Showing 1 words to 3000 words out of 196133 words
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
_True Life story_
Nimcyluv sarauta
_*Arewabooks@Nimcyluv*_
1.
Jimeta/Yola
Njoɓoli Rugar Rome
Gudu Saniyar take tana bin ta a baya itama, hannunta riƙe da sanda na korar Nagge,
tamkar wanda suke wasan tsere haka Saniyar ke gudu a cikin jejin ita ma bata fasa
bin ta ba, sauran Naggen suna gefe guda ko wacce na cin ciyayi wanda bisa kuskure
tana can tana bin Saniya ɗaya tilo, sauran Naggen suka faɗa cikin gonar wani
manomi, a yunwace suka rufarwa albarkatun gonar. Cikin siririyar muryarta mai nuni
da Yarintar ta, da kuma nuna cewa ita ɗin zallar bafullatanar Yola ce ƴar Usul.
"Waru! Waru! Waru" shi ne abin da yarinyar ke ta nanatawa cikin hausarta ta Fulani,
yayinda Saniyar tuni tai mata nisa cikin gajiya wa da bin Saniyar ta tsaya a wajan
wata gaɓar ruwa tana riƙe ƙugunta ta ce "Bone, lalashewa ta samu Nagge Aradu" da
sauri kuma ta ɗauki sandar tana ƙara yin kan Saniyar ganin ta tsaya da gudun da
take, cikin sa'a ta cimmata tana zuwa ta kama ƙahonta tare da ƙifƙifta idanunta
alamar zallar fitsarar dake tattare da ita "d'ume ngid'd'a?" Ma'ana "me kake so?"
Kallon ta Saniyar ta yi sai kuma ta kaɗa jela tare da zubewa a wajan ta shiga shura
ƙafafuwa kamar zata mutu, cikin tsoro haɗi da razani HALISA ta ce "Jomirawo ka
taimakeni" ta faɗa tana kallon Saniyar wacce tai male-male a ƙasa ga wani ruwa mai
kama da jini na fitowa ta ƙasanta, kuka Halisa ta sanya domin idan Saniyar ta mutu
a nan wajan ta shiga uku, itama watan mutuwarta ya kama. Tsayar da kukan tai kafin
ta fara duba cikin jeji babu kowa sai ita, ga wani kwantaccen baƙin hadari dake
ƙasa wanda a koda yaushe zai iya tashi.
Juyawa tayi ta nufi wajan wata bishiya inda ta hangi ƙaramar igiya a jiki, tana
zuwa jikin bishiyar ta zame hular Fulanin dake kanta, nan da nan sumar kanta ta
sauka wacce take jajir babu alamar baƙi ko ɗaya, gashin ba wani cika ne dashi ba,
kawai tsayin gashi gareta, domin har fatar tsakiyar kanta ana iya ganowa. cikin
sayin jikinta ta fara jan igiyar tana ƙoƙarin kunce igiyar gaba ɗaya daga jikin
reshen bishiyar, kamar daga sama taji saukar wani abu mai sanyin gaske zuwa
kafaɗunta. Cak ta tsaya tana sauraren yadda abin ke tafiya sululuuuu a jikinta har
ya gama sauka, hannunta ta miƙa da nufin kama abin da ya sakko mata domin bata da
tsoro ko kaɗan, cikin rashin sa'a hannunta ya sauka saman ƙaton kan maciji wanda
yake kwance a jikinta, wani santsi-santsi ta ji a jikin macijin ga wani sanyi sosai
dake ratsa fatar jikinta, bata gama yadda da abin da zuciyarta ke ayyana mata ba, a
hankali ta juya wani ihu ta kurma wanda ya yi daidai da ɗaukewar numfashinta, baya
tayi zata faɗi kafin ta kai zuwa ƙasa macijin ya yi wata girgiza cikin sakanni ya
juye zuwa wani saurayi wanda jikinsa ya ke sanye da wasu haɗaɗɗun kayan sarauta na
farin saƙi, fari ne tas amma kamar Fatar mace haka fatar hannunsa da sauran jikinsa
suke gaba ɗaya gashi ya kwanta luff. Zubewa ya yi a ƙasa ta faɗo jikinsa idanunsa a
kan fuskarta, ya jima yana kallonta kafin cikin izza da nutsuwa ya ce "kin
tsoratani, kin tsorata kanki Danejo, banyi niyyar zuwar maki ba yanzu" Danejo sunan
da ƴan rugar Rome suke faɗawa Halisa ke nan. Sai da ya gama Kallon ta sosai, kallon
da ya jima bai mata ba tun tana zanin goyo matsayin Jaririya. Ɗaukanta ya yi ya
nufi inda Naggen suke yana zuwa ya tarar da wannan Saniyar dake Shure Shure ta
haihu, ashe daman ciwon haihuwa ke damunta. Halisa ya kalla yana sakin Murmushi
kafin ya zaro harshesa waje sai ga wani zobe ya bayyana, cikin sauri ya saka mata
zoben mai ɗauke da tambarin wata masarauta, kafin ya yi Girgiza sai ga shi ya sauya
kama, kamarsa a fuska na nan, amma kayan jikinsa sun sauya sun koma irin kayan
Fulani sak komai da komai, goya Danejo ya yi a bayansa, ya ɗauki jaririn Saniyar
cikin nutsuwa ya fara kaɗa Naggen zuwa Rugar Rome. Kamar ƙifatawar idanu haka ya
ƙaraso Rugar..
Iskar dake kaɗawa na alamar tashin hadarin ya sanya matashin ɗaga kansa sama, yana
kallon yadda gajimare ke haɗa kansa. A nutse kuma ya fara bin Rugar Rome da kallo
ba wata babba bace, amma Ubangiji ya albarkaci rugar da dabbobi musamman Nagge,
gasu manyan gwanin sha'awa yawancinsu jajaye ne kafin ka samu farar saniya zaka
daɗe. Wasu sun dawo daka kiwo wasu kuma na hanya sbd rashin yawaitar mutane da babu
a rugar, daidai wajan wata bukka ya Ƙarasa yana gyara riƙon da ya yi wa Jaririyar
Saniyar kafin ya ce "Sannunmu dai" ya faɗa a taushashe jin shiru ya sanya ya ƙara
buɗe muryarsa mai sanyi ya ce "Afuwanku dai" daga cikin bukkar wata ƙaramar murya
ta amsa da faɗin "Waye nan?" Ta faɗi hakan tana fitowa, lokacin da Idanunta ya
sauka acikin ƙwayar matashin gabanta taji ya faɗi saboda yadda taga ƙwayar
idanunsa, gane cewa kamar ta tsorata da yanayinsa ya sanya ya lumshe idanunsa kaɗan
tare da buɗewa ya ce "Ga ɗan uwanki na kawo shi, arado bashi da lafiya ne can na
ganosa yashe a jeji ba rai, har naggenku ya samu zuri'a" yana faɗin hakan ya ajjiye
Jaririyar Saniyar a ƙasa wacce take jajir da ita Kuma ƙatuwa. Shatu dai binsa take
da Idanunta domin bata taɓa ganin mai kama dashi a rugar ba sai yau, kallon da yaga
yai yawa ne yasa ya ce "Shai a mata magani" a hankali ya sauke Halisa Dajeno ya
kwantar a ƙasa a nan gaban bukkar kamar zai juya ya tafi sai kuma ya ƙurawa zoben
hannunta idanu wanda yake sheƙi sosai ga tambarin masarauta nan ya fito sosai a
jikinsa, a ransa yake ji kamar bai dace daya mallaka mata wannan zoben ba, amma
bashi da wani zaɓi dole ya bata ta haka ne kawai zai lalubota a duk sanda ta ɓace
masa, tun tana ciki yake fama da rainonta lokacin haihuwarta ne kawai bai sani ba.
Ba tare da ya ƙara cewa komai ba ya juya da sauri ya fara tafiya tare da shankwana,
yana barin wajan ya ƙara yin girgiza wata iska mai daɗi da guguwa ta mamaye gaba
ɗaya cikin Rugar Rome. Nan take ya koma asalin macijinsa kamar yadda ya bayyana a
farko, yana iya komawa duk suffar da yaga dama cikin ƙaramin lokaci amma zama
maciji yafi masa daɗi sbd yawaitar macije dake cikin jejin daya zagaye Rugar Rome,
a haka ya sulale tare da komawa cikin jejin.
Iskar dake kaɗawa ce tai sanadiyyar farkawar Dajeno daga barcin dolen da macijin
ya sanyata a ruɗe ta miƙe tana dafe kanta dake mata ciwo sosai cikin sanyin murya
ta ce. "Miyyati Allah" Shatu dake gefen Dajeno tana ɗaure Naggen a garken dake dab
da bukkar ta ce "Nassu, ka shigo" Shiru Danejo tai kamar zata tuna wani abu sai
kuma tai saurin ware manyan idanunta ta ce "Shai Shatu ina Dadana ya tashi daga
barci hoo?" Shatu ta ce "E, yana ta kiranka baka dawo ba, ciwonsa ya tashi yana ta
masa zafi" da sauri Danejo ta faɗa cikin bukkar Idanunta ya sauka akan Dada (her
mother) tana kwance a rufeta da wani farin zani jikinta sai rawa yake, fara ce
matar sosai amma yanayin jikinta kamar ta shekara 60 nan kuma ba tafi shekaru 50 ba
idan ma ta cika. "Shannu shannu Dadana" Idanu Dada ta buɗe da ƙyar ta ce "Zakiyi
Albarka Halisa ki riƙe gaskiya da amana ki zama mai haƙuri ki daina saurin fushi da
rashin kunya" Kallo juna sukai da Shatu da Halisa wacce akafi sani da Dajeno "Dada
me yasa kake shaiwa haka?" Dada ta kalli Shatu kana ta juya ta kama Hannun Dajeno
ta haɗa dana Shatu ta ce "Meyasa ba zance haka ba? Shatu kece ƙarama Halisa ita ce
babba amma zafin zuciya ne da ita, rauninta akai na yake, kuma dole na tafi na
barta" da sauri Shatu ta kalli Dada tana faɗin "Ina zaka Dada kuma?bayan Rugar Rome
ina muke dashi" Dada ta numfasa ta ce "Babu da inda yafi wannan Rugar, zan tafi
zuwa ga Mahaliccin daya samar da Rugar Romen, ciwon nan ba zai barni ba kuɗin
amanata ce musamman ke Halisa" Dajeno kasa cewa komai tai sai ƙurawa Dada fararen
idanunta da tayi zuciyarta cike da fargaba. "Dadana ba zaki mutu ba, idan kin mutu
wa muke dashi a nan rugar wazai dinga kulawa damu?" Dajeno ta ƙare maganar cikin
sanyin murya gaba ɗaya jikinta yai sanyi sosai. Shiru kawai Dada tai can kuma ta ce
"Hamma Yabi ya dawo?" "A'a birni da nisa Dadana yace gobe zai kai ki can asibitin
birnin". Jinjina kai Dada tai Dajeno ta miƙe bayan ta ce Shatu ta kula da Dada
yanzu zata wajan Sarkin ruga ta amso magani.
Cikin sanyin jikin nan nata take tafiya kanta a ƙasa domin bata fiya kallon mutane
ba, a yadda jikin Danejo yake da sanyi zaka ɗauka babu ruwan ta, musamman da
fuskarta yai kala dana salihai amma zafi da zuciya gareta, ga kuma taurin kai da
naci akan abu, idan tace zatai to tabbas zatai, amma idan tace A'a babu wanda ya
isa juyata ko Dada sai dai ta zuba mata Idanu. Abin birgewa ga rayuwar Halisa
Dajeno tana da saurin yafiya, da kuma tausayi da kuma kawaici. Cikin tafiyar
nutsuwa ta Ƙarasa gaban wata bukka wacce tafi ko wacce bukka kyau da girma a cikin
Rugar Rome. "Shai shai Mene haka kamar makauniya ina kwaɗa miki shandan nan Aradu"
da sauri Danejo ta ɗaga idanunta ta kalli Gwaggo Niyabi wacce ke zaune tana kaɗa
audiga, murguɗa baki tai ba tare data ce komai ba, jin tai shiru yasa Gwaggo faɗin
"Ko njid'ud'a?" "Magani za'a bawa Dadana" Gwaggo Niyabi ta ce "To baya nan" shiru
tai kamar zatai Mgn sai kuma ta juya sai da tayi nisa kaɗan Gwaggo Niyabi ta ce
"Yaka Dajeno waru" tsaye Dajeno tai domin ba shiri suke da Gwaggo ba, Murmushi
Gwaggo tai sosai kafin ta numfasa ta ce "Idan kinje ki tambayi Dada waye
mahaifinki, mene yasa daya rasu bata bar Rugar Rome ba, ta tafi danginta ko dangin
mijinta" da mamaki Danejo ta ce "To bayan Baffa ya rasu mene na tambayarsa, ki
daina maganar Uwayena" Gwaggo ta miƙe tana kallon Danejo "To ana gab da kurarku a
Rugar Rome, domin bama son mara gurbi" harara Danejo ta watsa mata ta ce "Miyidi
saro'am" ma'ana ina son iyayena "Kalleki mai ƙaton baki da ƙwalaƙwalan idanu" tana
faɗin hakan ta kwasa da gudu zuwa bukkarsu.
Da ƙyar suka samu zazzaɓi Dada ya sauka tasha paracetamol sai 12 na dare ta samu
barci. Shatu ma barci take kusa da Dada a hankali Danejo ta miƙe daga kwancan da
take har yanzu fararen kayan Fulani ne sanye a jikinta, hula ta ɗauka ta rufe kanta
a nutse ta fita daga cikin bukkar kai tsaye garken shanun dake dab da bukkar ta
nufa, wanda aka kunna musu wuta tana ci kaɗan kaɗan. Gobe da sassafe take son
tafiya tallan kindirmon. ƙwarya ta ɗauka ta tsuguna tare da kama nonon jikin wata
Nagge ta fara tatsa gaba ɗaya hankalinta baya jikinta sai a lokacin maganar Gwaggo
Niyabi ta faɗo mata, a haka ta gama tatsar nonon acikin ƙwayar ta ajjiye can gefe
guda a bukkar tasu. Gari na waye ba tare da yin wanka ba ta shasshafa ruwa ƙafa duk
lam'a ta dungura sallah. Dada na gefe tana kallon yadda take sallah tana son tuna
wani abu amma ta kasa har zuciyarta take jin kamar yadda Danejo ke sallah ba haka
ake yi ba, amma ta kasa ganewa da kuma tuna yadda ake?. "Ina Hamma Yabi?" Danejo ta
kalli Dada tace "Mi naddi mo (na kira shi)". Jinjina kai Dada tai, Danejo sai
kallon Dada take kamar zatai shiru sai kuma tace "Dada waye Baffa?" Da sauri Dada
ta juya gabanta na faɗuwa sosai na rashin amsar tambayar Danejo tace "Kamarya
Halisa? Baffa mahaifinku ne kuma ya rasu mene?" "Na sani Dada, ina dangin Baffana
suke me yasa muke zaune a Rugar Rome?" A hargitse Dada ta ɗaga hannunta tare da
ɗauke Danejo da mari sai kuma ta fashe da kuka ta ce "Wacce masifa ce wannan kika
koya Dajeno? Bance miki nice Dangin uwa dana uba a gareku ba? Ban gaya miki ba
Halisa?" Hawaye na sauka a fuskar Halisa ta ce "Kiyi haƙuri Dadana ba zan sake ba,
ban san mene yasa nai miki wannan tambayar ba" kasa magana Dada tai saboda hakin
daya fara cin ƙarfin ta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi Danejo na ƙwala ihu ta shiga
kiran sunan Hamma Yabi wanda ke garken shanu, tattara Dada Hamma Yabi yai zuwa wani
ƙaramin asibiti dake gefen Rugar, suna zuwa kusan sune na farko amma abin mmki sai
kwasar wasu ake ana barinsu sbd cin hancin da suke bawa Nurse's ɗin, har lokacin
tashi yai ba'a samu damar duba Dada ba a haka suka dawo gida.
Yola South
Abti America
Babbar makaranta ce Wacce ta kasance Private school tun daga primary school har
zuwa University makarantar dake da ita, Abti America mallakin mataimakin shugaban
ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na yanzu Atiku Abubakar ce. Makarantar na cikin
Yola South ko ace Yola town duk ɗaya. Makaranta ce wacce sai ɗan wane da wane suke
zuwanta duk wanda ka gani a ciki to ka tabbatar ubansa ya mallaki arziƙi ba dukiya
ba.
Adamawa/jimeta.
Yola shi ne babban birnin jihar Adamawa. Yola South ana kiranshi da Yola town acan
fadar lamiɗon Adamawa yake ma'ana gidan sarauta (LAMIƊO'S PALACE).
Yola North, jimeta kenan. Acan fadar gwamnati yake, jimeta yafi kyau haɗuwa da
tsari fiye da Yola South. Manyan abubuwa gaba ɗaya acan Yola North wato jimeta
suke. Babu wani nisa tsakanin Yola South da Yola North/jimeta hasali ma roundabout
ne ya raba tsakaninsu, akwai wani roundabout mai ƙwayoyin ƙwaryar nono da ludayi a
kai muna ana kiransa da Yola roundabout, akan hanyar express yake daga shi sai wata
ƙofa, to wannan ƙofar shine da zarar ka shigeta ka shiga yola kenan, sunan ƙofar
“JIPPAJAM” da kuma “JAƁƁAMA” Ma'anar Jippajam shi ne Ka sauka lafiya. Wannan idan
kazo fita kenan ta cikin yola zaka ganshi, idan shiga garin zakayi kuma za ka ga an
rubuta Jaɓɓama ma'ana Sannu da zuwa.
Njoɓoli wani ƙauye ne sosai dake cikin ƙauyukan dake zagaye da Yola south wato yola
town,ƙauyen yawancinsu fulani ne makiyaya,amma akwai manoma ma, babu nisa da cikin
gari, sannan suna da tashar mota mai tafiya ƙauyen a cikin yola. Wannan kenan.
Tana tafe hannunta riƙe da sanda tana kaɗawa, a hankali bakinta ke motsawa tana
karanta 1,2,3-10 cikin fillatancin karatunta bai nisa ba, babu arabi ba boko kuma
ba za'a kirata da jahila ba,ita dai gata nan ne dai, ba wanka sosai ma'ana ba
tsafta.
Go'a 1 D'id'i 2 Tati 3 Nay 4 juy 5 Je go'o 6 haka ta dinga maimaitawa har ta
ƙarasa can nesa da gate ɗin makarantar Abti America. Ajjiye ƙwayar kanta tai tare
da neman waje ta zauna tana jira a tashi duk da cewa ba'a talla amma sbd ƙarancin
masu sai da kindirmo yasa ake siyan nono a wajanta sosai. Tana zaune wata mota baƙa
ta taho da gudu gadan-gadan zata take Danejo cikin tsoro da firgita har tana ture
ƙwayar nonon Danejo ta miƙe tsaye tare da fasa ihu tana ƙanƙame jikinta idanunta
rufe sbd gaba ɗaya motar kanta tayo da alama giyar motarce ta ƙwace. Motar na gab
da taka Dajeno ba zato taji an saka hannu tare da yin sama da ita...
😌 let's see yadda zaku amshi labarin HALISA DAJENO wanda ya faru a gaske bawai
fiction story bane.
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
Nimcyluv sarauta
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
2.
Ihu Danejo ta fasa lokacin da taji an saka hannu tare da yin sama da ita cikin
muryarta ta Fulani ta ce "Mi boni Dada'am mi nasti tati hande mi mayi" gaba ɗaya ta
tsorata ta ɗauka motar za tabi ta kanta. Jin an direta gefe guda ya sanya ta buɗe
idanunta a hankali a tsaye ta gansa nesa da ita kaɗan hannunsa harɗe a ƙirji yana
ƙare mata kallo tare da nazartar yanayinta. Kasa daina kallonsa Danejo tai sbd
yanayin shigar jikinsa wani farin yadi ne a jikin nasa amma yai baƙiƙƙirin sbd
dauɗar daya haɗa gaba ɗaya yadin ya yayyage har ana iya ganin farar fatar jikinsa,
sumar kansa rabi furfura rabi baƙa. Ajjiyar zuciya ta sauke da sauri kuma ta juya
sbd ƙarar motar da taji sai a lokacin lura da shegewar motar cikin Abti America.
Ƙugu ta riƙe tana fari da manyan idanunta cike da tsiwa ta ce "Shai mutum ya tsaya
yaga yadda ake tijara aradu ina iya fasa gilahin moto ɗin" daga bayanta taji murya
mai sanyi ta daki kunnenta ance "Zaki biya?" Juyawa tai ta kallesa mutumin ɗazo ne
dai wanda ya taimaketa kafin motar ta bigeta, harara ta banka masa ta ce "Kai
Almajiri Sukajo meye ruwanka dani? Ina ruwanka idan moto ya takani, da kayanka duk
a yage" ta faɗa tana murguɗa masa baki. A hankali ya nanata kalmar “Sukajo” a ransa
idan ya fahimta Sukajo na nufin “Saurayi” Girgiza kai kawai yai ba tare da yace
mata komai ba ya juya zai bar wajan. Da sauri ta sha gabansa tana faɗin "hani
inbano ina ka kai mini kindirmon shaniyata? Waye ya tittila a tumbinsa?" Juyawa yai
tare da kallon ƙwayar nonon babu komai a ciki sbd tuni ta zubar da nonon dalilin
tsoran da taji, amma ta kasa fahimtar ita ta zubar ɗin. Yana dai tsaye bai ce komai
ba can kuma ya kalli cikin idanunta da sauri ta ɗauke nata idanun tana murguɗa masa
baki cikin ƙasa da murya ya ce "Siya akai ai" baki ta buɗe ita ai ba taga wanda
yazo ya siya ɗin ba kuma gaba ɗaya nonon aka siya kenan? "Ina kuɗin to ɗan Almajiri
mai yagaggun kaya?" Da hannu ya nuna mata ƙasan ƙwayar yana rufe idanu da buɗewa ya
ce "Gasu can" ta durƙusa ta ɗaga ƙwayar sai ga kuɗi da gudar dubu ɗaya da ɗari
biyar guda biyu sai ƴan ɗari guda goma. Zaro idanu tai waje jikinta na rawa ta ce
"Kai ɗan Almajiri mai ƙarya wannan kuɗin duk na kindirmona ne? Ai aradu kuɗin yai
yawa" hannunsa dake harɗe a ƙirji ya wara tare da ɗaga kafaɗa ya ce "haka suka
bayar ai" "su waye?" Shiru yai mata yana ƙoƙarin juyawa ta ce "Mene wannan a
ƙafarka?" Zaro idanu waje yai tare da yin baya ganin tana ƙoƙarin zuwa inda yake
yasa yai saurin faɗin "ke fillo bayanki" juyawa tai da sauri amma babu kowa a wajan
tsaki taja tana kakkaɓe zanin jikinta ta ce "Mai ƙarya dai ɗan wuta" ta ƙare zancan
tana ɗago kanta babu Almajirin kamar yadda ta raɗa masa suna babu ko inuwarsa sai
wani farin Zomo data gani kyakkyawa dashi ya ƙura mata idanu, itama kafesa tai da
idanu kamar zata kamasa sai kuma ta ɗauki ƙwayarta ta nufi bakin hanya inda zata
samu motar da zata kaita Njoɓoli. Da idanu Zomon ya bita har tayi nisa sosai yana
kallon sanda ta samu abin hawa, girgiza yai yana kaɗa kunnuwansa sai gashi ya