Showing 114001 words to 117000 words out of 196133 words

Chapter 39 - IDAN BA KE by Nimcyluv sarauta

09 Jun 2026

113

kallo, sai nace masa
yaya? Sai kawai ya miƙe yabar wajan, wata rana na ce ko kana buƙatar wani abu, sai
naji ya ce.
A'a, ina ji kamar ke nake cikin barcina, nasan ƙwayar idanunki, kai tsaye na shaida
masa ni ce really mother ɗin shi biological. Ya kasa yarda ya ce mother ita ce
babar shi, nasan shi Dr ne a ɓoye a zahiri kuma Malami kuma lecture kuma kai D.N.A
test komai ya nuna ni ce babar shi, tun a lokacin Aliyu ya ɗauki ma'adanin ajjiye
sirrin shi saɓanin baya da yake da zuciyar shi, ni na bawa Aliyu shawarar kai Dada
Rugar Rome, a lokacin da akai mata kurciyya, Dada ta zauna wajan Abokin mijina,
yana da ɗa Yabi, suna zaune da matar shi Shatu, fitar Dada daga masarauta ya yi
daidai da bayyanar cikin jikinta, nan take aka Shaida mini ni kuma na faɗawa Aliyu,
duk sati sai yaje Rugar Rome, kaya kala-kala yake kaiwa Dada, lokacin da ya jima
bai ce ba, shi ne suka shiga mayuyacin hali, Aliyu da kan shi amshi haihuwar Danejo
ya gogeta da zaitun ya rungometa ya kuma raɗa mata suna Halisa ya ɗora da Danejo,
duk sanda zashi yana ɓoye kan shi baya bari aga fuskar shi, sunyi sabo da Halisa ya
goyata a bayan shi, yana mata waƙa wani lokacin ya ce _IDAN BA KE ba Aliyu_ har
takai shekaru biyar lokaci kuma Aliyu ya kwanta ciwo na tsayin shekaru, daga nan ne
bai ƙara waiwayar Rugar Rome ba, sai lokacin da za ai masa aure da Zahrah, rigima
sosai ya yi mini akan baya so, shi fa Halisa kawai zai rayu, na rasa soyayyar da
Aliyu ke mata,amma hakan baya rasa nasaba da soyayyar da ya kewa Khadijah, ba iya
Halisa ba son da Aliyu ya kewa El-bashir ya ɓaci, duk abin da El-bashir ke masa ya
sani, amma ya ce ba zai taɓa cin mutuncin jinin Besty ba"
Tai shiru tana ƙara ɗaukan ruwa ta sha kafin ta ce. "Auren Halisa da Yaa Sheikh ba
tsautsayi bane, everything that happens is a plan, Aliyu planned how to marry his
adopted daughter. I also supported him, na koma Rugar Bello da Aliyu kafin lokacin
nai musu bayani suka fahimta, nan take kuma ya maye gurbin Mahaifinsu na shugaban
Rugar, shi ne yasa a karɓe Naggen su Halisa daga wajan shugaban Rugar Rome, wannan
shi ne" jikin kowa ya yi sanyi ana zaton wuta a maƙera sai gata a masaƙa.
Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh ya ce.
"Malam ya akai kasan Inda Khadijah take bayan mun wayi gari ba ita cikin
Masarauta?" Kamar Yaa Sheikh ba zai magana ba sai ya gyara rawanin kansa yana
miƙewa tare da sauya waje, so yake ya yaki ce Dada daga gare shi tunda sirika take
wajan shi, ƴarta yake aure, bayan ya zauna ya ce.
"Abba na buɗe idanu a wajan Mother, Soyayya ta gaskiya ta nuna mini, ban san ya
akai na kasance wajanka ba, amma mother ta shaida yaye aka kawo ni wajan Umma
A'isha, lokacin shekarar Besty ɗaya a duniya, mun shaƙu sosai mun taso tare komai
tare, babu abin da nake sha'awa irin yadda Abba ke karatu tare da mutane tun ina
shekara goma na sauke Alkur'ani na shaddace Hadisai, a makaranta ɓangaren Islamic
nayi na samu abin da nake so, ina gamawa na juya fannin likitanci, lokacin da Mai
martaba ya nemi auren Besty ban damu ba, lokacin data bar gidan nan a Matsayin
Matar shi, dukkan wata walwala tawa ta ɗauke sai kuma a lokacin na gane ba Soyayya
ce ya shaƙuwa ba, abin yafi kama da wanda ka ke so ka rayu da shi irin ta har abada
ɗin nan, tun a satin farko na aurenta nake yawan mafarkinta tana kuka, bata cikin
kwanciyar hankali, kai tsaye na fahimci Aljani ne a jikinta wanda da bai bayyana
kan shi ba sai yanzu, baya ƙaunar kuma ta kasance a gidan mijinta, a wannan lokacin
kuma ta samu cikin El-bashir wanda ya ɗagawa wasu jama'ar dake cikin masarauta
hankali, bayan haihuwar El-bashir aka sakawa Besty idanu, Aljanin jikinta ya takura
mata, bayan shekaru huɗu da haihuwar El-bashir na saka Almajirai na saukar
Alkur'ani suka kwana suna yi, 10 a Sakoto tayi mini nasha wahala kafin Aljanin
yabar jikinta ta samu barci, sai dai tashin da tayi ta tashi da babbar ƙaddara ta
baza tare da fita daga cikin masarautar, komai take akan idanuna cikin sauri nabi
bayanta, da ƙyar na kamata zuwa mota na samu wani gida na ajjiyeta,naci gaba da
kula da ita tsayin shekaru 3 lokacin El-bashir yana sa shekaru 7. A lokacin kuma na
mayar da ita Rugar Rome, a shekara ta 8 da haihuwar El-bashir ta haifi Halisa,
wacce take shekaru 17 yanzu El-bashir kuma 25 suna da tazarar shekara 8, nasan El-
bashir yana mini kallon wanda na kashe masa mahaifiya ko na salwanta da rayuwarta,
wanda kuma bashi da wayo hakan ta faru akwai wanda ya zauna gina shi akan tubalin
ƙiyayya dani, Auren Zahrah kuma babu shi akai na domin ba a aure da ciki, na amince
zan aureta ne sbd hankalin Father ya kwanta dani kuma nayi masa biyayya kamar yadda
Ummul ta ce, na kuma rufa mata asiri, ya akai ta samu cikin ɗan waye ban sani ba,
amma nasan tana da dalilin aure na, na kuma san duk wanda ke farautar rayuwata"
"Ikon Allah, Al-hakkumu bowayi gagara misali!" Cewar Uncle Bashir.
Engineer kunya ta kama shi, tsoro da fargaba suka wanzu a zuciyar shi, tashin
hankalin shi ɗaya kada gasky tayi halinta akan shi.
"Sannu Aliyu, Sannunka kai da mahaifiyarka bamu da baki ko kalmar gode muku, kin
cancanci ki zama uwa ta gari" Abba Hakimi ya juya kan Zahrah ya ce.
"Ina da ikon da Malam, kuma nasan mahaifiyar shi zatai mini karar haka, nayi miki
al'ƙawarin da zarar ki ka faɗa mini gasky akan wannan jaririn to lashakka Malam zai
aureki a karo na biyu" kafin Zahrah ta ce komai wayar Yaa Sheikh ta ɗauki ƙara
ganin sunan Dr ya sanya ya ɗaga kiran.
"Hello Dr Ibrahim ke magana" Yaa Sheikh ya jinjina kai Dr ya ce.
"Mrs Yaa Sheikh Aliyu haydar ta farka daga suman da tayi, akwai babbar matsala muna
nemanka yanzu" Yaa Sheikh ya miƙe tsaye yana faɗin
"Gani nan" Ummul ta kalle shi sai ba tayi magana ba, Mother ce a sanyaye ta ce
"Aliyu ya dai?" Ba tare daya kalli kowa ba ya ce.
"Matar malam" duk suka kalle shi da rashin fahimta "Wace haka?" Cewar Mother sai a
lokacin ya fahimci mai ya yi ya ce "Ta farka kuma da matsala cewar Dr i think am
going.."
Abba Hakimi ya ce.
"Ɗan da kata, ina jinki Zahrah" Cikin kuka Zahrah kamar ranta zai fita ta ɗaga
hannu tare da nuna direction ɗin da Father yake zaune ta kasa cewa komai sai kuka
take tari na sarƙe numfashinta.
"Ɗan Father ne, shi ne ya yi mini cikin na rantse da Allah Abba.....

IDAN BA KE
Isn't free book is for sale, nrml grp 500 for Special grp 1k posting har weekend.
08119237616
[1/8, 7:03 PM] Abk: Cak Yaa Sheikh ya tsaya daga tafiyar da yake, tunda ake wannan
abun bai taɓa jin maganar data buge shi irin yanzu ba, ya kasa juyawa gani yake
kamar ba gasky bane, ji yake kamar ya nutse a wajan dan kunya, babu wacce yake jin
nauyi acikin wannan al'amarin kamar Mother, Father gumi kawai ke yanko masa idan ya
miƙe sai ya koma ya zauna
"Kin san me ki ke faɗa kowa? Kalamanki sunyi tsauri, tsaurin da ba ko wanne kunne
zai iya ɗauka ba" Zahrah ta ce
"Abba ina son Yaa Sheikh, akan soyayyar shi na yanke shawarar faɗa maka gaskiya,
wallahi Father shi ne Uban jaririn nan" da ƙarfi cikin ɗaga murya Father ya ce.
"Ƙarya ki ke, munafuka Algunguma ni zaki yaudara,ina matsayin abokin uban naki? Sbd
kuka ko muryarta baya fita ta dubi Father sai ta ɗauki wayarta tare da shiga vedio
ta play akan wani vedio tare da juya screen ɗin wayar zuwa ga father,
Kasancewar suna waje ɗaya da Abba Hakimi ne yasa shima yana daga zaune yanke hango
vedion.
"Amma ba zaka ka manta da vedion nan ba ko? Shi kaɗai ya isa ya zama shaida a
gareni?"
Jikin Father rawa kawai yake da ɓari. Su biyu ne a cikin vedion a ɗakin hotel
Zahrah na zaune Engineer Aliyu wanda aka fi sani da Father tsaye yana riƙe da waya
a hannu. Zahrah ta dube shi da kyau ta ce
"Na faɗa maka ina ɗauke ciki kuma naka baka yarda ba, ga Pregnancy Test ɗin da nayi
maybe zaka fahimta daidai" Father ya kalli Zahrah kafin ya karɓi result ɗin ya duba
ya ce.
"Kin tabbatar ciki na ne Zahrah?" Ta ce "Of course YES! Kada ka manta kai ne ka
amshi virgin ɗina" Ya yi murmushi ya ce.
"Ni ɗin? ni ki ke kira na amshi Virgin naki?" Ta miƙe tsaye ta ce "Oh! Ka manta
before hakan ya kasance nayi Virginity test?"
_The only way to know whether or not someone has had sex is to ask. There are no
physical examinations or tests that can reveal whether or not a person has had sex
before. No, not even so-called “virginity tests._
Ya ce "Ban manta ba, kawai nayi mmkin yadda cikin ya shiga ne, amma ya kamata a
zubar da shi kafin kowa ya sani" ta ce "Tab wai ba, ciki ɗaya, ciki biyu, ciki uku
duk kana sani subar dashi a wannan karan ba zan yi ganganci da rayuwata ba, kuma Dr
ya tabbatar cikin ba zai fita ba ka nemi mafita" Ya sauke numfashi ya ce.
"Ok shikenan, amma waye Deen da kuke mu'amala da shi kada kiyi mini ƙarya nasan
komai kina nufin shi bai isa ya ɗora miki ciki ba, ko shi ba namiji bane?" Yana
sauke magana ta ɗora da faɗin.
"Ya isa har ya kai, ba gwanda shi ba, tsakani na da Deen ya sauke mini sha'awata,
ta hanyar romance wani abu mai kama da sex bai taɓa shiga tsakanina da shi ba"
Father ya ce.
"Ki aure shi mana" da ƙarfi ta ce "I can't, cos I don't love him anymore ba zan
aure shi ba, idan kuma kana son Ubana ya san halin da ake ciki fine, Dady ne da
laifi daya sahale maka shiga gidan shi sama taka da sunan wayewa, sai yanzu nake
jin baƙin ciki da kuma taƙacin ilimin da nayi na shige ƙa'ida gabaɗaya wayewar
gidanmu bata amfane ni da komai ba" a rikice Father ya ce.
"Calm down please Beb, yanzu me ki ke so ayi?" Ta ce. "I want to marry your son
Aliyu" a firgice Father ya ce. "Kin san me ki k cewa, Aliyu fa? Kai ba zan iya ba"
ta ɗauki jaka ta ce. "Ok fine, zan sanar da Dady komai" ya yi saurin riƙota ya
rungome sosai ya ce.
"Is okey, na amince ki auri Aliyu kuma zan yi masa ta ƙarfi yadda dole sai ya
aureki, kuma ki ɗora alhakin cikin akan shi" Zahrah tai dry ta ce
"Gaskiya kai ɗan iska ne, ka ɗorawa ɗan ka cikin ka, to ɗan shi ne ko ƙanin shi?"
Father ya yi murmushi ya ce.
"I've no option, what ever yanzu muje ki ban kayan daɗi, banda ina mugun so da
ƙaunar Barrister wallahi da aurenki zan, amma inawa Barrister son da ba zan iya yi
mata kishiya ba" ta taɓa baki.
Cikin sauri Abba Hakimi ya ce. "Stop the video"
Ya faɗa yana runtse idanunsa ganin ana ƙoƙarin sake aikata zina ta vedion.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Uncle Haroon da Uncle Bashir suke ta
maimaitawa Jadda ta kece da kuka ta ce.
"Ashe dai ɗaga nono ya tabbata akan Ali, na haifi karuwi a cikina, na haifi ɗan
taure mai bin ƴan iskan mata, Allah ya saka mini Allah dai ya saka mini haihuwarka
da nayi, da nonona daka sha da tarbiyyar dana baka, wacce masifa ce wannan mutum
kamar wani Ayu!" Mai martaba ya yi ta jin abun banbara kwai, wai namiji da suna
Hajara, ganin abin yake kamar wani wasan kwaikwayo ko labarin littafan hausa da ake
faɗa..
"Ina jinki Zahrah"
A hankali ta ce "Tunda mukai haka da shi ya tafi ya fara neman hanyar da zai sanya
Yaa Sheikh ya aure ni, cikin haka aka samu matsalar daya sanya Yaa Sheikh dawowa
daga Madina ba shiri, lokacin da ya amince da aurena kafin ya faɗawa Dady ni ya
fara sanarwa, nasan da komai. kullum da fargabar yadda zan kasance da Yaa Sheikh, i
love him with all my heart and soul, ganin bani da mafita ya sa na nemi Deen da
ƙawata Surrayerh, ita ta bani shawarar neman yarinya...." Ta faɗa musu duk yadda
tsara plan na ɗaukan Halisa da yadda suka kai Dada asibiti, daɗin da ɗawa sun ƙara
yi mata asiri wanda ya yi tasiri a jikinta shi ya sa bata fiye damuwa da son zuwa
wajan mahaifiyar ta ta ba. Ta share hawaye ta ce
"I knw i made a mistake, but isn't my fault domin Deen ya amshi cikin da bana shi
ba da hannu bibbiyu, burinsa shi ma ya ɗorawa Yaa Sheikh laifin cikin, mun su dayin
auren Aliyu ya kasance dani yadda zan iya cewa bakwaini na haifa, hakan bai kasance
ba nasan na cutar da Yaa Sheikh da maganin dana bashi daga baya kuma na fahimci
tabbas ya je wajan Halisa be tunda matar shi ce, Sai yanzu na gane dalilin da ya
sanya Aliyu baya raɓar inda nake. Ci,sha, ya bani baya takura ni"
Tunda ake wannan abun banda kuka babu abin da Mother take ƙirjinta har ɗagawa yake,
baƙin cikin mugun tabon da Father ya barwa ya ranta shi ke damunta.
Abba Hakimi ya juya kan Father ya ce. "Engineer ka ɓata wayonka, ashe zaka iya yiwa
ɗan daka haifa sharrin da zan gina baƙin ciki a zuciyarsa, ya kuma ɓata kyakkyawan
tulabin halayyar shi da yake ciki?,
Nayi mamaki na kuma kasa fahimtar da gaske abubuwan da kake ji wani waje zai iya
faruwa a inda ka ke" Father ya goge zufa ya ce.
"Na amshi laifina, amma bani ka ɗai bane a family wanda yake son ganin bayan Yaa
Sheikh, sai ki faɗa musu sunan mutumin daya koma Deen" Yaa Sheikh dake tsaye har
yanzu sunan Allah kawai yake ambata a cikin ranshi, idanunsa sukai jajir jijiyoyin
kansa sun fito, sai huci yake fitarwa.
Zahrah tai shiru ta kasa cewa komai Father ya ce.
"Bani ki ka tunawa asiri ba?" Kai tsaye ta ce
"Duk abin da ya samu shamuwa watan bakwai me ya ja mata" Ya ce.
"Ok fine sai ki sanar da su Saif-wazir shi ne Deen stop lying to them" Abba Hakimi
ya dafe kai ya ce.
"Saif-wazir? How can that be possible? Meye nashi na son cin mutumcin Malam? Me ya
yi masa?" Daga bakin ƙofa Saif-wazir daya shigo yanzu ya ce.
"Saboda ka fifita ɗan wani fiye da ɗan daka haifa a cikinka Abba" Abba Hakimi ya
miƙe tsaye bai tsaya jiran komai ya saka hannu ya ɗauke Saif-wazir da mari ya ƙara
ɗauke shi da mari, ya jera masa guda biyar a jere da sauri Mai martaba ya riƙe
hannun Abba Hakimi ya ce
"Idan rai ya ɓaci, nutsuwa ke nemu shi, marin ba mafita bane" Saif-wazir ya kalli
Abba ya ce.
"Like this, irin haka sune suka sanya mini tsanar Yaa Lee, kaƙi bawa yaran daka
haifa space a zuciyarka, har dukiyar dana mallaka sai dana rasata dalilin Yaa Lee,
bani da masaniyya akan Zahrah zata iya auren Yaa Lee wata rana, amma nasan Babanta
Best friend ɗin Father ne, na nemi connection da ita na tsara plan ɗin yadda zata
jawo hankalin shi harta su kasance abu guda na ɓata masa suna, sai ya zamana bana
nasara Yaa Sheikh ko sha'awar dawowa Nigeria ba ya yi, a haka har Allah ya kawo
ranar da aka haɗasu aure kasa barci nayi don farin ciki burina zai cika, Abba ka
mareni kasa an saka ni acinin mari, tun kafin nai wayo har boarding school nai duk
dalilin Yaa Lee, mene laifina dan nayi kishi da shi,bayan nasan ko mutuwa kayi
bashi da gadon ka tunda ba ɗan ka bane"
Ya ƙare maganar yana hawaye. Tunda Abba Hakimi yake ba'a taɓa masa rai irin na yau
ba, ya kama hannun Saif-wazir ya ce
"Aliyu shi ne komai nawa, tunda ya so ƴar dana fi so fiye da komai, ya kareta daga
mugwaye azzalumai, ya kula da ita hai ta haifi Halisa, akan yarinya ƙarama ya zaɓi
aci gaba dayi masa kallon gwauro, tuzuru, wasu na jifan shi da maganganun rashin
ɗa'a akan me ba zan fifita shi fiye daku ba? Me ya Umar-khan bai complain ba? Me ya
sa Ishaq-Hakim bai complain ba sai kai? ba zan aibata ka ba, amma kaje na yafe ka,
ka nemi wani uban!"
"Kada ayi haka Abba, don Allah a saisaita abi komai a sannu" Abba Hakimi ya ce.
"Sarauta ta girmi tsofa, amma ba zan iya yin haka ba, dole Saif-wazir yabar mini
gida" Umma A'isha ta ce
"Ya zama dole, tunda ya zaɓi hakan" Saif-wazir ya kalli Umma A'isha ya juya ya
kalli Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh dake fuskantar ƙofa, sai kawai ya yi murmushi
yabar gidan bakiɗaya.
Mother ta goge idanunta tas ta ce "Allhamdulillah! Hakan ya yi mini daɗi ko ba
komai nasan halin uban yarana, banyi mamakin yadda Mamana Fattoumah bata son ka,
akwai abin data gani tare da kai, Aliyu ina son ka ƙarasa cike mini sakin da kayi
wallahi na gama zama da kai"
Father ya girgiza ya ce
"Abin da ba zan taɓa iyawa ba kenan Maryam, ko sakin da nayi miki ban san nayi ba,
wlh ina son ki ba zan iya rabuwa dake ba _*IDAN BA KE*_ am nothing absolutely
nothing"
Uncle Haroon ya sauke masa wasu tagwayen maruka wanda ya sa Father saurin runtse
idanu yana dafe fuska.
"Shasha ban taɓa jin kunya a rayuwa irin ta yau ba, ka kunya tamu gaban mutanan da
suke da ƙima da martaba a idanunmu, tashi kabar wajan nan" Mother ta ce
"Yaje ina? idan yabar gidan nan ka tabbata ya ƙarasa ciki mini raguwar saki ɗayan"
Cikin tashin hankali ƙarara Father ya ce "Wlh ba zan iya sakin ki ba, duk abin da
za kiyi" yana faɗin hakan ya miƙe jiki ba kuzari, sai da yaje bakin ƙofa Mother ta
ce
"Mu haɗu a Court"
Mai martaba idanunsa akan Dada wani irin sabon son ta na ƙara taso masa ya nisa ya
ce.
"Allah ya kyauta, Ubangiji kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu. Ya cire masa ƙyashi da
hassada" duk suka amsa da abin. Ummul ta duba agogo tare da miƙewa ta ce. "Zan tafi
Allah ya ki ya ye" Sai a lokacin Umma A'isha ta ce.
"Kiyi haƙuri da abin da aka aikatawa Yaron ki Aliyu, ki yafe mana" Ummul tai
murmushi ta ce "Barrister Maryam za ki bawa haƙuri ita ce uwar Malam, kawai zan
nemi Alfarmar ya bini zuwa wajan ka kanin shi" Umma A'isha zatai mgn Abba Hakimi ya
ɗaga mata hannu ya ce
"Allah ya tsare"
Ummul tabi bayan Yaa Sheikh suka fita, ita ke driving shi yana gefen mai zaman
banza, ba tare da sanin su Abba Hakimi sun biyo bayansu ba. A haka suka shiga cikin
asibitin lokaci guda motocinsu sukai parking, har kawo lokacin ba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login