Showing 171001 words to 174000 words out of 196133 words
shi kuma ya tsaya tare da buɗe ƙofar
Halisa, yana shiga ya sameta zaune inda tayi sallah hannunta riƙe da Alkur'ani, bai
ce komai ya karɓi Alkur'anin tare da ajjiyewa waje guda, kana ya dawo ya ɗauketa
cak tayi saurin haɗe fuska ta ce "Meye haka?"
He just staring at her face yana hango rigimar gaske ya zauna saman kujerar dake
kusa da bed ya yi nishi like he so much tried. Yana sakin fuska ya ce
"Tubarkallah, Zawja kada Kiyi lukuta fa" ita da kanta mmkin yadda Jikinta ya buɗe
bakiɗaya take tayi ƙiba taban mamaki musamman hips ɗinta wanda yake ƙara tabbatar
da girman cikinta. Muryar na rawa gudun shiga hakƙi ta ce
"Sabahul khair" Ya kama fuskarta tare da juyo da ita amma sam taƙi yarda ta kalle
shi ya yi mata shiru yana saka hannu ta baya tare da rungomota zuwa jikinsa
hannunsa yana shafa cikinta daya kumburo sosai a hankali ya manna labɓansa a
wuyanta yana goga mata hancinsa, tattausan gemunsa na shafar fatar wuyan nata,
tsikar jikinta ya tashi sosai sai da ya gama shafar inda yake so da yake tsole masa
idanu kafin yace
"Meke faruwa?" Tayi shiru ya sauke numfashi a nutse tare da miƙewa da ita ya ce
"don't tell me, but ki saka Allah cikin lamarin ok?"
Ya kwantar da ita da ita tare da durƙosawa ya ɗaga rigar Jikinta duk tana binsa da
idanu ya sumbaci cikin tare da yin addu'a ya shafa, kafin ya yi magana wayarta ta
fara ringing ya dubi wayar haɗaɗɗan pictures ɗinsu ne shi da ita a screen
wallpaper. “Hamma El”
Yaga an rubuta bai ɗaga ba ya miƙa mata tayi saurin ɗaukan wayar tana kwaɓe fuska
cikin rigima da shagwaɓa ta ƴar auta ta ce "Hamma"
Ta cikin wayar ya ce
"Princess, gani nazo wannan neman rigimar ya yi yawa" ta marairaice fuska tana
sakin kuka ta ce "Uhm ni dai a'a" ya kalli harabar gidan Yaa Sheikh banda ƙamshin
flowers da kukan tsuntsaye babu abinda kake ji gwanin sha'awa gidan."Ina Compound"
tayi saurin cewa
"Gani nan" ta goge hawayen idanunta tare da ɗaukan hijabi, ya dubeta da kyau ko'ina
na jikinta sheƙi yake musamman fuskarta, a haka zata fita Compound masu aikin duk
suna nan, ya miƙe fuska a kame
Ya ce "Ki cire tunanin fita Compound" yana faɗin haka ya fita, tayi shiru domin
bata gane me hakan yake nufi ba, ta kira El-bashir ta ce ya shigo. Ta fita zuwa
main parlour hannunta riƙe da waya a zaune ta samu Yaa Sheikh yana kallon labaran
tashar Aljazira, tana nan tsaye El-bashir ya yi sallama ya shigo hannunsa zube
cikin wata Marron ɗin Double Breasted suit, ya saka Derby shoe sai ƙamshin
Thierry mugler yake,ya yi murmushi dimples ɗinsa irin na Halisa ya bayyana yana
ƙoƙarin zubewa gaban Yaa Sheikh ya gaida shi yaji Halisa ta faɗa jikinsa tare da
ƙanƙame shi da kyau tana kuka kamar ranta zai fita. A tsorace El ya rungometa yana
faɗin
"What happened Princess?" Domin ji yake da wani abu ya sameta gwara shi ya same
shi, ita kaɗai suke jini ɗaya uwa ɗaya uba ɗaya, banda haka bashi da kowa sai na
biyunta Yaa Sheikh. "Am sorry Hamma, kayi haƙuri ba zan sake maka harara dako in
kula ba, kai kaɗai zakai mini soyayyar da babu gori cikinta kuma tabbatacciya kayi
haƙuri"
Shi dariya ma ta bashi, Yaa Sheikh kuma ya kwashe karatun nata tas, bai kalli inda
suke ba, idanunsa dai ya yi jajir ainun kamar wanda wutar kishi ke damunsa, El ya
shiga ƙoƙarin zameta sbd cikin Jikinta tana kuka ta ce
"Please Hamma El ka tafi dani kaji, bana jin daɗi wallahi ai da ba zaka so ka rasa
ni ba" yaja hancinta ya ce "Ba gaki ga Abba ba?" Ta maƙale kafaɗa, ya girgiza kai
ya ce "Wlh daman Mom tace ba wani abin kirki a kiran ki, rigima ce"
Ya zameta yana durƙosawa gaban Yaa Sheikh ya ce "Good morning Abba" Ya jinjina masa
kai alamar lafiya fuska kuma sake yana jin El-bashir ya zuciyarsa,sosai yake ƙaunar
yaron. Ta ce
"Ka zauna mana"
Ya harareta ya ce "Ke gidanki ne, ni kuma wajan Abbana nazo" ya gyara zama daidai
ƙafafuwan Yaa Sheikh ya ce "I'm starving aban breakfast" tayi wani irin murmushi ta
ce "Laa Anty Zahrah ce zatai breakfast maybe ta gama" daidai lokacin Zahrah ta fito
cikin kwalliya ta zuba lace Idanunta sun faɗa sunyi zuru-zuru. Ta nemi waje ta
zauna tana ɗan yin murmushi tace "A'a baƙo mukai ne?" Idanun El akan plasma bai ce
komai ba, Halisa ta ce
"Anty Zahrah kin gama breakfast ne?" Ta ɗan saci kallon Yaa Sheikh taga gabaɗaya
basu yake kallo ba, ta ce
"Ban ba, bana jin daɗi"
Halisa ta jima tana kallonta kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Allah ya
sauwaƙa"kitchen ta nufa ta fara shirya abu mai sauƙi irin very liquid ɗin nan wanda
ba zai ja lokaci ba, fried indomie tayi ta saka mata su carrots, onion, da sauran
vegetables. Tana da garin kunun tsamiya ta dama kunun tsamiya, kana ta tafasa shayi
da zuba ginger da barkono da na'a na'a. Kana ta soya ƙwai tasan ba lallai El ya sha
kunun da tayi ba. Tana gamawa tayi wanka ta shirya cikin wata simple light blue ɗin
abaya wacce ta fidda shaps ɗinta, ta fito sai ƙamshin turare take.
Yaa Sheikh ya kasa riƙe kansa ya dinga satar kallonta har ya ɗora idanunsa a kanta
da kyau, wani kasala ya saukar masa musamman da suna haɗa idanu ta tura masa
ƙaramin bakinta na tsiwa ya zame idanunsa yana girgiza kai a ransa yake sanya mata
albarka.
Ta zauna so close to him tare da ɗora kanta a ƙafaɗar hannunta a gemunsa tana ja
idanunta akan El-bashir ta ce "Prince the breakfast is ready" Ya miƙe ya ce "Ok
Little Our Princess Abba's girl" ya nufi dining room ɗin dake main parlour, Halisa
ta juya suka haɗa idanu da Yaa Sheikh taja gemun ta ce "Habibi ƙalbi let's go" ya
riƙe hannun nata,ganin idanun Zahrah ya sanya ya saketa ya ce
"Part ɗina, cikin freezer Honey" ya yi maganar ba tare daya faɗi ainahin abinda
yake so ba, ta fahimta sai ta miƙe ta ce
"Okey Yallaɓai"
Tana barin wajan Zahrah ta ce "Amma kasan kayi ba daidai ba" a taushashe ya ce
"Da?"
"Daka riƙe hannunta bayan kasan ranata ce" ya ɗago ya kalleta da kyau, kamar zai
shiru sai ya ce "aikin da ki ka kasa tayi,ke zaki breakfast baki ba, ita kuma tayi
tazo inda nake ta gaishe ki, kefa? Ko ina kwana babu" Ta ɗauke kai ta ce "Amma ina
da niyyar gaisheka" kafin ya yi magana Halisa ta ƙwalla masa kira ta ce "Ɗan babyna
Abbana Yaa Sheikh banga zumar ba"
Ya miƙe tsaye tare da ajjiye wayar shi ya nufi upstairs, yana zuwa ya sameta
durƙoshe gaban freezer yana zuwa ya saka ƙafa ya zungureta bata kallesa ba ta ce
"Ina take" a hankali ya ce
"Stand up" ta miƙe da ƙyar kafaɗarta ta sake tayi saurin shigewa jikinsa tana
"Wayyo Abbana" ya riƙo ƙugunta tare da binta da kallo ya ce "Zaki iya haifar yara
20 anya?" Ta zare ido ta ce "Tab ai na gama daga wannan"
"Kidding" ya furta domin shi da gaske zuri'a yake son mai yawa tunda familynsa basu
da yawa. Ta ce "Sakeni to" ya kalli ƙirjinta ya kalli bakinta ya ɗauketa ya ɗora
saman freezer kafin tayi aune ya fara bata wani cikakken sumbata yana birkitata,
yana shafa duk inda yaso baya son yi abin kunya inda yaji abu ya yi masa sai ya
fara faɗin..
"Yasubuhanallah! Ya Allah Ma sha Allah" cikin ƙaramin lokaci ya ɗorata akan network
duk tana cewa bata so suka hargitse juna, ƙarar da taji yasa tayi saurin dubawa ta
zare idanu ganin ya kusa yaga mata gaban riga. Ta sakkowa da sauri yana shirin
kamota tayi waje tana maida numfashi, a hanya sukaci karo da Zahrah da take da
wayar Yaa Sheikh da ake kira, ta bita da kallo kishi ya mamaye zuciyarta fal!
Tana shiga ta samu Yaa Sheikh ya kifa kansa da jikin freezer ta ce "Ana kira" yana
yin magana zai fallasa halin da yake ciki, ya miƙe tare da juya mata baya "Are you
already?" Ta faɗa tana shirin dawowa gabansa ya yi saurin ɗaga Jallabiyar shi yana
shigewa bathroom.... Misalin 5 na yamma motar Yaa Sheikh tayi parking a harabar
gidan Abba Hakimi, ya fito yana gyara zaman babbar rigar jikinsa, Halisa ta buɗe
ƙofa ta fito sanye cikin duguwar riga kamar kullum ta zumbula hijab, ga liƙab a
fuska hadda safar hannu, tana fitowa ta ɗage liƙab ɗin tana haɗe fuska tare da tura
baki ya yi murmushi mai sauti cikin kamala ya ce
"Yanzu ki ka amsa sunan Matar Malam" Tayi gaba sbd haushin hijabin take ji ga cikin
daya fara takura ta, duk ta damu kanta ya kuma ƙara fuskarta ƙiba tayi wata ƙatuwa,
ita ta fara shiga cikin gidan bakinta ɗauke da sallama, Abba Hakimi da shigowar shi
kenan ya ce "A'a wa nake gani kamar matar?" Ta nemi waje kusa da shi ta zauna ta ce
"Ni ce Jon wuro ina yini" ya dinga ya ce "Ma sha Allah,sannu kinji Allah ya bada
lafiya" Umma A'isha ta ce
"A'a tashi daga nan kada ki danne mini miji, jibi yadda ki ka zama narkekiyya ni
ƴar nan" Ta juya tana amsa sallamar Yaa Sheikh ya zauna saman kujera cikin tarin
nutsuwar nan na shi ya gaida su. Umma A'isha ta ce "Me kake bata ne? Wannan ƙibar
ai ta shige ta hankali" Halisa ta ce "Soyayya yake bani, ke kam matar nan mene
damuwarki da ƙiba ta ne?" Abba Hakimi ya ce
"Kishi take baki da ita" Mother ta fito ita da Dr A'isha cikin farin ciki ta ce
"Oyoyo ga Daughter ma sha Allah, aure ya karɓe ki" ta zauna Halisa ta gaida ita ta
ce
"Mother wai baki koma gidan Father bane?" Kai tsaye ta ce "Eh, Aku"
Tayi murmushi kawai ta ce "Allah sarki Farther tausayi kuke bani ne" Dr A'isha tayi
mmkin yadda Halisa taƙi ko kallonta balle ta gaisheta.
Abba Hakimi ya ce
"A'isha ta samu matsala da mijinta, harta dawo gida" Ya juya ya kalleta fuska haɗe
ya ce
"Ɗauki tarkacanki ki koma" cewar Yaa Sheikh. Ta ɓata fuska amma sosai taji daɗin
jin muryarsa ya buga mata wata gigitacciyar tsawa ya ce "Out immediately"
Ta fashe da kuka sosai tare da jan mayafi tayi waje. "Me ya sa?"
Yaa Sheikh ya kalli Abba Hakimi rai ɓace ya ce
"Shirme tayi, bayan ita ce bata haihuwa ya rufa mata asiri...
08119237616
[2/9, 7:03 PM] Abk: Duka suka bishi da kallo, Mother ta ce "Idan har haka Dr A'isha
ta yaudari kanta" Abba Hakimi ya kasa magana, sbd a iya saninsu babu wata hujja
data nuna cewa Dr A'isha ce bata haihuwa, a kullum mijinta take nunawa matsayin
wanda ke kawo naƙasu kuma likitoci sun ƙara tabbatar da hakan. "Amma a ko wanne
lokaci Likitoci sune suke bada tabbaci akan mijinta shi ne baya haihuwa, ya akai
reshe ya juye zuwa mujiya?"
Umma A'isha ta ƙare tana kallon Yaa Sheikh da alama suna jiran su ji ta bakinsa ne
kuma yaja baki ya rufe yaƙi cewa komai, suna da tabbacin kuma ba zai ce komai ɗin
ba, na bayan ma daya furta ta kaishi ƙarshe ne.
Halisa ta kalli Mother ta ce "Ni dai wallahi yunwa na keji" sai a lokacin Yaa
Sheikh ya ɗaga fararen idanunsa tare da kallonta, abincin da taci kafin su taho har
mamaki yake, amma yanzu har tana neman wani?.
Mother ta ce "Shi yasa gaki nan kamar an zuba yis tubarkallah, me zaki ci" Halisa
ta sakko ƙasan carpet tana miƙar da ƙafarta wacce ta kumbura, a nutse ba tare da
kowa ya lura ba ya dinga kallon ƙafar dole akwai dalilin kumburin. Ta buɗe baki
cikin takurawa irin ta masu juna biyu ta ce
"Kawai ni duk abinda kuke da shi a bani zanci"
Umma A'isha ta kada baki cikin zulaya ta ce
"Bafa Abbanki Yaa Sheikh ke bamu kuɗin cefane ba" kamar jira take ta bata martani
da
"Mijina bashi da rowa, idan ku kai mini rowa na haifi ɗana haka zaku haɗu da shi"
"Da waye zamu haɗu?" Umma A'isha ta sake faɗa, domin Halisa jikar ta ce shi ya sa
bata damuwa da sakin zan can nata. "Gwarzon mijina ba irin tsohu na kujera" Sai a
lokacin Mother ta sake cewa
"Yanzu kuma kan Ubana kika dawo" Ta juya kan Yaa Sheikh ta ce
"Malam ka ɗauke matarka duk ta Ishemu" Yaa Sheikh ya ɗan faɗaɗa fuskarsa yana mai
yin baya kaɗan ya ce
"Wajan Ummul zamu, taci a can" Mother ta riƙe baki ta ce "Kana son faɗa mana Ummul
tafi kula maka da Matarka ko?" Ya miƙe tsaye yana shafa fuska zuwa gemunsa, Halisa
ta kama jikin kujera ta miƙe tana faɗin "Ai wallahi tafi so na, shi ya sa nake son
ɗanta kamar hauka I love you Abbana so much love" tuni ya yi waje ta zura hijabi
tana cewa
"Kuma ba zan dawo ba sai na haihu" Umma A'isha ta kada baki ta ce
"Allah ya raba lafiya, mu ai haka muke so" Abba Hakimi da addu'ar fatan alheri da
samun farin ciki na har abada ya bisu, Halisa macace tana son Abbanta bayan kallon
miji da take masa, tana masa kallon komai nata shi ya sanya bata riƙe kanta akan
soyayyar shi, tana da kaifin baki kamar reza tunaninta kullum kaifafa yak. Yaa
Sheikh yana riƙe kansa sbd bai saba ba, kuma halinsa ne haka baya iya bayyana yadda
yake ji sai dai ya nuna shi a aikace, jajir tacce ne, ya gode Allah da son da ya
kewa Halisa bai rufe masa idanu ya kasa nuna mata kuskurenta a duk sanda tayi ba
daidai ba.
Yaa Sheikh na fita ya tsaya jingine da jikin motar shi yana shaƙar iskar dake
wajan, tafiya yake son yi mai muhimmanci amma baya son barin baya da ƙura, Halisa
nada ciki tana tsananin buƙatarsa Zahrah na cikin damuwa da muradin jinsa a
jikinta, ya kuma abinda ke faruwa babu wata cikakkiyar fahimta da fuskantar juna
tsakanin matan nashi guda biyu! Laifin waye? Nasa? Ko Halisa da take ƙarama kuma
uwar gida? Ko kuma Zahrah mai zuwan yanzu data kasance Amarya kuma gaba da Halisa a
shekaru.
Horn ɗin mota ya dawo da shi cikin tunaninsa ya ware idanun yaci karo da motar
Father dake shigowa cikin gidan lokacin kuma Halisa ta fito hannunta riƙe da jakar
da Mother ta bata, Yaa Sheikh ya ɗauke idanu yana daidaita kansa da kyau tare da
juyawa ya miƙawa Halisa hannu ta kama ya dawo da ita kusa da shi yana amsar liƙab
ɗin hannunta zai saka mata ta ce
"Modibbo ka barni kamar zan faɗi nake ji" ya riƙeta da sosai ya ɗaura mata daidai
kunnenta cikin lallashi ya ce
"Dole ki saba Zawja"
Mother ta ce "Kinga na manta na baki wannan....," Maganarta ya tsaya lokacin da
sukai idanu biyu da Father ya fito daga mota shi da Maimoon, Auta sama sai Zeefa da
kuma Jaddada. aka shiga kallon kallo, Father ya yi baƙi ya lalace ya fita
hayyacinsa kamar ba mijin nan nata ɗan gayo ba, Jadda baki ya mutu sbd halin da ɗan
ta ke ciki, babu jimawa kuma wata motar ta sake shigowa Uncle Haroon da Uncle
Bashir ne a ciki. Yaa Sheikh ya juya zai shiga mota Uncle Haroon ya ce
"Malam Aliyu ai da ka tsaya ko?" Ya saki hannu motar tare da harɗe hannunsa yana
rufe idanu. Mother ta kalli Maimoon da Idanunta ya yi jajir sosai, ta ce.
"Are you sick?" Maimoon ta kasa magana ta fashe da kuka tana zubewa a ƙasa tare da
riƙe ƙafar Mother, Zeefa da Auta Fattoumah ma sukai elxty what Maimoon did.
Kuka suke sosai gwanin ban tausayi, a raunace Father ma ya tsuguna ya ce "Maryama
na sani, wallahi na sani kuma hakkinki dana Yaa Sheikh ke bibiyar rayuwata, ban
cancanci ki tausayi mini ba idan nayi kamar na haƙura dake sai naji babu wacce nake
buƙata a cikin rayuwata sai ke ɗin nan, wallahi Barrister IDAN BA KE na tabbatar
rayuwata zata iya salwanta, babbar isharar da Ubangiji ya nuna mini yadda ƴata ga
cikina Fattoumah take cewa ta tsaneni, wacce kalar jarrabawa ce wannan" Ya fashe da
kuka ganin yadda Mahaifinsu ke kuka ya sanya gabaɗaya ya ran suka sake fashewa da
kuka sosai. Ya ƙara riƙe ƙafarta ya ce
"I made a mistake, a mistake I can't fix,But let's take this as the determination
of the existence of Muhammad,
Destiny is the cause, be patient and forgive me for the blessings of God and our
children"
Tausayi ya kama Mother irin tausayin _Mata zuwa ga mijinta_
Uwa uba yaranta da rayuwarsu ta fara lalacewa. Jadda ta matse hawaye ta ce "Harfa
cewa nayi zan ɗaga mishi nono, gashi tun ban ɗaga ba rayuwarsa tana gantali
tsakanin duniya da lahira, ni dai an fitar mini zakka a cikin yarana naga Nahwu
naga aya akan Aliyu, amma hannunka ba zai taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ba, kiji
tausayinsa ko ɗan mitsitsi ne ki yafe masa kana ki koma gidansa ku rungumi yaranku"
ta kece da kuka sosai ta ce
"Wallahi gorin duniya nake jiye musu, a dinga nuna su da baki ana babansu ya yi wa
wata cikin shege harta haihuwa"
Uncle Haroon ya kada baki ya ce "Sai haƙuri fa"
"To ba ya zama dole ba? Haka fa Ubanku ya yi daman ance shi hali ɗan akene ya mutu
tare da bar masa mugun gado"
Uncle Haroon ya yi shiru
Jadda ta ce "Naga duk kun tsare ni da idanu? Ku ɗin nan Ubangiji ne ya taƙaita da
kuma ƙarfin addu'a kwarankwasa da a shegu za kuzo duniya, muta ta addu'a kullum ina
kuka cikin dare sbd Ubangiji yafi duba zuciyarta har ya shiryu, shi ya sa duk
abinda zaka aikata a duniya ka tuna cewa zaka haifa, idan baka haifa ba za'a haifa
maka, gado kuma jini yake bi gashi nan Ali ya kwashe Iskancin da ubanku ya yi"
"Yanzu ai ba wannan maganar ake ba"
Ta kalli Uncle Bashir ta ce "To ita nayi niyya babu ruwanka dani" Engineer Aliyu
dai yana tsugune ya ƙara cewa "Ki rungumi ƙaddara ki dawo gareni don Allah, wallahi
wallahi Ina son ki IDAN BA KE I can't be..."
"Ya Isa, Allah ya yafe mana baki ɗaya" cewar Mother. Ta ɗago Auta Fattoumah ta
rungome Idanunta ya yi jajir, Jadda ta ce "A'a bana son mugun abu irin naku na
lauyuyi cewa zaki na yafe maka Ali kuma zan koma gidanka" kai tsaye ta ce
"Zan koma Albarkacin yarana" Father ya saki Ajjiyar zuciya. Zeefa ta ce "Father ka
tashi Mother ta yafe maka" ya miƙe ya dubi Yaa Sheikh ya ce "Ka yafe mini kai ma
Aliyu don Allah" Yaa Sheikh ya jinjina kansa kawai yana buɗe ƙofa zai shiga mota.
Jadda ta zabga Salati ta ce "Muhammadur Rasulullah s.a.w wa nake gani haka kamar
ƴar Fulani wacce aka ce ta sai da nono"
"Ni ce" Halisa ta sauke Glasses tana faɗar haka, Jadda ta ce "To baki da lafiya ne
naga kin kumbura?" Tayi shiru sai kuma ta ce "Allahamdulillah"
"A'a wallahi da sauƙi, ina lafiya a wannan ƙibar kamar anyi miki fanfo, koda yake
ai ga Malam nan yasin da ban gane shi ba, kalli yadda kumatu