Showing 3001 words to 6000 words out of 62823 words
Chapter 2 - UKUBAR KISHIYATA Sirrin Da Ya Rushe Aure by Ummee Yusuf
ja tsaki tukun ta d'auka tare da cewa " my ameen"
Daga d'ayan b'angaren kuma Al'ameen yace " haba Latifa ya kika shige d'aki kika barni,abincin ma sai na rok'a sannan za 'a bani kuma keda wa kike waya tundazu wayarki busy?"
A zuciyarta tace kaji dashi d'ansa ido.amma a zahiri kuma tace " my Ameen mama ce ta k'irani amma gani nan zuwa".tana fad'an haka ta mik'e tare da ajiye wayan ta fito main palour.
A kan dinning table ta hango shi ya zuba tagumi da hannaye 2 yana kallon yaran larabawa da suke ta wasa a tashan m.b.c3.
Damuwa ce k'arara shimfid'e akan fuskanshi saboda shi ya kasance mai matukar son yara.
Ta iso daf dashi ta tsaya amma baima san da mutum a kusa dashi ba saboda yayi zurfi a tunani.
Hannu tasa ta dafa kafad'an shi,ya juyo a d'an firgice yana kallonta,can ya d'an kak'alo murmushin yake yace " har kin iso?"
Bata amsa ba sai zagayawa da tayi taja kujera dake opp da nashi ta zauna ta zuba mishi ido for some seconds sannan tace " nasan kana cikin damuwa mijina kaman yanda nake ciki nima koma ince nama fika shiga damuwa saboda ni mace ce.amma ina so kasani cewa komai yayi farko toh tabbas zaiyi karshe,saboda kullum cikin fad'awa mahallincin mu muke nasan ba zai barmu haka ba,dan ma bana fad'a maka yanda nake tsayuwar dare saboda wannan babban bukatar namu,ga malamai da nake basu abin sadaka suna taimaka mana da addu'a.ina son ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai zo da sauki.haba my Ameen kai da kake namiji ma kana haka ni kuma inyi yaya kenan?"tace tana mishi murmushi.
Ajiyar zuciya yayi sannan yakamo hannunta na dama yana murzawa a hankali.fuskarsa d'auke da tsadaden murmushinsa dake k'ara fito da aininhin k'yan sa yace " shiyasa nake godewa Allah daya bani mata saliha mai kwantar min da hankali a duk lokacin da nake cikin damuwa,dan haka bana k'yashin baki komai nawa dan nasan a hanya mai k'yau zaki sarrafa su".
Murmushin jin dad'in yanda mijinta ya yarda da ita ta saki sannan tace " toh ya isa haka ranka ya dad'e,irin wannan yabon ai sai kasa kaina ya fashe.bari in baka abinci kaci ko?"
Gyada mata kai yayi still yana murmushi.
Warmers d'in ta fara bubbud'ewa tace " me zan zuba maka ur highness?"
" Duk abinda kika zuba min zanci".yace yana kallonta.
Plate ta d'auko ta zuba rice nd stew da yaji naman rago zallah sai peppe soup d'in kayan ciki ta turagaban shi tace " Bismillah".
Cin abincin ya fara suna hira sama-sama har ya gama ya kora da ruwa sannan suka dawo palour suka zauna kallo tare da canza channel zuwa al'jazeera news har zuwa karfe goma da rabi na dare snnan suka koma up stairs part d'in Al'ameen .
Suna shigowa bedroom d'in bai tasaya wata-wata ba ya fad'a bathroom yayi wanka,yana fitowa Latifa ma ta shiga wankan kamin ta fito har yayi shirin bacci cikin kayan baccinsa dark blue masu taushin gaske.
Yana kwance akan gado ta fito,akan idonshi ta shirya cikin wata arniyan night wear, yana kallonta yana had'iyan yawu.
Yamutsa fuska ta fara tana wash-wash,bayan ta gama fesa turarukan ta masu kamshi yana kallonta amma takaici ya hana ya tanka mata mata ba.
Ganin ba zai kulata ba yasa tace " my Ameen wallahi wani irin ciwon kai nake ji kuma gashi ina son yin nafilfilu cikin dare".
"Uhum..." yace yana kallonta.
" Zan je insha magani in d'an kwanta kamin lokaci yayi" tace tana wani dafe goshi.
" Toh "kawai yace mata tare da juya mata baya.
Yana jinta ta bud'e k'ofa tayi ficewarta ba tare da damuwa da halin da ya shiga ba.
Yana jin ta rufo mishi k'ofa,ya juyo yana kallon k'ofan cike da takaicin hali irin na Latifa da kullum bata tashi rashin lafiya ko ibadarta sai sai sun zo kwanciya,a ko wani lokaci da abinda za ta kirkiro dan karma ya nemi wani abu a wajanta.in har ta yarda suka kwana waje d'aya toh fa lalle tana da wata tana da wata muhimmiyar bukatarta a wajan shi.
Tana zuwa part d'inta ta kulle k'ofa harda murza key.
Wayanta ta dauko ta kira Salees,video call suka fara, tana kwance akan gado ba sutura a jikint shima haka sai maganan batsa suke yana cewa shafa min nan murza min can.wai duk su a dole zasu biya bukatar su a haka.kuma shaid'an ya basu sa'a abinda suke nema,su basu kwanta sai wajan karfe ukun dare sannan suka.( WA'IYAZUBILLAH)
Fa'za da shamsiyya suma suna can sun luluk'a tasu duniyar domin ba zaman 'yan uwa suka d'uki kansu ba face masoya saboda sun gama yankewa kansu hukuncin basu ba aure koda zasuyi toh sai dai tsakaninsu zasuyi.
Ba wanda yasan wannan sirrin nasu a gida sai abokanen tambad'ewarsu.
Suna kwance kan gadansu ko wacce tsirara bayan sun tabbatar da sunyiwa k'ofar part d'insu key
Sai shafe-shafen da lashe-lashen juna suke duk sun fita haiyacin su.
Basu samu bacci ba sai wajan karfe 2 dare suka kwanta rungume da juna ba tare da sunsa koda kayan bacci ba.
Al'ameen bawan Allah yana can abin duniya ya ishe shi,da yaga kwanciyar bazata mishi ba ya mik'e ya shiga bathroom ya d'auro alwala ya kama nafila , bai kwanta ba sai da yaji idon shi yana rufewa saboda bacci kuma ga wani natsuwa ta musamman data sauko mishi a zuciya.ba b'ata lokaci ya haye gadonshi ya kwanta nan da nan bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi.
✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍
[3/24, 6:46 AM] Ummee Yusuf: . 🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
😭😭😭😭😭😭
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
💫*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*💫
*Gidan zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*🤝
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~ADDU'AR DA ZAKUYI A LOKACIN DA ZAKU SHIGA TOILET~*
بِسْمِ اللَّهِ. اللَّهُـمَّ إِنِّي أَعُـوذُ بِـكَ
مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبَائِثِ
*~Bismillaahi. Allaahumma 'innee 'a'oothu bika minal-khubthi walkhabaa'ith.~*
*~In the Name of Allah. O Allah, I seek protection in You from the male and female unclean spirits.~*
*~part four~*
Da washe gari Al'ameen da ya tashi har yayi shirin fita bai ga idon Latifa ba wanda ya saba da hakan,wucewa yayi abinsa zuwa office ko kallan dinning table dake shake da kayan break fast baiyi ba.
Sai kusan 11Latifa ta farka sakamakon bata kwanta bacci da wuri ba,kuma sai a lokacin tayi sallahn asuba bayan tayi wankan ta shirya.sannan ta fito yin break fast
Serving d'in kanta tayi cikin kwanciyar hankali duk da taga Al'ameen bai tab'a abincin ba amma ko a kwalar riganta.
Bata dad'e da fara cin abincin ba Shamsiyya da Fa'iza suka fito rik'e da hannun juna suma sun sha k'yau,kujera suka ja suka zauna.
"Ina kwana Aunty " suka ce a tare.
"Lafiya my sisters yau baku da lec ne?"ta amsa musu.
Shamsiyya ce ke zuba musu abincin a plate d'aya,ita kuma Fa'iza tace " eh yau bamu dashi sai gobe".
Latifa ta saba da ganin suna cin abinci a plate 1 wani lokacin kaman suyi feeding junan su,amma ko kad'an bata tab'a kawo komai a ranta ba,gani take tsaban shak'uwa ce irin na 'yan uwantaka ta haddasa musu hakan.
Sun fara cin abincin suna hira jefi- jefi ,sallaman da suka ji shi yasa su amsawa tare da kallon mai shigowa.
Fad'ad'a fara'a latifa tayi ganin wacce ta shigo,cikin jin dad'i tace " Aina'u kece,k'araso mana".
K'arasowa wacce aka kira da Aina'un tayi taja kujera ta zauna sannan ta jawo plate ta fara.serving kanta tace" uhum besty sai yanzu ake break fast sai kace a london muke?"
" Ke bana son tsiya ko gaisawa bamuyi ba zaki fara ko?"Latifa tace tana mata hararan wasa
Kamin ta bata amsa su Fa'iza suka gaisheta,amsawa tayi tana tambayan su karatu suka amsa mata da Alhamdullilah sannan suka cigaba da cin abincin.
Bayan sun gama
Latifa ta kama hannun Aina'u suka mike tare tace " taso mu shiga daga ciki,dama nemanki nake ruwa a jallo".
Hararan wasa Aina'u ta aika mata sannan tace" kuji ta sai kace da gaske,in nema na kike baki san hanyan gidanmu ba ko baki da no wayata?"
Latifa janta tayi sukayi hanyan part d'inta tana mita tace " in kika fara tsara zance ko tambaya lawyer albarka".
Suna shiga part d'in Aina'u ta fara shirin zama kan kujera,Latifa ta k'ara janta tace" ke zancen sirri ne yafi karfin nan zo mu k'arasa bedroom".
A kan gadonta suka zube,bud'e wani d'an karamin fridge dake gefen gadon Latifa tayi ta fito musu da drinks masu sanyi a ciki.ta rik'e d'aya ta mik'awa Aina'u d'aya.
Drink d'in hannunta Latifa ta kurawa ido ba tare da tasha ba kuma batayi magana ba ,Aina'u ta dafa mata kafad'a tace " sis re u alright?"
Kai ta d'ago tana kallon Aina'u tace " wallahi besty ina cikin babban matsala nd i dont knw wat to do shiyasa nake neman ki saboda nasan zaki samo min mafita.my Ameen nd his relative are worrid akan rashin haihuwata,abinda nake tsoro shine karsu gaji su tilasta mishi yayi aure.nd am sure yana auren matar shi zata haihu since dagani har ke munsan abinda ta hanani d'aukan ciki,komai zai iya rushewa muddin nayi sake wata ta shigo ta haihu coz yanda nake juya dukiyan shi inyi abinda naga dama ina gani zai zama nata da abinda ta haifa... ...wayyo bansan wani hali zan kasance ba " tace da matukar damuwa a fuskanta.
Aina'u shan drink d'inta take hankali kwance ba tare da wani damuwa ba tace" ni na zata ma wani babban al' lamari ne,yanzu akan wannan d'an karamin abun kike wani d'aga hankalinki,toh bari kiji ta inda aka hau ta nan ake sauk'a.abin nufi wajan boka zamu koma sai dai wannan karan harda iyayen shi zai had'a mana"
Cikin jin dad'i da kuma yarda da kawarta tace " oh my god! Sam na manta da zancen bokan nan kiga time d'in da Al'ameen yake min yanga muna zuwa wajan shi a cikin satin maganan auren mu ya kankama.gaskiya am luky to have u as a frnd".
Gyara d'an karamin veil dake kanta Aina'u tayi tana smilling sannan tace " ni zan fad'i haka dan abinda kike min ko blood sister na baza ta iya min haka kinga dole nima in damu da sha'aninki beside tun muna yara muke tare".
" hmm Aina'u kenan shiyasa any time nake cewa da low kika karanta in kika fara tsara zance ba magana".Latifa tace tana dariya tare da mikewa tayi hanyan sip d'inta dake cikin d'akin.
Bounches na kud'i ta d'ebo a ciki ta zuba a wani black hand bag d'inta tare da d'auko wani veil shima black.
Veil d'in ta yafa akanta sannan ta juyo zuwa ga ban Aina'u tace " ke tashi mu tafi tun yanzu kinsan ba'a bori da sanyin jiki".
"U re right my besty muje da wuri" Aina'u tace tana ajiye drink d'in hannunta saman fridge sannan ta mik'e suka sauko down stairs.
A main palour suka tarar da Shamsiya zaune akan kujera while Fa'iza tayi pillow da cinyarta suna hiran au,bounch d'in 1k guda 2 Latifa ta ciro a cikin hand bag d'inta tare da mik'o musu tace " ga wannan kusa driver ya kai ku gida ku bawa mama sak'onta,zamu je unguwa da Aina'u.ku gaishe min da ita".
Amsa mata sukayi da " toh sai kun dawo"
Sun fitowa direct parking space suka nufa,wata hadad'en mota ash colour Latifa ta bud'e ta shiga driver seat Aina'u kuma ta bud'e gefenta ta shiga ta zauna.nan taja motan suka fita a gidan.
Tafiya suke cikin jeji Laifa ta manta hanya saboda tun zuwanta na farko kamun auren su da Al'ameen bata k'ara zuwa ba.Aina'u ce mai nuna mata hanyan har suka iso inda zasu ajiye mota domin saman dutse zasu hau,anan bokan yake.
Sun sha bak'ar wuya kamin su samu nasaran hawa bama kaman Latifa da take da k'iba na
fitan hankali,sai gumi take had'awa ga kuma nishi da take kaman mai haihuwa.
Bukkan kara guda 1 tal suka gani a saman dutsen inda bokan yake da zama,sai da suka d'an huta sannan suka nufi bukkan.
Tsawa aka daka musu akan su cire takalman su,a tsorace suka cire takalman suna waige-waige ko zasu ga mai maganan.
" ku shigo ta baya-ta baya.."suka kara jin tsawan sai dai wannan yafi na d'azun.
Kamo hannun Aina'u Latifa tayi ta rik'e gam sabida tsoro sannan suka fara tafiya ta bayan kaman yanda aka umarce su.
Suna dab da shiga cikin bukkan suka ji muryan d'an k'aramin yaro yana cewa " wayyo zasu taka ni umma" .
Nan suka suka tsaya kaman an dasa suJikin sune ya fara b'ari barin ma da boka yace kan d'an autan aljani tsibiritu suka kusan takawa.Latifa kam ji take kaman ta saki fitsari a wando .
" ku shigo"aka ace musu.
Da kyar suka cigaba da tafiya ta bayan har suka shiga cikin bukkan da duhu ya mamaye kaman dare,wani haske ne ya fito cikin wani jan k'warya ya haska cikin bukkan kuma sai a lokacin boka ya bayyana a gaban su cikin wasu kaya ja-jaye ga rabin fuskarsa ma ta sha fenti ja.cikin babban murya yace su zauna.
Zama sukayi a inda ya nuna masu har yanzu Latifa tana rik'e da hannun Aina'u gam.
Aina'u ita tayi karfin halin bud'e baki da niyan yiwa boka bayani amma ya dakatar da ita ta hanyan d'aga mata hannu.
Shiru sukayi suna kallonsa yana ta wasu surkullen sa can ya d'ago kai yana kallon Latifa yace" tsibiritu da maniru su fad'a abinda yake tafe dake,kina so a rufe bakin mijinki dana dangin shi akan rashin haihuwarki kuma a kawar da idon shi akan ko wace mace ko ba haka bane?"
Cikin jin dad'in hango nasara tace "hakane boka"
Dariya ya kwashe da shi sannan kuma ya turbune fuska a lakaci1 yace "aikin ki mai sauk'i ne in kika kawo kitsen bakin jaki da makahon bunsuru da sauro mai ido 1shiken nan sai yanda kikayi dasu "
Zaro ido waje Latifa tayi cikin tashin hankali tana kallon Aina'u bakinta yana shaking jin abubuwan da ya kirga a ina zata same su?
Aina'u ce ta d'an gyra zama tace " ayi mana afuwa boka irinn wannan abu ai sai ku,zamu bada kud'i a taimaka a nemo mana".
Wasu surutai ya fara da wani yare yana kallon sama can ya dawo da kanshi kasa yace " tsibiritu ya yarda zai taimake ku sai ku ajiye kud'in acan ya nuna musu wata b'akar k'warya,belt d'in yan dubu guda 2 ta fito dasu hannu na karkarwa ta jefa a ciki nan da nan kud'insukak bace bat.
"Aikin ki ya kammala sai dai akwai wani d'an uwan mijinki kiyi hankali dashi zai iya b'ata miki aiki a ko wani lokaci".boka yace ba tare da ya kalle su ba.
Zatayi magan Aina'u taja hannunta suka fita daga cikin bukkan.
✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . 🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀🙆♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
😭😭😭😭😭😭
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
💫*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*💫
*Gidan zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*🤝
*~part five~*
Aina'u bata saki hannun Latifa ba sai ďa suka zo har inda suka ajiye mota,bude motan tayi ta tura ta a ciki san an itama ta zagayo ta bude tashiga gidan gaba.
Latifa d'aura kanta tayi a kan stairyn motan ta sauk'e ajiyan zuciya.
Juyo da kanta tayi saitin Aina'u tace " kin san Allah badan kina tare da ni a wajan nan ba,da abinda zai hani sake gudawa a jikina".
Aina'u ta tuntsire da dariya saida tayi mai isar ta sannan tace " matsoraciya kawai harda gudawa hahaha" tacigaba da dariyanta.
Had'e rai katifa tayi tana kallon yanda ta dage tana mata dariya tace " wats funny here, da zaki wani dage kina dariya haka?yauwa meyasa kika hana ni magana bayan kina ji yace akwai d'an uwan my Ameen da zai iya rusa min duk aikina.da kin bari ko sunan shi na tambaya".
Aina'u tace " kada ki soma wanman gangancin saboda boka nan ba'a yi masa musu kuma ba'a wucewa gaban shi.kinga da yana so ki sani da kan shi zai miki bayani".
Key tayiwa motan suka fara tafiya tace " oh god ya zanyi ne?"
"Abinda zakiyi kawai kiyi taka tsan-tsan da'yan uwansa"Aina'u ta bata amsa.
Shawara yanda zatayi da 'yan uwan Al'ameen Aina'u take bata har suka shigo garin k.d,direct gidan su Aina'u tayi dake kawo a bakin k'ofan wani yamutsesen gida tayi parking.
Hand bag d'inta ta bud'e ta ciro bounch 200 guda1 ta mik'awa Aina'u tace " ga wannan ki rik'e ba yawa besty nagode sosai".
Karb'a Aina'u tayi tana mata godiya tace "baza ki shigo ku gaisa da umma ba ?"
Gurgiza kai Latifa tayi a zuciyarta tana ina zataiya shiga gidan nan amma a zahiri kuma tace " no besty kinga yamma tayi sosai yanzu kila ma my Ameeen ya dawo,soo gwara na karasa ki gaishe min da ita.sai next time in nazo zan shigo mu gaisa".
Murmushi Aina'u tayi tace" shikenan sai munyi waya "daga nan ta bud'e motan ta fita Latifa taja tayi gaba abinta.
Burinta na karshe ya cika dan yanzu duk cikin dangin mijinta ba mai yi nata maganan rashin haifuwa balle kuma shi uban gayyan wato Al' ameen ya zama rakumi da alaka sai yanda tayi dashi dan duk wani documents da files dinshi masu amfani da mahimmaci a hannunta suke tana wandaka da dukiyarsa yanda taga dama.
Yanzu abin nata yayi gaba saboda boka ya bata sa'a har cikin gidan wasu samarin nata suke biyota a sunan yan uwanta dan haka gidan kullum a cike yake suna shagalinsu.
Fa'iza da shamsiya suma abin nasu yayi nisa dan suma kullum cikin kawo kawaye suke, su shige bangaren su,tare da saka key suyi abinda suka ga dama, cikin haka suka samu wata da ake kira Binta wacce jarabarsu tazo iri daya dana su fa'iza dan haka yawanci tana gidan su kwana tare su tafi makaranta tare.
Kaman kullum yauma Al'ameen ya dawo daga office ya tarar da latifa da salees da wani abokinshi suna hiran su hankali kwance a waiting palour.
Sallama yayi ya shigo, tashi Latifa tayi da saurita, ta taro shi tare da karban jakan hannunshi tana mishi sannu da dawowa ya amsa cikin sakin fuska,su salees ma suka gaishe shi ya amsa sannan suka wuce bangaren shi tare da ita.
Bayan ta taya shi cire kayan jikn shi ta hada masa ruwan wanka sannan ta fito tace"ruwanka na jiranka my Ameen "
Murmushi yayi ya mike zuwa bathroom.
Ganin haka tace"bari inje in had'a maka abincinka kafin ka fito ko?"
du
"duk yanda kikayi gimbiya dai daine".
Wuce