Showing 39001 words to 42000 words out of 196133 words
maid ɗin ta ce "Yes Maaah, how can I help you?" Surry ta ya motsa
fuska tana kallon maid ɗin ta ce "Ina buƙatar, Abaya's, perpumes, body spray, body
lotion, shower gel, everything na mace masu kyau na ƴar 17yrs ki haɗu ki kawo mini
yanzu" Maid ɗin ta rusuna ta ce "Insha Allah Maaah, enjoy your time" ta juya da
nufin tafiya Surry ta ce "hiii nace ba" Maid ta ce "Yes" Surry ta miƙe tsaye tana
ƙare wa wajan kallo ta ce "Ki tabbatar body lotion ɗin sai sauya fata cikin kwana
biyu" Maid ɗin tai murmushi cikin hausar ta ta ce "kada ki damu kinji" kaya masu
mahaukacin kyau aka haɗawa Surry ga tsada ka cika aiki, komai na babban company aka
zaɓo, ta biya kuɗi aka loda mata kayan aleda daga mall ɗin Specialist Yola ta nufa,
tana zuwa ta samu Danejo zaune a gaban room ɗin da aka kwantar da Dada, ta miƙe
tsaye fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Sannu da hanya Adda" Surry ta haɗe rai ta ce
"Ba nace bana son Addar nan ba, kice Anty" tai ƙasa da kanta tana wasa da hannu "Ya
na ganku a nan?" Danejo taƙi cewa komai sai Shatu da ta ce "Ana duba Dada ne" ta
jinjina kai tare da neman wajan zama, sai duba lokaci take tasan anytime Zahrah
zata iya nemanta sbd shirye-shiryen zuwa event anjima. Likitocin suka fito Danejo
na ganin haka ta shiga room da sauri Shatu ta mara mata baya, Surry tabi bayansu A
zaune ta samu Dada cikin ranta ta ce "Wow, ashe Halisa gado tayi" Kyakkyawa ce
sosai Dada ajin ƙarshe, ta faɗaɗa fuska idanunta akan Surry wacce ke mata sannu
cikin sanyin muryar ta ce "Allahamdulillah, ke ɗaya yau?" Surry ta ce "Wallahi,
hanya ta biyo dani bama sai an faɗa mata nazo ba, anjima likita zai sallame ki"
Dada ta ƙara sakin murmushi ta ce "To ba damuwa, Allah ya saka muku da alkairi,
Halisa ta faɗa mini aiki sai dai ban gane ba" Surry tai murmushi ta ce "Oh! Daman
ƙawata zatai aure shi ne za a ɗauke ta aiki sbd mun yaba da hankalinta, kuma duk
shekara ko wata za a dinga biyan ta kuɗin aikin, kuma sa a sakata a makaranta akan
wannan sharaɗin da tace zata cika muka kawo ki asibitin" da sauri Danejo ta kalli
Surry domin tasan ba haka akai ba, bakinta na rawa kasancewar bata barin magana a
ciki ta buɗe baki ta ce "Lalashewa ta sameki Anty Aradu ƙarya ne ba haka akai ba,
shewa sukai zan..." cikin sauri Surry ta tare Danejo da faɗin "wannan daban ne
kinji ƙanwata Halisa, zo kiga kayan da na siyo miki" tai shiru tana ware idanunta
itafa haka kurum ba za a dinga rainata mata hankali ba. Surry ta buɗe ƙatuwar
shopping bag ɗin ta shiga zaro dugwayen riguna kala-kala, masu kyau da tsari.
"Wannan kayan duk na mene?" Cewar Dada domin ganin kayan ya sanya kanta sarawa ta
rufe idanu da sauri. Surayyerh ta ce "Kaya ne, na kawowa ƙanwata Halisa ta fara
amfani da su kafin mu tafi da ita" Dada ta kasa cewa komai domin tana ganin tafiya
da Halisa wani wajan ba ƙaramin babban ƙibi bane a rayuwarta, kuma ba zata jure
kalar rayuwar da suke ba, Halisa tana da saurin baki bata da haƙuri wani lokacin
kana yi mata take maka zafin rai gareta. Surry ta ce "Anjima Dr zai zo, zuwa anjima
ko da safe zamu zo mu tafi da Halisa ɗin, akwai wani Sani mai p.o.s a wajan shi
zaki dinga karɓar kuɗin aikin Halisa na duk shekara, zan baki number waya koda kina
buƙatar jin muryar yarinyar ki sai ki bawa mai p.o.s ɗin ya kira, gaba ɗaya aikin
shekara biyu zatai...." Da sauri jikin Danejo na rawa ta ce "Wallahi ba inda zani,
ba zan biko ba taimakon da ku kaiwa Dadata Allah ya saka ni dai ba zani ba daman
wayo nayi muku dan ku kai Dadata asibitin burni...
Pay before you read.... IDAN BA KE it's paid book 500. Via 6850917335 Na'ima
Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.... Don Allah kada a
fitar😒😂.
SARAUTAR MARUBUTA
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Subuhanallah yi haƙuri bata kula ba" Surry ta faɗa da sauri
tana kama hannun Halisa ba tare data bari ta buɗe liƙab ɗin ba. Ita dai Halisa
kallon Yaa Sheikh take kamar idanunta zai faɗo ta cikin liƙab ɗin.
Yaa Sheikh ya ratsa ta gefen Halisa zai shige tayi saurin shan gabansa tana kwace
hannunta, duk da ta tsorata da yanayin shi amma bai hanata ƙara binsa da idanu ba
da ƙarfi ta ce.
"Laa Wallahi shi ne, Balarabe ashe zan sake ganinka?" Dam! Zuciyar Surry ta buga,
Umar-khan zai magana Abba Hakimi ya girgiza masa kawai alamar yai shiru.
A wannan karan ba Yaa Sheikh bai kalli yarinyar dake gabansa ba, sai ƙara ɗauke
idanu yake gefe guda, ganin yadda ya yi mata ya sanya Halisa ta saka hannu ta cire
liƙab ɗin tare da matsawa gaban Yaa Sheikh ta ce "Baka gane ni ba? Nasan ka gane ni
ni ce fa Halisa Danejo Rome ka manta ni?
Ina kaje bana ganinka?" Tarin makami da ya yiwa Saif-wazir yawa ya sanya ya
hangame baki, anya yarinyar nan ba aljana bace ko kuma wacce Aljanu suka shafa?.
Khalil Ahmad Sarki ya juya da sauri ya kalli El-bashir dake can gefe ɗaya yana
waya, ya ƙara juyawa ya kalli Halisa wacce ɗan ƙaramin bakinta ke motsawa tana yiwa
Yaa Sheikh rantsuwar Wallahi ya gane ta yana sani yaƙi kulata. Ahmad Sarki da har
yanzu yake kallon Danejo sai ya juya ya kalli El-bashir makami kamannin su na
rikita masa lissafi musamman da yaji muryar Danejo wacce take iri ɗaya data El-
bashir sak! Sai dai ita ɗin macace saɓanin El-bashir da yake namiji. "The wonder
never ends" Khalil ya furta a fili na dafe kansa.
Danejo ta ce "Yanzu baka gane ni ba, nice fa? har ka taɓa bani mangoro?" Yaa Sheikh
ya ware fararen idanunsa sosai tare da sauke ganinsa akan zagayayyiyar fuskar ta,
kai tsaye ƙwayar idanunsa ta shiga cikin nata. Danejo ta haɗiye sauran maganar sbd
idanun Yaa Sheikh da sukai mata kaifi, a kallo ɗaya da ya yi mata ya saka mata
shakkar shi, tsoro da kuma ganin girman shi. A hankali ya zame hannun yana mai
barin wajan Danejo ta bisa da idanu..
"Kin san shi ne?" Danejo ta kalli Saif-wazir kamar zatai magana sai kuma ta murguɗa
masa baki Surry ta kama hannun ta suka shige cikin gidan su Zahrah.
Saif yai dariya son ran shi ya ce "Akwai rigima Yaa Sheikh za ai raino" Khalil
Ahmad Sarki ya daki kafaɗar Saif ya ce.
"I couldn't understand, wai wace yarinyar nan? Na ruɗe fa" Saif ya ce "wato abinne
gaba ɗaya is complicated, muje mu zauna" Ya juya zuwa ga Abba Hakimi wanda ke
sauraran su ya ce "Abba ita ce ƴar fillon da nake baka labari"
Abba Hakimi ya jinjina kai cikin nutsuwa ya ce "Ikon Allah ya kamata mu zauna,
Umar-khan maza kira mini Barrister Maryam a waya" Umar-khan ya ce "To Abba" Abba
Hakimi ya yi gaba Saif-wazir ya bi bayan shi, Umar-khan ya tsaya kiran Mother a
waya.
Khalil Ahmad Sarki ya nufi inda El-bashir yake tsaye ya zuba hannun shi cikin
aljihun wandon shi ɗaya hannun yana shafa sumar kansa.
"Kaga abin da na gani kowa El-bashir?" El-bashir ya juya zuwa ga yayan nashi kamar
ba zai magana ba sai kuma ya ce "A'a duk an cika waje da ihu me zan gani haba kun
zama kamar wasu mata" Khalil ya ce "let's keep a joke a side wata na gani mai mugun
kama da kai" El-bashir ya nuna kansa yana fiddo idanu waje ya ce "Ni kaga me kama
dani?" El-bashir ya tambaya yana gyara tsaiwar shi. Khalil Ahmad Sarki ya ce "Ai
kamannin har sun ɓaci hatta beauty point da gashin girarka daya rabe biyu, hatta
muryarku iri ɗaya ne El-bashir na girgiza" a karo na farko El-bashir ya yi
murmushi kawai yana girgiza kansa ba tare da ya ce komai ba, hakan ya fusata Khalil
ya ce "Ya ina magana akan abu mai muhimmaci kana dariya?" El-bashir ya jingina
jikin mota baka iya gane yanayin shi ya ce "Me zance Abu Juwairah? Kawai kun haɗu
da aljana banda haka ina za a samu wata mai kama dani? ni ba ƙanwa ba ni ba ƴa ba,
Please mu bar wannan maganar" Khalil zai magana wayarsa ta shiga ringing ganin
matarsa ce Oum Juwairah ya sanya yabar wajan yana amsa sallamar ta.
Tunda suka shiga ɗakin Danejo bata kalli inda Zahrah ke zaune ba, kanta a ƙasa ta
haɗe fuska sosai. Zahrah gabanta ya faɗi ganin yadda cikin kwana biyu Halisa Danejo
ta sauya kamar ba ƴar fillo ba, fatar ta na ƙyalli ko'ina na jikin fes yake duguwar
rigar da Surry ta bata ta saka mai purple ta amshi jikinta sosai.
Surry ta ce "kina ta kallon ƴar fillo kamar baki san taba lokaci na shigewa" Zahrah
ta sauke numfashi ta ce "Kada dai ki mata matsayin mai aikatau zaki cikin gudana
ƴar fillo" Danejo ta ɗago kai ta kalli Zahrah cikin sautin siririyar muryar ta ta
ce "Ban manta ba, sunana Halisa Danejo Rome ba ƴar fillo ba" Zahrah taja tsaki ta
ce "Ji banza ina cewa a cikin ruga muka ɗakko ki? Banda warin shanu dana Kindirmo
me kike? Har kece za kice wai ke ba ƴar fillo bace?" Danejo ta shiga kallon Zahrah
zuciyarta na jin zafin maganganun data faɗa mata idanunta har ya cika da ruwan
hawaye saboda ba zata iya mayarwa da Zahrah magana ba bisa umarnin Dadarta.
Surry taja gefe guda tana murmushi jin daɗi ba tare da kowa ya lura ba, ita kanta
baza taso tun yanzu Halisa ta fara mayarwa da Zahrah magana ba. Cikin sauri ta ce
"Zahrah dama shiryawa ki kai yanzu 1:30 ance 2:00 daidai jirgi zai tashi" Zahrah ta
miƙe ta ce "Ina son haɗuwa da Deen wlh kwana biyu bana iya barci Surayyerh abin
cikina masifa yasa mini ba zan iya jurewa ba idan ban samu abin da nake ba dole
naje naga Deen" a fili Surry ta ce.
"Wallahi baki da tunani Zahrah ganin Deen a halin yanzu bai dace ba kuma nasan abin
da zaku aikata" a zuciyarta kuma ta ce "Well-done Zahrah ban fatan ki daina bibiyar
maza tun yanzu" Zahrah ta ɗauki hijabi tare da juyawa ta kalli Surry ta ce "Meye
sunan abin da kika bawa yarinyar nan ta saka bani" Surry ta amshi liƙab ɗin hannun
Danejo wacce ta haɗe rai sosai taƙi yarda ta ƙara kallon inda Zahrah take.
Cikin sauri ta gama shiryawa babu mai cewa Zahrah ce ta nufi ƙofar baya akan nan da
20 minutes zata dawo.
Tana fita Surry ta kalli Halisa ta ce "Kina ji ƙanwata, Kinga wannan mutumin da
kika ganu har kika ruɗe kina cewa Balarabe?" Halisa dai kallon Surry take kafin
Surry ta ce "To shi ne mijin Zahrah, ina so ki nutsu ki fahimta Kinga daga can kano
Madina zaku shige, kina wanka sau biyu ko sau uku a rana, haka ma brush da saka
kaya masu kyau...." Ta ci-gaba da faɗa mata komai na yadda zata gyara jikinta da
tsafta ta ɗora da faɗin "Kin fara Al'ada ne?" Danejo ta girgiza kai. Surry ta ce
"stop raising your head, magana zaki" ta ce "Ni ban san wani Al'ada ba" Surry ta
zare ido sai ba tace komai ba, ta shiga lodar kayan shafawa ta sakawa cikin jakar
Halisa tare da faɗin.
"Kada ki kuskura ta gani ko da wasa, idan ta gani ma ki san me za kice kar ki
ambaci sunana"
Abba Hakimi ganin maganar mai muhimmanci ce ya tattara ya barta zuwa lokacin da za
su koma gida ayi a gaban kowa, duk family su san matsayin yarinyar.
Yaa Sheikh yana kwance saman gadon hotel ɗin da suka sauka idanunsa rufe kamar mai
tunani daga shi sai farar Jallabiya ko barcin ya kasa, har lokacin bai bawa auren
muhimmanci ba, balle ya sakawa ran shi nauyi wata ƴar mace ya hau kan shi, iya
auren daya san da gaske an ɗaura kuma matarsa ce bisa tsarin addinin Musulunci, na
ƴar fillo kam yama mance da shi at all baya tunanin shi.
Ya miƙe a hankali zuwa bathroom tare da sakarwa kansa shower ya jima kafin ya fito
ɗaure da bathrobe a jikinsa, cikin sauri ya shirya cikin wani kyakkyawar Voyel mai
manyan zane maroon colour ya ɗora farar Alkyabba ya wani irin sahihin kyau kamar
Prince Hamdan bin Mohammed.
Ya fito cikin parlourn ɗakin ƙamshin Roja ya cika ko'ina a wajan wanda ya jawo
hankalin Khalil dake waya da Oum Juwairah ya ɗago kai bai san lokacin da ya ce
"Masha Allah" duk rashin tsaurin idon mutum ba zai iya tsayawa gaban Yaa Sheikh ya
yi ba, Ilhamar da Ubangiji ya bashi ta musamman ce, a kallo ɗaya yake dagula
lissafin mutum. Yaa Sheikh da jikinsa ya bashi kallon shi ake ya ɗago kai suka haɗa
idanu da Khalil ya kafe shi da ido alamar lafiya? Wannan kallon fa? Khalil ya shafa
kai sbd Kunya ya ce "Muje ko?" Yaa Sheikh yana gaba Khalil na bayan shi, cikin
nutsuwa yake tafiya har suka ƙarasu wani room a ƙofar room ɗin suka ci karo da wani
saurayi rungome da mace wacce take rusa masa kuka kamar ranta zai fita. Yaa Sheikh
ya ɗauke ido da sauri a ransa ya ce "Asstagafirullah Yaa Allah" Khalil kuma ya taɓe
baki a haka suka fitar zuwa reception na hotel ɗin daidai nan kuma Mai martaba da
abokin nasa El-bashir suka fito suma, haka Abba Hakimi da nasa abokan Umar-khan,
Ishaq-Hakim, Saif-wazir. Father daman yana can ba Alhj Farouk mahaifin amarya.
Jirginsu Yaa Sheikh daban na Amarya da ƴan uwanta da suka yanki tickets daban.
A airport suka haɗu baki ɗaya har lokacin Zahrah bata taho ba, Danejo tunda
idanunta ya sauka akan jirgi ta gigice tsoro ya kamata.
Yaa Sheikh da Abba Hakimi da kuma Mai martaba Ahmad Sarki tare da Father duk suna
Vip. Sauran kuma suna nrml waje. Jirginsu ne ya fara tashi babu jimawa Zahrah ta
ƙarasu wajan ta sha kwalliya cikin wata lafaya mai kyau da tsada. Tofa kallon ya
dawo kan Danejo ta rantse da abin da zai kashe ta ba zata shiga jirgin ba kuka
sosai. Wasu nayi mata dry. Da ƙyar Surry ta lallaɓata gudun abin da zai je ya dawo
ta zauna kusa da ita.
Danejo ta ƙanƙame jikinta wanda yake rawa hawaye na zubuwa daga cikin idanunta ta
ce "Na lalashe Dadata na kaɗe, na bushe shikenan zai a shige sama dani" Surry ta ce
"ki nutsu Halisa babu abin da zai sameki kinji ko?" Ita dai kuka take when the
plane will take off numfashinta ya tsaya cak Surry ta shiga girgizata tana amsar
ruwa tare da yayyafa mata da ƙyar ta dawo daidai ta fara yunƙurin amai yaƙi zuba,
lokaci guda ta fita hayyacinta jirgin yana wullawa sama ta fara wata uwar ƙara tana
faɗin "Na mutu, Wallahi na mutu.."
Misalin 4:45 manyan motocin da suka ɗakko dangin amarya daga airport suka shiga
parking a harabar gidan Mother. Wasu ƴan uwan Zahrah da yayar mahaifiyarta da
ƙanwar mahaifiyarta sune suka kamo Zahrah da aka rufe mata fuska zuwa cikin gidan
sauran friends suka bi bayansu. A parlour akai musu masauƙi su gaisa da dangin miji
kafin a basu masauki. Jadda dake zaune ta ce "Wai ina matar Gadangar ne sai wasu
yamutsastsun fuskoki nake gani?" Ladidi ta ce "Gata nan Zahrah buɗe fuskarki ai
miki bayanin dangin miji" Mother dai na zaune hankalinta na can waje guda sai kaɗa
ƙafa take.
Dr A'isha ma na zaune taci uban kwalliya kana ganinta kasan ba talauci inda take,
Yaya Halima ma haka, sai Momi tare da ƴan uwan father, da matar Uncle Haroon.
"A meye haka? Alsulhu khair buɗe fuskar uban kowa ya gani"
"Ai Hajiya kin san amare da kunya" Jadda ta ce "kaji masifa ko? Waye sa dake wace
ke? daga gidan wa zuwa ina?" Ladidi tai shiru amma Jadda ta fara ƙular da ita.
"Muhammadur Rasulullah s.a.w wannan ai uwa aka aura Aliyu ba mata ba? Gidan ubawa
Aliyu zai kai ɗirkekiyyar matar nan ni kai na ta kusa haifata yau na shiga uku da
gaske wannan ce matar Malam ɗin?" Jadda ta faɗa bayan ta saka hannu ta buɗe fuskar
Zahrah. Surry na gefe tana danne dariyar dake ranta.
"Maryam zo kiga abin al'ajabi yoo Allah na tuba ko ke ai kinfi matar malam kyan
gani? Allah sarki Gadanga an haɗaka da uwar mata" sai kuma ta fashe da kuka sosai
ta ce "Innalillahi ashe har gashin doki take saka zunubi babba" ta saka hannu ta
kama hannun Zahrah ta ce "Wanne tsinannen abu ne wannan kuma?" Ta faɗa tana duba
farcen hannun Zahrah.
"Haba Hajiya wannan abun duk na mene? Ya daga kawo yarinyar sai cin mutunci?" Jadda
ta miƙe ta nufi kan me maganar ta dungure mata kai ta ce "Algunguma ai duk duniya
an gama cutar Malam an haɗa shi da arniyya" "Arniyya wacce ira kuma Hajiya?" Ladidi
ta faɗa rai ɓace. Jadda ta kunce ɗan kwalin kanta tare dacin ɗamara ta ce "Arniyya
ƙatuwa ma, mene bambancin su? ga tafkeken zunubi ba tausayi ba komai aka cirewa
doki gashin shi aka saka mata, gata narkekiyya mai idanu a tsakar kai, gashi ta
wani ɗashe kamar mace mai shigar sabon ciki Innalillahi masifa ta saukarwa Malam"
gaban Zahrah ya faɗi tai saurin rufe fuskarta.
Dr A'isha ta fashe da dry wacce tun ɗazo take danne ta. Yaya Halima girgiza kai
kawai take kafin ta ce "Kuyi haƙuri don Allah muke ga masauƙi can" Mother
hankalinta na kan Danejo wacce take ɗan ɗaga liƙab ɗin fuskarta tana leƙewa da sun
haɗa idanu da mother sai ta mayar ta rufe.
Babu wanda Jadda bata ciwa mutumcin ba kafin su bar wajan. Mamaki ya kama Ladidi
ganin uwar mijin ta Zahrah ci kanku ba ta ce ba. Kwanan su biyu suka koma Yola aka
bar Zahrah tare da Halisa.
Yaa Sheikh ne durƙushe a gaban Abba Hakimi da Uncle Haroon sai Uncle Bashir ga
Mother da Yaya Halima da kuma Momi matar Abba Hakimi. "Ina magana kayi shiru
Aliyu?" Abba Hakimi ya faɗa cikin sassauta murya. Yaa Sheikh ya ɗago kan idanunsa
ya sauka akan yarinyar da ake nuna masa, ya ƙara duban Halisa da kyau sai yanzu yai
mata cikakken kalo ya mai da idanunsa kan Abba Hakimi ya ce.
"Wace? kamar ban waye ta ba?" Uncle Haroon yai murmushi yana jinjina halin Yaa
Sheikh. Abba Hakimi ya ce "Amma kasan Rugar Bello? Ka kuma san Arɗon rugar ka gane
abin ya faru,ka kuma shaida zoben hannunta?" Yaa Sheikh ya ɗan kallin kyakkyawan
hannun Danejo wanda yake maƙale da zoben da yake so har ransa nan take ransa ya
ɓaci, a lokacin ya tuna everything ya shanye mmkin kamannin da yake gani a fuskar
yarinyar, shi kam a rayuwa ko zai so mace ai banda ƴar cikinsa wannan gwaliliyyar
yarinyar bata shige raino ba, ita za a kalla ace wai matarsa? Shi kam ya zai yi da
mata biyu ba?. Yai shiru yaƙi bada damar da za a karanci halin da zuciyarsa ke
ciki. Uncle Bashir ya ce "Da alama ya fahimta"