƙamshi yake idanunsa cikin white Sunglass wanda ya ɓoye faɗawar na shi
Idanun,
Farar shadda ce a jikinsa sai ɗaukan idanu take babu Alkyabba dai hirami kafaɗa da
kan shi, alamun har ya yi wanka ya sauya kaya a hotel ɗin daya sauka.
Mimi da Alhaji Farouk suka miƙe, Alhaji Farouk ya miƙawa Yaa Sheikh sukai subawa a
hankali cikin nutsuwa ya ce
"Ya mai jiki?"
"Jiki sai addu'a Yaa Sheikh" Ya jinjina kai yana duba lokaci kafin ya ce "Allah ya
bada lafiya"
Umar-khan ya ce
"Za mu iya ganinta?"
Da sauri Alhaji Farouk ya ce "Eh, In sha Allah muje muje" gabaɗaya ya ruɗe sbd
nutsuwar Yaa Sheikh da kwarjinin da ya yi masa a idanu.
Jagora sukaiwa Yaa Sheikh har zuwa ƙofar shi kaɗai Dr ya bawa damar shiga. Tana
kwace amma sai da zuciyarta tai kyakkyawan bugawa sbd ƙamshin turaren shi wanda ba
zata taɓa mancewa da shi ba, ta rufe idanu hawaye na silalowa daga gefen idanunta,
sai yaushe zata daina mafarkin shi? Komai na shi gizau yake mata ta kasa jurewa ta
amsar ƙaddara. Yana tsaye kanta yana mmkin yadda ta faɗa ƙwarai duk ta lalace, a
kallo ɗayan da ya yi mata ya fahimci da gaske zuciyarta tai mugun kamowa da ciwo
wanda ba a son irin shi
"Ya jiki?" Maganar da tai silar faɗuwar Zahrah daga kan gadon ya yi saurin saka
hannu ya taro ta, ta juya sukai idanu biyu wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke
hawaye wani na korar wani, tayi saurin cire drip da jinin da ake ƙara mata, tare
da fisge na'urar Oxygen ɗin dake aiki a Jikinta, babu ƙwari a Jikinta amma haka ta
miƙe tana zuwa ta faɗa jikinsa ta rungume shi tana sakin wani irin kuka wanda yake
nuni da ka tausaya mini ka taimaki rayuwata.
Sanin cewa zuciyarta a yanzu matacciya ce, abu kaɗan za ai mata ta lalace yasa ya
ɗan daidaita ya shafa kanta kaɗan ba tare da ya ce
Komai ba, muryarta a hankali ta ce "Ka taimaki rayuwata ka aureni Malam, ka tausaya
mini zuciyata babu daɗi kamar zan mutu" wani irin kuka take gwanin tausayi ya
janyeta daga jikinsa tare da zaunar da ita saman gadon ta ce
"Saboda Allah, da soyayyar da ka kewa Annabi Muhammad s.a.w" ya kalleta da kyau
yana nazartar yanayin kafin ya ce.
"Na amince, zan aureki"
Ta saki murmushi while hawaye na zuba ta ce
"Na gode Allah ya saka da alheri Ubangiji ya ƙara girma" Ya jinjina kai sukai shiru
ta kalle shi ta ce "Nasan takura maka akai, ko tausaya mini kayi ba dan kana so na
ba ko?" Ya nuna mata pillow ya ce
"Huta, barci" ta ce
"Nayi barci har na gaji, yanzu bani da wani damuwa daman kai ne damuwata" sai yaji
tausayinta, sai yanzu ne yake gane cewa duk wanda yake hauka akan SO! To kawai a
rabu da shi, so babban abu ne da kan iya tarwatsa zuciyar mutum murus ya lalata
masa rayuwa ya ɗauke masa farin ciki yanzu ya shaida haka.
"Matarka? zata amince dani, na maka al'ƙawarin ba zan taɓa janta da faɗa ba ko tayi
zan haƙura domin tayi mini komai datai mini halarci har ta amince ka aureni, wlh
idan ni ce ita ba zan iya barinka ba, balle ka auri wata ina maka son da Ubangiji
kaɗai ya sani kuma shi ne zai zama shaida, kana da kima kwarjini tarin da haiba
wacce ba kowa zai iya Fuskantarka da wani shirme, nasan zaka zauna sani bisa takura
kayi haƙuri,kai mini adalci ba laifina bane"
Ya girgiza mata kai a taushashe cike da kulawa ya ce
"Ba takura, ki nutsu zamu zauna gida ɗaya tare"
tai murmushi tana ɗan riƙe ƙirjinta. Ya taimaka mata ta kwanta ta ce
"Kada ka tafi don Allah"
Ya jinjina kai yana tsaye kanta tana kallon shi tare riƙe hannunsa har barci ya
ɗauke ta.
Fita ya yi, zuwa office ɗin Dr. Dr ya ce "Ko iyayenta basu san tana ɗauke da Cancer
ba, wanda kuma munyi scanning yaci ƙarfinta abu ne mai wahala ta tsallake wata
biyar a raye a duniya" Yaa Sheikh ya ce "Subuhanallah!" Dr ya ce "Yana da kyau ta
ƙare watanni biyar ɗin nan da farin ciki, kada ita kanta tasan cewa akwai Cancer
Jikinta hakan zai ƙara taimakawa wajan murmurewar Jikinta"
"Ba wani aiki?" Dr ya ce
"For now babu, domin taje ƙarshe sai dai fatan samun sauƙi wajan Ubangiji" ya miƙe
yana godiya. Daga nan sukai sallama Yaa Sheikh ya nufi Rugar Bello a hanya ya kira
Abba Hakimi sukai magana mai ɗan tsayi kana ya kira Ummul daga nan ya ajjiye wayar.
Halisa na zaune tana azkar Idanunta ya kumbura sbd kwana tayi tana kuka sai dab da
Subhi barci ya ɗauke ta, kasancewar ta saba ta shi yin Sallah ya sa bata makara ba
Ta miƙe da ƙyar tana dafe kanta Idanunta na lumshewa sbd barci ga wani irin
matsanancin feelings dake damunta ta rasa yadda zatai da rayuwarta, harta mata
tsayin lokacin data ɗauka ba tare da Yaa Sheikh ba, she miss his torch, his kiss,
his body his everything daya shafe shi amma zafin ranta ya kasa bari ta yarda tai
kewar, tana ƙoƙarin kwanciya mother ta buɗe ƙofa ta shigo lokacin wasu masallatan
nata sallah ta ce "Barka da safiya Mother" bata amsa ba ta ce "Kije, ki haɗa mana
breakfast, ga wanke-wanken ma da mopping" a raunace ta ce "Ina maid ɗin? Bana jin
daɗi" ta ce "Allah ya sauwaƙa mai aiki kuma mun sallameta ke zaki koma yin komai"
Kamar zatai kuka ta ce
"Bari gari ya yi haske to"
"Yanzu na ce, kafin Abba Hakimi su tafi kai kuɗin Auren Zahrah" kamar an caka mata
wuƙa a zuciya haka taji hawaye ya sakko mata, mother tai waje. Ita kaɗai ta dinga
kuka babu mai rarrashi
wayarta ta ɗauka da niyyar yiwa Maimoon ko Dr A'isha magana a online sai taga anyi
mata magana da prvt number, kamar ba zata shiga ba sai kuma ta buɗe abin data gani
ya yi mugun tayar mata da hankali ta dafe cikinta da sauri wanda ya murɗa fitsari
ya taho mata, tai downloading picture ɗin Yaa Sheikh ta gani rungome da Zahrah a
ɗakin asibiti a ƙasa kuma aka ce. "Mun gode sosai Halisa da shirmanki ya bawa
ƙawata damar samun cikar burinta, yanzu Yaa Sheikh na Zahrah ne har abada ki fara
kokawar neman mijinki domin yanzu wutsiyyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, ke da Yaa
Sheikh har abada.....," Bata ƙarasa karantawa ba ta nemi ganinta ta rasa ta kuma
kasa fahimtar komai ta fasa wata ƙara tana faɗin..
[1/24, 7:40 AM] Abk: "Wallahi ƙarya ki ke, baki isa ki auri abin da na fiso a
duniya ba, dole ki rasa kamar yadda ki ka rasa" gabaɗaya Jikinta rawa yake har ya
gaza ɗaukan ƙafafuwanta ta sulale ƙasa tare da yin zaman ƴan bori.
Wani irin kuka take mai tarwatsa zuciya da sanya mutum cikin damuwa, duk wanda ya
ganta sai ya tausaya mata, hannunta na rawa ta ɗauki wayarta tare da kiran Dr
A'isha. Ringing ɗin farko aka ɗauki wayar tare da faɗin.
"Hello!"
Halisa ta ce "Adda A'isha na shiga uku, ba zan iya ba" Dr A'isha tai murmushi tana
kallon ɗaya wayar hannunta kafin ta fita daga inda take ciki, ta nemi bakin gado ta
zauna ta ce
"Shiga uku dame Halisa?" Cikin shassheƙar kuka murya bata fita sosai ta ce
"Da gaske Abbana aure zai yi wallahi, kuma Zahrah zai aura ba zan iya jurewa ba,
ina jin kamar zuciyata zatai bindiga" Dr A'isha ta kaɗa ƙafa ta ce
"Meye abin damuwa? You need a divorce paper, and you got it, I think you will be
happy". Halisa ta dafe ƙirji ta ce "I love my husband, ina son mijina kin san ban
tsane shi ba, ba kuma zan iya barin wata ta aure shi ba, yanzu ya zan?"
Dr A'isha ta runtse idanunta tana jin kamar wuta Halisa ta watsa mata a ƙirji da ta
ce _She loves her husband_ ta kasa cewa Halisa komai ta shiga dannar zuciyarta sbd
zafin da tayi..
"Na zama shasha, na rasa meke damuna" Dr A'isha ta ce "It's over, kin yi sake when
all is gone, yanzu sai da kibi hanyar da zaki hana Yaa Sheikh ya auri Zahrah, idan
ba haka ba kina kallo zai haɗa shimfiɗa da ita"
Ta sauke numfashi ta ce
"Kin san saki uku ya yi miki, ke da Yaa Sheikh har abada domin rama abin da ya yi
miki, shi ne hana shi auren Zahrah"
Halisa ta goge idanunta ta ce "Bana jin Abbana zai mini saki har uku, kuma anƙi
faɗa mini saki nawa ya yi mini"
"Kira ki tambaye shi mana?" Ta girgiza kamar Dr A'isha na gabanta.
Jin tayi shiru ya sa Dr A'isha ta ce "Ko ki je inda yake" sai a lokacin ta ce
"Ya yi tafiya"
"Zuwa ina? Yaushe zai dawo?" Cewar Dr A'isha.
A raunace wasu hawayen na biyu mata zuwa saman kuncinta ta ce
"Ban sani ba, bani da labarin yaushe zai dawo"
Dr A'isha tayi murmushi Idanunta akan mijinta wanda ya shigo daga masallaci kallo
ɗaya tayi masa ta ɗauke kai.
A hankali ta ce "Ask Abba Hakimi, you'll get the information Catch you later" tai
hanging up na kiran. Idanunta kan waya
Abubakar ya ce
"Sweetheart waya da Subhi yau babu ko azkar?" Ta yi masa kai ka ɗauka bada ita yake
ba.
Ya ƙara cewa "Dr na"
"Abubakar" ya buɗe baki da hanci yana kallonta ɗauke da mamakin yadda ta kira sunan
na shi babu ko risinawa ta ce "Dr kin san me ki ke cewa?" Ta ɗago idanunta fes akan
shi ta ce.
"Nasan kana da labarin ban taɓa yin hauka ba ko?" Ya jinjina mata kai ya ce "Elxty,
The way you called my name surprised me"
"To, Allahamdulillah tunda sunanka ne Abubakar ɗin" ya ce
"Meke damunki ne Dr?"
Idanunta ya sauya kala ta ce "Kai ne damuwata Abubakar, domin ka hana ni abin da
nake buƙata tsayin shekaru bayan a koda yaushe ina iya mutuwa,ko kafi so na mutum
ban bar masu yi mini addu'a ba? Burinka kenan nasan cewa kai ne baka haihuwa fa"
Da damuwa ya ce
"Ina tauhidinki ya tafi A'isha? Ni zan baki haihuwa?" Ta ce
"In a capital letters YES! ka duba Halisa matar malam, shekaru nawa na mata?
Gabaɗaya yaushe sukai aure amma yanzu cike ne da ita haihuwa take shirin yi, ni
kuma ina zaune a tutar babu"
Ya kai hannu zai riƙe ta domin wallahi gani yake kamar wacce Aljanu suka shafa ko
wacce kwakwalwarta ta taɓo
"Ras nake Abubakar, ina son faɗa maka cewa na gaji ne kawai I'm tired"
"Tired of what, Dr?"
A fusace cike da kallon wulaƙanci ta ce
"Your married, na gaji, na gaji, na gaji wallahi ka sake ni, naje na auri wanda
zuciyata ta rayu da son shi, daman aurenka is my destiny i know tun ba yau ba"
Ya dafe kai ya ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, ni ki ke faɗawa haka Dr? Kin san abin da
kalamanki zasu iya jefani? Kin san tasirunsu cikin zuciyata, kin san son da nake
miki,
Kada kiyi amfani da jarabtar da muka tsinci kanmu ki cutar da rayuwata, haihuwa da
rashinta daga Allah suke, ta yiwu yaran ba alheri bane a garemu shi ya sa Ubangiji
bai azurtamu da su ba, shi da kan shi yana cewa yana jin tsananin kunyar wanda bai
azurta su da haihuwa ba, ki riƙe ƙaddara ki kuma yarda da ita shi ne cikar
imaninki"
"Shut up your mouth Abubakar Tijjani Asase, ka haifeni ne? ko malami ka zama da
zaka zauna kana faɗa mini Allah ya ce Annabi ya ce, tunaninki ni daƙiƙiyya ce ko?
Lemme repeat myself I'm tired I need my divorce paper immediately!"
"Wallahi Allah, ba zan sake ki ba, sbd ina son ki IDAN BA KE ki ɗauka rayuwata ta
zo ƙarshe ne, ki sani matata ce ke igiyar aurena ke yawo akan ki, da alama baki son
rabauta da aljanna ki koma wajan ɗan uwanki Yaa Sheikh ya yi miki darasin dake
cikin aure A'isha"
Yana kawowa nan ya fice daga cikin bedroom ɗin zuciyar shi babu daɗi.
Halisa tunda suka gama waya da Dr A'isha take zube a ƙasa tana auna maganganunta,
Hawayen fuskarta yaƙi tsayawa.
Ta miƙe da ƙyar jiki a sanyaye ta nufi Main parlour sanye da hijabi
Kitchen ta nufa aikin data tarar dai da gabanta ya faɗi, ta ta shi akan wahala
aiki koma ba sabon abu bane wajanta, tun a rugar Rome.
Zata kunce nagge duk yawansu ta tafi kiwo, ta tatsi nono ta tafi talla ta dawo tayi
aikin gidan, amma ƴan watannin da tayi tare da Abbanta Yaa Sheikh Aliyu haydar
Aliyu
Ya sangarta ta, ya bata farin ciki, ya bata tarbiyya, ya kula da ita bata aikin
fari dana baƙi sai ɗaukan darasin zazzafar soyayyar shi
da karatun da yake mata,
ita kanta bata san ya take jin kanta ba, ta manta ita ce Halisa Danejo Rome. Ta
dawo amsa sunan Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu, yanzu kuma data dawo Princess shi
ne za a haɗata da aiki har haka wanda ta mance yadda ake yin shi.
Lallai aure rahama ne, cikar ƙimar mace gidan mijinta. "Mena aikatawa kai na ni
Danejo?"
Ta yi ta surutu ita ɗaya taci kuka ta ƙoshi she just missed, amma me?
Shi ne abin da bata sani ba, tana buƙatar Mentoring kanta a cushe yake. A hankali
ta fara wanke-wanken ta gama tas, kana ta gyara kitchen ɗin.
Kasancewar an gyara wanke ta saka a inji malkaɗe ta malkaɗa. Gefe guda ta kunna gas
ta ɗora ruwan kunnun shinkafa. Ruwa ta zuba cikin pot ɗin ta kawo kwakwa wacce ta
goga ta zuba cikin ruwan, kafin ruwan ya rafasa ta koma wajan kullin ƙosan ta haɗa
shi. Ta ɗora kasko ta zuba mai daidai yadda zai sha kan ƙosan, ta zuba albasa cikin
man ta barshi ya yi zafi sosai.
Daidai lokacin ruwan data zuba ya tafaso tare da kwakwa, ta kawo haɗin kullin
shinkafar tare da muciya a nutse take zubawa tana damawa har ya yi kauri yadda take
so. Ganin bata gama ba ya sanya ta rage gudun gas ɗin man data ɗora, tana gama haɗa
kunnun shinkafar ta juye a wani babban flas. Ta goge wajan daya ɓaci ta ajjiye flas
ɗin gefe.
Ta dawo kan man data ɗora, ta haɗa ƙosan wanda ya sha kayan ƙamshi da ƙwai da
tafarnuwa.
Is taking long kafin ta gama soya ƙosan, ta ɗauki paper ta saka ƙasan flas sbd
gudun gumi ya lalata shi,ta juye tas ta ƙara ɗaukan wata paper ɗin ta rufe saman
shi. Ta ajjiye gefe guda.
Ta ta fasa tea da ginger da tafarnuwa da sauran kyan ƙamshi da barkono kaɗan. Shi
ma ta juye cikin mug ta goge wajan tas, tana gamawa ta koma Main parlour ta share
tai mopping ta kunna boner ta saka turare mai ƙamshi sosai ta fesa air-con.
Nan da nan parlourn ya ɗauki ƙamshi, a lokacin gabaɗaya Jikinta ciwo yake da ƙyar
take buɗe ido ga damuwar zuciya, ga feelings ɗin dake damunta har tsoro abin ke
bata, nan da nan za ta jita a jiƙe. Ta shirya breakfast ɗin lokacin goma saura
minti biyar cif. Mother ta fito cikin wata green ɗin atamfa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login