Showing 75001 words to 78000 words out of 196133 words
ta
tafi can Rugar su" Umar-khan ya ce "Ruga kuma? Ba ƴar uwarki bace meye haɗinta da
Ruga?" Zahrah ta ce "Ruɗewa nayi, gida zan mayar da ita" Yaa Sheikh dai ya ɗauke
ƴar amanar shi ya nufi Library room da ita. Umar-khan ya miƙe daman yazo akan batun
zakkar da Yaa Sheikh ɗin zai raba sbd zuwan Ramadan. Ummul ma ta nufi kitchen ranta
fes.
A daddafe Zahrah taja jiki zuwa part ɗinta tana shiga jini ya ɓalle mata a rikice
ta kira number Deen yana ɗagawa ta fashe da kuka ta ce.
"Na shiga uku Deen kamar haihuwa zanyi ko bakwaini?" Ta cikin wayar ya ce "Haihuwa
kuma?" Tai masa bayanin komai. "How many times zan ce ki daina shiga sabgar
yarinyar nan? Kina son rusa mana plan nan ko?" Nishi Zahrah take sosai jini na
fita a jikinta ta ce "ba wannan ne matsalar ba, yarinyar kamar tana da Aljanu kuma
tana iƙirarin zata tona mini asiri, ga yadda Yaa Sheikh yake nuna kulawa gareta ya
fara bani tsoro ina son mijina" Deen ya buga mata tsawa ya ce "Ni ki ke faɗawa kina
son mijinki? Me kike nufi?" Ta ce "ina nufin abin da nace mana Deen, wallahi ina
son Aliyu ba zan iya rabuwa da shi ba, duk abin da ka ke nema zan maka amma banda
rabuwa da Yaa Sheikh" Deen ya furzar da Iska yama rasa me zai ce. "Kisan yadda zaki
ki fito yanzu na kai ki asibiti idan ki ka haihu a gidan ko ki kai ɓari ba ruwana"
yana faɗin haka ya kashe wayar, a daddafe Zahrah ta shirya bayan ta saka pads da
tsumma bata tsaya jiran komai ba ta nufi wajan bisa umarnin na Deen ɗin, Address
ɗin daya bata tafi ta samu motar shi a gefe guda tana zuwa ta zube a ƙasa, Deen ya
ɗauketa zuwa mota suka nufi asibiti..
_2hours Left_
Deen ne zaune a gaban a gaban Dr ya ce "kana nufin kace cikin dake jikin Zahrah ya
zube?" Dr ya ce "haka ne, duk yadda muka so dakatar da cikin mun kasa, sai dai hqr"
Deen ya dafe kai gaba ɗaya plan ɗinsa ya ruguje ya ce "Amma Dr kwanaki munyi
ƙoƙarin cikin ya zube, wani Dr ya ce ba zai taɓa zubewa ba" Dr ya gyara zama ya ce
"Anya? Sai dai idan baya so ya zubar da cikin, amma cikin ƙaramin lokaci za a iya
zubar da cikin" Deen ya yi shiru idan haka ne akwai wanda yake son yaga Zahrah ta
sha wahala ko ya tuna mata asiri. "OK Thank you" yana fita ya ƙarasa ɗakin da
Zahrah take, ita kanta Zahrah ta rasa me zatai farin ciki ko ɓacin ciki? Kuka ko
dry?. Sai dare aka sallameta Deen ya kawota har ƙofar gida ta lallaɓa ta shiga. A
hankali yake tafiya yana tattare Alkyabbar jikinsa dawowarsa kenan daga sallar
Issha kai tsaye kuma part ɗinsa ya nufa, kwana biyu yana stressed kansa sosai, yana
buƙatar yaje Nigeria kafin zuwa Ramadan shi ya sa yake ƙara takura kansa. Yana
shiga bedroom yaji ta rungomesa ta baya ta ce "Abbana sannu kaji" ya jawota gabansa
idanunsa akan bakinta ya ce "Sallah?" Ta ce "Nayi Abba, Darasi zaka bani" yana da
ayyuka amma dole ya ware lokaci ga karatun ta. Akan table ya zauna itama ya nuna
mata waje ta zauna, littafin Fiqhu ya buɗe ya ce.
"Nutsu sosai, abu mai muhimmanci ne" ta miƙe tsaye tare da dawowa wajansa ta zauna
saman cinyarsa ta ce. "Abba zanfi ganewa haka" ya ɗauke idanu ya lura kwana biyu
taiwa jikinsa kyakkyawan sabo, hannunsa ya zura ta ƙasan nata hannun ya ɗora kansa
a wuyanta a hankali ya sauke numfashi cikin nutsuwa ya ce.
_“Babin dake bayani akan abubuwan da suke ja ayi wanka”_ zata juya ta kalle shi ya
sakar mata nauyin kansa ya jima a haka kafin ya ce.
"Abubuwan dake jawo wankan Janaba, wanka ɗaya ne, amma ya kasu kashi kashi, ko
wanne kuma akwai dalilin dake sawa ayi, idan nace Janaba ina nufin najasa" ya yi
shiru yana lura da Yadda ta nutsu tana bin duk inda ya nuna da hannu da idanu. A
hankali ya ɗora da cewa.
"Fitar maniyyi a cikin bacci, ko a farke, daga namiji ko mace, ta hanyar lafiya da
jin daɗi, saboda hadisin da ya ce, “Idan ruwa ya fita a yi wanka.” Wato idan ruwan
maniyyi ya fita, a yi wankan janaba" ya ƙara yin shiru na wani lokaci kafin ya ce.
"Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, amma da ya farka babu alamar fitar
maniyyi, babu wanka a kansa. Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, bayan ya
farka sai ya ga maniyyi a jikinsa, wajibi ya yi wanka. A nan ana nufin ko da kayi
mafarki kayi mu'amala mace kuma baka fitar da komai ba, to wanka bai hau kan mutum
ba, idan kuma akasin hakanne dole ai wanka" ya saurara da maganar ya ce.
"Kin gane?" Ta girgiza kai ta ce "Wallahi Abba ji kawai nake ni wannan karatun bana
ganewa, sai abu ɗaya naji kana faɗa wai Mani..." Ya jima yana kallonta yama rasa ta
ina zai ɓullo mata ya numfasa kaɗan ya ce.
"Bakin ce ke matata mace? To idan nayi mu'amala dake ake nufi mu'amala ta aure" ta
tuntsire da dry ta ce "Ina ji ci-gaba" ya murmusa a ɓoye ya ɗora da cewa.
"Idan mutum ya tashi daga barci sai ya ga maniyyi a jikinsa, amma bai yi mafarkin
saduwa ba, wajibi ya yi wanka, saboda samuwar maniyyi a tare da shi, wanda fitarsa
ne yake jawo wanka" tayi saurin kallonsa ya ware mata idanu sosai ta ce.
"Abba to kai ma ka gani dana kwana tare da kai" tambayar ta Girgiza tunaninsa bai
tunanin cewa tana ganewa ba, sai kawai yai mata shiru ta juya gaba ɗaya suka
fuskanci juna ta ce.
"To gsky misali zaka bani idan ba haka ba, ni bana gane karatun naka Malam" a
taushashe ya ce "ban gani ba" ta ce "To sbd me? Kai mafarkinne ba kayi ko me?" Ya
numfasa sosai tare da ajjiye littafin ya riƙe fuskarta a hankali ya ɗora tashi
fuskar saman tata, ya kama hannunta ya ɗora saman gemunsa suka kalli juna a hankali
kuma ya sauke idanunsa akan ƙaramin bakinta ya ce.
"Sbd da kwaila na kwana...
Paid book
500
08119237616
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Mene kwaila?" Ya yi shiru zata sake magana Yaa Sheikh ya sanya
hannu tare danne bakin a hankali ya ce "Shhhhh shiru" dole tai shiru badai ta rasa
abin faɗa ba. Yaci gaba dayin karatun cikin salo da nutsuwa yadda zata fahimci
komai ta kuma gane abin da yake magana akai. Ya lura kuma tana ganewa duba da yadda
tayi shiru, bayan sun kammala Halisa ta kalli Yaa Sheikh dake murza hannunta ta ce
"Yaa Sheikh ya zan gane wankan janaba ya hau kai na?" Da hannu ya nuna ta kawo
kunnanta tayi saurin miƙa masa kunnen ya ɗora bakinsa ya faɗa mata magana tayi
saurin kallonsa tana zare ido ya ɗaga mata gira ya rungometa sosai a jikinsa a
taushashe ya ce "Zaki Albarka, tare da zuri'ar ki" Halisa ta kalle shi ta ce "Yaa
Sheikh"
Yaƙi magana ta ce "Yaa Sheikh mun gama darasin?" Ya ɗaga mata kai tare da cewa "Sai
wanda zaki ban" tai murmushi tana son ganin idanunsa amma yaƙi yarda ta gani sbd
juyewar da sukai "Yaa Sheikh me ya sa ake son kashe ka? Kuma ina gani kana kuka
cikin barcina kana cewa na taimaka maka ni kuma inaƙi" Ya dubeta yana nazartar
maganganun nata kafin ya ce "Kina son sanin sirrin Abbanki?" Ta ɗaga masa kai
alamar eh ya riƙe fuskarta yana ɗora tasa kai ya ce. "Mafarki ƙarya ne, wani
lokacin gsky ke kam naki ba daidai ba ne" buɗe baki tai zatai magana ya sakar mata
wani hot kisses a lips ɗinta idanunta cikin nasa al'amarin ya girmi tunaninta ji
take tamkar ba Yaa Sheikh ɗinta ba, wani irin sahihin abu yake mata ta kasa jure
al'amarin hawaye ya shiga gangaro mata ganin ƙirjinta na ɗagawa tana riƙe hannunsa
sosai ya yi saurin sakinta tayi luu zata koma baya ya yi saurin dawo da ita zuwa
jikinsa..
El-bashir ne tsaye a gaban motarsa idanunsa sanye cikin Sunglass ya zuba hannun a
cikin aljihu, farar t.shirt ce a jikinsa sai wandon uniform na ƴan sanda. Ya daɗe
tsaye a inda yake kafin wani saurayi ya ƙarasu wajan yana sarawa El-bashir ya ce
"Mun gama dukkan wani binciken da muke a Company amma babu wata hujja dake nuna an
zuba haramtattun kaya a kamfanin sarrafa shinkafa na Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu"
El-bashir ya jinjina kansa ya ce "Okey, kaci gaba da saka idanunka" Yasir ya ce
"Amma sir ga shawara, mai hana kabi ta wata hanyar kai ka zuba hudar iblis cikin
kayan nasu, tunda na samu labarin kayan nasu yana gab da shigowa, idan har aka kama
kayan kamfanin sarrafa shinkafar dole sai an nemi shugaban kamfanin kaga a nan ka
jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ka kai Yaa Sheikh gidan yari, kuma ka ɓata masa
suna tare da lalata kamfanin baki ɗaya" El-bashir yai shiru a hankali kuma ya juya
ya shiga mota yana cewa "I'll think about it" El-bashir yana son privacy life shi
ya sa bai fiya fita da wasu securities ba, infact ba kowa yasan abin da ke
zuciyarsa ba. Burinsa bai shige yaga bayan Yaa Sheikh har ƙarshen rayuwa ba. Direct
masarauta ya nufa, yana buɗe ƙofa yaci karo da Khalil wanda ya fito daga ɓangaren
Mai martaba. "Am glad you are here, yanzu nake shirin kiranka Mai martaba na son
ganinka" El-bashir ya ce "Ok tom" har ya yi gaba Khalil ya ce "hold on, nayi maka
magana baka ɗauki abin serious ba ko El?" El-bashir ya jingina da jikin mota yana
kaɗa key ya ce "Maganar me kenan Yarima? Na manta fa" Khalil ya ce "Maganar
yarinyar da nace kuna kama sosai, kamar ya ɓaci fiye da tunanin mutum shi ya sa
abin ya tsaya mini rai" El-bashir ya kalli yayan nasa da kyau yana sakin murmushi
ya ce "Na kasa fahimtar me kake nufi Yarima, i don't even have a wife balle nace
ita ta haifa mini yarinyar har muke kama, kuma dai nasan kaf cikin masarauta ba
wanda ya haihu ɗan ya ɓata right? Infact banga wata kama ba"
"Amma mu ai munga kamar ko? Da Fulani Atine za taga yarinyar ina da yaƙinin zata
tai tunanin abin da nake tunani" El-bashir yai gaba abin sa ya ce "Ai shikenan, ni
wannan kamar bata gabana" Khalid yai murmushi yana ganin gabaɗaya akwai sauyi a
rayuwar El-bashir ɗin. Daga nan ɓangaren Mai martaba El-bashir ya nufa, kasancewar
baya cikin fada yasa damai bai tunanin zuwa can ba. Yai tsaye har sai da akai masa
iso kafin ya shiga ƙawataccen parlourn wanda ya sha ado da kayan sarauta kala-kala.
Da mmki El-bashir yake kallon Abba Hakimi yana tunanin mene ya kawo shi garin a
wannan lokacin? Ko abin da yake tunani ya faru ne?. Ya nemi waje ya zauna yana
faɗin "Barka da hutawa Daddy, Allah ya ƙara girma" Mai martaba Ahmad Sarki ya sauke
numfashi kafin ya kalli Autan ɗan nasa ya ce "Mubasshir ka shirya dai?" El-bashir
ya ce "Dady ina? Akwai aiki habaka" Mai martaba ya yi shiru na wani lokaci kafin
ya ce "Aikin hajji, ina son ziyara tare da miƙawa Ubangiji buƙata tuna, Khalil ya
kammala komai jirgi zai ta shi gobe" El-bashir bashi da ra'ayin zuwa aikin hajji
wannan shekarar baki ɗaya amma hakan kamar wata dama ce a gare shi. Abba Hakimi
daman yasan ba lallai El-bashir ya kulasa ba, kamar yadda baya kula Yaa Sheikh ga
mmkinsa sai yaji ya ce. "Barka da hanya Abba Hakimi" Abba Hakimi ya yi murmushi
irin nasu na manya kafin ya ce "Allhmd Mubasshir" El-bashir ya ce "Yaa Sheikh
lafiya yake dai ko?" Ba Abba Hakimi ba hatta Mai martaba sai da ya kalli El-bashir.
"Kaji ance bashi da lafiya ne?" Ya girgiza kai Mai martaba ya ce "A gidan shi zamu
sauka kafin fara aikin hajji, naji ance shi ne zai jagorancin sallar Taraweeh da
Tahajjud a masallacin ka'abah" El-bashir ya miƙe ba tare daya ƙara cewa komai ba,
gabaɗaya suka bi bayan shi da idanu.
"Ina tunanin amsar Halisa daga hannun Yaa Sheikh, ba zan iya bari tai shekara guda
ba" mmkinsa maganar Abba Hakimi ya kasa ɓoyewa daga kan fuskar Mai martaba sai
daya ja numfashi cikin tarin martabawa da bawa Abba Hakimi girman na shi ya ce "Don
me ya sa?" Abba Hakimi ya ce "Don ya magantu, ina sanin ina alƙibilar Aliyu take
akan aure dama mace baki ɗaya, ka sani na sani Aliyu kaifi ɗaya ne, ba a taɓa sauya
masa tunanin dama shi ne a kwakwalwar shi ba. Lokaci yana shigewa shekaru na ƙara
girma a tare da Yaa Sheikh, ban san ina tunaninsa yake ba, ban san mene tsarin shi
ba, amma a wannan karan ba zan zuba masa idanu ba, ina da yaƙini da kuma tabbacin
Yaa Sheikh ba zai saurari Zahrah Farouk ba, ina son saka masa soyayyar Halisa ko ta
halin yaya" Mai martaba ya jinjina kai yana mai jin cewa gasky Abba Hakimin ya
faɗa. "Hakan yana da kyau" Abba Hakimi ya ce "Da zarar an kammala aikin hajji ka
tawo mini da ita, nasan ba zai ce komai ba" tattaunawa sukaci gaba dayi.
El-bashir na fita ya nufi sashin Fulani Atine ya sameta ita da tarin kuyanginta
bayan sun fita ta kalle shi ta ce "Sarkin gobe na Wannan masarauta ya akai ne?" Ya
tura hannunsa cikin sumar kansa tare da fesar da Iska mai zafi sai kawai ya juya
kamar wanda mayan ƙarfe ke janshi.
"Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba aje ba. Ko yanzu goma ta faɗi tafi
biyar albarka, sahun giwa kuma ya zarce na raƙumi, ƙadangaren bakin tulo ban fito
ba sai dana shirya ja muje zuwa El-bashir Ahmad Sarki" Fulani Atine ta faɗa tana
sakin wata dariya ita kaɗai. Kafin ta sanya ai mata iso da Jakadiyya. Fulani
Balaraba tana ɓangarenta babu mai jin kanta daga ita sai ɗan ta Khalil Ahmad sarki
suke mu'amala.
Iska mai ƙarfi ce ta mamaye cikin dokar dajin da suke, kafin wani kuka da ihu mara
daɗin saurare ya maye gurbin iskar. Wata kururuwa Prince Bilal ya saka bakinsa na
fitar da hayaƙi cikin jin daɗi da farin ciki, murya mara daɗin Amo! Ya ce.
"Sandu kayi ƙoƙari ban taɓa zaton matata zata kasance a Madina, ka tabbatar ita
ce?" Sandu ya ɗaga fikafiki yana shawagi a sama ya ce.
"Naga zoben a hannunta, na ganshi ta fito daga makaranta ita ce" Prince Bilal ya
ƙara sakin dariya ya ce "Lokacin ya yi da zan nunawa wancan Bil'adama ɗin bai isa
ba, bashi da ƙarfin ikon da zai rabani da matata a karo na biyu, idan a lokacin
baki da iko yanzu ina da ikon da bai isa yaja dani ba" Sandu ya yi dry sosai har
lokacin shawagi yake a sama ya ce "Da tuni na ɗakkota zaren dake hannunta yasa bani
da ikon tunkararta" Prince Bilal ya ƙara kwarara ihu wanda ya ƙara hargitsa dajin
da suke ciki farin ciki mara misaltuwa yake ji a ran shi ya ce "Zani, zani lallai
zani idan har Ramadan ya zo bana da iko ko kaɗan dole naje yanzu" yana faɗin hakan
yabi iska ya ɓace.
Wajan sati biyu kenan da shan poison ɗin da tayi, taji sauƙi sosai ta koma
makaranta, sosai take fahimtar karatun da har malamai take bawa mmki ɓangaren Yaa
Sheikh bai saurara wajan bata karatun addini ba, musamman karatun Alkur'ani.
Al'amarin da yake bashi mmki duk yawan karatun Alkur'ani da zai mata ba, nan take
zata haddace wani lokaci kallonta kawai yake wani lokacin kuma sai ya yi murmushi a
ɓoye yana da yaƙini da taimakon wasu a karatun nata. Tun yana mata surah ɗaya ya
koma biyu. Zarah ce zaune a gefen bed ɗin ta hannunta riƙe da waya tana lalubar
number Surry. Daily ta danna babu ɓata lokaci Surry tai picking call ɗin "Ai ta
kiran number ki ba a samu, meke damunki Surry?" Surry ta ce "Nothing ya akai?"
Zahrah ta sauke numfashi ta ce "Cikin jikina ya ɓare Surry ki ta yani murna" da
ƙarfi ta cikin wayar Surry ta ce "What,ya zube?" Zahrah tai shiru kamar mai nazari
sai kuma ta ce "Haka ne, amma ya naga kamar kin firgita" ta ƙirƙiri murmushi ta ce
"A'a farin ciki ne ya yi mini yawa, congratulations" Zahrah tai murmushi ta ce
"Naje anyi mini ɗinki tas, na dawo kamar budurwa duk da Dr ɗin ƙi ya yi wai sai na
bashi rabon shi" Surry tai dry sosai ta ce "kice zamu samu ɗan Dr kenan?" Taja
tsaki mara sauti ta ce "Ba wannan ba, nifa na fasa aikin nan da Halisa, da kai na
zan tunkari mijina nasan ba zai gane komai ba, tunda na riga nayi ɗinki, yau ɗin
nan nake son zuba masa maganin cikin shayi" Surry ta ce "That's great, za a sha
amarci kenan?"
"Uhm bari kawai ashe yarinyar Aljanu gareta? Itafa tayi sanadiyar zubewar cikin
nawa" Surry ta saki murmushi kawai kafin ta ce "To gida zaki dawo da ita?" "Ina
tunanin haka, nifa wlh idan naga yarinyar gabana faɗuwa yake sam jini na bai haɗu
da ita ba, yanzu ma zuwa zanyi naci ubanta na sakata aiki ba tai ba" kashe wayar
tayi tana miƙewa tsaye tana mmkin yadda cikinta yake a kumburem kai tsaye part ɗin
Halisa ta nufa a hanya taci karo da Yaa Sheikh tun safe daya fita sai yanzu ya
shigo gidan a hakama sai daya gabatar da sallar Issha dan haka a gajiye yake sosai
ga ciwon kan dake neman tashi.
Murmushi tayi ta ce "Wlcm My Excellency" ta faɗa tana rungome shi ya ɗan jinjina
mata kai taƙi sakin sa ta ce "Can i help you naga ka kaji sosai" ya zareta a
jikinsa a hankali kamar wanda akaiwa dole ya ce "No thanks" ta ce "Ok bari naje
wajan yarinyar can naci ubanta na sata aiki ba tai ba" ta juya ya yi saurin riƙe
hannunta da mmki ta kalle shi sai taga ya sassauta fuskar shi..
"Uhm haka ake tarbar miji? I need green tea" she can believe Yaa Sheikh shi ya riƙe
mata hannu har ya yi mata mgn cike da kulawa. Ta juya idanu ta ce "Bari na saka ƴar
fillo ta kawo maka My Excellency, ni kuma zan shirya amsar mijina yau" ya ɗauke ya
jima kafin ya cire hannunsa a nata ya ce "Ba zaki iya ba ke? Ita kullum cikin samun
lada take" ta zaro ido ta ce "Wace? ladan me kuma?" Ya kame fuska sosai kamar bashi
ya yi maganar ba. "Ok bari na karɓo maka love You My Excellency" ya sumbaci gefen
fuskar shi kana ta juya zuwa kitchen a karo na farko. Yaa Sheikh yana shiga part
ɗinsa ya nufi ƙofar da kai tsaye zata kaishi har sashin Halisa. A hankali ya murɗa
handle ɗin tare da turawa, idanunsa yaja ya rufe sbd ƙamshin daya ratsa hancinsa
wanda ya haifar masa da kasala a jikinsa, da ƙyar yaja jikinsa zuwa bedroom ɗin
ganin bata parlour yana shiga