Showing 54001 words to 57000 words out of 196133 words

Chapter 19 - IDAN BA KE by Nimcyluv sarauta

09 Jun 2026

115

bakin.....

08119237616
Paid book
Not edited
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Shiru" ya ce yana sakin bakin tare da mai da Idanunsa kan
glass cup ɗin da ya tsiyaya tea aciki. Ta tura baki gaba ba tace komai ba duk da
irin ƙaiƙayin da bakin yake mata, haka nan taji kamar ana mintsininta akan Halisa
yi magana cikin sauri ta ce.
"Nima ina jin yunwa na sha shayin naka?" Cak ya ajjiye tea ɗin daga hannunsa yana
ɗaukan tissue tare da goge bakinsa, ta ɗauki shayin daya rage zata kai bakinta ta
ji ance "A'a" ta ajjiye cup tana miƙewa tare da bin bayansa, sahun tafiya da yaji a
bayansa yasa ya tsaya, tayi saurin dawowa gabansa suna haɗa ido ya ware mata manyan
idanunsa masu kaifi ta tura baki ta ce "Na sake magana banga ka riƙe bakin ba ai"
Yaa Sheikh ya girgiza kai kawai tare da shigewa bedroom ɗinsa yana ɓoye yanayin
fuskar shi. Ta kalli inda ya shiga sai kuma ta juya tana kwashe tray ɗin. A main
parlour ta samu Zahrah zaune tana breakfast ga wata maid nayi mata tausa a ƙafa.
"Ke zonan" cewar Zahrah Halisa ta dawo ta zauna tana ɗauke kai gefe guda, saboda
har yanzu bata mance mari da zagin da Zahran tai mata ba, Zahrah ta ajjiye spoon
ɗin hannunta wanda take shan tea da shi ta ce.
"Kai breakfast ɗin sai yanzu? Ko bai ta shi bane" Halisa ta kalle ta sai kuma ta
ɗauke kai tana faɗin. "Shi ya ce na tsaya" Zahrah ta ce "Shi Yaa Sheikh ɗin?" Tai
shiru ba tare da ta ce komai, tasan indai zatai magana to zata saki layi ne, Maid
ɗin ta kalli Halisa da sauri, ai ko ita da tayi shekara da shekaru tana aiki a
gidan Yaa Sheikh magana bata taɓa haɗa su ba, infact ko parlourn shi bata san ya
yake ba, Ummul ce kawai take kai masa breakfast ita ma iya dining room, sai ya gama
yabar wajan take zuwa ta kwashe, idan kuma yini gida zai yi a ranar basa taɓa zuwa
part ɗin, Umar-khan ne ke kai masa dinner, bai fiya cin lunch ba sai dinner,
anytime yana tare da butar shayi kamar buzu. Mamaki ya cika Maid ɗin jin abin da
Halisa ta faɗa wai shi ya ce ta jira? Who is she to him?.... "Whatever, Ke yama
kika ce sunanki?" Maid ɗin ta ce "Bara'at" Zahrah ta ce "Ok, duk wani aiki na part
ɗin nan, zuwa part ɗin Yaa Sheikh ya dawo hannun wannan yarinyar, idan kun kammala
abinci na Yaa Sheikh ita zata dinga kai masa, bana son na dinga ganin wani abu na
ba daidai ba, bana son surutu da hayaniya yana saka mini ciwon kai, ko a gidan
ubana ban taɓa sanin hanyar kitchen ba, to a nan ba zan fara saninsa ba, kuna gama
girki ki bata ta kawo mini nawa" daga Halisa har Bara'at kallon Zahrah suke, suna
mamakin ƙarfin ikon nata, duk da cewa Bara'at bata san matsayin Zahrah ba, amma
tasan dole da akwai abin da ta taka a gidan... Zahrah ta kaɗa ƙafa tana faɗin "Ku
ɗauke idanunku daga kan mijina, daga nesa kuka ganshi ku sauya hanya, duk abin da
kuke nema ni zaku faɗawa, koda abin cin gidan ne ya ƙare" Bara'at ta ce "Ok, amma
kula da abincin gidan yana wajan Ummul" It's your problem, I just finished planning
what I want" ta juya kan Halisa tana faɗin.. "Jeki breakfast ki saman a bedroom"
tana faɗin hakan ta shige part ɗinta, Halisa ta bita da kallo a zuciyarta tana
mmkin halin Zahrah. Miƙewa Bara'at tayi Halisa ma haka, tabi bayanta har zuwa
sashen kitchen, ma'aikata ta gani mata da yawa ko wanne da abin da suke a kitchen
ɗin. Da sauri Bara'at ta nufi wajan Ummul tana ce wa "Yau naga abin mamaki Ummul"
kyakkyawar matashiyar matar wacce zata iya shekaru 50 zuwa sama ta kalli Bara'at ta
ce. "Da akai me Ukkuti Bara'at?" Bara'at ta sauke numfashi ta ce "Wata mata na
gani, mai iko da isa, wallahi na tsorata da yanayinta" Ummul tai murmushi tana
ajjiye abin hannunta ta ce "Faɗimatul-zahrah bin Umar Farouk, matar Yaa Sheikh" a
tare duk suka ce "Matar Yaa Sheikh?" Ummul ta kallesu ta ce "Na manta ban shaida
muku bane, sai a haƙuri da juna ko?" Idanunta ya sauka akan Halisa wacce take dube
dube duk abin da suke faɗa tana ji amma hirar bata gabanta, Ummul ta girgiza kai
kawai, tana mai jin wani abu a ranta, yarinyar tana nan dai babu sauyi a tare da
ita kamar yadda yake nuna mata ita a waya. Hawaye ya sakkowa Ummul ko yanzu ta mutu
ta yi farin ciki, Aliyu ya samu gefen rayuwar shi kamar yadda yake faɗa mata a koda
yaushe.
Bara'at ta ce "Ummul wace ita kuma wannan?" Ummul ta ce "Masu gidan ce" "Masu gidan
kuma?" Cewar Suhaima Ummul ta ce "Ina nufin mai aikin Zahrah ce" ta kalli Halisa da
kyau tana mai sakin murmushi ta ce "Sunanta Halisa, ƴar uwar Zahrah ce an bawa Yaa
Sheikh riƙon ta amana ne, zatai amfani da sunan Halisa bin Sheikh Aliyu haydar
Aliyu" Halisa ta ƙarasu wajan Ummul da sauri fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi
ta kama hannun Ummul ta ce "Laa kema kin sanni ashe, kuma kin san anyi...." Ummul
tayi saurin rufe bakin nata tana cewa "Ba'a yin surutu a ɗakin girki, Bara'at akwai
tray tana shirya breakfast ki bawa halisa" Bara'at ta ɗakko tray ta bawa Halisa ita
kuma ta ce a kitchen ɗin zata zauna ta ci.
Bayan ta gama cin abincin Ummul ta miƙa mata farar madara mai ɗauke da zuma a ciki,
batai musu ba ta amsa "Nima ina son na iya girki sosai, ina son yi wa Yaa Sheikh
girki mai daɗi" Ummul tayi kamar bata ji zancen na Halisa ba, taci gaba dayin aikin
gabanta tana son a akai gidan ciyarwa Yaa Sheikh abincin akan lokaci.
Zahrah na tsaye a gaban mirrow anci uwar kwalliya sai ƙarinin mai take, wayarta
dake ringing ta ɗauka ganin sunan Deen ta ce "Uhm maye daman nasan babu mai kirana
sai kai" daga cikin wayar ya ce "Ba wannan zaki tambaya ba, fara duba number" da
sauri Zahrah ta duba number da mmkin take kallon number ta Saudiya ce,what does
that means? Ya katse mata tunani da faɗin "Ki daina mamaki na riga ki sauka a
Madina, ke kawai nake jira, don't make any mistakes nazo da maganin da ki ke
buƙata, ina son ganinki" The surprise of his behavior prevented Zahrah from
speaking. "Wallahi ki san yadda akai ki ka zo, ko ki ganni a gidanki" yana faɗin
haka ya kashe wayar babu jimawa ya tura mata address ɗin inda yake, Zahrah ta dafa
kai da sauri kuma ta juyawa zuwa ɗaya bedroom ɗin nata a nan ta samu Halisa tana
shirya mata kaya a wardrobe, zama tayi ta ce "Ke kin fara menstrual?" Halisa ta
ɗauka gyaran kayan take nufi kai tsaye ta ɗaga mata kai alamar eh. Juyawa tayi ta
nufi part ɗin Yaa Sheikh.
Fitowar shi kenan daga Library room ɗinsa, ya zauna sanye da wata tattausar
Jallabiya a jikinsa hannunsa cikin sumar kansa, cikin nutsuwa ya gyara zama akan
duguwar kujerar da yake kai hannunsa riƙe da Cup yana shan green tea wanda Ummul ta
kawo masa da kanta, speaking calmly ya ce da Khalil.
"Uhm surutu dai" Ta cikin waya Khalil ya saki dariya ya ce "Ya muke da matarka?
Allah ya nuna mini ranar da zata barbabaɗa tana ɗauke da cikin Yaa Sheikh, koda
yake kace baka son ta ai, auren dole akai maka" Yaa Sheikh yaja idanu ya rufe yana
jinsa fresh sbd barcin da ya yi, cikin son dakatar da Khalil ya ce.
"Wallahi ba auren dole bane, ni na zaɓi matata It was completely my plan..." Katse
wayar ya yi jin yana faɗin abin da mai shirya ba, tare da rufe kansa. Tsaye ya
ganta a kansa babu sallama ya ɗauke kai kawai yana ci-gaba da danna waya tare da
duba abubuwan da Umar-khan ya tura masa.
Ta zauna kusa da shi tana cewa "My Excellency baka fito ba har yanzu hope lafiya?"
Kai kawai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba, ta haɗe jikinta da nashi tana
cewa "Daman nace ina neman permission zamu shopping da ƴar fillo" har lokacin
idanunsa yana kan waya bai ce komai ba. Ta shafi fuskar shi tare da cewa "Ba
jimawa za mu yi ba kaji My Excellency" Jotter ya ɗauka da pen ya yi rubutu kana ya
ajjiye mata a gefenta haka kurum yaji harshensa ya harɗe baya jin yin maganar.
Ganin ƙoƙarin rungome shi take son yi ya ɗan miƙe tsaye, yasan cewa hakƙinta take
nema, kuma yasan girma da ƙarfin hakƙi amma ya zai? He's not interested at all,
baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin.
Tabi bayan shi da kallo, tana ji a ranta dole ne ma tayi gaggawar aiwatar da burin
dake ranta, Yaa Sheikh ya dawo hannunta sai yadda tai da shi tayi imani da Allah
idan ya zo hannunta shi da wata ƴar mace kuma har abada, ba zai iya kallon kowa a
matsayin mace ba dole sai ita, What is the solution? where will she start and what
will she do now.

"You can go,
Ina buƙatar gyaran part,
With food" shi ne abin da ya rubuta mata a jikin Jotter ɗin, ta duba kenan dole
mutum ɗaya ya tsaya, ita gasky ba wani gyaran ɗaki da zata iya, bayanta ciwo yake
idan ta yi,kuma bata saba ba. Fita tayi ta samu Halisa a main parlour a kwance
barci ya ɗauke ta tunda ta farka da asuba bata koma ba, gashi tai aiki ta gaji
sosai bata san barcin ya ɗauketa bama sbd kallo take. Tana zuwa ta fisgo ƙafar
Halisa zuwa ƙasa ta faɗo daga kan kujerar, a tsorace ta ce "Hande en boni me na yi
Anti?" Zahrah ta ce "Ai hutu kika samu kenan? Ai babu ranar da zaki huta, zaki ta
wahala har abada, kije ki gyara part ɗin Yaa Sheikh, ki kai masa lunch zan fita
unguwa" kanta a ƙasa ta kasa cewa komai, tana zaune a parlourn Zahrah ta fito cikin
wata duguwar riga ta yana mayafi hannunta riƙe da hand bag, kamar yadda Zahrah bata
kulata ba itama bata kula ta ba. A compound ta ci karo da Umar-khan yana fitowa
daga mota hannunsa riƙe da takarda. Ya ce "Evening" ta share sa, ta nufi wajan wani
da alama shi ne drivern gidan.
Kai tsaye Umar-khan gidan ya shige ya samu Halisa zaune kanta a ƙasa tana gyangyaɗi
ya ce "Matar Malam" tai saurin jan mayafin abayar ta ɗora a kanta tana yi masa
murmushi ta ce "Ina yini?"
"Lafiya, barci a nan kuma? Yaa Sheikh ɗin yana ciki?" Ta ce "Ban sani ba" ya
jinjina kai ya ce "Ok bari na duba, kije ki kwanta mana" ita dai ba tace komai ba
ya nufi Part ɗin Yaa Sheikh barci yaci ƙarfinta, ta kwanta nan ƙasan carpet.
Umar-khan ya zauna bayan ya gaida Yaa Sheikh ya ce "Na cike komai na makarantar,
gobe aka bada izinin ta fara zuwa, Mother ta ce komai cikin gaggawa take buƙata" ya
miƙawa Yaa Sheikh file ɗin takardun Halisa bai amsa ba, sai tsare Umar ɗin da idanu
da ya yi, Umar yana fahimtar shirun na Yaa Sheikh hakan ya sa ya ce.
"Al Aqeeq International School for Girls, Safiya Opens 7:30 ita ce makarantar" Yaa
Sheikh ya jinjina kansa tare da miƙewa ya shigewa ɗaki. Wajan mintuna goma suka
fito tare da Umar-khan wata Milk ɗin jallabiya ce a jikinsa, sai golden ɗin
Alkyabba daya ɗora a kan jallabiyar, ya fito a babban malaminsa sai ƙamshin Roja
yake bazawa, yana fitowa idanunsa ya sauka akan Halisa wacce ta cure waje guda tana
barci, ya tsaya cak tare da kallon Umar-khan, Umar ya nufi ɓangaren Ummul babu
jimawa suka dawo tare, Ummul ta kallesa ta ce "Malam za a fita ne?
Ba kaci abincin kirki ba?" Ya ɗan ɗauke kai zuwa hanyar fita yana faɗin. "Sanyi zai
illata ta, a sauya mata waje" sai a lokacin Ummul ta lura da Halisa.
"Tom babu damuwa, Allah ya tsare" ta nufi wajan Halisa ta shiga tashinta tare da
faɗin "Matar Malam, matar Malam" ta buɗe ido tana kallon Ummul ta ce "Maza ta shi
ki koma ɗaki, a kwai sanyi zai kama jikin ki" ta buɗe ido sosai ta ce "Anti Zahrah
ta dawo ne?" Ummul ta ce.
"Fita tayi ne? ta shi lokacin sallah ma ya yi ai muje ko" har part ɗin Halisa Ummul
ta shiga, akan idanunta Halisa tai alwala kana tai Sallah. Ummul ta ce "ƙarfe biyar
kizo ɗakina, zan nuna miki yadda ake cikakkiyar sallah, na fara karanta miki
Alkur'ani, yanzu ki kwanta wajan ƙarfe 4:30 ki tashi ki wanka ki wanke baki, ki
sauya komai na jikin ki, kinji ko?" Ta tura baki sosai ta ce "To wannan duk na mene
Ummul" Ummul ta ce "zaki sani ne" ta fice daga ɗakin.
Yaa na fita kai tsaye Al Masjid an Nabawi ya nufa sbd wani karatu da yake dashi na
musamman, kuma acan yake son yi Sallah ma, da kuma zaman tattaunawa da za su yi da
mahukunta kula da Masallaci harami ana son naɗa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu
matsayin limamin masallacin Haramin wanda zai jagorancin sallar Taraweeh da
Tahajjud, gaba ɗaya azumi saura wata guda ya rage a fara.
Tamkar uwa mahaifiyya haka Yaa Sheikh ya ɗauki Ummul yana ɗaukan minti goma yana
magana da ita, tasan kusan komai nasa kuma tasan da yawa abin da Mother bata sani
ba, tunda yafi rayuwa a Madina fiye da Nigeria. Sai bayan sallar issha Zahrah ta
shigo a gajiye tana tafiya da ƙyar idanunta ya yi jaa, Halisa ta bita da idanu
ganin yadda take tafiya kamar yaron da akaiwa shayi. Duk yadda Halisa tasu taga
dawowar Yaa Sheikh bata gani ba, barci ya ɗauketa a Main parlour. Ƙarfe 12:30 ya
shigo gidan shi kansa a gajiye yake sosai, ganinta a parlourn ya sanya ya tsaya
yana binta da idanu, a hankali ya dubi lokaci sai kuma ya shige part ɗinsa.
Kiran sallar asuba ya farkar da ita, da mmki take bin makeken gadon da take kai da
kallo, an rufe ta da wani haɗaɗɗan duvet mai ƙamshi ga laushi an kuma rage ƙarfin
a.cn ɗakin, ita dai tasan a parlour ta kwanta waya kawota nan? Ko ita ta shigo da
kanta.
Ta miƙe ta nufi toilet yadda Ummul ta koya mata haka tayi, tai wanka da ruwan zafi
ta shafe jikinta da Vaseline Intensive Care Cocoa Glow Body Lotion.

Shiryawa cikin Abaya ta ɗora hijab a nutse take duba littafan da Ummul ta bata,
Ubangiji ya bata fikirar hadda ce, da yawan lokaci ita abu a kanta yake zama, duk
wani abu mai muhimmanci bata wasa da shi. Tana zaune taji saukar muryarsa a
kunnanta yana data kabbarar sallah, shiru tai bata taɓa tunani muryar shi takai
daɗin haka ba sai yanzu. Sallah ta gabatar sannan ta nufi ɓangaren kitchen ta samu
tuni sun Bara'at sun fito. 6:30 Ummul ta ce tayi sauri ta shirya za a kaita
makaranta, wani tsalle tayi ta rungume Ummul daɗi ya kamata jin za a kaita
makaranta abin da take buri a rayuwarta. Ta shirya ta fito tsaf a cikakkiyar ƴar
fillonta Ummul na ganinta tai murmushi tana cewa "Kije ki gaida Abban naki" Halisa
ta ce "Abba kuma Ummul" ta ce "Eh, uban riƙon ka ai uba ne jeki maza" hannunta
ɗauke da yam balls ta nufi ɓangaren shi.
Cikin siririyar murya tai sallama tare da shiga tsaye ta gan shi cikin kyakkyawar
shiga mai ɗan kauri sbd sanyin garin da aka tashi da shi, hannunsa goye a bayansa
ta ƙarasa cikin da sauri tana durƙusawa har wajan ƙafafuwan shi ta ce.

"Jamɓanduna,
Noi sare,Noi kuɗe" ta jera hausuwar ma'ana _“Ina kwana, ya ya gida, ya ayyuka”_ ya
ware gajiyayyun Idanunsa a kanta, yana bin shigar makarantar nata, ta ɗaga kai ta
gan shi tsaye ta miƙe tana kallonsa, ya dubi yam balls ɗin hannunta da raguwar na
gefen bakinta. "Jiya nai barci baka dawo ba, yanzu kuma wai makaranta za a kai ni
inji Ummul" ya jinjina mata alamar _"Eh"_ yana ƙoƙarin juyawa tayi saurin riƙe
ƙugunsa da hannu ɗaya ta ce "Miyetti masin, Allah ya ƙara arziƙi"
Ɗan ƙaramin bakin maganar kawai yake bi da kallo, gumi na tsastsafo masa ta
goshinsa ta saki kyakkyawan murmushi ta ce "Mijina" da sauri ya kalli cikin
idanunta ta ɗauke nata idanun sai murmushi take sbd daɗin zata makaranta.

A hankali ta buɗe baki a taushashe kuma cikin ƙasa da murya ya ce "Matar m......"
Maganar ta tsaya sbd yam balls data tura masa a cikin baki ta dinga tsalle tana
cewa "Nayi maka wayyo daman ance baka cin abinci" ya lumshe fararen idanunsa tare
da nufar kujera har lokacin tana riƙe da shi. Yana zama ta zauna a ƙasa Yaa Sheikh
sai mai da numfashi yake sam bai niyyar cin komai ba, bisa dole ya shiga tauna yam
balls ɗin bakinsa yana goge zufar dake goshinsa, wanda kuma shi kansa ya san zufar
ta mece ce. Ya ɗauki bottle water tare da tsiyayawa a cup bayan ya sha ruwan ya mai
da numfashi. Halisa ta ce "nace Ummul tayi maka wani na cinye gaba ɗaya tas" gently
ya buɗe idanun a kanta ganin yadda yake bin fuskarta da kallo sosai yasa tai masa
kyakkyawar murmushi tana lumshe idanu tare da buɗewa kamar yadda yai, a hankali ya
ɗan ranƙwafa daidai kanta ya sanya fararen tafukan hannayensa tare da kama fuskarta
da kyau babban hannunsa yasa yaja kumatunta numfashinsa na sauka a fuskarta ya ce.
"Zaki fasa mini kai da surutu Matar Malam, shiru kan na ɗinke bakin......

Not edited
Paid book
₦500
08119237616
Sarautar marubuta.

_Ubangiji ya haɗamu da alkairan da suke cikin jumma'h. Mu haɗu Monday❤‍🔥
_
[1/3, 4:48 PM] Abk: _I unite you with the greatness of God a daina fitar mini da
littafin IDAN BA KE. What you want will not be difficult for you to buy. This is
not appropriate at all.🫰🏿har zuwa ake a nuna mini wai an samu book ɗin Idan ba ke as
free irin ga masifaffiyar nan bari nai ta ihu a media😂 I love my book lovers
wherever they are. Amma don Allah a daina fitar da book ɗin... It's 500 via
6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616_


Kasa ƙarasa maganar ya yi sbd gemunsa data kama tana cewa "Yasunan wannan abun?
Kuma da gaske ni matar malam ce, naje na faɗawa Ummul nace kace mini matar malam?"
Ya lumshe idanunsa na wani lokaci kafin ya buɗe su a kanta tare da ɗora hannunsa
akan nata data riƙe gemunsa ya zare yana girgiza mata kai.
Zata sake yin magana ya miƙe tsaye yana nufar hanyar bedroom ɗinsa dole

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login