Showing 195001 words to 196133 words out of 196133 words

Chapter 66 - IDAN BA KE by Nimcyluv sarauta

09 Jun 2026

110

sosai. Umar-khan da Hafsat a tsayin
shekara shida ɗin nan yaransu biyu, haka Maimoon da Khalil, El-bashir Ahmad Nuran
Sarki da Fattoumah Aliyu ɗan su ɗaya mai sunan mai martaba a yanzu kuma shi ne
Sarkin Sokoto.
Arziƙin Yaa Sheikh ya ninka haka bisa jajircewa da taimako.
*20 year's later*
Gidan cike yake Hala da Rohna sai kuka suke kamar ransu zai fita Hala ta ƙanƙame
mahaifinta tana cewa "Abbi ban so, ban son auren kada a rabani daku na fasa auren"
kuka take sosai Yaa Sheikh yana ƙaunar yarinyar shi ƙwarai komai nata na Halisa ne
shi yasa yake jinta daban a zuciyarsa. Ya rungumeta yana bubbuga bayanta shekarun
shi 60 cif ya zama babba mutum wanda ake kwatance da shi a hankali ya ce "Sorry
Mamana, sorry" ta girgiza kai tana riƙe shi Rohna kuma Halisa ta riƙe tana cewa
"Mami ki ce Abbi kada ya basu mu" school mate ɗinsu sai vedio suke musu haka
photographers abin ya zama wani extraordinary. Mother da Dr A'isha suna kallon ikon
Allah basu taɓa sanin haka Yaa Sheikh yake ƙaunar yaransa ba sai yanzu. Daga gefe
guda aka saki tsaki mai kyau Hakimi ya juya zuwa ga ɗan yaron da ba zai shige 16yrs
ba, baƙi ne shi sosai har sheƙi yake gabaɗaya shi ne ya banbanta a cikinsu ba zaka
taɓa cewa daga cikin Halisa ya fito ba, shi ne last born nata.
Labɓansa jajaye ne tas haka idanunsa farare ne gabaɗaya jikinsa zanan tattoo ne
ra'ayin shi ya bambanta da duka sauran yaran. Ya ƙara jan tsaki yana saka hannu
tare da har gitsa sumar kan shi wacce ta zama irinta Yaa Sheikh kala biyu. Hakimi
ya ce
"Abraham what exactly wrong with you?" Ya ɗaga manyan idanunsa yana miƙewa tsaye
tare da bada faɗi idanunsa na lumshewa kamar mai jin barci a hankali speaking
calmly ya ce
"I don't know what exactly wrong with me, wannan ihun yana gab da fasa mini kai
Please Hakimi do something i need to rest duk an cika mana gida da ihu kamar gidan
mutuwa"
Hakimi ya ce "Yaron nan baka da hankali, Big sister's naka suna kukan rabuwa da
Mami da Abbi damu kanmu amma kana zancan iska"
Abraham ya watsa hannu tare da buɗe ido sai ka ɗauka shi ne babba ya ce
"And so what? Na faɗawa Abbi yaran nan ba zasu iya zaman aure ba, dani ya yi wa ta
gidan ubanwa zan zauna ina kuka" Hakimi yabi ƙaramin ƙanin nasu da idanu yana mmkin
faɗin ran yaron har tsoro yake bashi. Abraham rai ɓace ya saka hannu ya fisge Hala
daga jikin Yaa Sheikh daidai lokacin angwayen suka shigo jin abinda ke faruwa.
Idanun Abraham har wani ruwa ruwa ne yake kwanciya cikinsu ya kalli Junaid-Ali ya
ce "Brother take your wife ta dame mu" Junaid-Ali ya yi murmushi ya ɗauke Hala cak
tana zunduma ihu ya yi waje da abar shi.
Haka ya ƙara fisgo Rohna ya damƙawa Abuturab ya ce "And you too take your wife" shi
ma ya riƙe Rohna yaran sunyi mugun shaƙuwa da iyayensu sosai. Huda kuka take sosai
na rabuwa da ƴan uwanta haka Hakimi idanunsa ya yi jajir banda uban tafiya Abraham
ko a jikinsa sai ma riƙe kan shi da ya yi da hannu bibbiyu sbd juyawa yake baya
ƙaunar hayaniya. Halisa ta juya zuwa bedroom ta dinga kukan rabuwa da yaranta
tausayinsu ya kamata.
Yaa Sheikh ya haura upstairs. Sauran ƴan bikin suka shiga mota zuwa rakiyar amare.
Yana daga kwance ya miƙe zumbur yana jan lafiyayyan tsaki ya ce
"Ni meye nawa laifin da ba za a yi mini aure ba?" "Kai yanzu idan akai maka auren
kayi me?" Ya girgiza kai kawai yana jin tambayar rainin hankalin da Hakimi yake
masa.
Ya haura upstairs zuwa part ɗinsa har ya juya ya ce "And don't forget wallahi
babbar mace nake so In sha Allah irin 40 to above ɗin nan ko 50" yana faɗin haka ya
shige part ɗinsa yana taune lips.
Surry har yanzu babu mijin aure, Jadda nan tsofa ya gama cin ƙarfinta Ummul daman
bata zo bikin ba sbd bata ƙasar bakiɗaya.
Shigowa ya yi ƙamshin Roja ya shiga hancinta ta ɗago suka kalli juna idanunta a
kumbure ya yi murmushi yana zare Glasses ɗin idanunsa ya ce "Mene ya samu Mami ne?"
Ta kwaɓe fuska ta ce "Are questing me? Bayan an rabani da yarana" ya jawota jikinsa
ya ce "Oh! Sangartar Abraham ya yi yawa zo muje na baki wasu ƙwayayen haihuwar
yanzu ki ƙinƙishi"
Ya bugi ƙirjinsa ta ce "Ina tausayin Rohna" "Ni Hala" ta kalle shi ta ce
"Hala gaba take da Rohna fa?" Ya rungumeta yana zame hannunta daga riƙe fuskar shi
ya ɗauketa yana cewa
"Mamana halinki ta ɗauka, mijinta zai sha barbaɗa da surutun ba a tambayeta ba amma
bata da juriya kamar ki that's why" ta lumshe idanu ta ce "Thank you Abba, ka gama
yi mini komai I love you"
Ya yi mata rumfa sosai ya ce "Ni ne da godiya, kin bani Mamana, Kin bani Khadijah,
kin bani Mother Maryama (Huda) da Abba Hakimi, ga auta Ibrahimul-khalil Abraham,
kin zame mini komai kin mamaye mini gida da zuri'a masu Albarka, *IDAN BA KE*
that's means babu YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU" ya rufe idanu ta ce
"Allahamdulillah, Allah na gode daka bani miji kamar Yaa Sheikh i love You Habibi
ƙalbi"
Idanun Yaa Sheikh ya yi jajir bakinsa ya shiga rawa ya faɗa buga kan shi, Halisa ta
tsaya kallon ikon Allah cikin sarƙewar harshe da wata In-ina ya ce
"I.... I... I...." Wasu irin hawaye Masu zafi suka sakko daga cikin idanunsa yana
matseta kamar zai rabata gida biyu cikin In-ina ya ce
"I.... I.... Lov...love... I love You" dam! Zuciyarta ta bada sauti sbd tasirin
kalmar tunda suke sai yau ya ce mata I love you, ya yi murmushi itama tayi murmushi
ta gama fahimtar a yanzu ba Yaa Sheikh ɗinta bane kawai ya juye zuwa MUTUM DA ALJAN
tana ganin yadda jikinsa ke murɗewa kamar wani maciji ya ƙara ɗaga murya ya ce "I
love you Zawja" yana faɗa yana rungumeta sosai ta ce "Allahamdulillah" tana faɗa ya
ce "I love you Haliyserh Sheikh Aliyu haydar Aliyu I love ƴar fillo,I love you
Danejo I so much love you princess Queen of my heart IDAN BA KE ba Sheikh Aliyu
haydar Aliyu Allahamdulillah"
"Abraham laɓe ka kewa su Abbi" ya kame fuska hannunsa riƙe da iphone system zai
kaiwa Yaa Sheikh ya duba masa wani abu shi ne ya kai bakin ƙofa yaji ana I love
you. Ya juyawa har ya je bakin ƙofa ya ce
"Yaa Hakimi can i ask you?" Hakimi ya ce "Sure, go ahead I'm listening"
Abraham ya ce "A cikin mata wace tafi iya soyayya irin romantic love ɗin nan"
Hakimi ya ce "Wannan sai dai Malamai ai sune suka san kan soyayya" Abraham ya ce
"Ohh! I'll catch you MALAMA malama zan aura" Hakimi ya juya yana cewa "Sannu *MIJIN
MALAMA* (Upcoming book).

_Allahamdulillah. Nan na kawo ƙarshen littafin IDAN BA KE Book 1&2 Ya Allah ka
sanya littafin ya zama hujja gareni ba hujja akai na ba, Ya ka datar damu duniya da
lahira Ubangiji kaga manufarmu ka sanya mu gane gasky ka kuma shiryemu kada ka
barmu da iyawarmu, dabararmu wayonmu ka sanya mu amsa tambayoyin da duk za'ayi
mana😭_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login