Showing 33001 words to 36000 words out of 196133 words
Abba"
Abba Hakimi ya ce "Mafi mushkila"
Bayan fitar Saif-wazir Momi ta ce "Amma bana ganin wannan auren ya ɗauro fa?" "Me
ya sa A'isha?" Momi ta ce "Naga babu wani na Sheikh a wajan sai Saif" jinjina kai
kawai Abba Hakimi ya yi yana ci-gaba da rubutun shi ta ce "kayi shiru?" Bai kalleta
ba ya ce "Idan kika sake cewa I'll do the same thing, aure ba shaidu da sadaki yake
buƙata ba? Saifuddeen ya ce shaidu wajan 20 a wajan, Zoben da suka amsa kin san
darajar shi kam?, Aure ya ɗauro kamar na ko wanne ma'aurata" Momi tai murmushin jin
daɗi ta ce "To Allah ya sa albarka,ya sanya matar shi ce har aljanna sai a faɗawa
Barrister" nan ma Abba Hakimi ya ce "A'a Maganar ta tsaya iya mu, bana son ko su
Umar-khan da Ishaq-hakim suji, hatta Barrister Maryam da mijin nata bana son suji"
hira sukaci gaba dayi.
Ƙarfe 4:5 daidai Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya fito sanye cikin dark blue ɗin shadda
jamper da babbar riga, sai ƙamshin Roja yake wanda ya a cika parlourn. Ƙafarsa
cikin Leather shoe sumar kansa wacce ya rufe da hirami ta sha Ginger Geminal Oil-
hair daga sajansa zuwa gemu sai kyallin Luxury Beard oil yake. Bakinsa sai ƙamshin
LB Breathe herbal sugar breath freshener spray. Fitowar shi cikin parlourn ya yi
daidai da shigowar Abba Hakimi, Umar-khan da Ishaq-Hakim na binsa a baya. "Daman
yanzu nake shirin zuwa sashin naka sai gaka" zama ya yi Sheikh yana gyara Babbar
rigarsa yau ba saika Alkyabba ba, a nutse cikin kamala murya mai ɗauke da kwarjini
ya buɗe baki ya ce "Barka da yamma Abba" kallon kallo akai tsakanin Umar-khan da
Ishaq-Hakim jin yau Sheikh bai In-ina ba, Abba Hakimi kam murmushi kawai ya yi
hakan bai wani dame shi ba ya ce "Yawwa Sheikh Dadynka Mai martaba ya sauka yanzu
kai suke jira" Sheikh ya duba agogo ya riga yasan sai biyar jirgin zai sauka yana
komai bisa tsari. Bai ce komai ba ya miƙe tsaye Abba Hakimi ya bisa da kallo yana
mmkin sauyawar Sheikh da yawan lokaci kamar mai cin naman wahainiya yanzu zaka
ɗauka yana da yara kusan biyar sbd yana yin kamalar shi, amma fuskarsa bata nuna
shekarunsa ba kullum cikin kame ta yake.
Yana fita aka buɗe masa bayan mota, Umar-khan yaja Ishaq-Hakim da Saif-wazir suka
shiga mota ɗaya sai airport. Zuwansu airport ɗin ya yi daidai da saukar jirgin har
lokacin Sheikh na mota bai fito ba. Khalil Ahmad Sarki ne ya fara ɗakko daga cikin
jirgin sai Mai martaba Ahmad sarki na uku ya shiga ɗakko cikin nutsuwa hannunsu
riƙe da sanda, fari kyakkyawa da shi wanda zai iya yin shekaru wajan 65 da haihuwa.
bayan sakkowar Mai martaba wani saurayi ya shiga sakkowa ganin saurayi ya sanya
hantar cikin Saif-wazir juyawa, nan take kuma ya tuna da abin da idanun shi ke maza
gizau. Zai iya yin shekaru 25 da haihuwa fari kamar mahaifinsa mai martaba har yari
Mai martaba kyau da haske, Three-piece dinner suit a jinkinsa saɓanin Khalil Ahmad
Sarki dake cikin shiga ta sarauta. Gaba ɗaya suka zube tare da gaida Mai martaba
Ahmad Sarki. Khalil nata ware idanun ganin Sheikh can ya leƙa bayan mota ya ganshi
zaune ya rufe idanun shi. "I expected to see you right here" Sheikh ya buɗe idanu
ba tare da ya ce komai ba, cikin tsokana duk da Sheikh ɗin gaba yake da Khalil ya
buɗe masa ƙofa yana faɗin "Ango kasha ƙamshi, Finally the Sheikh will get married,
praise the couple's line" har lokacin dai Sheikh bai kula Khalil ba sai fitowa da
ya yi daga cikin motar a hankali ya ƙarasa Wajan Mai martaba ya ɗan sunkuyar da
kansa Mai martaba ya ce "Yau gani ga Sheikh tunda yaƙi zuwa inda muke" ya lumshe
idanunshi tare da buɗewa ya saki murmushi wanda ya sanya kyansa fitowa sosai.
Sheikh da Mai martaba suka shiga mota ɗaya, Khalil ya shiga bayan motar su Saif-
wazir Mai martaba ya kalli matashin saurayin ɗan na shi ya ce "El-bashir..." Wanda
aka kira da El-bashir ya ware ido murya a sake ya ce "Mai martaba zan zo" yana
faɗin hakan ya juya yana tsayar da mai texsi...
Abu kamar wasa ɗaurin auren Sheikh ya rage saura kwana uku cif. Har lokacin da
Sheikh da El-bashir ba a haɗu ba, Sheikh ba manta da wata Yola baki ɗaya balle
Auren da yake kansa na ƴar fillo. A ranar aka kammala gina Bankunan Sheikh na Lagos
da Abuja, tare kamfanin sarrafa shinkafa an zuba komai da komai ranar buɗewa kawai
ake jiran Sheikh ya saka sai kuma ɗaukan ma'aikata.
Yana kwance a bedroom ɗinsa dake gidan father ya miƙe da sauri kamar wanda aka
tsikara yana sanye da embrodiery Islamic jallabiya a hankali ya shiga duba contact
ɗin wayarsa abin kunya ko number Maimoon bashi da ita, number mother ya kira aka
ɗauka cikin dry akace "Yarona ya akai?" Muryar Dr A'isha ta sanya ya kwaɓe fuska ta
ce "Ya akai? Ya kamata nazo na saka maka albarka" numfashi ya sauwaƙe "Uhm
Maimunatu fa?" Mamakin maganar Sheikh kai tsaye ba In-ina ta cika Dr A'isha da
sauri ta ce "Sorry who am I speaking with?" Kashe wayar ya yi gaba ɗaya. Dr A'isha
ta juya ta ce "Maimoon kije part ɗin Sheikh wani yana kira" "wani kuma Aunty?" Dr
A'isha ta ce "haka dai na fahimta" Maimoon ta miƙe tare da saka hijabi tasan tana
zuwa haka zata ci ƙaniyarta. A parlour ta same shi hannunsa riƙe da Black tea wanda
ya aka saka zuba a ciki. Jikinta duk rawa yake ganin yadda ya tsareta da idanun ya
zame idanunsa ciki rashin tsammani ya ce "Kinga Aljani ne?" T ɗaga idanu da sauri
ta kalle shi ta ce "A'a Yaa Lee kayi haƙuri" ya share zan can tana da zaune sai da
ya gama shan tea ɗin son ran shi can ya ce "ki nemi number yarinyar nan" sai kuma
ya yi shiru ta miƙe tana faɗin "na fahimta" waje tayi kai tsaye ta nufi upstairs
part ɗin father lokacin ya gama raba Invitation baki ɗaya "Daughter ya akai ne?"
"Father number Anty Zahrah zaka bani mu fara gaisawa kafin tazo" father yaji daɗin
haka sosai ya bata number Zahrah ya ce "Baku fara shirin bikin babban yaya bane?"
Ta ce "Father anjima zamu saloon gobe mai zana henna zata zo tai mana" waje tayi da
sauri ta koma part ɗin Sheikh tare da kai masa number Zahrah.
Zahrah na zaune with her best friends ana musu henna sbd anjima suna da event.
Wayarta tayi ƙarar da sauri ta duba text ɗin data gani ya girgiza mata lissafi ta
miƙe da sauri ta nufi bedroom ɗinta ganin haka ya sanya Surayyerh bin bayanta ta ce
"Wai what's going on Zahrah looks so worried what's up?" Zahrah ta ce "na shiga uku
Surayyerh kinji abin da Sheikh ya ce" Surayyerh ta amshi wayar ta shiga karanta
saƙon Sheikh a fili.
_I agree to marry you, on one condition if you become a good woman like Hurul-in,
idan na sameki a yadda ba zan taɓa a daren zan tsinke igiyar aure ukun nan..._
"Tab ga ƙoshi ga kwanan yunwa, yaya za a yi yanzu?" Zahrah ta ce "Ba wannan ba
Zahrah cikin dake jikina shi ne matsalar, kuma zan iya zuwa ayi mini ɗinki yadda
Sheikh ba zai gane cewa na san namiji ba" Surayyerh ta ce "Ina da shawara kawo
kunne kiji" ta raɗawa Zahrah a kunne Zahrah ta ce "Wow wlh na ɗauka jakar ƙwaƙwalwa
gareki yanzu ta ina zamu fara nema, Kinga dai yanzu kira ya saman urgent" Surayyerh
ta ce "Deen?" "Mtwss kina da matsala tsakani na da Deen sai after married, muje"
shiryawa sukai Surayyerh na driving mota Zahrah na baya har zasu shige cikin Abti
America idanun Zahrah ya sauka akan ƙwaryar Kindirmo nan da na kwaɗayi irin na masu
yaron ciki ya tasu mata cikin sauri ta ce "Stop the car Surayyerh" Surayyerh taƙi
tsayawa da sauri Zahrah taja burkin mota "Innalillahi zaki kashemu Zahrah are you
at of your sense?" Zahrah ta fita da sauri tana zuwa ta ɗauki ƙwaryar kindirmon ya
shiga sha ba tare da tunanin daga ina ya fito ba, sai ta gama sha kwaɗayi ya faɗa
ta kalli ƴar fillon wacce kanta ke ƙasa tana rusa kuka da iya ƙarfinta bata san ma
Zahrah ta zo wajan ba ta ce "ke nawa ne kuɗin ki?" Ta faɗa tana yatsuna fuska,
Halisa Danejo Rome ta kasa magana sai kuka a hankali Zahrah ta ce "ke dallah riƙe
kuɗin ki mtwss" Surayyerh ta ce "Zahrah yarinyar nan kamar zatai daidai da
tsarinmu" Zahrah ta kalli Danejo da kyau sai kuma ta saki murmushi ta ce "Ƴar
ƙanwata lafiya kike kuka?" Danejo ta ɗago kanta idanunta ya yi jajir cikin kuka ta
ce "Dadata ce zata mutu bata da lafiya" Zahrah ta ce "Ayyah ki daina kuka to" ta ce
"To ai mutuwa zatai bani da kowa kuma" Zahrah da Surayyerh sukai murmushi Zahrah ta
ce "Kina son ta samu lafiya kuci gaba da rayuwa da ita?" Danejo ta ɗaga kai da
sauri ta ce "Ina so Aradu ina so" Zahrah ta ce "Good, zan kaita asibitin kuɗi" da
sauri Danejo ta riƙe hannun Zahrah ta ce "Da gaske kike? Hamma Yabi yace zai kaita
asibitin burni shi ne aka kashe sa" Zahrah tai alamar tausaya wa ta ce "Wayyo ni
zan kaita zan kashe kuɗi sosai har ta samu lafiya amma da sharaɗi guda ɗaya idan
kin amince" Danejo tai shiru alamar tunani da sauri ta ce "Wanne sharaɗi" Zahrah ta
ce "Kinga tunda zan taimake ki nima ki taimake ni taimako na rana ɗaya nake buƙata
shi ne madadin alheri da nayi miki" Danejo tai murmushi wanda ya sanya zuciyar
Zahrah bugawa sbd kyan yarinyar ta ce "Na yarda zan miki taimakon Adda" Zahrah tai
murmushi tana ɓoye jin daɗin ta, ta juya suka kalli juna da Surayyerh ta ce "Tom
shikenan idan kina so na kai Dadarki asibiti ta samu lafiya nima ina so ki kwanta
da mijina na rana ɗaya ranar da akai kaini gidansa zai amshi budurcinki a matsayin
nawa....
*Last free pages*
_A nan na kawo ƙarshen free pages mu haɗu a paid group ga wanda suka biya, idan
mutanan da suka biya basu kai 200 ba zan haƙura da sakinsa a whasap na buga shi
zuwa kasuwa, ko kuma na sake shi iya AREWABOOKS.... Bugagge na takarda dubu ɗaya ne
1k... A whasap kuma mutum zai biya 500 (ɗari biyar har a gama labarin)... Ka tura
kuɗin ka ta nan 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank. A tura shaidar
biya ta wannan number 08119237616 ƴan nijar sun yi mini magana._
Sai mun haɗu a paid grp masoya❤🔥❤🔥
❤🔥❤🔥 time al'amarin daban yake salo wanda ban
this
taɓa zuwa da irinsa ba.
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Mijinki zai amshi budurcina a matsayin naki?" Danejo ta sake
maimaita tambayar cikin rashin fahimta kamar taso ta gane budurcin, tun da a
lokutan baya Dada nayi mata faɗa akan ta kame kanta sbd ita ɗin maca ce mai ƙima da
kuma daraja.
"Kinga ba wani abu ne na tashin hankali ba, ki nutsu ok" ta juya kan Surayyerh tana
ɓata fuska ta ce "Please Surry explain to her" Surayyerh ta kalli Danejo tana
sakin murmushi kafin ta ce
"Yama sunanki?" Danejo ta kalli Surry kamar ba zatai magana ba sai kuma ta ɗauke
idanunta zuciyarta na bugawa ta ce. "Halisa Danejo Rome" Surry ta jinjina kai ta ce
"Ok Good, yawwa ƙanwata Kinga duk mun girmeki zaki iya ce mana Anty mai ma kuke
kiran babbar yaya a yaranku?" Danejo ta ce "Adda" ta taɓe baki ta ce "Whatever kice
mana kawai Anty, Kinga ƙawata aure za tayi cikin satin nan, kuma bata da lafiya
sosai shi ya sanya ta nemi taimako akan ki zauna tare da mijinta na rana ɗaya
kawai, rana ɗayanma bai shige awa guda ko 30mnts ba,idan kin amince yanzu sai ta
ɗauki Dadarki zuwa babba asibiti ai mata magani"
Danejo tai shiru saboda har ranta bata gama fahimtar zan can nasu ba, ita tsoro ma
suke bata Wallahi musamman data gansu manya ko wacce da gashin indo anci uban
kitson ƙari. Amma da abin da suke buƙata da rayuwar Dadarta wanne yafi? Wata
zuciyar ta tambayi Danejo, Dada ita ce komai na rayuwarta, farin cikinta, jin
daɗinta. Da ita zata zauna har abada bada su ba. Cikin sauri ta kalli Surry ta ce.
"Kuma yana amsar budurcin nawa zan dawo Rugarmu wajan Dadata?" Baƙin ciki ya cika
zuciyar Zahrah, jin yadda Danejo ke ta nanata kalmar “budurcin” zuciyarta kamar
zatai bindiga sbd tsabar kishin dake damun zuciyar ta. Surayyerh ta kalli
Zahrah,Zahrah ta ɗaga mata kai alamar ta amsa da "Eh" kawai.
"E, da kin kammala aikin naki zamu dawo dake ai ba can zaki zauna ba" Danejo tai
murmushi ta ce "Aikin ba wahala Aradu na yarda nidai" ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya
Zahrah ta sauke na jin daɗin kafin ta ce.
"Shiga mota muje Rugar taku" Danejo tai shiru kada taje kuma masu yanke kai ne,
haka kurum su yanke kan a banza. "Shigo muje mana?" Surry ta faɗa domin tuni Zahrah
ta shiga motar tare da yi mata key. Ƙwaryar nonon ta ɗauka tare da shiga inda Surry
ta nuna mata, ta shiga a tsorace bakinta sai rawa yake na tsoro, a haka Zahrah taja
motar tare dabin direction ɗin da map ke nuna mata har suka isa Rugar Rome.
Da gudu Danejo ta fito tana ƙanƙame ƙwaryar kindirmonta. Surry ce ta fara kallon
rugar Zahrah ta dinga taɓe baki kamar wacce taga makusa domin Rugar Rome abin
sha'awa ce ba ƙazanta cikinta.
"Bari na faɗawa Sarkin ruga anyi baƙi ko?" Da sauri Zahrah ta riƙo Danejo ta ce
"A'a kada ki faɗawa kowa, sbd zasu hana akai Dada asibiti muje kawai" cike da
gamsuwa ta yarda ta nufi bukkarsu, suka bi bayanta. A kwance suka samu Dada
idanunta nayin sama kumfa na fita daga cikin bakinta kamar ko yaushe, Shatu na gefe
tana jijjiga Dada sai ihu take domin jikin Dadar ya yi tsamari fiye da ko wanne
lokaci. Surry ta zaro idanu sosai bata ɗauka ciwon yai girma har haka ba, da sauri
ta ce "Kamata muje Zahrah subuhanallah haka jikin nata ya yi" Danejo na kuka ta ce
"Na shiga uku na lalashe Dadata kada ki mutu ki barni kinji" Zahrah ji take kamar
ta shaƙe Danejo sbd baƙin ciki haɗa jiki da zatai da mijinta nan da bada jimawa ba,
hakan ya sanya taji harta fara tsanar yarinyar. A mota suka saka Dada shatu da
Danejo suna baya kusa da mahaifiyar tasu, a wannan lokacin Surry ke driving motar,
Zahrah na gefe lokaci zuwa lokaci tana kallon Danejo ta madubi anya batai kuskure
ba?.
A Specialist Yola motarsu tai parking nurse's suka fito da gado kai tsaye tare da
saka Dada akai, kasancewar Babban asibiti ne kuma an san Zahrah Farouk cikin
ƙaramin lokaci aka buɗewa Dada file aka fara yi mata medical check up.
Dr ya fito da sauri Surry ta miƙe tsaye ta ce "Dr ake ciki?" Idanunshi akan Zahrah
ya ce "ki saman office" yana faɗin hakan ya shige Office ɗinsa. Surry ta kalli
Zahrah ta ce "Muje Madam" ta tsuna fuska ta ce "No I'll wait here, kije yadda ake
ciki let me know" ta girgiza kai tare da bin likitan zuwa office nasa. Yana zaune
akan kujera ta same shi bayan sun gaida Surry ta ce.
"Dr ya ake ciki ne?" Dr ya sauke numfashi yana zare Glasses ɗin idanunshi ya ce
"Allahamdulillah kun kawota lokacin da ya dace, matar na jin jiki wani ƙari ne ya
fito mata a ciki shi ne ke wahalar da ita" Surry ta ce "Thank God, yanzu mene
mafita zuwa yaushe zata samu lafiya?" Ya gyara zama da kyau yana duba file ya ce
"Zaku biya kuɗin da za ayi mata aiki, a daren yau misalin 10 za a yi aikin, muna da
ƙwararrun likitoci cikin kwana ɗaya biyu komai zai daidai a ɗora ta bisa magani"
cikin jin daɗi Surry ta ce "Dr hakan ya yi, nawa ne kuɗin?" Ya ce "Dubu ɗari biyu
da hamsin ne har magani" ta miƙe tsaye tana ɗaukan waya da hand bag ta ce.
"Ok bari naje na biya kuɗin" tana faɗin hakan ta fito ta samu Zahrah zaune tana
waya, Danejo da Shatu sun rakaɓe waje guda sai zare idanu suke. Danejo ta miƙe da
sauri ta nufi wajan Surry domin tafi fuskar rahama akan Zahrah muryarta na rawa ta
ce "Ina Dadata? Tun ɗazo ban ganta ba ina kukai mini ita?" Zahrah ta ja tsaki Surry
kuma tai murmushi ta ce.
"Haba ƙanwata kin san babu inda zamu kai Dada sai wajan likita,ya ce gobe zata fara
magana ki kwantar da hankalin ki" fararen haƙoranta masu kyau suka bayyana dalilin
murmushi da tayi ta kalli Shatu ta ce "Shatuna Dada zata lafiya, aradu wannan ƴa
ƴan albarka ne dole nayi musu aiki suma" Surry ta girgiza kai ta ce "ku zauna nan
yanzu zamu dawo, kada kuje ko'ina har abinci zamu kawo muku" a tare suka ce "To
Adda"
Surry da Zahrah suka nufi wajan biyan kuɗi, tare da cike komai da komai.
Driving take jifa jifa tana murmushi Zahrah ta gaji ta ce "Wai murmushin me kike
haka Surayyerh ko tausaya mini bakya yi wata zata kwanta da mijina?" Surayyerh ta
girgiza kai tana bin waƙar dezell can ta ce.
"Yarinyar ce abin tausayi bake ba Zahrah" Zahrah ta ce "kamarya? Mijina zai san
wata bani ba" Driving amma bai hanata fashewa da dariya ba sosai tana buga kan
motar
"What funny Zahrah? Serious daneja ko Danejo take ita ce abar tausayi, look how
young she is bana tunanin zata iya ɗaukan al'amarin namiji,and she didn't
understand what we meant".
"And so what kuma? Idan har za a amshi budurcin nata? Look Surayyerh ni bana
tausayin ta yadda na kai tsuhuwar ta asibiti dole ta cika mini nawa aikin"
Surayyerh ta juya kaɗan ta kalli Zahrah ta ce "I don't feel sorry for her
either,kawai Sheikh ba zai iya haɗa jiki da ita a yadda take ba, dole a sauya ta"
Zahrah ta ce "like how wanne sauyi?" Kai tsaye Surry ta ce.
"Ta daina warin da take, ta zama mai tsafta ƙamshin ya zauna mata ki sanya ta nutsu
sosai nutsuwar da shi kansa zai fahimta cewa eh da gaske ke ɗin ce" da ƙarfi Zahrah
ta ce "Tab hauka kenan, Please stop it bana son jin haka.." Surayyerh taja tsaki a
ranta ta ce "mahaukaciya"
Maimoon ce ke zaune tana tura baki Mother ta ce "Oh kina so ace ni na hanaku yin
kwalliya a