Showing 27001 words to 30000 words out of 196133 words
Dada wacce ke sanƙame bata san meke faruwa ba
sbd halin da take ciki. Bata taɓa ganin anyi kisan kai a gabanta ba, yaushe gashi
an kashe mata yaya wanda ke kula dasu shi kaɗai ya rage musu. Halisa Danejo Rome ta
shiga halin firgici ita kaɗai tai ta razana har lokacin idanunta bai motsa daka kan
gawar Hamma Yabi ba a haka Asuba ta risketa. Sarkin ruga da Giɗaɗo ne suka shigo
bukkarsu Danejo ba neman iso domin basu damu da cewa Dada matar da za a nemi aminci
a wajen ta bace. "Allahu Akbar Allahu ya jiƙan Yabi shai abu bai kyau ba sam"
Sarkin ruga ya girgiza kai ya ce "Allah sharki aradu harbi har biyu dole ya mutu"
da sauri Danejo ta miƙe jikinta na rawa ta kama hannun Giɗaɗo ta ce "Da gaske Hamma
Yabi mutuwa ya yi? Da gaske ba zan sake ganin Hamma ba?" Ta faɗa cikin rauwanin
muryar kana ganinta kasan damuwa ta jima da kama zuciyarta ta samu waje ta zauna.
"Ya mutu mana kamar yadda Baffanku ya mutu ba zai dawo ba" ƙurr ta kafe Giɗaɗo da
idanu kafin taja numfashi mai tsayi sai kuma ta sulale a wajan ta faɗi babu
numfashi.
A hankali take buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi, hannunta ta kai tare da dafa
kanta wanda yake mata ciwo sbd barcin data daɗe ta nayi. "Sannu kin farka Danejo?"
Shatu ta furta cikin murnar ganin Danejon na motsi bayan suman da tayi. Danejo ta
juya tana kallon Shatu kafin a hankali ta buɗe baki ta ce "Ina Hamma Yabi? Ya tafi
da Dada asibitin burni?" Shatu tayi saurin faɗin "Hamma Yabi ya mutu ai kuma har an
rufe shi a ƙasa" zuciyar Danejo ta buga da ƙarfi tana runtse idanunta sosai tsoro
da fargabar makamar rayuwarsu ta dirar mata a zuciya, yaya za tayi da Dada? Ina
zata samu kuɗin asibiti ko shanu zata siyar? Mai Hamma Yabi ya yiwa wannan mutunan
da shi kaɗai kawai suka kashe cikin Rugar Rome?.
Juyawa tayi ta sake kallon Dada wacce kawo yanzu ko motsi ba tayi ruwa ma idan aka
bata ta gefen baki yake zubewa, hawayen da take maƙalewa suka sakko daga cikin
idanunta Shatu wacce ke shirin yin kuka ta ce "Kuka ki ke Danejo? Me akai miki ba
ga Dada ba muna tare da ita?" Danejo ta goge idanunta da kyau ta ce "Ba kuka nake
ba, ki zauna wajan Dada bari naje wajan sarkin ruga na dawo" miƙewa tayi jikinta
sanye da fararen kaya na Fulani sumar kanta ta naɗeta da wani zare mai ɗauke da
kuran duwatsu masu kyau. Kanta a ƙasa take tafiya cikin sanyin jiki kamar ko yaushe
a haka ta ƙarasa bukkar su Sarkin ruga ta tsaya daga waje tana neman iso. Matar
Sarkin ruga ta ce "A'a Danejo ne bismillah shigo" kamar ba zata shiga ba sai kuma
ta shiga ta samu Sarkin ruga zaune yana shan kindirmo a diririce ta ce.
"Jamɓanduna. _Ina kwana_" Ya ce "Jamni.. _lafiya_" zata sake yi masa wata gaisuwar
ya dakatar da ita da faɗin "mene ya kawo ki?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta
ce. "daman cewa nayi ko zaka sayi nagge guda biyar daga cikin garkenmu?" Kallon
tsaf ya yi mata yana sakin murmushi kafin ya ce.
"Yabi bai faɗa miki ɗan cewa gaba ɗaya ba naggenku bane? Kiwo kawai aka baku?"
Cikin rashin fahimtar maganar Sarkin ruga Danejo ta ɗaga kanta da sauri ta kalle
shi tana faɗin "Dada ta sanar mini gaba ɗaya garken na Baffanmu ne, shanuwan sa ne,
kuma kowa ya sani Hamma Yabi ma yasan da haka" Ya ce "E, to buɗe kunne kiji kaf
cikin garken naggen nan guda biyu ne naku, sauran duk mallakina ne kuma yanzu zan
ɗauka aje kasuwar burni a siyar dasu, idan kina buƙata sai a haɗa da guda biyun
naku a siyar daga nan sai ku biyawa Baffan naku bashin da ake binsa ma" kasa cewa
komai tayi ganin ƙarfen ƙafa da ake shirin yi musu, wanne irin son zuciya ne
Wannan? A nagge sama da hamsin ace guda biyu ne nasu? Me ya sa Hamma Yabi bai taɓa
cewa naggen Sarkin ruga bane? Da gaske nasa ɗin ne ko ba haka bane?. Jiki a saɓule
ta dawo gida zazzaɓi na rufeta sbd fargaba. Kenan tana ji tana gani Dada zata sake
mutuwa ta barsu basu da kowa a duniya?.
Sheikh Aliyu haydar Aliyu na zaune yana duba yadda ginin bankunan guda biyu suka
ɗauki harami cikin ƙaramin lokaci tare da kamfanin sarrafa shinkafa. A nutse cikin
kulawa da haibarsa kamar kullum ya miƙawa Umar-khan Album ɗin. "Ina fatan komai ya
yi yadda kake so?" Kallo ɗaya Sheikh ya yi wa Umar-khan a hankali ya juya kansa
yana mai jinjina shi a nutse alamar "Ya yi" Umar-khan yai murmushi kaɗan yana
jinjina halin Sheikh da yawan lokaci ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita.
Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai miƙe ƙafafuwan shi saman table a
hankali ya fara tunanin yadda zai gina rayuwar shi wanda zai sanya father farin
ciki duk ƙoƙarin shi na gano abin da ke sanya father yaji zafin shi har haka ya
rasa, da yawan lokaci abubuwan na damun shi nunawa ne kawai ba ya yi. Zuciyar shi
na shiga tunani na tsayin lokaci. Miƙewa ya yi cikin kulawa ya shiga takawa a
parlourn na shi, ƙarar wayar shi ta dakatar da shi daga tunanin da yake jin
ringtone ɗin is different ya sanya ya fahimci mai kiran na shi. Farar Alkyabbar shi
mai fidda ƙamshin Roja ya ɗauka tare da ɗorawa saman jallabiyar jikinsa banda dole
ko hannun shi bai son a gani sbd tsarin halittar jikin na shi. Kansa a ƙasa ya nufi
Main parlour babu kowa sai Hajjir bai ko kalle ta ba ya nufi sashin Abba Hakimi. A
zaune ya same shi saman ladduma gabansa ɗauke da kayan marmari sai ƙwaryar zuba da
kuma ta fura da nono. Zama ya yi yana fuskantar Abban na shi cikin mutunci bakin na
motsa wa alamar gaisuwa Abba Hakimi ya yi murmushi ya ce. "Ba sai kace ba,
Allhamdulillah" Sheikh Aliyu a lumshe idanunsa yana mamakin yadda Abba Hakimi ke
fahimtar zuciyarshi da yawan lokuta.
"Naga baka shirin auren naka, kamar dai you're not ready if i not mistaken?" Sheikh
ya buɗe idanu da kyau akan Abba Hakimi cikin mantuwa domin gaba ɗaya ya manta da
batun komai cikin In-ina yana riƙe Alkyabbar dake jikinsa da kyau tare da karkatar
da kansa yana rufe idanu ya ce. "A...a...au au aure kuma A a Abba?" "E, Aure mana
Sheikh haka za ka yi ta zama babu aure ni ma da kaina ban goyi bayan hakan ba, kayi
aure kamar yadda Engineer ya buƙata ko dan samun kusanci da shi" Sheikh zai magana
Abba Hakimi ya ƙara ɗaga masa hannu ya ce.
"Kada kai musu, ka amince Allah ya sanya albarka, Engineer ya buƙata ka tura kuɗin
lefin ita yarinyar tun da ba auren kake so ba, yi maka za ayi na fanshe ka na bada
kuɗin lefen kamar yadda suka ce 2.5m zai isa komai na lefen" Sheikh ya ware idanu
jin wai 2.5m kuɗin lefen yarinyar da ko sanin kamarta bai ba,baya buƙatar kuma ya
sani ɗin.
Cikin kyakkyawan lafazi Sheikh ya sake furta "2.. 2.. 2.5m A aaaa Abba yai yai yawa
fa?" Abba Hakimi ya girgiza kansa yana mmkin yadda Sheikh babu abin da ya sani dan
gane da rayuwar mace.
"Meke sani Sheikh Aliyu? Kasan kayan mata da tsada, ko kai Alkyabbar nawa kake
siya? Duk Alkyabbar ka tafi nawa kuɗi sosai, kuma a arziƙin da Ubangiji ya yi maka
dan an taɓa 2.5m har wani abu ne?" Shafa gemunsa zuwa sajansa kawai Sheikh ya yi
bai damu da auren ba, amma yaji daɗin yadda Abba Hakimi ke nuna kulawarsa ga duk
abin da ya shafe shi.
Abba Hakimi bai nunawa Sheikh ya san komai ga Bankunan da yake shirin buɗewa ba,
dan haka sai ya ce "Ka tashi kaje can gidan, kuɗi kuma daman hakƙina ne na aurar da
kai daga nan har sadaki" jin Sheikh yaƙi cewa komai ya sanya Abba Hakimi ɗago kansa
ganin Sheikh ɗin ya yi zaune jingine jikin kujera ya dafe kansa da hannu bibbiyu
zufa na yanko masa tsakanin gashinsa jikinsa na rawa kaɗan kaɗan.
Girgiza kai kawai Abba Hakimi ya yi tare da jawo rubutun da ya yi da safe ya
tsiyaya a cup ya zuba zuma a ciki ya juya kaɗan tare da ajjiyeta gefe guda zuwa
lokacin da Sheikh ɗin zai daidai a hankali shi kuma yaci gaba da duba wani littafin
Tafsir.
Mother na zaune tana girgiza ƙafa cikin damuwa take kallon tilin kayan lefen dake
parlourn, da sunan kayan lefen yarinyar da Sheikh zai aura. Yaya Halima ta ce.
"Na daɗe banga kayan lefe mai yawan haka ba, shi Sheikh ɗin har nawa ya bada?"
Motar ba ta ce komai ba sai Dr A'isha data kalli kayan da kyau ta ce. "Kalli fa
Yaya iya gold guda biyar ne, Wallahi sai na ɗaukar wa su Maimoon kowa ɗaya abar
shegiya da ɗaya kawai" Mother ta kalli Dr A'isha ta ce. "Tsinke na kayan nan babu
mai ajjiye mini cikin gidan nan, balle su Maimoon su saka ba su rasa komai ba, a
barwa wacce aka siyawa". Dr A'isha ta ce "Amma Barrister kalli kayan fa? Ni dai sai
na ɗauka dukiya ai ba hauka bane" cikin faɗa Mother ta ce "Wai meke damunki haka
A'isha akwai abin da kika rasa ne balle kayan nan su dameki idan su kike let me
know I'll buy it for you" a sanyaye Dr A'isha ta cewa yayat tata "Am sorry Yaya"...
"Sai haƙuri Barrister" cewar Yaya Halima wacce take babba a cikinsu. Miƙewa kawai
Mother tai tana faɗin "Idan ban yi haƙuri ba kashe kai na zan? Ina nan dai wlh sai
na aurawa Sheikh wata macan ya haɗa mata biyu" Dr A'isha ta ce "Wai ya kaga Sheikh
da mata biyu" Dr A'isha ta kalli Yaya Halima ta ce "Nifa ina da shawara Yaya
Halima, mai zai hana mu kai kayan lefen nan da kanmu zamu ƙara ganin ita Zahran da
ake faɗa sai mu ganu tarbiyyar ta" Yaya Halima ta ce "Gulma zamu kenan? Maza ke
kaiwa a bari su kai kawai?" Dr A'isha ta ce "Please mana Yaya Please" da ƙyar Yaya
Halima ta amince ta ce zata nemi Engineer domin tasan yadda Mother ta ɗauki
Al'amarin ba lallai tai magana ba.
Da daddare duk suna zaune a parlour Mother, Yaya Halima, Dr A'isha dasu Maimoon da
auta Fattoumah. Motar Sheikh tai parking a gidan da gudu Fattoumah ta miƙe yana
faɗin "Yaa Lee Mother ta Yaa Lee nan" murmushin jin daɗi Mother ta yi ba tare da ta
ce komai ba. A hankali ya fito da ƙafafuwansa waje kasancewar shi kaɗai ne da kansa
ya yi driving hakan ya sanya gajiya ta saukar masa, yana fitowa Fattoumah na zuwa
wajansa da gudu ta ce "Wlcm Yaa Lee" lumshe idanunsa ya yi tare da buɗewa, ganinta
ƙarama kuma autarsu ya sanya ya sassauta fuskarsa tare da sunkuyawa ya ɗauke ta da
hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya rufe motar. Gemunsa taja ta ce "Yaa Lee ina kake
zuwa muna ta missing naka" ya ware idanu bai ce komai ba sai hancinta da yaja
kaɗan.
Da idanu suka bisa yana sanye da shadda ruwan madara babbar riga da jamper bai saka
hula ba sai hirami daya rufe kansa da shi fuskar shi mai ɗauke sanje zuwa gemu ta
bayyana ta cikin hiramin daya gewaye fuskar. Ƙamshin Roja tuni ya mamaye parlourn
da ƙamshi, Maimoon da Zeefa duk suka miƙe tsaye suna sakin murmushi a tare suka ce
"Sannu da zuwa Yaa Lee" bai kalle su ba ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga
Fattoumah dake masa surutu, bayan ya zauna saman kujera ya daidaita nutsuwarsa da
kyau cikin ƙasa da murya ya ce. "Barka" ya faɗa kai tsaye ba tare da In-ina ba, Dr
A'isha da Yaya Halima suka kalli juna. "Dani ka ke ko Yaya Halima?" Bai kula Dr
A'isha ba ko kallonta bai ba domin yasan nemen magana ce. Tai dry ta ce "Ka gama
kame fuska duk girmata da kayi dole ace da mijin iya baba, ko yanzu goma ta faɗi
tafi biyar albarka dole na amsa sunan uwa a gare ka" miƙewa yai da Fattoumah ganin
Dr A'isha na neman fasa masa kai da surutu. Kai tsaye Upstairs ya nufa ɓangaren
father domin amsa kira. Yaya Halima tabi bayan shi da kallo ta ce "Sannu Dr da
tsaurin ido, lallai karanki ya kai tsako Sheikh kike faɗawa haka? Sai da Barrister
Maryam ta yi aure ta haifi Sheikh da shekaru huɗu ba aka haifeki?" Dr A'isha tai
dry ta ce "Wallahi yaya ƙarfin hali ne kawai, amma ba ƙaramin kwarjini ya yi mini
ba, gashi ko inuwata bata samu albarkar kallo balle Ni" dry gaba ɗaya sukai. a
zaune Sheikh ya samu Father hannunsa riƙe da jarida idan kaga Sheikh da Father ba
zaka taɓa cewa Sheikh ne ɗa ba, domin yafi cika idanu da jiki tsayi faɗi uwa uba
fuskar Sheikh data samu sumar ƙwarai ta ƙara fidda asalin shi. A kan carpet ya
zauna yana sauke numfashi kansa a ƙasa bakinsa na rawar gaida Father ya yi saurin
ɗaga masa hannu ya ce. "Bani da lokacin jin faa kakkkkka yayyyya, na kiraka domin
ka shirya zuwa Yola wajan Zahrah kafin akai lefe jibi, umarni na baka Aliyu ba
shawararka nake nema ba" Jinjina kai kawai Sheikh ya yi bai ce komai ba. "Tashi
kaje idan ka zauna ba zaka amfane ni da komai ba, zan bawa Saif-wazir address ɗin"
miƙewa tsaye Sheikh ya yi sai da yaje bakin ƙofa Father ya ce "Ka kwana a nan, ban
amince ka koma gidan Hakimi ba daga nan har ɗaurin aure" Sheikh ya juya da sauri ya
kalli Father wato ya fahimci duk abin da yake masa baya damunsa shi yasa ya sanya
Abbansa cikin al'amarin. Juyawa ya yi kamar yadda ya ce ya nufi Part ɗin nasa yana
tattare babbar rigarsa.
Washegari tunda ya yi sallar asuba bai koma ba, sbd wani irin mafarki da ya yi,
abin ya tsaya masa yana son neman fassarar mafarkin wajan Abba Hakimi amma ya kasa,
baya son mafarkin ya dangancin wani jinsi wanda ba nashi ba. Ƙarfe 7 daidai ya
shirya cikin Milk ɗin shadda gezner bai saka babbar riga ba, sai golden ɗin
Alkyabba daya sanya ya ɗora golden ɗin hirami, da ƙyar ya yi breakfast ɗin da
Mother ta kawo masa shi ma sai da ta zauna ya gama jan ajinsa yaci kana ta fita
ganin ko ƙala bai ce mata ba. Yana gamawa shirya wa Saif-wazir ya jashi zuwa garin
Yola da taimakon Map. Sai da sukai nisa sosai sun ma bar Commission Quarter's ɗin
sun nufi wani waje kamar daga Sama Saif-wazir yaji Sheikh yai gyaran murya kaɗan
alamar ya tsaya. Waje ya nema ya yi parking gurin kamar jeji kamar ƙauye kuma.
Cikin nutsuwa ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa, a hankali ya fara bin
wata hanya hannunsa goye a bayansa. Sai da ya yi nisa sosai kana yaja ya tsaya.
Kwance ya ganta kanta kife a ƙasa jini na zuba kaɗan a goshinta sai ƙwaryar
kindirmon dake gefe guda hannunta guda riƙe da cikinta, da sauri ya zame idanunsa
daga gare ta sbd kansa da yaji ya sara yana ƙoƙarin barin wajan wasu ƴan Fulani
riƙe da Sanduna suka gewaye shi ɗaya ya ce "Aradu mun kama masu fyaɗen yara" Sheikh
ya ware idanu amma bai nuna komai ba, wani ya ce "Wannan kamar kidnama waye kai?"
nan ma shiru ya yi bai ce komai ba, Labo da yafi su iskanci ya kalli inda take
kwance ganin jini a kanta ya ce "Aradu fyaɗe ya yi mata, kuma tunda kayi mata fyaɗe
dole doka ta hau kanka" Sheikh trying to explain amma harshe ya sarƙe. "Kai ku
saurara" Saif-wazir wanda hankalinsa bai kwanta da yadda Sheikh yabar motar ba, ya
faɗa yana nufu wajan. Ƴan Fulanin suka tsaya ya kalle su sosai ya ce "Kuna hauka
wanne irin fyaɗe mai yasa baku da tunani ne, yayi muku kama da wanda zai aikata
haka?" Labo ya ce "Alkur'an sai na raɗeka da wannan sandan, ga jini nan muna gani
ya kwantar da ita, dole kawai ya amshi hukunci" Saif-wazir ya ce "Wanne irin
hukunci kuma?" Labo ya ce "Kai maza kira mana Giɗaɗo" abu kamar wasa kafin kace
wani abu kusan gaba ɗaya ƴan Fulanin Rugar Bello suka zagaye Sheikh. Giɗaɗo ya
kalli Sheikh kana ya kalli Labo ya ce "Zaro mana zoben hannunsa daka gani mai
tsaida ne" Labo ya kama hannun SHEIKH tare da zare zoben, kusan mutuwar tsaye
Sheikh ya yi yama rasa me zai ce, sai gumi dake yanko masa ya shigo ne domin
tsinkar wani ganyen magani kalli yadda tsautsayi ya rutsa da shi. Kamar daga sama
yaji Giɗaɗo na faɗin "Allhamdulillah mun riƙe wannan zoben matsayin sadaki" Saif-
wazir ya ce "What sadakin me?" Giɗaɗo ya ce "Ai yanzu muka aura Wannan Balaraban
aure da yarinyar nan, ni ne waliyin yarinyar Labo kuma waliyin Balaraban hakan shi
ne hukuncin duk wanda ya yi wa wata fyaɗe a Rugar Bello, yanzu da shi da ita mata
da miji ne halak ɗin sa ce....
Free pages yana gab da ƙare wa biya kuɗin ka domin shiga Paid book tuni sun yi nisa
da karatu😂 .... Biya 500 ta Wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu
Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616. Ƴan nijar sun yi mini magana.
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
_*Nimcyluv sarauta*_
15....
Saif ya ce "Aure kuma? waya ɗaura, dawa kuma?" Sheikh gyara tsaiwa ya yi zufa na
yanko masa ta cikin naman jikinsa,kalmar auren ta gigita masa tunani dama lissafi
baki ɗaya. Labo ya kalli Saif-wazir ya ce "Aradu aure aka ɗaura musu, babu wanda ya
isa ya warware shi sai ikon Rabbi.. kai Giɗaɗo maza jawo mana su cikin Rugar Bello"
cikin gargaɗi Saif-wazir ya nuna Labo da hannu ya ce "Saurara fillo kake kowa, an
faɗa maka aure wasan yara ne? Kuma wanda kake cewa zaka aura masa ita already yana
da aure wajan matar shi ma zamu, don haka babu wani aure idan ma kunyi sai ku
warware auren yanzu nan" Labo ya ɗaga sanda sama gaba ɗaya sauran Fulanin suka ɗaga
sanda sama tare da zagaye su Sheikh "ƙarya kake Aradu ina shemeka na sheme banza
Alqur'anin Allah, aure kuma dole ne hukuncin duk wanda ya yi fyaɗe ko ya nemi
lalata ƴar mutane ke nan, ku shige muje Rugar Bello" Saif-wazir zai magana Sheikh
yaja numfashi da ƙyar yana girgiza masa kai domin sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi
musamman da yake ɓangaren Fulanin suka shigo tsaf za su yi musu gayya. And he
doesn't want that to happen. "But Sheikh....," Sheikh ya ware idanu wanda suke
ɗaukan hankali kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya yi ƙasa da murya kamar wanda
aka ɗauke wa In-inar ya ce. "Saif-wazir" kallon Sheikh kawai Saif-wazir yake cikin
mamaki.
Suna ƙoƙarin tsallake ta su shige Labo ya yi saurin faɗin "Waye zai ɗaukar maka
matar ka? yadda ka kawo ta nan haka zaka ɗauke ta mu ƙara sa