Showing 174001 words to 177000 words out of 196133 words
ya zazzago"Halisa ta
kai da su Uncle Haroon, Maimoon ta gaida Halisa. Kana Yaa Sheikh ya shiga mota tare
da yin key bakinsa ɗauke da tasbihi ya nufi hanyar zuwa wajan Ummul, yana fita
motar Umar-khan na shigowa daga wajan aiki bankin Yaa Sheikh. Driving yake a nutse
duk da bai wani saba da tuƙan na shi ba, amma ba zai jure ana driving matansa ba.
Halisa ta juya ta kalle shi ta ce
"Kayi haƙuri Habibi ƙalbi"
Ya saka hannu ya kamo nata tare da ɗora a fuskarsa, bai ce komai ba. Ta ce "Ina da
kishi bana son ko wacce ta raɓeka Habibi, amma banwa kai na adalci na amince da
ƙaddara ko zan mutu don kishi kada ka damu, ina neman alfarma ka bawa Zahrah ƴan
cinta na Matarka"
Ya sauke numfashi cikin nutsuwa ya ce
"Allhamdulillah" ta kalle shi tana jan gemu ta ce "For?" Ya sha corner ya ce "Zawja
tayi hankali" tayi kicin-kicin da fuska tana zame hannunta ta ce "Oh da mahaukaciya
ka aura" Ya juya ya kalleta sai kawai ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba.
Gatekeeper ya buɗe masa gate ya dinga zubawa Yaa Sheikh addu'a neman zama lafiya.
Ya shafa Aljanu sai bai ji kuɗi ba, ya amshi jakar hannunta ya buɗe ya ɗakko kuɗi
ya bashi. Jakar ya bata ta ce "Kai Habibi ka riƙe mini mana" yana riƙe hannunta
zuwa cikin gidan ya ce "Ba mijin novels bane ni"
A kusan tare muryarsu ta ratsa parlourn dattijo ya amsa shi da Hajia halisa ta
gaishe su ta ce
"Wannan tsofaffin kamar tattabaru kullum kuna tare" Dattijo ya ce
"Matar Malam gidanku" tayi dariya. Yaa Sheikh ya miƙe tare da nufar part ɗin Ummul,
ya yi sallama ta amsa tare da bashi izini tsaye ya sameta gaban wardrobe tana gyara
clothes ɗin ta, ya nufeta ta rungume shi sbd baya girma a Idanunta. *Yaa Sheikh
Aliyu haydar Aliyu* baya jin kan nashi matsayin babba a gareta.
Ya tsuguna ya gaidata ya nemi waje ya zauna, kallon da yake tayi mata ne ya sanya
ta lura akwai wani abu ta ce
"Arɗona ya akai?" A taushashe ya ce "Ki bani labarin Abbi" tayi shiru sai kuma ta
zauna ta ce
"Na faɗa maka, me kake son ji kuma" Ya kalleta ba tare daya amsa ba ta ce.
"Mahaifinka samun kamar shi za a jima, kamar yadda kake cewa Matarka *IDAN BA KE*
ba zan iya rayuwa ba, haka yake duban cikin idanuna ya ce "Ummul-khairy kina da
haƙuri, Ubangiji ya biya ki, *IDAN BA KE* zan yi rashin wani sashe daga cikin
rayuwata" tayi shiru alamar tana jin zafin abin sosai amma ta jure ta ce
"Bayan kasancewar shi Arɗon Rugar Bello, shi ɗin ma'abocin shiga jeji ne, har aka
yi rashin sa a ya faɗa gidan tururuwa, tunda daga wannan lokacin yake jinya sosai,
ya fara gane-gane amma bai faɗa mini ba, daga ƙarshe ko yana gida sai ace an ganshi
waje kaza, na share duk ban damu ba, ashe a faɗawa gidan tururuwa da ya yi, ya samu
matsala Aljanu suka ratsa jikinsa wanda lokacin daya yana iya fahimta ko jin abinda
ba ko zai ji ba, idan na damu sai ya ce meye ne ƴar matana akwai wanda zai maye
gurbinki gareni, yana nan zaki samu, wani lokacin cikin dare zai ta shi ya fita
jeji babu jimawa sai ya dawo, da safe na sake gani ya dawo mutum biyu kenan, sai ya
ce kada na wani damu, mahaifinka har magunguna yake bayarwa ya ɓoye wata laya acan
Rugar Bello ya ce kada a taɓa fito da ita sai lokacin da wani jininsa ya ɓukaci jin
wani abu daga cikin rayuwarsa" ta goge hawayen idanunta ta ce "Magana ta Gasky ban
taɓa ganin mutum kamar mahaifinka ba, nagartar shi ta kai, yana da zafi ƙwarai amma
yana da sauƙin kai baya ɗaukan duniya ta zafi, idan na kalleka sai naji kawai shi
nake gani baka ɗauki komai nawa ba, baka ari wani abu daga wajena ba amma babu
abinda ka bari na Mahaifinka everything"
Ya saka hannu ya goge mata hawayen idanunta ya ce "Allah ya yi masa rahama, ina son
Abbi kamar yadda nake son Ummul" ta ja hancinsa ta ce "ina tunanin lokaci zuwa
Rugar Bello ya yi a fito da layar a duba mene cikinta" Kafin ya yi magana suka ji
muryar Halisa Ummul ta ce "Shigo" tana shigowa ta juya zata fita ganin uwa da ɗana
zaune saman gado Yaa Sheikh sai narkewa Ummul yake. Ummul ta miƙe ta ce
"A'a dawo mana ni tashi zan yi" Halisa ta ce
"A'a daman kawai yunwa nake ji" Ummul ta kalli Yaa Sheikh ta ce
"Bata ci abinci ba kuka taho?" Yaa Sheikh ya kwanta gadon Ummul yana sauke numfashi
ya ce "Ita take cinye abincin gidan fa, ni da Fatymerh bamu da ci" Halisa ta haɗe
fuska taƙi cewa komai sbd ganin idanun Ummul, ta ce "Shige ya danna miki wannan
ƙafar bari na kawo abinci" ta fita ita kuma ta shigo bedroom ɗin tana zama ya jawo
ƙafar ya dinga danna mata, idan ya kalli ƙafar sai ya kalli fuskarta shi kaɗai ya
saki murmushi ta ce "Wai Habibi me ka kewa dariya" ya ce "Kalli hancin ki Zawja
kamar fanke, Asstagafirullah" ta ɗauki pillow ta cilla masa ya cafe ta ƙara ɗaukan
wani ta cilla masa sai kawai ta fashe da kuka ta ce "To waye ya jawo mini idan ba
kai ba" ya rungumeta bakiɗaya ya ce "Sorry zo nayi miki waƙa".... Misalin 9 na dare
ya shiga sakkowa daga kan upstairs ya nufi part ɗin Zahrah yi mata sai da safe, ya
sameta kwance Idanunta yana kallon gefe ɗaya wayarta can nesa da ita, Ya yi sallama
ta amsa a hankali tana tashi zaune ya jima tsaye yana kallonta kafin ya zauna kusa
da ita cikin taushin murya ya ce "Lafiya"
Tayi murmushi kanta ƙasa ta ce "Ya Ummul? jikin Halisa su Abba Hakimi" ya tsora
mata idanu yana son gano meke damunta, ganin yaƙi magana ta ce
"Nayi abinci ban sani ba ko zaku iya ci" nan ma bai magana ba sai can ya ce "Ina ki
ka iya?" Ta ce "Nayi searching by Google" ya jinjina kai ya ce "Come" Ta kalle shi
ta ce "Halisa" bai magana ba ya saka hannu ya jawota jikinsa ya rungometa, a
tsakanin nan ya lura Zahrah nada haƙuri, kuna da alama haƙurinta shi ne zai
taimaketa Allah baya taɓa mutum da mugwayen abubuwa dole ya baka wani abu wanda za
ai misali da shi, tabbas tana da haƙuri ya kuma ji tausayinta Halisa kuma zafi
gareta ta iya masifa amma tana da saurin yafiya. Ya ƙara rungometa jin ta sauke
numfashi a kunnenta ya ce "Fatymerh Zahrah" tayi murmushi sai taga bata damu ta
neman komai wajansa ba, a karo na farko wani abu mai kama da SO ya gilma a
zuciyarsa game da ita ɗin. Ya ɗago kanta duk ta rame amma tana da kyau sosai itama
babu zato taji ya ce...
[2/10, 1:34 PM] Abk: *_Arewabooks@Nimcyluv75_*
Ransa ya ji ya ɓaci for no reason ya sauketa daga jikinsa yana miƙewa tsaye
hannunsa zube cikin aljihu, slowly ya sauke numfashi trying to control his anger,
cikin nutsuwar nan tasa mai jan hankalin mutane gare shi ya shafa kai a hankali ya
ce.
"Da kin huta, munci abinci" tayi murmushi ta ce "To babu damuwa sai a zubar, daman
ba lallai ku iya ci ba" bai kalleta ba ya nufi waje yana faɗin.
"Ba kyau albazaranci, ki fito da abinci za a bayar" kai tsaye ya buɗe ƙofa ya yi
waje, not too long ya dawo ya sameta a parlour hannunta riƙe da warmer ta miƙa masa
ya amsa tare da sake fita, ta na nan tsaye ya ƙara dawowa ya saka key ya rufe
gidan.
Tayi ta kallonsa jin kamar idanu na yawo a kansa, gently ya juya yana zuba mata
idanunsa da yake rufewa sbd tsananin gajiya da son yaji ya samu kansa cikin hutu ko
ya yi barci ishasshe. "Need something?" Ta yi ƙasa da kai sbd kwarjinin da ya yi
mata, yau ɗin sai ta ganshi yafi kullum cikar zati ta ce
"Karatun? Ina nufin wankan da kai magana" ya ƙarasa kamar zai tsaya inda take sai
ya dubeta da kyau cikin kulawa ya ce "Zuwa safe, ki kula"
"Okey good night sweetheart" tayi part ɗinta, shi kuma ya yi addu'a ya shiga tofawa
a ko wanne lungu na parlourn, kafin ya kashe hasken ɗakin.
Direct wajanta ya nufa, tun tuni zuciya da gangar jikinsa ke jansa zuwa gare ta,
ƙofar a buɗe take ya buɗe bata parlour ya shige bedroom bakinsa ɗauke da sallama
cikin sanyin murya.
"Wasalamu Alaika Yaa Sheikh" ta faɗa tana miƙewa da ƙyar frm head to toe yake binta
da kallo. "Me ciki"
Ya faɗa cikin sigar wasa ta ɓata fuska ta ce "Ai dai daga wannan Shikenan, matarka
ta haifa maka" Ya saka hannu ya ɗagata yana murmushi ba sosai ba ya ɗorata a gadon
ya ce "Lallai yarinya"
Ta ce "Abba"
Ya kalleta bai amsa ba ta ce "Me ya sa ka ke son ce mini yarinyar bayan kasan yanzu
nima uwa zan zama"
Sunna ne zama da matarka kayi hira koda baka da ra'ayi ko baka da surutu hakan yasa
ya ce "A sbd ke yarinyar ce" ta ɓata fuska sosai ganin haka ya lumshe idanunsa ta
ce "Tashi ni yau na yafe kowa ya kwana a bedroom ɗin shi, wlh takura ni ka ke Abba"
Ya maƙale kafaɗa yana shafa sumar kansa tare da kwanciya saman cinyar ta ya ce
"Ni ba inda zani kawai ki barni ina nan, ina gadinki da killata kuma sannan, na
baki kula idan akwai buƙata kenan" ta saki baki jin babban malami kamar Yaa Sheikh
yana zage yana rera mata waƙa kafin ta ce komai ya riƙe kumatunta yana girgizawa ya
ce
"Ko na tafi sai na dawo, sadakin ki sai na kawo zuciya ya nai mini zillo....," Ta
tuntsire da dry sosai ta ce "Wow What a nice voice, Habibi kafi mawaƙin murya mai
daɗi" bai kulata ba ta ce "Daman ka iya waƙa? Malami guda?" A taƙaice ya ce
"Malami Sahabi ne? Ba gashi kin yi dry ba"
"Don Allah sake mini kaji." Ya miƙe zaune ya ɗauki ƙafarta ya ɗora saman cinyarsa
ya shiga danna mata, yana tsananin jin tausayin mace mai ciki, bare Ƴar fillonsa
kuma gudan jininsa.
"Tab Yaa Sheikh da waƙa!" Ya kame kansa da kyau ya ce "Ki kula, kada a barbaɗi baki
mara saiti"
"An gama jarumin, gwarzona mijina aljannata kuma ubana duniyata, I love you so much
Modibbona" ya girgiza kai kawai. Ta ƙara cewa
"Ina son ka" yaji kalmar har ƙasan zuciyar shi, tsigar jikinsa ta tashi wani abu na
fisgar shi musamman da cikin Jikinta ya ƙara sanyawa ta dawo kamar ba ita ba,
jikinsa ya saki ya yi baya ya kwanta itama ta kwanta tana ɗora kanta a ƙirjinsa ta
danne masa ƙafa da ƙafarta ta ce "Yau ba darasi ne?" A hankali ya ce "Ayu ki ka
maidani?" Taja hancinsa ta ce "Kawai na san ɗan Ummul da zalama akan darasin auren,
baka da haƙuri" neman magana take da abinda za a fara yi masa surutu akai har ya yi
shiru sai ya ce
"To nace ki huta yau" Ta ce "Ni kuma ina buƙatar ka yau ɗin nan yanzu ma" Mamakin
ƴar rainonsa ya gama cika shi ba ko wacce mace ke tarar mijinta kai tsaye ta ce
tana buƙatar shi ba, sbd jan aji da iyayi irin na mata, bayan aure zama ne na
dindindin, a koda yaushe miji yana cewa yana buƙatar matarsa rana ɗaya zaki iya
warewa ki nemasa koda shi ɗin bai nema ba, hakan zai sanya ya ƙara jin son matarsa
ƙwarai da gaske a ran shi.
"Baki jin kunya?" Tayi fari da fararen idanunta ta ce "Mene abin kunya, kai da ka
ke nema kunya kaji? Kullum kazo da ƴar murya, sai ni zanji nauyi? Kenan na cutar da
kai na ko bayan kai mijina ne ni kuma matarka ce" ya fahimci dai shi ɗin take
buƙata, daman shima tausayinta ya keji nan da nan ya farke rigar barci tare da
cilli da ita, wannan lokacin Halisa ta nunawa *Yana Sheikh* Abbanta ita ma macace
ta san kan duniya, ta shayar da shi mamaki yana riƙe kansa amma sai da taso sashi
yin abin kunya da zarar yaji bakinsa ya buɗe zai ce "Yasubuhanallah Allahu Akbar".
Bayan komai ya daidaita ya rungumeta ya ce "Allah ya yi miki Albarka".
Da Subhi kusan tare suka tashi ya yi alwala ya sanya Arabian jallabiya da farar
hula kansa, abin mamaki yana zuwa ya samu Zahrah zaune saman ladduma tana kallon
sama, suna haɗa idanu ya jinjina mata kai tare da rufe ƙofar ya nufi masjid.
Misalin 11:00 Zahrah ta fito kusan a tare kuma suka fito da Halisa wacce take jera
breakfast a dining room, suka kalli juna Halisa ta ɗauke tana faɗin "Ina kwana?"
"Lafiya lou" ta faɗa tana murmushi ta ƙara da cewa "Sannu da aiki, ya jikin naki da
kin kira na tayaki aiki ai" Halisa ta ce "Don my me, zan iya" ƙamshin turaren shi
ya bayyanar musu da sakkowar shi, Suka juya kusan a tare wani irin kallon ya kewa
Halisa da sauri ya ɗauke kai yana gyara zaman alkyabbar shi, Halisa ta daure bata
je gare shi ta rungume shi kamar yadda ta saba ba, duk da cewa girkin ta ne amma
babu daɗin yin haka gaban Zahrah.
Ya ja kujera tare da zama Zahrah ta ce "Ina kwana?" Ya yi mmki domin bata taɓa
gaida shi ba bisa ra'ayin kanta. Ya jinjina mata kai Halisa ta zuba masa breakfast
kana ta zubawa kanta, Zahrah ma babu kunya taja plast ta haɗa tea. Shiru wajan ya
ɗauka Yaa Sheikh yana lura da yadda Halisa ke gumi sbd azabar yaji, ya dubi abinda
ta ke ji ganin bai san mene ba, ya saka hannu ya ƙwace plate ɗin ya tura mata
soyayyan ƙosan daya sha kayan ƙamshi da tea mai kauri wanda bai ƙarasa sha ba. Ta
ce "Nifa shi na keso" Ya ware gajiyayyun Idanunsa akanta ba tare da ya ce komai ba,
ta fahimci shirun nasa ta ce "Ɗan silif ne wallahi daɗi sosai Habibi" ya ajjiye
bottle water yana goge bakinsa da tissue ya miƙe yana faɗin.
"Duk an gama zuba yawo ciki" kamar jira take ta ce "Wata rana sai na ɗore maka
yawon cikin baki" Zahrah duk sai ta zama uncountable kamar wata maid, sosai taji
yadda suke wasa da dariyar kamar wa da ƙanwa sun birgeta, she wishes ace ita Yaa
Sheikh ya kewa haka. Ta goge Hawayen daya zubu mata a ɓoye.
Can ya zauna saman kujera ya ce "Jeki Library ki ɗakko ƙawa'idi guda uku" ta ce
"To" tana barin wajan ya ce "Fatymerh Zahrah" ta amsa da "Na'am" da hannu ya ce ta
zo. Ta miƙe ta dawo wajansa ya kama hannunta ya ce "Kina lafiya?" Ta amsa da
"Allahamdulillah" ya jinjina kai yana riƙe da hannunta har Halisa ta dawo, sosai ta
gani amma bata nuna ba ta koma gefensa ta zauna suka sanya shi tsakiya, ya buɗewa
Zahrah babin da zai musu, yasan Halisa ta sani amma baya son nuna bambanci itama ya
amsa ya buɗe mata. Cikin sanyi da taushin murya ya ce.
*Babin raɓewa wanka*
Ya yi shiru, cikin nutsuwa ya shiga bayanin kamar yadda ya yi wa Halisa lokacin da
suke garin Makkah!. Ya ɗora da faɗin.
"Akwai wakan jinin haila, Janaba na jima'i, wankan jinin biƙi, wankan juma'a,
wankan shiga garin Makkah, wankan mutuwa, shi ne rabe-raben wanka" sukai shiru baki
ɗaya musamman Zahrah ya ɗora da faɗin.
"Janaba: Janaba ɗaya ce daga cikin abubuwan da suke wajabta wanka, wanda yake
hanyoyin kasantuwa da janaba sune kamar haka; *Fitar Mani* Idan maniyyi ya fita
daga mace ko namiji to wanka ya wajaba, amma kafin wankan ya wajaba sai ya zama
maniyyin ya fitane ta hanyar jin daɗi, kamar kallo ko wasa ko tabe-tabe ko
jingina.., amma idan ya fita ba ta hanyar jin daɗi ba ya fitane ta hanyar wahala,
kamar ya taka wuta ko harbin kunama ko kuma wutar lantarki ta ja shi, to wannan
wanka bai wajaba a kan shi ba sai da kawai ya yi alwala. Shi wannan fitar maniyyi
da ake Magana akan shi ko dai ya fita a farke ko kuma ya fita ana barci, idan ya
fita ana farke shine ake maganar an ji dadi ko ba'a ji ba, amma idan ya fita ana
barci ne to ba wata maganar jin dadi wanka ya wajaba"
Yanayin yadda yake bayanin kaɗai ya isa ka fahimci magana bata dame shi ba, shi ya
sa gabaɗaya ko wa'azin shi za'a tura mutum ake jinsa muryarsa mai sanyi ce cikin
haiba ya ce
"Na biyu, saduwa da iyali idan har an tabbatar miji da mata sun zama turmi da
taɓarya babu shakka wanka ya wajabta a gare su, inma namijin ya fitar da maniyyi ko
mai fitar ma haka ma macen, idan mutum sai sadu da Iyali sau goma to wanka ɗaya ne
ba goma ba.Idan mutum ya sadu da mace kuma yake so ya jinkirta wankan janaba zuwa
an jima to abinda zai yi shine ya yi tsarki sai ya yi alwala, domin alwalar tana
rage kaifin janaba, sannan kuma tana kara kuzari lokacin da ake so aƙara saduwar.
Idan mutum ya sadu da mace sai bai fitar da maniyyi ba wanka ya wajaba akanshi
kamar yadda bayani ya gabata, to bayan ya yi wankan sai kuma ya ga maniyyi ya zubo,
to anan idan wata sabuwar sha'awace ta fitar da wannan maniyyin wani wankan ya kama
shi, amma idan janabar da ya yi wa wankace maniyyinta ya zo yanzu to alwala kawai
zai yi" Ya rufe littafin yana amsar ruwan da Zahrah ta miƙa masa ya sha kaɗan ya
ajjiye ya ce. "Mu tsaya nan, sai gobe In shaa Allah, kafin nan ga yadda ake wanka"
Suka kalle shi ya kame fuska ya ce
"Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai siffatul ijza' (ta
wadatar), kuma wacce
ake kira siffatu
kamal' (ta kamala). Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi
ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da
zaka fara yi shi ne: zaka karkato bakin
mazubin ruwanka, ka
wanke hannunka sau
uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka ɗebo ka wanke gaban ka, a dai-
dai lokacin da
zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko
waninsa) wanda yake
wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana
kayi tsarki kenan to
daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a
alwala ta sallah zakayi sai abu ɗaya shi ne wanke
ƙafafuwa to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shi ba, to daga nan sai ka tsoma
hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka ɗebo ruwa ba
sai ka murmurza kanka saboda ko wanne gashi da
ya buɗe a lokacin da
maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya
koma yanda yake, don
gashin dan Adam yakan buɗe musammam
gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani
abu daban, bayan haka sai ka ɗebi ruwa a cikin