Showing 126001 words to 129000 words out of 196133 words

Chapter 43 - IDAN BA KE by Nimcyluv sarauta

09 Jun 2026

116

ma daga wanka ta fito ko shiryawa ba tai ba,
ta nufo wajan na shi.
Tana zuwa ta nemi zama kan cinyar shi, ya yi saurin riƙe hannunta tare da ɗago
kanshi idanunsa ya sauka akan fuskarta idanunsa ya sauka tsakiyar nata tayi saurin
janye nata, saboda kaifin na shi idanun. A hankali ya ajjiye littafin yana jawota
tare da zaunar da ita saman ƙafafuwan shi tayi saurin juyawa suka fuskanci juna!
Ya dubi bakinta ganin kamar tana cin abu tare da saka hannu ɗaya ya tallafo haɓarta
tare da saka hannu ya buɗe bakin nata, ya buɗe idanunsa akan ta, tare da mayar da
idanunsa cikin bakin tayi saurin riƙe hannun ta ce
"Abba ina so, kada ka cire" ya kame fuska tare tsare ta da idanu a hankali ya zare
raguwar ƙanƙarar dake bakinta "leƙe ko? baki san mijin naki ba ne" tayi murmushi ta
ce "Abba naga ka ƙara babba, kayi kyau shi ne fa" ta ƙare maganar tana son ƙwace
ƙanƙarar daga hannu shi.
Shiru ya yi hakan ya sa ta ce "Ka bani to, yawuna duk ya tsinke" ya ƙara haɗe fuska
ta ce "Don Allah, wallahi zan maka amai idan baka ban ba"
Ya sauke numfashi yana juya idanu a hankali ya ce "Me ya sa? sanyi zai miki illa
fa?"
Ta saƙalo wuyan shi hannunta ɗaya tana shafa sajan shi zuwa dugun gemun shi ta ce
"Kawai naji ita nake so, bana son komai sai ita"
ganin da gaske ice ɗin take so, gashi nan tana ƙoƙarin kakarin amai ya yi saurin
zura mata a baki, taka duguwar ajjiyar zuciya idanunta na lumshe duk ta narke a
hannun shi.
A hankali ta ji saukar hannunsa a flat ɗin cikinta ya shafa kaɗan, tayi saurin
kallon shi, Yaa Sheikh soyayyar abin da ke cikin matar malam ɗin ya mamaye zuciyar
shi, yana ƙara yiwa Ubangiji godiya daya azurta matar da zuciyarsa ke so fiye da
komai, da samun cikinsa jininsa ke kwance a ƙasan mararta.
"Allhamdulillah!"
Ya faɗa a taƙaice. Halisa ta ce "Abbana mene?" A daidai kunnanta ya ce "My
kankanaty, baki san azumi nake ba? Ohya ɗaga ni" ta ce
"Azumin me Yaa Sheikh?" Halisa Said while playing with his beard.
Ya ɗaga ta daga jikinsa yana nufar bathroom ya ce "lokaci, sallah" yana ƙoƙarin
shiga cikin toilet ɗin yaji ta rungome shi ta baya hannunta bakiɗaya ta saka ta
riƙe ƙugun shi, ƙirjinta dake gogar bayan shi ya sanya tsigar jikinsa ta shi, ya
rufe idanu a fili ya ce
"Yasubuhanallah! Ya Rasulullah! Zaki ɗauki hakki" ta saki dariya sosai ta ce "hakin
me zan ɗauka Abba?" Yana ƙoƙarin magana yaji saukar hannunta inda bai yi tunani ba,
ya zare hannunta daga marar shi kamar zai kuka, duk ya ɗan birkice ya kame fuska
tare da juyawa ya ce "Burinki ki karya azumi? Allah ya takaita mini wahala an kira
sallah na yarda mata shaiɗanu ne wannan ɗaukan hakƙi ne Zawja"
Ya yi saurin turata baya tare da tura ƙofar tana dariya ta ce
_“I love you Yaa Sheikh Ya shehin malamina”_ Ya girgiza kai kawai kamar yadda Ummul
ke yi idan abu ya bata mamaki, ya daɗe tsaye yana mai da numfashi, ya tabbatar da
kafin a kira sallah tai masa haka to ya yi wahalar banza babu inda azumin za shi.
Wanka ya yi sosai kana ya ɗaura alwala, ya fito jikinsa na zubar da ruwa ƙamshin
Lifeline skin care pro plus shower Gel na fita daga Jikinsa ya shirya cikin wata
white Embrodiery design jallabiya, ya ɗora hirami tare da rufe kan shi sai fuskar
shi da gemunsa dake bayyane, direct fita ya yi ƙamshin Roja ya sanya Abba Hakimi da
Mai martaba kallon direction ɗin duk da sun riga san waye, bai magana ya nufi
Masjid. Bayan yaja sallah ya dawo gida kai tsaye part ɗin shi ya nufa, Mother na
zaune ita ma idar da sallarta kenan ta kammala shirya wa Yaa Sheikh kayan buɗe
baki. Ta kalli Halisa data fito sanye da blue ɗin hijab ta ce "Daughter ga Abincin
Yaa Sheikh maza zo ki kai masa" kafin Halisa tai magana Abba Hakimi ya ce "Ba dai
ita ba, ki kai masa da kan ki, idan kin kai kice ina buƙatar ganin shi da zarar ya
gama" Halisa bata ji daɗi ba, amma ta kasa cewa komai ganin Abba Hakimi ya haɗe
fuska sosai. Mother ta kai masa ta kuma sanar masa umarnin Abba.
Suna zaune duka a parlour Dada ta fito wani ihu Halisa tayi tare da rungome Dada
idanunta cike da hawaye ta ce
"Dadata nai ta jiran ganin ki" Dada tai murmushi sosai wani daɗi ya kamata ta ce
"Ke kam baki girma" Umma A'isha ta ce "Ba batun girma, ni dai abin da ke tare da
ita nake ji, garin tsalle tsallen nan zai a zubar da shi" Mother ta ce
"Ah Allah ya ki yaye Umma, na lura wasan jika da kaka ki kewa Daughter" ita Halisa
hankalinta na wajan Dada ta ce "Ina ki kai shiga, Dadata nayi missing naki da yawa"
Data ta zauna tana cewa "Munje wajan El-bashir duba jikin shi" Annurin fuskar
Halisa ya sauya jin ance El, bata mance abin da ya yi wa Abbanta ba, kuma ita ma ba
zata taɓa son shi ba. Ta zauna tana cewa
"Ina Shatu?" "Tana Rugar Rome, za a kawota gobe idan Allah ya kai mu" Halisa ta
miƙe ta ce
"Bari na faɗawa Yaa Sheikh kin zo ko?" Ba walwala a fuskar Abba Hakimi ya ce
"Kada naga ƙafar ki a part ɗin shi" tayi saurin cewa "To me ya sa, bayan lada zan
samu" Mother ta ɗauke jin za a fara halin, Umma A'isha murmushi kawai take, Dada
kuma tai shiru dan ba huruminta ba ne.
"Haka na ce, muddin ki ka je ki tabbata zaki bi iyayenki Masarauta" ta haɗe fuska
idanunta na kawo ruwa cikin rawar murya ta ce
"To a gasky Jon wuro ban gane ba, gwara kawai mu koma makka zaman can yafi daɗi
tunda babu saka idanu" Abba Hakimi maganar ta dage shi, yasan kuma da iyakar
gaskiyar ta take faɗa. "Tashi kibar wajan nan Dajeno" cewar Dada ta miƙe tare da
yin bedroom ɗinta ta ce "Mutum da mijinta"
Gabaɗaya sukai kamar basu ji me ta ce ba, Abba Hakimi ya tura a kira Zahrah ba
jimawa ta fito ɗauke da jaririn. Zamanta kenan ƙamshin Roja ya daki hancinta, tayi
saurin lumshe idanunta nutsuwa na saukar mata, ta tsare Yaa Sheikh da idanu shi kam
bai kalli inda take ya nemi waje ya zauna saman kujera yana rufe.
"Aliyu na kira ka domin kayiwa Yaron Zahrah huɗu ba" Ya kalli Abba Hakimi na wani
lokaci kana ya jinjina kai, da sauri Zahrah ta miƙawa Yaa Sheikh babyn da yake ta
barci gwanin sha'awa ya ƙara girma, a hankali ya ɗora bakinsa a kunnen bbyn tare da
yin Bisimillah kana ya yi masa huɗuba da suna.
MUHAMMAD.
"Ma sha Allah, Rabbi ya raya Muhammad" cewar Umma A'isha Dada ta amshi yaron,
hawaye ne ya dinga sauka daga idanun Zahrah ji take kamar taje ta rungome Yaa
Sheikh ta ɗora kanta a shoulder ɗin shi tayi kuka mai yawa ko zai tauyasa mata, ta
goge hawayen ta ce "Na gode Yaa Sheikh, don Allah kayi haƙuri ka yafe mini"
Kamar daga sama su kaga Father ya faɗo parlourn hannunsa riƙe da Zeefa ya fita
hayyacinsa ya zube gaban Mother ya ce
"Maryam ashe zaki iya kai uban yaranki ƙara court?" Tai masa Shiru idanunta akan
Auta Fattoumah ta miƙa mata hannu da sauri ta nufi mother tana zuwa ta rungometa,
Maimoon na tsaye taci kuka ta ƙoshi komai ya daina yi mata daɗi. "Ki tausaya mini
ki janye wannan ƙarar" tai wani irin dariya tana kaɗa ƙafa ta ce
"Wallahi Allah kaji na rantse maka Engineer Aliyu sai ka sakeni wannan cikon ɗayar
da Jadda ta hanaka ita nake buƙata yanzu" kamar zai kurma ihu ya ce
"Wallahi ba zan taɓa rabuwa dake ba Barrister sai dai mu zauna daga ni harke ba
aure" Mother ta ce "Ka zauna dai? Amma ni aure babu fashi wata ɗaya ya yi yawa
banda darajar idda, kuma banda abinka baga uwar shegen ɗanka nan ba sai ka aureta
kuci gaba daga inda kuka tsaya"
Da sauri Auta Fattoumah ta ce "Mother bana son babyn na tsane shi ba ɗan uwanmu
bane" Mother ta ce "He never been your brother Mamana, tafi bedroom ki kwanta"
Father ya yi saurin janye Auta Fattoumah ya ce "Ta tafi ina? Ƙafata ƙafar yarana
idan kin damu da su ki dawo gare su, na shirya shi ga Court duk abin da zaki kiyi
amma ba zan taɓa sakin ba" ya ɗauki Auta Fattoumah tana rusa ihu ya saka hannu ya
kama na Zeefa da Maimoon sukai waje.
Da sauri ta miƙe zata bi bayan shi Abba Hakimi ya ce "Kada ki fara" takaici ya sa
tayi bedroom tana sakin kuka. Abba Hakimi ya kafa ya tsare daga Halisa ta fito yake
fatattakarta bedroom, Ogan da kan shi ya fito yana fitowa suka haɗa idanu da Abba
Hakimi, bai ce masa komai har Yaa Sheikh ya gama zaman shi ya koma part ɗinsa, ya
kasa barci ɗumin jikin matar dana gudan jinin shi kawai yake so yaji, gashi gobe
Alhamis zai ta shi da azumi still, ya miƙe da ƙyar ya nufi bathroom ya saukarwa
kansa ruwa mai sanyi ko zaiji sauƙi, ɓangaren Halisa kusan haka ne, cikin dake
Jikinta ya ƙara mata muguwar sha'awa ta buƙatuwa fiye da kima, gashi ita babu
damara ta dinga malelekuwa a kan gado, da ƙarshe ta miƙe zaune tare da fashewa da
kuka, su duka sai bayan sallar asuba barci ya ɗauke su.
Washegari parlourn Abba Hakimi ya cika da mutane har wanda Yaa Sheikh bai zata ba,
Uncle Haroon, Uncle Bashir, Mahaifin Zahrah da Mimi, tare da Surry, Mother, Umma
A'isha, Dada, Yaya Halima, Dr A'isha. Sai Ummul dake zaune gefe guda cikin wani
white lace mai kyau da tsari, ƙamshin Roja da taji yasa ta ɗago kanta zuwa inda
jarumin ɗan nata yake tsaye, Yaa Sheikh mamakin yadda duk mutanan suka zo lokaci
guda yake, ya nemi waje kusa da Ummul babu ko kunya ya zauna. Aka buɗe taro da
addu'a Kafin Abba Hakimi ya kalli Uncle Haroon ya ce "Haroon ɗan fito mini da dairy
ɗin nan" Uncle Haroon ya miƙawa Abba Hakimi, shi kuma ya buɗe wajan deal ɗin su da
Yaa Sheikh da saka hannu da komai. A hankali ya miƙewa Yaa Sheikh ya daɗe kafin ya
saka hannu ya amsa. Abba Hakimi ya ce "Ka duba deal ɗin nan, ka yanke hukunci
tsakanin ni da kai ga shaidu a gabanmu, ka riƙe amana? Ko dai kaci Amana? Kai inama
zaka ci wata mana bayan baka son ta, ba zaka taɓa son ta ba har abada....
[1/14, 10:34 AM] Abk: _*Ga masu buƙatar yi musu tallah su yi magana 08119237616,
har kullum Idan ba ke na kuɗi ne akan ₦500 🫰🏽1k for Special*_


Uncle Bashir ya ce "Abba Hakimi da anyi masa afuwa, hakan ma kaɗai ya isa yaji
nauyinka" Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh yana jinjina ƙarfin hali da zurfin cikin
shi ya ce "Anya Bashir? Ai Aliyu bai ɗauki hanyar da zamu shirya ba, basshi ya faɗa
mini saka hannun waye wannan a cikin dairy ɗin?" Yaa Sheikh ya rufe ido ya buɗe,
yana mai ta'ajujin abin a ran shi, gabaɗaya ya manta da batun wani deal a tsakanin
shi da Abba, shi bai ga abin ɗaga zancan ba idan ba so Abban yake ya kunyata shi
gaban sirikan shi ba. "Sa hannuna ne"
Ya faɗa a taushashe yana mai daidaita zaman shi babu tsoro akan idanunsa, cikin
nutsuwa ba kwanakwana ya shaidawa Abba Hakimin haka. "Hakan na nufin kaci amana
kenan Yaa Sheikh?" Yaa Sheikh ya yi shiru he refuse to answer the question. Ya
ƙara cewa "kamar ba babban malamin da ya yi magana akan al'ƙawari da muhimmancin
shi ba?" Yaa Sheikh ya zare nauyin Abba Hakimi da yake ji cikin ladabi ya ce
"Abba na fa ce maka ba zan iya ba? Ka manta ne?" Dr A'isha tayi saurin cewa "Ba
zaka iya riƙe amanar ba?" Ko inda take bai kalla ba, amma yadda ya kame fuska waje
guda zaka san mganar ta, sam ba tayi masa ba, kuma bai fiya son shisshigi ba a
rayuwar shi.
Abba Hakimi ya yi murmushin manya ya ce "To ka amsa mata mana?" Yaa Sheikh ya harɗe
hannunsa a ƙirjin tare da yin baya idanunsa rufe, Ummul kanta a ƙasa ba ta ce komai
ba, amma ita kanta zurfin cikin Yaa Sheikh yana damunta kuma a shirye take da huran
da Abba zai masa
"Kada na sake tambaya kayi mini shiru Aliyu" Yaa Sheikh ya ce.
"Abba nifa na nemi aurenta, taya zan riƙe wannan deal ɗin?....," Dr A'isha ta ƙara
cewa "hakan nuni da cewa kana son Halisa? Ko dai har yanzu kallon ƴar raino ka ke
mata kuma ƴar ka?" Bai kulata ba, daman tasan ba zai tanka taba ɗin kamar yadda ta
tsammata
Kamar daga sama kuma taji ya ce "Zan rayu da ita, daga nan har sanda zan numfashin
ƙarshe a kafaɗunta" maganar Yaa Sheikh ta girgiza dukkan jama'ar parlourn musamman
Zahrah wacce zuciyarta tai masifar bugawa, kenan ta rasa Yaa Sheikh? Ba zai taɓa
son ba har abada? A ɓoye ta dinga shassheƙa kuka tana gogewa duk abin da take akan
idanun Mimi
Uncle Haroon ya yi murmushi sosai wanda Yake nuna jin daɗi ya ce
"Kamar Aliyu ya kawo ƙarshen dramar ko Abba, yana son matar shi, matar shi na son
mijinta" kai tsaye Abba Hakimi ya ce "He must pay for what he did" ya gyara zama
sosai fuska babu walwala ya ce "Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu, ko ka ce Dr Aliyu
haydar Aliyu, kai mutum ne mai daraja, ni kuma ba mutumin banza bane, akan idanun
jama'a na soka da alheri kai kuma ka bijire mini? Ba damuwa nasan alkairi ce ita a
rayuwarka ko yanzu, am happy for her data samu namiji kamar ka, amma kafi dace da
samun kamarta,ita ɗin macan sirri ce, mai nuna soyayyar mijinta a ko wanne lokaci,
Na fahimci son da ka ke mata tun kwanaki a waya, So ba ƙarya bane, gaske ne, kuma
tsararren abu wanda yake zane a zuciyar ko wanne bawa, amma ka sani..,"
Ya yi shiru na wani lokaci can ya ce "Za ai muku sabon aure da Halisa, dukkan wani
abu da ake a biki dole kayi da arziƙin da Ubangiji ya baka, kuɗin na gani ina so,
kayan lefe komai da komai, kafin lokacin auren ka gyara sabon gidanka dake G.R.A,
kafin zuwan wannan ranar kada na sake ganinka a gidan nan balle inda Halisa take, a
wannan karan ka tsallake umarnina zaka sha mamakins, zaka san waye ni" tunda Abba
Hakimi yake magana Yaa Sheikh yake kallon shi, a ran shi ya ce "Tab, ka kashe
Aliyu" a zahiri kuma ɗauke kai ya yi gefe guda, Ummul sai a lokacin ta ɗago kai ta
kalli Abba Hakimi. Yaya Halima kuma ta ce
"Wanne lokaci aka sanya bikin to?" Ya ce "Zuwa lokacin da zata rabu da abin da yake
tare da ita lafiya" duk suka kalli Abba Hakimi cikin kamala Ummul ta ce
"Abba a dai yi haƙuri, wata tara da yawa, ina laifin ta haihu a gidanta? hakan
kamar zaifi nutsuwa" ya kalleta ya ce "Ummul-khairy ko dai baki bar mana Aliyu
bane?" Ta yi saurin cewa "Halak malak ɗan kune ba nawa ba, kayi haƙuri" ya jinjina
kai
Mai martaba ya ce "Bari na shigar Maganar na bada haƙuri madadin Yaa Sheikh, ayi
masa afuwa a saka sati uku Allah ya nuna mana lokacin" Mother ta ce "Allah ya ja da
ran Mai martaba godiya muke" Abba Hakimi sam ba haka yaso ba amma ya ɗauki niyyar
da satin uku sai Yaa Sheikh yaji jiki. Mother ta ji daɗi sosai, zata ribaci satin
ukun wajan gyara Halisa ta zama cikakkiyar mace, mai ƴanci a wajan mijinta, zata
saka ayi mata haɗin na musamman daga wajan A'isha Aliyu Garkuwa.
Za taiwa Halisa huɗubar da zata saka ta ja Yaa Sheikh a ƙasa, wanda zata kaishi
bayyana dukkan abin da yake ran shi. Abba Hakimi ya juya ya kalli Alhaji Farouk ya
ce "kawo yanzu kun san abin da ya faru da yarinyar wajanku, ba sai an sake
maimaitawa ba" cike da tarin kunya da kuma tsananin ladama akan ɗaukaka ilimin boko
fiye da komai ya ce
"Na sani, muna ƙara bada haƙuri akan wannan babban kuskure da wawta da ta aikata a
gareku, shi kuma Engineer Aliyu court zata rabamu da shi, ya amshi ɗan shi ya haɗa
da sauran yaran shi" Mother ta wani irin murmushi ta ce "Ɗan shege ba zai samu
gurbi zaman cikin yarana ba, balle a cikin zuƙatan su, kuje can dai kusan yadda ku
kai" Mimi ta juya ta kalli Mother ta ce "Maryam ai dole ace da mijin iya baba, dole
a kira kishiyar uwa da sunan Umma, kamar yadda za a kira Muhammad da sunan Muhammad
Aliyu" Mother ta ce "Amma akwai bambanci tsakani halak da haram kin sani, tazarar
dake tsakanin sama da ƙasa mai girma ce, sai ki gane kiwa kan ki hisabi" Mimi ta ce
"Kema ki sanya a ranki ba a sauyawa tuwo suna, haɗa Muhammad da yaranki ya zama
dole" Mother zata sake magana Abba Hakimi ya daka mata tsawa cikin faɗa ya ce
"Maryam bana son shirme, wai me ya sa mata basa raina abin magana ne?" Yaya Halima
ta ce "Barrister kada ki sake magana" wani abu mai ɗaci ya tsayawa Mother, Dr
A'isha ta haɗe fuska tana jifan Mimi da harara ta ce "Amma yaya Halima kin san abin
akwai ciwo, a dinga haɗa maka nagartattun yara dana shege?" Da hannu Abba Hakimi ya
nunawa Dr A'isha hanya ya ce
"Fita waje Aishatul-humaira" ta miƙe rai ɓace tare da yin waje abinta. Yaa Sheikh
ya gyara zama bayan ya ɗan kalli kowa ya sauke ajjiyar zuciya, kamar wanda aka
tilasta yin magana ya ce.
"Taci gaba da riƙe Muhammad, har zuwa shekarun da Ubangiji ya ƙayyade uba ya amshi
ɗan shi, idan Allah ya kawo mata mijin aure kuma ta kan iya dawo da shi wajan
Muhammad,amma kuskure ne ɗorawa yaron da bashi da laifi hukunci, ba shi ya zaɓi
haka ba, da ɗa da dukiya Ubangiji kaɗai ya san mai morarsu" Umma A'isha da yaya
Halima suka haɗa baki wajan faɗin
"Haka ne, Ubangiji ya datar damu" suka amsa da "Amin" Zahrah ta kasa jurewa ta ce.
"Ka ce idan na samu mijin aure, mijin aure na jima da samu gashi nan a gabana, don
Allah Yaa Sheikh ka tausaya mini kada ka cutar da zuciyar dake son ka, ko baka so
na zan zauna da kai har ƙarshen rayuwa" ya ɗauke kai yana ƙoƙarin tashi tayi saurin
riƙe ƙafar shi ta ce
"Ka dubi girman Allah, koda hakan zai zama taimakon ka na ƙarshe, ko zai zama
jahadi" ya ƙara ɗauke kai dan ya san ba zai iya abin da take so ba sam, ta sake shi
da sauri da rarrafe ta ƙarasa wajan Ummul ta riƙe ƙafarta ta ce
"Ke kaɗai zai ji maganar ki, ki taimaki ni Ummul don darajar Annabin harama" Ummul
ta girgiza kai tana murmushi ta ce "Wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login