Showing 183001 words to 186000 words out of 196133 words
"Kiyi haƙuri nifa ba mayya bace"
Zahrah ta furta a raunace.
"Kaji mafisa ko? Babu dama kayi magana sai a ƙullaceka, to aniyyar ko wanne ɗan
ƙaniyya ta bisa duk yadda kaso da kame baki sai an saka ka faɗar zunubi"
Daidai lokacin Yaa Sheikh ya fito cikin wata Jallabiya Ash colour mai laushi da
santsi, ta kwanta sosai saman farar fatar shi, ya naɗe kan shi da hirami.
Yadda fuskarsa ke motsawa tana faɗaɗa zaka fahimci yana cikin farin ciki mara
misaltuwa. Ya dubi Zahrah da ta bar wajan tana goge hawaye.
"Hufii, to don Allah haka ba yafi ba? Da cewa nayi ta tashi tabar wajan Alkur'an
sai ta tsaneni yanzu dana kame baki nayi magana a nutse ba gashi ta fahimta ba,
Alsulhu khair!"
"Eh gwarai ga sulhu nan"
Dr A'isha Said
"Lafiya?" Yaa Sheikh ya furta a taushashe ƙamshin turaren shi na Roja ya cika
wajan, wanda ya sanya Dr A'isha sauke numfashi a ɓoye tana riƙe kanta.
"Matarka ta kura, ta hanata ɗaukan baby"
Jadda ta zare idanu tana dafe ƙirji sai kuma tayi shiru ganin yadda Yaa Sheikh ya
kafe ta da idanunsa masu tsananin kaifi da sanya mutum shiga cikin nutsuwar shi
"Allah ya raya Baby Ubangiji ya sanya albarka" Umma A'isha ta ce "Allah ya sanya
kuma matar malam tayi hankali" Sai a lokacin cikin sakin fuska yana jan jikinsa
ganin Ummul na zuwa ya furta.
"Matana da hankali"
Mother ta ce "Ba shakka"
Duk abin nan da ake hankalinta na kan Fattoumah ita da Father daya bar wajan yanzu.
Idanun da sukai yawa a wajan ya hana Yaa Sheikh rungume Ummul kamar yadda ya saba,
a hankali yake binta da idanu wanda take ganin tsananin farin cikin dake cikin su.
Suka amsa mata sallamar. Tayi murmushi ta ce "Barrister ya jikin Faɗima? Abu bai yi
daɗi ba Ubangiji ya ki yaye ya kuma taƙaita ya bata lafiya" Mother ta ce
"Amin Ya Allah" Dr A'isha ta dinga kallon Ummul ganin yadda take komai a waye cikin
nutsuwa da kamala, da shigar nan nata wanda ba a rabata da ita Abaya's masu kyau da
tsada.
"Can Mubasshir ya sameni, ina ga ya manta da na tura resigning letter " Mother ta
ce
"Ikon Allah, amma ba lokacin barin aikin ne ya yi ba?"
"Not at all,There is a reason why I joined the police force, and now I let El-
Bashir finish the job". "To Allah ya taimaka" Ummul tayi kyakkyawan murmushi ta ce
"Anyi baby kuma, Allah ya raya ya bawa mahaifiyar lafiyar shayarwa" suka amsa da
Amin. Ta juya ta kalli Yaa Sheikh ta ce "Arɗo You left your wife alone, and i think
she's crying".
Bai ce komai ba, bai kuma motsa ba idanunsa akan Jaririyar hannun Ummul, yana jin
son yarinyar da komai na wanzuwa a zuciyar shi.
Ya juya zuwa Room ɗin da Halisa ke ciki, har lokacin barcin wahala take yana daga
bakin ƙofa ya shiga ƙare mata kallo sai kawai ya girgiza kai fararen haƙoransa a
bayyane alamar dariyar ya yi mai kyau a fili ya ce
"Ƴar kwailar matata"
Ya fita zuwa reception Zahrah na ganinsa ta goge hawayen idanunta tana miƙewa tsaye
cikin inda inda ta ce
"A.... You" ya bita da kallo tayi murmushi ta ce
"Congratulations sweetheart, ina maka murna da samun babyn" bai ce mata komai ya
kama hannunta zuwa ciki ta ce "Zan koma gida"
A hankali ya ce
"Zuwa anjima" ta ce "To zan jira nan" ya dubeta da kyau ta ce "I wanted to be alone
kawai fresh air nake so" Cikin ɗaga murya ba wasa ya ce
"Fatymerh Zahrah!"
Sai kawai ta fashe da kuka ta ce "Am sorry, ba zan iya jure abin da Jadda zata faɗa
ba, daman Halisa na kawo Thank God ta sauka lafiya zan koma" ya riƙe hannun da kyau
ya nufi ciki da ita, sai da suka je corridor ya rungomota jikinsa ya ce "Sorry"
"Na kasa jurewa, na jawa kai na mugun tabo, wanda ya sanya na kasa samun soyayyar
ƴan uwanka, na kasa samun taka soyayyar balle nayi zaton samun baby tare da kai,
lalai na cancanci haka" Ya yi mata shiru yana dai rungume ta ita.
"Yaa Sheikh" ta ɗago kanta ya kalleta yana lumshe idanunsa ta ce
"Don Allah kada ka barni, nayi al'ƙawarin zama dakai ko ba zan samu farin ciki ba"
Ya share mata hawayen ya ce
"Ki riƙe Allah" ya faɗa yana zare ta a jikinsa tayi murmushi ta ce "In sha Allah"
Haƙurinta yana ƙara bashi yaƙinin tabbas Ubangiji ba zai barta haka ba. "I love You
sweetheart"
"Wife" ya ce kawai... Har Issha El-bashir bai shigo ba. Walking slowly yake tafiya
a world ɗin, hannunsa zube jikin aljihun wandon Camouflage-print cargo trousers sai
Sleeveless jersey tank top a jikinsa, idanunsa maƙale da Sunglass black. Yanayin
yadda yake tafiya sai sanya kasan jinin Mai martaba Ahmad Nuran ne yake gudana a
jikinsa.
Fuska a haɗe babu walwala sbd zafin zuciyar da yake ciki.
Ya murɗa handle ya shiga suka haɗa idanu da Fattoumah ya ɗauke ido ganin Mother ya
yi tsaye zube da aljihu.
"Sai haƙuri, Allah ya bi mata kadinta" Ya shafa kai ya ce "Oops it's okay"
Ya fito da waya yana dannawa fita Mother tayi a sanyaye Fattoumah ta ce "Uncle"
"Angela" El ya furta yana zama tare da kama hannunta ta ce "Kada ka barshi Uncle
muguwa ne"
Ya runtse idanu yana ayyana azabar da Baba mai gadi ya ganawa Angela ɗin shi.
"Ya zan na bar wanda ya san gonata kafin na sani? He most pay"
Ganin tana ta kallonsa ya ce "Mene Angela?"
"Fitsari zan yi" ya saka hannu ya ɗagota ya ce "Zaki iya takawa?" Ta girgiza kai
domin har ɗinki akai mata. Cak ya sunkuceta zuwa toilet, ihu! Ta fasa sbd azabar
zafi lokacin da fitsarin zai fita tana kuka sosai jikinta na rawa da ƙyar tayi, sam
El bai damu da ganin jikinta ba ya fahimci ita ɗin kawai yake ba wani abu nata ba,
ya taimaka mata da wanke wajan tana miƙewa ta shige jikinsa tana sakin wani kuka.
Yadda take kukan zaka san wahala take sha, ya riƙe da kyau a jikinsa a hankali yake
cewa
"Sorry, am sorry Angela" ya ɗauketa zuwa bed ɗin tana kwance a cinyar shi yana waya
a hankali ya ce "Oh, ina buƙatar a shige da shi state C.I.D, kafin shiga Court"
A tsawa ce ya ce
"Zanci Ubanki ɗan iska, kai baka san waye ni ba You hve no idea akan abin da zan
aikata" cikin ladabi ya ce "My bad"
El-bashir Said "I, El-bashir Ahmad Nuran Sarki ka kula ba wanda zan ɗagawa ƙafa
akan matata" ya sauke wayar rai ɓace. "Uncle me ya sa ka ke faɗa?" Ya dubeta yana
ƙoƙarin sauke numfashin shi.
"Angela zaki aureni" Sosai Fattoumah ta san kalmar aure, sbd wayonta shekarunta
kuma sun kai ta sani tayi murmushi tana ɗauke kai. Ya kamo fuskarta yana zare
Glasses ɗin idanunsa ya ce
"Ba zan iya jira ba, fitar da nayi sai dana tabbatar igiyar aurena ta hau kanki
Binta, You're now Mrs El-bashir Ahmad Nuran Sarki, El loves you Angela"..... Halisa
ta dinga mamaki wai ita take da yarinya, ita ta haihu, ita ta zama uwa. Sai ta
fashe da kuka musamman idan taga babyn na motsi. Da zarar taji ƙamshin turaren Yaa
Sheikh take rufe idanu bata mance azabar data sha ba, ita kam gwara first night da
wannan azabar ta haihu.
Zuciyar Babban malamin babu daɗi yana ta so ya keɓe da ƴar fillonsa amma taƙi
yarda. Umma A'isha ta zauna wajanta. A hankali motar shi tayi parking Umar-khan ya
fito da sauri ya buɗewa Yaa Sheikh, lokacin 6:45 na safe sanyi na busawa ya Fito
cikin kyakkyawar tufa kamala da Ilhama ya ƙara wanzuwa a jikinsa. Cikin tarin
nutsuwa yake sanya ƙafar shi ta daba,kana ya maye gurbinta dana hago har ya isa
ƙofar Room ɗin. Bakinsa ɗauke da sallama Umma A'isha ta amsa masa, hannunta riƙe da
babyn dake kuka sosai yin duniya kuma Halisa taƙi bata nono, da zarar ta bata taji
zafi zata cire kuma nonon ya cika sosai. Muryarsa da ƙamshin turaren shi ya sanya
Danejo kame fuska Umma A'isha ta amsa tana faɗin.
"Allahamdulillah, Ya Zahrah" ya jinjina mata kai yana zama saman kujera daman Umar-
khan bai shiga ba, ya shige wajan Mother dake kula da Fattoumah.
"Matar Malam riƙe ƴar nan mai azabar kuka, zan duba Faɗimatu" Tayi shiru "Magana
nake" nan ma tayiwa.
"Kawo ta" Ya faɗa in clam and golden voice. Umma A'isha ta bashi ita yana amsar ya
ɗorata a ƙirjinsa yana jijjigata amma taƙi yin shiru.
Ƙaramin yatsar shi ne ya sanya mata ta shiga tsotsa ya dinga shafata yana mata
karatu a kunne har tayi shiru.
"Wannan fushin?" Ya faɗa yana leƙa fuskarta ta tashi zaune ta ce
"Amma Abba ai baka kyauta mini ba" ya ware idanu ya ce
"To fa, dame?" Ta tura baki gaba ta ce "Baka ce mini haka haihuwar yake ba ai" Ya
dawo kusa da ita ya ce "Wanne suna ki ke so?" Ta kalli Jaririyar dake ta tsotsar
hannun mahaifinta ta ce "Ummul-khairy" ya tsora mata idanu sai ya zaro zam-zam daga
jikinsa ya bawa babyn, kana ta tauna dabinon ajwa ya saka mata, ya yi mata kiran
sallah kana ya yi mata huɗuba da Ummul-khairy. Ya ce
"Allah ya raya mini Mamana yadda take kama da babarta ka sanya kada tayi rigimarta"
Halisa ta ce "A haka dai ka aura daga nan har Rugar Rome"
"Eh tana tallan Kindirmo ba" Ta ƙara cewa "Abba nifa na gama haihuwa ba wasa nake
ba" Ya dubeta ya ce "Tare mukai komai fa, Na baki ciki, ki kayi rainon shi, kina
laulayi ina kulawa dake, a haka fa akace an tsaneni, naƙudar jiya akai mini dukan
tsiya" tana ƙoƙarin magana taji ya ɗage rigarta bakiɗaya tare da kafa....[2/17,
7:28 AM] Abk: *_Arewabooks@Nimcyluv79_*
Ihu ta saki ya yi saurin zame bakinsa yana saka hannu ya dungure mata kai, ta
marairaice ta ce
"Zafi fa, kuma daman...,"
"Shhhh" ya furta yana ɗora hannu tare da ƙarewa wajan kallo.
"Mene wai?" Bai iya magana sosai ba, sai daya haɗiye ruwan daya zuƙa ta ce
"Kafa shanye" ya lumshe idanu speaking calmly ya ce "Na sani"
"Me ya sa?" Halisa asked
Yaa Sheikh ya ce "ƙaya na ciri miki" tayi ta kallonsa tana ganin wayo ita dai kawai
ya yi mata
Ya zame idanunsa dake yazo a fuskarta tare da ɗaukan bbyn dake kuka ya ɗora mata
ita a cinya cikin kasalar data saukar masa ya ce
"Feed her" "Ciwo yake fa"
Ya dubeta ya ce "Na cire abin ciwon" kafin tayi magana taji ya sakawa bbyn a baki
kamar jira take ta cafke.
Ta fasa ƙara wacce ta razana Little Ummul.
"Wayyo Allah zata cire wayyo Ummul, wayyo Dadata" mmki ya cika Yaa Sheikh. A
hankali kuma ta sauke ajjiyar zuciya lokacin da taji ya rungumeta gabaɗaya a
jikinta yana kallonta
Tana kallon Little.
"Thank you, thank you"
Ya ce cikin laushin murya ita kuma tayi ƙasa da kanta tana son taji thank you ɗin
ta mece ce?
Ya riƙe hannunta cikin nasa yana ƙara shigar da ita jikinsa yaja numfashi ya ce.
"So lucky to have you in my life, Zawja.
Thank you Zawja for sending this amazing present to me…. I loved it and it will
always be very special to me, Of all the gifts you have given me, this surprise
gift will always be the most special because it came as an unexpected surprise and
it will always stay fresh in my memories and my heart"
Ya tallafo haɓarta cikin nutsuwa tare da yin copping face ɗinsu.
"Can i say you're the best wife ever? Am proud of you Ƴar fillo"
"Am also proud of you Habibi ƙalbi, you means alot to me you're the father of my
children I love you so much"
Ya tsora mata idanu bai san me ya sa a lokuta da dama take karantar zuciyarsa ba,
kafin ya faɗi komai ta gama karanta. Ya gode Allah, daya bashi macen rufin asiri
"Yaa Sheikh"
Ya dubeta bai amsa ba.
"I love You" yaji _I love You_ ɗin har ƙasan zuciyar shi, ta ƙara kashe masa jiki
tsigar jikinsa ta shiga ta shi tana zubewa. Manna mata sumbata a goshinta cikin
kamala irin ta mutanan ƙwarai masu nagarta da sanin hakƙin Iyali tare da zuri'a. Ya
furta.
" لضمتك بين ذراعي للأبد،"لو كان العتاق يثل كم أحبك
"I love you Abbana"
Ya fahimci so take ya furta mata wannan kalmar da tayi watanni tana jiran jinta a
bakinsa amma ya kasa..
Ya ɗauke kai tare da saka hannu ya ɗauki Little da tayi barci, babu inda tabar
babarta har fari da komai hakan ya sa ya ƙara jin son yarinyar na wanzuwa a
zuciyarsa. Juya mata baya ya yi. Ta ce
"Habibi" yaƙi juyawa.
Ta saka hannu taja gemun dan shin da taji a gemunsa kamar an zuba masa ruwa ya
sanya ta ce "Abul-khairy ku...."
Tayi shiru jin ya juya ya sake rungumeta tare da ɓoye fuskarsa a wuyanta
Ta saka hannu ta amshi Little ta ajjiye gefe guda, a ranta take jin kuka yake abin
da bai taɓa yi ba, bata taɓa gani ba.
Yaƙi yarda ya saketa balle ta kalli hawayen.
"Please Habibi stop stop..!" Ya dakatar da ita
da faɗin "Princess, my wife. You have given me the biggest blessing of my life. I
treasure this moment of being the father of my child. Thank you for gifting me this
bundle of joy and happiness"
"Thank you, ina jin nafi ko wacce mace dace da miji mai nagarta da sanin hakƙin
iyalinsa, miji ba fahimta da shiga cikin lamarina, mijin da soyayyata bata rufe
mishi idanu wajan ganar dani kuskure, miskilin mijin da zai sanya ni a gaba da
kalamai masu daɗi duk kame kai da miskilancin shi, Thank you Dear Lord"
Hawayen daɗi ya shiga fita daga Idanunta jin ya kama hannunta ya zura mata zobe, ta
fahimci the best gift daya iya bayarwa shi ne Ring.
Wani lokacin ya ce Allah ya yi miki Albarka wacce hakan yake ƙara sanya *Halisa
Danejo Rome* cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa.
So da ƙaunar mijinta *Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu* kuma *Dr Aliyu haydar* ya gama
gigita rayuwar *Princess Halisa Ahmad Nuran Sarki*
Ya kasa magana ya shiga sauke mata wasu lafiyayyun kisses ta ko'ina ya mance a
gadon asibiti take kuma ita ɗin ɗanya ce, jikinta ɗaya ne.
"It seems that Little Ummul will have a sister nearby, or in this hospital"
Khalil Said yana ƙarasa shigowa cikin room ɗin, daman Umma A'isha da Mother duk
suna room ɗin da aka kwantar da Fattoumah. Yaa Sheikh was speechless ya kasa furta
komai ya kame fuska da kyau babu alamun wasa, amma fuskar shi ɗauke take da annuri
da hasken farin ciki. "Kai Hamma daka tsaya a waje ai"
"That's what i was telling him" Khalil ya juya ya kalli El dake tsaye sanye da navy
blue na suit ya zuba hannu a aljihu.
"Kace mini me? Magaji yaushe ka fara sharri"
El ya ce "Goodness, bance maka mata da miji ne ciki ba, ai naga zuwan Abba tun
farar Safiyya"
Khalil ya watsawa El harara ya ce "Kai yake Abbanka not me, ja jiki"
Maimoon dake shigowa hannunta ɗauke da flast wanda Ummul tazo da shi yanzu ta ce
"Haka ranar nan ya ce wai rawar kai gareni irin halinmu ɗaya"
Khalil ya zaro idanu ya ce
"Ni ne mai rawar kai ɗin?" El ya ɗaga hannu zai make Maimoon Khalil ya ce "Kana
taɓa mini mata sai jikinka ya faɗa maka dan ubanka"
Ƙwafa El-bashir ya yi
Ya ce "Wannan yarinyar ficika da ita sai gulma"
"Eh babu komai, ficika kuma gata can kwance a gado kaje kaji da kwailar daka kwasa
shi ya sa kake ta zarya daga Sokoto zuwa Kano, Kano to outside country"
Maimoon taja jiki tare da haɗawa Halisa tea mai kauri sai tiriri yake, ta zuba mata
farfesun kayan ciki fal plate "Abba zo muci" caraf ya ce
"Waye zai ci abincin me jego kayan ƙazanta" Maimoon ta kwashe da dariya ta ce
"Wallahi ko ni ba zan iya ci ba"
Mai jiran kaɗan balle wacce aka jefa da kashin kaza, ta saki kuka wanda ya farkar
da Little ta ce
"Abba wai ni ce ƙazama, kai ma ba za kaci ba"
Yaa Sheikh ya lura da gangan Khalil yake son taso masa da rigimar ƴar fillon kafin
ya ce komai
Ta ce "Ai shi nawa ne, ni tasa ce kuma dan kaji yanzu kafin ku shigo ya saka
bakinsa a n...."
"Don Allah" Yaa Sheikh ya furta daidai kunnenta yadda ita kaɗai zata ji shi kam ta
fasa wannan zancan a gurin nan ai ya banu da Khalil, ga Mubasshir,ga Maimunatu...
El ya ɗauki bbyn ya dinga kallon ciki so da ƙauna ya ce "Me za a na ce mata to?"
"HALA" cewar Yaa Sheikh yana miƙewa tsaye ganin yadda Halisa tayi kicin-kicin da
rai sbd bai ci abinci ba. "Wow suna mai daɗi Hala"
Yaa Sheikh ya yi waje abinsa kai tsaye kuma Fattoumah yaje dubawa a nan ya samu
labari ashe Tun asuba jirgin su Mai martaba da Dada da su Fulani ya sauka, hadda
Yaya Halima.
Mai martaba yana can gidan Abba Hakimi. Shi ma daga nan harabar asibitin ya
tsaya,yana nan tsaye yana waya yaga shigowar mota ganin ɗaya daga cikin motocinsa
ce ya sanya ya ɗan buɗe idanunsa baya ya ajjiye wayar shi daga kiran Umar-khan.
Zahrah ta fito sanye da shigar kamala hijabi har ƙasa hannunta riƙe da basket suna
haɗa idanu da Yaa Sheikh ta saki murmushi ta ce
"Good morning sweetheart" Ya jinjina mata kai har ranshi yake son yaga ya kyautata
mata amma ya kasa ta ce "Ya sister Halisa da daughter?" A hankali ya ce
"Allahamdulillah, wife"
Zahrah ta ce "Bari na shiga,naga kamar fita zakai ko?" Nan ma ya ƙara jinjina kai
yana lumshe idanunsa, yana jin zuciyarsa babu daɗi sam da ganin halin da Zahrah
take ciki, ya kasa samu kalmomin da zai amfani dasu wajan fahimtar da ita halin da
yake ciki, sam wannan kariyar da wasu can Aljanu suka bashi bai ji daɗin ta ba,
idan ƴar iska Ubangiji ya ɗora masa Soyayyarra da? Shi aka cutar. rayuwa kenan!.
State C.i.d
Kai tsaye nan Yaa Sheikh ya sauka Khalil da kan shi ya yi driving nasa sai El wanda
yake jin kamar zuciyarsa zata faso idan yaga ɗan iskan tsohon ji yake kamar ya saka
bindiga ya harbe banza.
Mai kula da sashen bincike da fyaɗe da kan shi yazo wajan Yaa Sheikh bayan sun
gaisa ya ce "Kada ka damu Yaa Sheikh, zamu aika shi court daga nan kuma za a yanke
masa hukuncin bayan fitar da hujjoji"
El ya ce "How long za'a ɗauka kafin zuwa court duk wani fyaɗe kuma wanda yake da
aure hukuncin kisa ne fa? A bani dama na harbe ɗan taure" Ya yi murmushi
"Clam down prince, zai girbe abinda ya shuka imma irin ya fidda ƴaƴa masu kyau ko
akasin haka" dole El ya haƙura.
Yaa Sheikh ya koma gida domin ya huta ya samu cikakken tunanin da zai yiwa Zahrah
bayani.
A can asibiti da mamaki Zahrah ke kallon Mimi da Alhaji Farouk tare da wasu ƴan
uwanta. "Zahrah" Mimi ta kira sunanta muryarta na rawa hawaye ya cika mata cikin
idanunta.
Zahrah ta juya da sauri zata shiga mota, Mimi tabi bayanta cikin rashin sani ta
bangaji wata budurwa, budurwar ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta saka hannu ta ɗauke Mimi
da