Showing 12001 words to 15000 words out of 196133 words
iyaka da mahaifiyarta, babu
abin da zai iya a gareta, sai dai ya sanya Safwan yai wani abu akai. "Uhm ni kayi
magana mana" ta faɗa tana jijjiga hannunsa kai ya ɗaga mata ya ce "E, kina zuwa ya
kiga ta samu lafiya" Murmushi tai Wanda ya bayyanar da kyanta a hankali ya dinga
ɗauke mata tunani harta manta da batun gida sulalewa tai ta kwanta saman ƙafarsa
barci ya ɗauketa.
ISLAMIC UNIVERSITY OF MADINA.
_Jami'ar Musulunci ta Madinah_ masarautar Saudi Arabiya ta kafa jami'ar bisa
umarnin sarauta a shekarar 1961 a tsattsarkan birnin Musulunci na Madina. Koda yake
wasu sun danganta akidar Salafiyya da bude jami'ar, ana ganinta a matsayin rashin
fahimta sakamakon halayyar da cibiyar ta ke da ita ga kowane akida. Jami'ar ta sami
takardar shaidar digiri na jami'a ba tare da banbanta ta ba daga Hukumar Kula da
Ilimin Kimiya da Nazari a watan Afrilun 2017.
Jami'a ce mai tsarin gaske musamman Ɓangaren Addini. Ga nagartattun Malamai, da
yawan ɗaliban na son karatu a jami'o'in Saudi Arabia sbd dalilai masu yawa. Manyan
jami'o'in Saudi Arabia an basu shaidar yabo a bangaren ilimin kimiyya. Wasu daga
cikin jami'o'in Saudi Arabia suna cikin manyan jami'o'i a duniya dangane da
cibiyoyin bincike. Jami'o'in Saudiyya suna ba da kyakkyawan yanayin binciken
ilimin, ta hanyar ingantattun cibiyoyin bincike. Yankunan ilimi da al'adu iri daban
daban a jami'oin Saudiyya. Akwai daliban duniya daga sama da kasashe 165 da ke
karatu yanzu haka a jami’o’in Saudiyya. Baya ga manyan masana ilimi da ma’aikata da
ke aiki a waɗannan jami’o’in. Jami'o'in Saudiyya suna ba da cikakkiyar kulawa mai
kyau ga ɗalibanta da kuma malamanta. ire-iren wannan manyan dalilai yasa akeso da
burin karatu a jami'o'in Saudi Arabia.
Da sauri ya fito daga ɓangaren hall ɗin da aka ɗauki darasin Islamic Studies and
History. Kansa a ƙasa ya tatatare hannayensa cikin milk ɗin Arabian jallabiya daya
saka sai wani ƙaramin baƙin hirami da yai rawani dashi, ɗaya hiramin kuma ya ɗora
saman kafaɗarsa. Wasu matasa ne manyan suke take masa baya hadda wasu securities.
Yanayin yadda yake tafiyar kaɗai zai tabbatar maka babu sassauci a zuciyarsa,
idanunsa yai jajur bai taɓa shiga ta shin hankali na yau ba, yana zuwa bakin wata
farar mota jikin Umar-khan na rawa ya buɗe masa murfin bayan motar ya shiga,
Malamin na shiga mota, Umar-khan ya shiga gaban motar bayan driver ya shiga. Da
sauri Driver yai wa motar key ganin haka yasa Saif-Wazir ya shiga wata motar kai
tsaye daga cikin University ɗin Prince muhammad bin abdul'aziz international
airport suka nufa.
Ta cikin madubin motar Umar-khan yabi Sheikh Aliyu Haydar wanda ke bayan motar da
kallo, ya jingina da jikin Kujera sai huci yake fitarwa, ya rirriƙe Jallabiyar
jikinsa da hannu bibbiyu, gumi na tsastsafo masa ta tsakiyar goshinsa sbd yadda
zuciyarsa ke masa zafi da ta fasa. Girgiza kai Umar-khan yai cike da tausayin
yanayin yadda Sheikh Aliyu Haydar ke gabatar da rayuwarsa. Juyawa yai yaci gaba da
kallon yadda driver ke sharara gudu, har suka ƙaraso filin tashi da saukar jirgin,
The plane is ready to take off. Tun daga bakin wajan securities ɗin suka firfito
tare da mamaye motar Sheikh, Umar-khan ya buɗe murfin motar ciki. Sauri Sheikh
Aliyu Haydar ya fito a wannan lokacin ma kansa a ƙasa, yana hawa strains ɗin jirgin
Saif-Wazir na biye dashi, sai Umar-khan wanda ya ɗan tsaya yana amsa kiran Father.
Cikin damuwa Umar-khan ya ce "Kayi haƙuri Father, Sheikh ba zai taɓa aikata hakan
ba, zargi ne kawai ake masa, yanzu jirginmu zai tashi be patient Father" tsaki
Father yai ta cikin wayar kafin ya kashe. Yana shiga jirgin aka bawa Pilot daman
keta hazo, a hankali jirgin ke zagayawa a ƙasan kwalta ya jima a haka kafin ya kete
zuwa sararin samaniya.
Jeniyar motocine suka tabbatar da Father Sheikh Aliyu Haydar ya ƙaraso gida
Nigeria, da sauri ya miƙe daga zaunan da yake yana zaga haɗaɗɗan parlon gidan, tare
da jiran shigowar Sheikh ɗin. Da mamaki Umar-khan ke bin ƴan jaridu da kallo, daga
na gidan Redio, T.v, media. Abin har yai tsamari haka yana da tabbaci Sheikh ba zai
taɓa aikata abin da ake tuhumarsa ba, zargi ne kawai. A nutse ya sakko da ƙafarsa
daga cikin motar kai tsaye ƙofar shiga cikin gidan nasu ya nufa, Umarninka da
Saif-Wazir na karesa daga ɗaukan da ƴan Jaridu suke masa. Sako ƙafar da Sheikh
Aliyu Haydar yai cikin parlon yai daidai da lokacin da Father yake sauke masa wani
lafiyayyan mari wanda yasa Umar-khan saurin juyawa ya fita, domin ba zai iya jure
ganin ana cin zarafin babban mutum akan idanunsa ba kamar Sheikh Aliyu Haydar,
Saif-Wazir Hawayen da yake maƙalewa ne suka sakko masa, da sauri ya karawaw Umar-
khan baya. Cikin faɗa da tsawa Father ya ce "Ka kyauta Aliyu Haydar, ashe wannan
dalilin ya hanaka auren tsayin shekaru talatin da huɗu? Ka yaudareni kaci amanar
Musulmai kana fakewa da karatun addininka kana lalata yaran mutane a makarantar
Jami'ar Madina?" Har wannan lokacin kan Sheikh a sunkuye yake banda cukurkuɗe
Jallabiyar jikinsa da yake da hannu babu abin da yake. Father ya girgiza idanunsa
cike da hawaye ya ce "Ba shakka biri yai kama da mutum, tunda nake baka taɓa zuwa
wajena kace Father na zaɓi yarinya ina son aurenta ba,You betrayed me Aliyu, you
deceived me as your father" Ya faɗa yana saukewa Sheikh wani marin cikin tsawa ya
ce "Talk Aliyu, kayi magana ka amsa mini Sheikh..!!!" Father ya faɗa yana Girgiza
kafaɗar Sheikh. Ɗago kai Sheikh yai bakinsa na rawa laɓɓansa na karkarwa alamar
yana son cewa wani abu, amma sam ya gagara sbd rashin iya magana da bai ba. "Ban
damu da duk yadda zakai magana ba Aliyu, a yanzu ba zanwa ƙinƙinarka uzuri ba ka
bani amsa da gaske wata kaiwa ciki?" Shaaa hawaye ya sauka fuskarsa Sheikh sbd
yadda yake son furta wani abu ya kasa. Matsawa ya yi kusa da Father yana buga
hannunsa a cinya a hankali hannu na rawa ya miƙa tare da kama kwalar rigar Father,
idan ya ɓalle bottle ɗin gaban rigar Father sai ya mayar rufe, da ƙarfi ya buga
ƙafarsa yana riƙe wuyan Father hawaye ba zubu masa cikin ƙinƙina ya ce.
"Ya....ya.... ya Allah..." Ya ƙare mgnar cikin ƙinƙina yana mai buga ƙafarsa a
ƙasa.
Share as so much as you can💋... Not Edited👏🏻
#Sarautar marubuta
#True life story
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
_*Arewabooks@Nimcyluv*_
Follow my account👇🏾
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
7...
"Heeeyyy..faaa..Father,babb babu uhmuuu macen dana taɓa laaahhh latawa" a wahale ya
Ƙarasa maganar sbd zafin ƙinƙinar dake cinsa take basa wahala, yana buga ƙafa a
ƙasa tare runste idanunsa zuciyarsa na maza zafi da raɗaɗi sosai na cin zarafi da
sharrin da ake son yi masa, amma ko kaɗan fuskarsa bata nuna damuwar da yake ciki
ba, ƙinƙinar ita ke azabtar da zuciyarsa wacce take kassara dukkan wani mafarki
nasa. Hannun Sheikh dake wuyan Father ya ture cikin ɗaga murya ya ce "Ok ƙarya za
ayi maka kenan Sheikh? Mutane dubu nawa ne a makarantar ba ace sune suka aikata
haka sai kai? Kasan halin da ake ciki yanzu gidan Jaridu na gab da sakin labaran?
Mata nawa ka lalata, mata nawa kai wa ciki?" Cikin zafin maganganun Father Sheikh
ya ƙara runste idanunsa kansa ma sara masa, shiru kawai ya yi ba tare da ya ce
komai ba. Father ya yi tsaki yana juyawa zuwa upstairs har lokacin bai dai na faɗa
ba. "Kaje ka kare kanka daga zargi Aliyu, at anytime jami'an tsaro na iya zuwa, You
are accused of a serious crime, we have no evidence to defend you in court"
"Wanne Irin Court Father? Laifin Aliyu har ya yi girman da za a kaisa court?
Wallahi babu mai kai mini ɗana Court" Hajiya Maryam wacce suke kira da Mother ta
ƙare maganar tana sakkowa daga upstairs, domin lokacin da motocin su Sheikh suka
shigo Sallah take. Father ya Kalli Hajiya Maryam tare da nuna Sheikh wanne yake ta
damƙi Jallabiyar jikinsa. sam bai damu da duk zargin da za a yi masa ba, idan
ƙaddararsa ce ta zo da haka babu yadda za ayi ya goje mata. "Sai ki tilasta masa ya
yi magana, na faɗa masa ya nutsu ya ajjiye ƙinƙinarsa a gefe ya bani bayani, amma
yaƙi, kina tunanin iyayen yaran zasu ɗaga masa ƙafa ne akan laifin fyaɗe da ya yiwa
yaransu? Sbd kasancewarsa Malami kuma mamallakin S.A.H BANK..? ki Ajjiye son da ki
ke masa a matsayin ɗanki, ki kwatantanta adalci tsakaninsa da sauran yaran daya
lalata Maryam" Cikin faɗa Mother ta ce "Look Aliyu, idan kai ba zaka iya ƙwatarwa
ɗan ka ƴanci ba, zan shiga ko'ina domin ganin an wanke Sheikh daga zargin da ake
masa, ba abin kunya bane ace wai kai ne mai bada goyon baya akan Aliyu Haydar ya
aikata hakan?" Father wanda Hajiya Maryam ta kira da Aliyu dake sunansa aka sakawa
Sheikh ya yi Murmushin ta kaici. "Idan taƙamar maki Lawyer ce, kada ki manta su ma
yaran Gwamnati na iya ɗaukar musu lauyoyi, dake da gwamnati sai ku zuba muga, kada
ki manta daga can Madina aka zo da zan can, an kai maganar state C.i.d idan jami'an
Nigeria bata ɗauki mataki ba, na Madina zasu ɗauka suna gab da bashi takardar kora
daga aiki" yana faɗin hakan ya haura sama cike da baƙin cikin abin da Sheikh Aliyu
Haydar ya ja musu a cikin Alhhali.
Mother ta bi bayan Father da kallo, tana mamakin rashin ko'in kula da Father yake
nunawa Sheikh kamar ba ɗan cikin sa ba. Juyawa tayi tare da kallon Sheikh da har
yanzu kansa yake ƙasa tasan he never talk domin damar maganar bata damesa ba, sbd
ƙinƙinar da Ubangiji ya jarabce shi da ita. Tana ƙoƙarin yi masa magana ya juya da
sauri zai bar parlourn sbd raunin daya hango cikin ƙwayar idanun mahaifiyar ta shi.
Yana saka kansa zai bar parlourn Umar-khan ya shigo da sauri jikinsa na rawa ya ce.
"Innalillahi wacce irin masifa ke shirin tunkaro Mother?" Mother na ɓoye damuwar
ranta ganin yadda Umar-khan ya firgita ta ce "Me ne ya faru Umar-khan?" Idanunsa
akan Sheikh wanda ya ɗan jinkirta da fitar Umar-khan ya ce "Na rasa tayaya ƴan
Jaridu suka samu wannan labarin, gaba ɗaya sun cika gidan nan da waje baki ɗaya,
duk yadda securities sukai ƙoƙarin hana faruwar hakan amma abu ya gagara" Sheikh na
jin haka ya juya alakar tafiyarsa zuwa haɗaɗɗan sashinsa dake cikin gidan nasu.
Mother ta bi bayansa da kallo kafin ta juya ta kalli Umar-khan tace "Na jima banga
mutum mai taurin kai da tsayayyiyar zuciyar irin Sheikh ba, duk abin da za ayi masa
ba zai taɓa cewa komai ba" Umar-khan yaja numfashi yana mai ƙara gasgata zan can
Mother, domin babu wanda bai san Sheikh da kafiya ba. "Yanzu ya za mu yi Mother?
Al'amarin nan ya shige tunaninmu, ba tsammaci haka ba" Mother ta zauna kujera tana
tunani ta ce "Zan shigar da ƙara Court, da kai da Saif-Wazir kuji da ƴan jaridu
subar ƙofar gidan nan Immediately"
"Court Mother? Waye zai tsaya masa? bakya tunanin shiga Court ɗin kamar latata
rayuwar Sheikh ne?" A taƙaice Mother tana danna waya ta ce "Hakan ne mafita Umar-
khan, batun lawyer ni ce zan tsayawa ɗa na da kai na" "but Mother" hannu ta ɗaga
masa cikin sakin murya ta ce "Umar-khan...!!! Stop asking to much" jinjina kai yai
ya fita yana jinjina girman yadda abin ya lalace cikin ƙanƙanin lokaci haka.
Sheikh na shiga bedroom ɗinsa yaja numfashi sbd wani sassayan ƙamshin turarensa na
ROJA daya daki hancinsa wanda ya jima da zama abokin hirar ɗakin. Ƙamshin daya
haifar masa sauƙi a zuciyarsa, kasa zama ya yi ya shiga kaiwa da komowa a tsakiyar
bedroom ɗin, tunani fal ransa wacce yarinya ya lalata? ba mace ɗaya ba har mata da
yawa, kuma harda ciki? Bayan tunda yake maganar minti 20 bata taɓa haɗa shi da mace
ba, idan ka ɗauke mother. Bai taɓa jin sha'awar mace ba, duk daɗin muryar mace bai
taɓa ji ba, kamar an saka masa tsanar mata haka yake ji a ransa balle a wayi gari
yau wata ta birgesa ba. Yinin ranar a sashinsa yake, Mother ba tai tunanin zuwa
wajansa ba, ta san ba zai taɓa saurararta ba, koda Maimoon ta nufi part ɗinsa ɗauke
da try na dinner yadda taje haka ta dawo, bugun duniya yaƙi buɗewa haka ta juya
tana mai jin tausayin yayan nata.
Mother dake zaune a Parlourn Father dake cikin sashinsa ta gyara zama ta ce "I
couldn't believe what was happening,Aliyu is your son, you gave birth to him. Me ya
sa ka yarda a ranka zai aikata hakan?" A nutse Father ya ɗaga kansa ya kalli Mother
kafin ya ce "na fiki sanin ɗana ne, tunda akan idanuna ki kai Labour ɗinsa, amma
hakan baya nufin zan saka masa Idanu, sai yanzu na fara tunanin tsayin shekarun da
Aliyu ya kwashe a wannan duniyar ba tare da tunanin yin aure ba, kamar ko wanne
namiji, nasan Aliyu nada lafiya balle nace, ke shaida ce how many times da zan kira
Aliyu nace ya fitar da matar aure ya ce na bashi shekara ɗaya ko wata kaza? He is
thirty-three years old now, but to this day there is no thought of marriage in his
mind. Ni da kai na, na fara shakku da tantama idan ba lalata yaran mutane yake"
wani irin ɗaci Mother taji a ƙasan zuciyarta, wanda ya sa ta fara ladamar yarda da
Mijin nata da tayi. Magana ɗaya zai yi a janye Case ɗin amma yaƙi infact bai damu
da matsalar ɗan nasa ba. Miƙewa tsaye ta yi tana kallonsa idanunta na sauyawa amma
ta hana kanta zubar da hawaye ta ce.
"Court zata tantance mai gaskiya, kuma zata wanke Sheikh daga sharrin da ake masa"
tana faɗin hakan tai waje cikin ƙonar zuciya. Bayanta yabi da kallo yana faɗin "If
you give evidence that Aliyu is innocent, zan tsaya wajan karɓar masa haƙƙinsa
Maryam" sosai kalamansa suka daki kunnanta amma ta share.
Tana zuwa parlour ta samu yaranta zaune sun zabga tagumi "Maimoon zugi driving
nawa, Zeefa ke da Fattoumah ku zauna, I'll be back 10:00 ki tabbatar kunyi alwala
tare da sallah kun kwanta barci, kada na dawo naga kuna kallo ok" Fattoumah ta ce
"Mother ina zaki? Yaa Lee har yanzu bai fito ba fa?" Mother ta ce "Kada ki takura
Sheikh, idan kika takurasa sai ya shaƙeƙi tas kafin ya baki amsa, You better be
careful, bye my babies"... "Bye Mother" fita sukai har lokacin wasu ƴan jaridun na
ɓoye suna jiran ganin motar Sheikh ta fito. Maimoon na fita taja motar da gudu ta
ɗauki hanyar da zata kaita Maiduguri road.
Tafiya kawai Danejo take babu takalmi kalbar kanta duk ta hargitse duk wanda ya
ganta a wannan lokacin babu tantama zai kirata da mahaukaciya wacce ta jima cikin
ciwon haukan. Tafi futu futu baya hayyacinta baki ɗaya,ita kanta ba zata taɓa tuna
kwanakin data shafe tana tafiya ba, kuma abin mamaki ko gajiya ba tayi duk wanda ya
ganta tambayar duniya idan zai mata ba zata taɓa kallon inda yake ba, balle kuma ta
bashi amsa. Cikin ikon Allah ta samu kanta a gefen Rugar Rome inda take zuwa kiwo,
tana zuwa nan ta yanke jiki ta faɗi babu numfashi. A hankali jikinta ya shiga
Girgiza wani hayaƙi nafitowa ta jikinta a hankali hayaƙin ya cure waje guda, a haka
ya rikiɗe zuwa suffar Prince.. idanunsa na kanta yana ƙoƙarin zuwa inda take yaji
an daka masa tsawa wacce ya sanya ya tsaya da zuwa inda take, ko ba a faɗawa Prince
ba ya san wane yake masa wannan tsawar domin shi kaɗai ya isa ya yi masa tsawa ya
saurara.
"Ka Saurara Prince, kada ka kuskure ka taɓa Bil'adama ɗin nan" Prince ya juya
idanuna ya sauka akan mahaifina wanda yake cikin suffar mutane cike da kamala.
"Matata ce Abba, ina da ikon taɓa ta a lokacin da nasu kada ka hanani aikata hakan"
Wanda aka kira da Abba ya kalli Prince ya ce "Ban san yaushe ka zama mai son zuciya
ba, zuciyoyi nawa zaka baƙantawa? yanzu bayan wannan ƴar tayin kaje ka saka bawan
Allah cikin masifa me ya yi maka?" Prince yana huci ya ce "Abba wannan bawan Allan
shi ke shirin rabani da farin cikina, na jima da sanin haka shi ya sa na fara yin
abin da ya dace, kashe sa naso yi ma.." Abba ya kalli Prince da mmki kafin ya ce
"Shi ne daidai da rayuwarta, shi ne Bil-adam shike da ikon kasancewa da ita, ba kai
ba da kake Hallitar Ubangiji ta ban ƙasa ina rabaka da son zuciya, koda muke aljanu
hakan bai zama lasisin da zamu cutar da wata hallita dake duniya ba, ko me zakai ba
zaka taɓa iya cutar da shi ba" A hargitse Prince jiki na rawa yana rikiɗewa zuwa
suffar aljanu ya kalli Safwan ya ce "Kai ne ka faɗa masa abin da na aikata ko? Kai
ke ko?" Kafin Safwan ya yi magana Prince ya ɗaga sa zuwa sama tare da buga ƙasa da
jikin dutse yana ƙoƙarin sake ɗaga Safwan, Abba yai wata kururuwa hakan yasa Prince
yin kururuwa shima lokaci guda suka koma aljanu...
08119237616...
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
*_Nimcyluv sarauta_*
_*E.O.W*_
9...
"You're under arrest?" Umar-khan daya fito daga cikin mota ya ƙara maimaita kalmar
ɗan sandan wanda ya yi ɓadda kama cikin kayan gida. Ɗan sandan ya kalli Umar-khan
fuska ba walwala ya ce "As you heard" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Shi ne
kalaman da Saif-Wazir ya faɗa domin Umar-khan kasa motsawa ya yi idanunsa a ƙasa
baya taɓa jin zai iya haɗa idanu da babban mutum kamar Sheikh Aliyu Haydar cikin
wannan halin. "Yallaɓai kayi mana afuwa mu shiga ciki mu tattauna, ba sai an tafi
da Yaa Lee police station ba please" Wanda aka kira da Yallaɓai ɗin ya ce "Stop
interfering with our work, because we know our work well, kuma wane ya faɗa maka
police station zamu kai Aliyu Haydar Aliyu? State C.i.d zamu" da tsoro sosai akan
fuskar Saif-Wazir ya ce "C.i.d? Wajan da ake ajjiye manyan masu aikata criminals,
ƴan fashi,ƴan daba, Kidnappers Sheikh bai dace da wannan wajan ba, don Allah kada
ko taɓa mana martabarsa.....," Ishaq-hakim ya katse Saif-Wazir da faɗin "har yanzu
ba a tabbatar da abin da ake tunanin ya yi ba, zargi ne kawai" Wani daga cikin
ma'aikatan ya ce "Say whatever you want to say,We must arrest Sheikh Aliyu Haydar
Aliyu" cikin zafin zuwa Ishaq-hakim ya kalli ɗan sandan yana nu nasa da hannu ya ce
"Idan ta ƙamar kai uniform ne a jikinka mu kuma mune da garin, wallahi idan ya
tabbata Sheikh bashi da laifi sai munyi Shari'a da kai" yana faɗin hakan ya juya da
sauri ya nufi babban gate ɗin shiga gidan Hakimi, kasancewar daman a ƙofar gidan
suke. Sheikh dai na tsaye tamkar ba akan sa ake wannan muƙabalar ba, ya tsorawa
hannunsa dake maƙale da ankwa ido shi kaɗai zai iya fasalta halin da zuciyarsa ke
ciki sai kuma Abba Hakimi dake iya fahimtar raunin zuciyar Sheikh ɗin lokaci guda.
Suna ƙoƙarin saka Sheikh cikin wata baƙar mota mai kyau wacce babu wanda zai iya
ganin Sheikh ɗin a ciki gyarar muryar Abba Hakimi ta karaɗe wajan. Cikin mutuntawa
da tarin ladabi duk jama'ar wajan suka sunkuyar da kansu ƙasa. A hankali