Showing 111001 words to 114000 words out of 196133 words
cewa komai da sauri kuma ya rufe tafin ƙafar Halisa da bargon
asibitin, a tsari nashi babu abin da za a gani a jikin iyalinsa sai fuska itama
dan ta zama dole ne.
"Da alama an yiwa zuciyar Malam mugun kamo, naga alamar ya kusa zama jani talau"
sai a lokacin Yaa Sheikh ya ware gajiyayyun Idanunsa akan Khalil ya ce. "Kamar
amaryar a lalle?" Khalil ya saka dry ya ce "Ai ba kamo na aure ba, kamo na zuciyar
data kamo da soyayyar wani, _Love of the opposite sex_"
"To akwai wanda na taɓa cewa ban so?" Khalil ya ce "Eh, babban misali ƴar fillon
nan kace baka sonta, ƴar ce wajanka, auren dole ne fa ko ka manta" Yaa Sheikh ya
kame fuska yana yin gaba ya ce "True love, between heart to heart, ka daina
munafurci Khalil Ahmad Sarki, Ubangiji ya yi hani da shi"
"Ba batun munafurci, nafa ɗauka zanga ka rame ka fita hayyacinka, kasan auren dole
masifa ne" Yaa Sheikh ya tsaya cak tare da juyawa suka kalli juna sai kwarjinin Yaa
Sheikh ya cika idanun Khalil, kusan age mate ne tsakanin Yaa Sheikh da Khalil shi
ya sa yake yawan jan Yaa Sheikh da hira,wani lokacin ya biye masa wani lokacin ya
share. Ga mamakin Khalil sai yaji Yaa Sheikh ya ce.
"Wanne kalar so ka kewa Oum Juwairah? yaushe kuka haɗu" Khalil was silent trying to
remember the time, day, month, and year. "I can't remembering, but a school muka
haɗu, time ɗin shekarunta 20"
Al'ajabin ganin murmushi mai laushin cike da kamala a fuskar Yaa Sheikh ya kusa
zautar da Khalil ya ce.
"What make you laugh?"
Suna tafiya a jere sun jima kafin Yaa Sheikh ya ce. "Shirmen Khalil, ka kwatanta da
yarinya da akan idanunka aka raini cikinta, ka raɗa mata suna, ka goyata a bayanka,
ka raineta da hannayenka, ka kalli Kyakkyawa fuskarta ta yarinta ka ce _IDAN BA KE_
ba zan iya rayuwa ba, ya zaka kwatanta da Oum Juwairah?"
Khalil ya ce "Tab, to ai ba zan iya haɗa son ta dana ko wacce ƴa mace ba, zan ce
mata IDAN BA KE ba zan ƙara aure ba"
Yaa Sheikh ya girgiza kai ya ce "Ka ɗauka idan ba ita babu rayuwar wanda ya reneta
ne, ba komai ake bayyanawa ba, wani abun sai dai gangar jiki tayi aiki" Khalil ya
saki baki domin ya gama ƙaddara wa ba Yaa Sheikh ne gabansa ba, yafi masa kama da
Yaa Lee. Har suka ƙarasa harabar asibitin Khalil ya kasa cewa komai.
Suna zuwa suka shiga mota, daman zuwan Khalil ƙasar kenan, Abba Hakimi da Mai
martaba a mota ɗaya, Umar-khan ya jasu domin El-bashir yana barci.
Ɗaya motar kuma ta Yaa Sheikh Khalil ya shiga masanin driver Yaa Sheikh bai fiya
driving ba sai dole, motar da Khalil ya shigo da ita asibitin kuma tun ɗazo Ishaq-
Hakim ya tafi kai saƙon mother.
Kasancewar Khalil baya driving a hankali duk da faɗan Yaa Sheikh amma sai da ya
riga su Umar-khan zuwa, cikin sa a yana sauka motar su drivern su Maimoon na sauka.
"Am lucky wallahi da rabon zanga amaryar dake wahalar da zuciyata" Yaa Sheikh ya
taɓe fuska ya jima da sanin Khalil na son Maimoon amma taƙi bashi dama.
Suka fito kai tsaye Yaa Sheikh ya yi cikin gida suka jera da Abba Hakimi da Mai
martaba suka zama kamar wasu abokai ko sa'anni. Naomi tunda ta hango Khalil ta haɗe
fuska ya ƙarasa yana cewa. "Autar Mother an girma" Auta Umar-khan ta ce "Ina yini
Uncle K" ya ce "Lafiya" Zeefa ma ta gaida shi ya ce "Maza ku shiga anjima samu
shopping amma banda mara gaida mutane" Maimoon ta ƙare haɗe fuska ta ce
"Ina yini Uncle?" Ya haɗe fuska ya ce.
"Yana kwano, ni ki ke bawa wahala ko Moon?" Ta tura baki ta ce "Me nayi kuma?" Ba
wasa a fuskarsa ya jingina da jikin mota yana harɗe hannu ya ce.
"Saboda ina son ki? Shikenan na haƙura kije ki auri wanda ki ke so, nima zan nemi
wata, be happy" maimakon tai farin ciki sai yaga ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye
na zuba a idanunta. Ya saka hannu ya tallafo haɓarta ya ce.
"Meye kuma? Na ɗauka farin ciki zaki yi?" Ta fashe da kuka ta kasa cewa komai.
Ganin ba mutane a wajan ya miƙa mata hannu ya ce "Zonan" kanta a ƙasa ta ƙarasa
wajan shi sai kuka take kamar yarinyar, ya riƙe hannunta ya ce.
"Ya akai? Meye na kuka Prince guda kince baki son shi ba dole na haƙura ba" ita dai
Maimoon kuka kawai take ya riƙe hannun ya ce. "Ok tell me, do you love me? Do you
want to marry me?" Ta kasa cewa komai ta yi saurin shigewa jikin shi tana kuka, ya
saki dariya yana rungometa ya ce "Oh! Ina ganin halin kwailaye ni Ibrahimul-khalil"
Shiru parlourn ya ɗauka, Abba Hakimi, Mai martaba, Father wato Engineer Aliyu,
Uncle Haroon, Uncle Bashir, sai Oga Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu!
Ɓangaren mata kuma, Mother, Umma A'isha, Zahrah, sai Yaya Halima, tare da Jadda
wacce ta kafa ɗauri a gaban goshi kaɗan take jira.
Aka kasa samun maiwa su Abba Hakimi bayani Jadda ta miƙe ta nufi bedroom ɗin Zahrah
baby boy ɗin na barci cikin kwanciyar hankali ta figaloshi tana Asstagafirullah! Na
taɓa ɗan shege da tayi.
Tana zuwa ta ɗora jaririn a kan cinyar Zahrah ta ce
"Ubangiji kawai nake tsoro ba wani shege, a yau idan Malam bai saki Zura take kowa
wallahi ban cika ƴar banza ba, kuma duk abin da aka kashe na aurenki sai an biya,
tunda cakawa Malam akai, ashe dauɗa aka bashi raguwar masu gajeren wando" ta
girgiza kai ta ce.
"Na rantse da zatin Ubangiji nafi shekaru arba'in rabon da naga ɗan shege sai yau a
gidan Hakimi" Abba Hakimi ya kalli Umma A'isha ya ce.
"Meke faruwa Aishatul-humaira?" Umma A'isha ta sauke numfashi ta ce.
"Matar Yaa Sheikh ce ta haihu ɗazo, yaro namiji" Da sauri Father ya kalli Zahrah
wacce take kuka sosai. Yaa Sheikh ya yi ƙasa da kan shi, Abba Hakimi ya yi ta
jinjina kai. Uncle Haroon ya ce.
"Ikon Allah, haihuwa kuma bakwaini kenan?" Jadda ta ce "Wanne bakwaini? Shekararran
ɗa a ciki, kalli fuskar yaron da kyau, da ƙyar bai gado iskanci a ciki ba" "This is
complicated, Sheikh kasan da cikin ne?" Yaa Sheikh ya yi shiru can ya ce.
"Ku tambaye ta" Uncle Haroon ya ce "I'll do the same thing har sai ka ban amsa,
kasan da cikin Zahrah" Yaa Sheikh ya ce. "Eh" gabaɗaya suka kalli Yaa Sheikh Father
ya ɗaga hannu zai ɗauke Yaa Sheikh da mari daga bakin ƙofa aka ce.
"Kada ka kuskura hannunka ya sauka akan ɗana Engineer Aliyu" suka kalli bakin ƙofar
zumbur Mother ta miƙe tsaye tana nuna matar da hannun ƙirjinta na ɗagawa kamar zata
shiɗe ta ce
"Ummul-khairy!" Ummul tai murmushi hannunta riƙe da key ɗin mota, Abba Hakimi ya
kalli Ummul da kyau kaifi ya ce. "Ɗanki kuma?" Ta ƙarasa shigowa ta nemi waje ta
zauna ta ce.
"Na katse muku hanzari ko? Ku gama sai muyi magana daka baya" Father ya ce.
"Ni da ɗan dana haifa a cikina za kice ɗan ki?" Ummul ta girgiza kai kawai ta juya
kan Zahrah ta ce.
"Kin tuna magana ta? The day you slapped me, you insulted Aliyu's grandfather, nace
zan nuna miki ikona a lokacin da ki ka san wacece ni, In sha idan harni na haifi
Arɗo a yau zan baki divorce paper ya zauna da zaɓin zuciyar shi" Father ya miƙe
cikin faɗa da ɗaga murya ya ce.
"Ke awa? Ni nake da ikon saka Aliyu ya yi abin da nake so bake ba, ɗana ne
mallakina ne" Ummul ta juya ta kalli Mother ta ce
"Barrister Maryam me ya sa kika ɓoyewa mijinki, while I doesn't f****** care" ta
juya kan Father ta ce "Tunaninka me? Biyayya Yaa Sheikh ya yi maka, baka san cewa
kafin ya amince sai daya samu yarda ta ba? Na maka uzuri"
Abba Hakimi ya gaji da jin duk wannan maganganun ya ce.
"Zahrah ɗan waye a hannunki" cikin kuka ta ce "Yaa Sheikh" Jadda ta miƙe tare da
dungure kan Zahrah ta ce.
"Annamimiyya to Allah ya isan malam Alkur'an"
"Aliyu? Kin tabbatar ɗan Aliyu ne?" Ta jinjina kai ya ce "Ya akai kuma kika san
Aliyu bai da lafiya? Kuma yakai ɗan ya zama na Aliyu bayan mu'amala bata taɓa haɗa
ku ba" ta fashe da kuka sosai ta ce. "Don Allah Abba kayi mini alfarma idan na faɗa
maka gaskiya ba zaka bar Yaa Sheikh ya sakeni ba, don Allah Abba wallahi zan iya
mutuwa idan babu Aliyu nayi ladama" ya jinjina kai ya ce "Inaji" ta share idanuna
ta ce.
"Ba ɗan shi bane, lokacin da mukai aure ina da cikin wata huɗu" Jadda ta hangame
baki ta kasa cewa komai. Ta ɗora da faɗin. "Nayi ƙoƙarin ganin na samu mu'amala da
Yaa Sheikh domin na ɗora alhakin cikin akan shi amma ya rusa duk wata ƙofa, har
maganin sha'awa na zuba masa wanda na tabbatar ba zai iya jurewa ba sai ya keɓe da
mace,amma bai kulani ba, Ummul ke sanar dani ai bashi da cikakkiyar lafiyar ɗa
namiji sai na faɗawa Father" ta rushe da kuka sosai ta ce.
"Don Allah Ummul kada ki rabani da mijina don Allah Kiyi haƙuri" Ummul murmushi
kawai take. Father kunya ta mamaye shi, ya kasa haɗa idanu da kowa tashin hankalin
shi bai shige yadda Ummul ke iƙirarin Yaa Sheikh ba ɗan shi bane.
Abba Hakimi ya sauke numfashi ya ce.
"Aliyu ya akai Halisa ta zama ƙanwar El-bashir?" Yaa Sheikh ya yi shiru Ummul ta
ce.
"Bari kaga babbar hujja sai ka gasgata da idanunka" ta miƙe tare da fita, wata
iriyar zabura Mai martaba ya yi dashi da Umma A'isha lokacin da sassanyar muryarta
ta ratsa cikin parlourn....
Littafin kuɗi
₦500
08119237616
Mai son posting har weekend 1k[1/6, 7:18 PM] Abk: Ba iya su Mai martaba ba, hatta
Mother ta girgiza da ganin wacce ta shigo, wani abu yake shirin faruwa mai kama da
almara banda haka yaushe zasu ganta a daidai wannan lokacin?
Abba Hakimi ya sauke numfashi yana girgiza kansa da son tabbatar da abin da
idanunsa suke gane masa, da gaske ita ce. Har kawo lokacin Mai martaba bai gasgata
abin da ƙwayar idanunsa ke gane masa ba, ya ƙarasa gareta yana mai gyara Alkyabbar
jikinsa.
Idanu cikin idanu wato eyeballs to eyeballs.
"Fulani" Mai martaba ya furta cikin rawar murya yana riƙe hannunta, ta dai kalle
shi ta kasa cewa komai amma irin kallon da take masa yafi kama da kallon wanda ka
sani shekara da shekaru.
"Fulani ke nake gani, da gaske ke ce?" Farin cikinsa ya kasa ɓoyewa har bai san
lokacin daya rungometa ba a gaban mutanan ya ce.
"Allhamdulillah! Lallai Ubangiji ya yi gaskiya,duk wanda ya yarda da Allah to zai
isar masa, you're still alive. Zuciyata bata yaudareni ba da kullum take faɗa mini
kina raye saɓanin wasu da ki ka zama matacciya a idanunsa, Shukru ilaika Ya Allah"
Ya saketa a hankali har lokacin bata ce komai ba, kamar bata gama dawowa daidai ba,
duba da yanayin yadda take kallon mutane.
Umma A'isha ta ce
"Nana idanuna ke gane mini ikon Allah, da gaske ke ce Nana?" Gabaɗaya idanunta ya
cika da hawaye bata taɓa tunanin zata ƙara saka ƴarta a cikin idanunta ba, Wacce
ake ta magana a kanta sai binsu take da kallo zaka ɗauka bata taɓa saninsu ba sai
yanzu. "Besty"
Ta ce tana nufar inda Yaa Sheikh yake zaune shi ma yana binta da idanu, tana zuwa
ta zauna kusa da shi tana riƙe hannunsa ta ce.
"Besty where is my daughter, ina Danejona take?" Abba Hakimi ya yi murmushi mai
sauti ya ce "Idan duniya da gaske daman bai ci a manta Besty ba"
Sai a lokacin Ummul ta saki murmushi itama tana bin su da idanu kafin ta ce "Ta ya
ya zata manta wanda yake kula da ita da wanda ya reni yarinyarta?"
Uncle Haroon ya ce
"Na kasa fahimta, kuyi mini dalla-dalla, Khadijah ba cewa akai ta ɓata ba? Ina aka
sameta aure ta sake har ta samu yarinya kamar Halisa? Ya akai Yaa Sheikh ya san
inda take, kuma ya akai Aliyu ya auri Zahrah bayan yasan akwai cikin wani a
jikinta? Meye dalilin El-bashir na son kashe jininsa, Ya akai Yaa Sheikh ya zama
ɗan matar nan bayan gabaɗaya mun Shaida ɗan gidan Engineer Aliyu ne da Barrister
Maryam? A fitar da zuciyata daga cikin zullumi wallahi kai na kulle kamar wani
drama haka nake ganin abin" Ummul ta ce.
"You don't have to be worries, i think this is the right time daya dace gaskiya ta
kuri ƙarya, kowa kuma ya san abin da yake ɓoye, duk abin da zai je ya dawo ku ɗauka
tsararre ne daga Ubangiji, hukumu lillahi ya tsara komai a lokacin daya so, ya
kashe wanda ya so, ya kuma raya wanda ya so, kada muyi baƙin ciki, har abada ba zan
taɓa amsar Arɗo daga wajanku ba, ina son dai kuyi mini adalci akan abin da zan faɗa
muku" Ummul is an educated, beautiful, intelligent woman in the community.
Mother ta riƙe hannun Ummul cikin kuka ta ce
"Don Allah ki rufa mini asiri Ummul-khairy, Wallahi ina son Aliyu kada ki rabani
dashi, ina jinsa kamar ɗan dana haifa a cikina" Father baya gane karatun da ake
idan hankalin shi ya yi duba to ya tashi.
Ummul ta ce.
"Kada ki damu Barrister, kawai ina son nunawa Engineer ƙarshen shi da yake son
tirsasa Aliyu yin abin da bai niyya ba, nayi imani da Allah ko kai ne ka haifi
Aliyu to a wannan karan ba zai iya yi maka biyayya wajan sakin Halisa ba"
Tai shiru tana sauke numfashi ita kanta zuciyarta babu daɗi a hankali ta ce.
"Ka tuna lokacin da matarka ta haihu acikin asibitin Specialist Yola dake Jimeta?"
Father ya jinjina kai yana furta.
"I remember the day, we went to visit Yola"
Abba Hakimi kallon Ummul kawai yake sai yanzu ya lura gabaɗaya nutsuwarsu ɗaya da
Yaa Sheikh, har yarda take juyawa hannunta da yadda take son tankwashe ƙafa lokaci
zuwa lokaci kuma tana son girgiza kai musamman idan abu ya bata mmki, ko acikin
wayayyun mata masu tarin ilimi da wahala a samu kamar Ummul-khairy Abdullahi Abdul-
majeed.
Ummul ta miƙe tsaye sai kuma ta zauna ta ce.
"A wannan rana ni ma ina cikin Specialist Yola, lokacin ina ɗauke da cikin Aliyu
rayuwa ta mini zafi, bana da kowa mijina daya kasance Arɗo cikin Rugar Bello Allah
ya yi masa rasuwa, wanda kuma kashe shi akai akan wani cikar buri, iyayena sun yi
nesa dani, infact bana cikin Familynmu sbd fushin da mahaifinsa ya yi, baya son
Abou-Aliyu ni kuma na kafe shi nake so, ya ce naje idai auren Fulani ne zan gani,
lokacin da mukai aure da Abou-Aliyu Arɗon Rugar Bello ban sha wahala ba, mun rayu
cikin farin ciki walwala kwanciyar hankali da jin daɗi, ban taɓa ɓatan wata ba.
Rana tsaka Arɗo ya shigo gida da ciwon ciki a ranar bai kwana da rai ba, gari na
wayewa aka naɗa sabon Arɗo, a cikin satin ciki ya bayyana a jikinsa, na fara shiga
wata sabuwar rayuwa, nasha wahala da taimakon Ubangiji na raini cikin nan, ranar
haihuwa a daddafe naje asibitin Specialist Yola dake ina da file acan, aka amshe ni
ina shiga kuma aka shigo da Barrister Maryam itama tana naƙuda, mu duka mun sha
wahala mun ɗauka ba zamu kai labari ba, cikin ikon Allah Barrister Maryam ta haihu
kuma namiji amma ya zo babu rai, sakamakon duguwar naƙuda da ruwan da babyn ya sha
a ciki, tana Haihuwa ni ma na haihu, kyakkyawan jariri duk da wahalar rayuwar da
muka sha amma girman Aliyu ya bani tsoro, sumar kanshi har rufe ido take saboda
yawa, tun a lokacin sumar kan nashi kala biyu ne, nayi farin ciki amma na kasa
bayyana shi a fili, a lokacin tunanin yadda zan kula da shi kawai nake, na lumshe
jajayen idanuna zuciyata cike da zullumi a hankali na kalli Barrister Maryam na ce.
"Ina tunanin addu'a za mu yi da Ubangiji ya sauke mu lafiya, baƙin ciki bai kamace
mu ba" cikin kuka ta ce.
"Dole nayi kuka, baki san tsayin shekarun dana ɗauka ina addu'ar Ubangiji ya bani
ciki na haihu, saboda uwar mijina ta takura mini tana tunanin ni juya ce, gashi
Allah ya amshi addu'a ta kuma Ubangiji ya amshi abin dana haifa" Nayi murmushi
kawai ina sauke ajjiyar zuciya mai nauyi kafin na furta.
"Riƙe Babyna idan kina so bani naki wanda ya rasu" bisa mamakina sai naga Barrister
Maryam ta tsorata komai take tunani a lokacin ohu! Kamar na shiga ranta na ce.
"Kada kiyi kaddama, ki ɗauka ɗana Aliyu shi ne wanda zai kawo daidaito tsakanin ki
da uwar mijinki, mu duka muna cikin damuwa bani da hali bani da ikon kula da Aliyu,
bani da wadatacciyar cimar da zan samu ruwan nonon shayar da shi, wandon da zan
sakawa Aliyu bani dashi, ina da zuciyar nema da tawakkali amma a wannan karan na
gaza, na bar miki Aliyu duniya da lahira na bar miki shi, ki ɗauka shi ne ɗan da ki
ka haifa yanzu, ni kuma Ubangiji zai bani wani a lokacin da ya so" ni kai na nasan
na faɗi hakan ne, akan rashin mafitar da bani da ita, da kuma son nemawa Aliyu
kyakkyawar makoma, ilimi, nagarta, kyakkyawar tofa. Farin cikin Barrister Maryam ya
kasa ɓoyewa da sauri ta amshi Aliyu,ni kuma na ɗauki babynta, babu wanda yasan abin
nan sai mu uku, ni, ita, da kuma wacce ta amshi haihuwarmu" Ummul tai shiru tana
sauke numfashi idanunta ya yi jajir, ta ɗago kai taga kowa kallonta yake anyi shiru
ana sauraranta.
Yaa Sheikh kallon Ummul ɗinsa kawai yake wacce itama take kallon shi.
Khadijah Dada tana kusa da Yaa Sheikh taƙi matsawa, ƙuruciyar shekarun sun motsa
yadda take very close da Yaa Sheikh koda iyayenta Abba Hakimi Umma A'isha ba tayi,
sun tasu tun suna ƙanana.
Ummul ta ɗauki ruwa ta sha kafin ta ɗora da faɗin. "Ban san cewa kuskura nayi ba
wajan sadaukar da jinina ga wacce ban sani ba, kullum da soyayyar ɗana nake kwana
nake tashi, gabaɗaya jama'ar Rugar Bello sun ɗauka ɗana ya jima da rasuwa, ni kuma
nasan yana nan yana rayuwa a duniya, gidan da yake, da rayuwar da yake duk na sani"
tai shiru kafin ta ce.
"Babban kuskuren da ki kai Barrister Maryam barin address details naki a jikin
file, na amshi komai wajan Dr, ashe har photo taiwa Aliyu, ganin rayuwar da nake
ciki ba sauyi na fara tunanin komawa gidan iyayena, senato Abdullahi Abdul-majeed,
a lokacin ya sauka kan mulki, ban sha wahala ba, domin iyayena suna bala'in so na,
na tattara komai nawa na fara neman aikin police na samu, lokacin nasan halin da
Aliyu yake ciki, shekarar farko ta zaman Aliyu a Madina a shekarar nima na sauka na
haɗa plan da komai, naje masa matsayin ƴar aiki ya kuma ɗauke ni, shi kaɗai yake
rayuwa Umar-khan ke musu girki da komai, a zahiri plan ɗin El-bashir ne zuwana
gidan Aliyu,a baɗini kuma nawa plan ɗin ne domin na samu connection da ɗana, tun
kafin bayyanar komai haka kurum Aliyu zai sakani a gaba da