Showing 6001 words to 9000 words out of 196133 words
tare da barin wajan
idanunta cike da hawayen baƙin ciki. Wata mata wacce ta fito cikin parlourn ta
kalli Zahrah ta ce "Why are you shouting?" Murmushi Zahrah tai ta ce "No Mimi ina
game ne, akai mini game over" Zama Mimi tai ta ce "Ok, kwana biyu na jin labarin
Deen a bakinki? Lafiya dai?" Zahrah ta ce "Baya nan ne Mimi" Mimi ta ce "Ai fa,
naga idan yazo sai ku kai awa uku zuwa huɗu a part ɗinki kwana biyu shiru" Murmushi
kawai Zahrah a haka Binta ta kawo mata haɗin salad ɗin. Mimi tabi Zahrah da kallo
kafin ta ce "Wai lafiyarki ƙalou kuwa? Kullum cikin cin haɗin Salad kike?" "Lafiya
Mimi, kawai zuwa makarantar nan ke sani gajiya da kwaɗayi naji bana son cin komai"
Mimi ta jinjina kai ta ce "Lallai, ni banga me zaki da kuɗi ba da kuka zaɓi
lecturing Zahrah" ba tare da data amsa ta ba ta ce "Mimi ina Daddy ne?" Mimi ta
ɗauki waya ta ce "Jiya ya dawo, but yaje kano wajan wani babban abokinsa" "Ok"
cewar Zahrah a nutse Mimi ta kalli Zahrah cikin damuwa sosai ta ce "Fatima-Zahrah
yaushe kike tunanin yin aure ne, boko kin gama ta, completely sai abin da yai
saura, familyna sun fara mini surutu akan wai na zuba miki idanu, wasu har cewa
suke maybe yawonki kawai ki ke, ni dai nasan ba haka bane i trust you babyna"
marairaicewa Zahrah tai kamar ƴar 20 nan kuwa shekaru 31 take da shi. "Mimi kin san
familyn nan naki basu san darajar karatun boko ba, ta ya ya zan haɗa karatu da
aure? Kana yin auren kuma ace ka haihu, kuma ba zan iya haɗa aikina da aure ba gsky
Mimi a barni zuwa 35 na gama komai sai na fara tunanin auren, su kansu mazan ai mai
ilimin boko suke buƙata ba kuwa ya damu da ilimin addinin nan ba, suna buƙatar mace
wayayyiya a very educated women" murmushi Mimi tai cike da gamsuwa da maganar ƴarta
kafin ta ce "Na fahimta, ko Dadynki sai dana kammala University mukai aure muna dai
soyayyya a waje, dake kuma na wuri na shiga shcl shi ya sa na gama before we
getting married" jinjina kai kawai Zahrah tai hankalinta akan salad ɗin da take ci
sbd yadda cikin jikinta ya sanya mata kwaɗayi kala-kala. Da sauri Mimi ta ce
"Subuhanallahi, maza kunna mini Plasma ɗin nan ki jonata da DS.TV tafsirin Sheikh
sai shigeni" kwaɓe fuska tai kafin ta ce "Mimi wai kin damu da wani Sheikh, ni
wallahi ban son tafsirin ɗin ko kaɗan, ga wata ƙinƙina da yake, da ƙyar fa yake iya
karatun sbd ƙinƙina wani time ɗin har hawaye yake to me za'a gane?..." Da idanu
Mimi tabi Zahrah tana mamakin jikar ƙirjinta a kullum "To ai kuwa da yadda, ƙinƙina
kuma ai larura ce kuma a hakan Ubangiji ya ba shi bawai Zahrah".
Gudu take sosai hankali a tashe sai haki take ita kam sam ba zata iya irin wannan
wasan na sai da rai ba, wacce ƙaddara ce take shirin bibiyarta ne? Tsayawa tai tana
mai da numfashi, sai a lokacin idanunta ya sauka akan wasu fararen Kurciyo masu
kyau da tsari ita a rayuwa tana son ko wacce kalar dabba ta daɗe tsaye tana
kallonsu, ɗaya daga cikin kurciyoyin ya tsora mata idanu. Tunawa da tai ana gab da
fara wasan macijn ya sanya ta ƙara saurayi domin samun wajan ɓoya. Girgiza
kurciyoyin sukai wata iska da guguwa ta mamaye ilahirin wajan iskar data kasance
mai daɗi sosai wacce ta haddasawa Halisa Dajeno rufe idanunta wani barci na
fisgarta a hankali ta sulale a wajan babu jimawa barci mai nauyi ya ɗauketa.
Kurciyoyin suka rikiɗe zuwa wasu samari masu zubin halitta ɗaya daga ciki wanda
yake sanye da farar Alkyabba mai taushi wacce ta sauka har ƙasa ta rufe masa
ƙafafuwansa yaja numfashi a hankali cikin ƙasa da murya ya ce "Danejona ba zata iya
wasan nan ba" ɗayan dage gefensa ya ce "Haba Prince me ya sa kake da taurin kai ne?
Sarki yace ka yanke duk wata alaƙa tsakaninka da bil-adam musamman wannan yarinyar
Danejo amma kaƙi" murmushi mai taushi Wanda aka kira da Prince yai yana sake kallon
Halisa Dajeno ya ce "A wannan karan ba zan iya yiwa Sarki biyayya ba, babu haɗi
tsakanin mutum da aljani, amma kasan ba zan iya zutar da wani rai ba, muddin idan
ba Danejo zai cutar ba? Na jima a jikin mahaifiyar Danejo tun tana da cikinta, amma
rana ɗaya akai mata magani suka rabani da ita, wanda ya sanya na kwanta jinya,
wannan dalilin yasa na koma kan ɗiyarta Danejo na shirya duk wani abu da sarki zai
faɗa, ƙarshe dai ya ce zai koreni daga duniyar Aljanu ba?" Ɗayan zai magana Prince
ya daka mishi tsawa ya ce "Ka saurara mini Safwan" ya faɗa idanunsa na juyewa zuwa
kalar na aljanu a tsorace Safwan ya ce "Afuwa nake Yariman Aljanu, yanzu me ka
shirya akan raba Danejo da wasan macijin nan?" Gyara Tsaiwa Prince yai tare da
durƙosawa daidai inda Danejo take kwance tana barci ya ɗauke ta cikin nutsuwa ya ce
"Ubangiji nake nema ya bani Sa'a, ina son Matata bana jin zan jure ganinta da duk
wani wanda zai cuceta, balle kuma ya taɓa mini ɗana dake cikinta" buɗe baki Safwan
yai da Mmki yace "Prince yaushe ta zama matarka? Har kuka samu ɗa?" Murmushi Prince
yai yana shafa cikin halinsa wanda yake jin farin ciki na ratsa masa zuciyarsa
kafin ya ce "Matata ce ita ɗin, duk wanda ya shirya rabani da ita to ya shirya
zuwansa lahira, bani da lokacin magana Safwan, maza ku ɓace daga wajan nan" kamar
gilmawar walƙiya haka suka ɓace, nan da nan Prince ya rikiɗe zuwa Almajiri mai
yagaggun kaya. A nutse ya fara tafiya da ita zuwa cikin Rugar Rome dai da yaje
daidai bakin bukkar su Danejo ya ajjiyeta da sauri ya bar wajan, sbd gaba ɗaya
jama'ar Rugar suna filin da za'a gabatar da wasan Maciji. Prince ya ce "Ubangiji ka
bani Sa'a da nasara" yana faɗin hakan yai Girgiza nan take ya zama ƙaton wani baƙin
maciji mai narkeken kai a hankali ya sulale ya fara tafiya tsakanin bukkokin Rugar
Rome har ya Ƙarasa wata bukka kai tsaye ya kutsa kansa ciki, kwance ya samu wani
maciji shima baƙine sosai, da alama shi ne macijin da Matarsa Danejo zatai wasa
dashi. Kallon kallo aka fara tsakanin Maciji Prince da kuma Macijin da Danejo zatai
wasa dashi. Kamar haɗin baki haka suka fasa kai a tare lokaci guda kuma suka nufi
kan juna.
Bala'i kada a manta labarin ya faru a gaske babu ragi babu ƙari👌🏾. Muje zuwa
#Sarautar marubuta
#True life story
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
Nimcyluv sarauta
_*Arewabooks@Nimcyluv*_
4.
A kusan tare macizan guda biyu suka ƙara fasa kai tare da kaiwa juna sara, ko wanne
maciji ƙoƙarin jiwa ɗan uwansa ciwo yake da ganin ya kashesa har lahira. Gaba ɗaya
macizan suka sarƙafe juna tare da nan na ɗewa waje guda ko wane huci yake yana
fitar da hayaƙi ta baki nisan yadda Prince wanda ya a rikiɗe zuwa maciji ya matse
macijin da Za'ai wasa dashi, gaba ɗaya ya ji masa rauni a hankali kuma Prince ya
buɗe bakinsa ya fara haɗiye Macijin zuwa cikinsa sai daya haɗiyesa tsaf kafin ya
sulale gefe guda ya kwanta yana mai da numfashi Wahala, sai fasa kai yake kamar
zaici babu zuciyarsa tayo sama baki ɗaya zai iya sarar ko waye a wannan lokacin.
Sarkin ruga ya kalli tarin jama'ar da suke wajan hadda Shatu da Hamma Yabi, da
sauran mutanan rugar kafin ya numfasa ya ce "Lokaci ya yi ake a kawo mana Halisa
Dajeno Rome cikin fili, domin su fafata da maziji yau ranar tace" Wani mai suna
Giɗaɗo ya rusuna tare da faɗin "Yanzu za'a kawota" yana faɗin hakan ya kalli Hamma
Yabi tare da faɗin "Maza jeka kawo ɗiyar taku, tana ɓata mana lokaci" Hamma Yabi ya
ce "Yanzu za'a kawota" yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi bukkarsu tun daga
nesa ya hangeta kwance a bakin bukkar inda Prince ya kwantar da ita tana barci.
Cikin sassarfa ya ƙara yana faɗin "Assha Subuhanallahi barci a ƙasa Danejo" ya faɗa
yana ɗagota tare da jijjigata sosai, da sauri ya buɗe idanunta tana zabura "Hamma
Yabi yaushe na dawo nan?" Kallonta yai ya ce "Kina nufin baki san lokacin da kika
kwanta a nan ba?" Girgiza kai tai ta ce "Aradun Allah ban shina ba, kawai naji iska
mai daɗi ta lulluɓeni wani barci yazo mini daga nan ban san komai ba" Girgiza kai
yai yana kama Hannunta ya ce "Danejo ƙurushiya, maza muje sarkin ruga na jiranmu"
dafe ƙirji tai cike da tsoro ta ce "Na shiga uku na lalashe, Kur'ani na manta yanzu
hamma yabi shikenan mutuwa zan, zan mutu na bar Dada? Zan mutu banyi karatu na zama
babbar mace ba? Don Allah kada na mutu yanzu bana son wasan nan" rirriƙeta Hamma
Yabi yai sosai ya ce "Ma zaki mutu ba Danejo, sai na kai ki burni Kinyi karatu kin
zama babbar mace abar ƙwatance, sai kin zama mace ta farko wacce zata kawo sauyi
cikin Rugar Rome, ki daina kuka kinji" kai ta ɗaga masa kafin da sauri ta ce "Kuma
zan zama wannan mutumin na jikin bango?" Zare idanu Yabi yai kafin ya ce "Wannan
gwamna ne fa" murɗa baki tai cikin shagwaɓa ta ce "Ni dai irinsa nake son zama"
Yabi ya dungure mata kai ya ce "Aradu ƙarya kike, ina zaki iya yin siyasa tayaya
zaki zama gwamna daman mata na zama gwamna ne?" Banza tai masa bai ƙara ce mata
komai ba ya jata zuwa filin da za'a gabatar da wasan.
Giɗaɗo dake tsaye shi da Sarkin ruga suna jiran zuwan Hamma Yabi da Danejo ya ce
"Me ya sa ka zaɓi Danejo kasan ba zata iya wasan ba" murmushi Sarkin ruga yai kafin
ya ce "Ina son ganin bayanta ne, kuma a hankali zan ƙarar da zuri'ar Manga a cikin
Rugar nan, wannan macijin na tsafi ne hatta mutuwar Manga ni na shiryarta"... "Amma
me Manga yai maka haka?" Cewar Giɗaɗo. Sarkin ruga ya ce "Sirri ne.." kaifin su
ƙara magana Hamma Yabi ya ƙaraso hannunsa riƙe da Danejo wacce ta ƙanƙamesa sosai
jikinta na rawa da ɓari.
Alƙalin wasan ya ce "Yawwa yanzu zamu fara, Danejo ta shigo cikin fili jama'a ku
buɗe idanunku da kyau yau za kuga wasa wanda baku taɓa ganin irinsa ba" Halisa
Dajeno Rome na tsakiyar fili ko kuka ta kasa a wannan lokacin ta tsaya ne kawai
tana jiran taga ta inda mutuwa zata zo mata, domin abune mai wahalar gaske ace yau
ta rayu ko ta tsira da ranta. Sarkin ruga ya bada umarnin a fito da Macijin, da
sauri Alƙalin wasan ya nufi bukkar da macijin yake. Yana kwance sharkaf yau lamo a
ƙasa tare da yin gammo da jikinsa, wani irin zabura yai tare da fasa kansa a
lokacin da alƙalin wasa ya shigo cikin bukkar, ƙuri yai masa da idanu yana ƙare
masa kallo. Ko me ya tuna Ohhu a hankali ya fara sauka daga dokin zuciyar ya koma
ya kwanta, shi kansa Alƙalin wasan ya tsorata jikinsa na rawa yasa hannu ya ɗauki
Macijin da ƙyar sbd nauyin da yake da shi.
Tun da Halisa Danejo Rome ta saka idanunta akan macijin taji gabanta ya faɗi,
jikinta ya ɗauki rawa hawaye suka fara sintiri a saman Fuskarta, bata taɓa ganin
maciji mai girman wannan ba, tama rasa wacce kalar addu'a zatai duk da ba wani abu
ta iya sosai ba. Alƙalin wasan ya ajjiye macijin nesa da Halisa, aka fara kallon
kallo tsakanin Danejo da Macijin, an shafe tsayin wasu daƙiƙo aka rasa waye zai
fara kaiwa wani hari tsakanin Danejo da Maciji Prince?. Zaro idanu tai waje ganin
ya fara warware tare da yin tsayi sululuuuu kuma ya nufo inda take, tana ja baya
yana biyota har ya ƙaraso dab da ƙafarta tare da tsorawa zoben hannunta idanu. Juya
tai tana neman inda zata gudu can idanunta ya sauka akan wani ƙaton dutse. Da sauri
ta ɗauka tare da riƙewa a hannunta, ganin haka yasa Macijin bin ƙafafuwanta suuu
haka ya dinga sufa a jikinta, har ya naɗeta ciff kansa daidai Fuskarta yana tsora
mata idanu tare da kallon cikin idanunta.
Jirkinta na ɓari ta ɗaga dutsen tare da kwaɗa masa a tsakiyar kansa, wani kalar
ihun azaba macijin yai yana fasa kai kamar zai sarata, sai kuma ya saki kansa tare
da ɗorasa saman ƙirjinsa gaba ɗaya naman Macijin rawar azaba yake, kansa tuni ya
fashe ya fara zubar da jini. Ganin nasarar da Halisa Danejo Rome ta fara samu yasa
Hamma Yabi da Shatu tare da sauran jama'ar Rugar Rome suka fasa ihun murna, Sarkin
ruga da Alƙalin wasan hankali tashe suka kalli juna tare da faɗin "Me ya samu
macijin nan? Ki dai asiri akaiwa Yarinyar nan?".
Halisa a tsorace Macijin a tsorace amma a haka cikin dakiyar zuciya ta ƙara ɗaga
dutsen a karo na biyu ta ƙara bugawa Maciji, Innalillahi a wannan lokaci kururuwar
da Macijin yai sai da kowa na wajan yaji, jini ya sake ɓalle masa a hankali ya
sulale ƙasa baya ko motsi alamar ya mutu... ajjiyar zuciya ta sauke haka kurum taji
kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tai a wajan ta shiga rera kuka tausayin macijin ya
kamata musamman yadda taga jini na zuba a jikinsa, Hamma Yabi ya ƙaraso wajan
Halisa Dajeno Rome tare da ɗagata yana dariya ya ce "Danejon Dada kin kashe
macijin, kin kashe sa bana faɗa miki cewa ba zaki mutu ba? Zamu samu ƙwayar nono da
Nagge masu yawa" ƙanƙame Hamma Yabi tai cikin kuka ta ce "Bana so Hamma Yabi, mu
bar nan wajan kaina juyawa yake, bana son ganin jinin nan kaji" hannunta ya kama
sukai gefe guda. Cike da taƙaici Sarkin ruga yake bin Macijin da kallo bai taɓa
tunanin haka ce zata kasance ba, cike da baƙin ciki ya amshi wani sanda ya shiga
kwarɗawa macijin aka tun macijin na motsi har ya daina jikinsa yai face face da
jini tare da raunuka. "Ka ɗauke sa ku cillar a gefen gaɓar ruwa wani abin yai
kalace dashi" Giɗaɗo da Alƙalin wasan suka ɗauki Macijin tare da nufar cikin jeji
da shi. Suna zuwa suka cillar gefe guda da sauri suka juya cikin Rugar Rome.
Sanyin gaɓar ruwan daya ratsa cikinsa ya sanya ya fara Girgiza yana juyi tare da
murmurɗe jinsa gefe guda, wani kalar ihu yake mai nuni da azabar da yake ciki, ya
daɗe cikin wannan halin kafin yai Girgiza tare da rikiɗewa ya dawo siffarsa yadda
yake fitowa a mutum ba Aljani ba, yana kwance sambal gefen ruwan Farar Alkyabbar
jikinsa duk ta ɓaci da jini. A hankali ya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa inda
yake zubar da jini, runste idanun yai sosai cikin ƙasa da murya ya ce "Ya Allah"
yana nan ƙwance yaji iska ta mamayesa baki ɗaya kafin kace wani abu iskar ta
ɗaukesa zuwa sama.
Duk farin cikin dasu Shatu suke ciki banda Danejo rasa abin da yake mata daɗi tai,
gashi jinin Dada ya matsa ga tunanin dake wanzuwa a cikin zuciyarta. Dada ta kalli
Shatu ta ce "Farin ciki za kiyi Halisa ba damuwa ba, da tuni an rabani dake Allah
bai ba, akwai ƙaddarorin da suke biye dake, amma duk wahala duk tsanani waya rana
zaki zama abar ƙwatance tabbas zaki samu miji wanda zai kula da maraicinki" Danejo
ta ce "Dadana nifa ba marainiyya bace, ina dake ga Hamma Yabi ga kuma Shatu"
jinjina kai Dada tai idanunta akan zoben hannunsa Halisa ta ce "Ina kika samu
wannan Halisa?" Girgiza kai tai cikin damuwa ta ce "Ban sani ba Dada, kawai na
gansa a hannuna"... "Bana son ƙarya fa" da sauri Halisa ta ce "Da gaske nake miki,
kalli kiga" ta faɗa tana nuna mata tambarin zoben, Dada ji tayi kansa ya sara
idanunta akan Zoben da sauri ta riƙe kanta tare da rufe idanunta, kamar mai son
tuna wani abu babu abin da take gani a cikin idanunta sai tambarin masarauta dake
manne cikin zoben. Ganin yadda Dada ta rirriƙeta kanta ya sa Hamma Yabi fita da
gudu ta tatso mata kindirmo mai zafi, da taimakon Halisa Dajeno Rome suka bawa Dada
kindirmon nan da nan zufa ga shiga saukar mata bacci ya ɗauke ta.
Juyawa Halisa tai ta kalli Shatu dake barci a nutse ta kalli Hamma Yabi ta ce
"Hamma yaushe Dada zata samu lafiya ne? Kullum a ƙwance take ina tsoran na rasa ta
aradu" Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya ce "Ba zaki rasa Dada ba, gobe zan koma
asiti bamu da kuɗin kai ta asibitin burni" Da sauri Danejon ta ce "A siyar da Nagge
to" zare ido Hamma Yabi yai ya ce "Aradu ƙarya ne, Uban waye zai taɓa Nagge ai mu
dasu mutu karaba" ba tace masa komai ta miƙe tsaye tare da yin waje lokacin rana ta
faɗi, can gefe ta nema ta zauna ita ɗaya sai tunani take a haka har akai magariba
tana zaune, ganin duhu ya fara yasa ta miƙe tare da zagayawa bayan bukka ta kwaɓe
kayan jikinta, halittar jikinta ta tsorawa idanu, musamman ƙirjinta tana mamakin
abun mene amfaninsu a jikinta? Ita a gareta basu da wani abu kullum sai dai su ƙara
girma. Ruwa ta sheƙa babu ko sabulu tana gamawa tai alwala, wasu kayan fulanin ta
ɗauka farare ta saka tare da Ajjiye waɗan can, da sauri tai sallah tana gamawa taci
tsiran da Hamma Yabi ya kawo musu, tana ci ta kwanta barci domin da wuri take son
zuwa kiwo ta dawo ta tafi tallan kindirmo.
Ciki zafin nama Prince ya saka hannu tare da ɗauke Safwan da mari ya ce "Ka fita a
sabgata, kaje ka faɗawa Sarki halin da nake ciki ya ɗaukeni, kuma kasan yana gab da
rabani da matata wanda ba zan iya jure hakan ba sam" Safwan ya kalli Prince cike da
mamaki ya ce "Ban taɓa ganin mai taurin kai a duniyar Aljanu irinka ba Prince,
cutar da yarinyar nan kake fa, babu haɗi tsakanin mutum da Aljani na faɗa maka,
abin kunyane ka rasa wacce zaka so sai Bil adam? Allah zai saka mata fa" banza
Prince yai da Safwan a wannan lokacin rabinsa na mutum rabi kuma na siffar Aljani
da sauri ya juya zai tashi sama Safwan ya ce "Ina zaka? Ba dai wajanta ba?" Prince
ya ce "Ba zan iya yin wasu daƙiƙo ba, ba tare da naga matata ba, da matata nake son
kwana a yau ɗin nan" yana faɗin haka ya ɓace ɓat kai tsaye Rugar Rome ya nufa.
Halisa juya cikin barci taji wani sanyi na ratsa mata jiki, ga wani mafarki da ke
ƙafafuwanta sai motsawa suke amma ta kasa koda motsi bada ji take kamar ana
danneta. Can dai ta farka a firgice Innalillahi a ruɗe ta fara kallon inda take,
tana kwance tsakiyar dokar daji ba gida gaba ba gida baya...
Waye ya kawo Halisa Dajeno Rome cikin dokar daji?...
#Sarautar marubuta
#true life story
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
https://wa.me/+2348119237616
5..
A zabure ta miƙe tsaye tana ƙarewa cikin dokar dajin kallo, babu abin da ya bata
mamaki irin yadda