Showing 135001 words to 138000 words out of 196133 words

Chapter 46 - IDAN BA KE by Nimcyluv sarauta

09 Jun 2026

105

Mother ta nemi waje ta zauna ta ce
"I saw that you were crying" ta yi murmushi ta ce "Barci na fara"
"You supposed to do that, but not now" Halisa ta ƙara yin murmushin ƙarfin hali
tare da yin ƙasa da kanta irin al-kunya nan ta Fulani
"Your grandfather is calling you, ki saka hijabi ki fito"
A sanyaye ta ce "To" ta miƙe tare da ɗaukan wani hijabi sage green ta saka
Kyakkyawar fuskarta ta bayyana wacce ta ƙara haske da cika, ta zura slippers ta
nufi Main parlour. Cikin ƙaramar muryarta tai sallama ta nufi tsakiyar parlourn ta
zauna ƙasan carpet ta ce "Gani Jon wuro" Ya kalleta ya ce "Tashi ki bi mijinki
Halisa" zuciyarta ta buga da ƙarfi tai ƙasa da kanta ta kasa cewa komai, Yaa Sheikh
ya jingina da jikin ƙofa idanunsa a kanta, sai yanzu ladamar furta abin da ya ce ta
lulluɓe shi, amma a yanzu ko haƙuri ya bayyanar Abba ba zai ji ba, kuma ba zai
saurara ba.
"Magana nake ki tsaya mini, ba daman an saka muku ido ba? Yanzu an cire tashi ki je
Allah ya tsare ya bada ladan aure" hawayen da take maƙalewa ya gangaro zuwa
fuskarta cikin Muryar kuka ta ce
"Kayi haƙuri nai kuskure Jon wuro ba zan sake ba, ina neman alfarma a gareka ka
janye batun na bi wani, ka barni na zauna tare da ku" da sauri Mother da Umma
A'isha suka kalli Halisa ba wasa ko sakin layi a cikin maganarta. Abba Hakimi ya ce
"Mijinki ne, bana wani ba ra'ayinki shi ne zaki ba, amma ai kina son shi meye
dalilin haka?" Ta saki murmushi sosai ta ce "Bana son shi Abba, bana son zama da
shi, ina son ya bani ta kardar sakina kamar yadda ya furta" Mother ta ce "Ai ba ai
sakin ba, cewa ya yi idan ki ka tafi kuma ai kina nan" ta kalli Mother ta dawo ta
kalli Yaa Sheikh ta ce.
"Amma ai ya yi niyya? Kuma Ubangiji da ita yake amfani Mother, Yaa Sheikh jikina ya
ke so bani ba, ba kuma farin cikina ba, na ɗauka shi da kan shi zai ce naje ga
dangina sai naga saɓanin haka, ban san kowa ba sai Hamma Khalil da Hamma El duk da
bana jin zan amshi shi matsayin yayana, ba zan zauna da Yaa Sheikh ba, ba zan zauna
da shi ba, zanta zama a wajanka Jon wuro zuwa sanda zan haihu ya sakeni nayi idda
na samu miji nai aure" Yaa Sheikh ya runtse idanunsa jiri na neman ɗaukan shi, yana
hasko rigima a idanunta amma bai hasko wannan tashin hankalin ba, wanda ba zai iya
ɗauka ba kuma ba zai jure hakan ba.
"Daughter kin yi kuskure, kin fahimci Yaa Sheikh ba daidai ba, kada kiyi amfani da
ƙaramar ƙwaƙwalwarki ki datse soyayyar dake tsakaninku, kada ki hau tubalin da zai
kai ki zuwa ladama, ita *DAUƊAR GORA* ciki kan shata (Real Smasher)" Halisa ta
fashe da kuka ta ce
"A lokacin na so shi,kamar bana son kai na, babu abin da nake muradi a duniya sai
shi kaɗai a rai na, Mother tana bi jire bani Abbina da yanzu ni ba Matar shi ba ce,
kawai yanzu naji ba zan iya zama da shi ba" Mother zatai magana Abba Hakimi ya ɗaga
mata hannu ya ce
"Ba a shiga sha'anin mata da miji sai kiji kunya, ki bari tabi abin da zuciyarta ta
yanke mata" _A decision of the heart,
What the heart chooses._
"Allah ya kyauta,ya kawo sauƙi cikin lamarin" cewar Umma A'isha. Abba Hakimi ya ce
"Jeki Allah ya yi miki Albarka!" Ta miƙe tsaye zata koma bedroom bai san mene ya
faru ba, sai ganin shi ya yi tsaye a gabanta riƙe da hannayenta ya kafeta da
jirkitattun idanunsa masu laushi da nuna tsantsar buƙatar miji zuwa ga matar shi.
Ya kasa magana sai launin idanunsa daya sauya ƙwarai, zafin zuciyar shi ya fi
ƙarfin ya bayyana yadda yake ji a cikinta, tamkar gobara ce ta tashi wani ke ƙara
tuttula mata fetur.
"Nasan ba gasky bane Zawja" ya faɗa a taushashe cikin wata kalar muryar shi kan shi
bai san ya faɗi hakan ba. Ta kalli cikin idanun shi ta ce "Babu ƙarya a irin riƙon
da kayi mini, babu kuma wasa a irin darussan daka bani, dan haka ban taɓa ƙarya ba
kuma ba zan fara akan ka ba Malam Yaa Sheikh"
Ya fesar da numfashi ya kasa magana ya yi ƙoƙarin jawota ya rungome ko zai ji
nutsuwa tayi saurin bige hannunsa ta ce.
"Ina jin al-kunya sbd shekaru da furfurar dake tare da kai, baka duba halin da zan
shiga ba da ace ka sakeni, ka manta da kai ɗaya nayi sabo, dan haka wannan ya zama
First and last da zaka ƙara kai hannunka jikina, domin na haramta a gareka,
kyautatawa ɗaya zan maka shi ne ɗan ka da zan raina a cikina na kuma shayar da shi
nonon da ka ke kwaɗayi" cikin harshen larabci ya ce
"Zawja ki fahimta *_IDAN BA KE_* kamar babu Aliyu ne" ta kalle shi sosai ta ce.
"Sai wata rana" ta juya da sauri zuwa bedroom ɗinta, kuka na ƙwace mata, Allah ya
ji ya gani tana son Abbanta amma dole ya barta ko yasan zafin so da kuma raɗaɗin da
take ji na abin da ya yi mata. Yaa Sheikh ya sulale ya zauna saman kujera ya dafe
kai da hannu bibbiyu, daman tuni su Mother suka bar wajan. _When all is gone_
A wanann rana da kuma daren zuƙatansu da zuciyoyinsu basu zauna lafiya fa, _The
night was long for them, a dark night and the heart was filled with sorrow_ sun
rasa ya ya za su yi, _The night that prevented them from sleeping, the love and
passion for each other entered their hearts more and more_
Da asuba Yaa Sheikh bai iya jan jam'i ba, sbd zazzaɓin daya rufe shi da wani
wahalallan ciwon kai, da ƙyar ya iya zuwa masjid ɗin.
Da azumi ya tashi har wajan ƙarfe 12 bai ta shi ba. Misalin 2:45 ya shigo cikin
parlourn sanye da shadda cream colour babbar riga da ƴar ciki, ƙafarsa sanye cikin
Black Gustavo parent italian leather Tassel Loafers sai ɗaukan idanu takalmin ya
ke, hannunsa maƙale da Rolex na Companyn Daytona. Ƙamshin Roja ya sanya Ummul ta
ɗago kanta, suka haɗa idanu tayi saurin janye nata, domin ƙarara tashin hankali ya
bayyana a fuskar shi, Dattijo da Hajia suka kalli Yaa Sheikh ta ce.
"Mai gidana shigo mana kai tsaye" ya dai tsaya ta ƙara cewa "Lafiya dai?" Ya ƙara
yin shiru ta gyara zama ta ce "To kaci kan ka, wallahi nafi ƙarfinka sai dai uwarka
gata nan" Ummul dai tayi murmushi kuma bata kula Yaa Sheikh ba, alrdy Mother ta
sanar mata komai, hakan ya yi mata daɗi duk da abune mai wahala Halisa ta ce dole
sai ya rabu da ita, ya ƙarasu ciki ɗauke da Sallama kan akan cinyar Ummul ya gaida
kakannin na shi.
Shi bai magana ba Ummul ba tai ba, can ta ce "Ɗaga ne da na kawo maka lunch" ya
girgiza kai ya ce "Azumi" ta ce "To Allah ya bada lada" a hankali taji gabaɗaya
kan shi ya ɗauki zafi sosai ta taɓa kan ta ɗauke hannu ta ce "Baka da lafiya?" Ya
ce "Lafiya lou" tai ta kallon shi. Ta cire hiramin ta dinga shafa sumar kan shi
tana masa addu'a, a haka taji saukar numfashi shi ta leƙa taga ashe barci yake.
Wasa wasa sati guda ya shuɗe, na biyu ya shafe, na uku ya shige sati huɗu cif bai
sanya Halisa cikin idanunsa ba, ko gilmawar ta baya gani.
Halisa kuma sai ta fahimci baya gidan take fitowa parlourn suyi hira, da zarar taji
motsi ko ƙamshin turaren shi take barin wajan. Tana shan wahala amma haka take
jurewa cikin dare tayi ta kuka tana riƙe ƙafa, ta faɗa sbd buƙatar mijinta da take,
Yaa Sheikh baya bambance Alhamis da Litinin kullum cikin azumi yake,ya rame sai
fararen idanunsa da suka ƙara fitowa. Zahrah ce kwance gadon asibiti Jikinta na
rawa, na'urar room ɗin sai ƙara take, Surry ta riƙe ta riƙe Muhammad sosai, cikin
sauri Mimi da Dr suka shigo ganin ba zai iya ba, ya ƙara kiran wasu likitocin aka
nufi emergency da ita, da ƙyar suka shawo kan matsalar. Alhaji Farouk da Mimi suka
kalli Dr ta ce "Ban fahimta ba Dr mene ya samu yarinyata?" Ya gyara zama yana zame
Glasses ya ce "Bayan hawan jinin da take da shi, ciwon zuciya ya shige ta da ƙarfi,
bai kai matakin aiki ba, amma irin shi da wuri yake kisa, domin ganin yarinyar ku
ta ci-gaba da rayuwa a duniya ya zama dole ki bata abin da zuciyarta ke so" Kuka ya
ƙwacewa Mimi Alhaji Farouk ya ce "Me take so har haka? Idan kuɗi ne akwai komai
take so za a siya mata" Mimi tana kuka sosai ta ce "Abin da Zahrah ke so, kuɗi bai
isa ya siye shi ba, ko da zaka ƙarar da gabaɗaya dukiyarka ne, ba zaka sama mata
Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu ba" Alhaji Farouk ya miƙe ya ce "Dole naje na samu
mahaifiyar Yaa Sheikh da Abba Hakimi tun da mahaifin shi baya duniya ya zama dole"
Cikin dare wajan ƙarfe 3 Halisa na zaune a saman kujera hannunta riƙe da ice cream
wanda Maimoon ta siyo mata a Havilla, ta saka a freezer ya ƙara sanyi tare da
ƙanƙara. Ta lumshe idanu tare da siɗe ƙaramin cokalin da baki sanyi na ratsa ta
sosai, yana ƙara sanyata cikin wani hali feelings mai tsanani na ta so mata, ta
ajjiye ice cream tare da miƙewa tsaye daga ita sai Riga da wando na Pajamas white
colour Yaa Sheikh's favorite colour ta sanya Scuff faux-shearling slippers sai
ƙamshi take ƙirjinta ya ƙara cika, ta miƙe zata juya zuwa cikin bedroom kenan ta ji
an ɗaga ta cak tare da fara tafiya da ita...[1/18, 1:37 PM] Abk:
https://vm.tiktok.com/ZMYJCVDeF/

Ka shiga link ɗin ka faɗi kalma ɗaya mai kyau akan littafin idan ba ke👆🏾08119237616

Ko ba a faɗa ba, tasan shi kaɗai ne zai iya yi mata haka, ta shiga kokawa zata
ƙwace kanta amma ta kasa, ta daddage ta fasa ihu ta ce
"Wallahi zan maka ihun kwarto idan baka sauke ni ba" bai shirya tunan asirin da
take shirin yi masa ba, ya yi saurin dire ta ƙasa yana riƙe da hannayenta, kalmomin
da zai mata bayani yake ta harhaɗowa a bakinsa amma ya kasa samun cikakkiyar kalma
ko ɗaya, ganinta kusa da shi ba ƙaramin barazana bace ga zuciyar shi da kuma abin
da ke addabar shi tsayin satittika.
Ya numfasa yana riƙe kan shi gudun kada ya yi abin kunya a gaban ƴar ƙaramar
Yarinyar dake neman jan shi a ƙasa ya ce "Zawja ni ne kwarto?"
Ta kame fuska tare da ɗauke kai can, ganin yadda muryarta ke tasiri a zuciyar Yaa
Sheikh take saukar masa da nutsuwa yasa ta ƙara tsuke ɗan ƙaramin bakinta.
A raunace cikin wani sabon yanayi mai wahalar fassaruwa YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR
ALIYU ya furta.
"Zawja ƴar fillona come to your husband, why are you doing this to me, am I
stranger?" Cikin ƙarfin hali, da rashin nutsuwar Zuciya data gangar jiki ya furta
hakan.
Halisa ta ƙwace hannunta tana yin nesa da shi taƙi cewa komai, babu alamar tausayi
akan fuskarta... Taurin kan yarinyar ya bashi mamaki bai san lokacin data sauya ta
zama mai kafiya da naci haɗi da zafin zuciya ba. "Anya kina son rabauta da ribar
dake cikin zamantakewar aure Zawja? So ki ke na zama Ayuu!?"
Ya yi shiru da nufin ko zata tanka masa amma tai mursisi dole ya tsuguna ya lashe
aman da ya yi mai datti da wari, daman tabarmar kunya da hauka ake kwashe ta.
"Na yi miki al'ƙawarin idan akan taɓa jikin ki da nake ki ke wannan kumfar bakin,
to na haƙure zuwa lokacin da ranki zai fari, bana son ki ƙaura cewa Idanuna, IDAN
BA KE ba san ya nake b" sai lokacin ta kalle shi ta ce.
"YAA SHEIKH" Ganin kamar da gayya ta faɗi sunan na shi ya sa kawai ya bita da
Idanu, yanzu ta dai na bashi mamaki, kallon mara tausayi wacce bata amsar uzuri
yake mata.
Ta kalle shi ta ce "Ba jikina ne bana so ka taɓa ba, so nake ka haƙura dani na
tsayin shekarun da suka rage maka a rayuwa, ka yi zuciya ka bani takardar sakin
daka furta kuma ka ayyana a ranka YAA SHEIKH ALIYU" cikin rawar murya YAA SHEIKH ya
ce
"ƙarya na ke, iya laɓɓa kawai na furta haka, IDAN BA KE babu wata rayuwa da zan
iya" dariya ta so kama Halisa amma ta danne tana dafe ƙirji ta ce "Asstagafirullah,
Allah na tuba ka manta ƙarya haramun ce?" Bai ƙasa a gwiwa ba wajan furta.
"Ni ba Manzo ba, ni ba sahabi ba, ni bawa ne na Allah, a koda yaushe zan iya kauce
hanya!"
Ta ware hannunta irin "Anyway, is not problem"
Ya langwaɓe kai ya ce
"Kin yarda IDAN BA KE babu numfashin Aliyu" ta nuna shi da hannu ta ce
"Wallahi ba zan koma gidanka ba, idan har ni ce kwanciyar hankalinka to ka shirya
tafiya lahira da kwanan kabari" tana faɗin haka ta juya tana kaɗa masa ƙugu wanda
suke ƙara sanya YAA SHEIKH cikin wani hali wanda shi kan shi ba zai iya furta ko
fasalta yadda ya ke ji ba.
Ya zube akan kujera yana dafe kan shi, bakinsa ɗauke da addu'ar samun sassauci da
rahamar Ubangiji. Ya miƙe a sanyaye tare da nufar part ɗinsa yana zuwa ya nufi
bathroom ya sakarwa kan shi shower da ruwa mai sanyi, ya daɗe tsaye yana mayar da
numfashi. Ya ɗaura alwala yana fitowa ya saka Jallabiya Viridian green mai ƙaramin
hannu, ya ɗauki hirami ya ɗora a kan shi tare da ɗaukan prayer mat ya shimfiɗa.
Sallah ya yi raka'a biyu raka'ar farko ya karanta Fatiha da Surah Kafiroon, ta biyu
ya yi Fatiha da Surah Al Ikhlas. Cikin sujjadar ƙarshe ya shiga faɗin.
" ‫ َفِإ َّنَك َتْقِدُر َوال‬،‫ َوَأْسأُلَك ِمْن َفْضِلَك اْلَعِظيم‬،‫ َوأْسَتْقِدُرَك ِبُقْدَرِتَك‬،‫َالَّلُهَّم ِإِّني َأْسَتِخيُرَك ِبِعْلِمَك‬
‫َأ‬ ‫َأ‬

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login